Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

take tace “Ai Adda zata dinga kai muku abinci.” Dada tace “Wallahi ba inda zan koma dama mijin na sonta ne ma ga abin arziki amma gida ‘Kayan-‘kayau haka, Allah ya kaimu Ammar yayi aure na tare gidansa.”


Tunda ta dawo ba taga Dada ba hankalin ta ya tashi gashi bata da waya balle ta kira Mommah ga ‘yar banzar yunwa da take ji.

Da sauri ta fito main parlour sai ta tarar Ammar d’in baya nan, har ya tafi kenan yana ajiyeta, kamar wanda ake kora. Dama shi ya kawota shi Imran d’in wai yaje Abuja a ranar amma zai dawo da daddare.
Wuni guda tana cikin bedroom yunwa kamar ta kasheta, ga shi bata iya shan tea mai madara ba, dole ruwan lipton take ta sha. Tana juyo ‘kamshin girkin Shaheeda amma ko yunwa zata kasheta ba zata ce ta sammata ba.

Vest ce kad’ai a jikinta, sai Gashinta da tayi gammo da shi, ta fito main parlour ta zauna ta kasa ta tsare tana jiran Imran. Don bata son ya dawo bata sani ba,
Kuka ta keyi sosai saboda zuwa lokacin ta galabaita, dama tun asali bata iya ri’ke yunwa ba.
Yana bud’e ‘kofar parlourn ta taso a galabaice take tafiya har ta isa wajensa. Idanunta yana luuuu alamar lumshewa ta nuna masa cikinta, kafin kace mai tuni jiri ya d’ebeta ta zube a wajen. Da sauri ya tarota kafin ta kai ‘kasa a rud’e yake kiran sunanta yana jijjigata, amma ina Shatu an ji yunwa ta suma. Dai dai lokacin da ya d’ora bakinsa yana son hura mata iska don ceto numfashinta dai-dai lokacin Shaheedah ta bud’e ‘kofar sashenta take idon ta yayi kyakykyawan gani bakin Imran cikin na Shatu...........

Ps*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-26

Elegant Online Writers......

Da sauri ta zaro ido had’e da sakin kaskon turaren wutar da yake hannunta. ‘Karar abinneyasa Imran saurin d’agowa idanunsa cikin na Shaheedah da yake hango tsan-tsar bala’i a cikinsu. Cikin azama ya mi’ke yana gyara zaman Shatu a jikinsa, har a lokacin hankalinsa a tashe yake ganin bata dawo dai-dai ba. Da sauri ya d’aga ta cak rungume a jikinsa ya shimfid’eta kan kujera. Shaheeda kuwa ‘kara ware ido take tana kallon abinda yake wakana, yarda Imran yake wani lalla’ba Shatu. Da sauri ta ‘karasa wajen cikin masifa ta janye shi, ganin yana ‘ko’karin d’aga rigarta, duk hankalinta ya tashi gani take wani abin yake shirin yi, bata san Shatun bace bata da lafiya. Tayi saurin janyeshi tana furta “Wai Imran mai ye haka, a gabana kake nani’karta, a haka kake kwana gaya min Mai zaka yi da ita?” Tsaki ya ja, ya tureta gefe “Bari in gama ceton rayuwarta tukun sai kiyi duk abinda za kiyi.” Ta mayar idon ta kan Shatu,
Sai kuma ta saki tsaki “Munafurcin banza Wallahi ‘karya take yi, lafiyarta ‘kalau, karuwanci ne kawai.” Imran bai bi ta kanta ba sai d’aukan Shatu da yayi da sauri ya shige da ita part d’inta. A gadon ta ya kwantar da ita sannan ya shiga bathroom ya d’ebo ruwa ya watsa mata a fuska, sai a lokacin ta kawo ajiyar zuciya, numfashinta yana fita sama-sama. Ta bud’e idonta akan Imran da yake tsaye a gefenta. “Ruwa” tace masa a cikin wata galabaitacciyar murya.

Da sauri ya fice a kitchen d’in ta ya samu ruwan, sai kuma yayi tunanin ruwan zai iya ‘kulle mata ciki musamman kasancewar cikin bakomai. Da sauri ya jona kettle, ya koma d’akinta kafin Ruwan ya tafasa. Sam a tsorace yake baya son wani abu ya sameta ya san Mommah ba zata ta’ba yafe masa ba.
A jingine ya sameta jikin Gadon a ‘kasa, idanunta a lumshe da alama tana jin jiki. “Kiyi ha’kuri yanzu Ruwan zai tafasa kin ji” karo na farko da yayi mata magana da muryar tausasawa, wanda har yasa ta d’ago ta kalleshi, kallon da ya jawo abubuwa da yawa, kallon da ya jawo mata tsananin ‘kaunarsa har taji zuciyarta na bugawa tamkar ta fasa ‘kirjinta ya fito,
Yanayin yarda yake mata magana abu ne abin so a wajenta, ba ta’ki su dawwama a haka ba yana nuna mata kulawa. A hankali tace “Ruwa fa nake son sha.” Ya girgiza kai “Idan kika sha ruwa cikin ki zai yi ciwo saboda bakomai a ciki, ina zuwa.” Da sauri ya fita daga d’akin.

Tea ya kawo mata mai zafi, sai dai yana saka shi a bakinta tayi saurin girgiza kai. “Why?” Ya furta a hankali. Muryar da ta tsarga mata har zuciyarta taji tsigar jikinta ta tashi abinda bata ta’ba ji ba,wani yanayi take jin kanta a ciki, yanayin son kusantar d’a Namiji. Duk da bata banbance yanayin ba tunda ba sanin menene sha’awa tayi ba,Ganin ya ‘kura mata ido yasa tace “Ba na shan madara.” Dafe kai yayi “Oh God mai zaki sha yanzu?” ‘Kara lumshe ido tayi tace “ka kaini wajen Mommah ita kad’ai nake son Gani.” Ware ido yayi kamar yarda ya zame masa al’ada yace “Ganin Mommah a wannan lokacin ai masifa ce a wajena don tsaf zata iya yi min baki.”
Murmushi ta saki bayan ta ga ya fita, ta bi bayansa da kallo, tunani sosai ya shiga zuciyarta ina ma su zauna a haka dimin da’imun cikin farin ciki da walwala, kamar yarda Burin Mommah da fatan ta yake kullum.
Yana fita part d’in Shaheedah ya bud’e, tana zaune cikin tashin hankali idanunta yayi ja alamar ta ci kuka sosai. Zama yayi a gefen hannun kujerar da take, ya rungumeta ta gefe, murya a cunkushe yace “Please Habibteey I need a help.” Kallon banza ta watsa masa, kallon da ya bashi mamaki har bai san sanda yace “Ni kike wa wannan kallon?” Tsaki taja ta mi’ke “Ai wallahi Imran zaka san ni ka wula’kanta akan waccen ‘kwailar yarinyar kullum zancenka mai zaka ya da ita? Gashi yau Allah ya toni asirinka na ga zahirin abinda zaka yi da ita. Shame on you wallahi.” Ransa ne ya ‘baci har bai san sanda yace “Haram na aikata? duk da ba abinda kike tunani bane kuma idan shi d’in ne ma ai halak d’ina ce sadaki na biya aka d’aura aure, kawai ina ganin yarinya unconscious sai in tsallake na barta saboda ina tsoronki sai na bari Allah ya kama ni ko?”
Yana fad’in haka ya wuce Dinning da niyyar ya d’ibarwa Shatu abinci, ya bar Shaheedah a tsaye baki a sake tana kallonsa, cikin tsananin mamaki har murza ido take don ta tabbatar, zahiran ta ga Imran ne dai tsaye, Imran da Antyn ta da su Hameedah su kayi Al’kawarin ko za suyi yawo tsirara sai sun mallaka mata shi. Shine yau a tsaye yake Gasa mata magana son ransa, lallai dole su tashi tsaye aikin Mommah yafi na su ‘karfi. Har ya d’ebi abincin yana shirin fita ta yi saurin daka tsalle ta fisgo shi da ‘karfi ta baya. Da sauri ya juyo ransa a ‘bace yace “Me ye haka?cika ni.” “Ba zan cika ka ba sai ka bani abinci idan yaso kaje kaci na Shatun tunda ka riga ka raba mana kwana.” Ran sa a ‘bace ya mi’ka mata plate d’in abincin, ya fita da sauri tunanin halin da Shatu take ciki.

A toilet ya same ta tana ta kelaya amai ta galabaita sosai, ya tsaya daga bakin ‘kofa yana yi mata sannu. Jiri ne yake d’ibarta haka ta fito tana yin kamar ta fad’i. Da sauri ya ri’keta ya rungumota jikinsa. Hankali tashe yake mata sannu. Ta bi shi da kallo ita ba tayi tsammanin ma zai dawoba. Kwantar da ita yayi da sauri ya shiga kitchen d’inta, Allah yasa ya iya girki ya fara ‘ko’karin soya mata ‘kwai mai kauri.

Cikin mintuna kad’an ya gama suyar ya had’a mata tea mai Milo zalla yayi shi da kauri sosai. Yau dai su Imran anyi abin arziki.

Yana ajiye abincin yayi ‘ko’karin mi’kar da ita zaune, rabin jikinta duk a jikinsa yana jin yanayin yarda jikinta ya d’au zafi hakan yasa d’imin jikinnata yake shigarsa sosai, daurewa kawai yake amma lamarin ya fara fin ‘karfinsa. Sharewa yake a zuciyarsa yana yakicewa yana sanyawa a ransa ba sha’awa bace, ina ai bata kai munzalin da zaiyi sha’awarta ba,Mai ma zai yi da ita? shi har kullum kallon ‘kanwarsa yake mata. Zame ta yayi daga jikinsa don abin ya soma fin ‘karfinsa, ya jinginata da bed d’in, ita kanta hakan yafi mata kwanciyar hankali saboda yarda turarensa ya ke sanya ta cikin wani ba’kon lamari. A hankali yake bata tea d’in wani sa’in cikin rashin sa’a idanunsa su sar’kewa cikin nata. Da sauri yake d’auke kai baya son al’amarin yayi tasiri mai girma a zuciyarsa.



——————

Dai-dai lokacin da hakan take waka na a tsakaninsu, a lokacin Shaheedah hankalinta yana can a tashe,ta rasa yarda zata sanya kanta taji dad’i. Tabbas ya zama dole a daren yau ta yi amfani da maganin nan ta kuma kulle ‘kofarta idan yaso yaje ya sauke bu’katarsa akan Shatu. Sam ba zata jure ba, ba zata jure zama da Shatu a matsayin kishiyarta ba, tabbas idan hakan ta kasance zuciyarta zata buga. Ta kai Mari ta kai gwauro tana tunanin yarda zata soma. Da sauri ta d’auki ‘kullin maganin ta isa part d’in Imran cikin ikon Allah kuwa ta tarar da baya nan.
Da sauri ta bud’e heaterr da ke gefen gadonsa, da yake ajiye da ita saboda kullum cikin dare sai ya sha tea kamar buzu, ko da yake gida da irin heaterr a side bed drawer d’insa. Ta kunce ‘kullin maganin da sauri ta zazzaga, ta mayar ta rufe. Cikin azama ta koma side d’inta. Sai da ta shiga bedroom sannan ta saki ajiyar zuciya gani take kamar burin ta ya cika an gama, gobe da sassafe Shatu zata jewa da Mommah Mummnan labari, wanda ita zai zamewa mahaifiyarta da su Hajja labari mai tagomashin dad’i. Ta kwanta flat a kan gado tana sakin murmushi, duk da ta wani gefen zuciyarta na zafi ta san yau Imran zai kusanci Shatu, kusancin da zai zamo masa tamkar d’and’ane first and last a rayuwa, don boka ya tabbatar mata matu’kar ya sha maganinnan to kuwa ba zai gushe a rayuwa ba sai da tsananin ‘kiyayyar Shatu.




———— Gefe d’aya Imran yana can yana fama da Shatu, da ta sake narke masa, bayan gama cin abincin ma amai tayi. Hakan yasa dole ya kira Doctor ya gaya masa. Doctorn yayi masa prescribing magani yace ya siyo ya bata. Hakan yasa dole ya tafi siyowa. Ko da ya dawo Shatu ta sake galabaita, da kyar ta sha maganin ta sha kuma lucozade d’in da ya siyo mata. Sannan ya shiga ya had’a mata ruwan wanka mai zafi. Yana fitowa ya mi’kar da ita tsaye sai sannan ya kula da ‘yar ‘bingilar rigar da take jikinta, wanda da ita da babu duk d’aya. Idanunsa suka sauka kan matasan boobs d’inta da sauri ya d’auke kai, zuciyarsa tana bugu al’amarin da har mamaki ya bashi, yayi saurin juyawa ya fice daga bedroom d’in yana fad’in “Please ki daure kiyi wanka ki sha magani zaki samu sau’ki insha Allah.” Yana shiga bedroom d’insa ya kulle da key ya bar key d’in a jiki don ma baya so Shaheeda tazo ta saka masa ciwon Kai.

Sai sannan ya saki ajiyar zuciya tabbas shi kansa ya san ya wahala kuma ba don komai yayi ba,fad’an Mommah ne baya so. Ga shi a week d’innan yake saka ran shirin sa na komawa turkey da Shaheedah ya tabbata,baya son yayi abinda zai sosa zuciyar Mommah ta hana shi tafiya. Gwara ya lalla’ba ya tafi ya bar mata ‘yarta idan yaso idan ta girma idan yana da ra’ayi ya tare da ita.

Toilet ya shiga yayi showering kan sa sannan ya fito d’aure da toilet a Jikinsa, kafin yayi shirin saka kaya sai da ya kunna heater d’insa, sannan ya shafe jinkinsa da lotion jergens sannan ya sa turarensa a jikin pyjamas d’insa farare tas dasu jikinsu kamar auduga, ‘kafarsa sanye cikin room sleepers wani mai gashi a jikinsa, zama yayi a gefen gadonsa yana kunna babbar plasma tv d’in dake jikin bangon bedroom d’in, yayi mamakin da Shaheedah bata biyo shi ba,
A zuciyasa yace “Kishi kumallon mata ban da abin Shaheedah mai zanyi da ‘kwailar yarinyar nan? Duk da yau da na ganta ta bani mamaki yarda ta fi Shaheedan cika ta ko ina duk da ‘kan’kantar shekarunta. Ya lumshe ido yana sake kallo surar Shatu a cikin ‘yar ‘bingilar rigarta. Da sauri ya kawar da wannan tunanin had’e da cewa “God forbid idan ba so nake su Ali da sauran mutane su saka ni a wa’ka ba” ya ware ido yana tunanin yarda zai shiga tashin hankali idan hakan ta faru ina zai ‘boye kansa?” Murmushi ya saki yana tunanin yarda lamarin zai kasance. Da sauri ya mi’ke had’e da cewa Allah ya kiyaye yana ‘ko’karin yakice tunanin daga zuciyarsa.”


Tea ya had’a mai zafi yana sha yana kallon series na korean film,har ya shanye ya ‘kara zuba wani, shima ya shanye sannan ya mi’ke ya kashe t.v d’in ya kwanta. Ba zai kira Shaheedah ba don ya san ko ya kira ta wula’kanta shi zata sake yi yau dai kam zai bar ta sai ya koya mata hankali.

Amma mai? Sam ya kasa barci surar Shatu tsaf ta mamaye idanunsa da zarar ya rufe ido ita yake gani, wata zazzafar sha’awa Na ratsa duk sassan jikinsa, tun daga kansa har zuwa babban d’an yatsan sa tun yana d’aukar lamarin wasa har abin ya fara gagararsa. Da sauri ya mi’ke a daddafe ya fita direct sashen Shaheeda ya nufa......

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-27

Elegant Online Writers.......


Cikin rashin sa’a bayan ya murd’a ‘kofar d’akin ya tarar da ita a rufe. Nocking ya shiga yi tun yana yi a hankali har ya koma yi da ‘karfi amma Shaheedah bata bud’e ba. Cikin tashin hankali ya koma part d’insa ya samo spare key na part d’in nata sai dai ya tarar da d’akin ya ‘ki bud’uwa alamar da key a cikinsa ta baya. Jikinsa a sanyaye ya koma bedroom d’insa. Cikin yanayin da shi kansa ba zai iya misaltawa ba, yanayin da ko yana saurayi bai ta’ba shiga irinsa ba.

Kwanciya yayi ruf da ciki a kan gadon sa yana runtse ido da addu’ar Allah ya lafar masa da
Abinda yake damunsa, amma abin ka da yanayi na sihiri abin ‘kara gaba yake masa. Ganin yana neman hallaka yasa ya mi’ke yana tunanin samun fita, ji yake kamar yaje waje ko karuwa ya nema duk da bai ta’ba aikata zina ba. Sai dai take zuciyarsa ta hasasho masa halalinsa Shatu, tsoron Allah ya shige shi yaga gwara yaje ya kusanci Shatun domin ita halaliyarsa ce, da yaje yana bin matan banza a titi. Da sauri ya mi’ke bayan zuciyarsa ta gama hasasho masa Shatu ce mafitarsa.

Ya dad’e a tsaye a ‘kofar d’akin yana sa’kawa da warwara tsawon mintuna talatin yana shawarar shiga ko ya koma, amma jin lamarin yake kamar zai iya rasa ransa matu’kar bai kusanci mace ba. Ransa a ‘bace yana jawa Shaheedah Allah ya isa ya bud’e d’akin Shatu ya shiga.
Kwance ya sameta tana barcinta peacefully alamar lafiya ta samu,
Ya dad’e yana ‘karewa kyakykyawar surarta da kyan fuskar ta kallo, zuciyarsa tana ayyana masa tabbas idan ya kusancetan zai ajiye komai ya rungumi matarsa su zauna lafiya, ya kuma nuna mata soyayya sosai zahiran wa bad’inan ko da hakan yana nufin abokannasa za su tara mutane suyi masa dariya. Yanzu kam ya amince yana son Shatu So kuwa ba na wasa ba, yanzu ne ya fahimci yana da abinda zai yi da ita, ya ‘kalubalanci furucinsa na Me Zan yi da ita? Ashe wannan lokacin zai zo da zai ji son Shatu? Ya runtse idanunsa yana switching light d’in d’akin, zuciyarsa na harba masa da ‘karfi wai yau shine yazo Gadon Shatu da niyyar sauke bu’katarsa ta aure, tabbas Allah Alhakamu mai juya lamari yarda ya so ya kuma tsara shi a lokacin da yaga dama.

Kyakykyawar rungumar da yayi mata da ‘kamshin turarensa da ya ziyarci hancinta shi ya farkar da ita daga barcin wahalar da ya d’auketa,cike da tunani da tsananin ‘kaunarsa a ranta, don bata sam ma ta yi barcin ba, saboda yanayi tunanin da ta lula.

Gaba d’aya ta ji ya lula ta wata duniya, duniyar da bata ta’ba mafarkin shiga nan kusa ba.yanayi mai wuyar fassaruwa, yanayin da zata so ta dawwama a cikinsa dimun da’iman, ko da ace mafarki ne ba zata so ta farka ko a tashe ta ba, balle ta tabbatar zahiran ne abinda yake aiwatarwa a jikinta. Imran mutum ne na daban da ya iya nunawa mace zallar soyayya tattali da shagaltar da gangar jikinta a wani al’amari can daban da ya zama sirrinsu ne. Sirri ne mai wuyar fallasuwa ga ma’aurata masi koyi da sunnar manzon Allah da yace a ‘boye hakan kada a fallasashi. Mai fallasa shi kuwa ya zama daga cikin mutane mafiya shashanci a duniya.

Shi kansa Imran ya lula wata duniyar, duniyar da bai ta’ba tsintar kansa a cikinta ba a lokacin da yake mu’amalantar Shaheedah, akwai banbanci mai tarin tazarar gaske, banbancin yana yin taushin fata santsinta da laushinta, da wani kuma al’amari daban da bai ta’ba jin sa a baki da sassan jikin Shaheedah ba. Tabbas yanzu ya yarda mata ma suna suka tara ya yarda ko wace mace da baiwarta. Ya samu Shatu a yanayin da yake so matarsa ta kasance kuma ko a aljannah aka bashi za’bi akan Shatu da hurulaini zai yi fatan kasancewa da Shatunsa. A kunnenta yake ta jera Alhamdulillah ala ni’imatihi, sai wasu zantuttuka da ya dinga fad’a mata tun kafin ya kai ga sanin ta d’iya mace, wanda zantuttukan kad’ai sun isa sanya ta ‘kololuwar alfahari idan kuwa ta tuna dasu ko da nan gaba ne sun isa su saka ta nishad’i ta kuma san tabbas Imran ya kai ‘kololuwa a cikin. ‘Kaunarta.

Komai ya kammala cikin hukuncin ubangiji ya kuma samu Shatun sa fiye da tsammaninsa ciki da waje sai dai yace Alhamdulillah.
Ita kuwa duk da tsananin azaba da taje ji bata saki baki tayi masa kuka ba, kamar yarda Shaheedah tayi shi kansa ya san Shatu akwai dauriya kamar yarda yake son matarsa ta kasance.

A cikin daren ya had’a mata ruwa mai zafi, ta gasa jikinta sosai tana yi tana daurewa don ba ‘karamar azaba ta sha ba. A gefen Gado ta zauna shi kuma ya fita da sauri cikin azama ya had’o mata tea mai zafi ya kawo mata sannan ya bata pain reliever ta sha, yana yi yana kallon fuskarta yana sakar mata murmushi alamar lamarin yafi gaban furtawa a baki. Ita kuwa tsananin kunyarsace take d’awainiya da ita don haka ta mi’ke da sauri ta zira hijab. “Muyi Sallah” ta fad’a a hankali murmushi ya sakar mata “zaki iya” ta d’aga kai kawai tana wasa da yatsunta. Saboda Shatu akwai Ibada kuma malamanta na Islamiyya sun gaya mata kada tayi wasa da ‘kiyamallaili itace makamin ‘kare dangi.

Sun yi salloli duk da ita a zaune tayi don ba zata iya yi a tsaye ba ya kama kanta ya dinga zubo addu’oi har abin ya bata mamaki ashe yana da ilimin addini haka, sam a haka sai ka zata bai damu da ibada ba. Yana shafawa ita ma ta shafa, tana shirin mi’kewa ya kama hannunta “Gwara da kika tuna min dama na shigo a wani yanayi shi yasa ba muyi sallahr ba amma yanzu ma da mukayi lokaci bai ‘kure mana ba.” Ya ja ajiyar numfashi sannan ya mi’ke yana kama ta ta mi’ke tsaye a kunne ya rad’a mata “ubangiji Allah yayi miki abarka ya bani ikon kyautata miki sannan kuma don Allah ki manta abinda ya faru.” Ta d’aga kai tana murmushi, da kansa ya zare mata hijab d’in ya d’auketa cak sai kan Gado, su kayi kwanciyarsu cikin yanayi na matu’kar jin dad’i, ya kuma rungumeta tsaf a jikinsa kamar wani zai ‘kwace masa ita.”


——————-
Shaheedah kasa runtsawa tayi cikin daren, kuka kuwa ita kanta ba zata iya irga adadin da tayi shi ba, kukan take ba ‘ka’k’kautawa tana dana sanin bata zuba masa maganin ba. Bayan ya gama buga ‘kofar tana le’kensa ta ga kuma san da ya fito daga bedroon d’insa ya shiga d’akin Shatu. Hankalinta tashe ta shiga buga kanta a jikin wardrobe tana kuka, ga numberr Antynta ta ‘ki shiga. A zuciyarta ta dinga ayyana shikkenan yau Imran ya d’and’ana wata macen duk da dai ta san i gobe aure ya mutu murus. Tunaninta ne ya tsaya cak lokacin da ta tuna iya zallar maganin na zubawa a shayi ta bashi ya sha bata bashi na naman ba. Ta zaro ido da sauri tana mi’kewa bata son a samu matsala, zuciyarta ta shiga harbawa ya akayi ta manta? Bayan mutumin ya ja kunnenta akan kada tayi kuskure yanzu tsoronta d’aya akan mai zai faru? Bata son lamarin ya juye kanta. Da sauri ta sake buga wayar Antynta cikin sa’a a lokacin ta shiga. Hankali tashe ba tare da gaisuwa ba tace “Na shiga uku Anty.” Da sauri Antyn tace “Da aka yi me? Kin kuwa duba time Shaheedah past 3:00am fa.” Cikin kuka ta shiga bata labari. Antyn ta zabga salati “lallai kuwa Shaheedah dole kice kin shiga uku ba ke kad’ai ba ma har ni. Wace irin wauta ce wannan? Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna sai fa da na ja kunnenki akan kada ki bada maganin ba tare da mahad’insa ba saboda shiriritarki yasa nace duk sanda zaki bayar ki nemi shawarata saboda in tuna miki yanzu ga shi kinje kin ji’ka mana aiki. Sai ki jira zuwa wayewar gari muga abinda zai faru. Yanzu na san ko na kira Shuwa wayarta ba shiga zata yi ba tana can tana yawon banza.” Kuka Shaheedah ta saka kalmar Na shiga uku kuwa ba ta bar bakinta ba.

Ai kuwa Shaheedah yarda ta ga rana haka ta ga dare gashi taje ta ga Imran bai dawo d’akinsa ba. Ta tabbatar har a lokacin yana tare da Shatu, hakan ya dad’a d’imauta zuciyarta, ta tabbatar da maganin yayi aiki da yanzu wani zancen ake ba da ba wannan ba.

Har Asuba tana jiran wayar Antynta. Sai da aka idar da sallah sannan Antyn ta kira, duk da ita Shaheedahn ko sallahr ta gagara yi. Da azama ta d’aga wayar cikin murmushi Antyn tace “ki kwantar da hankalinki boka yace wa Shuwa bakomai tunda har ya sha na shayin, sakin zai yiwu ‘kiyayyar ce nan gaba zata iya gushewa amma kafin lokacin za’a san abin yi in dai sakin ya yiyu za’a yi musu farra’ku. Yace na tsananin tsanar a cikin naman yake.” Shaheedah da sauri ta saki dariya cikin zakwad’i tace “Har naji dad’i da wallahi hankalina a tashe yake. Ina godiya Anty na samun kamarki sai an tona really proud of you yanzu shegiya yau zata je musu da black news.” Ta she’ke da dariya Allah dai ya bar mana Anty shuwa” Anty tace ameen ai ta cika aminiyar ‘kwarai.”



(Masoya na kuyi ha’kuri da jinkirin da aka samu yau biki muke wallahi shi yasa ma zaku ga typing d’in kad’an ba haka na so ba. Sannan gobe insha Allah ba typing ina da babban uzurin da zai ri’keni zuwa jibi dai insha Allah zaku ga typing mai yawa. Wallahi ina sonku sosai kamar yarda kuke son books d’ina domin da bazarku nake taka rawa💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿💃🏿)

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-28

Elegant Online Writers.


Cikin daren ya farka yaji kansa yayi nauyi yana wani irin sara masa tamkar zai rabe gida biyu. Zai iya cewa tunda yake a rayuwarsa bai ta’ba jin kwatankwacin wannan ciwon kan ba. Idanunsa har dishi-dishi suke ga ni. Da kyar ya mi’ke yana ture Shatu daga jikinsa ‘ko’kari yayi sosai ya kai kansa bakin ‘kofa, zuciyarsa na hassala da bugawa da ‘karfi ya fice daga d’akin, burinsa dama ya fita don sam baya son ganin Shatu da take kwance a gefensa, tsanarta sosai ta d’arsu cikin zuciyarsa, fiye da
Kwanakin baya. Da azama ya isa part d’insa. Turus ya zauna a gefen resting chair da

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment