Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saka harpic, yana sakin ajiyar zuciya a zatonsa ya gama amma ina juyawar sa ke da wuya ya ga undies d’inta zube a ‘kasa da sauri ya ja baya,kamar ba zai yi ba sai kuma yayi tsaki ba dolena nayi ba duk wanda na kira kamar na tarawa kaina jama’a ne kowa kuma da fassarar da zai yi masa.idanunsa a runtse shima undies d’in ya d’auke shi ya saka a toilet bin kafin da safe ya kira ta wallahi sai ta wanke masa toilet tsaf duk dama gobe zai bar gidan sai ta ci kanta ita kad’ai, da kyar ya wanke bed sheet d’in kawai don baya son yin wani cikin friends d’insa by mistake ya shiga ya gani wallahi da shima barin sa zai yi ta zo ta wanke to yana gudun ‘bacin rana kada ayi zaton wani abu yayi da ita shi kuwa Allah kada ya nuna masa wannan ranar da wani ido zai kalli jama’a bayan tarin cika bakin da yayi akan cewa MAI ZAI YI DA ITA. Yana gama wankewa ya cilla shi cikin washing machine sai sannan zuciyarsa ta dinga tashi ai kuwa ba ji ba gani ya dinga kwara amai sai da ya gama aman yayi brush yana gamawa ya fice da sauri murya a cunkushe yace wallahi ban yafe ba banza ‘kazama.😂 ya gyara gadonsa tsaf ya bad’e bedroom da turaren wuta da room freshner. Sannan ya fice parlour baya tunanin zai iya wanka a toilet d’in wallahi dole key ya d’auka a daren gwara yaje gidansa yayi wanka. Yana had’e rai ya fito, ai kuwa suna ganinsa Ali da shegantaka ya taso”wai ya aka yi ne yalla’bai mai amarya tazo yi part d’inka ko dai har ka fara sonta ne?”harara ya zabga masa “matseni in gaya maka” Abdul yace “ai abin bai kai na matsewa ba in dai wannan ne ai baya ‘buya abinda zamu gani ‘kunshe a mahaifarta muzo mu sha suna.” “Mtsww God forbid wallahi sai kace irin ku ai ni tunda nace muku ba abinda zanyi da yarinyar nan to kuwa zaku sha mamaki ba ku san waye Imran ba.” Dariya su kayi sosai suna kallo ya fice Ali yace “mhmn a dai juri zuwa rafi yalla’bai wata rana tulun zai fashe” Abdul ta tuntsire da dariya yace “d’an iska ranar mayar da martani ba.” Yana jin su murmushi kawai yayi ko don tanadin iskanci da suka yi masa ai ba zai kusanci yarinyar nan ba haka zai saketa wallahi da zarar shirinsa ya kammala. (To kowane shiri ne wannan mhmmn wani abin sai d’an gidan manga)



Ita kuwa tana bedroom d’inta bayan tayi wanka Night gown a jikinta da cup d’in tea a hannunta tana sipping a hankali so take ciwon marar da yake d’an damunta ya lafa mata. Hafsa ta shigo d’akin idanunta a kanta ta zauna a gefen gadon “wai ina kika shiga ne? Ban ganki wajen dinner ba?” Hafsa ta fad’a tana shafa kanta.
Murmushi shatu ta saki a karo na farko taji tana son rufa masa asiri saboda sam bata son haushinsa da mommah take ji tace “wallahi period pain ya hanani fita d’azu fa kamar na mutu dole kuwa nayi kwanciyata side d’in su Ya Imran.” Hafsa ta girgiza kai “ashe da gaske yake wallahi na zata ‘karya yake har na had’a shi da mommah sai kije ki wanke sa a wajen mommah don wallahi ta kunnu da yawa cewa take zai zo ya sameta don ma Hajiya mama tana hanata tace ba huruminta bane da tuni ta kira shi ta sulle shi sai kije ki wankeshi.” Shatu ta mi’ke ta tafi wajen mommah. Tsaf ta wanke shi kuwa mommah ta jata jikinta “oh am sorry daughter to da kika yi zamanki a can hope ba abinda yayi miki kuma kin sha magani?” Daga kai tayi tana kwanciya a cinyar mommah da take feeling d’inta kamar Innaji she really love mommahnta to the extent.



Da safe Dahda ya shiga wajen hajja gaishe ta da kyar take amsa gaisuwar. Sister’s d’insa ma duk suka gaisheshi anan yake sanar da Hajja tariyar shatu ita ma kamar yarda kawu sa’idu ya tsara sati mai zuwa Hajja ta ta’be baki”To ni yanzu ina ruwa na nayi magana kaje ka yayata ni a bakin duniya ai ba abinda zance maka manga aje Allah yayi albarka gobe-gobe ma zamu tattara komatsanmu muyi gaba ba kuma zamu sake dawowa ba kamar yarda ka bu’kata kuma ina son ka jini da kyau dama ka samu fili ka siya ka fara yi min gini anan kano duk san da na tashi zuwa na dinga zuwa can na sauka na san mallakina ne. Shashasha ana yi maka gata baka san gata ake maka ba duk an mallakeka da
Surkullen fulani.” Murya can ‘kasa Dahda yake amsa mata “Insha Allah Hajja za’a Gina,amma tafiyar da kun bari wani satin idan shatun ta tare.” Hameedah mai son ganin ‘kwaf ta gaban Hajiya ta saka baki “eeh Hajiya mu bar shi wani satin idan ta tare sai mu tafi cab amma za’a ga ‘kwailar amarya ai ni na zata ba yanzu zata tareba. Dahda ya zabga mata harara don sam basa shiri da hameedah baya son halayenta gaba d’aya.ya mi’ke yana yiwa Hajiya godiya bayan ya ajiye mata ma’kudan kud’i da niyyar yi mata toshiyar baki. Bakin Hajja kam yana mutuwa tsaf saboda kud’i.nan ta shiga jera masa albarka. Yana fita hameedah ta shige part din zainab ta bata labarin tariyar. Hankalin zainab ya tashi don basu kawo tariyar nan kusa ba sun zata sai ‘yar su ta riga ta mallake gida tukunna sai ga sabon labari ya bayyana a zuciyarta tace ashe kuwa sai na tashi tsaye kafin kwa’bata tayi ruwa.


Tsaf yayi wankansa ya shirya cikin shigarsa ta musamma farin filtex d’insa da hula damanga takalmi bartozzi ya d’ora agogon rolex d’insa a damtsen hannunsa kana ganinsa kamar ka sureshi ka sace. Sai zabga ‘kamshin turarensa da yake mix yake different colours ‘kamshinsa daban yake.
Direct part d’in mommah ya nufa cikin tafiyar izza kamar Kuma ‘kasaita kamar yarda ya saba yi kullum. So yake yaje ya dam’ki ‘yar gidan mommah ta wanke masa toilet duk da yasa an wanke amma sai ya wahalar da ita.

Cak tayi da tea cup a hannunta tana ‘kare masa kallo cikin shigar doguwar rigar ta ta shadda as usual yanzu ma kanta ba d’ankwali. Sarai yaji idonta a kansa yayi mata banza yana dur’kushe a gefe yana gaida su dada da Hajiya mama da momma. Dada ta dubi shatu tsaki tayi “kiji min ‘yar banzar yarinya ba zaki gaida mijinnaki ba.” Da sauri yace “ta bar gaisuwarta jeki bedrroom d’ina da toilet ki gyara min” ya fad’a yana tsareta da ido tsaki momma tayi “akan me duk ina house helpers d’in gidan da sai ita zata gyara maka don wani sabon iyayi gidan ma da yau zaka barshi.” Dada ta zabura tace “Auzubillahi kuji min mata tana neman jawo mana masifa da ranar nan ruguzu ta fad’o mana aikin mijinnata ne ba za tayi ba to kuma idan bu’katar ta yake fa ba iya sharar za tayi ba tashi ki fice kafin na kai miki mangara a’a wallahi ba ruwana idan rashin kunya zaki saka ta dinga yi masa ba kuwa zanje zaman d’akin nan ba ki hana a raya sunnahr muhammaduna rasulillahi d’an Abdullahi. Kai tashi ka bi matarka kaji.” Mommah gaba d’aya ran ta ya ‘baci har ya mi’ke a zafafe tabi bayansa suna zuwa corridor tace “kai ji mana kuma wallahi ko hannu ka ri’ke mata ban
Yafe ba.” Tana fad’a ta juya Imran shi dariya ma ta bashi ya juya kawai a zuciyarsa yace “kin san kina tsoron hakan kika yi mata aure kash ina ma bana gudun ayi min dariya da ayau zan mayar miki da shalelen taki cikakkiyar mace.”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-23


ELEGANT ONLINE WRITERS........


Suna shiga bed room d’in ya ja ‘kofa ya rufe, fuska a d’aure yake kallonta,ya tsareta da ido sosai kafin yace,”sakonki na jiya ya isar min, wai ke ki nuna min kin cika mace ko?har kin fara period, amma ban san ke wawuya bace sai yanzu,wa yace miki mace tana bari ma a gane tana period? Baki san abin kunya bane hakan?” Turo baki tayi kawai tana kallonsa,sai kuma a lokacin wata shahararriyar kunyarsa ta kamata,ta ji sam bata kyauta ba yanzu shikkenan ya gane mata sirrin ta? Sirrin da mommah tayi ta jan kunnenta akan kada ta bari a gani, da sauri ta runtse idonta.
Tsaki ya ja “Dama kafin na dawo ki tabbata kin fitar da ‘kazantarki daga toilet d’in ki kuma wanke min bin d’ina,and then lastly ki tabbatar kin wanke anything dake toilet d’in ya dawo kamar sabo, wawuyan yarinya kawai.” Ya fad’a yana kai mata ran’kwashi, daga haka ya fice ya kuma kulleta da key ta baya.

Sai sannan shatu ta bud’e idonta, tana sakin ajiyar zuciya, a hankali tace “Wai ni Shatu mai na aikata mutuminnan yanzu zai sake min kallon ‘kazama.” Tsaki ta ja ta shige toilet d’in, very neat ta samu toilet d’in,amma haka nan ta ‘kara wankeshi.


Momma jin shirun yayi yawa, da sauri ta danna kiransa a waya don hankalinta sam ya gaza kwanciya. Tsawon lokaci wayar tana ringing shi kuwa yana kallo yana driving ya’ki receiving call d’in sai murmushi yake, ya san mai take yiwa bata san ko bindiga aka saka masa ba zai iya aikata abinda take tunani ba.

Ji yayi text message ya shigo, ya bud’e yana murmushi had’e da ware ido kamar yarda hakan ya zame masa jiki. “Wallahi ka aikatawa yarinyar nan wani abin sai ka sani.” Dariya yayi sosai har da dukan sitiyari. A zuciyarsa yace “Ai kuwa yanzu wasan zai fara Mommah.”


