Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ranta a ‘bace tace “mai tayi muku? Mai tayi muku zaku yi mata wannan hukuncin?””an daketa d’in ko zaki rama mata ne ita har ta isa ta doki shaheedah ta kwana lafiya wacece ita a gidan?”muryar tsagera hameedah ce mai wannan tsaurin idon tana fad’a tana yiwa mommahn wani banzan kallo. Imran kansa sai da yayi mamaki Ammar kuwa da ya shigo yanzu yaji furucin hameedah akan mahaifiyarsa bai san sanda ya waska mata mari ba. baki bud’e kowa yake kallonsa babbarsu falmata tace “kana hauka ne Ammar ‘kanwar ubanka ka Mara?” Ita dinma wani kallon banza yayi mata yace “‘kanwar ubana tafi uwata ne?nawa hameedan take ina ce shakara biyu ta bani shekara nawa tawa uwar ta bata da zata gaya mata magana?” Yana fad’in haka yaja hannun shatu da mommah suka fice daga kitchen d’in bayan yayiwa Imran kallon banza,yana tsaye ana zagin mahaifiyarsa ya kasa d’aukan mataki.

A bakin gado ya zaunar da mommah idanunta kawai yana zubar da hawaye, hakan ya ‘kara tunzira zuciyarsa ya mi’ke a zuciye zai fita mommah tayi saurin ri’ke hannunsa tana girgiza kai tace “kada kaje Ammar hakan ma da kayi nagode maka ko bakomai yau na san na haihu ka ‘kwatar min ‘yancina Allah yayi maka albarka d’auki shatu ka kaita clinic ayi mata dressing ciwukannan.” Kallonsa ya mayar kan shatun dai-dai lokacin da Imran ya turo ‘kofar ya shigo, murya can ‘kasa yayi sallama, Ammar jan hannun shatu kawai yayi suka fita sam baya son ma ganin d’an uwannasa gani yake kamar an canja musu shi Imran mai zuciya Imran mai tsananin son mommah mai gudun ‘bacin ranta, yau shine ya zama haka a gabansa ake cin mutuncin uwarsa ya kasa magana ya kasa kata’bus.Yana kallo suka fice ya bisu da kallo da ajiyar zuciya, sannan ya samu gefen mommah ya zauna, kansa ya d’ora a kafad’arsa wasu ‘kwalla da bai san na menene ba suna ‘ko’karin zubo masa, ya kama hannun mommah murya can ‘kasa furucin “Am sorry mommah” ya fito daga bakinsa, bata kalleshi ba illa d’auke kai da tayi “kiyi ha’kuri ita ma yarinyar bata kyauta ba na tambayi masu aiki sun gaya min duk yarda aka yi ita ta kwatantata da muciya saboda raini ita kuma tayi saurin hannu ta mareta bata san wannan yarinyar ba ‘kyaleta za tayi ba, ko ta’kyaleta a lokacin sai ta nemo abinda zata rama gaba kad’an please momma kiyi ha’kuri amma kiyi mata fad’a” wani kallo mommah tayi masa sannan ta zare hannunta “wacece yarinyar sunanta ne baka sani ba ko kuwa canja mata suna kayi Imran anya kuwa jininka ce fa ita,duk duniya ku ya kamata ku nuna mata gata tunda bata da wasu sha’ki’kan y’an uwa kazo kana ce min wani bata kyauta ba, rashin kyautawar mai tayi? ‘Dirka-d’irkan mata su zauna suyi mata jina-jina sannan ace wani bata kyauta ba to ba ha’kura nayi ba wallahi wannan karan sunyi da y’ar halak ni kad’ai kuma Na san abinda zan musu tashi ka bani wuri mai kayan haushi kawai ka zo ka cika ni da wani zancen banza da wofi zanyi maganinku ne gaba d’aya daga kai har dangin ubannaka sai na shayar daku mamaki.” Imran zuba mata ido kawai yayi ya ma kasa magana sam ba ya son hayaniya d’abi’ar dahda tsaf ya d’auko shi yasa yaji har kansa ya fara ciwo. Jan pillow yayi kawai ya kwanta a gadon mommahn ya ri’ke kansa da yake d’an sara masa.
Mommah ta dubeshi kawai tayi tsaki ta mi’ke ta bar masa bedroom d’in tana cigaba da ‘kananan maganganunta.



Koda dahda ya dawo duk da girkinta ne ranar ko ‘keyarta bai gani ba, tana part d’inta ta tasa shatu a gaba tana lalla’bata ta sha peppe soup ko kad’an ne kafin tayi barci. Amma shatu fir ta’ki yau zuciyarta a hassale take da ‘bacin rai sun riga sun kai zuciyarta ‘kololuwa a ‘bacin rai duk ‘ko’karin mommah da Ammar haka suka gaji suka ‘kyaleta suka zuba mata ido sai ajiyar zuciya take saukewa tana hura hanci.



Gefe d’aya kuwa amaryar dahda zainab ta saka shi a gaba tana gaya masa ‘karya da gaskiya a gaban y’an uwansa ta tattara lefin gaba d’aya ta d’orashi kan baiwar Allah mommah, Dahda kawai jinsu yake yana girgiza kai ya san abinda matarsa zata yi ya san wanda kuma ko da kuskure ba zata aikata ba.Da ya gaji da ji mi’kewa yayi ya shige part d’insa ransa a ‘bace shi yasa ko da wasa baya son danginsa su ziyarceshi. Sai da yayi wanka sannan ya fara jera kiran mommah a waya amma ta’ki picking,gaba d’aya jinsa yake kamar maraya ta riga ta’bata shi ta sangarta shi baya iya ta’buka komai ba tare da taimakonta shi wannan auren matsala babba Hajja ta gangamo masa sam a tsarinsa bashi da niyyar ‘kara aure. Ganin ta’ki picking calls d’insa hakan ya sashi mi’kewa ya dangana ga part d’inta.


A zaune ya sameta kan sallaya ta d’ora kanta a saman gado tana jan carbi fuskarta da alamar ‘bacin rai sosai. A hankali ya taka wajenta ya zauna a gefen gadon, motsinsa ne ya sata saurin d’ago da kai su kayi four eyes lallausan murmushi ya sakar mata yana dafa kanta yace “Haba Dija na me ya faru? Yau ko ‘yar sannu da zuwan ma babu.” Still fuskarta a d’aure ta mi’ke ta fara nad’e sallay sai kuma hawaye sharr ya biyo fuskarta ta dur’kushe a gabansa ta kife fuskarta a cinyarsa ta saki kuka, kuka mai cin rai da tunda yake bai ta’ba ganin dijansa nayi ba. hankalinsa ne ya tashi da sauri ya dafa kanta sannan ya mi’ke tsaye ya d’agata rungume ta yayi sosai yana fad’in “yi shiru ki gaya min menene me suka yi miki?” A hankali yake fad’a mata cikin cool voice. Dijah kukan take sosai kafin ya fara wiping tears d’inta a cikin wani salo na matu’kar soyayya da son cooling zuciyarta. Shi kad’ai yasan yarda kukan dijan yake d’aga masa hankali “Don Allah Dija kiyi shiru ki fad’a min wai menene? Bana son kanki yayi ciwo please.” Ganin damuwa ‘karara a fuskarsa ya sa ta tsagaita kukan nata ta fara bashi labari, tana gamawa ta d’ora da fad’in “don haka dahda na gaji a wannan karan dole ne a san abin yi ko Imran ya fasa auren can da aka ‘kir’kireshi don a wula’kanta ni ko kuma ya had’a da za’bina ko kuma wallahi na bar gidannan don ba zan zauna ba’kin ciki ya kamani ba zuciya ta ta buga Allah ne kad’ai yarda nake jin ciwo a zuciyata kullum matsalata dangin miji sun saka kayi aure ka auri ‘yar uwarsu ban ce komai ba ko bakomai hajja tana da iko da kai to nima a barni nayi iko da nawa d’an idan kuma ba haka ba na bar maka gidan ka zauna da duk wacce suke so ka aura,amma dole wannan karan nima Imran yabi umarnina a matsayina na uwarsa da ta kawosho duniya.” ‘Kuri manga yayi mata da ido ganin yarda take masifa wai dijan sa ce haka dijan sa mai ha’kuri mai sanyin hali ita masifar danginsa yasa ta juye ta koma masa mai fad’a, sam bai ga lefinta ba ya tabbata an kaita ma’kura dama ance shi mai ha’kuri bai iya fushi ba a duk sanda aka ‘kureshi dole yayi mata abinda take so ko don ya faranta mata zuciyarta ta sauka daga fushin da take idan ba haka ba yana tsoron yana tsoron ranar da zata fara mayar da martani ga hajja, ya san tabbas abin ba zai yi kyau ba.Hannunta ya kama yana matsawa a hankali,murya ‘kasa-‘kasa yace “It’s enough ‘yan mata na dijan manga gaya min mai kike so ayi?” Murmushi ta saki zuciyarta na rage zafin da take mata, ta haka manga yake samo lagonta a duk sanda tayi fushi shi yasa basa dogon fad’a suke shiryawa. Ta gyara zamanta a jikinsa tana masa kallon cikin ido “in dai manga na yana son ganin farin cikina to ya amince da ‘kudirina ta haka zaka’kwato min ‘yancina a wajen ‘yan uwanka so nake ka aurawa Imran shatu ya had’asu su biyu ta haka kawai zan nuna musu power ta nima na dasa musu ba’kin cikin da suka dasa min ba dai shatu bace ba sa so to ita zata zama kishiyar d’iyar tasu ‘yar so.” Kallonta yake cikin nazarin anya tana cikin sense d’inta idan ban da haka wacce shatun? Wannan ‘yar ‘kwailar bayan haka ta san ko sama da ‘kasa zata had’e Imran ba zai kar’bi shatu matsayin mata ba amma bari ya tambayeta wacce shatun take nufi? “Wai wacce shatun kike nufi dijah?” Ya fad’a yana sake ‘kure ta da kallo, dariya ta saki tace”au muna da wata shatun ne bayan ta gidan nan shatu na nake nufi shatu da suka yiwa duka saboda ta ta’ba d’iyar gold to ita nake nufi” girgiza kai manga yayi shima yana murmushin yace “amma dai wasa kike ko? Idan ban da haka wannan yarinyar da bata wuce 14 ba za’a yiwa aure banda haka ma kin san halin d’anki ba yarda za’ayi ya amince da wannan batun.” Momma ta marairaice fuska tana kwanciya a kafad’arsa tace “please dahda don’t say No kai kad’ai ne last hope d’ina kaga dai da kayi aure ban ce maka komai nayi ha’kuri duk da zuciyata na hurting sosai kullum a haka nake kwana amma na san dole ne kabi umarnin hajja indai kana son ganin daidai please ka cika min burina don Allah ka amince.” Tausayinta ne ya kamashi ya fara shafa bayanta amma shifa yana tsoron lamarinnan ya san halin Imran da ba’kar zuciya ban da haka ma yarinyar is too young “
Dijah ba fa wai na’ki bane ‘kan’kantar shatu nake dubawa bana son ayi abin da za’a tauye mata ha’k’ki matsayinta na marainiya kada mu cuceta ta yama zata iya kishi da shaheedah apart from that ma ta ya kike zaton Imran zai amince da auran shatu?” Murya can ‘kasa tace “shi yasa bana so ka fad’a masa ya zama sirri tsakanina da kai so nake sai dai suji an d’aura da shatu kawai ko bakomai nima power ta ta uwa ta fito Ba kuma tarewa za tayi ba har sai ta gama school, shi kuma Imran ka barni dashi na san ta yarda zan ‘bullo masa shekaru kuwa ba abin ji bane duk da ba tarewa za tayi ba mutanen da ma a shekarunta tuni sun jima a d’aki. Ni dai abinda nake so da kai kawai ya sirri tsakanina da kai nima anan ko ‘yan uwana ba zan gayawa ba insha Allah sai dai suji” d’aga mata kai yayi “zan cika miki burinki dija na ko don ki cigaba da kasance min sanyin idaniya ta yanzu tashi muje ki bani abinci I have gists for you” ya fad’a yana kashe mata ido d’aya. Shi yasa kullum manga yake narka mata da zuciyarta take kuma kishinsa don ya san salo salo na kama zuciyar mace.






To fa masu karatu ya zata kaya ne kun amince ayi auren ko a barshi tabbas dai akwai rigima kwantacciya.😂Imran mijin shatu ko ya zata kasance? Ku biyo ni next month insha Allah na tafi hutu typing wahala

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-17


ELEGANT ONLINE WRITERS.....



Cikin daren kamar an mintsineta ta mi’ke duk da jikinta da yake ciwo hakan ba zai hanata aiwatar da ‘kudirinta ba a karo na barkatai ta sake kaiwa dogon mudubinnata ziyara,shatu ta sake ‘karewa ciwuwwukan da suka ji mata kallo cikin matsanancin ‘bacin rai ta girgiza kai muryarta a dashe tace wallahi ba zaku kwana lafiya ba ayau yarda kuka saka ni ‘bacin rai sai na hanawa idanunku barci. Ta isa inda ta ajiye ‘kullin ‘kai’kayinta tana murmushi “yau akwai rawar asosa casss a gidannan” sai kuma ta tuntsire da dariya murya a ciki tace “mu zuba ni daku shege ka fasa” ko takalmi bata saka ba don kada mommah taji takunta ta fice daga part d’in mommahn cikin sand’a.

Duk windows d’in bedrooms d’insu ta dinga zugewa a hankali tana hura musu sai kuma aka ci sa’a duka gadajennasu a jikin windows suke sai da ta taka abu sannan tsawonta ya kai.tana gama hura musu tayi saurin juyawa ta shige general parlour karaf suka ci karo da Imran zai shiga sashensa bayan ya gama aiyukan da zaiyi a system d’insa a parlourn,da sauri ya kai dubansa kanta har zaiyi magana sai kuma ya ta’be baki ya shige part d’insu, shi yanzu tsoronta yake ji sosai ba ya son ya fad’a tarkonta. Shatu tayi murmushi kawai ta shige part d’in mommah tana jira a fara rawar asosa.
Tana zaune kuwa a gefen gadonta ta fara jiyo iface-iface a general parlour ihu sosai Ta jiyo hakan ya sata fitowa daga d’akinta sai taga mommah ma da dahda sun fito daga d’akin mommah. Momma da sauri tace “koma ciki shatu ke da baki da lafiya bari muje muga menene” bata so hakan ba amma hakan ta zauna kan kujera.bayan dahda ya kalleta yayi mata alamar t zauna.
A parlour suka samesu gaba d’aya sai ihu suke har da masu ludaya da
Cokula suna sosawa. Shaheeda kuwa daga ita sai guntuwar vest sai ihu take tana kiran Imran ya taimaka mata shi kuwa yana tsaye yana mamakin mai ya samesu tabbas ya tabbata shatu ce tayi musu ramuwar gayya saura ‘kiris ya saki dariya a karo na farko da lamarin yarinyar ya daina bashi haushi sai dariya, yarinya sai shed’ananci kamar zuriar shaid’anu.Dahda da mommah fad’i suke “subhanallahi mai ya faru?” ‘Kannen dahda sai cewa suke ya taimaka musu jikinsu kuwa yayi rud’u-rud’u salati dahda yasa yace suje su suturce jikinsu su tafi asibiti.amma ina lamarin ya girmama har da masu birgima a ‘kasa. Ammar ne yace “Dahda anya ba aljannnun gidan nan bane suma suka shafesu kmar yarda suka yiwa hajja” dahda ya girgiza kai ba mamaki ammar yanzu dai kira doctornmu ya dubasu” shi dai Imran yana daga gefe sai murmushi yake yana hango kuma shatu data la’be bayan ‘kofa tana zabga dariya kamar yace ga babbar aljannahr can sai dai yaja bakinsa yayi shiru kada ya jawowa kansa daga ruwan hammata ta bashi ruwan tsarki.

Kafin doctor yazo haukane kawai ba suyi ba sai da Ammar ya shigo ya sanar dasu shigowar doctor sannan Imran ya kalli shaheeda ransa a ‘bace yace “Go and cover your body ko kunya baki ji” wani kallo ta watsa masa kafin tayi magana doctor ya shigo da sauri Imran ya dafa kansa ya jata ya turata d’aki yana tsaki. Ko da ta shiga d’aki hijab kawai ta zira ta sake fitowa a guje. Doctor ya gama dubasu sannan ya fito da allura ya fara yi musu don dama dahda yayi masa bayanin ciwon. Sai kusan ‘karfe 4:00 na dare sannan abin ya lafa musu amma fa sunji jiki duk jiknnan yayi luhu-luhu balle idonsu.basu koma d’akunansu ba don suna tunanin tabbas aljannun ne tun da a d’akin da hajja take sauka suka sauka yau kam sun gasgata zancen hajja. Jin shigowar su mommah yasa shatu shiga d’aki da sauri tana tuntsira dariya. Amma mamakinta d’aya me yasa Imran bai tona mata asiri ba karo na biyu kenan yana kamata da irin wannan.shi kansa Imran tunda ya shiga d’aki yake smilling shi kad’ai ya lura yarinyar nan comedian ce ta bugawa a news.

Da safe ma basu koma d’akin ba a sashen amarya suka koma zama suna sake la’antar mommah don a cewarsu aljannu take turo musu ai kuwa indai sune su zuba su da ita gida dai baza su barshi ba sai sun kai kwanakin da suka ‘kayyadewa kansu tunda a goben zasu tafi abuja kai lefe. Hameedah tana sake girgiza ‘kafa ranta a matu’kar ‘bace tace “wallahi wannan matar muka ‘kyaleta nan gaba raba mu za tayi da yaya manga gaba d’aya dole mu tashi tsaye a kanta mu har a gaya mana malamai mu da
Muku jinin barebari.” Falmata ma cewa tayi”wallahi kuwa naga alama kuma lefe tayiwa kanta tunda hajja tace mu kai kada ma mu nemi danginta wallahi kaiwa zamuyi ke kuma shaheedah sai kin dage sosai duk abinda muka kawo miki kada kiyi wasa dashi munyi al’kawarin sai mun dasa mata ninkin ‘bacin ran da ta sakawa manga sai mu zuba mu gani tana ji tana gani Imran sai dai ta hange shi daga ness” gaba d’aya suka saka shewa har da amarya zainab. Fanna na gyara zama tace mai yafi wannan takaici ace d’anka yana auren ‘yar kishiyarka kuma zainab ke kin samu d’a daga sama kamar yarda uwarta ta samu manga daga sama suke juya mana shi son ransu.” Dariya suka ‘kara yi.


Ko da ta gama shirin school tana fitowa general parlour ta gansu murmushi ta saki ta fara wa’kar ado gwanja ta casss. A harzu’ke suke kallonta,Hameedah ta mi’ke da sauri tana jifanta da wani irin kallo “ke don uwraki da wa kike?” Shatu rausayar da kai tayi gefe kafin tace “kawai don ina wa’kata sai ki zageni” fitowar Imran da Ammar kenan sunyi shirin fita su ka ji hameedah tana wallahi sai na sake jibgarki kamar yarda nayi miki jiya shegiya mai idon aljannu.” Imran waro ido yayi yana kallon hameedah mamaki fal ransa lalle bata san sharrin yarinyar nan ba bata san itace gayyar aljannun da suke wajigasu ba, har shatu ta karkace zata yi rashin kunya Ammar ransa a ‘bace ya jata “wuce ki tafi school tun d’azu driver na jiranki kin tsaya jan magana.” Baki ta zun’buro irin na shagwa’ba “Yaya Ammar uwata fa ta zaga.” Harara ya zuba mata “kin wuce ko sai na mangareki tayi ta zaginki ma yana tsiro ne? Oya maza-maza wuce school kafin na sameki a wajen” sum sum ta wuce har taje ‘kofa ta juyo da ‘karfi tace “an fad’a d’in a sosa cass a sosa iya da razor.” Imran bai san sanda murmushi ya ku’buce masa Ammar kuwa darawa yayi sosai yace “kai shatu danger” hameedah kuwa ‘kwafa tayi tana zabgawa Ammar harara.


Kashegari kuwa suka isa abuja dangin baban shaheeda suka kai lefe ba tare da dangin mommah ko d’aya ba duk da kuwa suna cikin abujar. Haka suka dawo da sha tara ta arziki duk da suma ba lefen wasa suka kai ba lefene na gaske na gani a fad’a na kuma d’orawa a instagram,a yayata a duniya. Biki kuwa aka saka shi sati uku cif don suma dangin uban shaheedahn a shirye suke tsaf kuma masu farcen susa ne tabbas kuwa za’ayi biki na kece raini. Bayan sun dawo kano da kwana d’aya suka wuce maiduguri hannayensa dam’ke da sha tara ta arziki. Mommah ba tace musu Komai ba duk da ta tambayi Hajiya mama kuma ta tabbatar mata ba a gaya musu kai lefen ta basu ha’kuri. Hajiya mama ta girgiza kai a cikin wayar tace”Lala lala dijah ke zan bawa ha’kuri kiyi ha’kuri da jarrabawar da Allah yayi miki ta fitinannun dangi miji kina zaune ubangiji zaiyi miki sakayya suma fa mata ne kuma sun haifi mata ki zuba musu ido yanzu ubangiji ai tun a duniya yake sakayya ba kayi ba ma anyi maka ina ga kayi kiyi ha’kuri kullum shine abinda zan iya ce miki.” Hawaye ya zubowa mommah sai dai ba ta nunawa hajiya mama kuka take ba tayi godiya ta kashe wayar a zuciyarta tace “akwai ranar ‘kin dillaci ranar da zata cusa musu nasu ‘bacin ran dole ne su girbi abinda suka shuka d’a dai nata ne kuma ba zata bari su juya shi kamar yarda suke muradi ba.



*****************
A hankali awanni suka yi ta shigewa suna zama kwanaki daga kwanaki kuwa,har satittikan biki suka zo gidan a hargitse yake kowa sai shiri yake ana ji da lamarin bikin to ba dole ba ta kowane side jikan farko kuma d’an gaban goshi ake yiwa Aure,tun ana saura sati biki dahda yasa shaheedah dole ta koma gidan babanta duk da ba haka suka so ba uwarta taso ta tsaya ta cigaba da banka mata mallakin mallaka sai dai dole ta tafi. Hajja ma ana saura satin tazo ta tare a part d’in dahda daga gefe a babban parlournsa akwai wani bedroom and toilet anan ta baje danginta kuma suna d’aki mai Aljannu.

Mutanen katagum ma sun hallara ciki kuwa har da Dada tsohuwa mai ran ‘karfe. Tuni mommah ta fara gyara d’iyarta tsaf fatarta ta goge a spa haka nan an yi mata saloon gashin nnan an jawo shi tsahonsa har da na Mamaki.

Suna dawowa daga spa a gajiye suka tarar Hajiya mama tazo ita ma da ‘yan uwanta na yola ga Hafsa da Nahna da sauri shatu ta rungume uncle Hisham shi kuwa duk da nauyin da tayi masa haka ya shiga wulwulata yana fad’in a cafe a cafe ‘yar gidan mommah mai mommah ke baki ne kika yi wani fresh har glowing kike?” Kayan dad’i” ta furta tana murmushi har hushiryarta ta fito. Still Ammar yayi yana kallonta har bakinsa ya gaza shiru yace “mommah ‘karin gashi kika kaita aka yi mata da wankin fata?” Gaba d’aya gurin ba wanda baiyi dariya ba Hafsa tace “Ammar ko dai kana ciki ne a d’aura gobe da kai kawai.” Girgiza kai yayi “Ina ni ina rigimar shatu ni ‘kabilar ibira ma zan aura sun fi iya kula da miji” shatu ma harara ta zabga masa Allah ya kiyaye ma in aureka kayi fari da yawa ni nafi son irin Yaya Imran wanda baya magana sosai kai kuwa surutu kamar parrot.” Dariya sosai parlorn duka suka ganin Imran yana tahowa yana ware ido alamar yaji zancenta sarai. Tamke fuskarsa yayi ya zuba kallonsa akan shatu da tayi saurin jan gyale ta rufe fuskarta alamar kunya tsaki “kada ma ki saka rai da samun irina ke ai irinki Ammar d’in ne ya dace dake sai kuje ku haifi parrots d’in”Dada tsohuwa ta ta’be baki “Yo Allah na tuba kada dai inga mutum yazo yana ‘yar murya kana ganin yarinya zankad’aziyya wanke hannu ka ta’ba da mai matarka ta ka tafi ta to ku ku zama shaida ko nan gaba kada Imran yazo yace a bashi balarabiyar nan.” Tsaki yaja yana mi’kewa “MAI ZAN YI DA ITA? Ni kuwa God forbid gayyar ‘kazanta da surutun tsiya Ina da mata ta ‘yar gayu ta bugawa a jarida.” Ran shatu ne ya ‘baci tun da take bata ta’ba jin haushin kalamansa ba sai yau hawaye ya fara bin fuskarta.

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-18


ELEGANT ONLINE WRITERS


Sosai take hawayen saboda kalaman Imran sun ‘bata mata rai. Momma ta jata jikinta da sauri tana jifan Imran d’in da harara “fice min daga nan tunda burinka ya cika ka saka shatu kuka yo itama su’butar baki Tayi idan banda haka mai za tayi da kai a haife ka haifeta tunda ka ninka shekarunta.” Ficewa yayi ba tare da yace komai ba Allah ya tsari gatari da saran shuka” ya raya a zuciyarsa.

Ana gobe kamu masu tafiya abuja suka dinga dandazon tafiya dangin mommah dai ba suje ba a cewarsu bikin namiji suke zo ba ruwansu da dangin mace sun san ma kun sunje wula’kanci zasu sha,gida ya d’ad’e ba kowa daga mommah sai danginta suke Ta tsara yarda bikinsu zai kasance.Juma’a ne d’aurin aure don haka ranar asabar za suyi dinner lahadi suyi bud’ar kai ango ma alhamis d’in zasu wuce da abokansa da suka zo daga wurare da dama wasu ma ba ‘yan ‘kasar nan bane.


Don haka yau part d’insu na samarin gidan a cike yake sosai don ma babban parlour ne sai bedrooms guda hud’u a ciki don gidan dahda ba dai girma ba gari guda ne. Tana zaune a gefen dada tsohuwa tana shan dariyar labarin da dadan take bata na Imran da yake yaro yana tsoron saniya ita kuwa sai dariya take su antynta nahna suna zaune suna cire mata jan lallen da akayi mata na salatip ba ‘karamin kyau yayi ba ya haskaka kyakykyawar ‘kafarta ta.tana mi’kewa mommah Ta shigo parlourn tana dubanta daga ita sai wata riga da tsayinta yaje mata gwiwa sai skinny black pant ajikinta gashinta kuwa an tufke mata shi guda biyu ya

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment