Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tai ta dau abincin da aka zuba tai daki.

Tana zaune a kasa, jikinta duk yai datti, Goggo ta kalleta sannan ta nuna mata toilet da kayan da ta fito dashi, ta juya ta fita.

Adam ya kalleta yace "kiyi wanka kici abinci ki kwanta mayi magana gobe."

Kai ta daga mai alamar to, sannan tace "nagode nagode...."

Hawaye suka zubo mata.

Adam ya juya ya fita....

***********

Tunda tai sallar asuba bata koma ba ta tsaya gyara slide din da zasuyi presenting.
Karfe bakwai ta mike tai mikar gajiya sannan tai wanka ta shirya, Adam na kwance nata sharar baci.

Kayanta ta kwasa ta fito, yana tsaye a waje sanda ta fito, murmushin da batasan dashi bane ya fito, tabbas tanasan mutum taga yasan aikinshi, lalai kasarmu tana cikin wani hali ace masu kwazo da san aiki sune wadanda basuda aikinyi.


Tana shiga yaja suka tafi, ba abinda wani yace a cikinsu har suka isa cikin station din, yana parking tace "yanzu zan fito."

Ba matsala

Abinda yace kenan ya fita.

Ciki ta shiga, tana shiga ta daure fuska sosai, sunyi meeting dinsu sun gama, nan wadanda zaku rakata suka shiga tasu motar sukai gaba akan sai sun hadu acan, dan sun san bata yawo da mutane a motarta.

Zainab na fitowa taji karar text a wayarta, kallan wayar tai ta bude, Wlh Zainab sai naga karshenki, yadda kika koran daga aiki shekara biyu kenan na rasa wani aikin, ni zan zama ajalinki wlh

Tana gama karantawa tai tsaki tare da wucewa ta shiga office dinta, printing dinsu tai sannan ta kara duduba komai ta fito waje.

Mota ta shiga suka dau hanya.

Tun da suka fara tafiya mota ke binsu a baya, Khalid ya kula da hakan sau dai da alama ita bata sani ba tana ta dube dube a tablet.

Daurewa yai yace "tare muke da wadancan?"

Juyawa tai ta kalli bayansu, sannan tace "a'a wadanda muke tare sun wucemu da kusan 20min."

Shiru yai yana kara kallan motar ta glass, kallansa tai tace "menene?"

"Bin mu suke."
Bin mu? Ta maimaita cikin tsoro, text din dazu ne ya fado mata.

Kallanta yai ta glass yace "kinsan su waye?"

Bakinta na rawa tace "a'a"

Tunowa da mai kukan jiya yai, kai ya girgiza da sauri yana cewa may be hanyarce daya.

Jitai yace "bari muyi kamar zamu siya abu muga."

Tace to

Kusa da masu sai da kwan zabi suka tsaya nakan hanya, Khalid ya juya baya, gani yai motar ta tsaya a bayansu kadan, yanzu kam yasan tabbas binsu akeyi, kurawa motar ido yai, maza ne a cikinta kusan guda biyar.

Kallanta yai itama kallansa take, yace "kin ma wasu laifi ne?"
Shiru tai hakan yasa yace "please ki fadamin insan ya zamuyi, ga meeting kina dashi ga wadanan, in muka tsaya biye musu zaki rasa abinda zaki je yi."

Wayarta ta ciro ta bude text din ta nuna mai, karantawa yai sannan yace "kinsan number?"

Tace "a'a amma daga alamun text din cikin mutanen dana kora ne."

Baisan sanda yai wani murmushi ba.

Fuska ta hade tace "meye?"

Yace " seat belt."

Sawa tai tana kallansa haryanzu so take taji murmushin rainin hankalincan na meye."

Ganin bashida niyyar magana yasa tace "tsoro kake?"

Batare da ya juyo ba yace "me nayi da zan tsorata? Mai laifi ai shine da tsoro."

Yana kaiwa nan ya fizgi mota da gudu.........

(Ai nikam jinai motata ta makale, ashe gudu sukai suka barni a baya......)


*Ayusher Muhd.*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Associationđź’ˇ

Shafi na Goma

Wattpad/@AyusherMohd.

*Excuse me a Zauren BieBie nake? Excuse me nan ne Zauren BieBie?....*
Lol kuna sani Dariya da sarar nan, wannan shafin naku ne duka wadanda ke left da wandanda ke right....One Love


*********

Kanta ne taji yana juyawa yanda yake gudu da motar, ga hanyar sam batada kyau kallansa tai tana san mai magana taga ya ja motar sun shiga wata kwana a Zaria.

Suna yin kwanar yai parking, ya fito daga motar ya rufe sannan ya dawo titi, sai a lokacin motarsu tazo da gudu suka wuce a tunaninsu sun wucesu ne.

Juyowa yai tare da ajiyar zuciya sannan yai dan murmushi dai kace me aikin security.

Karasawa yai jikin mota, ya bude sannan ya shiga juyowa yai ya kalleta, itama shi take kallo tace “fada kukai?”

Fada? Ya fada cikin mamaki sannan yace “ni da banda laifi akan me zanyi fada da wani?”

Fuska ta hade tace “da wa kake kenan?”

Baice komai ba sannan yasa key ya tada motar, idanta ne ya dan fito tace “in kuma basu tafi ba fa?”

Yace “sai muji me suke so.”

Haushi ya kamata batace komai ba, juya motar yai suka koma kan titi, suna fita daga cikin garin Zaria suka tadda motar nan a gefen titi, kallansa tai tace “sune?”

“Me kika musu ne haka?”
Shiru tai batace komai ba sai tsoron abinda zai faru fa take.

Khalid yana zuwa kusa dasu suka hau kan titi tare da nunamai yai parking.
Khalid ya kalleta yace “saura hour nawa?”
A hankali tace 2

Bude kofa yai ya fita, kusa dasu yaje yana neman mika musu hannu suyi musabaha, babba cikinsu ya buge hannunsa yace “matarcan zaka bamu.”
Cikin mamaki Khalid yace “wacc kenan?”

“Karfa ka raina mana hankali ta cikin motar can, ba Zainab Aliyu Tahir bace?”

Khalid ya kallesu yanzu kam ya gane aiki su akai basu mansan ta ba.

Murmushi yai yace “wai dama Zainab kuke nema?”

Eh, bamu ita.

Dariya yai yace “ba ita bace, yayarta ce wannan sunan ta Zarah, baku ganta bane? Zo ku duba ku gani.”

Cikin mamaki suka karasa jikin motar, wanda ganin an nufota yasa gaba daya hankalinta ya gama tashi.

Gani tai Khalid ya bude kofar wanda idanunta suka firfito shikenan ya zo ya bada ita, Adam, Nabila, rayuwata........

Muryar Khalid taji yace “kun ganta?”

Ido suka kura mata dayan ya kalli dayan cikin yaren nufe yake mai magana wai itace? Yace kamar ita kamar ba ita ba.

Khalid yai dariya yace “hala bakwa kallan program dinta ne amma da kuna gani zaku ganeta.”

Shiru sukai suna kara kallanta, Zarah wai sun dauka Zainab ce ke?

Zarah? Me mutumin nan ke shirin yi? Ta fada a ranta cikin mamaki, murmushi yai yace “mun biya ta tv station ne saboda zamu koma kaduna inda muke da zama.”

Shiru sukai suna kara kallan Zainab.

Khalid ya rufe kofar sannan ya kallesu yace “amma me yayarta ta muku?”

Ba mutawa ba aiko mu akai, kasan inda take? Suka fada suna kara kallan pic din da aka turo musu, amma itafa ance yau zata kaduna sannan ya akai kuka hau motar da aka nuna mana tata?”

Khalid yai dariya yace “ita ga wuce da ragowar staff din, saboda tana sauri dan 10 zasuyi meeting din, da tare zamu taho to mu bamu shirya ba.”

Yanzu kam sun dan yarda dan dama hoton ba yanzu tayi shi ba.

Khalid yace “kuyi hakuri dan Allah karku ma yayarta komai, bansan meya faru daku ba.........”
Malam karka soma mana wa’azi whve ka bamu gu, neman halak dinmu muke.

