Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da ‘karfin hali tace “Maraba lale da mutanen turkey dirar yaushe kuma?” ‘Ko’kari yayi sosai wajen mayar da dukkan damuwarsa ya saki murmushin ‘krfin hali kafin yace “Jiya muka iso muna Abuja, ya ha’kurin Dada?” Mommah ta gya’da kai kafin tace “Kun kyauta, Dada kuma anzo sa’i sai dai Allah ya gafarta mata yasa kuma can ta fi mata nan. Ina Hakimar take?” “Allah yaji ‘kanta ya bamu ha’kurin rashinta.”
Ya amsa mata yana bagarar da waccen tambayar ba don ya rasa amsarta ba, sai don ba ita bace a gabansa. Mommah ta bi shi da kallo tana kallon yarda yake kallon yaran ta san tambaya ce fal a bakinsa, amma ya rasa ta yarda zai fara, hakan yasa tace “Akram ku gaida uncle ‘din ku.” Yaran suka zuba masa ido kafin su fara gwarancinsu, yana murmushi yake amsa zuciyrsa fal da mamakin yarda Akram ‘din ya ‘dauko zahirin kamanninsa “Mommah yaran wanene?” “Na Shatu” Direct ta ba shi amsa tana mamakin tambayar tasa wato da gaskiyar Hisham da yace bai san an yi haihuwar ba, idan kuwa haka ne waye ya turo wannan message ‘din, akwai alamar tambaya akan hakan sai dai ba yanzu za tayi masa ba sai nan gaba. Ta mi’ke ta fice daga ‘dakin ba tare da ta sake waiwayarsa ba. Shi kuwa flat ya kwanta akan bed zuciyarsa cike da tunaninnika da dama Musamman Shatu yau da ya gani ta zama Hamsha’kiyar mace ta ko ina ta amsa sunanta na mai kyau.”



Mommah na shiga kitchen ta ga Shatu na aikin abincinta duk da ta kammala tana juye su a wammers, ga ikeey a gefenta da take ta kukan noodles zata ci. Mommah ta ja Ikeeyn tana rarrashi kafin ta kalli Shatu tace “Ko ka’dan kada ki bashi fuska ba ruwanki da shi, tunda dai kinga an riga an saka ranar ku da Ammar bana son wani abu yasa a fasa Ammar ne abin a tausayawa yanzu tunda shi ba shi da mata shi kuwa ya rasa ki yana da inda zai je yaji sanyi, yara kuma alamu sun nuna bai san da su ba, don haka kada ki nuna masa nasa ne. Ni da kaina idan ta tunkareni da zancenki zan sanar dashi Ammar zan bawa ke ko ma na riga bashi. Ki kula sosai bana son zubar da aji.” Shatu ta sunkuyar da kai a hankali tace “To Mommah.” “Yauwa ki kiyaye don yanzu haka ya zata kina da aure kamar yarda Hisham ya sanar masa, sai dai a yau idan na dawo a gaban Hajiya Mama zan sanar da shi yaransa ne, aure kuma ba ki dashi sai dai Ammar za ki aura kin ji me na gaya miki?” Shatu ta ‘daga kai kawai a zuciyarta tace ma “duk zancenku kuke ba ni bace a gabansa.”



A gurguje tayi wankan Ta ‘dauko set ‘din mayukanta na makari ta fura mutstsika wa a fatarta da take walainiya kamar ta tarwa’da, ko powder bata saka ba kasancewar gidan mutuwa za suje, ta zira tight trozer ‘din ta da half gown, sannan ta kawo after dress bugun Larabawan Oman ta saka sea blue mai touches ‘din maroum don haka ta yane kan ta da mayafi maroum. Sosai tayi kyau kamar ka sure ka gudu musamma da ta saka medical Glass ‘dinta fari tas da shi da zagayen ba’ki sai ta fito zam kamar Bahabashiya. Duk da ba wata kwalliya ta fesa ba illa lip gloss da ta goga a le’benta.


Takalmi flat ne a ‘kafarta amma yanayin yarda take tafiya sai ka zata hill shoe ne, taku take gaba ‘daya’kugunta da sassan jikinta na rausaya kamar ganyen bishiya. Yarda ya kafa mata ido har bai san san da ya kur’bi tea ya ‘kwareshi ba, hakan yasa duk gurin suka kai duba ga yarda yake kallo. Mommah ta’be baki tayi kawai ta cigaba da shan shayinta. Ita kuwa Shatu tana ‘karasowa ta ha’de rai shi sai ya ga ma kamar harararsa take, ganin yarda suka zuba masa ido sai abin ya bashi kunya da sauri ya mayar da idonsa kan tea cup ‘din da yake hannunsa, amma ‘kasa-‘kasa kallon fresh fingers ‘din Shatu yake yi da suka sha zanen lalle. Tunda yake bai ta’ba yarda lalle abin kwalliya bane sai yau da ya gan shi a hannun Shatu. Tamkar ya sa hannu ya dam’ko su yayi ta shafar su, gaba ‘daya yaji zaman cin abincin ya gundireshi da sauri ya mi’ke ya kai hannu zai zari tissue kamar ha’din baki ita ma Shatu ta kai hannu zata ‘dauka hannayensu suka ha’de just like magnet, wani yarr Shatu ta ji a jiknta tayi saurin ‘dauke nata hannun tana kallonsa, “Sowie” yace wanda muryar sa ba ta fito ba illa la’b’ban bakinsa da suka motsa. Shatu ta ‘dauke idonta tana sakin wata ajiyar zuciya.
Yana juya baya ya ji Akram yace “Mommah uncle waye wannan?” Ya fa’da cikin gwarin hausar sa, da sauri Mommah tace “Go and ask him.” Cikin takaicin wai bai san ‘ya’yansa ba. Yaron yana zuwa ya ‘daneshi, yana cewa “uncle wa?” Imran da sauri ya rungumeshi yana kallon cikin eyes ‘din yaron irinnasa sak ba banbanci, har zai wuce sai wani tunani ya shige shi da sauri ya koma dinning area ‘din idanunsa cikin na Mommah yace “Mommah idan dai har Shatu tayi aure to da cikina tayi aure saboda wannan yaron da ni yayi kama, don haka auren ta bai halarta ba ina da damar maka shi court ya sakar min matata!” Gaba ‘daya gurin suka zuba masa ido...



Kuyi manage da wannan ina gidan mai jego.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?

Wannan ne complete wancan mistake ne

42



Hafsa da Nahna dariya ta so ku’buce musu sai dai suka gimtse kawai. Yayin da Ammar gabansa ya shiga dukan uku-uku, yaji ganinsa na neman ‘daukewa, tashin hankalinsa ‘daya kada dai ace Imran kome ya zo yayi da Shatu, tabbas kuwa da zuciyarsa ta buga. Da kuma ya sanya hakan a mizani na rashin halarci matu’kar iyayensu za su sake yarda da Auren Imran da Shatu shi kuma ya tashi a tutar babu da ba’a yi masa adalci ba.


Mommah ta’be baki tayi a fusace tace “Sai ka ‘daura himma.” Ta mi’ke ma ta bar table ‘din gaba ‘daya tana ‘ko’karin yakice ‘bacin ran da ya taso mata, na abubuwan da duk suka faru a lokutan baya. Imran kuwa wucewa yayi da Akram aka fa’darsa zuciyarsa fes da samun mafita don ko ba’a yi DNA ba ya tabbatar wannan ‘dan nasa ne ko makaho ya shafa zai yarda da hakan.



A ranar su Hajja su kazo gaisuwa bisa tilastawar Kawu Sa’idu. Har da Zainab aka taho. Lokacin da su Mommah suka zo suka tarar dasu. Zuciyarsu gaba ‘daya sai da ta kusan bugawa da suka ga yarda Shatu da twins ‘dinta suka Koma. Yara kamar ‘diyoyin larabawa jajur dasu ga suma ba’ka si’dik kwantacciya a kansu ga shi jikinsu dumimi a murje gwanin sha’awa. Idanuwan kowa a kansu yake don ma Mommah tana tofe su da addu’oi kafin su shiga taro.