********************************

Cikin kuka da tashin hankali take kallon mahaifiyrta, “Yanzu Anty duk burin da naci ya tafi a banza kenan? Yarinyar nan tarewa za tayi? Kuma ana nufin itama Imran mallakinta ne kamar yarda yake mallakina? Tana da right da komai a kansa, zata had’a jiki dashi? Komai da zaiyi min zai mata?” Cikin tashin hankali ta sake rintse ido. “Na shiga uku Anty pls kiyi wani abu mana, wallahi ji nake kamar zuciyata zata buga.” Tsaki Zainab tayi kafin tace “Ke bana son shashancin banza ki tsaya ki saurari abinda zan ce miki,ko jiya munyi waya da shuwa ta tabbatar min da ta koma gurin mutuminnan abinda ya sake ce mata kenan dole ki san yarda kika yi kika bashi maganinnan yaci a nama, a kuma ranar da yaci ake so lallai ya had’a shimfid’a da ita, yace min wallahi da zarar anyi haka kashegari zai sake ta kuma ba zai sake waiwayarta ba.” Kukan ta sake saki “Ni fa anty a sake wata shawarar wallahi ba zan amince ya shafi jikinta ba,balle har su had’a shimfid’a Imran nawa ne ni kad’ai.” Tsaki Anty tayi ta mi’ke a zuciye tace “Sai ki shirya zama da ita din-din-din a matsayin kishiya,ni dai abinda naga zan iya yi kenan shashasha ko meye abin damuwa?abin rana d’aya lokaci d’aya, kuma wallahi kika sa nayi asarar kud’ina ranki ne idan yayi dubu zai ‘baci,kin san nawa na kashe? Ban da tafiya cikin jeji da shuwa ta kwana tana yi a garinsu, to kije kiyi yarda kike so, ki bari suyi surkullensu na fulani su su mallakeshi,kin san dai yarinyar nan ta fiki komai da komai.” Runtse idonta shaheeda tayi murya na rawa tace “zan gwada Anty Allah ya bani iko.” Antyn ta dafa ta yauwa “ko ke fa idan kika yi hakan shine zaki samu kansa,ki ci karanki babu babbaka.” Shaheedah ta saki ajiyar zuciya tana dafa hannun mamanta tace “Amma Anty ta yaya zai amince ya kusanceta bayan kin san ba son auren yake ba.” Anty tayi murmushi “Yaro-Yaro ne ai ba yanzu zakiyi ba sai lokacin da muka so ta bar gidan,a lokacin dama kin tsara tafiya Abuja sai ki bashi a nama yaci,to kafin ki tafi ki tabbatar kin bashi desire tablet a cikin tea da safe mai ‘karfin gaske,idan ya bu’kace ki kice period kike ko kuma kafin maganin ya fara aiki kiyi sauri ki tafi shikkenan fa fa’kat, burinmu na farko zai cika.” Dariya shaheedah tayi ta rungume Antyn ta cikin tsananin farin ciki,hankalinta kam yanzu hundred percent ya kwanta.



Da yamma kafin a kai amarya Momma ta kira Imran, ba ‘bata lokaci yazo, tana kallonsa su biyu a
Parlourn tace “Nasiha zan maka Imran a matsayina na mahaifiyarka duk runtsi duk wuya ka kula da iyalinka,amana ce ubangiji ya dan’ka maka a hannunka, kayi adalci a tsakaninsu Imran kada kaga ita wannan yarinya ce ka cuceta ko ka zalunceta,zata tare nan da kwana shidda....” da sauri Imran ya zaro ido yace “kwana shidda Mommah ai naga tayi ‘karama.” Mommah tsaki tayi”Ni kaina ba’a son raina hakan zata faru ba ba yarda zanyi ne, sai dai ina son in ja kunnenka hakan ba yana nufin na baka lasisin kula ta bane, wallahi ban amince ba kada wata mu’amala ta had’aku,
Ka bar ta tayi karatunta please Imran.”

Ransa a ‘bace ya saki ajiyar zuciya yana tunanin mai zai kaishi kusantarta ko shi ya kawo maita duniya, gaskiya bai ji dad’in lamarin tariyar nan ba, har hakan ya gaza ‘boyuwa a
Fuskarsa,sai dai bai ce komai ba ya mi’ke ya tafi bayan ya zaro key d’in part d’in shatu na gidansa ya mi’kawa mommah kamar yarda ta bu’kata.


Tunda ya koma bedroom d’insa ya zubawa kayan da abokansa suka had’a masa na komawa gidansa kallo,idan ka ganshi zaka yi zaton kayan yake kallo,Sai dai tuni zuciyarsa ta tafi tunanin neman mafitar yarda zaiyi da auren Shatu, tunani iri-iri ya shigeshi wata zuciyar tace kawai ya saketa ya gudu da matarsa su bar ‘kasar, a duk shawarwarin wannan ce tafi tsaya masa.




Tsaf Amarya Shaheedah ta fito a cikin shigar laffaya sai zabga ‘kamshi take kai kace anyi ‘barin turare a jikinta,sanye take cikin pink d’in laffaya, ta dai rufe kanta amma idonta ko alamar kuka babu,
Burinta a yau ya cika na auran Imran, kamar yarda ta dad’e tana mafarki,yau dai ga ta a matsayin matarsa,don haka take jin kamar taje ta kai kanta ganin su masu kaiwar basa sauri sun tsaya sai zagaye suke da ita wajen ‘yan uwa.


Gida yayi kyau ya sha kayan alfarma na gani a fad’a,sai zabga ‘kamshi yake. Amarya tun daga haraba take sakin murmushi cikin laffaya.

Kowa ya yaba sannan masu kawota suka tattara suka tafi, ‘yan mata zuciyarsu cike da burin samun irin gidan ko makwafinsa.



Ango dai tunda abokansa suka fara siyan baki yake sakin tsaki,burinsa suyi su tattara su tafi,tunda ya dad’e yana jiran wannan ranar a matsayinsa na kamilin saurayi.

Abubuwan da suka faru a daren abubuwane da baza su manta su ba a kaf tarihin rayuwarsu,ango dai ya riski matarsa sabuwa dal a leda sai muce Allah ya kawo ‘kazantar d’aki.


*************


Tsaf tayi shirin makarantar ta ta fito, tana isa parlour taji ‘kamshin turarensa a parlourn, tayi mamakin ganinsa a yau d’in don rabonsa da zuwa gidan kwana hudu kenan cif tun bayan da amaryarsa ta tare. Yayi kyau sosai cikin black blue d’in yard d’inkinsa na kullum ne a jikinsa,gajeriyar riga mai gajeren hannu kan sa ba hula, hakan kuma sai yayi masa kyau. Har zata wuce da sauri Dada ta ‘kwalo mata kira “zo nan ‘yar nema baki ga mijin ki bane?” Bakin ta ta turo murya a cunkushe tace “Dada na makara fa.” Tsaki Dada ta ja cikin masifa tace “Allah dai wadaran naka ya lalace uwarki ce ta d’aure miki wani abu can, an ce wani sai kin yi tsinanniyar boko matar da za’a kai d’akin miji jibi ace tana yawo a gantale don wauta ko ‘yan magungunan gyara na daka ban ga ana baki ba,balle aje ga batun gyaran jiki,sai anje an cuce shi an kai masa ke salam kamar kazar da ba maggi ba gishiri,ko da yake ina ruwa na ke da uwarki ku zaku yi da na sani,ki wuce ki koma ciki yau ba zuwa wata makarnta idan kika tare idan ya zama dole kya je.” ‘Kwalla ce ta kawo idon ta,murya a cunkushe tace “Test ce fa dani zaki ce wani ba zan je school ba.”Mommah ran ta a ‘bace tace “Dada ki bar ta taje idan yaso goben sai ta ha’kura insha Allah ai kema dai zaki so ace ‘yar jikar ki ta zama likita.” Dada ta gyara zama cikin masifa tace”To kuwa idan har zata je makarantar nan sai dai wannan ‘katon banzan ya kaita ba Ammaru ba da kullum za’a dinga tashin sa da sassafe kai ta makaranta don an gan shi salihin bawa.” Ko kallon in da Dada take bai yi ba,ya mi’ke yana yiwa Shatu kallon sama da ‘kasa a
Zuciyarsa yace “Ai dama Ammar d’in aka aura wa ita.” “Ki nemi mai kai ki school ba abinda nazo yi ba kenan.” Cikin ‘bacin rai Mommah tace “Wuce kije ya kai ki idan yaso ya zubar da ke a titi,saboda ka ga na kyale ka? Kwanan ka nawa rabon ka da gidannan sai kace a kanka aka fara aure to kai zaka kai ta daga yau kuma kai zaka cigaba da kaita, wuce ku tafi Shatu kada kiyi late ai ha’kkin ta akan ka yake.” Dada tace “‘kwarai kuwa.” A ran sa yace yau zaku ga ha’k’ki wallahi sai nayi mata abinda ba zata sake shiga mota ta ba.


