Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zumudi tace "Ummy an bamu sabuwar Teacher."
"Haba? Yaushe?"

"Hmmm yau din nan."
Dariya Zuwaira tai tace "lalai da alama Zainab na san sabuwar teacher din nan?"

Cikin jin dadi tace "eh sosai sosai, Ummy kizo gobe na nuna miki ita."
Dariya Zuwaira tai tace " abin harya kai haka?"

Tace "eh tana dariya."

Kayanta ta canja taci abinci ta wuce islamiya, tana dawowa Dady na nan, tana shigowa gida kafin tai ko sallama ta ruga tana cewa "Dady yau an banu sabuwar Aunty."
Dady ya kalleta da gudu ta karaso ta hau cinyarsa tana cewa "Dady an bamu sabuwar Aunty."

Dady yasa dariya yace "Ummy ta fadamin, lalai Zainab naji da wannan Auntyn."

Dariya tai tace "gobe kazo muje na kaika ka ganta."
Ummy ta kalleta tace "sankai, akace ni za'a fara kaiwa?"
Dariya sukai nan suka shiga hira har dare yai.

Da safe Zainab ana shiryata ta tubure akan lalai itafa sai Ummy da Dady sun kaita makaranta sunga Auntynta, duk yanda Ummy ke lalabata bata bar kuka ba.
Dady ya dauketa yace "yi shiru yar gidana muje muga Auntyn nan."

Ummy ta zura Hijab dinta suka shiga mota tare, driver ya taho shi kadai dan ya maida Ummy, tunda daga makarantar Dady zai wuce.
Suna isa tana sauka daga cikin taxi, tsallako titi tai Zainab na fitowa cikin murna tace "Ummy gatacan."

Taci gayu sosai kai bakace malamar makaranta bace,  sanye take da doguwar rigar atamfa fitted gown wacce ta zauna mata tsam a jiki, mayafi ta yafa a saman kanta tana rike da takardun ta, ta rataya hand bag dinta.

  Ummy ta kalli Zainab tace "ya isa haka nan inta iso sai ki mata magana."

Dady ne ya karasa fitowa daga mota, daidainan ta karaso, fuskarta a sake take sosai harta karaso gun, cikin fara'a tace "Zee."
Da gudu Zainab ta karasa ta rike hannunta, tare suka karaso gun.
Dady ta kalla sannan ta kalli Ummy, cikin fara'a ta gaisheta, Ummy ta amsa cikin nuna farinciki.
Dady ta gaisar, ya amsa yana cewa "shikenan hankali ya kwanta?"
Fuskarta dauke da tambaya ta kalli Ummy tace me?
Ummy tai dariya tace "tun jiya aka dage sai munzo munga sabuwar Aunty."
Fara'arta ce ta karu sosai ta kalli Zainab, Dady yace "tanada san mutane, sannan da alama kinada saukin kai hakan yasa take sanki sosai."

Murmushi tai tace "bakomai ai da na kowa ne."

Ganin yara duk wanda yazo indai a class dinsu yake zai nufota ne yasa sukai sallama suka tafi.

Ummy ta koma gida shikuma ya wuce gun aiki.

Da daddare suna kwance a daki kamar masu bacci Ummy tace "da ace matar nan zata yadda da ita ta taimakama Zainab da lesson din, naga sam basa shiri da Auntyn da take zuwa yanzu."
Dady ya juyo yace "nayi wannan tunanin dazu nima, toko zaki bita ko zuwa karshen satin nan ne ki tambayeta?"

Ummy cikin gamsuwa tace to.

Sati na zuwa Ummy taje da kanta, ba wani dogon nazari ta amince da hakan wanda yasa Ummy jin dadi.

Sai ya kasance duk asabar da lahadi Aunty Basma na zuwa gida tana koyama Zainab karatu.

Lokacin da abu ya fara faruwa.
A koda yaushe Dady yana zama a gida ranar asabar da lahadi, yana hutawa saboda hidmomi.
Yanda yake jiyo dariyar Zainab daga sama ne yasashi kallan Ummy yace "da alama wannan matar tana san Zainab dayawa."
Ummy tai murmushi tace kana ganin nima yanzu nayi kawa bayan malamar Zainab?

Mikewa yai yace "bari naje naga yanda ake karatun.

Ummy batare da wani abu ba tace ya kamata, mikewa yai ya sauko kasa, bangaren da yake na Zainab ne knda take wasa da kuma inda ake koya mata karatu ya nufa.

Kofar a bude take, yana lekawa yana suna wasan hide and seek, Zainab ta dage tana nemanta.

Tsayawa yai yana kallan ta yana murmushi, Aunty Basma ce tamai alama dayai shiru, Zainab tana neman Aunty ta cafko Dady."

Tana bude ido taga Dady shagwabe fuska tai tace "dady kuma?"
Dariya yai yace "nidin ne sai akai me?"
Dariya sukasa gaba daya, ido ya zubawa Basma wacce ke sanye da riga da skirt na material silk ya kamata dam, ga kanta ba dankwali, maida kallansa yai kan Zainab yace "ayi karatu."
Ya juya, wajen magrib tai sallama akan zata tafi.
Dady yace "bari na saukeki dan zan fita nima."
Ummy tace "Basma ki tsaya ya saukeki."
Kallan Ummy tai tace "ina fita zan samu taxi."

Ummy tace "ga sauki hankali a kwance?"
Godiya tawa Ummy wacce ta dauko mata turare da man shafawa ta bata, tare suka fito dukansu suka mata sallama Dady da Basma suka tafi.

Suna tafe a hanya ake ta famar damunta a waya, kallanta yai yace "ki amsa mana!"
Kallansa tai tace "in amsa ince me?"
Yace "in bakyasan amsawa sai ki kashe wayar."
Juyowa tai ta zubamai ido, yanda take kallansa ne yasa ya gangara gefen titi, kallanta yai yace "menene?"
Tace "bakomai."
Kallan na menene to?
Tace "kawai ina tunanin yanda zanji in nai aurene? Saboda wannan zamanin daga zarar mace ta girma an dinga magana kenan."

"Kinada kyanki ba masoya kika rasa ba meye naki na damuwa?"
Shiru tai batace komai ba............
Tin daga wannan rana lamari ya fara baci tsakanin Dady da Basma, Ummy har ta fara tunanin kamar yanda yake kallanta bai dace ba, sannan irin shigar da takeyi ta fara damun Ummy.

Sai dai taya zatai magana? Matar da bata iya magana duk yanda aka muzguna mata?

Yanda take nunawa Zainab so kuwa inka ganta sai a dauka itace mahaifiyar tata.

Kwatsam wata rana Basma tazo ta dauke kafa, a makaranta ma ta ajiye aikinta, Ummy ta fara damuwa saboda a lokacin kawayene su duk da daurewa take.

Ganin ba labarinta yasa Ummy da Zainab wacce ta dameta da zancen Aunty sukaje har gidanta, a lokacin Dady yayi tafiya saudiya.
Sanda sukaje akace ai batanan tayi tafiya.
Ummy suka fito suka koma gida, Dady na dawowa daga saudiya ya canza gaba daya, ko zama a gida bayayi bare yai wasa da Zainab balle har suyi yar hira da Ummy."

Wannan hali daya tsira ya tada hankalin Ummy gashi a lokacin Allah yaima mahaifiyarta rasuwa, dakyar ya barta taje gombe tai kwana uku, sam yanzu zaman nan baya mata dadi, komai ta tambaya da fada yake amsa mata gashi sai sunyi bacci ma yake dawowa

Rana kwatsam Basma ta aiko mata da katin bikinta.
Ummy tai ta murna ta kirata a waya tana tayata farin ciki.
Ansa biki wata shida a wannan lokaci Zainab tana shekara tara.
Har gida Ummy taje ta tadda anata gyara musu gidansu, ga kayan lefe nan na gani na fada, Basma yanda ta karbesu ne yasa jikin Ummy yai sanyi, yau ko yanda ta saba jan Zainab a jiki batai ba.

Sai dai Ummy ta mata uzuri akan bakin dake gidan ne.

Haka suka koma gida su biyu wanda yanzu haka suke yininshi.

Ana sauran kwana biyu biki Dady ya shigo gida da wuri, murna Ummy tai tayi, sukaci abinci tare y zauna yana duba homework din zainab har lokacin baccinta yai.
Kallan Zuwaira yai fuska a tsuke yace "dama fada miki zan na sai gida a can kusa da gun aiki na."

Cikin farin ciki tace masha Allah, kai Allah ya sanya alheri.
Jibi zan kara aure.
Kafin ta gama rufe baki wannan kalmar ta daki kunnenta.

Kallansa tai da sauri tace "me?"
Yace "aure zanyi sannan nan da kwana biyu za'a daura."

Sake baki tai ta kalleshi, mikewa yai zai wuve daki, da sauri tasa hannu ta riko rigarshi tace "haka ya dace miji ya sanar da matarsa zai kara aure? Haka addini ya koyar? Meyasa wani sa'in san zuciya ke neman mantawa da abinda ya dace?"

Hawaye ne suka zubo mata, ta dago ta kalleshi tace "zan hanaka aure ne bayan kayi niyya? Amma haka ya dace........."

Zuciyarsa ce tadan raunana, da sauri ya dagota ya rungume yace "kiyi hakuri."

Hawaye ne suka shiga zubo mata, sai dai san zuciya irin na namiji wai sai ce mata yai yaje gun wacce zai aura tundazu yakejin sha'awa, haka ya biya bukatarsa tana hawaye......

Dady y canza gaba daya ta kasa gane kanshi har tunani takeyi anya shine mutumin data sani da??????

A ranar bikin basma ya kasance ranar bikinsa hakan yasa Ummy ta aika mata da sako a waya akan bazata samu damar zuwa ba.

Haka ta zauna ita kadai a gida babu mai mata tausar kirji, Zainab a wannan lokaci itama duk ta canza saboda ganin yanda mahaifiyarta take cikin damuwa, ga gida ita kadai.

Tunda aka daura auren Dady bai taka kafa yazo gidansu ba har sai dayai wata biyu, a lokacin Ummy tanata fama da rashin lafiya saboda ciki, wanda ita kanta bata sani ba, ta dauka damuwarta ce yasata shiga wannan hali.

Gaba daya Ummy ta zabge, Zainab duk ta canza itama, inta dawo gida sai dai ta zauna kusa da mahaifiyarta, anan take cin abinci suyi bacci tare, Ummy na kokarin daurewa dan ta nunawa Zainab ba abinda ke damunta.

Sai dai Zainab tun tana daukan wayar Ummy ta kira Dady ana kashewa harma ta hakura ta daina.

Ummy kam ganin amai yaki karewa gashi intai abinci dakyar take iyaci yasa tai tunanin zuwa asibiti.



*******
[10/27, 10:41 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

Page 18

Yau watansa biyu kenan bai tako cikin gidan ba sai dai yana aiko kudi yana kuma sawa akai musu kayan abinci.

Yau Ummy ta tashi da wani irin zazzabi sai amai take kwarawa, da alama dadewar datai bata samu ciki na ga girma shiyasa cikin ke wahalar da ita, tana zaune a falo, dauriya kawai takeyi saboda taga gaba daya hankalin Zainab ya tashi, jin sallama ne yasa Zainab tai tunanin driver ne datace inya dawo zai kai Ummy asibiti.
Tana budewa taga Dadynta, samun kanta tai kawai da fashewa da wani irin kuka.
Tausayinta ne ya kamashi don yana tsananin santa, juyawa tai da sauri ta shiga ciki.
Ya biyota shima cikin hanzari, cikin falo ta tsaya tace "Dady akai Ummy asibiti batada lafiya."

Kallan Ummy yai wacce jin sunan Dady yasata kokartawa ta mike ta kalleshi, nan Dady ya ga duk ta rame ta canza kamani, a hanzarce ya dauketa sukai asibiti su duka.
Anan ne yaji cewar Zuwaira nada juna biyu, aka bata gado akasa mata drip.
Sai dai me? Yana fitowa daga office din dr aka kirashi a waya, Zainab dake tsaye tana jiransa yazo taga yayi hanyar kofa cikin hanzari.
Kafin tai yunkuri har ya fice.
Da gudu ta fito amma ko motarsa babu, haka suka zauna a asibiti har aka sallamesu Dady bai kara ko lekowa ba.
Ummy ganin ta samu sauki ta cire komai a ranta saboda yar ta.
Sosai suke zama suyi hira in ta tafi skul ta zauna taita tunani, gashi ta kasa fada a gidansu, Zainab tun daga wannan rana bata sake daukan waya ta nemi Dady ba haka kuma bata karayima Ummy zancen ta kirashi ko baizo ba.

Haka suka cigaba da rayuwarsu har cikin Ummy ya girma, Zainab murna kamar me akan Ummy zata haifar masu baby.
Zainab na shekara goma sha daya Ummy na wata tara.
Wannan rana ita tafi ko wace rana ciwo a tattare da Zainab, taje makaranta, tana dawowa ta tarada Ummy a yashe a kasan beni gaba daya kasanta jini ne ya mamaye da alama ciwo ne ya kamata tana hanyar saukowa ta mirgina, dan har gefen goshinta a fashe yake.

Gaba daya jikin Zainab rawa ya fara, tama rasa me ya kamata tai, a hankali Ummy ta nemi data kira waya.
Jitai kanta na juyawa ganin jinin dake kasa, sai da Ummy dakyar ta kamo hannunta, firgita tai sannan ta dauko wayar a falo ta kira Dady, gaba daya ba a hayyacinta take ba, mai makon ya dauka muryar mace taji tace "hello."
Da sauri ta kalli Wayar sannan tace "Dady dady yazo Ummy....."
Kashe wayar akai, ganin yanda Ummy ke numfashi yasa ta fita da gudu ta kora driver dinsu.
Haka aka dau Ummy akai asibiti, ana zuwa aka kaita dakin tiyata, sai dai an cire baby amma jini yaki daina zuba duk yanda sukai yaki tsayuwa.
Ummy tai murmushi dakyar tace a kira Zainab.
Zainab ta shigo gaba daya haryanzu bata hayyacinta, Ummy ta kamo hannunta, Allah ne sai Zainab kadai sukasan me tace mata a wannan lokacin.

Mati driver wanda tsoro ya kamashi yasa yana kaisu asibiti ya nufi saban gidan Dady ya sanar dashi sune suka shigo dakin.

Ganin Ummy a kwance yasa dady ya nufeta jikinsa na bari, Zainab baya kawai tai ta sulale agun.

Dady hankalinsa yai masifar tashi, ya nufi Ummy cikin sauri ya kamo hannunta, wasu hawaye ne suka zubo mai, murmushi tamai da kyar daga wannan murmushin ciwo ya rikice, nan ya shiga kokarin sa mata kalmar shahada, ganin yanayinta yasa ya fita da sauri.
Dr ya kira, sai dai kafin suzo Ummy ta cika.....
Allah yai mana cikawa mai kyau Ameen ya Allah.

Haka Basma ta dawo gidan Ummy da gatan cikinta, kannen Ummy sunzo gaisuwa aka bar kanwar Ummy a gidan wato Sauda, nan ta zauna har akai arba'in itama ta koma saboda iyalanta.

Ansama Yarinyar suna Nabila, satin Ummy biyu da rasuwa Basma ta haifi Nusaiba.
Itama Basma tai kuka sai dai Allah ne kadai yasan kukan da takeyi.
Dady kam sai dayai sati ko kofa bai fita ba.

Haka Zainab ta taso, magana wannan inba ta zama dole ba bata yinta, duk yanda dady yaso su daidaita amma inaaa Zainab gaisuwa kadai ke hadata dashi.
In bata makaranta daki take daukan Nabila ta kula da ita.
Tundaga wannan lokaci Zainab tasa a ranta bazata taba bari Namiji ya zama shine yake da komai ba balle har yai tunanin dole ta zauna dashi, ba kuma zata taba bari mijinta ya wulakantata ba, a da auran ma tace bazatai ba.
Tayi karatu kamar zata kashe kanta dan a makaranta babu ko yarinya daya da take kawatar, saboda taga butulcin dake tattare da yarda da mutum.

Tundaga nan ta zama selfish kanta kawai ta sani bata tunanin kowa, abu in bai shafeta ba ko Nabila ba bata shigarshi.
Zama bai mata dadi ba a gida saboda ko ganin Basma tai da mahaifinta hango mahaifiyarta take a cikin jini.
Haka zainab ta gama karatu na nemi aiki a kano saboda ta bar kusa dasu.

Dady yaso hanata sai dai ba yadda zaiyi dan yasan bai isa ya hanata abinda tai niyya ba, Zainab ta dawo kamo gidan Aunty Saudah wato kanwar mamanta.
Anan ta fara aiki har takai matsayin da take a yanzu.
Ta hadu da Adam ne a wata rana lokacin sunji daukan rahoto, tana sauri saboda bata mata ran da akai, tana parking din mota tazo fita shi kuma ya taho zai wuce.
Bata sani ba ta budo kofar ta bigeshi, Adam wanda yake tafe yana waya ya danyi kara tare da kallanta.
Wani banzan kallo tamai tace "idan zakai wayar soyayya ka dinga kallan gabanka."
Ta rufe mota ta fara tafiya, baki ya saki da sauri yace "Baby zan kiraki."
Gabanta yasha yace "me kikace?"
Kallansa tai tace "kunne biyu gareka sannan baki daya ne dakai, ya kamata jinka yafi maganarka yawa, dan matsa ina sauri ne."

Tafiya tai wanda tabai Adam da baki a bude, kallanta yai sannan ya kalli zabgegiyar motarta a ransa yace "ah kin rika ne, ni ina nan na saki baki ina neman yanda zanyi ga wata wacce da alama ta jiku."

Juyawa yai ya tafi.
Washe gari yana zaune ya saka kwanan shinkafa da wake a gaba, takaicin cin shinkafar ya kamashi yace "Goggo wai dan Allah yaushe zaki mana yar dagedage nifa Allah na gaji dacin fara damai."

Radio dinta ta kashe tace "wato Allah wadan naka ya lalace, kana kwance kamar tsuma sai dai na baka kaci sannan har wai abincin ma sai ka zaba? Bayan duk ka cinye mana dan gadon mu agun dan islan karatun da kake."
Adam yai dariya yace "karki damu na kusa samun aiki ina daga cikin office ina shan sanyin AC mai dadi, gefe kuma ga lemo nan in kurba inci naman kaza."

Goggo ta tabe baki tace "sai ka tashi daga mafarkin da kake ko wallahi tinkiyar can ta cinye."
Da sauri yaja kwanansa gabansa yace "in ta cinye ince me?"
"Ina na sani kaci kazar mana."

Haka ya fito bayan ya gama cin abinci suka tafi gidan abokinsa Ziyad inda suke kallo.

Ana switching din tashar Muryar Arewa Adam ya ganta tana labarai( a lokacin labaran dare take)

Ruwan dayake sha ya feso waje ya zuba mata ido, Ziyad yace "Masoyin Baby soyayyar ta motsa ne?"
Adam ya zuba wa Zainab ido ba tare da yace komai ba.
Haka ya kwana yana juya abin a ransa, ai kam washe gari ya nufi cikin kano, sai dai inda suka hadu jiya bai ganta ba.
Tambayar Station dinsu yai yaje.

Tana tsaye cikin fada tanawa staff din gun fada akan  laifin daukan rahoto yanda ya kamata ta hangoshi ta glass, daga waje ya daga mata hannu.
Fitowa tai cikin mamaki tace "me kake anan?"
"Zuwa nai aban hakurin da ba'a bani ba jiya."

Mamaki ne ya kamata, tace "hakuri?"
Yace "eh in baza'a bani ba aban number waya."
Wani kallan banza tamai ta juya.

Tundaga wannan rana kullum sai Adam yazo station dinsu, tun bata kulashi har yanda yake neman magana yake sata murmusawa.
A hankali ta fara fahimtarsa, ga saukin kai komai tace zaice to, a lokacin Zainab ta fara tunanin wannan ne? Dan dama so take ta samu mijin daya dace ta dawo da Nabila gunta.

Adam yana santa so sosai a iya saninta, wanda har tausayin halin da yake ciki yake damunta, hakan yasa ta nunamai aiki zai samu tunda ko wata biyar basuyi da gama karatu ba.

Soyayya mai karfi ce ta shiga tsakaninsu, Adam kanwarsa daya sunanta Sadiya kamar yadda muka sani, wacce ke zaune agun kanin Goggo, ganin Zainab ta samu wanda takeso yasa ta fara ginin gida.
Adam da kanshi ya dinga zama akan aikin har aka kammala....

Tausayin mahaifiyar sa da za'a bari ita kadai sannan da tunanin aikinta yasa ta nemi su tafi da Goggo.

Haka akai auransu dan ta fadamai abubuwa kadan daga rayuwarta, ya kuma nuna shi zai share mata hawaye.
Ta yarda da Adam tana kuma ganin duk duniya idan har akwai namiji daya dayake santa to lalai Adam ne.
Dady kam gaba daya yai sanyi dan tun mutuwar Ummy gaba daya ya canza, sai dai ba yanda zaiyi ya maida hannun agoggo baya, sosai yake san su dawo daidai da Zainab sai dai itakam inaaa matarsa ma kallo bata isheta ba.

Ta nemi a bata Nabila amma Dady ya bata hakuri akan ta barta anan, sannan Nabilan itama tace tafisa nan saboda Nusaiba.

Ganin karta sawa kannenta rayuwar kuncin da take binne dashi a ranta yasa bata taba tada zancen Ummy ba, Nusaiba da Nabila aka barsu a matsayin duka yayan Basma ne wacce itama dana sani da wulakancin da Dady ya fara mata ya dawo da ita hankalinta.

Haka Zainab ta bar gidan sai dai ko waya bata taba hadata da mahaifinta, sai dai ta tambayeshi a gun Nabila, shima yana tambayar Nabila ya Zainab.

Haka rayuwarsu take Zainab tunda ta fara aiki har wannan rana bata taka ko kofar gidansu ba.


Wannan kenan..........

{Mata wandanda suka sanar dani ta Pc da wadanda suki magana a grp akan auren cin amana da rabasu da mazajensu da akai suma, Allah ubangiji ya kara muku hakuri, ya ba mijinku ikon yin adalci a tsakaninku, ya kuma kareku da karewarsa Ameen.}

Allah yasa mu dace..........


Ayusher Ce🏌🏻‍♀[11/9, 11:19 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
......................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

Page 19


Wani wahalalen kuka ne ya kubce mata toshe bakinta tai tanayinsa, ta dade a cikin dakin nan ba tare da ko fitila ta kunna ba, a hankalu ta taso ta turo kofar dakin ta fito.

Ba kowa a falan da alama sun shiga yin sallah ne, bangarenta ta wuce tana zuwa itama ta shiga toilet tai alwala.

Adam ne ya shigo tana kokarin tada sallah, Honey?
Juyowa tai ta kalleshi tare da yin murmushi, takowa yai a hankali zuwa inda take sannan yace "menene?"
Kai ta girgiza alamar ba komai, a hankali yasa hannunsa zai dauka a kan fusksrta, kauds fuskarta tai da sauri tace "ka dawo?"
Hannunsa ya maida ya sauke sannan yace "eh."
Hijab din ta karasa sawa sannan ta tada sallah, ta dade tana tasbihi kafin ta mike, kan gadonta hau ta kwanta.

Adam ya kashe laptop din ya matso yace "Honey kuka kikai?"
Bata juyo ba tace "a'a"
Ajiyar zuciya yai sannan ya fara danna mata kafafunta yana cewa "kinci abinci ne?"
Juyowa tai saitinshi a hankali tai wani lalaussn murmushi ta zubamai ido.

Kwanciya yai daf da ita suna kallan juna yace "Honey?"
Uhmmm

Shiru yai yana tunanin kalaman Sadiya, kallan Zainab yai yace "yaushe kika fara sona? Na dade inasan naji."
Murmushi tai har hakoranta suka fito tace "abinda yazo ma kenan?"

Kai ya daga alamar eh shiru tai tana tunani kafin tace "sanda kacemin ka fara sona saboda kudina?"

Dariya yai sosai harda mikewa ya zauna, tace "Da gaske nake."
Tsagaitawa da dariya yai sannan yace "yaushe na fadi haka?"

Tace "ka manta? Zuwanka station dinmu na hudu?"
Fuska ya rufe yana dariya yace "lalai Honey, wai dagaske lokacin kika fara sona?"

Tace "eh"
"Na dauka fa fada zakimin lokacin kinsan a rana kika fara min murmushi?"

Dariya tadanyi tace "am serious lokacin na fara maida hankali kanka, at least u are honest, nasan bazaka taba yaudara ta ba."

Jawota yai ya rungume a jikinsa, murmushi tai tace "kace Sadiya ta koma dakinsu Nabila."

Dagota yai ya kalleta, tace "badai ce mata zakai ta tafi gobe ba ko?"

Shiru yai yana kallanta fuskarsa dauke da nuna jin dadi, tace "ka barta tai 2weeks kaga dai bata taba zuwa ba."

Murmushi yai cikin gamsuwa.......

************


  Fitowa falo yai ya zuba mata abinci, Goggo dake xaune ita ma tana cin abinci ta bishi a harara sannan tace "batada hannu ne?"
Cikin falan ya shigo rike da plate, Sadiya dake zaune tayi shiru ya kalla sannan ya ce "Goggo to nawa ne."
Kaine zaka zubo abinci dan haka? Kadaiji kiki gaba gaba ma a kitchen zan ganka kana tuka tuwo."

Alama yamata datai shiru yana nuna mata Sadiya, baki ta tabe tace "kunya kake ko me?"

Haushi ne ya kamashi ya kalli Sadiya yace "Ki koma Dakinsu Nabila da kwana."
Da sauri ta kalleshi sannan tace "Yaya."
Goggo ya kalla wacce ke zabgamai Harara kamar idanta zai fado yace "badai ni nace ba Zainab ce."

Juyawa yai da sauri, Goggo ta kalleta tace "kikace gobe zaki tafi? Idanunta ne suka ciciko tace "kiyi hakuri Goggo nima goben naso tafiya amma bangama registration dina bane."

Shiru Goggo tai kamar bazatai magana ba ta zuba maga ido sai cewa tai "badai bakyasan tafiya bako?"

Da sauri ta kalleta tace "Goggo!"

A'a inba haka bane bar maganar, karki faramin wannan hawayen.

Sadiya tai kasa dakai tana share hawayen.
Mikewa tai ta dauko yar jakarta tayima Goggo sai da safe ta shiga dakinsu Nabila, tana shiga ta cilar jakar kan gado sannan tabi kofar dakin da harara, wannan mata.... tai kwafa.

Wayarta babba ta dauko ta fara dane danen ta tana chatting.....

Wajen karfe 12 na dare Zainab na bacci yaji wayarsa tai kara alamar text.
Idanunsa ya bude sannan ya jawo wayarsa, Yaya....
Abinda kawai ya gani kenan, number ya kalla, baisanta ba hakan yasa yai duba log din sa, ganin ya kira wayar yasa ya mike da sauri ya fito.

Knocking din dakin Sadiya yai a tsorace yana fatan Allah yasa ba ciwo bane ya kamata har ta kasa rubuta mai text.
Nishi yaji daga ciki wanda ya sashi hanzarin bude kofar, tana kwance da vest a jikinta da skirt din dazu, tanata murkusus akan gado.

Da sauri ya karasa yace "Sadiya lafiya? Meya sameki haka?"

Yai maganar cikin tashin hankali, Bayana yaya bayana zai balle, tana fada tana kuka cikin tsananin ciwo.

Sadiya tashi kisa riga muje asibiti, dan dagowa tai gaba daya rabin kirjinta ya fito, da sauri ya dauke  idansa daga kanta, ya hadiye yawo yace "daure ki tashi muje asibiti."

Mikewa ya nemi yi da sauri ta sa hannu ta kamoshi, juyowa yai da sauri, tace "yaya ka tausayamun."

Yanda idanunta sukai jaa yanayinta duk ya canza ga hawaye datake yi yasa tausayinta ya kamashi? Tace "dan Allah yaya ka bubugamin tsakiyar bayana, dan Allah kafin na mutu."

Baya? Ya fada cikin mamaki, luuu tai da idanunta kamar mai shirin suma ta fara

Please Login or Register in order to submit comment