Gaba ‘dayansu da kyar suke amsa gaisuwar Shatu ita kuwa ba abinda ya dame ta bayan ta gaishe su mi’kewa tayi ta fice daga sashen gaba ‘daya tana mamakin yarda Shaheedah ta koma kamar mai cutar ‘kanjamau.” A gefe can daga tsakar gida suka zauna ita da Hafsa da Nahna sai suka zamo tamkar wasu fitulu masu haskawa.



Suna zaune su Imran suka shigo, Idanunsa suka fa’da cikin na Shatu tayi saurin ‘dauke nata ta mayar kan nasu Akram da suka mi’ke da guru, suka nufesu direct Akram wajen Babansa ya nufa ita kuwa Ikram wajen Uncle Ammar ta nufa. Har sun wuce yaron yace “Uncle caya na amco ciweet a wajen Mimi na.” Imran yace okey bari na kai ka, har gurinsu ya ‘karasa dashi yaron ya mi’ka mata hannu “Mimi na ciweet.” Harara ta zabga masa tace “Ka sauka daga gurinsa ko sai na makeka, ka san shi ne?” Da sauri Imran ya watsa mata idanu yana kallon ‘dan ‘karamin bakinta da yaji tamkar ya kai mata sumbata a zuciyarsa yace “Sai tsiwar tsiya.” Shi kuwa Akram kuka ya saka jin fa’dan da Miminnasa take masa. Cikin zafin rai Imran yace mata “Zaki ba shi ko sai na ‘bata miki rai? Ni kike cewa kuma bai sanni ba ko? Daga ke har mijinnaki ku saurari sammaci zan ji dalilin da yasa kika yi aure da cikina a jikin ki.” Murgu’da masa baki tayi har da ‘dan guntun tsakin ta. Imran ya wara ido kafin yace “Ni kike yiwa tsaki?” Ta sake zuba masa harara ta ‘dauke Kai. A zafafe ya juya da yaran a hannunsa ya ma fasa shiga gidan mutuwar sai yaje asibiti anyi DNA test ‘dinnan. Idan kuwa ya tabbatar da yaron nan ‘dan sa ne wallahi sai yaci uban mijinta, sai kuma yayi shari’a da wanda ya ‘daura mata aure da cikinsa a jikinta. Tunanin da ya dinga yi kenan yana driving a motar da ya kar’bi key ‘dinta wajen drivern Alhaji Baba.


Sun da’de a asibitin kafin result ya Fito, a hakan ma don ya sakar musu ku’dine kuma private hospital ne. Sakamako dai ya nuna yaro nasa ne. Likitan cikin tsokana yace “Ai ba sai kayi DNA ba kamanninka da yaron kamar kayi kaki ka zubar ya isa a shaida ‘dannan naka ne ko tantama babu.” Imran murmushi yayi yana kar’bar takardar as evidence zuciyarsa a dugunzume da ‘bacin ran da wani banza can ya aurar masa mata, ya raya a ransa wallahi sai ya ‘daureshi kuma shari’a zasu zuma da shi har kotun ‘Koli.



A zafafe ya koma gidan mutuwar, ya tarar su Hajja har sun fito zasu tafi, don haka antsaitsaye suka gaishe shi har zai wuce Hajja tace cikin ‘bacin rai “Imrana idan ka sami lokaci ka zo ina son ganinka in ji dalilin wannan rama ta tashin hankali da Shaheeda tayi.” Wani kallo ya jefi Shaheedan dashi kafin yace “Ai bani zaki tambaya ba ita zaki tambaya dalili tunda ni dai ina bata ci da sha, ina kuma sauke mata duk wani hakkinta na aure.” Daga haka yasa kai ya shige gidan a ransa yake fa’din “Ke ce wannan yake a gabanki ni ba shi bane a gabana.” Gaba ‘daya sak su kayi suna kallonsa tare da tsananin mamakin sauyawarsa kamar ba Imran ba da suke juyawa son ran su. Hawayen takaici ya zubowa Shaheeda tace “Hajja kun ga abinda nake gaya muku ko?” Hajja ta girgiza kai “Na gani ba shakka wannan karan Dijah da ‘karfinta take, to wallahi gidan ta tarar mu zuba ni da ita shege ka fasa jar uba! Ban ga ta zama ba. Zainab ma da falmata da ran su ya gama dugunzuma ya ‘baci suka dinga sakin maganganu da alwashi iri-iri na son rai da ba’kin hali a zuciyarsu.


Ko da ya shiga gidan bai tarar da su ba sai su Mommah da Hajiya Mama, hakan yasa ya shiga rarraba ido yana son yaga ta inda zai hango ta rigima ce take cin sa sosai a ransa. Mommah ta kalleshi ta hango rigimar da take zuciyarsa a zafafe tace lafiya? Shima cikin dakiya da jarumtar da ya aro yace “Uwar yaronnan nake nema.” Ba Mommah ka’dai ba harta Hajiya Mama sai da gabanta ya fa’di lokaci guda kuma dariya ta kusan ku’buce mata. Mommah ta mi’ka hannu “Bani shi nan, ai ba ce maka yayi dole sai a hannun uwarsa zai zauna ba.” Yaro kuwa ya ma’ke kafa’da alamu sun nuna ba ya son zuwa wajenta, a zafafe ta ja hannunsa ya kuwa saka kuka. Hajiya Mama tace “Kema sarai kin san ba zai zo ba, yarda baya son mutane ba zama zaiyi ba ya tafi dashi ya kaishi can gida gurin uwarsa, tunda su ma sun gudu saboda mutane ni ban ta’ba ganin masu tsoron mutane irin Shatu da iyayenta ba sai kace wasu kuraye.” Mommah harara ta zabgawa Akram tace “Zan dawo gidanne zaka ha’du dani ne.” Imran ya mi’ke da shi a kafa’darsa zuciyarsa fes jin Shatu ta koma gida zai je ayita ta ‘kare ta gaya masa wani shegen bunsurun ne mijinta. Shi ka’dai yake tunani a zuciyarsa.

Tun a mota ya tasa Akram da tambaya, tamkar yaron zai fahimci mai yake cewa. “Kai ya sunan mijin uwar ka?” Akram dariya kawai ya ‘bangala masa Imran yayi tsaki idona idon mutuminnan sai sha’keshi ya mutu har lahira idan bai yi wasa ba shege mai ‘katon kai.” Sumbatun da yake yi shi da kansa ya saka kan sa dariya cikin ‘bacin rai kuma yace “Just like I know him.” Ya furzar da hucin ‘bacin rai mai zafi a bakinsa.



Da masifar gudu yayi parking kamar zai tashi sama, har hakan ya ja hankalin masu hidimar gidan suna kallonsa. Ya fito da ‘dan hanzari Akram a kafa’darsa.

A parlour duk ya samu su Hafsa Shatu ce kawai bata nan tana kitchen ya lura masoyiyar kitchen ce ta gasken gaske. Kowa yayi masa magana banda Ikram da tayi kamar bata san Allah yayi ruwansa anan, ya zuba mata wani kallo a ransa yace “Ja’ira mai kama da uwarta.” Sannan ya kalli Hafsa kasancewar ya san tafi Nahna sau’kin kai yace “Ina uwar yarannan?” Da hannu Hafsa tayi masa poiting kitchen cikin mamakin neman da yake mata, kuma wai wani uwar yarannan kamar bai san sunan ta ba. Nahna kuwa tsaki ta ja a zuciyarta tace “Ai kuwa in dai Shatu ce kai tsaye zan ce maka ‘kwalelenka.” Ta tuno a ranar da ta ‘dauko Shatu bayan ya ‘dauke mata budurcinta ya kuma zabga mata saki saboda rashin tausayi, ya zama dole ta ja kunnen Shatu ta kama kanta da wani Imran Allah na tuba meye wani Imran ragowar Shaheedah ga Ammar gallelen saurayin da yake matu’kar san Ta. Ta sake bin bayansa da kallo ganin gadan-gadan ya shiga kitchen ‘din, tabbas ta yarda maza ba su da kunya ko ka’dan wallahi.




—————————————-


Tun a Mota su Hajja bakinsu bai huta da zancen ba har sanda suka isa gida. Nan ma sallah kawai suka yi suka ‘dora daga inda suka tsaya.
Hajja ta shiga kiran malamai tana basu ku’din sadaka tana ayiwa ‘danta da jikanta addu’a suna cikin wani yanayi. Sannan ta kira malamin duba ta gaya masa matsalolin ta, al’kawari yayi mata akan insha Allah zai duba mata kuma duk abinda ake ciki zai sanar mata.


Gefe guda kuwa Hameedah ce da Zainab har da Shuwa suke sake ‘kulla-‘kullarsu. Hameedah ta gyara zama cikin masifa tace “Amma Shaheedah an yi shashasha yanzu cikin kika je kika zubar? Don wauta kuma kika gar’kama abin planning a hannunki gashi nan ya zu’ke ki tas kin dawo sai kace sillar kara, yo ba dole miji ya wula’kanta kiba, saboda babu mamora a jikinki.” Ta sake zabga tsaki “Ko mace ba za tayi sha’awar sake miki second look ba bayan tayi na farkon. Ke kuma zainab wannan karan zancen asiri ya kau a canja wata dabarar ki koma kissa da sharri ki ‘kwace mijin ki.” Shuwa ta zabura tace “Ai kuwa wannan malamin aikinsa kamar yankan wu’ka yake wallahi duk taurin kan Manga wannan karan sai yazo hannu.” Hameedah ta mi’ke a zafafe tace “Wallahi ba wani asiri da zai ci manga a yanzu dai idan da ya cishi yanzu ba zai ci shi ba domin kuwa Hajja tuni tasa aka yi masa dafa’i. Don haka ni dai ina gaya muku ku canja shawara ke kuma ki nemi sha ka fashe ki sha, kafin a fara ‘dora miki cutar ‘kanjamau.” Daga haka ta fice da sauri. Shuwa ta bi bayanta da harara kafin tace “Alhamdulillah na samo bakin zaren.. haba No wonder muyi ta asiri baya cin bawan Allahnnan ashe shegiyar uwarsa ce tayi Kane-Kane. Tabbas yanzu abin zai sauya salo sai mun yi farra’ku tsakanin uwar da ‘dan sannan mu zo mu asirceshi. Allah mun gode maka da ka fitar damu cikin duhu shi yasa fa ni dama matar nan sam ba tayi min ba hushinta nake ji, don daga ganinta fuska biyu ne da ita.”
Ta bu’de jakarta ta ciro conrainers na ‘kwayoyin magani ta cillawa Shaheedah tana fa’din “Saura ki yiwa uwarki asara dubu maitan kenan ta bayar aka sissiyo miki duk na waje ne hips kam da boobs har sai kin gaji dasu, duk su ‘yan mata suke sha yanzu ki gansu tumbul-tumbul dasu idan kika jure da sha duk wannan ramar sai ta zama labari, ki kuma zage ki samu ciki shine zai zauna dake ko ya’ki ko ya so.” Haka ta saka su a gaba da fa’da tamkar uwar da ta kawo su duniya. Har yamma tana gidan suna sake koya wa Shaheedad tsagerancin yarda zata mallake mininta ta mallake dukiyarsa har suma ta ‘yan musu tunda ance yanzu har yafi ubansa ku’di.



————————
Imran kuwa yana shiga kitchen ‘din ya mayar da ‘kofar ya rufe, har da murza key, hakan yasa Shatu saurin juyowa idanunta suka fa’da cikinnasa, da yayi kicin-kicin da fuska, ya matsa daf da daf da ita, har tana iya juyo hucin numfashinsa, idanunsa akan ‘kirjinta da suke ‘dagawa ta cikin riga saboda fargabar da ta risketa a lokaci ‘daya, Ta yi ‘ko’karin matsawa fuskarta a ha’de tace “Ka bari it is prohibited in Islam!” Bakinta ta zubawa ido duka sassan jikinsa na tashi musamman jin hucin numfashinta a fuskarsa duk da ba rungumeta yayi ba, amma tuni yaji wani zazzafan feelings ya mamaye ilahirin sassan jikinsa, lumshe idanunsa yayi yana jin ‘dacin furucin da ba zai fa’da “Ya sunan uban wanda aka ce an ‘daura miki aure dashi? Don ni da ubansa zanyi shari’a ba dashi ba.” Shatu ta ware idonta a kansa kafin ta ta’be baki tace “A dalilin sun maka me?” ‘Kuri yayi mata da ido cikin 'bacin rai, kansa tsaye kuma yace "Fashin mata mana." dariyace ta so kamata sai dai ta gintse ta ha'de rai a zafafe tace "sai ka 'daura himma." "Zan kuwa 'daura kema kuma sai na kaiki 'kara dan ban san me yasa kika yi aure alhali kin san nayi miki ciki ba." da sauri ta janye jikinta har tudun 'kirjinta na shafar sa ya kuwa runtse ido don jin shi yayi ya afka wata duniya bai san san da ya sa hannu ya ri'ko tausassan hannunta ba. tana shirin zamewa ya ri'ke su gam kafin yace "Mijin naki ma Aldayyus da zai bar ki ki dinga irin wannan zanen a hannu shashasha ne na ajin 'karshe, ji irin kayan da kike sawa." murgu'da masa baki tayi tace "Ina ruwanka, shari'a kuma muna jiran sammaci." ta fice daga cikin kitchen 'din cikin azama ta barshi a tsaye zuciyarsa na sake han’koron ‘bacin rai. Burinsa ya san wanene mijinnan nata a fili ya furta wanene kuwa idan ban da ri’ka’k’ken jahili kayi aure mace da ciki baka sani ba wallahi sai yaci ubansa. Ya fice daga kitchen ‘din da azamarsa



Da daddare suna zaune duk za su fara cin abinci, Imran ya fito daga bedroom fuskarsa a ha’de ya nufo inda suke baje akan dadduma suna shirin fara cin abinci. Zama yayi kusa da Alhaji Baba idanunsa cikin na Shatu kawai sai ji suka yi yace “Ke mijin naki bai zo ya ‘daukeki bane?” Alhaji Baba sai yaji maganar wata iri don bai san da zancen za’a wahalar dashi kafin a gaya masa bata da aure ba, ya dubi Imran yace “Tana da wani miji ne bayan ‘dan uwanka Ammar.....” Gaba ‘daya Imran ya fito da idanunsa cikin wata irin fa’duwar gaba idanunsa suka sauka kan Ammar sannan ya dinga bin mutane da kallo ‘daya bayan ‘daya kafin ya mi’ke cikin sarewar gwiwa da kasala ya shige ‘dakin da ya fito daga cikinsa.......




Saduwar alheri, amma don Allah ku daina damuna in ‘kara yawan pages ba ku san da yaya nake typing ‘dinnan ba, ba fa biyana kuka yi ba free book ne.

Ina godiya da wasu daga cikin group ‘din jiddatul khair da suka saka min ku’din data nagode sosai don haka ba zan gaza ba wajen fa’dar sunanku. Wasu kuma mu tara a wani pages ‘din, gaba ‘daya na sadaukar da wannan page ‘din gareku


Sakina Ibrahim Dayyab
Aisha sa’ad Abdullahi
Bilkisu ubaid
Zara Musa
Aisha Dan toro
Fatima Sunusi
Baraka usman
Aysher
Tees cuisine
Ummin khadija
Maman mubarak.

Thanks so much I really appreciated ❤️❤️
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?


43


Tun bayan shigarsa bedroom ‘din ya zauna gefen gado hannayensa ri’ke da kansa da yake matu’kar sara masa, yana fata abinda yaji ya kasance mafarki ne, ba zahiri ba. Ammar ne ya auri matar da ya saki? Kafin yayi aune ya ji zubar hawaye akan fuskarsa, da gaske zuciyarsa ‘kuna take tamkar ta fito daga ‘kirjinsa don tsananin bugu, lokaci guda zuciyarsa Ta dinga hasasho masa rashin adalcin da aka yi masa. Gaba ‘daya wutar tsanar Ammar ta bijirowa zuciyarsa.


Kamar an mintsineshi ya mi’ke da sauri hannunsa ri’ke da takardar gwajin ‘kwayar halitta da aka yi masa, zuciyarsa na sake ‘karfafa masa gwiwar hasashensa gaskiya ne ko da ace Ammar ne mijinta to tabbas wannan yaron nasa ne hakan yana nuni da cikinsa Shatu ta auri Ammar. Tashin hankali! Ya fa’da a fili. Da sauri ya fita parlourn.


Ya kuwa ci sa’a har a lokacin ba su gama cin abincin ba. Ganinsa kawai suka yi ya shigo da hanzarinsa tamkar zai kifa ya kalli Ammar a zafafe yace “Duk wanda ya ‘daura maka aure da ita ka sanar dashi ya aikata haramun domin da ciki na ka aureta, kuma wannan yaron tun ‘dazu na kaishi hospital aka tabbatar min ‘kwayoyin halittarsa irin nawa ne.” Alhaji Baba sak yayi cikin mamakin furucinsa kafin yace. “Waye ya sanar da kai an yi masa aure da ita? ba ayi auren ba amma ana shirin yi nan kusa.” Wani abu ne ya fa’da masa wanda da ya tokare zuciyarsa, har sakin ajiyar zuciya yayi kafin cikin sanyin jiki ya dur’kushe murya a raunane yace “To don girman zatin ubangiji ku yi ha’kuri ku yafe min abinda na aikata na sakin da nayi mata wallahi sharrin shai’dan ne da na zuciya.. kuyi ha’kuri ku mayar min da matata.” Wani kallo Mommah ta watsa masa wanda ya ka’da ‘yan hanjinsa. Cikin matu’kar ‘bacin rai tace “Wallahi idan kaga Shatu ta komawa aurenka sai dai idan bana raye.” Wata irin razana da fa’duwar gaba Ta riske shi ya runtse idonsa gam, yana sake jiyo amon sautin Mommah, da ta cigaba da magana a zafafe “Shatun da ka wula’kanta ka tozarta, ka tsallake ka barta cikin ra’da’di da zafin rashin budurcinta, a ranar da ka hai’ke mata ka saketa sakin tozarci, ka ‘dauke matar so kuka shilla uwa duniya, Bayan ta haihu Hajiya Mama da kanta ta kira ka a waya ta sanar da kai haihuwar amma saboda kai isashshe ne ko magana ba ka yiwa Hajiya Maman ba sai message ‘din banza da ka turo..” Imran da sauri yace “Ni Mommah!” “Kai ‘din fa, ko ‘karya zan maka? Dama saboda irin wannan na ajiye evidence.” Ta ‘dauko wayarta ta bu’de message ‘din a ma’adanar ta ta sirri da ta ajiye shi. “Ko ba kai bane? sannan saboda ma kada a dameka sai ka kama duk numbobinmu kayi blocking, shima ba kai bane?” Wata irin zufa ce ta fara zubo masa bayan ya karanta message ‘din hawaye kuwa tuni ya fara tsere a fuskarsa, tunani yake yi ko dai an zuba masa wani abu ya sha da har ya yi wannan rubutun don dai wallahi ba shi bane itama Mommah da za tayi masa adalci ta san ba zai aikata ba. Amma zai tsaurara bincike akan hakan matu’kar kuwa ya samu Shaheedah ce da aikata irin wannan abun wallahi shi ka’dai ya san hukuncin da zai yi mata. Mommah ta cigaba da magana a zafafe “Saboda haka in dai ni na haifi Shatu na haramta maka aurenta, kuma don in ‘kunsa maka takaicin da ka ‘kunsa mana,Ammar zan aurawa ita.” Wannan karan ba Imran kawai ba har ta Shatu ‘kirjinta dakan uku-uku yake yi.

Idanunsa sun ka’da sun yi ja sosai ya ‘dago ya kalli Alhaji Baba murya a raunane yace “Don Allah ka bata ha’kuri na rantse da girman Allah ban san wa ya aikata haka ba, kuma wallahi ban

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment