Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daddage ta saki wata tusa da ta d’umame motar gaba d’aya Allah ne ya kiyaye saura’kiris ya saki sitiyarin motar yaja wani wawan burki, ammar ya dinga’kok’arin’kinshe dariyar da ke cikinsa amma ina sai da ta bayyana a guje ya fice tuni ya fara kwara amai, Ammar ya fito masa da ruwa yana aikin jera masa sannu. Momma kuwa duk da tausayinsa ya shigeta haka ta gintse. Shatu sai dariya take yi tana’karawa momma tace “ wallahi shatu idan ya kamaki ba ruwana “ “ yo mommah ba k’yamata yake ba saura gudawa ma “ Mommah ta waro ido “ kada ki fara shatu idan ba so kike ya kashemu a titi ba kina ganin wawan burkin da ya sha Ba don Allah ya kiyaye Ba kowa a bayanmu ba da tuni mun mutu.” Shatu ta zaro ido “ momma mutuwa kuma a yanzun da zan fara jin dad’in rayuwa aradu ma ki daina wagga zance yo tunda nake ban ta’ba tunanin zan shiga wannan abin ba ban Ta’ ba ganinsa ba sai yau amalanke muke shiga garinmu da zanzo nan kuwa motar kayan miya Na shigo aradu dana shiga nan na zata aljannah nake “ mommah ta girgiza kai “To kada ki sake abinda zai zubar damu a titi motoci su take mu mutu.” Ta d’aga kai. Ya huta sosai kafin yace “ Ammar jeka Kai bud’e glasses d’in motar ventilation ya shiga ka fesa air freshners tabbas Ba mamaki mommah ta d’auko ajalina “ Ammar ya d’an shafa bayansa “ bros ba zaka mutu ba just because of her sai kwananka ya ‘kare Ka dinga daurewa pls mommah bata jin dad’i the way she looked at you ka dinga controlling temper Dinka” hannu ya d’aga masa “ jeka kayi abinda nace maka kawai ni Na san abinda zanyi muna zuwa gida I will pack everything nawa na tare “ Ammar ya zaro ido “ saura fa 4 months bikin ya zaka tare yanzu “ Imran tsaki yayi idan ban tare ba so kake na mutu ko?” Ammar ya juya yana’kunshe dariyarsa ya gama duk abinda ya sashi sannan ya dawo yana kallon yarda yake mayar da numfashi alamar ya galabaita a aman “ Bros mu tafi kada dare yayi “ mikewa kawai yayi ya mi’ka masa key d’in “ muje kayi driving I can’t do it “

Ta mudubin motar yake watsa mata harara ta saki baki sai barci take har da munshari ya sauke duk glasses d’in iska Na shiga motar a zuciyarsa yace “ Gwara a tafi haka “ momma dake kallonsa ta ta’be baki “ zan baka mamaki imran kada Ka shiga hankalinka “.






Idan ba’a commnts zan dakatar da book d’innan.....
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387


-6

ELEGANT ONLINE WRITERS ******




Ammar cikin nutsuwa yake driving har suka isa cikin garin kano’karfe 8:00 dai-dai, shatu lokacin har fitsari ta janga’ba a kujerar ba tare da sanin mommah ba.

A unguwar railway su kayi parking bakin wani tangamemen gida gari guda, da tafkeken gate, gani tayi kawai gate din ya zuge ba tare da tasan wanda ya zugeshi ba.Automatic gate ne. Ammar yayi packing a packing space. Momma ta bud’e ‘kofar had’e da jan hannun shatu a hankali ta waro ido ganin gurin da lema murya ‘kasa-k’asa tace “ shatu fitsari kika yi?” Shatu ta d’an ta’be baki “ To mommah fitsarin ne ai ya matseni kuma ina cewa zanyi zai fara masifa “. Momma tayi saurin rufe mata baki don kada imran da ya fice da sauri yaji “Muje kafin ya ankare “ da sauri shatu ta fita daga motar ammar yayi dariya yana tunanin yarda za’ayi da cakwakiyar’yar mommah da yayansa, yasan dai kwarai za’a buga show.



Suna shiga tangamemen falon kamshi ya doki hancin shatu ga sanyin A.c ta lumshe ido had’e da runtse ido tana bud’ewa tabbas dai da a mafarki taga wannan gidan to tabbas zata ce aljanna tayi mafarki da ita. Momma ta ri’ke mata hannunta ta kaita’kofar wani sashe suna shiga ta kaita wani d’aki kusa da nata “ daga yau ga d’akin Ayshata muje in nuna miki komai a toilet kiyi wanka ko da yake wannan wankan na yau yafi ‘karfinki da kaina zan miki da nace ma in kaiki saloon to bana so su fara ganin wannan daud’ar kannaki jira ni anan am coming.” Da sauri ta fita daga d’akin shatu ta sake ware ido tana kallon gadon yanzu wannan d’akina ne gado na da sauri tayi tsalle a gadon tana tintsira dariya “ ahe dai ina da gata muke zaune can a dajin Allah aradu innaji ta kwari kanta cabd’i”

Shigowar mommah yasa tayi shiru momma ta shige toilet ta zube kayan da yake hannunta duk mayukan wanke kaine da combs dama toilet din akwai dryer. Shatu ta fara’bata rai sam bata son a ta’ba mata kai da dai mommah zata gane da ta kyaleta. Momma ta zare du’kun’kunennan mayafin nata ta zaunar da ita bakin jaucuzi ta fara kunce tufkekken gashin kanta mommah tayi mamakin ganin tumulin gashin ta ji’kashi ta saka shampoo ta barshi for a minutes sannan ta fara had’a ruwan da zata dirje daud’ar Jikinta.
Sosai ta wanke kan sai sheki yake wajen wanka ne shatu Ta fara’boye-‘boyen jiki mommah Ta harareta “ zaki tsaya ko sai na ‘bata miki rai ke da ko irgar dangi baki fara ba to koma kin fara ni ba uwarki bace “. Shatu Ta d’an sunkiyar da kai mommah Ta saki murmushi “ Ashe kina da kunya.” Tas shatu Ta fito duk da dai sai a hankali zata baje amma ko bakomai anfi baya.


Fitowarta ne yasa momma ta tsaya domin ba kayan da zata bata tasa tsaki tayi tace “zauna nan ina zuwa bari na aika ammar ya siyo miki ready made kafin da safe mu shiga kasuwa “.


Tana fitowa babban falo ba taga ammar ba sai imran da yake zaune yayi wanka da fara jallabiya tas a jikinta mai gajeran hannu a jikinsa yayi kyau sosai kana ganinsa kaga mutum mai mutu’kar tsafta. Sai baza’kamshin turare yake yunwa ce take cinsa ya aika ammar yayi musu take away don baiga alamar masu aikin sunyi girki ba, may be basu zata zasu dawo ba.” ina Ammar?” Momma Ta fad’a tana tsatstsare sa da ido , Imran murya can’kasa yace “ Na aike shi eatery samo abinci.” “ sai ka tashi kai na aikeka samowa Aysha kayan sawa ba tazo da kaya ba “ ta fad’a tana juyawa ba tare da Ta lura da waro idon da yayi ba yana ji kamar ya rusa ihu ganin zata shige yace “ kud’in fa?” Ba tare da Ta juyo ba tace “ ka siya da naka “ dunkule hannu yayi ya daki d’aya cikin d’aya kamar ya tashi sama kuma ya juya da sauri ya fice daga cikin gida.



Da yaje ma rasa mai zai d’auka yayi ya d’auko mata riga da wando Na maza kawai bayan ya kintata tsahonta yaga ba zata zarta hakan ba. yunwa yake ji sosai amma mommah Ta sashi zuwa siyawa wannan bararojin kaya.


A falo ya ajiye kayan ya nunawa Ammar “ mikawa mommah “ ya zauna a dinning ya fara cin abincin” mintuna kad’an mommah da ‘yarta suka fito Ta saka riga da wando duk da Na maza ne sai sukayi mata kyau, mommah Ta gyara mata kai an tsaga an raba biyu, jelar gashin Ta sauka har dantsen hannunta gashi mai yawa masha Allah sai ‘kamshi take kallo d’aya yayi mata ya d’auke kai ya cigaba da cin abincinsa momma taja kujera tace “zauna “ Ta zauna tana hararar naman da yake ci tsoronta Allah kada ya cinye naman hakan yasa ta shiga tunanin yarda zata koreshi daga wajen ta kuwa daddage ta saki attishawa sai kuwa ga majina ta biyo hancinta da sauri ya furzo abincin dake bakinsa ya mi’ke da sauri ya bar wajen. Zuciyarsa na tunzirashi yayi mata dan banzan duka kawai. Ita kuwa dariya Ta fara babbakawa “ Nagode Allah yo mommah da fa cinye naman zaiyi kaf da banyi haka ba “ mommah duk da dariyar da take cinta ta gintse tace “ baki kyauta ba kings yanzu kin hanashi cin abincin Ba kyau kada ki sake Ammar bishi da abincin d’aki”. Ammar ya mi’ke yana murmushi sosai yarinyar take burgeshi shi kam sam bata damuwa sha’aninta take zubawa.


A parlornsu ya ganshi a zaune ya dafe kansa sosai tausayinsa ya kamashi ya ‘karasa da abincin yana dafa bayansa Bros sorry don Allah ga abincin momma tace a kawo maka “ zubawa plate din ido yayi yana saurin ja baya gani yake zai hango majinar a cikin abincin murya can ‘kasa yace “ ‘dauki Ka tafi dashi ba zan ci ba ta had’a Ta cinye kana tunanin yau zan iya cin wani abin ko mai na kai bakina sai na tuna ‘kazamar yarinyar nan bitch “ ya mi’ke ya shige bed room direct toilet ya shige ya sakarwa kansa shower.so yake yaji zuciyarsa Ta daina’kuna.


Yana dawo da abincin mommah Ta kalleshi “ baya ci ne?” Ammar a sanyaye ya d’aga kai yaja kunnen shatu dake zaune “ if you try it again Allah sai Na zaneki mommah kija mata kunne “. Narai narai tayi da idonta “ To ni ina ruwa na kawai atishawace fa tazo ya zanyi da ita to “ “ Excusing kanki za kiyi ki fita kiyi haka ake yi wai ke baki da manner ne?” Kuka Ta saka “ Ni ka daina min wannan maganar ban iyata ba idan bakwa san zama na kuma kawai kuce na tafi. Ya bud’e baki zai yi magana mommah tace “ Ammar ya isa ai da gaskiyarta to ya zatayi da atishawa fisabilillahi ni fa kada wanda ya ‘kara takura mata duk wanda Ba zai iya zama ba shi ya bar gidan. Ammar ya bud’e ido “Mommah......” “kada kace komai “ ita kuwa shatu plates d’in imran taja ta fara cin naman cewa takeyi “ Yo ai yayiwa kansa ni kuwa gaba Ta kaini......” Ammar murmushi yayi ya wuce yana furta “ Allah ya shirya “.
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-7


ELEGANT ONLINE WRITERS..........


Momma murmushi Ta sake saki ganin yarda shatu take cin abincin hannu baka hannu kwarya “ ci a hankali Aysha ba inda abincin nan zaije gashi nan ma idan baki ‘koshi ba ki ‘kara saki jikinki nan d’in gidanku ne kamar yarda kowa yake ji gidan ubansa ne.” Ammar’kunshe dariyarsa yayi ganin yarda momma ta hau da yawa yasa ya koma falon ya kunna t.v . Ai kuwa shatu a zabure ta mi’ke ta isa wajen tana sid’e hannunta “ Ikon Allah yau gani ga irin akwatin kallon d’an gidan mai gari da aka kaiwa amaryrsa da ya auro a niamey, aradu wannan tayi gomanta.” Sai kuma ta fara zabura tana tsalle ganin yarda mutane ke rawa a cikin t.v d’in ta ‘karasa tana shafawa Ammar mai zaiyi idan ba dariya ba. Momma da take gefe ta dafe kai anya shatu zata gyaru ta dawo kan saiti kamar yarda take son ta ta lura’kauyancine kawai a kanta zuciyar momma ta shiga tunani. Sai kuma ta mi’ke ganin yarda ammar yake tuntsira dariya tana zuwa ta figi hannunta “ wuce muje shashasha kina zaune yana ta tuntsira miki dariya ga sabon kamu ya samu wallahi Ammar ka kiyayeni ina lura da take-takenka ta wancan ce ta fito fili shi kyamarta take kai kuwa mahaukaciya ka d’auketa to ahir ka kiyayeni “Ammar ya guntse bakinsa “ Allah ya baki ha’kuri momma amma fa wallahi dole Na samu comedy a gidan ji fa yarda take acting wallahi illiteracy d’inta yayi yawa za’a sha fama “ “ ubanka ne zai sha famar ko ni? Ina ruwanku da ita to duk zaku ci ubanku da ni kuke zancen ashe ta imran ce ta fito fili “ Ta sake kwafa suka shige part d’inta hannunta ri’ke dana shatu.


Suna shiga d’aki shatu ciki ya kad’a to an ci abinda ciki bai saba ci ba da sauri Ta kalli mommah tana yamutsa fuska. Momma Ta dubeta had’e da dafa kanta “ Me ya faru ki daina fushi ki rabu da su zan yi maganinsu ai da ni suke zancen” Shatu Ta fara matse-matse “ Ni fa mommah ba zancensu ya dameni ba yo ni ina ruwa na ai gaskiya Ammar ya fad’a. “ “ Au ni na damu kenan to meye ya dameki kike had’e-had’en fuska” “ Kahi nake ji “ Momma Ta zaro ido to “ kashin kike ji kike tsaye anan, anan zakiyi min kashin?” Da sauri taja hannunta wuce muje na nuna miki inda zakiyi don ba mamaki ma baki san toilet sit d’in birni ba” da sauri shatu ta bita ji take kamar Ta saki kashin suna shiga ta hau duba inda momma ta nuna mata shatu ta waro ido “ A wannan abin fari ‘kal dahi zanyi kahin “. Momma tsaki tayi kafin ta furta “ idan ba kiyi anan ba a bakina zaki yi ?“. Ta sake le’kawa “ Ruwa ne fa a ciki aradu ba zan zauna ba inje ruwa ya zu’keni ya tafi dani “ Momma Ta dafe kai tana kallon shatun cikin takaici “ kada fa ki sake kiyi min kashi a wando ki hau ba wani ruwa da zai tafi dake duk gidan da zaki a garinnan yawancin irin wannan d’inne sai dai idan kin daina kashin” “ To zan hau amma ki tsaya ni” “ In tsaya ki ki cika min ciki da warin kashi to ba dani ba ki hau in kin gama wannan zaki ciro kina danna nan ruwa zai zo kiyi tsarki shi kuma kashin ba barinsa zakiyi ba ki danna nan ruwa zai tafi dashi kin jini ai da kyau?” Shatu Ta d’aga tana d’ofana akan seat toilet din ta zauna. Momma ta saki ajiyar zuciya Ta ja mata ‘kofa ta fita zuwa nata d’akin a gaijye take tubus banda soyayyarta da maryama ba abinda zai kaita d’aukar shatu musamman ita da mijinta da suka tsarawa kansu rayuwar turai basa son hayaniya sam shi yasa sam basu damu da haihuwa ba sai gashi ta d’auko shatu wanda Ta san sai tayi bore kafin mijinta ya amince da zaman shatu a gidan. D’akinta ta shiga wanka kawai take bu’kata da nutsuwa.


Shatu anyi abin kai bayan ta gama tayi tsarkin ta mi’ke sannan ta danna inda akace zata kore kashin idan ta gama ai ko sai tayi tsalle ta koma can gefe tana kallon ruwan abin kuma sai ya bata dariya ta sake dannawa haka tayi- tayi kafin ta gaji ta fito a zuciyarta take fad’in “ wato hi kahin ma wani matsayi ne dashi na musamman a Gidannan cabd’i Allah ya kyauta “. Ganin momma bata d’akin Yasa ta fita tana bilayin nemanta . Ganin bata ganta ba a d’imauce Ta fara’kwala mata kira duk gidan yana amsa kuwwar muryarta.

Da sauri d’aukacin mutanen gidan har su Imran suka fito tunanin ko ba lafiya ba, abinka da ba’a saba hayaniya a gidan ba, dai- dai lokacin mai gidan shima ya bud’e ‘kofar part d’insa ya fito don bai dad’e da dawowa ba yaji tashin muryarta. Da kallo ya bisu ganin sunyi cirko-cirko suna kallonta. Had’e fuska tayi tana binsu Da kallo “ To wai lafiya naga kun saka ni tsakiya sai wani kallo na kuke.” Imran tsaki yayi ya juya ya shige part d’insu da ya san ma itace ba zai fito ba to barcin gajiya ya fara fisgarsa ya jiyo hayaniyarta kai mommah ta d’ebo musu damuwa.Ammar da ya lura da Dahdansu yayi saurin cewa “ welcome dahdah “ girgiza masa kai yayi fuska a had’e yace “ who is she?” Ammar ya mayar da kallonsa kan shatu da take fad’in “ Wannan sa ido da yawa yake uwa ta fa na kira baku ba” Ammar yayi saurin katseta “ ke are you mad kin san da wa kike magana “ “ kai ka san mai kace inace mad d’in d’an garinku sai kayi tayi min yaren birni so nawa zance maka bana so “ Ta fad’a tana ta’be baki . Cikin tsawa Babannasa yace “Ammar am asking you who is she I said?” Mommah ce Ta fito daga’bangarenta turus tayi ganin taron jama’ar gidan Ta mayar da idonta kan dahda “ Ai ban san ka shigo ba ina wanka.” Fuska a had’e yace “ Yayi kyau kai kuma amsa min tambayata wace shashashace wannan?” Mommah ta had’e fuska “ diyar tawa ce shashasha to ko baka santa ba ai bai kamata daga ganin ba’ko ka kira shi da shashasha ba er maryam ce sister ta wani abu ne?” Wani kallo ya bita dashi sai kuma ya hau step d’in da zai kaishi ‘bangarensa.” Almasifatu shi kuma wannan d’in waye da naga duk kun firgita da ganinsa “. Momma ta waro ido Allah ya taimaka ya shige bai ji ta ba Ammar ya watsa mata wani kallo “ ke ubannamu kike kira Almasifatu?” Cikin ‘ki’k’kifta ido tace “ Aradu ban san ubanka bane yo ai da ba zan kira shi da haka ba.” “ zagi na kika yi kenan ?” Cikin kufula Ammar ya fad’a. Momma Ta dafe kanta had’e da jan hannunsa “ Bafa zagin ka tayi ba Ammar sai kunyi ha’kuri da ita kafin ta goge” Ammar ya kad’a kai “ki daina bin bayanta fa mommah cewa fa tayi ubannaka?” “ To kayi hakuri mana haba su a garinsu ai ba zagi bane hakan “. Shigewa part d’insu kawai yayi yana nanata kalmar AlMASIFATU. Momma ranta had’e tace “ Maza wuce d’akinki kada Na sake ganin’kafarki a waje sai da safe nan gidan bama hayaniya mai gidan duka yake “ sum sum ta wuce . Momma Ta dubi masu aikinta biyu da suke kwana su kansu a ‘boye suke saboda mai gidan ya sha fad’a mata baya san shirgi, ‘ya’yansa kad’ai sun isheshi “ ku kuma mai kuke yi anan? Yawon d’aukar news ko?” Da sauri suka fice ita kuma Ta shige ciki sam bata san yau zai dawo ba ba abinda Ta tanadar masa. Kitchen d’in da yake part d’insa Ta shiga saboda tsantsaninsa komansa anan yake ita take masa komai bai yarda kowa yayi masa ba. don haka ma yayi kitchen a part d’insa saboda kar ma wata rana tayi gigin saka masu aiki yi masa wani abin. To ashe dai imran a can ya gado tsafta.

Sai da ta d’ora abincin sannan ta’karasa bed room d’insa . A zaune ta ganshi da news paper a hannunsa sallamar ma ciki-ciki ya amsa ba tare da ya d’ago ba “ Yalla’bai barka da dawowa ina ta magana kayi shiru wai me ya faru ne?” Ya d’ago fuska a cusgune “ Da izinin wa kika d’auko bagidajiyat yarinyar can to bari kiji in gaya miki I can’t tolerate this nonsense maza-maza gobe ki mayar da ita inda kika d’aukota ai kin san sarai bana son hayaniya yaran ‘yan uwana ma ban yarda na ri’ke ba balle wannan yaran da bata da respect don haka ki mayar da ita, saboda bana son haihuwa da yawa Na ‘ki ‘kara aure so ba wani abu da zai sani ri’keta...........”
[8/21, 11:27 PM] Aysha📚: *🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-8

ELEGANT ONLINE WRITERS.........


Momma tagumi ta zuba tana kallon dahda “ Amma ka bari kaji er waye kafin ka fara fad’ar ba zaka ri’keta ba, er fa maryama ce maryama jinina da muka taso tare maryaman da na sha mama na bar mata, duk ba ma wannan ba bata raye wa kake so ya rike mata er ta wa take dashi idan bani ba.” Jikin dahda ne yayi sanyi “ maryama ta mutu?” Ya fad’a cikin taushin murya ba kamar yarda ya d’au zafi ba, innalillahi wa inna ilaihirrajiuna, momma ta ja ajiyar zuciya kafin tace “ maryama ta mutu nima d’azu kira ya ruskeni daga katagum muka tafi a can muka samu ita wannan er tazo ita kuma take sanar damu mahaifiyrta ta mutu.” Allah ya gafarta mata Allah yasa ta huta amma ina mahaifinta?” Momma gyara zama cikin kasa da murya tace” shima Allah yayi masa rasuwa “ Tausayin shatu sosai ya kama Alhaji, ya
Hau girgiza kai yana jaddada lamarin girman ubangiji “ Allah ya gafarta musu Allah kuma ya bamu ikon sauke nauyin ri’kon maraya “. Farin ciki ya ratsa zuciyar mommah sai sannan hankalinta ya kwanta da har ya amsa zai ri’keta “ Nagode dear bari na kawo maka abincin” .

Ta fara zuba masa abincin ya dubeta “ kiyi ‘ko’kari sosai akan yarinyar nan ki koya mata tsafta uwa uba tarbiyya don sosai na lura bata da manner, insha Allah nima I will try my best naga na kula da lamarinta don kamar nauyinta ne Allah ya d’ora mana.” Insha Allah mommah kawai take fad’a zuciyarta cike da farin ciki a take a wajen ya tura mata kud’i a account ya umarceta da kashegari aje ayiwa shatu siyayya. Godiya ta sake masa ta mi’ke don fita shirin barci.




******** kwananta biyar da zuwa gidan amma har ta fara murjewa, jikinta yayi kyau masha Allah duk da haskenta bai fito gaba d’aya ba . Duk wani abin da bata sani ba mommah ta koyar da ita yarda za tayi amfani dashi a gidan.Ta fara kuma ‘ko’karin ganin ta daina rashin kunya duk da har zuwa lokacin da yarinta a tattare da ita.

Abubuwa da dama bata iya cinsu har a lokacin da zarar taci sai tayi aman su saboda rashin sabo sai dai son cin nama shan madara da milo kuwa har dana maza da kauri sosai take damawa ta shanye.Ammar tuni ya fara sakin jikinsa da ita kasancewar yanzu duk ta d’an zubar da rashin kunyar an samo mata malami da zai dinga koyar da ita.Imran ne baya shiga shirginta .


Yauma da wuri ta tashi, tayi saurin yin wanka da brush don kar mommah tayi mata fad’a gashi ne dai bata taje shi ba bata son gyaransa sam bata’ki kuma mommahn Ta aske shi ba kamar yarda tace.


Ganin su mommah tayi suna ta aiki a gidan ta fara tunanin ko mai zai faru ake ta wannan aikin Ta kuma lura zuciyar momma sam ba dad’i don komai a sanyaye take yinsa. Momma ta dubeta tana amsa gaisuwar da take mata cikin nutsuwa” yauwa my baby kin yi wanka maza kije kiyi break fast kizo d’aki ina son ganinki “. Amsawa tayi da sauri tana isa kan dinning , Tayi turus ganin imran a dinning d’in yana break idanunsa ya zuba mata, da sauri ta dur’kusa tana gaisheshi imran ya had’e fuska. “ ke bar nan wajen before I slap you “ kallon ‘kasa-‘kasa tayi masa “ To ba yunwa nake ji ba zaka ce na bar nan.” Harara ya watsa mata sai kuma ya cigaba da abinda yake kafin bakinsa ya furta “ Dirty Girl “ zama tayi ba tare da san abinda yace “ kin san mai nace miki?”kamar doluwa ta hau girgiza kai “ ‘kazama nace miki Alhamdulillah na kusa barin gidan sai kuci’kazantarku ku kad’ai “. Ba tayi masa magana illa kallon plate d’insa da tayi yana shirin kai tsokar nama ta miyar turmeric baki ta saki murmushi kafin tace “ Ga kanan’kazami kana cin miya kamar gudawa.....” Ai da sauri ya furzar da naman bakinsa yayi wajen sink shatu ta tuntsire da dariya a hankali ta furta “ ba’kin mugu in dai ina gidannan ka daina ci ka ‘koshi “ sosai ya kuskure bakinsa ya bita da wani kallo kafin ya wuce shatu ta ja plate taci abinci tayi nak “ Allah gaba ta kaini ba gashima har nayi’kiba ba gobe ma ka sake ce min’kazama Allah mhmmn sai kuma ta girgiza kai.”



Da kyar take nishi sai kuma ta tuna kiran da momma take mata da sauri ta shige sashen mommah a zaune ta ganta ta rakfa tagumi idonta har ja yayi. Jikinta

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment