Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka hadu, kallanta yai, itama kallansa tai sannan tai kasa dakai tare da dauke hannunta.

Dagowa yai ya mika mata wayar, ta amsa tace “nagode yaya.”

Jeki inkin gama ki kirani.
Tace “nagode.”

Fitowa tai ya juya ya tafi.

Sai da motar ta kure sannan na kalli fuskarta, a hankali naga wani murmushi wanda ya fito daga gefen bakinta, ya sunan murmushin nan? Me yake nufi? Wa tayiwa? Abinda ya ziyarci kaina kenan ganin salaha Sadiya dauke da wannan murmushi yasa naji kaina ya juya........

*********Ayusher*******
[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Association💡

Shafi na Goma Sha Biyar

Wattpad/@AyusherMohd.

*Ayusher Muhd*


Juyawa tai hankalinta a kwance ta shiga makarantar, hannu tasa a jakarta ta dauko wayarta wacce na gani daga mai touch ta koma iphone, baki ma sake ina kallan ikon Allah, number ta danna sannan ta fara waya.
Kana ina?
Kazo ina jiranka a northwest.
Tana kai nan ta kashe wayarta, maimakon ta shiga ciki wucewa tai gefen inda motoci suke ajiye tana dadana waya, batai minti goma ba sai ga wata mota nan mai masifar kyau ta karaso, budewa tai ta shiga sannan yaja suka bargun.
Kallansa tai bayan sun fara tafiya tace "ina abin?"
Nan yasa hannu gefen kujerarsa ya ciro wasu takardu ya mika mata.
Amsa tai tana dubawa sannan tai tsaki sannan tace "tsaya."
Nan ya ja gefen titi ya tsaya, kallanta yai cikin kaguwa yace "Booboo na muje hotel din plz, am in a hurry...." ya fada yana daure hannunsa akan cinyarta.
Doke hannun tai tace "sai yaushe zance ma ka barni na gama abinda yafi komai mahimmanci a rayuwata?"

Kallanta yai jiki a sanyaye yace "kiyi hakuri, amma ya abinda kikeyi?"

"Haushi yasa ma abin baya birgeni, I didn't expect him to be that easy."

Ta kalleshi sannan tasa hannunta a saman goshita ts kwantar da kanta kan kujera, wani kwafa ta saki wanda ya sashi shan jinin jikinsa yace "muje?"
Tace "kaini naci abinci dazu na kasa ci saboda wannan yar iskar yarinyar."

Yace "wacce?"
Tace "Nabila take ko wa? I hate that girl."

Murmushi yai yace "me kikesanci?"

"Kaini Cilantro Restaurant."
Yace okay.

********************

  Zainab ce ta shiga cikin gida bude kofar falo tai, wanda yasa su kallan kofar.
Zainab ce ta shigo a tare sukace Aunty?
Zainab ta kallesu tace "wannan kiran fa? Bakuso dawowa ta bane ko laifi kukamin?"

Dariya Nabila tai tace "munji ba alamar karar gate ne bare na mota."

Da gudu Nabila ta tashi ta bude kofa, ganin ba mota yasa ta juyo da sauri tace "Aunty harya tafi?" Ta fada kamar zatai kuka.
Zainab tace "eh ya wuce yanada abinyi."

Zama tai a kasa dabas kawai ta sa kuka, Zainab cikin mamaki tace "menene?"
Nabila ta girgiza kai tace " malama dan jeki waje kiyi kukan asarar ki, mu dan Allah karki cika mana kunne."
Haushi ya kamata ta taso ta nufo kan Nabila, da gudu Nabila ta mike tai bayan Zainab wacce ta shiga tsakiyar falan.

Zainab ta kalli Nusaiba tace "Nusaiba menene kuma?"

Nabila tana dariya tace " saboda wanda take dakon sanshi baisan tanayi ba, ya tafi batamai sallama ba."

Zainab ta kalli Nusaiba wacce ke kokarin jawo Nabila.
Tace "wai dama da gaske kike? Lalai."
Ta kalli Goggo wacce ke kallansu tana cin cincin."

Nusaiba ta kalla tace "Nusaiba kin wuce kin zauna ko kuwa? Ke kuma in sake jin bakinki."
Ta fada tana kallan Nabila.
Wucewa tai ta zauna, Nabila tai kitchen, Zainab ce ta kalli Goggo tace "Goggo an tashi lfy?"
"Lafiya kalau, sun tafi makarantar."

Zainab tace "oh nama dan sha'afa."
Ta fada tare da wucewa daki, tana bude kofar dakin tace "Nabila."
Nabila data sha ruwa ta taho da sauri ta bita dakin.

Zainab na zaune a bakin gado ta shiga.
Zama tai kusa da ita tace "Aunty!"
Zainab ta juyo gaba daya ta kalleta yanayin fuskarta ne ya canzs zuwa tausayi, Nabila tace "Aunty daina, daina kallo na haka."

Zainab ta kamo hannunta sannan tadanyi murmushi tace "Nabila nagode."

Idanunta ne suka ciko amma fuskarta na kokarin bayyana murmushi tace "karki damu Aunty kedai kiyi kokari ki cigaba da zama cikin farinciki, shikedai ne abinda nake nema kuma na tabbatar Mama da tanada rai abinda zata nema kenan."

Zainab ce tai murmushi tace "sai kace kece babba."
Nabila tai dariya tace "in na nuna miki na girma sai hankalinki yafi kwanciya."

Zainab ta jawota ta rungumeta tace "in wani abu ya faru ki kirani kinji?"

Nabila ta goge kwallarta tace "To Aunty."
Zainab ta dagota tace "Dady fa? Yana nuna miki banbanci?"
Kai ta girgiza tace "bansa a kaina ba bare na gani."
Zainab tai dan ajiyar zuciya tace "in an kusa visiting kimin magana zanzo muku."

"Kin tabbatar? Kinsan zaku hadu da Dady da maman Nusaiba?"
Wannan damuwarsu ce insun gani sa tafi, inata kin zuwa miki saboda banasan kisan meke faruwa amma tunda kinsani banga abinda zai hanani ganinki ba."

Nabila tai dariya tace "Shikenan zan kiraki."

Jakarta ta zuge ta dauko kudi, mika mata tai dubu goma tace ke biyar Nusaiba biyar, Nabila ta amsa tace "mungode."
Zainab tace "in kara miki?"

Nabila tace "a'a abubuwa sun miki yawa, Aunty wai haka zaki cigaba da zama komai kece keyi?"

Murmushi tai tace "yana neman aiki, sannan banajin wani abin dan nayi komai, na tabbatar saboda hallarcin danamai bazai taba cin amana ta ba kamar wani wanda baisan hallacci ba."

Nabila ta sake dariya tace "dukda bansani ba nasan da Dady kike, wai dan Allah meya faru takamaimai."

Zainab ta mike tace " zan fada miki amma ba yanzu ba."

Nabila tadan turo baki tace "shikenan."

Dariya Zainab tai tace "borin ya motsa ne?

Nabila tai dariya itama tace "Aunty Allah ki dinga rufe kitchen dinki lamarin ciye ciyen goggo yayi yawa, ke kina can kina aiki danta na tsinanen bacci da jin dadi ita kuma sai ci da tsinanen kallo."

Zainab ta dan bige kanta kadan tace "wayace miki ana maganar manya haka? Kuma mamar Adam kamar mahaifiyata take."

Nabila tadan tabe baki.

Zainab ce ta mike ta bude drawer dinta, agamfa ta dako irindaya guda biyu da mayafinsu, tace gashi, sannan ta dauko jaka guda biyu suma iri daya.

Nabila tace "yaushe kika siya?"
Dariya tadanyi tace "duk sanda na samu naje siyayya ina siyowa saboda nasan zakuzo."

Nabila cikin jin dadi tace mungode.
Da gudu ta bude kofa tana kiran Nusaiba, man Nusaiba ta zo sukaga kaya suka hau murna.......


Adam kam tun bayan daya ajiyeta jikinsa a sanyaye ya dawo gida, shikansa baisan meya sameshi ba.

********


Gudu yake harya isa Danbatta, yana zuwa ya tada Abba a kwance akan gado a Er amma ba kowa a gunsa sai wata nurse, hankalin Khalid a tashe ya nemi number nan ya kira, Sabir ya dauka ya sanar dashi Zee ce ta bashi number din.
Nan ya ce gashinan zuwa, Umma kuka kawai takeyi, Asiya ma haka, shikam Abba gaba daya da alama baisan waye a kanshi ba sosai, sai jini dake zuba a ta kasan inda akamai aikin, Sabir na zuwa ya sallamesu waje, nan ya fara aikinsa na ganin ya daidaita abinda ke faruwa.

Shikam Khalid na zaune kusa da Umma, Asiya na gefensa.

Salmanu ne yace “bari naje na dawo Khalid.”

Khalid ya mike yace nagode Salmanu.
Nan ya wuce, Umma ce ta kalleshi tace “a ina ka sanshi?”
Yace “wacce nakewa aiki ne taban numbersa ta sanshi ne.”

Umma tace “amma mungode mata da alama mutumiyar arziki ce, Allah ya biyata.”

Khalid yai murmushi a kasan ransa yace “da alama kam.”

Sun dade kafin Dr Sabir ya fito, sanar dasu yai ba matsala sai dai ya samu barci abashi ya huta.”

*********

Shigowa Adam yai Gogo ce kadai a falan tana ta cin cincin dinta, Adam ya kalleta ya zauna a kusa da ita, kallansa tai tace “Sallamar kenan?”

Yace “nayi kina ta kallo ina zakiji.”
Harara ta maka mai tace “kai ka sani, ka kaitan?”
Yace “eh sai ta gama zata kirani.”

“Zadai ta gama yau ta kama gabanta ko?”

“Eh gobe zata tafi.”
Tace “ah to dan ni bansan bikin nan ya tashi tana gidan nan.”
Meyasa?
Tace “tambaya kake? Wayasan me zata sata in ba kowa a gidan? Ita waccen tana aiki, ni ina hidimar biki kai kuma kana can kana uban bacci.”

Dariya yai yace “Goggo kenan.”
Karar shigowar mota sukaji yace “Zainab ce?”
Tace “ita tana daki da yara sai dai mai daukan nasu ne kila.”

Adam ya leka yace “oh shine kuwa.”

Nan ya wuce daki ya sanar dash.

Kayan suka nunamai ya tayasu murna sannan suka fita dan kara shiryawa.
Zainab ta kalleshi, karasowa yai ya rungumeta tsam a jikinsa.
Murmushi tai tace “Honey.”
Yace “Ina sanki Honey harbansan yawan adadinsa ba, nagode da kasancewarki cikin rayuwata.”

Murmushi tai ta dago ta sumbaceshi tace “nima nagode da shigowarka cikin rayuwata.”

Tare suka fito, Zainab tai kitchen, gani tai anyi abinci, murmushi tai ta deba ta zuba ma wanda zai kaisu sannan ta kira Nusaiba ta mikamai, itama ta zuba kadan taci.

Nan su Nabila sukai sallama, suka shiga mota.

Nabila tace “Goggo asha biki lafiya.”
Goggo tai dariya tace “to, kuma kusha makafanta lfy.”

Nan suka kara sallama suka tafi tare da fatan Allah ya saukesu lafiya.

Zainab ta bisu da kallo kafin tace “Honey ajiyeni a office.”
Yace to.
Nan ta shiga suka tafi...........

*******AYUSHER MUHD*********
[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

Shafi na Sha Shida

A hayarsu ne yana tafe sundanyi shiru, kallanta yai yace "Yau Honey ba bacci sosai."
Kallansa tai tace "yanzu na daina ai, waccen zuwan nasu kaga na damu?"
Murmushi yai sannan yace " Dadyn fa? Haryanzu bakwa ko waya?"
Yanayin fuskarta ne ya canza ta juya kanta zuwa jikin window.
Dariya yai yace "sorry Honey bansan ya akai zancen nan ya fito daga bakina ba."

Bata tankamai ba har ya kara cewa "Honey ina Kwaro yaje ne?"
Kallansa tai fuskarta haryanzu ba a sake ba tace "yaje wani guri ne." Ta rasa meyasa ta samu kanta dakin fadamai babanshi ne baida lafiya."
Kafin yace wani abu tace "Sadiya fa?"
Kallanta yai da sauri, tace "menene? Da matsala ne?"
"A'a tana makaranta inta gama zata kirani."
To kawai tace tai shiru, suna zuwa ta sauka ta shiga shiru yai yana kallanta harta shiga ciki.

Office din editing ta fara shiga ta duduba ta wuce office dinta.
Shiru tai akan kujera tana kallan takardun da zata duba, waya ta dauka ta kira ciki, kace tazo.
Nan ta ajiye wayar, Ramlah ce ta kwankwasa, Zainab ta bata izini ta shigo.

A tsorace ta gaisheta, Zainab ta kalleta tace "ina report din danace ki kawon?"
Ramlatu tace "Am sorry yanzu nake karasa editing."

Wani wulakantacen kallo ta mata tace "yanzu kike me?"

Yawo ta hadiya ta kalleta tace "banida lafiya........"
Bakida lafiya?
A tsorace ta daga kai, Zainab ta dau wayarta ta kira director sannan tasa wayar a handsfree tace "Sir wannan wacce bansan ta yanda akai ta samu aiki anan ba."
Daga can cikin rawar jiki yace "Ramlah?"
Tace koma wa sunanta bai damenba sai dai kai da ka kawota inaso ka sanar da ita wannan shine dama na karshe da zan bata, idan harna kara bata aiki batamin zata taradda takardar kora a saman kafarta."

Director ya canza yanayin maganarss yace "Yahkuri Zainab, ni kaina bansan amfaninta ba, kiyi hakuri zan ja mata kunne."
Bata bashi amsa ba ta kashe wayarta, kallanta ti tace "dafatan kinji?"

Ramlatu wace ranta ya gama baci da yanda Director ya wulakantata yasa ta saukar da kanta kasa, Zainab tace "banida damuwa da duk iskancin da zakiyi, am i your mother? Ko nice babanki? Banida hadi dake rayuwarki ce sai dai inzakiyi iskancinki kije kiyi a hotel amma nan gun aiki ne, idan baki kawon report din nan in an hour ba bansan me zai biyo baya ba, Get out."
Ta nuna mata hanyar kofa, Ramlatu tana hawaye ta fita, tana fita ta shige toilet tasa kuka.

Zainab kam tana fita taja tsaki, ranta ya kara baci, wani abu ta hadiya na bakin ciki, maimakon ta duba takardun dake gabanta kwantar da kanta tai tare da rufe idanunta.

Mahaifiyarta ta hango kwance a kasan tiles, ga jini a malale ta kasanta, ita kadai a gida babu kowa, hawayene suka gangaro ta gefen idanunta wanda batabi ta kansu ba, hangota tai a rikice tana kuks ta rasa ta yanda zata taimaki Ummynta, kusa da ita kawai taje tana kuka tare da rike hannunta.
Kuka take sosai, a hankali Ummy tace "Uwata ki dsu wayata ki kira Kamisu driver."

Kalan cikinta wanda taketa murna zata samu kani ko kanwa tai, a tsorace tace "Ummy! Ummy....."
Jinin dake zuba ta kalla da sauri taja wani wahalalen numfashi sannan ta bude idanunta tana hakki.

Bakinta ta shiga motsawa tana kokarin maida kukan dake neman kwance mata ta shiga kokarin yi, da sauri ta jawo takardun dake gabanta ta fara dubawa.

Wayarta ta daga ta kira Sabir, daga can ya amsa yace "Zee!"
Tace "ya? Ya kiraka?"
Eh tun dazu harna gama na dawo office dina, hatsari yai ne?"
I don't know.
Yace "okay, amma meye hadinki dashi? Shine mijin naki?"
Dan karamin tsaki tai tace "kaifa matsalata dakai tambayar abinda baishafeka ba, nagode."
Bata jira mai zaice ba ta kashe wayarta.

Harkarta ta cigaba dayi, sai dai kasan ranta a ciki yake da tausayin mahaifiyarta da kuma tsanar mahaifinta.

•************

Sai yamma lis sannan ta koma northwest ta naka ma Adam kira, yana zaune a majalisa ana hira yaji wayarsa tai kara, mikewa yai da sauri ya matsa sukasa mai dariya Yaran Hajiya ya amsa kira.

Adam yace "kingama?"
"Eh yaya nagama."
Okay bari na taho.
Ya kashe wayar ya musu sallama, da sauri ya fada motarsa ya shiga y nufi makarantar.
Tana bakin inda ya ajiyeta, yana yin parking ta shiga ta zauna, juya kan motar yai suka fara tafiya ba tare da kowa yayi magana ba, can sai da suka danyi nisa tace "Yaya nagode sosai."
Ya kalleta yace "bakomai, kingama ko?"

Tai shiru tare da yin kasa dakai, kallanta ya sakeyi yace "baki gama ba?"
Kai ta daga alamar eh tace "bangama ba yaya, kayi hakuri."
Dariya yadanyi kadan yace "hakurin me? Ki zauna ki karasa a hankali, gobe zaki koma kenan?"
Tace "gobe Friday kuma ko naje ba zan iya gamawa in bazan takurama ba inasan in bari sai Monday."

Adam ya kalleta, kasa tai dakai tace "yaya kayi hakuri."
Da sauri yace "bakomai, kizauna sai monday din."

Shiru suka danyi kafin tace "Yaya kayi hakuri akwai lokutan da zakaga ina abubuwan da basu dace ba dan Allah inkaga haka kayi hakuri kamar yanda nacema rannan inada larura ne wlh wanda nikaina bana sanin abinda na aikata."

Kallan ta yai har yadansa tari yace "aljanu?"

Dariya tai jin yanda yai maganar, tace "a'a ni kaina bansan menene ba, saboda hakan ansha min duka."

Duka? Ya tambaya tare da dan kallanta.
Tana wasa da hannunta tace "eh yaya, kayi hakuri."
Idanunta ne suka ciciko jiyai tausayinta ya kara kamashi, yace "ya isa hakanan bansan yawan kukan nan."

Share hawayenta tai da sauri tace "nadaina, duk abinda bakaso bazan sake yi ba." Tai maganar tana girgiza.
Murmushi ne ya bayyana a fuskarsa yace "to."
Wani dadine ya kamashi a kasan ransa, yau gashi shine yake bada umarni ya saba a komai sai dai shi a bashi.


********
Ganin jikin Abba ya dawo daidai yasa Khalid ya fito yai ma Umma sallama akan sai ya dawo, kallanta yai yace "zan tambaya in za'a iya biyana da wuri inyaso sai na baki saboda yin abinci ga yan kananan kudadanen da ake amfani dasu a asibitin."

Tace "To khaleed, sannu Allah ubangiji ya daukaka ka, ya baka damar da zaka taimakemu."
Yace Ameen.
Asiya ya kalla yace "in na dawo Umma zata koma gida dan haka kije gidansu Salmanu, kafin nan, ko kuma ni nace yazo ya zauna a dakina kafin na dawo."

Umma tace "yazo din yafi sauki sauki."
Yace to, sai na dawo.

Fitowa yai ya dau hanya, bai tabajin dadin aikinsa ba irin yau, a da ya dauki aikin ne akan rashin abinyi, sai dai taimakon data mai yau tabbas yass ya kara girmamata a idansa, haushi ne yadan kamashi da ya tuns ba yanda zaiyi ya kama wannan mutumin.

Haka ya isa station din har lokacin fitowarta yai.
Zainab na fitowa ta hango motarta, karasawa tai ta shiga tare da ajiye kayan dake hannunta.

Khalid ba tare da ya juyo ba ya dan kalleta ta madubi kadan, gaba daya yanayin damuwa ne karara a fuskarta, daurewa yai yace "Nagode sosai da sosai."
Kallansa tai tadanyi murmushin yake tace "is okay."

Shiru yadanyi kafin yace "jikin nashi da sauki."
I know, abinda tace kenan ba tare da dogon nazari ba.
Khalid yace "kin sani?"
Shiru tai cikin waskewa tace "tunda kaje asibiti i will assume that."
Oh yace sannan ya tada motar, shiru tai ta zubawa window ido, yauce rana ta farko dayaga bata aiki a cikin mota, da alama an bata mata raine, ko mutumin nan ne? Abinda ya fado mai kenan, shiru yai yana tunanin yanda zaiyi ya tambayeta, daurewa yai yace "wannan ya sake kira?"

"Wa?"
Daga yanayin tambayarta ya fahimci baisake ba, shikenan.
Jin yace haka yasa ta fahimci yanayin da take, juyawa tai ta dau tab dinta tana dubawa duk da dai ba wani abu take ba amma batasan ya fahimci tana wani halin.

Yana sauketa ta wuce ciki, Goggo na zaune a falo tana waya da alama wannan bikin daya ishemu shi take magana akai, wanda mu kanmu mun kosa asabar tayi wato jibi a gama bikin nan mu huta.

Zainab bata tsaya a falo ba wucewa kawai ciki tai, Goggo ta bita da kallo, Sadiya dake daki a kwance ma batasan ta dawo ba.

Adam ta gani kishingide yana kallo a laptop dinta, yana ganinta ya taso da sauri yace "Honeyyy...."
Ya bude hannayensa alamar rungumeta, hannun tadan ture ta wuce toilet, tana fitowa ta ganshi a inda ta barshi ya shagwabe yace "Honeyyyy...." ya kara bude hannu.

Murmushi tai sannan ta shiga jikinsa ya rungumeta, dagowa tai ta kalleshi sannan ta canza kayanta, yace "Honney su Nabila sun isa?"
Ta kalleshi tace a'a kawai, fitowa falo tai ta nufi kitchen.

Sadiya wacce ta fito dan cin abinci itama suka hadu da Zainab, Kallanta Zainab tai cikin mamakin ganin kayanta a jikinta.
Sadiya ce ta kalleta tace "Aunty menene?"
Zainab tace bakomai, flask din ta rufe ba tare da ta zuba abincin ba, Sadiya ta fahimci me ta gani hakan yasa yace "Aunty nagode Yaya ya ban kaya inji ki."

Zainab ta kalleta kawai tai murmushi ta wuce ciki.

Goggo ta bita da harara tace uwar mijinki na zaune amma ko gaisheta da gida bazakiyi ba, in dazu kin shigo ina waya yanzu fa.

Zainab na shiga ta kalli Adam tace "yaushe ka ba Sadiya kayana ban sani ba?"

Kallanta yai da sauri yace "Honey dama naga zata skul ne batada abinda zata saka shiyasa."
Meyesa baka fadamin ba to? Kafi kowa sanin bazan hana kanwarka abu ba amma at least nasan meke faruwa."

Adam ya jawo hannunta yace "Am sorry Honey, gani nai da abuna da naki dayane."

Shiru tai kafin tace "meyasa in ina cikin wani hali baka taba ganewa harsai na fadama?"

Cikin mamaki yace "'menene?"

Kallansa tai tace "baka kula da yanayi na ba tunda na dawo?"

Murmushi yai yace "ai kin saba wani sa'in haka kike shigowa a gajiye, zo kiga na nuna miki nawa mukaci a ball din da akai yau."

Baki ta bude kamar zatai magana sai ta fasa.

Fitowa tai ta wuce dakinsu Nabila ta rufe, zama tai a kasan carpet ta sa kanta akan cinyoyinta.......

Goggo ta girgiza kai a kufule, Sadiya ce ta kalli Goggo tace "Aunty bata kula damu bane hala."

Goggo tace "ina fa tsabar iya iskanci ne." Taja tsaki.

Zainab tai shiru.....
Abinda ya faru a shekarun baya ne suka dawo mata................


*******
[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

Inalilahi wa ina ilaihi Raji’un yanzu abinda na rubuta jiya wata tacemin irin abinda ya faru da kanwar babanta kenan, Ya Salam, mace sai tai amfani da danka ta cuceka, dan Allah mata mu gyara halayenmu, bawai dan kinasan auran namiji sai kin shiga jikin matarsa kin cutar dasu ba, mata mu yima kanmu fada dan Allah, dama namiji ansanshi da sankai da kuma tunanin ya isa da kuma yanada dama, amma mata mu dinga duba rayuwar ‘ya’yan mu, in har mu munci riba in aka ci riba akan namu ‘ya’yan ya zamuji?

Allah ya sa mu gane Ameen, jin kalaman yarinyar nan ya tadamin hankali, domin su a wannan lokacin kanwar baban nata na nan, abinda ta haifa ya koma ita kuma auren daga baya iyaye rabawa sukai.

Allah ya karemu daga sharrin Zuciya.....
Ameen.
[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     ......................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

*Shafi na Sha Bakwai*


Asalin Labari.......

Zuwaira Muhammad Kabo shine sunan mahaifiyar Zainab, mahaifanta yan garin Kabo ne sai dai aiki ya daukeshi ya kaishi garin Gombe inda ya tare da iyalansa.

Yaransa guda shida, biyu mata uku maza, Zuwaira itace yar fari a gidansu, Zuwaira yarinyace wacce ta taso mai sanyi dan ko kananta neman raina ta sukeyi saboda sanyinta, kaninta mai bi mata a duk sanda aka mata abu shine yake zakewa ya amshi fadan, ko a gidansu bata taba neman kananta suyi aiki, harsai mamanta haushi ya kamata ta sa su yi da kansu.
Alhaji Muhammad Kabo ba mai tulin wadara bane sai dai Allah ya bashi rufin asiri inda yake zaune cikin gidansa hankalinsu a kwance.

A lokacin da Zuwaira ta gama secondary ta fara neman makarantar gaba da secondary Allah ya hadata da Aliyu wanda ya ganta a hanya, da farko bata amince dashi ba saboda tsananin shiru shiru da hakurinta, sai dai ganin yanda yake tsananin santa ne yasa hartake dan tankawa.

Soyayya mai karfi ce ta shiga tsaninsu wanda duk rashin magana irin na Zuwaira sai da kowa ya fahimci tsananin san da takemai.
Haka aka hakura da neman karatunta akan intai aure ta cigaba.
Aliyu yana aiki ne agarin Kaduna inda yake aiki a harkar wuta, wato NEPA, iyayensa yan garin Gombe ne, Aliyu nada babban family sai dai irin zuri'ar nan ne da ba ruwan wani da wani, saboda matan gidansu hudu, kowa da 'ya'yansa, kowa nada san kansa a haka suka taso, kowa baisan taimakan dan uwansa, gashi shima mahaifin bai damu dasu ba sabods yawansu.

Ansa bikin Zuwaira da Aliyu, anyi biki lafiya ta tare a gidanta daya kama haya a garin kaduna.
Zama mai tsafta sukai a tsakaninsu, duk da Aliyu nada saurin fishi da fada sai dai sanyin Zuwaira da hakurinta yasa Zamansu yin tasiri, domin ko ba ita tai abu ba inya fara fada hakuri take bashi, wanda hakan yake sawa dole yai hakuri.

Zuwaira shekararta daya ta haifi danta namiji, sai dai kafin suna Allah ya dauki abinci, ta sake samun ciki a lokacin tana shekara ta biyu da aure, sai dai kafin cikin yai girma ya bare.
Wannan lamari ya tada hankulansu, anyi ta dirka mata magunguna na gargaji tayi tayin na asibiti dan sai datai bari uku Allah ya bata haihuwar Zainab, Zainab ta kasance yarinyar da aka samu dakyar wannan dalili yasa Zuwaira da Aliyu suka dauki san duniya suka sa mata.

Sati biyu da haihuwar Zainab aka karama Aliyu matsayi sannan aka mai transfer zuwa Abuja.
Wannan kamari ya kara musu dadi, farinciki haryana neman yi musu yawa.
Sun koma garin Abuja cikin ni'ima da daukaka, abin al'ajabi shine tunda suka koma Abuja matsayin Aliyu ke karuwa, tun suna gida mai daki biyu suka sai gida makeke mai hawa biyu.

Aliyu na tsananin jin dadin wannan rayuwa da suka tsinci kansu a ciki, sai dai Zuwaira a hankali damuwa ta fara mamayeta ganin har yanzu ko bari bata sake ba ga Zainab har ta shiga primary.

Tunda Zuwaira tazo garin Abuja batada takaimai mai kawa saboda ita dama bamai shige shige bace.
Kamar yadda ta saba in Zainab ta tafi makaranta tagama gyaran gida sai ta daura abinci, tanayi tana dan kallanta ko kuma tana jin radio, wannan rana haka tana girki gefenta dan radio ne tanajin labarai, ganin abincin ya kamalu ne yasa ta kashe miyar sannan ta kwashe shinkafar.
Tana cikin hada cucumber salad wanda aka gama koyawa yanzu a radio taji motsin mota, murmushi tai dan tasan an dawo da Zainab kenan.
Zainab ce ta shigo da gudu har tana neman faduwa, da sauri Zuwaira ta dagata tace "yar gidan Ummy karkije ki fadi."

Cikin tsananin

Please Login or Register in order to submit comment