Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yi na yan dakiku kafin yace “tayi abinda tai ne saboda daukar fansar abinda Adam yama yayarta, ya rabu da ita saboda ke, in da hali ki yafe mata yarinyar has a difficult life.”

Shiru tai tana kallansa maimakon ta bashi amsar tambayar dayai mata sai jiyai tace “Ya zakai dasu Kabir?”

Kallanta yai yace “ya zanyi?”

Tace “eh I don’t plan to forgive them, sannan in har bai nemi yafiyar abinda ya mana ba banaji hankalina zai kwanta.”

Taya zaki dau matakin?

Shiru tai tana kokarin tattaro dauriyar ta, kallansa tai cikin dakewa kamar wanda gabanta ba faduwa yake ba tace “Dady zai bude min Tv station, sai dai bazai budemin ba sai nayi aure, anda ni yanzu banida plan na auran wani duba da yanayin yanda rayuwata take, bazan iya cigaba da ganin mutum azzalumi kamarsa yana cigaba da yin abinda yaga dama ba.”

So? Ya fada yana kallanta.

Kallansa ta sakeyi tace “i need your help.”

Ni?

Tace “eh me kake gani idan ka aureni?”
Dan yawon bakinta ta hadiya tace “ka aureni muyi aiki a tare a tv station din da Dady zai bude.”

Gaba daya maganar tazo mai sama ta ka dan har yama kasa cewa komai sai kallanta kawai da yake.

Ganin yanda yake kallanta yasa tace “ nasan yanda zakaji abin, amma na duba naga hakan ne kadai mafita daga ni har kai.”

Har ni?

Tace “eh, da farko bakada aiki kabar su Umma da tunanin kanada shi, sannan bakada tabbas din samun aiki nan da shekara uku ma nan gaba, haka zaka cigaba da yi musu karyar kana aiki? Haka zaka cigaba da rayuwarka?”


Samun kansa yai da wani murmushi sannan ya juyo sosai yana kallanta yace “sai na aureki a matsayin jari na?”

Shiru tai kafin tace “jari?”

Yace “Ba hakan bane? In aureki a matsayin me? Wanda kikeso? Wanda kike bukata? Ko wanda kike neman cika burinki dashi?”

Tace “koma menene zaka iya yin tunanin dakaga yama, amma kasan bada wata manufa na fadi hakan ba.”

Yce “okay mu barshi da zuciya daya kika fada, why me?”

Shiru tai kafin tace “kai kadai na yadda dashi.”

Wani murmushi ya sakeyi yace “kinsan halinane? Ta ina zaki yadda dani?”

Kallansa tai batai magana ba sai dai ta fara karzar farcenta.

Kallan hannunta yai sannan yace “kinasan muyi auren karya kenan ko me?”

Kallansa tai cikin dakewa itama tace “in ka fassarashi da karyar kenan.”

“In ban fassara ba fa?”


Ya fada yana kallanta sannan yace “in kuma naji inada wacce nakesan aura fa?”

“Sai ka aureta”

Haka kawai ya samu kansa dajin haushin wannan amsar.

Maimaitata yai yace “sai na aureta?”

Tace “eh, ra’ayinka ne, sannan kai mijin mace hudu ne, ban nemi komai daga gareka ba, let’s work as a partners, sannan nasan kafi kowa kishin kanka bazaka yadda da kudin da wani zai baka ba halak dinka ba, bazan shiga hakkinka ba balle na takura ma ba.”

Wani wahalalen murmushi yai yace “in kuma ban yadda fa?”

Yanayin fuskarta ne ya canza ta kalleshi.

Kallanta yai yace “meyasa kikesan yanke hukunci akan rayuwar wani?”

Rayuwar wani?

Yace “eh, aji ace na yadda munyi aure, in dawo gidanki in zauna in je gun aikin da yake mallakinki, me ya rage min keman?”

Kallansa tai tace “gun aiki daukanka nai kamar yanda nake da damar daukan duk wanda naga dama.”

Yace “Uhm hm”

Tace “wai kai bazaka taba bari ai nasara akan ka ba?”

Dan lebansa na kasa ya lasa kadan yace “bakya tunanin rayuwar da kike neman jefa kanki?”

Tace “ wace rayuwa?”

Taya zaki dauki daukan fansa a maimakon farincikin rayuwarki? Baki taba tunanin yin aure dan farin cikinki ba?”

“Bansan wannan ba, ban kuma nemi abinda ba zan samu ba, na sani ba wanda zai soni a yanda nake, tun daga kan hallayena har zuwa yanda tsarina yake, duk wanda zai aureni da wata manufar zai aureni, that’s why i choose you, ko zaka cuceni kamar yanda kace zakai a kalla nine na zabi ka cucenin sannan a kalla nasan tarbiyyar daka samu bazaka kawo mace cikin gida da sunan kanwarka ba.”


Wasu zaffafan hawaye ne suka zubo mata wanda yasa zuciyarsa yin rauni, wace irin rayuwa ta daura wa kanta?

Sharewa tai tace “kaci abinci Dady da matar gidan sunyi hidima gun shiryashi.”


Shiru yai haryanzu yana kallanta.........


******
Ayusher🏌🏻‍♀
[12/22, 8:58 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     .........................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

Gaisuwa Batuul Maman🥰 Wish you Allah's Khair and Noor

{49}

Idanu kawai ya zuba mata, ganin yanda yake kallanta yasa tace "menene?"

Wani murmushin takaici yai yace "haka kika dau rayuwar?"

Cikin dakewa tace "eh, ba hakan take ba?”

Kai ya jinjina sannan ya mike tsaye yace "am sorry amma bazan iya yin abinda kikeso ba."

Kallansa tai ta kafeshi da ido cikin wani yanayi na jin haushine karara cikin idanunta, idanta ya ciciko yana neman kawo kwalla.

Yana kallanta da idanunsa da sukai dan jaa yace “did i hurt your pride?”

Batace komai ba sai dai haryanzu idanunta da kallan da take mai yana bata janyesu ba, yace “nima you hurt my pride.”


Kansa ya dauke saboda rauni da zuciyarsa ta fara yi taya zata zata ce ya aureta da kanta sannan bawai a dalilin komai ba sai akan aikinta? Taya zata.....kanta ta kawar gefe tasa hannu ta tadan maida kwallarta, tace "kaci abincin, a kalla baka wulakantasu ba su."

Juyowa yai ya kalleta, kanta na gefe ya koma ya zaune tare dayin shiru.

Sun danyi shiru na yan dakiku kafin yace "me ya kaiki yin wannan hukuncin mara ma'ana? Taya zaki nemi ruguza rayuwarki saboda daukan fansa?”

Kanta na gefe itama tace "ya bazanyi ba? bayan mutanen can basuda hankali? In ba hauka na kansu ba meye na sako rayuwar aurena a cikin haukarsu? Meye damuwarsu da rayuwata? Aiki nake nayi iya yina ta ya zan yafe musu na hauka da jahilcin da suka nuna karara?”

Bata jira amsarsa ba tace "sannan duba wani hauka na san akoreka da sukai? Taya zasuce ka sanar da wani sirrin cikin gida?"

Kallanta yai yace "akanshi ne kawai?"

Juyowa tai itama tace "kasan wahalar danasha kafin gun ya koma haka?

Idanunsa na kanta yace "I thought ke kika sa kanki?"

Wani takaicine ya kamata ta dau pillow din dake gefenta, kallanta yai yace "ba dai makamin za'ai ba?"

Harararsa tai ta ajiye pillow din a kasa tare da cewa "kaci abinci naga alama in na kara minti biyar anan zuciyata ce zata buga saboda jin bakaken maganganu."

"Ni da kika yaba min bakaken maganganun fa? ince me?"

Kallansa ta sake tace "yaushe? Me nace?"

Kansa ya dauke, mikewa tai ta fita.

Da kallo ya bita cikin tausayawa rayuwarta.

Daga kofa yaji tace “Dady?”

Dady ne ya kalleta yana dariya yace “Zainab? Yana ciki?”

Cikin mamaki tace “naga lokacin tashi baiyi ba.”

Yana dariya yace “sai lokaci yayi? Ai yai dole na fito nazo mu gaisa da sirikina.”

Siriki?
Ta maimaita cikin mamaki, da sauri tace “Dady muje falanka inada magana.”

Kallanta yai yace “mayi daga baya, dan inada meeting, saboda mu gaisa na zo, yanzu zan koma.” Ai kafin ma ta sake magana ya tura kofar glass din.

Khalid ne ya mike tsaye da sauri, Dady ne ya karasa yana kallan Khalid cikin tsananin jin dadi, yace “tunda tacemin nasan bakon jikina ke bani kaine saboda ba kowa dana sani ta bangarenta inba kaiba, ganin kai din ne da gaske ya sani kara jin dadi.” Ya karaso inda Khalid yake cikin tsananin jin dadi.

Khalid ne ya tsuguna a kasa yana gaisheshi.

Dady ya zauna a kasa kusa dashi yana amsawa cikin tsananin farin cikin dani kaina na da dade banganshi a fuskarsa ba.

Khalid ya kalla yace “Zauna sosai.”

Khalid ya zauna samun kansa yai da kunyarsa, Dady ya jawo plate ya mika mai shima ya dau daya, kallan Khalid yai yace “dan zuba mana abinci”

Khalid ya shiga bubudewa yana cikin wani yanayi da bai taba fuskantar kansa ba ko a lokacin yin interview ne kuwa.

Dady kam dadi duk ya hanashi sukuni, Khalid ya kalla yace “shinkafar ta isa haka nan zubamin ganyen dayawa.”

Nan ya ajiye mai, Dady nata matsa kafarsa, Khalid ne ya kalleshi yace “ciwo take?”

Murmushi yai tare da daukan spoon, suka fara cin abinci, shikam dai Khalid ci kawai yake duk jinshi yake daban.

Ganin yanda kafar Dady din ta tashi yasa Khalid yai shiru.

Dady ya sha kunun aya mai sanyi sannan ya kalleshi yana murmushi yace “ba wani abin bane, ciwon sugar ne kasan in muka zauna sosai ko mukai tafiya dayawa sai tadan hau.

Sugar?

Khalid ya maimaita jiki a sanyaye dan yasan yanda ciwon ke da ila, kallansa yai yace “amma ba hawan jini ko?”

Dady yai murmushi, wanda yake nuna akwai.

Cup dinsa ya ajiye gaba daya jikinsa yai sanyi, Dady yana murmushi yace “ Khalid nagode sosai sosai, magana ta gaskiya tun farkon ganinka nai sha’awar dakewarka, jajircewarka da kuma nutsuwarka.
Nagode sosai da ajiyeta agidanku da kai kafin nazo, zannan nagode sosai dan ta dalilinka ne muka shirya ni da ita.
A koda yaushe ina ma Addu’ar dace wa a rayuwarka, sai kayi hakuri da ita batasan yanda zata nuna jin dadi ko fadar magana yanda ya dace ba, duk laifi nane.
Ita ta raini kanta, har takai wannan matakin shiyasa a koda yaushe bata tunanin halin da dan uwanta zai shiga nata kawai ta sani, nasan zaka gyara mata halayenta, a matsayina na mahaifinta na gaza.”

Hawayensa ya share wanda suka dan gangaro ta kwarmin idansa.

Khalid kansa na kasa baice komai ba sai dai gaba daya jikinsa yayi sanyi, zuciyarsa duk ta karaya.

Dady ne ya cigaba “daga haduwarku da Zainab zuwa yanzu ta canza halaye da dama, duk da kai bazaka gani ba amma mu munsan ta canza wanda ita kanta batasan ta canza ba, shiyasa ina jin tace na san bakon na shiga fatan Allah yasa kaine.”

Yad’anyi ajiyar zuciya yace “nagode sosai da sosai Khalid, ina ji a jikina rayuwar da zatai yanzu bayan ta aureka rayuwace mai tattare da farin ciki da jin dadi, yau tun safe in na tuna hakan sai naji farin ciki.”

Aure? Abinda ya fada a ransa kenan da sauri ya kalli Dady.

Dady ne yai murmushi yace “Nagode sosai Khalid, ina tunanin yaushe kake ganin ya dace muga juna da iyayenka?”

Iyayena? Abinda ya fada kenan? Dady yce “eh, ko yayi wuri?”

Gaba daya Khalid ya rasa me zaice, Dady ne yace “ka duba ka gani, dan matsalar muna bacci muna tashi ne bamu san sanda rayuwarmu zata kare ba, sannan kullum lokacin mu kara tafiya yakeyi, muna rayuwa ne bama duba hakan, duk sanda mukai bacci muka tashi to fa kwana daya daga cikin rayuwarmu ta ragu ne, ya kamata a koda yaushe mu dinga tuna lokacinmu tafiya yake, bansan dogon buri amma ina fatan ganin jikana kafin tawa rayuwar ta kare.”

(Allah yasa mu cika da imani Ameen)

Jikin Khalid ne yai sanyi sosai, me zaice? Ta ina zai iya cewa wani abu a wannan yanayin?

Dady ne ya kalleshi tare da mai murmushi yace “ me kake gani in ka kwana anan? Akwai BQ a ta baya, gobe sai ka koma?”

Khalid yace “ a’a bakomai zan wuce dan anjima.”

Dady yace “to ko musai flight ticket? Dan tafiyar akwai nisa.”

Khalid yai murmushi yace “bakomai zan koma a mota.”

Dady bai musa ba ya jinjina kai yace “ba laifi hakan.” Agoggo ya kalla, yace “dole zan koma office inada meeting nan da 10min, bani number dinka, sannan in ka isa ka sanar damu ka isa lafiya, sanda kuka gaya dace na haduwar sai ku fadamana.”

Amsar wayar yai ya samai sannan ya kira wayarsa ya mika mai.

Dady ya amsa cikin jin dadi ya mike yana cewa “kaci snacks din.”

Khalid ya mike shima yana mai sallama, hannunsa Dady ya kamo wanda hakan yasa Khalid kallansa, Dady cikin jin dadi yace “nagode.”

Juyawa yai ya fita Khalid ya zauna akan kujera tare da sa hannu ya rufe fuskarsa yana tunani abinda ke faruwa.

********

Zainab najin alamar fitowar Dady daga falo ta gangaro da gudu dan dama sallah kawai tai a daki ta fito tana jiransa, sai dai kafin ta sauko ya fice.

Mikewa khalid yai ya dan shiga toilet din dake falan ya kuskure bakinsa sannan ya tada sallah.

Zainab tana ganin ya tafi tai falo da sauri inda Basma take, kallanta tai tace “Hmm Dady yace miki wani abu?”

Tace “a’a wani abin ya faru ne?”

Tace “a’a”

Juyawa tai gaba daya tana san fahimtar meke faruwa ita dai batace ma Dady siriki ba bako tace, yaushe sunan bako ya koma miji? Da wani ido kuma zata sake kallansa? Salan ya kara maka mata wata bakar maganar?

Hannuta tasa tadan dafa goshinta sannan ta nufi falan.

Jin tayi sallama shiru yasa tadan turo kofar, ruku’u yake lokacin, ido ta zubamai haka kawai ta samu kanta da kallansa, a hankali ta dan lumshe idanunta sannan ta tsaya a jikin kofar.

Bayan ya idar ne ya kalli inda take, shi kansa ido ya zuba mata kawai ya samu kansa da mata addu’a samun farin ciki a rayuwarta.

Idanunta ta bude kamar wanda akace ta juyo suka hada ido, da sauri ya janye nasa idan itama ta dauke nata tare da shigowa ciki.

Daga can kujerar farko ta zauna a saman hannun kujerar kallansa tai da idanunta yan madaidaita, ta bude bakinta wanda yake dan karami cikin yanayin burin kunya tace “me Dady ya ce ma?”

Mikewa yai yana nike sallayar yace “abinda kika cemai?”

Juyowa tai tace “abinda nacemai?”

Dan kansa ya karkatar yace “badai cemin zakiyi bakice komai ba?”

Hade fuska tai tace “kaji na musa?”

Kallanta ya sakeyi yana tuno kalaman mahaifinta yace “Hakan kikeso?”

Mefa?

Ki aureni saboda aikinki?

Dakewa tai tace “eh.”

Kai ya jinjina yace “okay, let’s get married.”

Kallansa tai da sauri, wani murmushin takaici ya saki yace “amma karkiyi tunanin na amince saboda wani tunani naki na can daban, sannan na amince saboda mahaifinki ba ke ba, sannan na amince ne saboda ni karan kaina.”

Idanu gaba daya ta zuba mai, yace “aiki? Kiyi aiki har ila masha Allah, sai dai zan sanar dake abu biyu, abu na farko bazanyi aiki a tv station dinki ba in ma harta kama zanyi sai dai nabi sawon masu jarabawa nayi in naci na fara, sannan abu na biyu, gidanki bazan zauna a ciki ba in har kuma na zauna a ciki to zan tambayi nawa ne kudin hayar gidanki, in har naga zan iya shima kenan in ba haka ba sai dai ki hakura da gidan, sannan abu na karshe....”

Shiru yai yana kallanta, wacce itama kallansa take, yace “wannan sai bayan auran zan fada miki.”

Yana kaiwa nan ya dau wayarsa tare da nufota hanyar waje.

Sai daya zo daf da ita tace “Bazaka tabi bari koda wasa ai nasara akanka ba?”

Tsayawa yai ya kallo gefen da take zuciyarshi na kara takaici auren da take neman yi da shi saboda aikinta.

Kallanta yai yace “meyasa kika auri Adam?”

Shiru tai shima bai nemi amsar ta ba yace “ meyasa kika dau aure abin wasan yara?”

Yaushe nace ma haka?

Dan kansa ya juyar kadan tare da dawo dashi inda take yai yace “ inba wasan yara ba kin auri Adam saboda kina san samun mijin da zaki juya wanda bazai nemi hanaki aikinki ba wanda zai zama karkashinki bazai taba yi miki magana akan yawan aikin da kike ba, ba haka bane?”

Bata rai tai matuka bakinta ya shiga rawa, ta kafeshi da ido, yace “ni kuma yanzu kina neman yi dani saboda ba wani wanda kike gani a kusa? Ba haka bane?”

Mikewa tai a zuciye tace “haka nacema?”

Juyowa yai gaba daya yace “ba hakan bane? Ke da kanki kikace saboda aikinki, sannan kika bani damar yin aure sanda naso ba haka bane?”
Zuciyarta ce ta shiga tafasa tana sauketa, tace “ko hakan ne sai ka fadamin ta wannan muryar?”

Murmushi yai yace “oh na manta ashe ke order kika saba badawa bakya san a baki, amma ya zamuyi? Dan nima ba abinda na tsana irin a dinga bani order balle akan rayuwata.”

Cikin kufula tace “In bakayi kace bakayi sai ka fadamin kalamai marasa dadi?”

Ido ya zuba mata, yace “me kike tunani?”

Haushi ne ya kara cikata ji take kamar tai ihu saboda yanda zuciyarta ke tafasa.

Kasa cigaba tai saboda yanayin rauni da zuciyarta tai, kallanta yai shima tashi zuciyar na rauni yace “am sorry in kinji zafi, but ko zan sake maimaitawa abinda zan fada kenan, nagode da karba kirki kimin godiya, zan wuce.”

Tana tsaye har ya fita daga falan, shiru yai bayan ya rufe kofar, na mata tsauri? Abinda ya tambayi kansa kenan, yawon bakinsa ya hadiya sannan ya fita, yaso yace tawa matar babansu magana suyi sallama amma baisan ya sake shiga dan kila sai sun sake wani fadan.

Fita yai kawai ya bar gidan ya nufi tasha.

******

Zainab kam ko kafa daya ta kasa dagawa tana maimaita kalaman Khalid, cikin kufula ta fito tai sama da sauri tana shiga daki ta rufo kofar da key ta kwanta akan gado.

Tunda take a rayuwarta an taba fada mata bakaken kalamai irin na yau?

Meyasa ta cigaba da tsayawa tanajin kalamansa masu kona mata rai? Ai da sai tabar gun.

Idanunta ne suka ciciko kawai ta samu kanta da zubar da kwalla.


(Khalid gaskiya ka kama kanka🙄)

**********

Haka ya shiga mota yana tafe gaba daya zuciyarsa ba dadi, taya zata tunkareshi da aure saboda aikinta? Kenan haka sukai da Adam?

Meyasa take sa aiki a saman aurenta?

Idanunsa ya rufe zuciyarsa duk a dagule.


**********

Wanke kwanuka take a bakin rijiyar amma hankalinta nakan su Asabe dake cin dan wake, cikinta ne yai wani kara, takaici ya kamata wannan tsinaniyar Safiyan ta basu dubu goma tace zata kara musu amma gashi har yau sati daya kenan basuda ko sisi a gidan.

Kallansu Asabe tai wanda suka dauke kai gefe suma suna jin haushin ta, dan sanda sunada kudi haka zasu jiyo kamshin abinci amma ko yar mitsilar roba bata taba san musu ba dan haka itama lokacin ramawarta ne.

Cikin daki ta shiga Adam ta gani a zaune akan katifarsa, rike da waya haushi ya kamata ta kasa kusa dashi ta talle keyarsa.

Dagowa yai da sauri yace “Goggo lafiyarki? Wai ni ya na zama saurayi amma baki da aiki sai makeni?”

Wani banzan kallo tamai tace “saurayi agidan uban wa? Ka tashi ka nemo mana abinci ko sai na saka a gaba nata maka?”

Ina zan nemo?

Tace “nikam mun shiga uku bama zancen abinci ya kamata muyi ba zancen kudin haya ya kamata muyi, jibi kace ko?”

Yace “eh yazakiyi yanzu?”

“Ya zanyi? Da yake ni kadai nake zama ba dole ka fadamin zancen banza ba.”

Kallanta yai yace “to ai ni kinsan bani da hanyar damun kudi.”

Kallansa tai tace “Adam me kake gani in kace wannan Safiya ko Afaro take ta nemoma aiki?”

Kallanta yai, yace “ko?”

Tace “eh mana ba kace Driver din nan take so ba zata iya komai akansa? Ka hada yar dabara kace zaka hadasu a zance kadan cafki rabanka.”

Kai ya jinjina yace “aikam to amma wani irin aiki? Nifa kinsan bansan aikin wahala nafisan na ganni a zaune a gikin makeken office dina ina juyi akan kujera, ga sanyi AC na kadani, in na taso daga mota na wuce gun Matata Zainab na dauko nasara a mora mu dawo......”

Kansa ta sake tallewa tace “kai dai bakada hankali wlh, naga randa hankali zai shiga jikinka.”

Kwanciya yai rigingine yace “Goggo?”

Meye?

Dan Allah Zainab bata hadu ba? Duk da ba fara bace sosai amma ba baka bace can, sannan tanada dan kumarinta dai dai, ga dan tsayinta daidai, ga idanunta yar caras........”

Kamin shiru ko sai na sa muciya nai ta makama? Dan ubanka kasan da hakan kaje kai lalata da wata can kedara? Banda haske me tafi Zainab? Sannan yanzu kazo ka sani a gaba kana min tatsuniya?


Ajiyar zuciya yai, tace “maganar nan dana ma wlh ta tafi da komai na cikina, Adam taimaka ka samo mana ko bread ne mu cucusa, yasin yunwa zatamin illa.”

Kawo lace dinki.

Shiru tai tace “in zani wani gurin in sa me?”

Yace “kisa atamfa dolene sai kinsa wannan?”

Cikin takaici tace “Allah sarki Zainab sai dai kawai naga kudi ko kaya, wannan wannan ni dai ka cuceni wlh.”

Adam yace “kawo lace nidai dan nima yunwa ta gama tattare ni.”

Haka Goggo ta dauko lace din, tana ja Adam na ja haka ya fizge yai waje dashi.

Zama tai cikin takaici da jin haushin rayuwarsu.


******
Ayusher🏌🏻‍♀

*******
[12/23, 9:37 PM] +234 706 813 0709: 🍀A GIDANA🍀
.........................

*H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

   Wattpad link👉🏻  https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

Gaisuwa da Godiya gareki Maman Haneef 🥰ZeeKhalid na gaisuwa🤝
Ina kike Twins din Zainab😉? Tana godiya da zazzafan kaunarki gareta, jiya har rasa bakin magana tai da ina zanzaro mata tsananin kaunar da kike mata🤪Aka Biebie


{50}


Duk yanda yaso yau bacci ya daukeshi ya kasayi sai juyi yake akan dan karamin gadansa, ganin bacci yaki daukansa kawai ya mike ya fara karatun Qur’ani, cikin falalar karatun yaji bacci ya daukeshi.

Yana sallar asuba ya wuce daga can zuwa gun aikin da zasuyi, ya riga kowa zuwa haka ya fara aikin kafin su karaso har sai karfe 1, ya wuce cafe ya dukufa neman aiki, yana gamawa ya wuce shagon dayake zama sai magrib lis ya dawo.

A tsakargida ya tadda su Umma, sunyi dan malele ana zaune ana ci da yaji da manja suna hirarsu.

Yana shiga suka kalleshi cikin kulawa, karasowa yai ya xauna a gefen tabarma yana dariya yace “Umma yau kuma dan malele ake ci?”

“Kai dama ba kwanan ka anan, ga dai shinkafarkacan da wake aci lafiya.” Umma ta fada tana kallan Abba tacigaba “ku dai maza wlh sai a hankali, ni banga me dan malele yai ba.”

Abba ne ya kalli Khalid yana dariya tare da rage sautin radio dinsa yace “ku dai tunda kunaso kuci ni kam da inci abin nan gwara a bani kwadan kanzo.”

Khalid ya dauko kwanan sa da spoon ya zauna yana kallan su Amir da ko magana basayi sai cin abinsu, Asiya ya kalla wacce ta buda yaji dayawa a nata dai shishitun yaji take yace “sannu wannan uban yaji haka?”

Ruwa tasha tace “Yaya yaji.”

Zama yai tare da ajiye ledar bread din daya siyo, ya sa spoon yai shiru tunda yakai loma daya bai sake sa wani ba da alama ya tafi wani tunanin daban.

Umma ce ta kalli Abba, shima ya kalleta sannan suka maida kallansu kan Khalid.

Umma tace “Khalid lafiya?”

Kallansu yai yas murmushi sannan ya dau spoon din ya cigaba da ci.

Sai daya gama yasha ruwa ya shiga dakinsa yai sallah sannan ya dawo, lokacin daga Umma sai Abba a wajen, su Amir anyi bacci da alama Asiya tana daki.

Zama yai sannan ya kalli Abba sannan ya kalli Umma yace “Abba akwai abinda nake san fada muku.”

Hankulansu suka maida kanshi gaba dayansu, shiru yadanyi kafin ya dago yace “Umma me kuke gani in na kawo muku sirika nan kusa?”

Kallan Abba tai tace “sirika?” Da sauri ta sake cewa “aure?”

Dan kansa ya sosa tare da dan kallan Abba.

Dariya Umma tasa cikin jin dadi tace masha Allah, burin mu ya kusa ciki, masha Allah.

Abba cikin jin dadi yace “kayi tunani kyau, a ina take?”

Dan kallansa yai yace “kun santa.”

Mun santa? Suka fada a tare, yace “Zainab.”

Yanayin fuskar Umma ce ta canza tace “Zainab?”

Yace “Umm!”

Abba ne ya kalleta sannan ya kalli Khalid yace “tashi kaje.”

Mikewa Khalid yai cikin rashin fahimtar me Umma take nufi.
Kallanta Abba yai bayan yaga tafiyar Khalid yace “meke faruwa?”
Kallansa tai tace “ina san Zainab har raina kaima ka sani amma Khalid fa bai taba aure ba?”

Ajiyar zuciya Abba yai yace “ku mata kuna da taku matsalar, sai kuso mutum kamar me amma daga ta hadoku da ‘ya’ya sai ku fara canzawa, sam akan ‘ya’yan cikin ku sai ku nemi rufe ido, dan bazawara ce sai akai me?

Please Login or Register in order to submit comment