Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kamar baya jin dadi."

Da sauri Umma tace "meke damunshi?"

Kai Khalid ya daga alamar rashin sani sannan yace "ban sani ba wlh haka dai nakeji."

Umma ta kalleshi zuciyarta duk ba dadi, dan maganar gaskiya tana san zama da yarinyar ta fahimci tana da tabo na rashin uwa ga kuma takaicin namiji.

Abba ne ya kalleta ya sani sarai zuciyarta ba dadi sai dai ya zasuyi? Kallan Khalid yai yace "bari a kirata na mata magana."

Da sauri yace "bari na mata magana."

Kallansa sukai cikin mamaki, shikuwa yasan halinta dan zaman nan da sukai ya tabbata aka mata lagwalagwa ba abinda zai faru.

Knocking din dakin yai, daga ciki tana zaure rike da takardar Adam tace "waye."

Khalid yace "nine."
Mamaki ne ya kamata tace "ya akai?"
Magana zamuyi.

Umma ce ta mike tace "ko na mata magana?"

Khalid ya girgiza kai alamar a'a daga ciki tasa hijab sannan tace "shigo."

Tura kofar yai ya shiga a bakin kofar ya tsaya yace "kizo na kaiki kano, ku wuce da babanki."

Kallansa tai cikin mamaki tace "in wuce ina?"

Gidanku!

Fuska ta hade sosai tace "a matsayinka nawa kenan?"

"Na d'an gidan nan"

Baki ta bude cikin kuluwa da takaici tace "da nace ba d'an gidan nan bane kai?"

Yace "tambayarki haka ta nuna min."

Wata dariyar takaici tai sannan tace "korata kake kenan kome?"

Yace "ba korarki nai ba ina nufin ki bi babanki."

"Nafi karfin ka wulakantani wlh."

Wani mugun kallo tamai ta mike a tsananin zuciya ko kayanta bata dauka ba kawai wayarta da laptop da tab dinta ta dauka ta fito rai a bace.

Kofa ya bude mata alamar hanya, tsayawa tai tana kallansa cikin takaici kafin tai kwafa.

Umma ta gani a tsaye a falo, Umma na ganinta ta matso tace "Zainab."

Zainab tai kasa dakai idanunta suka fara neman rauni, dakewa tai tace "Umma zan wuce."

Tana fada tai hanyar neman fita, da sauri Umma ta rikota sannan ta dago da ita tace "ba korarki mukai ba Zainab, nikaina inasan zamanki anan sai dai ba yanda zanyi."

Kallan Khalid tai kenan shiya kawo wannan maganar?
Abba ta tsuguna tawa sallama sannan ta kalli Umma tace "nagode muku Allah ya saka da alkairi."

Umma ta dauko yar wayarta tace "samin numberki."

Nan Zainab tasawa Umma ta kira wayarta dashi sannan ta kalli Abba tace "Allah ya kara lafiya."

Khalid ta kalla wanda ke tsaye jikin kofar dakin Asiya, wani takaici ne ya kamata ta sake sallama da Abba ta fito.

Umma har tsakar gida ta rakora tana neman fita waje Zainab tace takoma.

Kayan abincin da aka kawo Khalid ya fito dasu, kalan Umma tai tace "Umma ki taimaka ki bar wadan nan dan Allah badan ni ba."

Jikin Umma ne yai sanyi, ta jawo Zainab ta rungume idanunta harda hawaye, Zainab ta share nata da sauri tace "Umma ki taimaka."

Kallan Khalid tai tace ya barsu.

Khalid ne ya fito waje, yana neman bude mota, kallansa tai tace "bani makulina."

Kallanta yai sannan ya kalli motar yace "wazai kaiki?"

"Banaji wannan ya dameka tunda motatace."

Kallanta yai yace "ki bari na kaiki tukun."

"Motarnan tawace sannan jikina ne banaji akwai damuwarka akai, bani."
Ta karasa tare da mikamai hannu,

Bai tanka taba ya shiga motar ya zauna, haushi ya kamata ta bude motar inda yake tace "fito."

Yace "shigo."

Tace "Malam fito ko?"

Yace "Malama shigo ko?"

Jitake kamar ta shakeshi, hankalinta harya kwanta zamanta anan ya koreta kuma yanzu yazo yana wani abu?

Kallanta yai yace "dare nayi."

Ranta a tsananin bace ta bude ta shiga baya yaja suka tafi, har suka isa ba wanda yawa wani magana, kaini gidana.

Kallanta yai yace "kamar......."

Kaini nace, kome zan da rayuwata ba damuwarka bane."

Dauke kai yai yana kaita gidanta ta amshi key sannan ta kalleshi ta wuce ciki.

Bala da gudu ya bude mata tana shiga tama Khalid text "You are Fired."

Yana fita ya gani, kallan gidan yai jiki a sanyaye sannan ya kira Dady ya fadamai.

Dady cikin jin dadi yahau godiya, alokacin ya taho gidan.

Zainab na zaune a falanta ta hade kafafunta tana kallan gida, komai na gidan bataso gani take komai anyi lalata dashi, kankame jikinta tai kawai tasa kuka.

Dady wanda ya shigo ne ya kalleta cikin tausayi, tana ganinshi tasa kuka sosai, tausayinta ne ya kara kamashi yace "tashi mu wuce saboda ba'asan fita."
Kallansa tai tce "Dady anan zan zauna."

Kallanta yai da sauri yace "bazai yiwu ba."

Tace "to kaini gidan Aunty."

Yace "wai akan me bazaki zo mu tafi ba?"

Kallansa tai ta rasa me zatace, tuno da kalaman Khalid tai wai gidan iyayensa ne, Dady yace "mu tafi kinji?"

Idanu ta runtse kafin ta daga kai.

Haka Suka hada kaya suka wuce Abuja, tunda taje gidan magana ba hadasu take da Basma ba, kullum tana daki kamar yanda ta saba, Basma kuma ta rasa yanda zatai ta shawo kanta, Dady ne inyana nan yake kiranta falo shima da Basma su zauna duk da batama Basman magana ko ta mata a kalla tana amsamai in ya sako maganar Basman

Sai dai hakan ba karamin birgeshi yake ba duk da ba san zaman take ba akalla yanzu tana zama a falan in yana nan.


*******


A can bangarensu Goggo kuwa haka suk nufi kauye ganin ba yanda zasuyi dan dakyar goggo tai bacci ranar a cikin mota, gidan kawu shehu sukaje Goggo ta kalli Adam tace "karka fito da kayan tun kafin a tozartamu mu fara shiga tukun"
Haka suka shiga gidan Kawu shehu, matansa biyu da yaransa su goma sha daya, sai Sadiya dasuka barmai.

Yana zaune a kan tabarmar kaba yana ta kankare kaho yaji ana ihun kawu Adam yazo.

Shiga sukai cikin mamaki kowa ke kallansu, makota sai lekowa ake ta kanga, Goggo nasa kafa ta taka kashin kaza, da sauri ta matsa gefe tafara cewa "matsalata da kauye kenan, kaji ko ina......."

Kallan da Kawu Shehu da matansa suka mata ne yasata tai shiru, haka suka zauna, kowa na musu kallan mamaki, Kawu shehu yace "dama kuna raye? Ai mu tuni muka cire tarihinku."

Goggo tace "wato mutuwa kake so muyi ko me?"

Matarsa Delu tace "tunda danki yai aure kika bishi shekara hudu ko kafarki mun gani? Ko falen atamfa kin aiko mana? A matsayinmu na masu rike miki 'ya."

Dariya Goggo tai tace "Adam ina taliyar da muka siyo dako ka shigo da ita."

Kawu shehu ne yace "basai an shigo da ita ba, meya kawoku?"

Adam yace "dama Goggo ce zata dawo nan da zama."

Delu tace "nan ina?
A wani dakin? Bayan mu kanmu gurin kwana wahala yake mana? Ruwa duk ya cinye mana gini?"

Kawu shehu ne yace "ki koma inda kika fito ki zauna nima yara rasa inda zasu kwanta mukeyi, lokacin da zaki tafi danace ki barmana gidanki me kikace? Hanani kikai a gabana kika saidashi ma abokina."

Goggo tasa dariya tace "wasa yakeyi kamar bakusan Adam ba, Sadiya nazo gani, tunda batanan bari mu wuce."

Har sun shiga mota Delu tace "taliyar, nan Adam ya bude mota dole ya cirota aka shiga da ita ciki."

Suka ja suka tafi, haka Goggo suka je kano wajen gidan Zainab Goggo tana kallan gidan tana hawaye, Dakyar suka samu gidan haya daki daya a cikin katan gida mai dakuna kusan goma ban daki daya daga can kasan unguwar gidan Zainab suka zauna, Haka suka saida motarnan Goggo tasai yar mitsilar tv canjin suka sai kayan abinci suka zauna a gida.

Adam kam takaicin rashin mota sam yasa ko fita bayasanyi, wannan lamari na kona mai rai matukar gaske.

Banda fada shida Goggo kullum ba abinda suke a gidan, haka ya nemi majalisa yake zama, kudin mota kam an sashi a gaba sai ciye ciye akeyi kai kace bazai kareba.

Duk gidan nan Goggo batawa kowa mutumci, dan garkame dakinta takeyi saboda batasan yara suzo mata kallo.

*********

Bayan wata uku..........

Wannan lokaci abubuwa da dama sun canza, su Nabila da Nusaiba an dawo, murna agun Zainab baya musaltuwa, Nabila kam taji bakin ciki dan jitai kamar ta je ta kashe Adam duk da batasan me ya mata ba amma haushin wulakanta hallacin Zainab yasata jin takaici matuka.

Su Khalid anyi Jarabawa, Zainab aka turowa takardun tai marking dan sai data turawa director din email akan ita zata dau ma'aikara dakanta, ganin yanda komai nasu yai kasa daga tafiyarta yasa yake lalabata, ta sanar kar wanda yasa suna sai dai ai amfani da numbers hakan yasa sanda tai marking batasan ko wanene na Khalid ba, sai dai akwai takarda daya wanda ita kanta sai datai bincike a google kafin tai marking dinshi saboda tsabar fasahar da aka rubuta ya wuce tunaninta.

Kusan duk kwana biyu sai tayi waya da Umma sosai wannan wayar ke debe mata kewa, har Allah yai ta kammala iddar ta, sannan ta tura ranar interview ga wadanda suka ci sannan tahau shirin dawowa.

Khalid dake zaune cikin shagon dayake aiki ne sako ya shigo mai, baki ya sake sosai dan bai taba yin jarabawa ance yaje interview ba sai wannan, wayar ya kurawa ido yana kallan sakon dan ya kasa gasgata abinda yake gani.......




*****
Ayusher🏌🏻‍♀
[12/3, 3:52 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀
     .........................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

{37}


  Goggo na zaune adan kucilin falanta da tana kallo, Adam dake kwance a dan mitsilin dakinsu ne yace "Goggo dan Allah rage magana haba, tsakani da Allah kallo da sassafen nan?"

Ranta a bace tace "ka fito ka bar gidan nan ko sai jikinka ya gayama? Ai tun jiya nace ka samo aran yar mota ka kaini gidan Hajiya Bilki."

Komawa yai ya ja bargo baice mata komai ba, haushi ya kamata ta taso ta shigo dakin da karfi ta yaye bargon tace "ko tsinaniya kujera banda ita sai dai na zauna a kasa amma kai ka shige cikin bargo banda uban bacci da yawon banza baka da abinyi."

Cikin kufula yace "koma me nake meya dameki? Ni ki barni da rashin matata dake damuna."

Wani kallan banza tamai tace "har wani rashin matarka? Nawane ragowar kudin mu?"

Kallanta yai yace "wani kudin bayan kin kwacesu?"

Yaushe?

Kallanta yai ya saki baki kafin yace "banasan wasa, wancan satin kikace nawane ragowar kudinmu nace miki dubu dari da ashirin kika ce na kawo miki darin baki yadda dani ba kinji kudin sunyi saurin karewa.

Kanta tadan sosa tace "ina nasa?"

Da sauri ya mike yace "bangane ba."

Hankali a tashe suka fara neman kudi a cikin dakin, hankalin Goggo yayi dubu ya tashi ji take kamar rayuwarta aka gutseri.

Gaba daya kayan dan kayan nasu suka fito dashi waje suna dubawa, sai dai bashi ba labarinsa.

Goggo ta kalli Adam tace “yaushe ka bani?”

Shiru yai yana tunani kafin yace “kamar da safe ne?”

Karya kake wlh, ni baka ban ko ficika ba, bayanda za’ai ka ban makudan kudi nai wazgarere dasu har sati daya bansan inda suke ba.

Gabansa ne ya fadi dan maganar gaskiya ranar ya ciro kudin daga masallaci sai majalisa yaje yana dawowa gida zai bata yaga wayam, kallanta yai yace “ki dai duba Goggo.”

Daga can makotanta ta kalla wadanda kowa ya fito yana kallansu, haushi ya kamata tace “ku kuma me kuke kallo?”

Asabe da dakinta ke kusa da nasu tace “kudai kusan barawon daya dauke a cikin ku dan mu gidan nan ba’a sata.”

Ran Goggo ya baci ta kwashi kaya ta shiga ciki, kallan Adam tai tace “fadamin, uban wa kaba kudin?”

Yace “wai Goggo wa nake dashi da zan ba inba ke ba?”

Zama tai dabas a kasa tace “yanzu ya kake so muyi?”

Yace “nizance haka Goggo yanzu ya zamuyi?”

Takaici ne ya kamata tace “wai uban me ma kake harynzu baka samu aiki ba?”

Ransa ne ya baci ya fita daga gidan, kanta ta rike wanda ke sarawa.

********

Gaba daya sun sa kaya a cikin mota, Nusaiba da Nabila sai murna ake za’abi Zainab.

Zainab dake daki ta kalli dakin, bata taba kawowa zata dawo tai dogon zama a gidan nan ba, duk da wata uku tai amma agunta dogo ne.

Jawo dakin tai ta fito, a falo taga Basma, fuskarta a hade tace “zamu wuce.”

Basma ta matso tace “Dady yace ki kirashi kafin ku wuce.”

To tace batace komai ba daga nan.

Basma tai shiru tanaji suna waya da Dady yana ce mata su tafi da mammab ya dinga kwana a dakin waje kafin asan yanda za’ai dan sam hankalinsa bai kwanta da barinta ita kadai ba, in su Nabila suka taho.

Suna sallama ta kalli Basma tace “mun wuce.”

Da sauri Basma tace “Zainab!”

Tsayawa tai batare da ta kalleta ba, Basma ta dan tako tace “Zainab ki yafemin, sharrin zuciya da sharrin kawaye ne ya sani yin abinda nai, akullum ina danasanin wannan abu, gashi dalilinshi bazan sake haihuwa ba.”


Kallanta tai da sauri, hawayenta ta share tai murmushi tace “hukuncin da Dady yamin kenan”

Gaba daya jikin Zainab ne yai sanyi, tama kasa ko cewa wani abu saboda mamakin wannan zancen.

Basma ta nufi kofa tace “Nusaiba banda fada dake da Nabila.”

Nusaiba ta dan turo baki sannan tace “Mumy mun wuce.”

Haka suka shiga mota Zainab ta shiga Mammab yaja suka tafi, gaba daya jikinta a sanyaye.


*********

Sam Khalid ya kasa gasgata abinda ke faruwa, yana fitowa daga shago ya nufi garage inda suke dan aiki, yana yi yana mamaki, sam zuciyarsa taki amincewa.

Haka ya dawo gida, sai dai sam ya kasa fadawa Umma da Abba, gani yake karsu sa rai azo ba’a dace ba, dan harya gaji da sanar dasu zaije jarabawa sai sun gama sa rai yazo bai samu ba, duk sai yaji ba dadi.

Shiyasa wannan karan ya barma kansa, in haryaje yaga da gaskene aka dace sai ya fada musu, dan ma yanzu hankalinsa ya kwanta ba bashin da ake binsu, duk sun biya, sannan Abba ba laifi in ya rike sanda biyu yana iya dan matsawa daga can zuwa can.

***********

Zufa ce ke karyo mata ta ko’ina, daga yanda take runtse ido zakasan mafarki take mara dadi, jin sautin numfashin Adam da Raziyya ne yasa ta sa hannunta toshe kunenta kafin a hankali ta bude idanunta.

Kwance take a kan gujera a falo, wani abu tadan hadiya tare da kunna fitilar wayarta, duk da Dady da kansa yazo aka kwashe komai aka sa mata sabo na gidan amma ganin komai take kamar yanzu ake yinsa.

Mikewa tai ta kunna watar falan kawai ta dako laptop dinta ta hau aiki, ta shirya abubuwa da dama wanda inta koma za’ai.

Haka tai ta aikinta har asuba tai, sallah tai sannan ta shirya, gadanta ta kalla, duk sanda zata fita yawanci Adam na bacci in bayayi kuwa to yana kitchen yana hada mata tea, wani abu ne mai daci ya zo bakinta hadiye shi tai sannan ta dau jakarta ta fita su Nabila na bacci.

A waje ta tadda Mamman, nan ta gaisheshi suka tafi, a hanya tacemai idan su Nabila sun shirya ka kaisu sumana siyayyar abin gida, yace “to Hajiya.”

Nan suka karasa ta fita tai ciki.

Mutanen dataga sun fara hallara ne tai murmushi tace “is good to be serious.”

Tana shiga station din taga duk staff dinsu a bakin kofa, hadda rike takardar da aka rubuta Welcome back.

Wani irin dadi taji dan dama wata ukun nan kamar mara lafiya tayisu saboda rashin aiki.

Murmushi ne yabayyana a fuskarta nan ta fara amsa gaisuwarsu cikin jin dadi, Head Director ne ya matso yana tafi, yace “barka Zainab yau kamar sallah nake jinta.”
Kallansa tai bayan sun gaisa tace “Yallabai inaji sai mun shiga meeting kafin a fara interview.”

Da sauri yace “an gama Hajiya.”

Nan suka wuce, Ramlatu ta gani ta taho da sauri, kallanta tai da sauri ta gaisheta, Zainab ta amsa sannan sukai ciki.

Sun yi discussing akan abinda zasuyi sannan ta bashi takardun da zaiyi reviewing na abubuwan da za’asuyi nan gaba.

Wani irin dadi yakeji na ganin Zainab balle data kawo abubuwan cigaba yasashi jin wani kwarin gwiwa.

Karfe goma tara daidai ta nufi dakin da za’ai interview kujerar ta ce a tsakiya, tana shiga ta zauna, kallan su tai tace “mu fara?”

Sukace eh,

Kowa ya shigo tana rike da takardar dayai jarabawa da ita, tana mai tambayoyi tana duba takardar, su takwas ne.

Number 5 aka kira, ba tare da ta dago ba ta shiga duba takardarshi, ganin wannan takardar da ta wahalar da ita ne yasa ta kara dudubawa tana kara bin komai, har ya iso ya zauna.

Rufe takardun tai sannan ta dago dan taganshi.

Kallansa tai idanunta suka dan fito, tasan ita tace yai Applying amma bata kawo ya ci ba.

Wulakancin da ya mata ta tuno, fuska ta daure sosai, sannan ta kalleshi, shima kallanta yai fuskarsa daidai ba alamar fara’a ba alamar daurewa.

Takardarsa aka miko mata, ta amsa tana duba sunanshi, skul din dayai result dinsa da sauransu.

Kallansa ta sakeyi, H.Director ne yasa dariya yana kallan takardunsa yace “masha Allah, irin wannan cik exams haka.”

Cikin jin dadi ya kalli Zainab yace “Da alama kema abin ya birgeki.”

Fuska ta hade tamau sannan ta kalleshi tare da ajiye biro din hannunta, nan ta fara watso mai tambaya, amsa yake bata yana kallanta, itama idanshi a kansa take mai tambayar.

Dan kai ta dauke bayan duk ya gama bata amsar tambayoyinta sannan tace “ka tabbatar ba satar amsa kai ba?”

Kallanta yai yace “satar amsa?”

Tace “eh from this naga Math ka karanta, then taya ka bada wannan amsar? Ta fada tana circling din takardarsa shafi na biyu.”

Wani dan murmushi yai tare da dan kauda kai kadan, dan ya fahimci da saninta take watsomai tambaya dan yanda ta dinga jero mai tambayoyi yanda yaga suna kallanta ya tabbatar ba haka tawa kowa ba.

Fuska ta hade tace “Murmushin me kake?”

Kallanta yai yace “da wanda yai satar amsa da masu kula da exams hall din har suka bari akai wanene mai laifi?”

Fuska ta kare daurewa tace “kana nufin satar amsar kai?”

Kallan na kusa da ita yai yace “Sir kasan yanda mukai Exams din nan it seems like she is not there.”

Nan ya mata bayani ba yanda za’ai wani yai satar amsa.

Kallan Khalid tai sannan tace “Idan aka baka aiki a news room ya zakai?”

Nan ya cigaba da bata amsoshinta, sai kara mai tambaya take sai da H.Director yace “Zainab ya isa haka wannan tambaya haka.”

Shiru tai tana mai wani kallo, kallansu yai ganin basa kallansa yadan daga mata kafada alamar ko a jikinshi.

Haushi ya kara tukota ta harareshi tare da cewa “next.”

Fita Khalid yai, har ta bude takarda ta kalli kofar inda ya fita sannan ta cigaba, sai da suka gama sannan ta fito.

A inda suke zaune ta ganshi, dauke kai tai ta wuce.

Shima yi yai kamar bai ganta ba yai gaba.

Tana shiga office dinta ta zauna, Malama shigo? D’an Gidan nan?

Haushi ya kara kamata data tuno maganganun daya watsa mata.

Tana zaune Ramlatu ta shigo dasu saboda ana nunu namusu ko ina.

Zainab tana dagowa suka hada ido, daure fuska tai ta maida kanta kan computer din dake gabanta, nan Ramlatu tace musu “wannan itace Director Zainab nasan kunganta agun Interview.”

Nan kowa ya gaisheta, dagowa tai ta kallesu, har Khalid sannan ta amsa tace “Sai kunji daga garemu.”

Nan suka fita, haka suka gama aka sallamesu akan su koma su jira sai an nemesu.


Khalid na fitowa ya runtse ido yana addu’a cikin zuciyarsa, wani irin yanayi yake ciki wanda shi kadai yasan ya yake ji.

Fitowa yai da sauri dan yaje gida ya kai musu labari.

Yana fitowa yaga wata mota tazo ta wuce, yarinyar dake janta kamar Raziyya.

Da sauri ya kara kallan motae sai dai ta riga ta wuce, shiru yai kafin ya juya ya nufi tasha.


Zainab kam kafadar da Khalid ya daga mata ta tuno wani mugun murmushi ta saki tace “ko a jikinka ko? Let me see in zaka juri wahalar da zan baka.”


Ta saki wani murmushin jin dadi, samun kanta tai cikin nishadi in ta tuno wahalar da zata bashi.


********

Ran Nusaiba a bace ta kalli Nabila tace “wai da gaske Aunty ta koreshi? Nifa Allah saboda shi na dage sai na zo.”

Nabila ta kauda kai tana latsa wayarta tace “aikinyi ne bakidashi wlh, haka a skul kika bi kika ishemu da zancen Ya Khalid kamar kanin Dady.”

Nabila tace “mijina ai yafi kanin Dady a guna.”

Miji? Nabila ta tambaya sannan tace “Allah kanki ba daya ba, da alama kina bukatar ganin likita.”

Ran Nusaiba ya baci tace “sai ki kaini ai.”

Mamman ne yce “ayi hakuri kar ai fada dan Allah.”

Nan kowa ya kauda kai har suka isa Jifatu.

*****

Khalid cikin sauri ya isa gidan, hannunsa rike da ledar ayaba da lemo.

Umma na ta shanyar kayan data wanke ya shigo, cikin jin dadin da ya kasa boyowa yace “Ummana.”

Kallansa tai tare da dan goge hannunta a zaninta tace “Khalid an dawo?”

Cikin jin dadi yace “Umma insha Allahu mun samu aiki.”

Idanun Umma ne suka fifito tace “aiki?” Yanda tai maganar kadai zakasan wani irin yanayi ta shiga mai wuyar fassarawa.

Abba da ya dosanu sandar sa guda biyu yana kokarin fitowa waje ne yce “Aiki Khalid.”

Cikin jin dadi yace “daga Interview nake yanzu.”

Wani irin dadi ne ya kama Umma harda hawayenta.

Fadar irin dadin da suka shiga a wannan lokaci ma wahala ne dan ni kaina nasan Allah ne kadai yasan yanayin da suka shiga duba da irin lokacin daya deba yana gwagwarmayar neman aiki.


(Yan uwa dake neman Aiki irinsu Khalid suma Allah ya dubesu ya basu)



**********

Ayusher🏌🏻‍♀
[12/4, 9:39 PM] Maman Ihsan Whatsapp: 🍀A GIDANA🍀
     .........................

   *H̝a̝s̝k̝e̝ W̝r̝i̝t̝e̝r̝s̝ A̝s̝s̝o̝c̝i̝a̝t̝i̝o̝n̝*

*Wattpad :-AyusherMohd*

Wattpad link👉🏻 https://my.w.tt/FKRWfhajS1

*ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻‍♀*

#OneLove❣

For you my dear Yan Sauyi members🥰Love you soo much🤝


{38}


Tana zaune tana kade sauran dake ta mata yawo akai, haushi duk ya bi ya isheta na rashin wuta da tun shekaran jiya wutar su ta samu matsala, wani uban tsaki taja data kalli taliya da manjan dake gabanta a roba wanda har yayi sanyi ta kasa ci saboda takaicin sauro.

Kofa ta bude ta hau korar sauran, tanaji makotanta nata hira da shewa a waje, wani uban tsaki ta sake jaa tace “ka rasa uban me suke banda zaman gulma.”

Buta ta dauka zata shiga bandaki, da sauri Asabe ta mike ta warce butarta tace “Tsohuwa wannan butar tawa ce”

Kallanta tai tace “wace tsohuwar?”

Asabe tace “to yarinya wannan butar tawa ce.”

Haushi ya kara tike Goggo ta waiga taga bataga butarta ba tace “to uban waye ya daumin tawa butar?”

Asabe tace “sai ki tambayi na gidan amma ba ni ba.”

Ta ja kafarta ta bar gun, Goggo ta hau neman butarta sai dai bata ganta ba, nan ta matso inda suke hira tace “uban waye ya dau min buta?”

Kande ta mata wani kallo tace “sai ki tambayi yaran da kika kira da danki tunda kinfi kowa sanin ba mai dau miki buta anan.”

Takaici ya kama Goggo ta juya rai a bace, waje ta leka, Adam ta gani suna zaune a kujera suna hira, rai a bace tace “Adamu!”

Kalamta yai yace “Goggo.”

Ka mikon butar nan ko kuwa?
Butar dake gefensu ya kalla sannan ya mike ya dauko ya kawo mata, yana shigowa tace “wuce ciki yanzu zan fito.”

Yace “hira muke.”

Ka wuce ko sai na makeka?

Fuska ya hade ya shiga ciki, taliyar data bari ya jawo ya juya ya hau ci, bayan gida ta tsaya yi hakan yasa ya cinye taliyar kafin ta fito, yana lokar karshe ta bude labulen ta shigo.

Kallansa tai tace “uban wa yace kacimin abinci?”

Yace “au zakici? Gani nai tun dazu kika ajiye shi gashi haryai sanyi.”

Ranta a matukar bace ta karaso tace “ni wai dan Allah yaran nan sai yaushe zakai hankali? Gaba daya ni bantaba ganin mutum wanda bashi da tunani ba irinka, kanyar mana da kudi ka kala min karyar ka bani, yanzu yar dubu ashirin din da muka siyo kayan abinci muke cancanawa kaci naka dazu amma yanzu ka tasa nawa ka handame.”

“Yahkuri Goggo na dauka baci zakiyi ba”
“Ko ba ci zanyi ba ai ka bari nace bazanci ba ko?”

Nadai baki hakuri ya isa haka nan.

Ganin zasu sake fadam da kullum suke ciki yasa ta zauna ta kalleshi tace “yanzu

Please Login or Register in order to submit comment