Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baici ace taje gidan matarsa daukan fansa ba, to yayar ma ta rasu? Garin ya?

Ganin ya kasa gani komai ga haushin baije test din ba kawai yasashi ya juyo dan takaici.

Zama yai a cikin mota yasa hannunsa akan goshinsa.

Wayarsa ce tai kara alamar text yana dubawa yaga kudi ne yaga ya shigo 20k, ganin sunan Zainab yasa ya fahimci itace.

******

Shiru tai bayan ta dawo office dinta, gaba daya kalaman Khalid ke yawo a kanta suna kara kona mata rai, meyasa ya raina Adam ne?
Wani karamin tsaki taja kafin ta ajiye wayarta data turamai kudi tana cewa in bazai iyaba ya ajiye aikin ai ba dole.

*******

Da kyar takecin soyayyan doya da kwai data gama yanzu, kana kallanta kasan cusawa kawai takeyi bawai dan tanajin dadin sa ba.

Tv din ma dake gabanta tana kallo ne amma yau batajin shaukin kallan yanda ta saba, ajiye zuciya tai tare da shan tea, tana dagowa daga ajiye cup din taga an kashe socket din tv din.
Sannan tazo gabanta tasa hannu ta dauke plate din datake cin abincin.

Goggo ta kalleta, Sadiya tace "zubomin nawa sai ki zo ki dau naki."

Goggo cikin kufula tace "da alama bakisan me ake kira da tarbiyar na gaba ba ko dayake ke da kika zo daga taimako kina neman ruguza........"

Yanda Goggo taga tana kumbura ne yasata yin shiru, bansan tarbiyar ba?
Da sauri Goggo tace "haka nace? Gaskiya bakiji da kyau ba."

Sum sum Goggo ta rabe ta gudu ta wuce kitchen tana cewa "kamar zata daken?"
Abincin ta zubo mata sannan ta fito, gani tai ta saki abincin goggon a kasa, baki Goggo ta saki ta matso da sauri.

Oh zubarwa nai? Bansani ba, ta fada tare da amshe nata.

Daki ta wuce rai a bace, Goggo ta sake baki gaba daya itakam da alama tazama ita ake taimako a gidan ba sadiya ba.

Kallan dakin su Zainab tai rai a bace ta nufi dakin, Adamu na kwance yana bacci rub da ciki, haushi ne ya kara tike ta.
Filo ta dauka ta dada mai, farkawa yai da sauri ya kalleta.
Cikin tsananin takaici da fada tace "har kana iya bacci bayan abinda kaja mana? Ko ince kake neman ja mana? Ka tashi ka kori waccen kedarar ko kuwa?"

Adam ya kalleta yace "wani bacci bayan sai yanzu ne na samu ina ta tunani?"

Baki ta tabe tace "tashi maza ka korerta tun kafin ta kashemu da ran mu."

Mikewa yai ya shigs toilet tsaki tai cikin takaici ta fito.

Adam yana fitowa daga toilet ya nufi kofar dakinta, hannu yasa a jikin kofar sai dai fargaba ya hanashi budewa, dakyar ya daure ya murda kofar tare da turata.

Tana zaune daga ita sai vest sai dai yau vest dinma ta dageta sama duk cikinfa a waje yake, wani abu ya hadiya sannan ya kauda kansa gefe.

Kallansa tai sannan ta dauke kanta ta cigaba da danne dannenta a waya, shiru yai yana nazarin kafin yace "Hmm Sadiya...."

Bata kalleshi ba hakan yasa ya kara tattaro dauriyarsa yace "dan Allah kiyi hakuri kizo ki tafi."

Abincinta kawai takeci kafin ta ajiye plate din ta kalleshi, shakewa nake hadomin tea.

Kamar zai musa sai kuma ya juya, Goggo na zaune yazo ya wuce da tea, yana bata ta kalleshi tace "fita."

Juyawa yai sum sum ya bar dakin.

Goggo ta kalleshi tace "zata tafin?"

A hasale yace "tace na fita, duk ba ke kika ja komai ba? Da kin barni na lalabata ai da ba haka ba, amma duk nunawar da kikai kinji me aka ce ba duk shi ya ja halin da muka shiga ba."

Mene mene? Wato laifina ne kenan? To ai ni na kawota ba dole ba? Ko kunya bakaji, ni Allah yasa ma baka karasa can ba?"

Kallanta yai kawai cikin takaici ya juya yabar gidan ma.

Ranta yakai kololuwa gun baci.


**********

Idanun Khalid a runtse yaji an bude kofar motar, shigowa tai fuska a daure tamau ta zauna, bai kalleta ba shima sannan baice komai ba ya ja motar suka fara tafiya.

"Naga kudi sun shigo dazu? "
Hmm
"Thanks."
Yau har suka isa ba wanda ya tanka, tana isa ta fita daga motar tare da bugo kofa da karfi.

Fitowa yai ya zubawa gidan kallo yana nazarin meke faruwa a cikin gidan nan?
Jakarsa ya dauka ya fita, yana hanyar danbatta ne ya kira Adam sai dai duk yanda ya kirashi bai dauka ba, hakan yasa ya ajiye wayar.

Mamaki ya kama Zainab dataga Goggo bata falan, dakin Goggon ta nufa tana kwance cikin kunar rai.

Zainab ta bude kofar tace "Goggo!"

Goggo ta dago da sauri tace "Zainab kin dawo?"

Jikin ne?

Tai saurin cewa "a'a kawai banajin zaman falan ne, tun azahar na shigo."

Ba karamin mamaki Zainab tai dajin hakan ba, kafin tace "tunda dai lafiya ai Alhamdulila"

Juyawa tai ta fita.

Dakin Sadiya ta kalla, kawai ta nufi daki, budewa tai.

Sadiya dake zaune tana waya, tana ganin Zainab ta gyara zamanta tare da kashe wayar.

Zainab ta kalli yanda take zaune daga vest sai dan wando, daurewa tai tace "Sadiya kina nan ashe?"

Cikin sanyin murya tace "eh yanzu na shigo, da muna hira da Goggo a falo."

Kallanta tai cikin alamar zargi, suna hira? Bayan Goggo tace tun azahar take daki? Sannan ita tunda take ma bata taba ganinsu suna hira ba yanda dai yaci ace uwa da 'ya nayi.

Okay kawai tace ta ja kofar ta koma daki.

Adam yau ma bainan, gashi jiya taji haushin tana mai magana baimassn tanayi ba, kuma haryanzu baiko kira yabata hakuri ba yanda ya saba.

Kayanta ta ajiye ta nufi toilet.

******
Sai wajen goma sha daya yauma Adam ya dawo, tana zaune daram akan gado ta cika ta batse dan bazata dauki wannan halin banzan ba.

Adam ne ya shigo sum sum ya bude kofar daki, ganin Zainab a zaune ne yasa gabanshi ya fadi, baki na rawa yace "Honey!"

Kallansa tai sannan tace "daga ina?"

Yana yar dariyar waskewa ya nufota, hannu tasa ta dakatashi daga tabata tace "daga ina?"

Nadan fita ne neman aiki.
Neman aiki?
Da sauri yace akwai wani baban abokina dayace na kawo takarduna.

Shine sai dare ka dawo? A wani garin suke?

Shiru yai kafin yace "Honey!"
Tace "jiya ma ba sai 11 ka dawo ba?"

"Sorry Honey zan dinga dawowa da wuri."

Matsowa yai ya xauna kusa da ita yace "sorry kinji na daina."

Kai ta daga alama to sannan tace "to."

Kwanciya tai ya zauna a kusa da ita yana shafa bayanta kamar yarinya hartai bacci.

Shiru yai yana tunani, a hankali ya mike ya cire kaya sannan yazo ya kwanta.

Juye kawai yakeyi ya kasa bacci, dazu yana ganin kiran Khalid yaki dauka, tsoro ma yake karya kara jin wani abin.

"Kazo dakina"
Text din daya shigo wayar sa kenan, kallan Zainab yai ganin tana bacci sosai yasa ya mike a hankali ya fito.

Dole yaje ya lalabata ta tafi, da wannan tunanin ya murda kofar dakin.

Tana kwance rub da ciki ya shiga, bata juyo ba tamai  alama dayazo ya zauna a gefenta.

Karasawa yai ya zauna, tadan kalleshi tace "Dan bugamim bayama Yaya."

Kallanta yai sannan yace "ciwon yake?" Kai ta daga alamar eh, shiru yai yana tuno Baby wato Fiddausi wace ke yawan ciwoka ciki kuwa harda ciwon baya wanda yafi matsa mata.

Shiru yai yana kallan Sadiya gabansa na faduwa, tace "bugamim."

Hannu yasa yana buga mata sai dai kalaman Khalid ne ke dawomai, ganin da alama tunani yakeyi yasa ta juyo tare da bude hannayenta.

Kallan kirjinta yai wanda duk rabi a waje yake sannan ya kalli fuskarta, tace "na bata ma rai kwana biyu ko?"

Shiru yai sai dunkule hannunsa dayake yana neman kin amincewa, tace "yahkuri yaya kasan na fadama inada lalura."

Ido ya kura mata yana kokarin danne sha'awar dake taso mai.

Hannu tasa ta jawo rigarsa ya fada kanta, a hankali ta dagoshi ta sa bakinta cikin nasa.

Yanda kasan jira yakeyi nan Adam ya birkice ya na neman fita hayyacinsa.

Sun riga sun shiga wani yanayi, nishi kawai kakeji dan yau har rigar jikinta sai daya cire.

Yoo abinda yake kwana yake yini dashi yau ya samu.

Zainab wacce ke rike da wayarta saboda kiranta da akai ta dauka takejin duk abinda yake faruwa.

Sakar wayarta tai ta fadi kasa, gaba daya jikinta rawa yakeyi neman mikewa take sai dai kafafunta sun kasa daukanta, da kama bango haka ta bi har dakin Sadiya.

Idanunta kumshewa kawai suke kamar mai shirin suma, handa takejin nishin Adam tana tsaye a jikin kofa ne yasa taji gaba daya tana neman zubewa kasa.

Da kyar ta iya sa hannu ta bude kofar.

Adam wanda gaba daya ya zauce da sha'awa har ya fara kokarin aikata aika aika, dan har kayanshi duka da nata ya cire ya cilar.

Tana bude dakin taga abinda ke faruwa kawai ta zube a kasa ta suma.

Adam wanda ana bude kofar ya dago cikin tsananin tashin hankali.

Sadiya kam ko nace Razy ta kalleshi sannan ta kalli Zainab, bataso tarwatsa komai cikin sauri ba sai dai tasan in ta bari waccen dan iskan kyankyasan ya cigaba da shiga abinda bai dameshi ba komai xai wargaje ne ba tare da tayi abinda ta dade shekaru tana jira ba.

Zainab na kalla wace ke sheme kasa a sume.

Goggo wacce ta kasa bacci saboda tsoron abinds kuliya zata aikata yasa ko abinci bataci ba sai yanzu da yunwa ta hanata sukuni ta fito shan dan tea.

Ganin kofar dakin a bude yasa tai ciki.

Zainab ta gani a yashe a bakin kofar a sume.
Ga Adam a kan gado gaba daya ya kame ya kasa ko motsin sa sutura.

Wani kwalelen ihu data saki ne ya razanani, sai da wayata da nake typing ta subuci😨


Hmmmm anzo gurin inji mai tsoron wanka🙊


*****
AYUSHER🏌🏻‍♀
[11/20, 9:16 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀
     .........................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

{29}


Goggo a rikice ta kalli Zainab, wacce ke sume sannan ta kalli Adam wanda da alama shima suman zaune yai, takaici ne ya kara kamata ganin sa zir ba ko kaya.

Idanu ta runtse cikin tsananin bakin ciki ta kalli Sadiya wacce ke kwance kan filo, tana kallan abinda ke faruwa.

Hankali a tashe ta garzayo kusa da Adam ta tsinkamai wani mari, a gigice ya farfado ya kalleta yace "Goggo!"

"Ka tashi ka sa kaya ko sai na guntile abin?"

Sai a lokacin hankalinsa ya dawo akan abinda ke faruwa, hankalinsa  a matukar tashe ya zabura yaja bargon da Sadiya ta luluba, kallan Zainab yai dake kwance duk jikinsa rawa yake ya kalli Goggo hannu tasa ta hankadashi ya zauna kan gado dabas tace "wannan wannan....."

Sai kuma tai shiru tsabagen tashin hankali da rasa bakin ma magana.

Tama rasa me zatamai ta huce, kallan Zainab tai sannan ta karasa tana neman dagata.

Adam ta kalla tace "kazo ka kamata mun kaita asibiti ko kuwa?"

Gaba daya a rikice ya matso kallansa tai tace wannan ma ina zai iya tuki?

Yau itakan wani mumunan mafarki takeyi haka?

Muryar Sadiya taji tace "in kun fita ku ja min kofar?"

Cikin tsananin kumburin fuska Goggo ta kalleta tace "in kofar gidan ubanki ce sai ki sani na kule tsinaniya mai sufar mayu."

Haka suka fita da Zainab Goggo tace mukaita daki.

Nan sukai daki da ita, kallan Adam tai cikin takaici kawai tasa hannu biyu tana dukanshi ta ko ina, shi kanshi kuka kawai yakeyi yana cewa "dakeni Goggo."

Sai da hannunta taji ya fara xafi sannan ta kalleshi cikin tsananin takaici sannan a zuciye ta fito daga dakin.

Zainab ya kalla, hannunta ya kamo kawai yana kuka, dan shi kansa baisan meya shiga kansa ba, dan ya tabbatar a yanda yajishi dazu da ba kowa ba abinda bazai aikata ba.

Kukan da yake ne ruwan ya diga a kan fuskarta, a hankali yatsun kafarta sukai motsi.

"Honey? Ki yafemin bansan meya shiga jikina ba wlh....."

Wadannan kalaman nasa ne suka doki kunuwanta, kanta taji yayi wani uban sarawa, mumunan a binda ta gani ta tuno.

A zabure da firgici ta bude idanunta tare da jan wani dogon mugun numfashi taja, bakinta da gaba daya jikinta suka hau rawa daga kwance.

Adam dake rude lulube da bargo ne ya kalleta, ganin yanda jikinta ke rawa, ga bakinta ya kara daga mai hankali, hankalinsa ne yai mumunan tashi ya matso yace "Honey Honey."

Gaba daya ya gama tsorata a rikice ya zura riga ya fito dan kiran Goggo.

******

Goggo wace tana ajiye Zainab ta shigo dakin Sadiya cikin tashin hankali da rikecewa ne ta kalli Sadiya dake kwance bayan ta maida kayanta ta kwanta kamar mai bacci.

Goggo ta yaye zanin gadon data luluba dashi tace "kin tashi kin bar gidan nan ko sai na gwaraku da bango kanki ya fashi? "

Sadiya ce ta juyo ta kalleta tace "idan kin isa kenan?"

"In na isa?" Goggo ta tambaya.

Sadiya tace "zan zauna harsai sirikarki ta dawo daga mutuwar wucin gadi datai na bata amsoshin tambayoyim da zata tambayen sannan na fita."

Za kuwa ki farka ki ganki a kabari wlh, wannan yarinya ban taba ganin tsinaniya irin ki ba, wlh ko ki tashi ki bar gidan nan ko kuma wlh ki ziyarci lahira."

Sadiya ta ja zanin gadon tace "ko zan tafi sai da safe ba uban da zai fitar dani a daren nan."

Goggo ta fizgota da hannu tana neman jawota ne Adam ya shigo a rikice yana kiranta.

Saketa tai ta fito da gudu tana cewa "menene?"

"Zai zainab"
A rikice sukai dakin da take, hanyarzu jikinta a rikice yake , hankali a tashe tace "mu tafi asibiti."

Nan suka kinkimeta sukai waje.

Asibitin Standard suka nufa, gaba daya dan Allah yasa gari bai waye bane sam babu motoci a hanya da lalai sai dai wani ikon Allah amma yanda Adam ke tuki, da kyar ya kaisu cikin asibitin.

Zainab gaba daya haryanzu ta kasa saita tunaninta, abinda ta gani ne yake dawo mata kawai ta ko ina jikinta rawa yakeyi.

Haka aka shiga da ita suka kwantar da ita wata nirse tazo dubata.

Adam zaune a waje shida Goggo sunyi tsuru tsuru, Goggo in ta kalleshi sai taji kamar ta rufeshi da duka, shikam sai matsar kwalla yake, can yace "Goggo ya zamuyi?"

Tambaya kake? Tambaya kake? Banda hauka da rashin tunani sau nawa ina fadama ka shiga hankalinka da wannan yarinyar? Tun farko ma uban wa yace ka tsintota?"

Adam ya share kwallar sa yace "na shiga uku Goggo, Zainab bazata taba yafemin ba, Goggo na shiga uku."

Haushi ne ya kara kamata ta runtse idanunta cikin takaici.

Wajen awa daya sannan nurse din ta fito ta kallesu tace "shock ne amma yanzu mun mata allurar baci so in ta tashi muna sa ran komai ya dawo daidai, da alama shock din  data shiga babba ne."

Adam yai shiru yana tausayin abinda zai faru.

Haka sukai Jugum a asibiti, harara kawai Goggo ke zabgamai tana neman mafita da yanda zatai kwacesu, dan itakam im Zainab ta koresu shikenan rayuwarta ta kare dan batasan yanda zata cigaba da rayuwa ba.

Kallan kafarta tai ashe ko takalmi bata sa ba, Adam ta kalla shima haka, tace Allah yasa ka sa wando ba rigar ka zura ba sokon banza."

Kasa yai dakai cikin tsoron halin da suke ciki.

Tunowa datai sun bar Sadiya a can ita kadai ne yasa ta kara shiga wani hali.


Kallan Adam tai tace "inaji dole naje na kuri tsinaniyar can kafin ta farka mu koma ta kulla ma sharri."

A tsorace ya riketa yace "Goggo ki taimaken karki tafi ki barni in Zainab ta tashi banssn yanda zanyi ba."

Cikin takaici ta bige hanunsa tace "kasan kana tsoranta ka aikata?"

Kasa yai dakai cikin tashin hankali, ya zatai da tsinaniyar can?

Haka har gari ya waye suna zaune, sai da Goggo tace "tashi ni kaje kai sallah zan daure in shiga gunta kafin ka dawo."

Mikewa yai yace "in na dawo zan tsaya a waje."

Kallan takaici tamai kawai ta wuce ciki.

A hankali ta bude kofar, sai data tabbatar tana bacci sannan ta shiga.

Zainab dake bacci ta kalla, tabbas tasan akwai tashin hankali mai karfi in Zainab ta farka, lalai ko za'a mutu haka zatai ta bata hakuri, itakam bazata iya rayuwa ba a gidan Zainab ba wlh.

Tana idar da sallah ta fito dan itakam inba korar magen can tai ba bazata taba samun nutsuwa ba.

Adam ta gani xai shigo ita kuma zata fita, da gudu ya karasa yace "Goggo ina zaki?"

Wani banzan kallo tamai tace "ban sani ba."

Tai wucewarta.

Tana fita taga adaidata ta shiga.



******

Karfe bakwai da rabi Khalid ya iso gidan, Bala ne ya kalleshi yace "ranka ya dade basa nan dukansu."

"Basa nan? Lafiya dai ko?

Bala yace "Hajiyarce ba lafiya suna asibiti."

Shiru yai yana tunanin ya tambaya yaji sosai ne? Amma yana ganin ba huruminsa banr hakan yasa ya juya.

Ya juya kenan Goggo na sauka a adaidaita, mai adaidaitan ta kalla tace "in dako ma kudin ka."

Kallanta yai yace "gaskiya Baba kiyi sauri."

Tace to.
Khalid ta kalla cikin alamar tambaya tace "wa?"

Gaisheta yai sannan yace "Khalid ne, wanda ke kaita gun aiki."

Oh matuki?
Yace eh, kafarta ya kalla ba ko takalmi, tace "an fadama batada lfy ko?"

"Eh, Allah ya kara sauki."
Tace amin, sallama ya mata ya juya.

Ciki ta shiga taba Bala kudin adaidaita sannan ta nade hannun rigarta kai kace mai shirin dambe ce ta nufi dakin Sadiya.

Cikin masifa ta bude kofar, a rikice ta kara kallan dakin, ba kowa a ciki sannan bako kayanta a ciki, hankali a tashe ta fara leleka dakunan gidan, sai dai ba ita ba labarinta, sai wayar zainab dake ta kara.

Daukan wayar tai ta dau takalmi ta fito.

Dawowa tai asibitin, a waje taga Adam, yi tai kamar bata ganshi ba tai hanyar ciki.
Da gudu ya taso yace "Goggo kin dawo?"

Tace "uban me kake anan? Kai da zakaje kusa da ita tana tashi ka nemi yafitarta?"

Shiru yai shidai kam yasan Zainab.

A hankali Goggo ta tura kofar daki, ajiye wayar Zainab tai a gefe ta ma Adam alama daya shigo, yana sa kafa cikin dakin Zainab ta mike ta zaune, kai kace mikar da ita akai.

A tare suka kalleta gaba dayansu hankulansu a tashe, kallan asibitin tai, sannan ta kalli Adam wanda ke makale a bakin kofa, Goggo ta kalla idanunta sunyi jaaa sosai ko dan bacci tasha?

Bakinta kawai take motsawa tana san magana amma ji take wani abu ya tokare a kirjinta, har makoshinta."

Ganin maganar bazata yiwu ba ta mike ta zo kusa da Goggo hanyar waje ta nuna mata, da sauri Goggo tace "Zainab kin farfado? Sannu kinji."

Idanunta ta runtse da karfi, Adam ta hango akan gado ba kaya shida Sadiya gaba daya sun fita hayyacinsu.

Da sauri ta bude idanunta, sannan ta nunawa Goggo hanyar waje.

Goggo tace "ya akai? Abu kike so?"

Zainab rai a bace ta kara nuna mata hanyar waje, sarai Goggo ta san me take nufi amma tace "Zainab?"

Bakin kofa ta nufa wanda Adam na ganin ta nufoshi ya zube a kasa yai kneel down tare da daga hannunsa  yace "Honey!"

Ko kallansa batai ba ta kara kallan Goggo ta nuna mata waje.

Goggo sum sum ta zo ta fice, suna fita ta rufe kofa ta sa key.

Sulalewa tai a jikin kofar ta zauna, gaba daya ta rasa meke faruwa, inama mafarki takeyi? Meke faruwa da rayuwarta.

Wayarta dake kara ta kalla, da kyar ta mike taje ta dauka, ganin gun aike ne yasa ta ajiye har ta katse.

Wayar ta kalla gaba daya ta kasa kuka, ta kasa ko magana, number Dady ta scrolling har tana shirin yin dialling ta tuna abinda tamai akan san zuciya irin tata, Ummy!!!
Abinda zuciyarta ta kira kenan, idanunta ta runtse, Alhakin Dady ne bina Ummy? Ummy Adam.....

Abinda zuciyarta ke fada cikin kukan zuci wanda ta kasa zubar dashi a kwayar idanunta.

Number kanwar mamanta tai scrolling, tunowa da yanda Aunty batajin dadi sosai itama gun mijinta wanda harda bakin cikin hakan yasa ta gaji da zaman gidanta yasa ta ajiye wayar ta kifata.

Nabila! Kina ina??? Rayuwata da alama tazo karshe......

Asibitin ta kalla sannan ta kara daukan wayar, number Khalid ta lalubo tamai text.

"Kace Bala ya dako ma key ka zo ka dauken a asibiti"

Khalid na kokarin shiga cafe ne wannan sakon ya shigo wayarsa, kallan sakon ya sakeyi shidai ya rasa meyasa yake tunanin gagarumin abu ya faru a jiya, daga yanda Zainab uwar san aiki da kuma yaga sirikarta ba takalmi.

Juyawa yai ya koma gidan.

Jin sakonta yasa Bala cikin rashin yadda yace "gaskiya ina tsoro.

Khalid ya nuna mai sakon, Bala yai shiru yana tunani, ganin Khalid abokin Adam ne a cewarsu sannan ga daga yanayin Khalid yana ganin ba mutumin banza bane yasa yai shahada ya dako mai spire key din da take ajiye gunsa.

Khalid ya hau ya nufi asibitin.

"Na iso?"

"Ka shigo ina sama"

Ciki ya shiga, Adam da Goggo na zaune jugum Goggo ji take kamar tasa kafa taita makawa Adam.

Ganin Khalid yasa Adam ya mike da sauri ya nufoshi.

Khalid cikin mamaki ya kalleshe yace "Adam?"

Adam ya kamo hannunsa yace "Khalid na shiga uku na........"

Adam..
Kiran da Goggo tamai ne yasashi yin shiru, Khalid yai shiru yana kara tabbatar da zarginsa.

Kamar tasan ya iso kawai ta fito ita da nurse, wacce take binta tana ce mata ta dawo ta zauna ko dan rashin maganar da takeyi.

Ko kallansu batai ba har Khalid din tai gaba.

Gaba daya ta canza, kafafunta ba takalmi bako mayafi a jikinta, rigace doguwa zuwa gwiwa ta bacci, da wando, sai hula a kanta.

Da alama halin da take ciki ma baisa tasan abinda ke sanye a jikinta ba.

Juyawa yai ya nufi inda take yace "an baki sallama ne?"

Bata ko kalleshi ba ta sauka har kasa, mota ta nufa ta kalleshi ta mai alama da ya bude.

Yana budewa ta shiga ciki ta zauna.

Kallan Adam da Goggo dake tsaye a bakin kofar asibitin yai sannan ya bude motar ya shiga.

Tafiya suka fara tana kallan motocin dake wucewa, Khalid yai shiru shidai yana tuki amma gaba daya zuciyarshi na tsoron kardai wannan yarinyar tayi wani abin?


Zainab a hankali wani zazzafan hawaye ya zubo mata, tunda ya sako kamar an koro kuka, duk yanda taso ta dane kukan ji tai ta fashe da wani wahalalen kuka mai matukar ratsa zuciya.

Ba karamin tashin hankali Khalid ya fuskanta ba, gefen titi ya gangara, sannan ya ajiye tissue a gefenta ya bude motar ya fita ya tsaya a jikin kofa, sai dai gaba daya jikinsa ya gama yin sanyi, tsananin tausayinta ne ya kamashi.

Kuka take iya karfinta, wanda ni kaina sai danaji hawaye😪


*****
Wai ina Razy ne🙄🙄yasin kafin na kamoki ki dawo yar🙊

Ayusher🏌🏻‍♀
****
[11/22, 5:03 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀
.........................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

{20}

Asiya na zaune tana ta mulmula iloka, daga gefenta kuma Abba ne zaune yana jin radio a gefensa, hannunsa rike yake da mafici da alama kuda yake dan kora in suka zo inda yake.

Kallan Asiya yai yace "Kannen naki na gun ball ko?"

Tace "dazu Umma tace na korosu amma Allah Abba suna dawowa da sukaga Yaya bayanan ni bansan ma sanda suka sake fita ba."

"Oh ni yaran nan bansan jaynarsu da kwallo ba, bare yau sun samu dama kuna hutun tsakiyar term."

Dariya tai tace "in lokacin islamiya yai sa dawo ai dole."

Umma ce ta bude labulen dakin tana sallama, Abba ya kalleta ya amsa.
Mayafinta ta cire ta zauna gefensa sai data kalli Asiya dake ta neman kudinta sannan ta kalli Abba tace "yau bakaji dadin da nake ki ba a rayuwar nan."

Abba yai dariya yace "kamar irin kin gama biyan bashin dake kanki duka din nan."

Dariya tai tace "wlh bakaga dana kai musu dubu biyar din nan a dunkule yanda naji wani dadi ba, ai insha Allahu tunda aka fara biyansu yanzun nan zamu gama."

Abba yai dariya yace "ai sai hamdalla."

Umma ta kalleshi tace "ni tun jiya nake san tambaya, dama aikin driver yana kaiwa dubu ashirin?"

Abba yace "eh dama yawanci

Please Login or Register in order to submit comment