Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani farfar da idanunta kamar mai aljanu, Adam baisan sanda ya fara bibaga mata bayan ba.

Can ta saki wani nannauyan ajiyar zuciya, sannan ta rike hannunshi dake bubugawa.

A hankali ya zare hannunsa sannan ya mike tsaye yace "ya daina?"

Ta daga kai tace "nagode Yaya."

Shiru yai yana kallanta, tace "ya akai?"
"Bakomai" yace sannan ya mike da sauri yace "ki huta."
Nagode yaya ta fada tare da kara dagowa kirjinta ya kara bayyana.

Da sauri ya fita daga dakin, yana fita ya furzar da wani iska tare da ajiyar zuciya, shiru yai.

"Ya Adam ina asibiti ciwon baya nane ya tashi."

Shiru yai bayan ya tuno wannan kalmar, da sauri ya girgiza kai tare da komawa dakinsu.

Yana fita Sadiya ta kwanta sosai tare da yin dan tsaki, sannan ta kira saurayinta video call.


*************


A daidai station dinsu yai parking, kallanshi tai kafin ta fita tace "yamai jikin?"
"Da sauki"

Okay, kawai tace tai shiru dan so take taji ko an sallameshi tunda bai fada mata ba ta ina zata kara tambaya?

Harta bude kofa yace "yana asibiti, mungode sosai."

Juyowa tai ta kalleshi sannan tace "to."

Kayanta ta kwasa tai waje.

Tana shiga taga Ramlatu a bakin kofar office dinta, bata ce mata komai ba ta bude ta shiga, knocking tai sannan tadan tura kofar a tsorace.

Zainab na zaune tana duba abu a computer din dake gabanta, tea dinta ta kurba sannan ta kalli Ramlatu kadan.

Shigowa tai jiki a sanyeye tace "Na gama."

Zainab ta mata alama data ajiye ta fita ba tare da ta ce mata komai ba."

Jiki a sanyeye ta ajiye ta fita, waya ce ta shigo ta dauka, director ne yace "ya maganar daukan staffs din nan? Kinsan na fadamiki zamuyi transfer din wasu zuwa kaduna."

Tace "wannan karan ni zan dauki ma'aikata dakaina ranka ya dade, in kuma baka aminceba bazansa baki ba kowa ka kawo."

Haushi ne ya kamashi, dan dai duk wani hanyar samun kudi itace ta kawo musu idea din kuma ita ke wucewa gaba amma da tuni ya kori yar rainin hankalin nan.
Zainab cikin gadara tace "mekace?"
Dariya yasa yace shikenan ai yanda kikace hakan za'ai, tace "zan ware wadanda za'akai kaduna."

"Ha'a shima ke xakiyi? Wannan ki barshi ni xan ware dakaina."

Kamar zata ce a'a sai kuma tace "okay."
Ta kashe wayarta.

Aikinta ta cigaba dayi ta fito tana duduba programs, editing da sauransu.

Khalid dake zaune ne ya kalli wayarsa, fitowa yai ya nufi cafe, yana shiga ya duba aikin da aka turo, shiru yai yana tunanin yaje test din? Dan yasan koyaje ma ba samu zaiyi ba, sai dai kasan ransa na bashi yakimin ya sake gwadawa komai na Allah ne.


Wata babbar mota wacce kallo daya zaka mata kasan ta jika da kudi ne tai parking ata gefensa kadan, da sauri driver din ya zuge glass din mota yace "bawan Allah a aina gidan Tv din Muryar Arewa yake?"

Khalid yace gashi can, ya matso yana nuna musu, driver din yace dan Allah in ba damuwa ko zaka rakamu?"

Am sorry gaba zakai sai kai kwana zakaga sign dinsu.

Mungode.

Ya koma yaja motar.

Mutumin dake zaune a baya ne yai shiru, babban mutum ne, ya rasa meyasa kwanan nan mafarkinta kawai yakeyi, yana tunanin lalai lokacin da zai daidaita tsakaninsu yayi, koda bazata yarda dashi ba yana ganin dolene ya nemi yafiyarta, shiyasa ya nemi su Nabila su dawo dan yana tunanin ganinta, dan mafarkin dayai jiya ya tada mai hankalin sosai wanda yasa yau da dsssafe ya nufo garin na kano.

Sun isa suka tsaya driver din yace "a aika tazo?"

Yace "a'a kabarta ta fito naga sun kuds tashi."

Hango Khalid sukai ya nufo gun, cikin mamaki driver din yace "Ashe anan yake aiki."

Khalid ya wuce ba tare da yace musu komai ba, sai data gama tsara takardar Application na daukan ma'aikata da zasuyi sannan ta fito.

Tana fitowa ta nufi motarta ta shiga, tana rufe kofa driver din nan ya kwankwasa.

Kallansa tai cikin mamaki tace "Mamman?"

Da sauri ya gaisheta yana dariya, Khalid ya kalleshi ya dauke kai.

Mamman yace "Tare muke da Yallabai!"

Yallabai? Tai tambayar jinta banbarakwai.

Yace "eh yau haka kawai yace muzo yanasan magana dake."
Juyawa tai ta kalli motar, sannan tace "in aiki ne ya kawoku ku gams ku tafi Allah ya kiyaye hanya."

Ta rufe kofa tace "muje."

Khalid yaja mota cikin mamakin abinda ke faruwa, suna gaba suna binsu a baya, Khalid yace "koma wanene tunda ya taso yazo ki tsaya ku gaisa ma........"

Cikin fada tace "a matsayinka na wa?"

Mamaki ne ya kamashi ya juyo da sauri yace "me?"

Tace "amatsayinka nawa kake neman sani abu? Aikinka tuka mota kai abinda ya dameka, tunda shi kazo yi."

Wannan kalmar ba karamin batama Khalid rai tai ba, mutuncin abinda tamai ne yasa ya daure sai dai ya juyo ya mata wani kallo.

Tace "me? Dan mahaifina yazo ganina sai ya zama dole sai naje?"

Mahaifi? Abinda ya maimaita kenan, cikin bacin rai yai parking.

A zuciye ya bude mota ya fito ya bude kofar inda take zaune yai wani murmushin bakinciki, ya kauda kai yace "da na dauka nine ban fahimci kyawawan halayenki ba. Tuki nake?"

Ajiye key din hannunsa yai yace "gashi nan, sai ki nemi wani mai tuken, dan banaji zan iya tuka wacce batasan darajar mahaifinta ba."

Ranta ne yakai kololuwa gun baci fitowa tai ta tsaya tace mene?

Bai tanka mata ba sai gaban mota daya bude ya dau jakarsa, kudin aiki na danai zan turama Adam account number dina.

Da sauri tace "Dawo nan."

Kallanta yai rai a bace ya nufi motar dake gefe zai wuce wanda suma sukai parking.
Da sauri Dady ya fito ya tsaya gabansa yace "ya akai?"

Khalid yace "bakomai ina wuni?"

Dady ya amsa sannan yace "naga ka barta a hanya ne."

Kallansa khalid yai tare da yin kasa dakai, Dady cikin sanyin jiki yace "kayi hakuri dan Allah, da alama saboda ni ka ajiyeta, ka tsaya anan zan mata magana, amma dan Allah kar saboda ni ka ajiye aikinka."

Shiru Khalid yai jikinsa yai sanyi, haushin Zainab ya kara kamashi.

Dady yai murmushi yace "na mata laifi ne shiyasa take haka, karka damu."

Khalid yai shiru yana kallan Dady ya nufi motar.

Zainab na ganinshi ta shige cikin mota, zuciyarta cike da al'amari kala kala.

Bude bayan motar ta daya gefen da take zaune yai.

Kanta na jikin window bata juyoba.

Zainab!

Sunanta Dady ya kira wanda yasa idanunta yin rawa suna neman yin rauni.

Zainab!

Juyowa tai cikin fada kasa magana tai sai motsa baki kawai datake yi idanunta suka ciciko....


***************
Goggo ke zaune tana hada jaka, sai zuba kaya take kai kace wani gari zataje.

Sadiya dake gefenta a daki tace "ni goggo sati zakiyi acan ne?"

Sati kuma? Gobe zanje da safe in dawo da yamma sai kuma jibi muje dinner

Sadiya cikin dabara tace "ki kwana acan Goggo kinsan kwana da biki yafi komai dadi."

Goggo ta kalleta tace "da gaske?"
"Ku zauna kusha hira sannan ku shirya daga can kuje dinner kinga da daddare sai ki dawo."

Kallan mamaki Goggo ta mata tace " ke da bakya magana yau bayanin na menene?"

Sadiya tai kasa dakai tai shiru, Goggo ta kalleta tace "ni lalen da yan mata keyi manya bamayi ko?"

Sadiya a ranta tace wannan mata, amma a fili tace "sunayi amma sai dai jaa."

Goggo tace "to ni ina zani ma gidan lalai babba dani."

"Indai lale kikeso na iya sai dai ba sosai ba."

Cikin jin dadi Goggo tace "haba?"

Eh bandai iya sosai ba amma lokacin a gida ina yima Yayata.......
Ta kai karshen maganar cikin wani yanayi na damuwa.

Goggo ta kalleta tace "ya akai ta rasu ne?"

Da sauri Sadiya ta mike tace "Bari na shiga toilet."

Ta fito daga dakin.........


******
Ayusher🏌🏻‍♀
*****
[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

Page {20}


  Kallansa ta juyo tasakeyi, idanunta ne suka fara rawa, tausayinta ne ya kamashi yace "Zainab."

Idanunta ta runtse wasu zafaffan hawaye ne suka digo a kasan idanunta ta bude su tare da saukesu akan Dady tace "sai yanzu? Sai yanzu? Kasan sau nawa ina jira akan kazo ka fuskanci yarka kuyi magana?"

Kallan mamaki ya mata, yace "Zainab."

Shiru tai tare da juya kanta jikin window, yace "akoda yaushe ina tunanin samunki muyi magana sai dai ina tunanin karna kara taso miki da mikin da kika samu ya bushe.
Na sani ban kyauta ba na sani abinda nai abu ne na halayen dabobi, sai dai nayi nadamar hakan, bansan meya sameni a lokacin ba, hakan yasa itama wacce ta kawar da hankalina akan matata na bata nata kakkarfan hukuncin wanda har abada bazata sake ba wani shawarar yin abinda tamin ba."

Yanzu kam ta juyo ta kalleshi tace "matar da kuke zaune lafiya tana cikin daula har wani hukunci ka bata daya kai na sa Ummy cikin kunci?"

Shiru yai yana kallanta a ransa yace "na sa an tsaida haihuwa ta har abada sai dai ta zauna da 'ya daya, wannan shine hukuncin ta."
Amma a fili murmushi kawai yai tare da kallanta.

Zainab cikin takaici tace "Ummy harta rasu batasan wannan cin amanar daka mata ba."

Yai shiru jikinshi ya kara sanyi yace "na sani Zainab, ki yafemin abinda na muku."

Yanda ya fadi kalmar ne yasa ta dake tace "Sau nawa kasan ina jiranka a dakinmu akan kazo muyi magana? Sau nawa kasan 'yarka na cikin wani yanayi da take neman taimakon mahaifinta? Sau nawa kasan wannan marainiyar tana kin cin abinci saboda tana tunanin mahaifinta zaizo ya sata taci dole? Sau nawa nake dauke Nabila na shiga da ita daki dan kawai ina fatan Mahaifina zai nemi shigowa? Sau nawa.........."

Muryarta ce tai rauni saboda yanda ta tuno abubuwan datai tayi saboda tanaso Dady yazo gareta suyi magana, ko a skul aka bata mata rai inta shigo a gabanshi zatace bazataci abinci ba ta wuce daki saboda tana fatan ai tasan Dady zai shigo.

Baki ya bude yana kallanta tare da girgiza kai cikin tsananin tausayinta, kenan duk abinda take saboda ya dubeta takeyi?

Hannunta ya kamo yace "Zainab!" Cikin rauni yai maganar wanda kawai tasa kuka........

Shi kanshi hawaye yakeyi, yace "Kiyi hakuri Zainab, ni in naga kina haka tunani nake kawai bakya san zama inda nake ne."

Ta dago idanunta da sukai jaa, tace ko hakan ne a matsayinka na mahaifi bazaka tsawatarmin ba? Ka taba tunanin wannan 'yar taka da batada uwa tana bukatar mahaifinta?

Dady idanunta ne suka kara fitar da kwalla ta tsananin dana sani, yace "Zainab."

Shiru tai kafin tace "kasan dalilina na yin aiki a nesa?"

Kallanta yai da sauri, tace saboda duk yanda nasa rai da zaka tunkareni kaki, hakan yasa na nemi aiki a nesa nasan inkai rashina tabbas zaka neman, yau shekara nawa da aure?"

Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un abinda Dady ya fada kenan cikin tsananin nadama.

Hannunta ta zare sannan ta share hawayenta tace "sai yanzu? Dakayi zamanka da iyalanka da hankalin kowa yacigaba da kwanciya."

Shiru yai dan gaba daya zuciyarshi ta gama karaya baima san me zaice ba, a hankali yace "Kiyi hakuri Zainab bakiyi sa'ar mahaifi ba, me yasa baki sanar dani ba? Ke macece mai fadar ra'ayinki, meyasa baki nunamin ni kike jira a koda yaushe ba?

Shiru sukai kafin can harya dauka bazatai magana ba yaji tace "Ummy."

Kallanta yai yace "Zuwaira?"

Hawayenta ta maida tace "kafin Ummy ta rasu ta riko hannuna tace "Zainab ga kanwarki nan, sannan wannan abin da mahaifinki yakeyi karki sashi a ranki, ba halinsa bane kema kin sani, mutum ne dayafi sanki akan kowa a duniya, na tabbatar zai zo ya sanar dake hakan, kiyi hakuri ki cire komai sannan ni ban rikeshi ba na kuma yafemai."


Tana kaiwa nan tasa kuka tana cewa "Ummy ta dauka da wuri zaka sanar dani, me yasa kadau wannan lokacin?"

Kuka take sosai wanda gaba daya jin kalaman Ummy yasa kansa ya fara wani irin sarawa, shiru sukai a cikin motar ba wanda ya iya cewa komai.

Ganin halin da Dady ya shiga ne yasa Zainab ta kalleshi tace "Dady!"

Kallanta yai kamar baya hayyacinsa, bai iya cewa komai ba sai idanunsa da sukai wani irin jaaaa.

*********

Mamman ne ya kalli Khalid yace "Aiki kake ma Zainab?"
Eh kawai yace.
Mamman yai murmushi yace "da alama baka jin dadin aikin, ko da yake Zainab mai mata aiki sai ya shirya." Yai dariya yace "Allah sarki harna tuno lokacin da Mamanta ke darai, yarinya mai san mutane da fara'a ga saukin kai, komai aka mata batajin haushi ."

Kallansa Khalid yai cikin mamaki, Mamman yai dariya yace "baka yadda bako? Tun bayan rasuwar mahaifiyar ta ne ko? Ahh tun sanda Mai gida yai aure ne ta fara canzawa."

Khalid yai shiru yana tunani, Mamman yace "ahh sorry ina ta ma zuba baka sani ba."

Shiru yai bai tanka ba sai dai yayi shiru yana tunanin kalaman daya zabga mata, da alama akwai abinda ke tsakaninta da babanta.

*********

Sun dade a haka kafin Dady ya dawo hayyacinsa, murmushi yamata ganin yanda hankalinta ya tashi ganin halin a a shiga, yace "kije gida ki huta, zan dawo wani satin."

Tausayinshi ne ya darsu mata wanda tun bayan rasuwar mamanta yauce rana ta farko dataji haka, tace "Abuja zaka wuce?"

Yace "eh"

Kai ta daga alamar to, shiru yai kafin yace "tunda gobe asabar zan kwana a hotel in yaso gobe mu hadu."

Kallansa tai batace komai ba, wayarta ya dauka a gefensa yafara sa numbersa gani yai Dady ya fito a jiki, bai taba tunanin tanada numbersa ba, da sauri Zainab ta amshi wayar, Dady yace "zan kiraki gobe."

Kai ta daga a hankali, fitowa yai daga motar ta bishi da kallo, tana goge fuskarta.

Motarsa ya nufa, Mamman ya bude mai da sauri, Khalid ne ya gaisheshi, Dady cikin jin dadi ya dafashi yace "Nagode sosai, badan ka tsaida ita ba da bansan sanda zamu fahimci matsalar dake tsakanin mu ba."

Khalid yai kasa dakai, Dady yace "kayi hakuri ka cigaba da aikinka."

Khalid yace "Insha Allah."

Har ya fara tafiya Dady yace "Bawan Allah."
Khalid ya juyo, kudi ya zaro mai kauri dan a kalla zaikai dubu goma ya mika ma Khalid, da sauri Khalid yace "nagode amma ka bar kudinka, Allah ya saka da alkairi."

Khalid ya juya ya tafi, Dady ya binshi da kallo cikin gamsuwa da mamakin halayensa.

Khalid na zuwa ya tsaya a jikin kofarta, haryakai hannu zai yi knocking yaga ta sunkuyar da kanta da alama kuka takeyi, hannunsa ya sauke ba tare da ya kwankwasa ba, tadan dade tana kukanta kafin ta share hawayenta, ganin duhu yasa ta kalli jikin window, kofar ta tura, wanda hakan ya bige Khalid.

Juyowa yai da sauri jin an bugeshi, fuska ta hade tace "Oh sry ashe da mutum."

Tsayawa yai yana kallanta dan ya tabbatar da saninta."

Matsawa yai sannan yace "key din."

"Key? Kace in turoma albashinka account?"
Shiru yai baice komai ba, harararsa tai sannan ta dau key din ta cila gun zamansa.

Kallanta yai kamar zai sake magana sai kuma ya fasa, budewa yai ya shiga yaja suka tafi.

Tunda ya fara tafiya tasa kanta a jikin kofar batace komai ba, har ya isa gida.


Jakarsa ya dauka zai fita tace "gobe kazo wajen 2 zaka kaini wani gun."
Okay kawai yace ya fita, ita kuma ta shiga ciki.

Goggo ta gani zaune a falo tana kallo, gefenta kuma plate ne da akaci abinci, hannunta rike da lemo ta bare tana sha.
Sadiya na gurin kafafunta tana mata lale.
Sallama kawai tai tace "Goggo sannu da gida." Tai ciki
Sadiya tace da dawowa.

Baki Goggo ta saki tace "wannan 'ya kwai yar rainin wayau, in tsohuwarkice kya cemin sannu da gida ki tafi?"

Sadiya ce ta juya dan ta dauka da Zainab din take, ganin ba kowa agun yasa ta guntse dariyarta.

Goggo ta harareta tace "ki tabbatar kin gama abinda zakiyi littinin ki tarkata ki bar gidan nan dan wlh in tsautsayi yasa Zainab tasan bamuda hadi dake Allah ne kadai zai kwaceki dake da waccen sokon."

Sadiya dai batace komai ba, ana gama mata lale ta shiga dakin ta.

Wayarta ta dauko tace "Gobe zata tafi gun biki, bansan wannan matar ko zata zauna a gida ba, amma kai ka shigo da yamma, in kaga text dina, in baka gani ba karkazo, kadai rike abinda na ce ma kafada ko?"

Yana dariya yace "ba dole ba, amma ni wai haka zakiyi ta bari........."
Kashe wayarta tai tare da jan tsaki.

Zainab kam tana shiga daki tai sallar magrib ta kwanta akan gado tare da lulube bargo a kanta, shiru tai tana tunani.

Adam ne ya shigo wanda yaje aiken Goggo na siyo mata takalmi.
Yana shigowa ya ganta a baje a falo tasha dauren leda an mata lale.

Baki ya saki yace "Goggo? Meye hakan?"
Ta kifamai kallo tace "meye hakan kamar ya?"

Yace "wai ni Goggo meke damunki dan Allah, biki sai kace bikin 'yarki?"

Hade rai tai tace "kai bansan iskanci, kai kanka kasan ban taba zuwa bikin masu kudi ba sai wannan, na saba biki a kauye ba wani abin arziki, wannan kuwa da muka hadu da ita muka zama kawaye kai kasan yanayin gidansu ai, so kake naje a ganni daban?"

"Lalai Amma duk da hakan abin ai yai yawa."
Tace "abinda yai yawa ya wuce waccen kuliyar daka kawo mana, duk da yau na moreta amma nifa ka dauke 'yan nan, sam ni batamin ba wlh."

Yace "to ai litinin zata tafi."
Harara ta sake mai tace "dauke plate din nan kaban takalmin, matarka dan iskanci ko kallan arziki batamin ba yau."
Ke dai Goggo Allah neman maganarki yayi yawa, ta gaji ne.

Baki ta tabe ta fito da takalmin tana gani.

Adam ne ya kalli dakin da Sadiya take sannan ya wuce dakinsa.

Zainab na kwance cikin bargo ya shiga.

"Honey? Bacci?"
Ya fada yana lekata, idanunta ta rufe tana jin motsinsa.

Murmushi yai sannan ya sake fitowa ya zauna a falo.

*************

Abba ne cikin jin dadi ya kalli Khalid yace "an dawo?"
Eh Abba ya jikin?
Abba yai dariya yace "kana gani kasan Alhamdulila ai, ka mika mana godiyar mu dan Allah."

Umma tace "zan mata wainar gero ka kai mata, dansu masu kudi bansan me sukeso ba."

Wainar gero? Ya maimaita
Umma jiki a sanyaye tace bataci?
Da sauri yace "a'a kiyi sai na kaimata."
Cikin jin dadi tace "to."

********

Yau tun wajen karfw 9 Goggo tai wanka, ta saka doguwar rigar da aka mata, zama tai ta shafa mai tasa hoda da kwalli, jakarta ta zuge sannan ta dauko takalminta ya fito.

Sadiya dake kitchen tana gyarawa taji Goggo tace "ke zo dauran dan kwallin nan."

Sadiya ta taho da sauri, tace "Goggo kinyi kyau."

"Na sani ai, dauran ni."
Ta mika mata, zama tak a falo Sadiya ta daura mata, sannan tace ina Adam?
Banga ya fito ba Goggo.
Tsaki tai tace wannan uban sakalan hala yana can yana asarar.

Kwankwasa kofar dakin ta shiga yi.
Zainab dake zaune tana tura takardar daukan ma'aikata, ya mike.

Goggo ta kalla cikin mamaki, tace "Goggo irin wannan gayu?"
Kan Goggo ya sake fashewa tace "ina wannan lusarin? Yazo ya mikani dan Allah."

Zainab ta kalleshi wanda jin kwankwasawa ne ya sa ya bude ido, murmushi tai tace "bari yazo Goggo, ina kwana?"

Baki tadan tabe tace "sai yanzu?"

Zainab tai dan dariya tace "ban baki kudin gudun mawar bako?"

Da sauri Goggo ta washe baki tace "Eh wlh, ganin abubuwa sun miki yawa ne yasa na kasa tuna miki."

Zainab ta koma ciki ta dauko wallet dinta tace "nawa zaki bata?"

Yanda kika bada, sai dai a can zan kwana.
Mamaki ya kama Zainab sai dai batace komai ba, ganin ba kudi sosai a wallet din yasa tace "bari naba Honey sai ya ciro ki bata dubu ashirin sai ki rike dubu biyar saboda sha'ani.

Ai wani dadi Goggo taji tace "Kai Zainab Allah ya kara miki girma, ya miki albarka, wannan 'ya akwai sanin darajar mutum wlh, ni sai naga ma kamar kin dan canza ko bakya jin dadi ne?

Adam daya fito daga toilet ne ya guntse dariyarsa yace "gaskiya ne Hajiya Goggo taga bugun Abuja zata fara kodaki."

Fuska ta daure tace "kayi shiru anan ko kuwa????"

Sadiya dake tsaye tana jinsu ta tabe baki sannan ta fara tunanin, Zainab zata fita dai ko? In ba haka ba komai nata ya wargaje ai.


**********
Ayusher🏌🏻‍♀
**********
[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*


Page 21

Goggo ta gyara zaman mayafinta tace "ka fito ko sai ranka ya baci?"
Zainab ce ta fito ta maida kofar dakin tace "bari ya shirya Goggo.

Washe baki ya sakeyi tace "Tunda dai ke kikai magana bari na jirashi."

Kallan takalmin kafarta tai mai irin dan dunduniyar nan ne tace "Goggo zaki iya tafiya da takalmin nan dai ko?"

Haushi ya kama Goggo a ranta tace "tunda ba tsohuwar ki bace dole ki yaban magana, amma a fili dariya tai tace "ba matsala zan iya."

Zainab ta kalli dinkin dake jikinta kai kace dinki yan mata, rigace doguwa amma anmata ado da design da ake yayi, da alama ita tasa mai dinki yi mata irin na 'yan mata.
Goggo ta kalli Sadiya dake tsaye a jikin kitchen, tace "ni hadomin shayi nasha kafin ya gama kalular tasa."
Ta wuce ta zauna akan kujera.
Zainab ta koma cikin daki tana guntse dariyarta.

Tana shiga tasa dariya, Adam da ya sa vest ne ya kalleta yace "Honey ke da Goggo ne ko?"
Da sauri tace "ya akai ka sani?"

Dariya yai shima yace "ke abinda ke saki dariya ai yanada wuya, yau kuwa tunda naga Goggo nasan sai ta saki dariya."

Zainab ta karasa dariyarta tace "kai ni Allah yasa kar 'yan gun bikin su mata dariya."

Adam yace "ah to ita ta sani, amma honey dubu ashirin da kikace a bata na gudun mawa, ai goma ma tayi."

Hade fuska tai tana kallanshi tace "ka cinye kudinka kenan?"

Yace "ban cinye ba."

Tace "ka bata hakan takai, kaga dai yanda suke da uwar amaryar."
Shiru yai yana gyara fuskarsa, tace "nasan tunda ka furta Allah sai ka rage, zan turoma 10k, nima ba kudi a account din.

Wani irin dadi ne ya kamashi ya matso ya fara sumbatarta a fuska ta ko ina.
Kafin ya juya ya fita.

Murmushi ta bishi dashi sannan tai shiru tana tunanin mahaifinta.
Wayarta ta jawo ta duba, ganin bai mata text ba yasa ta ajiye tare da yin ajiyar zuciya.
Laptop dinta ta kara jawowa ta shiga aikinta.

*********

Adam na fitowa Goggo ta bishi da harara tace "kaga dama?"
Yace "inkin gama tashi in kaiki."

Cup din ta mikawa Sadiya sannan tai waje, takai jikin kofa takalmin ya dan gurde kadan, waskewa tai tai saurin fita.

Sai da ya bata kudin duka ta sa a jaka sannan suka nufi gidan biki

********

Wajen karfe 11 wayarta tai karan text da sauri ta dauko wayar, ganin sunan restaurant din da zasu hadu da karfe 3 yasa ta saki murmushi, grand central hotel ya sauka kenan.

Kallan wayarta tai sannan ta cigaba da aikinta, sai 12 ta fito.
Kitchen ta shiga taga komai a gyare, murmushi tai saboda tasan Sadiya ce, nan ta fara yin abinci.
Sadiya dake daki a kwance tana waya ne taji kamshin abinci, yau kuma? Badai ba fita zatai ba?

Shiru tai tana tunani kafin ta dan mike ta fito.
Zainab na kitchen tana ta aiki ta shigo.
"Aunty aiki kike baki kirani ba?"

Zainab ta kalleta tace "wannan ma da kikai ya isa kije ki huta."

Cikin dabara tace "fita zakiyi ne Aunty? Naga ko abincin safe bakici ba."

Zainab tace "eh wlh zan fita anjima kadan shi yasa."

Dadi ne ya kama Sadiya wanda har batasan fuskarta ta bayyana hakan ba.
Sai ji tai Zainab tace " zakiyi wani abin ne?"
Gabanta ne ya fadi, ta kalleta da sauri tace "a'a"
Tana fada ta wuce ta fara yanka albasar da Zainab ta fito dashi.

*********

Umma ta kammala sa wainar a flask sannan ta amshi kulin da Asiya ta daka ta zuba sannan ta rufe.

Asiya ta kalla taci " kinci? Komai yaji?"
Dariya tai tace "Umma komai yaji sau nawa za'ai dandanen nan?"

"To sai me za'a hada mata dashi?"
Bansani ba wlh sai dai ko mu tambayi Yaya me takeso.
Shigowarshi ce tasa suka kalleshi a tare, Khalid ya karaso sannan

Please Login or Register in order to submit comment