Khalid ya shiga mota yaja ya bar gun.

Zainab ta kalleshi tace “me ya faru? Naga sun barmu mun wuce.”

Shiru yai kafin yace “ i just trick them hope bazasu gane ba har mu isa.”

Ajiyar zuciya tai sannan ta sauke window dinta tare fa shan iska, shiru tai tana tunanin wanda ya aiko a kamata a cikin mutane sama da 8 data kora daga gun aiki daga sanda ta fara zuwa yanzu.

Shiru tai tana tunanin ya akai yasan gana program? Sannan ya akai yasan basu ganeta ba? Ya akai yasan bazasu fahimci ita din bace?

Tadan kuramai ido tana tunanin lamarin.


Kauda kai tai a hankali tace “Thank You.”

kallanta ya danyi ta glass amma baice komai ba, yana tunanin me tama mutane haka?


************

Kusa da Goggo ya zauna a falo cikin rada yace “tana ina Goggo?

Harara ta makamai tace “aika fini sanin inda take.”

Mikewa yai ya nufi dakin goggo, Nabila ta dago ta kalleshi amma bata kawo komai ba.

Kofar dakin ya tura, a hankali saboda yana tsoron kar ya kwankwasa su Nabila dake falo suyi tunanin wani abin.

Tana kwance a kasan katifa daure da zani sai dai zani ya sauko kadan wanda hakan yadan bayyana saman kirjinta, da sauri ya juya baya, sannan ya juya zai fita.

Jiyai ance waye? Ta fada tare da saurin jan bargo ta luluba.

Yace “yahkuri bansan bacci kike ba.”

Ya Adam? Ta fada cikin alamar tambaya, juyowa yai da sauri yace “ya akai kikasan sunana?kin sanni ne?”

Kai ta girgiza da sauri tace “a’a jiya a gun Goggo naji tace “Adamu.”

Ajiyar zuciya yai sannan yace “dama fada miki zanyi daga yau zamanki a gidan nan sunanki Sadiya,sannan gobe zakiji ki gama registration dinki daga nan sai ki koma gida.”

Nagode amma me yasa zan boye sunana?

Yace “matar gidan batasan kina nan ba sannan ba dadi taga na kawoki bayan ban sanki ba.”

A hankali tace “kayi hakuri, sannan nagode Allah ya saka.”

Murmushi yi sannan yace an jima zansa ki fito a matsayin zuwanki kenan ku gaisa da mutan gidan.”

Kai ta daga alamar fahimta, zan shigo miki da abinci, da sauri tace nagode.

Murmushi ya sake yi sannan ya juya ya fita.


Yana isowa falan Goggo tamai wani kallo sannan tace “samin kati a waya ina san kiran mai dinki.”

Ba musu yace to.

Nabila tasa dariya tace “yau basa banba, Uncle baice wai Goggo meyasa katinki ke saurin karewa? Tai maganar cikin kwaikwayon sa.

Dariyar borin kunya yai yace haka nakeyi?
Nusaiba tace “sosai ma.”

Suka sa dariya, Goggo ta kalleshi cikin jin haushi.

********

Sun gama meeting komai ya tafi yanda take so, suna gama sa hannu aka kawo musu abinci, kallan mai ajiye musu abincin tai tace “dan kaima driver na yana waje.”

Okay tace tana gamawa ajiye musu ta dauko take away din da juice ta fito waje, ganin batasan motar ba yasa ta koma ta sanar mata batasan waye ba.

Zainab ta amsa ta fito dashi.

Yana zaune cikin mota yana karanta wani littafi a hanunsa, mikamai tai yana amsa ta juya ciki.

Cikin mamaki ya kalleta yau me ya sameta.

“Ex....Ina magana.”
Baisan dame zai kirata ba.

Hartayi gaba ta juyo ya nuna mata alamar na meye? Tace “an ba kowa ne kaine ba’a gani ba.”
Ta fada ta juya ta koma.

Sai kara jinjina ma Zainab sukeyi, suna kara nuna mata jin dadinsu nayin aikin da ita, daya daga cikin directors din yace “yanda kike workaholic din nan ha mijinki yake?”

Murmushi kawai tai bata ce komai ba, dan duk yanda take da mutum indai aiki ne ya hadasu batasan harkar rayuwarta ya shigo ciki.

Shima jin tayi shiru yasa bai sake cewa komai ba sai suka sako wani hirar.....


*Ayusher Muhd*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Associationđź’ˇ

Shafi na Goma Sha Daya

Wattpad/@AyusherMohd.


  Su Nabila na shiga daki Adam ya mike da gudu yai dakin Goggo, haushi ya turnuketa ta bishi da wata harara ta kaici tare da cewa "meye hakan?"

Adam ya mata nuni da daki sannan ya ruga, kai ta girgiza tare da jan tsaki na takaici, kwankwasa mata yai a hankali, sannan ya tura, riga take sawa da sauri ya koma ya maida kofar ya rufe yana cewa ni bana tashi zuwa sai tana wani abin?

Karasa sa rigar tai ta bude kofar tana kallanshi fuskarta dauke da murmushi.
Kallanta yai yace "hakuri na bude kina shiryawa."

Tace "bakomai ai masan ba da saninka bane."

Yace "ki dauko jakarki ki fito a matsayin yanzu kika zo."

To tace ta juya da sauri ta dauko jakarta ta fito a gaba ya sata har zuwa falo, har kasa ta tsuguna ta gaida Goggo, Goggo ta kalleta tace "ni kin tabbatar sace miki jaka akai?"

Kallan mamaki tama Goggo sannan ta kalli Adam, da sauri yace "Goggo wai meyasa kike haka ne? Bana fada miki ba?"

Share hawayenta tai tace "kiyi hakuri."

Goggo ta kalleta a haka dai gata mutum sai dai itafa tana mamaki ace kaf garin nan ba wanda ya tausaya mata ba kuma wan.........."

Adam ne yace "Goggo ki sake da ita kar Zainab ta gane wani abin."
Goggo ta maida kanta kan Tv harta fara kallo ta mike ta shiga kitchen ta dauko juice ta zauna tana sha tana kallanta.

Da Adam da mai suna Sadiya wacce ko sunanta na asali bamu sani ba sukai shiru.

Can Adam yace zauna.
Zamanta ta gyara sannan ya kwallawa Nabila kira itada Nusaiba.

Fitowa sukai gaba daya fuskarsu a hade.

Adam yace "Rigimanmun mu ya akai?"

Nusaiba ta turo baki tace "Dady yace gobe zai turo a daukemi."

Wani dadi ne y kama Goggo da Adam, wanda har Goggo bata san sanda tace "masha Allah hakan yayi dai dai."

Nabila ta kalleta tace "Goggo ai ba sai kin nuna murnarki a fili ba mun san dama dadi zakiji."

Goggo ta sa dariya tare da wayancewa tace "ba haka bane, ai zamanku a gidan yafimin dadi, ni da da nake zama ni kadai in Adamu ya fita? Yanzu kuwa kuna nan muna shan hirar mu?"

Nabila dai bata ce komai ba, sai yanzu suka kula da budurwar dake zaune a kasa.

Nabila cikin mamakin tace "wannan kuma fa?"

Adam ya sa dariya yace "Sadiya ce yau tazo daga Kura."

Sadiya? Suka tambaya a tare

Da sauri ya kalli Goggo yana mata nuni datai magana.

Goggo tace "baku san Sadiya ba? Kanwar Adam ce ai mahaifinsu daya."

Kallan Goggo yai cikin mamaki, tace "Sadiya ga kannan Zainab ku gaisa."

Nusaiba ta kalleta tace "amma kinfi Uncle kyau kuma bakwa kama, da alama ke mamanki kikayo."

Murmushi tai, Nabila kam kallanta kawai take amma batace komai ba.

Kallan Goggo tai tace "yau da wake zan dafa wlh."

Goggo tace "da dai ni kike dan kinsan bansan da wake."

Nabila tana dariya tace "sai kisa miya akwai ragowar ta jiya.

Tana yin kitchen Nusaiba ta bita.

Suna shiga Adam ya kalli Goggo yace "Goggo wani mahaifinmu daya?"

Tace "to kana san nace mahaifinka da mahaifiyarta daya bayan bakwa ko yanayi? Sannan in tsautsayi ya kawo Sadiya nan kusa fa?"

Sadiya tazo  nan tai me?

Haka dai ka iya ko kunya ma bakaji, sau nawa tana ce ma zakato kana hanata?

"To wai tazo tai me? Ni kinsan bansan takura."

Goggo tace "can kai ka sani, baka dauki na jininka ba gashi kana kinkimo da titi ai."

Sadiya tai kasa dakai, Adam ya kalli Goggo yace "wai Goggo meyasa kike haka ne?"

Goggo ta dauke kai tana shan juice dinta ta cigaba da kallanta.

Adam sai kokarin jan Sadiya da hira yake dan ta saki jikinta.


************

Bayanta tadan buga saboda ciwon da yake mata, sannan ta mike ta musu sallama, nan kowa ya shiga jinjina mata suka fito ita da staff din da sukazo tare.

Tana saukowa daga kan matatakalar da waje waya ta shigo wayarta, bata dauka ba saboda tana kara yin sallama dasu, suna karasa saukowa ya rage daga ita sai staff dinta ne, babban ya kalleta yace "Hajiya kinyi ba karya wlh."

Murmushi tai tace "sannunku da aiki kuma, thanks to you komai ya tafi normal."

Nan suka yi murmushin jin dadi.

Inda motarta take suka nufa, bakowa a motar hakan yasa ta dan wawaiga, sannan tace "kuje ku hau hanya, maybe ya dan fita ne."

Ah Hajiya bari mu jira ki fara tafiya.

Hira suka dan cigaba dayi jefi jefi take sa musu baki saboda bata fiya san yin hira fa na kasa da ita ba.

Khalid ne ya hangosu daga nesa hakan yasa ya kara hanzari dan isowa, yana karasowa yace "kuyi hakuri nadan je Massalaci ne."

Kallansa tai cikin mamaki, yau meke kanshi harda bada hakuri?

Zatai magana wayarta ta sake kara, nan ta dau wayar sai kuma ta kalli Khalid.

Kallanta yai cikin mamaki, sannan ya kalli wayar hannunta wanda baya iya gani.

Hello, ta fada tare da dan matsawa daga gun su.

"Hajiya Zainab! Wato kin gudu ko?"

Gabanta ne ya fadi tace "wanene?"

Wata muguwar dariya ya saki yace "wanene? Tambaya ma kike?"

Juyowa tai ta kalli Khalid, ganin haka yasa ya matsa kusa da ita, daurewa tai tace "mekake nema da ni ne? Koma wanene in dai har ya sanni na tabbatar yasan bana tsayawa maganar da batada amfani a waya, in kana da abin cewa ka tareni ka fadamin."

Tana kaiwa nan ta kashe wayarta tare da kallansa.
Are you akay?
Abinda yace mata kenan ta daga kai alamar eh, hannu ya mika mata yace muga number.

Mikamai wayar tai ya karanta number sannan ya mika mata sawa yai a wayarsa sannan yace "ko zakibi wadancan ku wuce?"

Cikin mamaki tace "why? Ni bana shiga motar da ba tawa ba."

Yace " i think suna nan kar su kara biyo mu, sannan in mun samu mun wuce dazu yanzo ba abinda zamuce musu da zai sa su yarda."

Shiru tai kafin ta daure tace kai fa?

Zan taho.

Abinda yace mata kenan yai shiru, ganin hkan ne mafita yasa ta nufi gun staff din ta sanar dash zata bisu mamaki ne ya kamasu, duk da ba haka suka so ba dan sun san har su isa kuma bazasu sake ba.

Harta bude mota zata shiga ta juyo ta kalli inda yake, in suka kamashi saboda ita fa?

Anya hakan shine daidai?
Karta ja mai bayan bai san hawa ba baisan sauka ba.

Kayanta ta ajiye a motar sannan ta dawo yana kokarin shiga motar,cikin mamaki ya kalleta.
Tace "ba haka kawai nake korarsu ba, duk wanda na kora yayi abinda bai dace bane, wannan muryarsa tamin kama data Dauda wanda na kora shekara biyu da suka wuce, kamashi nai yana neman lalata yarinyar da tazo neman aiki."

Tana kaiwa nan ta juya harta isa bata juyo ba ta shige motar suka ja suka tafi.

Shiru yai a gun kafin shima a ya shiga.


Sai wajen karfe shida suka isa garin Kano, gidsnta tace a wuce da ita, nan ta nuna musu suka ajiyeta, tana sauka sukai ajiyar zuciya a tare, sannan suka sa dariya.

Ahhh so awkward.

********

Bala ne ya bude mata kallan sa tai bayan sun gaisa tace "Yana hanya, zai karaso."

To Hajiya dama na ganki ne a wata motar."

Murmushi tai dan yanda ya kalleta dama tasan me yake nufi.

Ciki ta shiga, Nabila da Nusaiba ne sai wata a falan.

Mamaki me ya kamasu ganinta ta shigo, Nusaiba ta leka ta window da sauri, ganin ba mota yasa ta kalli Auntyn tata tace "Aunty ya haka?"

Jakarta ta mika mata ta amsa Nabila ta amshi ragowar kayan hannunta, tana cema Nusaiba wato ke in zan fita ko in zan dawo ba mi kike nema ba ko?

Dariya tai tace "ai ke Aunty tawa ce shi kuma, wanda zan aura ne"

Nabila tasa dariya tace " a ina zai aureki bayan baimasan kina yi ba?"

Zainab ta karasa ciki, turus ta tsaya tana kallan abinda ta gani a falan ta, Nabila ta kalla wacce tai saurin cewa "Sadiya ce kanwar su Uncle."

Zainab ta kara kallanta, kasa tai dakai tare da saurin cewa "Aunty Ina wuni?"

Zainab cikin mamaki tace "Sadiya?"

Tace eh nice.

Zainab tai shiru tana kallanta kafin tace "ya kura?"

Sadiya ta kalleta tace "lfy kalau."


Zainab ta kara kallanta anya ita ta gani a bikinta?

Nabila ce ta kalleta tace "Aunty Menene?"

Ciki ta shiga tana duba agoggo tare da cewa "ina Adam?"

  Ya kai Goggo gun mai dinki.

Shiru tai tare da kallan agoggo, gata batada numbershi balle taji halin da suke ciki.

Sadiya ta kara kalla tace "sai naga kamar kin rame."

"Na danyi rashin lafiya ne shiyasa."

Kai ta jinjina alamar fahimta sannan ta dau wayarta ta kira Adam.

Yana ganin kiranta ya gyara murya yace "Honey."

Tace "Honey kun kusa gamawa?"

Yace "yanzu muka iso, kinga Sadiya?"

Tace "Eh na ganta, ka kira Abokinka kaji yana ina?"

Ba tare kuka dawo ba?

Eh ka kirashi in kaji ka fadamin.

To ya ce ta kashe wayar, Nusaiba ta matso da sauri tace "ina Uncle din nawa yaje?"

Wani uncle din naki kike nufi?
Dariya tai tace "to yayana?"

Zainab ta girgiza kai kawai, kallan Sadiya tai wacce tai kasa da kanta.

Taci abinci?

Nabila tace "eh."

Zainab tai ciki, Nabila tabi bayanta.

Juyowa tai tace "lafiya?"

Nabila tace "Aunty kin tabbatar kanwar Uncle ce?"

Zainab cikin mamaki ta kalleta tace " me kike san cewa?"

Nabila tace "kawai na gane basa wani hira."

Zainab tasa dariya tace "kinada matsala Nabila, to in ba kanwarsa bace wacece? Me kika dauki Adam?"

Dariya tai tace "shirman nawa fa?"

Zainab tace "da alama kam, ki cire abin nan a ranki kiyi rayuwarki yanda ya kamata."

Kai ta jinjina sannan tace "Dady yace gobe zamu wuce"

Zainab tace "hutu ya kusa karewa ko?"

Nabila tace eh.

Murmushi sukai a tare Nabila, Zainab tace "a hakan ma na gode, dan in baku zo ba banaji zan dinga ganinki."

Nabila ta matso ta rungume ta, Zainab tai murmushi mai tattare da ma'anoni kala kala.



*Ayusher*
[10/27, 10:39 PM] Zuraiyah Zuzu 🌟: 🍀A GIDANA🍀

Haske Writers Associationđź’ˇ

Shafi na Goma Sha Biyu

Wattpad/@AyusherMohd.


  Tana tsaye a dakinta rike da wayarta, tana duba agoggo, anya ta zauna anan bayan abinda yake kokarin faruwa a dalilinta ne?

Sadiya na zaune a falo duk motsin datai idan Nabila akanta, wanda har ta daure tace "Lafiya?"

Nabila tace "lafiya kalau tunani nakeyi."

Sadiya ta dauke kai, yanda tai da kanta ne yasa Nabila ta kalleta har zatai magana sai ta fasa, jin an bude gate ne yasa Zainab ta fito daga dakinta.

Muryar Nusaiba taji tace "ashe Uncle ne."

Nabila tace wani uncle din tunda ke Uncle din naki biyu ne?
Nusaiba ta harareta tare da juyawa ta dawo ta zauna.
Nabila tasa dariya tace "Uncle din Aunty ne kenan, da dayan ne da munga fuskarki tafi haka."

Zainab kam Adam na shigowa bakin kofa tace "Honey dan zo."

Gabansa ne ya fadi, gaban Goggo ma ya fadi, a tare suka kalli Sadiya wacce ke zaune yanda suka barta, kallan Goggo yai wacce ta bugamai kallo ta mai alama da ka gani ko?

Adam ya kalleta yace "inzo?"

Tace "eh"

Sadiya ya kara kallo sannan ya nufi daki, a tsaye take hankalinta a tshe, a bakin kofa ya tsaya tace "shigo mana."

Gabansa na faduwa ya maida kofar sannan ya kalleta yace "lafiya?"

Yi maganar cikinsanhin jiki, kallansa tai tace "meya cema? Yana ina?"

Ajiyar zuciya yai yace "na kira bai dauka ba, amma wai lafiya?"

Tace "sake kira."

Kallanta yai sannan ya hau kiran Khalid, sai data katse ya sake kira sannan Khalid ya daga.

Alama ya mata da an daga sannan yace "Khalid kana ina ne haka? Zai......"

Hannunta ga harde tamai alamar X kenan karya fada, Khalid daga can yace " yanzu zan karaso, ina kan babban layi."

Adam ya kashe tare da kallanta yace "yana hanya, wai meke faruwa ne?"

Kallansa tai kamar zata fadamai sai kuma tai shiru, tace bakomai.

Shiru tai tana kallanshi a ranta tana cewa "honey am sorry, banso kaima ka shiga fargabar da nake ciki, in na san abinda ke faruwa na sanar maka."

  Menene?

Murmushi tai tace "Honey sai naga Sadiya?"
Yace "eh wlh dazu kin fita sai gata, kinsan ta dade tana damuna akan tana san zuwa."

Zainab tace ta kyauta, dama su Nabila zasu tafi gobe da safe sai ta koma dakinsu."

Da sauri yace "ai itama jibi zata tafi, ta zauna agun Goggo."

Fuskarta dauke da mamaki tace "jibi kuma?"

Yace "eh makaranta ta samu anan Northwest ne ko Buk? Shine tazo registration."

Hannu tasa tadan bigi kafadarsa cikin wasa tace "ko kunya wai kake cewa ko nan ko nan, gobe zata registration din kenan?"

Yana dariya yace "eh."

Tace "kuje tare zan turo ma kudi, ka tambayeta nawane kudin."

Kallanta yai cikin jin dadi sannan ya jawota jikinsa yace "Honey na gode sosai."

Murmushi tai tace "Kanwarka ce, da ita da su Nabila daya suke."

Dan huce yai kadan sannan yace "nagode Honey."

Dagowa tai t kalleshi sannan tace " naga bata saki jiki ba, ko dan farkon zuwanta ne?"

Yace "ai dama ita magana bata dameta ba sosai."

Tace "wa?" Sadiyan taka da kake cewa tana damunka

Please Login or Register in order to submit comment