Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da tsinaniyar magana?"

Wata dariya yasa sannan yace "Sadiya kam akwai surutu kila dan bata taba zuwa bane"

Jin karar bude gate ne yasa ta fito daga dakin, Adam ya biyota.

Goggo ce ta kalleshi da sauri dan tana zaune a falo ko kayanta data anso bata je ta ajiye ba data anso.

Ganin yanda ya fito fuska a sake ne yasa tasan ba abinda ya faru, nan ta mike ta nufi daki.

Sadiya Adam ya kalla yace "Sadiya kiyi godiya Auntynki ta biya miki kudin makaranta."

Sadiya ta kalleta tace "Aunty nagode Allah ya saka da alkairi......." hawaye ne suka zubo mata, Zainab zatai magana Nusaiba tai tsale tace "My yaya ya dawo."

Zainab ce ta wuce waje, Adam ya kalleta kawai sannan ya kalli Sadiya dake hawaye ya xauna akan kujerar dake kusa da ita yace "kukan na meye?"

Kallansa tai tana share hawaye tace "na rasa me zance ne."

Murmushi yai yace "to kinyi ya isa haka nan, kai ta daga alamar to.

Duk maganar a hankali yakeyi, dan dama Nabila bata falan yanzu da alama ta shiga daki, ita kuma Nusaiba na jikin window tana kallan Khalid.

Zainab ce ta fito ya rufe motar kenan ya goya jakarsa, juyowar da zaiyi taga gefen bakinshi na jini.

Idanu ta zaro hankali a tashe ta matsa tace "lafiya?"

Kallanta yai,tace "su sukama?"

"No ba wani abun, zan wuce sai gobe da safe in Allah ya kaimu."

Ya mata sallama yana neman wucewa, da sauri tace "meyasa suka dakika bayan ba kaine da kaifi ba?"

Baisan sanda ya juyo ba, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa har ya juya kuma sai ya kara juyowa yace "Ko am sake kiranki karki daga, inso samune ma kiyi blocking din number."

Batace komai ba, sannan yadan murmusa kadan yace "sannan ba dukana akai ba, sai da safe."

Ya fita, yana tafe yana cewa wai ka bari aka dakeka sai kace wani yaro, shiru yai yana tuno abinda ya faru.

Ko garin Zaria bai kai ba ya fahimci suna binshi a baya, hakan yasa ya gangara gefen titi yai parking din motarsa, suka karaso sukai parking kusa dashi.

Fitowa sukai suka zagayeshi ganin ba kowa a motar yasa ransu ya baci.

Babba ne ya kalli Khalid yace "ina take?"

Khalid yace "wa kenan?"

Cikin masifa yace " ina take?"

Khalid yace "wanda ya turoku bai fada muku ba a wannan motar ta taho ba?"

Wannan kalma ta hasala su hakan yasa bai an kara ba yaji an makeshi wanda yasa shi ya fadi, har gefen bakinsa ya fashe.

Dagowa yai rai a bace yace "me kenan?" Wnda ya nausheshin yace "kana tunanin tsoranka mukeyi?"

khalid ya goge gefen bakinsa sannan ya make wanda ya bugeshin, shima gefen bakinsa ya fashe, hannunsa dayamai zafi gun naushin yadan yarfe sannan ya kallesu yace " na kira police na tabbatar sun kusa isowa yanzu, in munje police station ma karasa maganar acan."


Jin zancen police ne ya sa suka kalli hanya da sauri, babban yace "mu zaka rainawa hankali?"

Khalid yai murmushi yace "dan Allah kar ku tafi, dan nafiso muje police station din a dau mataki akan ku."

Cikin yaran nupe dayan ya fara mai magana, anya ma tsaya? In aka kamamu fa an kama
Banza?"

Khalid ya kalli Ogan yace "bani wanda ya aikoku a waya muyi magana dan daga yanda wayarka ke kara tun dazj nasan shine"

Ogan ya kalli Khalid sannan ya zaro wayar yana neman dagawa Khalid ya warce.

Dayake jin ogan yai sanyi yasa bai kwace ba, sai leka titi suke.

Khalid ya daga wayar yana ji akace "kun biya bukatar taku? Na fada muku ai xsku sha romo gans kudi ga na can ciki."

  Khalid yayi mamakin jin wannan kalamai, yace "ohhhh am really sorry amma abinda kake neman yiwa matar aure bazai taba faruwa ba."

Jin haka ne yasa yace "waye kai?"

Khalid yace "wanda yasan daraja da mutuncin mace!"

Waye kai? Uban waye kai?"

"Ka shirya zuwa police station dan yanzu za'a tafi da yaranka, kaga lalatar daka nemi yiwa yarinya sai ya bayyana a idan duniya."


Hankalinsa ya tashi, wanda Khalid ya mikawa Ogan wayar da gudu suka shige mota suka arta a guje.


Ran Khalid ya baci dayaga haryanzu ba alamun yan sandan daya kira, idanu ya rufe tare da yin karamin ajiyar zuciya, nigeria kasata abinda ya fada a fili kenan tare da murmusawa, yanzu da itace aka kama har a gama lahanta mata rayuwa ba wanda zaizo cetanta.

Ransa ba karamin baci yai ba ganin ya dade a gun yan sandan basuzo ba yasa ya juya ya bar gun.

Yana tafe kalaman mutumin nan namai yawo, wani irin rashin imanine wannan? Kai laifi dan an hukuntaka sai ka nemi hanya mafi muni kace dashi zaka rama.

  Wayarsa ce  ta hau kara wanda ya dawo dashi daga tunanin dayai, ganin Adam ne yasa ya daga dan dama so yake ya kirashi.

Adam yace "Khalid ka wuce ne?"

Yace "yanzu zan hau mota naga magrib tayi."

Adam ya kalli Zainab da ta wasie tana dadana tablet dinta yace "ka dawo ka kwana anan dan Allah kaga dare yayi."

Khalid yace "karka damu yanzun nan zakaga na isa gida."

Adam yace "yau dai kadai yanda kasha doguwar tafiyar nan ka zo ka kwana anan."

Yace "to zan wuce gidan kawuna na kwana acan."

Adam yace "shikenan."

Har zasuyi sallama yace "Adam."

Adam yace "naam"

Yadanyi shiru saboda baisan yanda zaiyi yace mai karyabar matarsa ta dinga fita ita kadai ba, daurewa yai yace "ai kun shiga gida kenan ko?"

Dariya tambayar taba Adam yace "eh."

Khalid yace "to shikenan sai da safe."

Nan sukai sallama ya dan sosa kansa na jin haushin yanda yai tambayar.



********

Kallan Zainab Adam yai yace "yace a'a"

Tace "me?"

Yace "kikace wannan abokin naka ya kwana anan mana tunda tafiya mukai doguwa."

Ta sa dariya tace "wai dan nace haka ne ka kirashi? Tab lalai Honey kaima."

Tana kaiwa nan ta mike ta shiga toilet.

Tana rufe kofar tace dan an tausaya ma shine zaka wulakanta mutane? Kai ta tafiya din kafi ruwa gudu.....



Harya kwanta yaji kishir ruwa ta dameshi, mikewa yai ya fito a hankali ya nufi kitchen.

Ruwa ya dauko a fridge ya fara sha, daga gefe yaji kamar a na nufo kitchen din, da yake fitilar wayarsa ya kunna kawai ya haske wanda ke tahowa.

Sanye take da vest dinta sai zani data daura, ganin shigarta ne yasa yai saurin sauke fitilar tare da maida fridge din ya rufe.

Nabila dan haskamin hanys zan fadi dan Allah.

Abinda ta fada kenan cikin sanyin murya.

Adam ya haska mata hanya sai dai bai san sanda yake kara kallanta ba, harta karaso.

Kusa dashi ta tsaya wanda hakan yasa ya haska kansa yace "nine ba nabila ba."

Tace "Yaya baka kwanta ba?"

Yace "na kwanta ruwa naji ina san sha na taso."

Amma ki dinga sa hijab in zaki fito, ko bakiga da maza a gidan ba?

Ta kallesh tace "kai kadaine a gidan yaya, sannan bansan zan ganka ba, ga zafi nakeji, na kuma san kai ba masu halin banza bane."

Murmushi yai yace "hakane."

Sha ruwan zan tafi na kwanta.

Tace to nan ga fara shan ruwa, a zabure tai tsale ta matsa inda yake ta kankameshi kam jikinta na kyarma.

Hankalinsa a tashe yace "Sadiya Sadiya menene?"

Kyarma jikinta kawai yakeyi gashi ta matseshi tsam, da kyar ya banbareta yana jijigata, har yana neman kunna wuta ne yasa ta farfado.

A tsorace yace "lafiya?"

Tace "abu nai?"

Yace "eh yanzu kika kankameni."

Hawaye ne suka shiga zubo mata wanda tausayinta ya kara rufemai zuciyaaaaaaa




☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘☘
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Association💡

Shafi na Goma Sha Uku

Wattpad/@AyusherMohd.

*Jinjina Gaisuwa tare da Fatan Alkairi a Duk Inda Kuke Billy Galadanci da BillynAbdul....May Allah Always Help and Bless You🥰🥰🥰🥰Much Love*

  Cikin mamaki Adam ya kalleta yanda take hawaye ne ya bashi tausayi, yace "Sadiya?"

Hawayenta ta share tace "Yaya bansan meke damuna ba wannan larura tawa ni kaina na kasa ganeta."

Larura?

Ta kalleshi, zatai magana kenan sukaji alamun bude kofa, da sauri ta ja hannunshi suka bar kitchen din. Store ta turashi, sannan ta shiga tare da barin kofar a bude kadan tana lekawa.
Kuna wutar falan da akai ne yasa ta fahimci wacece, matsowa yai yace " wacece?"

Nunamai Nabila dake kale kalan falan tai, yace "to me muke anan? Laifin me mukai muke boyewa?"

Nabila ta kalla wacce ta shiga kitchen nan ma taga ba kowa, tabbas taji alamun magana tana bacci, ganin bakowa ne yasa ta koma daki, tana rufewa Adam ya kalli Sadiya wacce tace "yaya yahkuri ina tsoron me zatace ne in ta ganmu muna magana tsakar dare mu biyu."

Yace "ni dake a matsayin jini daya muke ko kin manta ne?"

Kanta ta saukar kasa tace "na manta yaya, yahkuri."

Murmushi yai yace "bakomai, jeki kwanta dare yayi sosai."

Kai ta daga alamar to sannan ta juya ta fita, tana fita ya fito ya nufi kitchen ya hau kwankwadar ruwa sannan ya juya ya shige daki ya kwanta.

Sadiya kam a hankali ta shiga dakin, Goggo nata jan uban munsharin bacci, ta kwanta a inda take kwanciya wato kasa.

Shiru tai tana tunani, kafin bacci ya dauketa.

Kamar yanda ta saba karfe bakwai ta gama shiryawa, Adam dake kwance yana bacci ta kalla sannan ta sunkuyo ta sumbaci kuncinsa, bargon ta gyaramai sannan ta dau kayanta ta fito daga dakin.

Sadiya ta gani tana ta wanke wanke tare da gyare gyare a kitchen.

Cikin mamaki tace "Sadiya me kike haka da safen nan?"

Nan ta tsugunna har kasa ta gaisheta, Zainab ta amsa tace "amma ke da zaki kwanta ki huta me kike a nan?"

Murmushi tai tace "Auntu kawai sai na hau kwanciya? Gwara dai na taimaka da wani abin."

Zainab ta fara hada tea dinta tana cewa "da sai ki bari in an tashi amma ba da sassafe haka ba."

Sadiya tai kasa dakai alamar kunya, Zainab cikin jin dadi tace "nagode."

Sadiya tace nice da godiya Aunty.
Zainab ta dau tea dinta ta fita.

A waje ta ganshi yana goge motar, karasawa tai gun, ganin bai ganta ba yasa ta danyi motsi da kafarta.

Khalid ya juyo ya kalleta tare da cewa "oh bansan kin fito ba."

Inda aka bigeshi jiya ta kalla sannan tace "hannuna."
Da sauri ya bude motar sannan ta sasu a ciki, shiga tai ciki ta zauna, sannan ya shiga shima.

Harya tada mota sai ji tai ance "Ina kwana?"

Mamaki ne ya kamata wanda har saida tace "dani kake?"

Baice komai ba ya fita da motar, kallansa tai sannan tace "daga jiya zuwa yau ka canza yanayin da kake kallo na ne?"

Cikin mamaki yace "name kenan?"

Tace "gaisuwar ta mecece? Ko dan abinda ya faru jiya yasa ka fara daukata abar tausayi?"

Jiyai baisan me ma zai ce mata ba hakan yasa yai shiru bai ce komai ba, dauke kai itama tai ta cigaba da dube dubem takardarta.

Yana san yaji ko number ta sake kiranta amma baisan ta yanda zaice ba, hakan yasashi yai shiru, dan jiya baccin dayai kalilan ne, yana ta mamakin wannan lamari, wato dan ankori mai laifi sai ya nemi lalata ma matar aure rayuwa saboda kawai cikar burinsa na daukan fansa? Lalai bata san me mugun nan ya shirya a kanta ba da........"

Jin wayarta na kara ne yasa ya kalleta ta glass din mota, jiyai tace "Nabila!"

Hakan yasa ya maida kansa titi, daga can Nabila tace "wai Aunty harkin tafi?"
Tace "eh da wani abin ne?"

Cikin shagwaba Nabila tace "yaufa zamu tafi."

Oh my Gosh!

Abinda ta fada kenan sannan tacigaba " wajen nawane?"

Tace "bansani ba wlh amma nasan bai wuce rana."

Zainab tace "ba matsala zan dawo lokacin lunch sai muyi sallama na koma."

Nabila tace "okay in naga an kusa lunch da kaina zan kiraki, nasan inkika shiga aiki mantawa zakiyi."

Zainab tai dariya sannan tace "to ki tabbatar kin kira."
Nan sukai sallama ta kashe wayar, harta danyi shiru sai tace "wajen 12:30 zaka dan maidani gida."

Okay!
Abinda yace kenan, shiru tai, har suka isa.

Suna isa ta fita tai ciki, juyawa yai da motar ya nufi police station, duk da dai yasan a banza zashi amma yana fatan y hadu da nagari.

Bayan ya shiga ciki ne ya sanar da su wata number yake so su bincika suga na wanene, officer din ya tambayeshi number wacece? Matarka ce ko mamanka? Ko kuma Yayarka ko kanwarka?

Kallansa yai yace "kanwatace."

Yace "wanene ke kiranta?"

Khalid ya kalleshi cikin jin haushin tambayar ya kai da aka fadama ana san ka taimaka ka nemi me number zaka tambaya wai number waye?

Ganin yanda Khalid ya ke kallansa ne yasa yace "oh ashe fa haka kace ko?"

Ran Khalid ya fara baci, daurewa yai yace "eh ga number."

Sai da ya gama karantawa sannan yace " yauwa meye sunansa ma? Sannan a ina zamu nemeshi?"

Khalid ya kalleshi yace "barshi kawai, dan da alama ba a nan ka dace ba."

Ya juya a kufule ya bar gun, Officer ya bishi da zage yana cewa a gidan uwarka na dace? Dan************

Khalid ya shiga mota rai a bace yaja ya bar gun, waya ya daga ya kira Salmanu, daga can ya daga yace "Khalid."

Khalid yace "Salmanu kasan wani a police station? Number nakeso amin tracking."

Salmanu yace "bansan kowa ba wlh sai yayan waccen."

Khalid yace "wanda suka yaudareka? Basu indai sune."

Nan ya kashe wayar ya juya can tv station din, yana isa ana turomai text na interview yana karantawa ya kifa wayar dan yanzu yama daina sa rai.

**************


  Goggo tana zaune akan kujera tanacin soyayyen dankali da kwai da Nusaiba ta soya musu, tana ci tana kallanta a tv.

Ita kadai ce a falan dansu Nabila na daki suna hada kaya, Sadiya kuma na wanka.

Fitowa yai daga daki yana mika, alamar yanzu ya tashi, Goggo ta kalleshi ta tabe baki tare da shan shayinta ta cigaba da cin dankalinta

Kallanta yai yace "Hajiya Goggo abinci akeci ne?"

Kallansa tai sannan tace "wai kai bakajin kunyar rayuwarka?"

Kallanta yai yace "me kuma nai?"

Tace "kalli karfe nawa? Ka baje kana uban baci kamar kasa, ko kunya ma bakaji."

Agoggo ya kalla karfe sha daya da kwata yace "to wai Goggo menene dan nai bacci? Kemafa kallan ki kike, kici kisha ki kwanta."

Ta harareshi tace "can ta matsema, nidai ina tuna ma ran asabar zaka kaini biki ran lahadi kuma za'ai dinner da daddare."

Wata dariya ya saka kafin yace "wai da gaske dinner din zakuyi?"

Tace "mu kawayen uwar amarya ne meye in munje?"

Yace bakomai Allah ya taimaka.

Tace "waccen magen daka kwaso yaushe zaka kaita makarantar ta gama ta tafi? Nifa kasan bansan a takuramin a dakina."

Yace "Zainab tace ta zauna adakinsu Nabila insun wuce yau."

Goggo ta kalleshi cikin zargi tace "ita da saka sallama gobe meye naka nacewa ta koma can?"

Yace "bani na fadaba Zainab ce tace saboda ke."

Goggo tace "to koma menene ka tabbatar ka sallemeta gobe."

Yace to naji, tana ina?

Tana daki.

Ta cigaba da cin abincinta.
Dakin ya nufa ya kwankwasa, daga ciki ta bude.

Kallanta yai yace "inkinshirya ki fito kici abinci kafin na shirya sai muje."

Tace "kai kaci abinci?"
Yace "ba matsala muje ko acan na samu wani abin."

Tace "to."

Fitowa tai sanye da kayan Goggo wanda sun mata yawa, yace "ina zuwa."

Sa sauri ya nufi dakinsu, Goggo ta bishi da ido.
Yana zuwa ya bude drawer din kayan Zainab, kayan da ta dade batasa ba ya dauko guda biyu sannan ya dawo da sauri  Goggo ta kara binshi da kallo.

A bakin kofa ya tadda ita ya mika mata, kallansa tai tace "na waye?"

Yace "kayan Zainab ne bata sashi saboda ya mata kadan,ki gwada ko zai miki"

Ta amsa idanunta suka ciciko yace "kar ki fara kukan nan naki."

Ta kalleshi tace "Yaya nagode."

Juyawa yai da sauri dan shiryawa.

***********

Bayanta tadan mike saboda dan gajiyar data taso mata sannan ta kalli agoggon hannunta, ganin lokacin ya kusa yasa ta jawo drawer din kusa da ita hoton dake ciki ta ciro, a hankali tasa hannunta ta goge sannan ta kura wa hoton ido, idanunta ne suka fara canza kala da sauri ta maida hoton ta rufe.

Sannan ta mike da dau wayarta.


*************AYUSHER**********
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Association💡

Shafi na Goma Sha Hudu

Wattpad/@AyusherMohd.

*Ayusher Muhd*

Baki Goggo ta saki dataga Sadiya ta fito daga daki sanye da kaya, duk da bata san Zainab da kayan ba amma tasan ina zata samo kaya inba na Zainab ba?
Sadiya ta matso ta tsuguna a gefen Goggo ta gaisheta, Goggo ta amsa tace “Kin shirya?”
Tace “eh.”
“Tafi da wannan kitchen ki zubo abinci.” Ta mika mata plate din hannunta.
Sadiya ta amsa ta mike ta nufi kitchen, Goggo ta kwafa ta maida kanta kan tv.

Nabila ce tafito daga cikin daki, zama tai akan kujera tare da kallan Goggo tace “Goggo naso ina nan za’ai bikin nan inje rakiya.”

Goggo ta kalleta tace “inkinje wa kika sani?”
Nabila tadan tabe baki tace “ba sai kin fadi haka ba Goggo nima neman magana ce, ko ina nan ba zuwa zan ba.”
Dariya tai tace “nima naso kina nan muje tare wasa nake miki, ai tafiya da dan rakiya yafi dadi.”

Nabila tace “Uhm.”

Goggo ta harareta ta kasan ido a ranta tana cewa wannan yarinya da tsinanen neman magana take.
Adam ne ya fito daga daki yana sa mabalin riga.

Wai harkai wanka ko me?
Goggo ta fada tana kallansa, Nabila ta kalleta tace “to in banda abinki Goggo dakalw yai?”
Goggo ta kifa mata harara tace “Nabila wai meyasa bakinki baya shiru ne?
Nabila ta kalli Adam wanda shima kalaman Goggo sun bata mai tace “Uncle dan Allah ka taimaka ka daumin hoto ka turamin.”
“Hoto? Nawa?”
Alama ta mai da Goggo tace “in zamusha ashoki.”
Adam yai dariya yace “angama, nayi alkawarin turuwa.”

Sadiya ce ta dawo dauke da plate biyu, ajiye daya tai a kusa da Goggo sannan ta ajiye ma Adam a inda yadan fiya zama tace “yaya gashi.”
Ta koma kitchen, daga ciki tace “yaya sugar fa?”
Yace “kadan.” Jim kadan ta fito da cup ta ajiye mai sannan ta zauna.

Yace “godiya nake kanwata.”
“Kanwa?” Goggo ta fada ba tare da ta sani ba.
Nabila ta kalleta tace “Goggo me kike nufi?”
Adam ne ya kalleta da sauri, dariya ta saki tace “dubamin ki gani Nabila, maza basa tashi cewa mace kanwarsu sai ta musu aiki.”

Nabila ta kalli Sadiya wacce tai shiru tana cin abicinta, wai Sadiya bakya magana ne?”
Murmushi tai ta kalleta tace “inayi.”
Nabila ta kalli Adam da Goggo tace “wai haka take? Ni sai naga kamar ba haka ya kamata ‘ya da uwa su dinga yi ba.”

Adam ne ya kwashe da dariya harya kusa kwarewa yace “Baki gansu a daki bane su biyu, sun iya kus kus cikin dare.”

Nabila ta kalleshi sannan ta kalli Goggo wacce itama kallanshi take tace “irin wannan dariya?”
Goggo tace “kuyi ku gama ku wuce lokaci na wucewa.”
Adam ya mike ba tare da ya kara cin komai ba ya dau plate da cup din yai kitchen, ajiyewa yai ya fito yai waje.
Sadiya ta mike itama ba tare da ta karasa ba ta kai kitchen ta dauko hijab ta fito.
Harzata fita Nabila tace “saduwar alkairi.”
A hankali tace “bazamu sameku ba?”
Tace “eh, sai kun dawo.”

Sadiya ta fita, a bakin mota ta tarada Adam ta bude ta shiga shima ya shiga, Nusaiba ce ta fito da gudu tace “Yayanane?”
Nabila dake zaune ta mike tace “Allah ya baki lfy dan wlh bakida ita.”

Cikin masifa tace “ke kika dauranun rashin lafiyar?”
Nabila ta daga kafada tace “kika daurawa kanki dai.”
Cikin masifa Nusaiba tace “ke kuma meye naki a ciki?”
Nabila ta fara hamma tace “ahhh nagaji.”

Ran Nusaiba ya kara baci, Goggo ta kalleta tace “fadan karshe ake mana?”
Nusaiba tace “ai munsan murna kike da tafiyarmu.”
Goggo tace “ni mikon ayaba a kitchen da alama neman magana kikeso.”

Nusaiba ta wuce kitchen ta dawo da ayaba ta mika mata.
Goggo ta amsa ta maida idanta kan tv.

*************

Zainab ce tai knocking din glass din baya, Khalid ya bude motar ta bude ta shiga.
Zama tai sannan ta kalleshi a ranta tace baya gajiya da zama a mota?
Khalid ne ya tada motar sannan yace “muje?”
Tace eh.
Nan ya fara tafiya, shiru sukai a mota kafin wayar Khalid tai ringing, dauka yana a handsfree yace “Salmanu zan kiraka.”
Yana neman kashewa cikin tashin hankali yaji Salmanu yace “Khalid yanzu bayan munyi eaya na fito zanje siyo kunun aya, naga Asiya a hanyar gidanmu.”
Asiya?
Khalid ya tambaya, Salmanu yace eh? Wai tsaytsayi ya samu Abba, da alama bandaki ya shiga ya nemi bin bango da kanshi ya fadi.

Cikin tsananin tashin hankali Khalid yace “yanzu Abban yana ina?”
Ya fada yana neman daukan wayar dan ya kashe handfree din.
Salmanu yace “munje Chemist sunce mu wuce asibiti cikin gaggawa, to gashi munzo asibitin su kuma sun ki karbarmu tukunna.”

Khalid hankali a tashe yace “bari na taho, zanzo yanzu.”

Zainab da tunda aka fara wayar hankalinta ke kan Khalid tana ganin ya ajiye ga kalleshi.
Juyowa yai ya kalleta yace “am soryy bansan ya za’ai ba Abbana ne bashida lafiya da alama dole naje.”
Kai ta daga alamar to sannan tace “amma naji yana cema ba’a karbesu ba.”
Yace “eh zanje inga meza’ai.
Zainab tace “inba damuwa ka kawosu nan asibitin Zaks, mai asibitin matarsa tare mukai makaranta.”

Kallanta yai yace “mungode zanje in abin bai yiwuba sai mu taho nan din, nagode sosai.”
Tace “to ko zaka kaini gida sai ka wuce da motar?”

Kallan mamaki ya mata, kanta ta kawar gefe.
Komawa yai ya zauna daidai sannan ya maida motar titi ya cigaba da tafiya.
Can ya daure yace “ko na maidake station din sai na wuce?”
Tace “a’a zan tafi da kaina, ka wuce.”

Shiru yai yana tunanin halin da Abba yake ciki, yana neman shiga gate tace ya ajiyeta anan, nan yai parking ta fito, harta rufe kofar tai saurin budewa tace “Ohh akwai wani dr Sabir a asibitin Danbatta, ta dauko wayarta tak searching din numbersa sannan ta mika mai wayar tace “ka kirashi zan mai magana yanzu.”

Khalid ya karanta number sannan ya mika mata wayar, kallanta yai tana amsa ta wuce ciki.

Juya kan motar yai ya dau hanyar danbatta.

Zainab na shiga gate ta tsaya ta kira shi, sai da wayar ta kusa katsewa ya daga “Zee?”
Tace “Sabir kana danbatta ne haryanzu?”
Yace “eh nemana kike ne?”
Tace “no abokin mijina ne zai nemeka yanzu plz.”
Yace ok, sanin halinta yasan yanzu zata kashe wayar yai saurin cewa “shikenan?”
Tace “akwai wani abu ne?”

Dariya yai yace “Zee kenan, abinda zakicewa wanda ya soki na shekara da shekaru kenan?”
Tace “nagode da taimako.”
Ta kashe wayar, daga can Sabir ya kalli wayar tare dayin murmushi yace “Zee kenan”

*******

Sai da sukai nisa yace “northwest ce?”

Tace “eh.”
Nan suka dau hanya, kallanta yai kadan yace “dazu Nabila ta tsorata ki ko?”

A hankali tace “eh.”
Yace “haka take, halinsu daya da yayarta sai dai ita akwai bin didigi.”

Sadiya tai murmushi tace “meyeasa basa yarda da mutane?”

Adam ya kalleta yace “karki damu da wannan.”
Tace to.
Sai da suka tsaya suka cire kudi ya bata sannan suka karasa northwest yace “in rakaki ne?”

Da sauri tace “a’a zan je in gama, ko zakaje ka dawo? In ma gama sai ma fadama?”

To kawo wayarki na sa miki numberta, nan ta mika mai yar nokia din nan me touch ya amsa ya saka mata sannan yace “inkin gama ki kirani.”

Harzata fita ta juyo tace “yaya nagode sosai.”

Murmushi yai yace “karki damu.”


Shiru tai tana kallansa, wanda harya tsargu yce “menene?”
Tace “ban taba ganin mutum irinka ba.”
Kansa ya shafa yace “ da gaske.”
Ta daga kai alamar eh, tace “irinka mata ke fatan samu? Aunty tayi dace.”
Kallanta yai yace “haka kike tunani?”
Tace eh.
Yace yau ce rana ta farko da wani ya fadan haka, kowa cewa yake nayi dace.”
Kai ta girgiza da sauri tace “duk da bansan halayen mutane sosai ba amma nasan itace tai dace, itama tanada kirki sosai ina kuma mata godiya.”

Washe baki yai, wayarta ce ta fadi tagun kafarsa, da sauri tasa hannu zata dauka, shima yakai hannu zai dauka hannayensu ne

Please Login or Register in order to submit comment