Tafiya suka yi sosai kafin su isa d’an ‘karamin building d’in mai tsananin kyau a ido,ginin kuma bungalow ne,gurin sam ba hayaniya. Da sauri Shatu ta kalleshi murya a cunkushe da tayi al’kawarin ba zata yi magana ba tunda taga ba hanyar makaranta yayi ba, ta san wata muguntar ya shirya mata saboda ance ya kaita makaranta.”please Yaya Imran ka mayar dani gida idan ma ba zaka kai ni school d’in ba.” Ko kallon inda take bai yi ba, ya zare seat belt d’insa yace “wuce muje malam ba dai sunce ha’k’kinki yana kai na ba,to yau zan sauke babban ha’k’kin kafin ‘kananan su biyo baya.”
Jikin Shatu ne ya d’au rawa don tun tana ‘kauyensu ta san menene aure tunda da friends d’inta da yawa da aka yiwa Aure. Ta kalleshi da sauri ta ga ya had’e rai, tuni idonta ya kawo ‘kwalla ta san matan. ‘Kauyensu suna bata labarin wahalar da suke sha har ruwan zafi ake saka su.”Don Allah Ya Imran kayi ha’kur.” Ba tare da ya kalleta ba yace “fita muje malama you are wasting my time,ai kin girma zaki iya d’aukan nauyin auratayya zaki kuma iya d’aukan duk wani abu da matan aure suke iya d’auka,tunda Babar ki ta aurar dake,ko baki san aure ba?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba Yaya Imran.” “To me yasa kika tsorata har da kuka? Kada kiyi min ‘karya fad’a min gaskiya kin san aure ne?wallahi kika yi min ‘karya kika bari na gane ‘karya kike min a yau zamu goge raini tsakanin ni dake don ba zan bar mana wajenan ba sai na mayar dake cikakkiyar mace mai amsa sunan matar aure,gaya min nace.” Da sauri ta fara wasa da hannunta jikin ta yayi sanyi sosai kamar ba Shatu Danger ba, ta sunkuyar da kai sosai hawaye sai zirara yake.
Shi kuwa dariya ce take son kama shi ganin tun ba aje ko ina ba ta razana alamar ta san duk abinda ake a aure,ya matse dariyar kafin yace “oya tell me ina jin ki mai ake a Aure?” “Iskanci” shatu ta fad’a murya na rawa sai kuma ta fashe da kuka “Don Allah kada kayi min kaji Yaya Imran wallahi Dijen gidan maigari tace da mijin ta yayi mata shine ta samu ciki.”
Still idon ta a ‘kasa take magana ta ma kasa kallonsa.shi kuwa dariya ce kawai take cin sa amma ya kasa yi,sai murmushi yake yana kallon yarda duk ta gigice. “Kin san meye iskancin Kenan?” Da sauri ta girgiza kai “Ban sani ba wallahi amma dai tace min cire kaya....” “yi min shiru fita muje ashe ma kin san komai yau kuwa zaki san menene iskanci,shashasha kuma Idan baka da aure idan kayi shine ake ce masa iskanci idan kuwa kana da aure raya sunna ake ce masa,Fita muje nace.” Ganin ba alamar wasa a fuskar sa yasa ta fita ‘kafarta na rawa al’amarin ya gigita ta sai kace ba Shatun Mommah danger ba. ‘kafar ta ta kasa d’aukanta a zafafe yace “ko sai nazo mun fara daga nan.” Da sauri tabi bayansa hankalinta a tashe,ta san yau kashin ta ya gama Yawo.”



Yana knocking Gate man ya bud’e gidan da sauri yana kai masa gaisuwa.gidansa ne da ya gina yake saukar guest d’insa turawa idan sun zo harkar business Nigeria. Ya tsaru iya tsaruwa yanayinsa tsarin turawa. Yayi kyau sosai parlor ne guda d’aya babba sai kitchen da toilet a parlourn sai 2 bedrooms.
Raku’bewa tayi a one seater tana chewing hand finger d’inta a tsorace take sosai tana kallo ya shiga bedroom ya fito daga shi sai singlet da gajeran wando da sauri ta runtse idon ta ganin ya nufo ta ta mi’ke a guje tayi hanyar bedroom.murmushi yayi yace “shikkenan kin hutar dani kin
Kai kan ki.” Tana shiga ta rufo ‘kofar sai dai abin takaici babu key a Jiki. Tana kallo ya shigo fuskarsa a had’e, ta dinga ja da baya tana ro'konsa "please Ya Imran!" "wuce toilet kiyi brush sosai malama." ta bud'e toilet d'in shima abin takaici babu key a jiki. Shatu ta zaro ido a hankali tace "Na shiga uku." Idanunta duk sun firgice, tana ji ya turo ‘kofar ya shigo idanun sa a kanta “Ba zaki yi sauri ba?” “Ni fa nayi brush d’ina a gida.” “Na sani ai wannan na musamman ne ba na son naje kissing d’inki naji bakinki ba daidai ba.” Ai da sauri ta zube a ‘kasa hawaye sha’be-sha’be.”Don daraja da girman iyayenkaw Ya Imran kayi ha’kuri.” “Idan na ha’kura za kiyi min abinda nake so?” Da sauri ta d’aga kai,murmushi yayi “okey taso ki fito mu d’aura al’kawari.” Da sauri ta mi’ke ta fito tana sakin ajiyar zuciya, sai kuma ta kalleshi tayi saurin d’auke kai “please amma ka fara mayar da kayan ka tukun.” Yayi mata wani kallo “Meye a jikin nawa? Ko naked kika ganni?” Da sauri ta girgiza kai “To kina feelinga sha’awa ta ne? In d’auke miki ita yanzun nan?” Da sauri nan ma ta girgiza kai ba tare da ta san menene ma sha’awar ba.
Ya ta’be baki “Oya zauna maza na fad’a miki sharad’ina.” Ta kuwa zauna ta ra’be a gefe kamar ace kyat ta gudu.”Zan kyale ki idan kin amince da sharad’ina,kije gida ki sawa Mommah rigima kice mata ba kya son auren idan kuma ta ‘ki kice mata ba kya son ki tare yanzu,kiyi ta kuka idan ba haka ba wallahi kika bari aka kawo ki gida na sai kin gaya wa aya za’kin ta zuwa zan miki abinda ake yiwa masu aure,kina ji na ko?” Ta d’aga kai da sauri. “Yauwa idan kika yi haka kin zama good girl kuma zaki yi karatu sosai,idan kuwa kika ‘ki ana kai ki zan miki ciki ki haihu kuma ba karatu kina jina?” Da sauri ta d’aga kai, yayi tsaki “Ba kai zaki d’aga min ba kice na amince da sharad’inka Ya Imran.” Da sauri tace “Na amince da sharad’inka Ya Imran.” Ya gyad’a kai yana mi’kewa had’e fad’in “Good Girl.”


‘Daya bedroom d’in ya shige yayi kwanciyrsa, don ba zai mayar da ita yanzu ba sai ya kad’a ‘yan hanjin Mommah tukunna. Murmushi yayi a zuciyarsa yana tunanin halin da Mommah zata shiga.

Mommah lokacin d’auko ta yana yi ta tura driver, sai dai me? Driver ya kira ta yace ai ance shatu ba ta zo makaranta ba.Mommah bata san san da ta zauna da’bas a kujera ‘kirjin ta yana bugu bata so ace hasashenta ya zama gaskiya ace Imran yaje ya aikatawa Shatu wani abun da kan ta ba zai iya d’auka ba. wayarsa ta dinga kira,kusan missed call biyar kafin ya d’aga murya a dashe tamkar yana cikin wani hali yace “Hello Mommah.” Bata san san da ta ‘kunduma zagi ba.”Gidan uban wa ka kai ta?” Dariya ta so kubce masa yace “Ba ko

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment