Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ina fa Mommah gamu nan muna tare.” Mommah ta saki salati “kuna tare a gidan uban wa?” “Haba Mommah ki kwantar da hankalinki ni fa mijinta ne ku da kanku ku ka fad’a to me ye na........” a zafafe ta katseshi “Wallahi Imran ka jini da kyau idan ka sake ka bud’ewa yarinyar nan sirrin da yake cikin aure zaka gamu dani nawa Shatun take?” Cikin dakiya yace “Amma ku kayi mata aure Mommah ku fa kuka ce duk hakkinta a wuya na yake..” “Uban ka nace Imran, kaci uban ka ka dawo min da yarinyar nan yanzunnan wallahi ko ranka ya ‘baci.” Ta kashe wayar tana jan salati “Na shige su nima wa ya aike ni?”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-24
Elegant Online Writers..


*_Masu son Littafin MIJIN MALAMA suyi following Acct ɗin nan a Arewabooks👇🏾_*
https://arewabooks.com/u/nimcyluv



Bai Tashi mayar da ita gida ba sai da yaga 3:00pm sharp, lokacin yunwa ta ci ta cinyeta. Ranta duk ya gama ɓaci da wannan mulkin mallakar, ta na kallo ya fito fuskar shi fresh da alama wanka ya yi ya fito. Ita ɗin ma watsa mata kallo ya yi “Tashi Malama kije kiyi wanka ban son ƙazanta, ba za ki shigar min mota ba sai kin yi wanka tun safe har 3:00pm” Marairaice fuska ta yi, idanunta yana shirin kawo ƙwalla ta ce “Don Allah Ya Imran ka bari idan naje gida zan yi” Ya girgiza kai ya ce “Ba zan iya ba kusan 7 hours rabonki da wanka, sannnan ki shigar min mota? yi sauri I have something to do kina wasting time ɗina” Miƙewa ta yi bisa tilas ta shige cikin ɗakin don yin wankan.


Suna parking ya watso mata kallo “kada ki manta da alƙawarinmu, idan kuma kin ƙi ki shirya karɓar haƙƙin ki na aure,don in dai na gan ki a gidana na san kin zaɓi zama cikakkiyar House wife” Ta ɗaga kan ta kawai,ta fice daga motar cikin azama. Imran ya bita da murmushin mugunta, ko ba komai ya san yau ya kaɗar da hanjin Mommah.

Tana shiga gida ta tarar da su Hajja a main parlour na gidan, bisa tilas ta durƙusa ta gaishesu, ko ba komai dole ne ta bi umarnin Mommah, sai dai ko kallo bata ishe su ba, har da masu harara da zabga tsaki, tana ji Hameedah tace “shegiya mai siffar jinnu” Girgiza kai tayi a zuciyarta tace zamu haɗu wallahi kafin ki tafi.


Ba kowa a parlourn Mommah, hakan yasa tayi saurin shigewa bedroom ɗinta, sai dai tuni Mommah taji motsin ƙofarta hakan yasa ta fito da sauri har tana yi kamar zata faɗi
A bakin Gado ta tarar da shatu tana zaune ta zabga uban tagumi,idanunta ya ɗan kaɗa alamar yunwa da barci ne a cikinsu,sai dai ita Mommah tuni tayi wa hakan wata fassarar ta daban.
Da sauri ta dafa ta tana zama a gefenta tace “Shatu hope ba abinda yayi miki? Ko ya miki wani abin?” Girgiza kai tayi hawaye na zuba a idon ta, ta rungume Mommah,hankalin Mommah idan yayi dubu ya tashi,ta
dinga salati tana tafa hannu “Tashi mu gani muje toilet.” Shatu ta riƙe hannunta tana girgiza kai “Mommah ba komai ni dai don Allah bana son auren yanzu bana son na tare please Mommah.” Kuka take sosai hankalin Mommah ya tashi,saboda bata tabua ganin Shatu a wannan halin ba.

“Kin tabbatar ba abinda ya yi miki?” Ta ɗaga kai kawai,tana ci-gaba da share hawayen fuskarta.Mommah ta girgiza kai “To me yasa ba kya son ki tare?” Kuka ta sake saki kafin tace “Mommah bana son na haihu yanzu,ya ce kuma idan na bari na tare yanzu sai ya buɗe min duk da wani sirri na aure" Mommah ta saka salati kafin tace “Amma Imran ya iya tsiya, bai dai yi miki komai ba bayan hakan ko?” Shatu ta ɗaga kai “Shi ke nan ki barni da shi ai ba ke kaɗai zaki tare ba da Dada zan haɗa ku,kuma ɗaki ɗaya zaku dinga kwana, ki rabu dashi tsokanarki yake ba abinda zai iya yi miki. Yanzu ki tashi kije ki ci abinci ko kin ci?” Tana share hawayenta tace “Ban ci ba tun breakfast” Mommah ta miƙe tana cewa “okey maza kije ki ci abinci,ni ma kasuwa zan je yanzu zan dawo.” Daga haka ta fice ita kuwa Shatu kwanciya tayi idanunta a lumshe tana tariyo moment ɗin da ya gaba ta. Gaba ɗaya jikinta Ƙamshin turarensa yake duk da tayi wanka. Ƙamshin da take masifar so,don haka ta kasa cire kayan.




Babu wani gyaran jiki da aka yi mata,duk da Dada tana ta maganar gyaran jikin, Mommah kuwa tace ba yanzu ba tunda yanzu ba zaman Aure za taje yi ba. Ita kuwa Dada da kanta ta bawa mai gadi kud’i yaje kasuwa ya siyo mata kayan magunguna tace suna tarewa zata fara banka mata.
Masifa take tana ‘karawa “Ni ban ga dalilin wannan tsiya ba ace wai Auren da aka yi ba yanzu miji zai tare da matarsa ba, to ba dani za’a yi wannan shirmen ba.”




Imran gani yayi kawai ana ta shiga da kaya na gani na fad’a, bugun turkey, ‘bangaren Amarya ya fara d’aukan harami kamar a ‘kasashen ‘ketare. Ransa ya gama ‘baci ya tabbatar shatu bata ji jan kunnen da yayi mata ba kenan. ‘Karshe don takaici ficewa yayi ya bar gidan zuciyarsa a hassale, musammman ganin yarda shaheedah ta hassala,sai kuka take masa.




Kashegarin Ranar Mommah ta shirya walima gagaruma, a kuma ranar aka yi kamun Amarya Shatu. An ci an sha an kuma yi wa’azi sannan Mommah tasa aka yi saukar Al’kur’ani, da niyyar Allah ya basu zaman lafiya ya sanya albarka a auren. Ango dai ko gidan bai zo ba.
Mutane da dama walimar ta burgesu, har suka gaza shiru suke fad’an dama haka aka dawo ake yi a kowane aure, aka rage bidi’a ko don samun albarka a Aure.

Tsirarun mutane ne suke fad’ar haka, yayinda majority abin bai burgesu ba, musamman dangin Dahda da suke ta’be baki suke fad’in Iyayi ne da son a sani, ta kuma nunawa mutane wai ita mai tsoron Allah ce. Bata ce komai ba duk da zancen yaje har kunnenta tace “Allah ne kad’ai ya san zuciyar bayin sa.” Don haka sam surutun jama’a baya damunta.


Rabuwar Mommah da Shatu, abu ne da girgiza zuciyarka in dai kana wajen, Shatu kuka take kamar ranta zai fita, musamman idan ta tuna al’kawarin Imran na aikata mata irin abinda aka yi wa ‘yar gidan maigari matu’kar bata saka Mommah ta janye auren ba,haka ne yake sake tunzura zuciyar Shatu take kuka kamar zata mutu.
Mommah ma kukan take, tana ji kamar ta saka Imran ya saki Shatu tausayinta yana sake tsirga mata.Ta rungumeta sosai a jikinta, tana rad’a mata kalamai masu dad’i, wanda duk uwa ta gari ya kamata ta gayawa d’iyarta,yayin sallamar Aure. Tabbas rabuwa da gida abu ne mai ciwo Shatu,sai dai fatan dacewa a gidan Aure.

Haka tana ji tana gani aka raba ta da jikin Mommah, su Anty Nahna suka jata jikinsu.

Kamar yarda ake a al’adance dole sai an kai ka wajen dangin miji, itama Shatu haka aka dangana ta da na ta dangin mijin. Sai dai ba wanda yayi musu kar’ba ta mutunci musamman Hajja da tace ba zata kar’bi amana ba,haka nan cikin yaranta bata amince wani ya kar’ba ba. Ta ‘kara da cewa “Ai ita ‘yar gata ce sai a mi’ka ta gurin uwar mijinta kuma uwar ri’konta mai zai dame ta?” Ba wanda ya tanka su kamar yarda Hajiya Mama ta ro’kesu, kada suyi abinda za’a tafi dasu a baki.




——————————————-
Gefe guda kuwa Imran yana can zaune a part d’insa, yana kallon Shaheeda da tabi ta nad’e masa a jiki,tana kukan shagwa’ba, zuciyarsa har ta fara tunzira da rashin ha’kurinta.
A zafafe ya janye jikinsa cikin kaurara murya yace “Wai Shaheedah ya kike so nayi ne? For Goodness sake, nace miki nima ba a son raina aka yi aurennan ba, ba kuma a son raina ta tare ba, ki barni mana kiga hukuncin da zan d’auka.” Cikin Muryar kuka tace “To kada ka kula ta please!” Tsaki yaja yana zabga mata harara “In kula ta ince mata me? Wannan yarinyar ‘karama kada ki sa wa zuciyarki ma banzan tunanin nan, ki barni na san yarda zan ‘bullowa lamarin.” Shaheedah ta shafa gemunsa tana murmushi, Hankalinta kam yanzu ya kwanta.


Duk bugun da dangin amarya su kayi, a ‘bangaren uwargida ba’a bud’e ba, hakan yasa aka sadata da nata ‘bangaren ko bakomai dai sun fita ha’k’kinta.


Masha Allah Aljannar Duniya. Haka kowa yake cewa idan ya shiga part d’in Shatun Mommah, yayi matu’kar kyau iya kyau. parlour ‘karami daga farko da bedroom d’aya da suka ji turkish furniture, sai kuma ka shiga wani Babban parlourn shima mai d’auke da Royal furnitures complete set da dinning set duka iri d’aya Golden and Milk colour,curtains d’in parlourn da kujerun irin d’aya. Ga manyan turkish carpets malale a kowacce kusurwa. Bedroom d’in irin kayan parlourn ne da alama haka suka zo a set. Sai kitchen shima Babba ne sosai da store a cikinsa,komai na kitchen d’in black and white ne, hatta tiles da wall tiles da cabinet d’in. Kai su Mommah sun yi ‘ko’kari sai dai muce Allah ya ‘kara zumunci.
Yarda ‘kasa yake haka sama yake sai dai shi sama bed roon uku ne da kuma terrace a saman gidan, saman ma ya sha turkish furnitures da Royal furnitures, adon Blue and Golden, d’ayan parlourn kuma Black and white.
Ko makaho ya shafa ya san part d’in Shatu yafi na Shaheedah komai da komai, babu ma had’i.



Duk ‘yan kai amarya suka watsa ya rage daga Dada ‘yar zaman d’aki sai Shatu. Babu abinda ya dameta tana zaune tana ‘karewa d’akin kallo, wani farin ciki yana ratsa ta, a zuciyarta tana tunanin wai ita dai Shatu, Shatun ‘kauye Shatu mai idon mujiya ta ‘kauyensu itace Allah yayi wa Gam da katar da alheri haka, kuka d’aya take na rabuwa da Mommah da kuma tunanin kada Imran yayi mata irin abinda aka yiwa ‘yar gidan mai gari da ba abinda zai dameta.

Dada tun tana mitar rashin shigowar ango har ta gaji ta fara gyangyad’i, ita kuwa Shatu ba abinda ya dameta ya shekara ma bai shigo ba matsalarsa ce. Ta shige had’ad’d’en toilet d’in ta tayi wanka tayi brush, sannan ta fito tayi shirin barci dama tayi sallahr ta. Ta you kwanta a gefen da Dada take kwance a gadon.


Cikin barci taji Dada ta d’aka mata duka “Ke tashi lusarar banza la’ilahailallahu mai zan gani haka? Don ubanki ina mijinna ki kika zo nan kika baje kina barci, ko kazar baki je kin kar’bo ba Muhammaurrasulillahi.
Shatu dai ranta a ‘bace take kallon Dada tace “Don Allah ki ‘kyaleni nayi barci na.” “Wallahi kuwa ba dai anan ba, ba zaki saka mu kwana mala’iku suna tsine mana ba, maza tashi muje shi kuma inji dalilinsa na ‘kin zuwa siyan baki,ko kuma kazar yaka mana ba’kin cikin muci?” Shatu ta mi’ke tana zira Hijabinta. Murya a cunkushe tace “Ni fa Ina da test kuma Mommah tace kada na sake na shiga d’akinsa.” Dada ta zuba mata dundu “Mommo nace ba Mommah ba ka ji min ja’irar yarinya, ita Mommahn zata ceceki a kabari ne idan ana jibgarki? Wuce muje.”
Dole ta bita suka fita babban parlourn da zai sada su da ‘bangarensa kamar yarda Anty Hafsa ta nuna mata.

Da hannu ta nunawa Dada ‘kofar murya na rawa tace “Ga ‘kofar nan sai ki buga ya baki kazar muje mu kwanta.” Dada kuwa ta hau bugu.
Cikin barci yaji bugun yayi yawa da kyar ya janye Shaheedah da take barci peacefully, ba tare da tunanin satar kwana su kayi ba. Ya fito yana kallon Agogo ‘karfe 2:45pm. Ya ware ido yana tunanin waye da tsohon daren nan?

Yana bud’ewa idanunsa ya sauka a kanta ita da Dada. Fuska a d’aure yace “Lafiya?”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-25


Dada ta masa kallon she’ke’ke kafin ta furta “Lafiya tana gidan ubanka Manga,tunda nan ban ga ana zaman lafiyar ba, ba ma wannan , mai kake nufi da ka barmu muke barci she’ke’ke kamar shi aka kawo mu muyi ko siyan baki baka zo ba,balle ka ja amarya ku tafi turakarka.” Fuska ya d’aure sosai yana kallon Shatu yace “Ba yanzu na shirya kar’bar aurenta ba duk san da na shirya zan zo siyan bakin yanzu dai ku tafi don Allah.” Dada salati ta saka tana fad’in “Ni jikar fad’imatu wallahi Dijah dai ba tayi sa’ar haifoka ba, wallahi shashasha ta haifa idan ban da dolo waye zai zubar da wannan indiyar dajin ya kama mai suffar turawa,mace a ‘kanjame to ai shikkenan ke wuce muje shi yasa mai za’a yi da auren cushe.” Fuska a d’aure Shatu tace “Ai sai da nace miki kar muzo kika ‘ki.” “Ki wuce nace muje ai wallahi yayi da ‘yar halak Moddibo uban Dijah ya wula’kanta bani ba da na haife kakansa shi kuma ya haifi uban Dijah, ita kuma ta haifo mana jaraba.” Bai yi magana ba ya mayar da ‘kofa ya rufe yana jin zuciyarsa na sake tsanar auren alamar aikin su Zainab ya fara ci.

Suna komawa d’aki,Shatu ta saka masifa tana jan pillow zata mayar da kai ta kwanta, Dada ta kwad’a mata duka “Tashi shashasha wannan mijin naki sai kin dage masa da addu’a da alama mutanen ‘boye sun shafeshi. Nima nan yau ba zan runtsa ba,yarda ya wula’kantamu d’in nan alfarmar manzo sai yazo yana binki.” Shatu mi’kewa tayi ta shiga toilet d’in don ta tuna a nasihun Mommah har da sallahr dare da tace ta ri’keta gam-gam itace makamin ‘kare dangi.



Da sassafe wayar Mommah ce ta tashe shi, lokacin bai fi 30mints da komawa barci ba,idon sa a rufe ya jawo wayar had’e da sata a kunnensa. Cikin muryar barci yace “Hello” Mommah tace “kana jina Shatu ta shirya ka kaita school kada tayi late.” Daga haka ta kashe Imran ya mi’ke zaune yana dafe kansa a ransa yace “Kai oh my God wannan Shatu wannan Shatu wallahi Mommah ko don haka dole na koma turkey gurin harkar company na dama can nafi wayo ba sai an ganni ba balle a d’ora min wata hidimar Shatu.”
Shaheedah ta mi’ke tana kallonsa, kafin ta yi tsaki ta furta “Wai lafiya naji kana ta magana kai kad’ai?” Mi’kewa yayi ya fice yana ce mata “Am coming.”


Yana murd’a ‘kofar bedroom d’in ya jita a bud’e, da sauri ya shiga ciki, idanunsa akan Shatu da take barci, santala-santalan cinyoyinta farare sol a waje, ya saka hannu ya d’aka mata duka a cinyarta. Da sauri Shatu ta mi’ke tana murtsika idanunta, ta ware idonta a kansa fuska a had’e tace “Lafiya?” Ya girgiza kai “Ni kike tambaya lafiya? Ki tashi ki wuce ki yi shirin school kafin in murtsike bakinki, kuma daga yau ki san yarda zaki dinga tashin kanki ki tafi school ba zan juri tashinki ba.” Daga haka yasa kai ya fice. Tilas Shatu ta mi’ke ta shige toilet, kafin tayi wankan sai da ta and wanke toilet d’in tas kamar yarda Mommah ta ja kunnenta. Ta kuma fito ta koma parlour ta gyara duk yarda yake son gyara. Duk da Mommah tace zata saka a samo mata mai aiki. Ta kunna burnerr turaren wuta gidan gaba d’aya ya d’auki ‘kamshi. A kitchen ake yinta don ba abinda ta iya dafawa sai indomie ita d’in ma ba wani ‘kwarewa tayi ba. Haka dai ta zauna ta cacca’ba musu indomien sai dai tayi ruwa jingim.

Da sauri ta fito taje tayi wankan,ta zura uniform d’inta, sannan ta tashi Dada ta sanar mata ta tafi school. Dada ta zaro ido “Makaranta kuma? Kai Allah wadaran naka ya lalace,jiya a kawo ki gidan miji yau ki tafi makaranta, sai kace makarantar ganin Annabi.” Shatu dai mi’kewa tayi da sauri ta fice, tana jin Dadan na ta mita ita kad’ai.
Turus tayi a kitchen bayan ta bud’e indomie d’in taga ta ca’be kamar me? Haka dole ta fice daga kitchen d’in kamar tayi kuka,saboda bala’in yunwar da taje ji.


A parlourn ta ta gan shi zaune yana danna waya,sai zabga ‘kamshin turarensa yake. Ta tsaya tana matsar ‘kwalla, jin idanu a kansa ya tabbatar ta shigo parlourn ba tare da ya kalleta ba yace “wuce muje.” Murya na rawa tace “Yunwa fa nake ji.” A harzu’ke ya d’ago yana kallonta,sai kuma yaja tsaki “ Maza ki mayar dani abinci ki ci.” Yayi tsaki ya fice don dole ta d’au school bag d’inta ta bi shi.


Suna fitowa Main parlour d’in suka tarar da Shaheedah Zaune,ta ci kwalliyar ta cikin lace fuskar nan ta sha makeup, colour d’in lace d’in ya amshi fatarta sosai. Tana ganin Shatu ta had’e rai har da jan tsaki, Shatu kuwa murmushi tayi a hankali tace “Ni da Aljana a cupboard.” Da sauri Shaheedah ta juyo tana kallonta sai kuma tayi tsaki “Ni ba zan kula ki ba,saboda takaici d’aya da na bar miki ya isheki, daren farko Miji ya kwana a d’akin kishiyarki alamar duk da kyannaki bai damu dake ba. Ta shige jikinsa murya can ‘kasa tace “Ko Habibi?” Shima d’in jan ta yayi jikinsa duk don su turawa Shatu haushi.
Shatu kuwa ko a jikinta sai ma dariya da tayi tace a fili “Na bar miki shi har abada in dai wannan ne kece ya ke gabanki, ni miji na yana nan zuwa.” Da sauri Imran ya juyo yana kallonta “Rashin kunya zaki yi mana? Ko mu sa’anninki ne?” Shatu turo baki tayi kafin tace “ita me yasa ba kayi mata magana ba sai ni?” Da sauri ya murd’e bakinta suka zama so close har tana jin hucin numfashinsa a fuskarta. Tayi saurin runtse Idonta “ Sa’arki ce ita?” Bud’e idanunta tayi a cikin nasa kafin tace “Ba sa’a ta bace Allah ya kiyaye ta zama sa’a ta, wannan tsohuwar.”Shaheedah a zafafe ta yun’kuro zata mare ta, Shatu ta kauce fuskarta “Wallahi kada ki fara fuska ta tafi gaban mari idan kuwa kika aikata wallahi zaki yi dana sani.” Daga haka ta fice ran ta a
‘bace. Ta fara tunanin Ina ma ta san hanya da wallahi ba zata bi motarsa ba.



Bayan ya gama lalla’ba Shaheedan ya fito ya sameta a bakin Motar, fuskarta a d’aure.
Bud’e Motar yayi ya shiga, sannan cikin masifa yace “Malama ko na tafi ne?” Ta shiga motar tana tunanin muguntar da zata shuka musu idan ta dawo.



Shaheedah na koma wa ciki ta shige d’aki, mahaifiyarta ta kira murya na rawa tace “Anty ko dai nayi usinga maganinnan?” Anty t zabga salati tace”baki da hankali ne zaki yi amfani dashi yanzu, ina zaki ‘buya idan ya nufeki da bu’katarsa? To kada ma ki fara wallahi sai nan da one month.” Shaheedah tace “Ni fa wallahi Anty na tsani yarinyar nan so nake kawai ta bar gidannan.” Anty taja tsaki “dad’ina dake rashin ha’kuri har yaushe tayi zaman da zaki ce kin gaji da ita, kada ma ki fara ‘bata min aiki na gaya miki.” Da kyar dai Shaheedah ta amince da shawarar Antyn ta.


Suna tafe a motar ya juyo yana kallonta, ita kuwa d’auke fuska tayi tana kallon waje. Imran ya girgiza kai kafin yace “Kin shirya kar’bar ha’k’kinki kenan shi yasa kika amince da tariyar? To ki shirya dama yau da daddare zaki san mai ma’anar kalmar aure take nufi, tunda sai da naja kunnenki akan hakan kin ga bani da laifi.” Ta’be bakinta tayi ba tare da ko kallonsa tayi ba. Parking d’in motar yayi dai-dai lokacin da suka zo makarantar ta su yasa luck ya kulle ‘kofar, ganin har lokacin bata kalleshi ba yasa cikin masifa ya juyo fuskarta,tayi saurin runtse idonta.Tsam yayi yana kallonta shi kansa ya amince Shatu kyakykyawa ce irin kyan da ake nufi zallar kyau, Gashin idonta kansa abin kallo, balle gashin gira da haka-yalan gashin da yake kwance gaban goshin ta. Dogon hancinta da idan tayi dariya yake pointing daga ‘kasa wajen tsinin hancin. Da ‘karamin bakin ta da yayi kyau da zagayayyiyar fuskarta da ta dace da dogon wuyanta. Bayan ya gama ‘kare mata kallon ya saki tsaki “Raini ne yasa ina miki magana kika yi min banza?” Shirun ta sake masa had’e da bud’e ido tana kallonsa. Ya girgiza kai “Anjima zamu goge raini fita min daga mota.” Murya a ciki tace masa “ina jin yunwa.” Tsaki yaja kafin ya zaro kud’i a aljihunsa ya d’ora mata a cinya “Sadaka na baki don bani nace ki fito da yunwa ba.” Ta d’auke kud’in had’e da saurin ficewa daga motar.


A makaranta kuwa bata da matsala kasancewar tana da sharp brain sosai,nan da nan take gane karatu don haka nan da nan ta kamo abokan karatunnata.


Dada da ta tashi rasa abincin da zata ci tayi, hakan yasa ta fita parlour, tana ‘kwalawa Imran kira don rashin sanin ‘kofar da zata shiga. Jin shirun yayi yawa yasa ta buga ‘kofar Shaheedah. A zafafe Shaheedah ta fito don tana jin ta sarai don a ‘karamin parlournta take. She’ke’ke ta tsaya tana kallon Dadan kafin cikin tsaki tace “Lafiya?” Dada ta girgiza kai kafin tace “Ba shakka Imrana ya auro dai-dai dashi, to wallahi kuwa ba dani za’ayi wannan iya shegen ba yau-yau zan bar gidannan ina dalili gida kamar gidan Aljannu a bar mutum da yunwa, don fitsara kuma ana tambayarsa lafiya.” Daidai lokacin Imran ya shigo. “Dada lafiya?” Ya fad’a yana kallon Dadan. Cikin masifa tace “Lafiyar kenan ita ta kawo haka, juya muje maza-maza muje ka mayar dani can inda na fi wayo zaman d’aki aka kawo ni ko zaman hora mutum da yunwa.” Imran yace “Baki cida abinci ba?” Dada ta juya “Ni daida muje ka kaini can wajen uwarku wallahi ba zanyi zaman d’akin ba dama ban da tsiya wata gemai-gemai dani za’a kawo zaman d’aki.” Imran ya bita a baya, shi hakan ma yafi masa, Dada Allah ya raka taki Gona.

Ko a mota mita Dadan take yi tana ‘karawa can kuma tace “Haka kawai a aura maka yarinya ace wani kada ka kusanceta sai ta girma, to wallahi ahir kada ka bi wannan layin halaliyarka ce
Ina dalili? Irin wad’annan yaran ai sun fi dad’in mu’amalar Aure.” Imran had’e fuska yayi kafin yace “Ni dai ban tambayeki ba.” yana ji ta cigaba da mita.

A ‘kofar gida ya sauketa ya ‘kara gaba don baya son ma had’uwa da Mommah.

Mommah da take sallamar su Hajja zasu wuce maiduguri ta bi Dada da kallo cikin mamakin ganinta.
Dada cikin fara’a take yiwa mutanen mai dugurin sallama, sai dai ba wanda ta samu kallon arziki daga wajensa.
Hajja ta sake kallon Mommah a karo na uku, tun bayan fitowarsu tace “Burinki ya cika kin had’a aure da Shatu da Imran, sai dai ki bud’e kunnenki da kyau kiji hakan ba yana nufin zan saka miki ido kiyi abinda kika ga dama ba, wallahi duk wani motsinki akan ido na yake, shima Mangan da kika gama dashi kwana kwanannan zan warware kaf sihirinki da yake kansa.” Mommah sunkuyar da kai tayi kafin cikin murmushi tace “Allah ya sauke ku lafiya, Hameeda Allah ya ‘kaddara saduwarmu.” Daga haka ta wuce tana kallon yarda Hameedan ta bita da kallon banza har da tsaki.

A bakin Gado ta tarar da Dada tana cin abinci hannu baka hannu ‘kwarya, tana yi tana bawa Hajiya Mama labari “Wallahi ni naga tsana da gaske Imrana yake baya son yarinyar nan don ko kazar amarci bai kai mana ba, kuma ya tsallake santaleliyar yarinyar nan zubin larabawa ya tafi wajen waccen ‘kashi da ran, ba ma fa wannan bane abin haushi ita kuma ‘yar taku Shatu bata iya girki ba a hakan zata ‘kwace miji, Wallahi Dija dai tayi asara, to gwara ma tazo ta san yarda tayi ta koya mata girki, don baki ga abincin da tayi yau ba wallahi ina tabbatar miki da naci sai nayi amai, yaushe kuwa Imran zai ci and wannan kwamacalar.”
Mommah zama tayi tana murmushi tace “Wai Dada ya naga kin taho?” Dada ta sake kai loma bakinta kafin tace “Ba dole in taho ba gidan Imran ba abinci, kuma wallahi ba zan koma ba, ‘kafa ta ‘kafar uwarki Habuja zan koma.”Hafsa ta mi’ke daga kwancen da

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment