Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

san Shatu ta haihuba, kuma ba ni nayi blocking ‘din numbers ‘dinku ba hasalima nima ina yawan kira bana samunku.” Mommah tace “Ai na gama magana, su da kan su sun san nayi ha’kuri da abubuwan da ka dinga yi min, wanda har hawan jini suka saka ni, na san kuma iyayena masu adalci ne wannan abinda kayi ba zai sa su su sani janye furucina ba, ko bayan raina Shatu Ammar na yarda ta aura. Don haka ga sadakinsa.” Ta bu’de jaka ta ciro dubu maitan ta ajiye gaban Alhaji Baba. Cikin tu’ku’kin zuciya Imran ya mi’ke ko ganin gabansa baya yi. Ita kanta Shatu ‘ko’kari take sosai wajen danne damuwarta da tuni ta saka kuka gani take kamar abin yayi masa yawa. Kuma ta amince da gaske Imran bai san da haihuwar nan ba. Jikinta a salu’be ita ma ta mi’ke ta shige bedroom, Mommah ta bita da kallon mamaki.

Alhaji Baba ya saki ajiyar zuciya shi kansa yana cikin wani hali da bai san yarda zai warware cukurku’dewar al’amurannan ba, ya zubawa sadakin da Mommah ta ajiye idanu, a fili ya furta “Tir’kashi! Amma Dijah da zaki fahaimceni da kin bari anyi abubuwannan a hankali.” Da sauri ya kalleta ganin ta saka masa kuka “Don Allah kada ku goyi bayansa, alhali yayi abinda bai kamata a goyi bayannasa ba, sai yanzu da yaga matarsa ta kwara’be ita kuma wannan ya ga ta goge sannan zai lalla’bo yace yana sonta, ni na tabbatar son sha’awa yake mata Ammar ne yake mata zahirin so, please ko bayan raina Ammar na amince ta aura.” Daga Alhaji Baban har Hajiya Maman shiru suka yi sun ma rasa tudun dafawa.


Shatu kuwa tana shiga ‘daki ta sulale akan gado, tausayin Imran ne gaba ‘daya ya cika zuciyarta duk da ba tana nufin ta komawa aurensa bane, amma bata son Mommah ta cigaba da zafafa masa. Turowar ‘kofar da aka yi ne da ‘karfi ya sata ‘dagowa. Anty Nahna ta gani sam fuskarta ba rahma, ta ‘karaso a ‘dakin a zafafe tace “Mi’ke zaune Shatu.” A sanyaye ta mi’ke tana goge 'kwallar da ta kwanta mata cikin idonta.
“Kada kice min kukan rasa Imran kike? Ko kuma kukan mutuncinki da Mommah ta kare? Cab da kuwa kin bani kunya na zata da ke za’a zage a ‘kwaci martabarki da mutuncinki, shine kika zauna kina kuka? Ba dai zuciyarki har yanzu tana son mutumin da ya gallaza miki a rayuwa ba? Da nace kuwa zuciyarki ba tayi miki halacci ba da kuma na kira ki da wacce ta rako mata duniya. Ki bu’de kunnenki ki ji abinda zan gaya miki da kyau, a yanzu ne zaki nuna wa Imran kuskurensa, a yanzu ne zaki ‘dandana masa guba irin wacce ya cusa miki, ki shayar dashi mamaki ki nuna masa kema mace ce Hamsha’kiya yanzu da ko ya sameki zai san mutuncinki da darajarki ba zai ce ya sameki a ‘bagas ba. ki nuna masa kin cika kin ri’ka kin tumbasa samun ki sai wanda ya shiryi. A zahirance ki nuna masa Ammar ne za’binki ko da a ba’dinance ba hakan bane. Kiyi gogayya da shi ki jashi a ‘kasa kada kuma ki sake ki bujirewa umarnin Mommah duk da ‘ko’karin kare martabarki da tayi, kiyi watsi da Imran ki kama Ammar shine ya dace dake. Kin ji mai na gaya Miki?” Shatu Ta ‘daga kai tana jin duk abinda Anty Nahna ta gaya mata shine gaskiya dole ta yakice soyayyar Imran ta yi wulli da ita matu’kar tana son siyawa kanta mutunci. Ta rungume Antyn ta Nahna tana sakin hawaye Na zallar samun nutsuwa.



Ammar kuwa tun da ya shige ‘daki ya kulle kansa ya da’de zaune dafe da kansa, yana jin zuciyarsa na suya, ina ma zai iya da ya sahalewa Imran matarsa, amma ina zuciyarsa ta kasa yi masa lamini soyayyar Shatu sake gauraye duk ilahirin sassan jikin sa take, baya jin zai iya rayuwa idan ba Shatu a tare dashi.




————
Lamarin Imran kuwa babu da’din ji, domin ya rasa mafita ya kuma rasa waye ya turo wannan sa’kon, zuciyarsa sunan Shaheedah ta ke Ta nana ta masa, hakan yasa a zafafe ya mi’ke. Dole ne ya nemo Shaheedah duk da sun koma barci amma asubanci zaiyi yaje ya tambayeta dalilin da yasa ta aikata haka.
Jirin da yaji yana ‘dibansa ne yasa ya tuna rabonsa da abinci tun tea ‘din da ya sha da safe, don haka ya mi’ke a hankali cike da ‘karfin hali ya nufi hanyar fita daga bedroom ‘din.


A kitchen ‘din take a tsaye tana ‘ko’karin dafawa Akram noodles da ya dameta da kuka. Jikinta sanye da Hijabin da tayi sallah da shi, fuskarta fayau ko powder babu, hakan ya saka idanunta fita dar dasu, dama ita tafi kyau ba makeup.

Jin ‘kamshin turarensa ya tabbatar mata shine ya shigo kitchen ‘din, don haka ta aro fuskar jarumta ta saka akan fuskarta, domin kuwa kicin-kicin tayi da fuska, tana zubawa Akram da ya isa wajensa harara tare da jawo shi da ‘karfi “Don gidanku matsa daga jikinsa saninka ma yayi da kake ‘ko’karin li’ke masa shashashan yaro kawai.” Kuka Akram ya fara yi yana ‘ko’karin ‘kwace hannunsa daga jikinta. Shi kuwa Imran sak yayi yana kallonta, yana son yi mata masifa amma yana shakkar kada ya sake cusa tsanarsa a zuciyarta. “Kiyi ha’kuri sabida ya zo wajena kika masa wannan fa’dan?” Wani tsaki taja kafin ta harareshi tace “Anyi masa ‘din ko kai ka haifa min shi?” Jikinta ya matsa sosai tamkar za su ha’de yana jifanta da wani irin kallo mai narka zuciya, cikin wata iriyar murya da tasa gaba ‘daya tsigar jikinta tashi yace “Idan ba ni na haifa miki shi ba amma ni na yi miki cikinsa, kuma cikin son ran ki da shau’ki.” Ta ja baya ha’de da ‘bata rai tace “Sai me don kai ka yi min cikinsa? Ai abu ne mai sau’ki kuma ko yanzu na yi aure wani ma zai min ciki na haihu.” Bai san lokacin da ya dam’ko ta ba cikin ‘bacin rai yana kallon cikin ‘kwayar idon ta da tayi saurin rintsesu saboda bata son idaninsa su yi mata tasirin da za ta kasa yi masa rashin kunya. “Ka cika ni.” Ta fa’da tana kicinyar ‘kwacewa saboda gaba ‘daya yayi kusa da ita tamkar ma rungumeta yayi “An ‘ki a cika kin sai kin sake fa’dar abinda kika ce yanzu, say it again.” Shiru tayi masa, hakan yasa ya samu wannan damar ya cugaba da magana cikin husky voice ‘dinsa. “Ba zaki Ta’ba auren wanda ya jiyar dake da’din da Na jiyar dake ba a first night ‘din mu, kada ki mance zafafan kiss da kika dinga aika min kamar dama ma jira kike Na zo, twins ka’dai sun isa ki shaida cewa ni ‘din gwarzon namiji ne, don haka ki taimaki kan ki kije ki sanar da Mommah ‘dakin mijinki zaki Koma, ni kuma in cigaba da jiyar dake da’di fiye da na wancan daren da ya gabata, Ayshatu na wallahi ina son ki, son da ni kaina bana yiwa kaina shi.” Tsaki ta ja duk da yanayin da ta tsinci kanta bai hanata yin furuci a zafafe ba “Kana so na? Yanzu da Na tashi daga fulanin daji Na tashi daga ‘kazama mai wari, wacce kake ‘kyama har kake gudun a kai ta gidanku, yaushe ka fara so na yanzu da Na zama educated da zaka iya shiga taro dani ba kuma zaka ji kunyar nunawa kowa ni ba a matsayin matarka, yaushe ka fara so na? Yaushe ka daina tunanin me zaka yi da ni? Lokacin da ka ‘dan’dani zumata ka gauraya da ni’imar da Allah yayi min shine kake ba’kin cikin Ammar shima ya ‘dan’dana ya ji ni’imata, ya samu tarin nutsuwa da baiwowin da Allah yayi min...” Da sauri ya sa tafin hannunsa ya rufe bakinta ruf cikin tsananin kishi yake furta “Ki fa’da min komai zaki fa’da amma please kada ki sake danganta kan ki da wani please Ayshatu forgive and Forget wallahi ina matu’kar son ki sai yanzu na fahimci dalilina na takura miki.” Hawaye ne kawai yake sauka daga idanunta, dalilin tuno wa’dannan abubuwan ashe Allah zai amshi addu’oin da take yi akan Imran? Dama bata haufi Ta san ubangiji mujibuddu’ai ne, amma yanzu lokaci ya ‘kure Mommah ta riga ta gindaya katanga mai ‘karfi tsakaninsu. Hannayensa masu tsananin taushi kawai ta ji a fuskarta suna goge mata hawaye, wani sanyi da nutsuwa suka zo mata ta lumshe ido, kafin a zafafe ta bu’de su ta kuma janye fuskarta, dole ta cusawa Imran tsanarta matu’kar tana so ya rabu da mahaifiyarsa lafiya tunda dai tace ko bayan ran ta bata amince su yi aure ba, cikin zafin rai ta shiga furta masa maganganu “Na tsaneka Imran, har abada kuma ba zan sake son ka ba ka riga ka cusa min tsanarka a zuciyata, ka fita a rayuwa ta Ammar nake so shi nake muradin Aure.” Sam bai san sanda ya jata jikinsa ba kamar magnet Lokaci ‘daya ya saki ajiyar zuciya yana furta “Ni kuma ina tsananin son ki ba mamaki son ki shine Ajalina I love you Ayshatu na and I really mean it...”


Turo ‘kofar kitchen ‘din da akayi ne yasa Shatu saurin zame jikinta, sai dai tuni idanunta suka sauka cikin na Ammar bata haufi ya riga ya gansu. A hankali ta furta ya salam!



Saduwar alheri.



Kamar yarda wasu daga cikinku suka bu’kaci a bu’de vip group, Alhamdulillah ‘korafinku ya kar’bu na bu’deshi akan farashin ku’di mafi ‘karanci daga 500 to above. Zaku dinga samun posting 2 times a day. Normal group kuma posting ba kullum ba. nagode da ha’din kan da kuka bani.



Da bazarku muke taka rawa!

[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?


44


Da sauri Ammar ya ‘dauke idon sa ‘kirjinsa yana dukan uku-uku, tabbas ya yi mummunan gani da kuma ace ya san hakan zai ganin da bai shigo kitchen ‘din ba. Ya runtse idon sa yana jin tamkar zuciyarsa za ta buga.


Shatu kuwa a zafafe ta kalli Imran “Burin ka ya cika, ya ganni tare da kai, wanda direct zai iya zargin wani abu wallahi ban yafe ‘batawa masoyi na rai da kayi ba.”

Shi ‘dinma wannan karan takaici ya gume shi da sauri yace “Na ji da’di da ya gani, wa ya aike shi shiga gonar da ba tasa ba, ko an gaya masa bakin rijiya wajen wasan makaho ne, ai wallahi ka’dan ma ya gani matu’kar bai janyeba wata rana sai yaga abinda zai saka idon sa makancewa. Kuma wallahi duk ran da kika sake kiransa masoyinki ko mijinki a gabana sai na kusa cinye bakinki saboda sumbata, shine purnishment ‘din ki.” Daga haka ya juya da sassarfa ya bar kitchen ‘din, saboda matu’kar zai cigaba da ganinta a hakan zai iya wuce gona da iri. Wani irin feeling yake ji na tashin hankali, wanda ya da’de bai samu kansa a wannan yanayin ba.


Shatu ta bi bayansa da kallo, ita kanta gaba ‘daya jikinta a mace yake, rungumar da ya kai mata a bazata ta haifar mata da kasala, ta tayar mata da duk wata kwantacciyar sha’awarta, ta runtse ido tana sake sha’kar ‘kamshin turarensa da ya gauraye jikinta gaba ‘daya.


Ammar da Ta tuna ya sata fita da sauri, da nufin taje ta fahimtar dashi kada ya ‘dora zuciyarsa a bigiren zargi.

Ta da’de tana knocking a ‘kofar bedroom ‘din kafin ya amsa murya can ‘kasa “Yes come in, a bu’de take. Ya fa’da yana mi’kewa da ‘kyar daga kwanciyar da yake, idanunsa sun ka’da sun yi jazur.


Jikinta a sanyaye ta shiga cikin ‘dakin, idanunta a ‘kasa tana wasa da fingers ‘din ta. Ammar kuwa idanunsa a kanta yana tuno a yanayin da ya ganta a jikin Imran, ga ‘kamshin turarensa nan ya baibaye jikinta don daga shigowarta bedroom ‘din ya na’de ‘kamshin turarensa, duk da zuciyarsa a zafafe take cike take da kishi, hakan bai hana shi sakar mata murmushi ba, yana yi yana kawar da ‘bacin ran da yake fuskarsa. “Welcome Amarya ta, shigo mana ki zauna.” Ya nuna mata kujera. Babu kuzari sam ta zauna har a lokacin idanunta a ‘kasa. Kula da ya yi ta kasa sakewa ya sa shi cewa “Ko baki zo ba dama ina da niyyar kiran ki, maganar lefe ki ba ni sizes ‘din ki idan kuma kin fi son ki siyo da kanki then sai na baki ku’din under wears ‘din ku siyo da su Hafsa, tunda na ji sun ce kanon za su bi mu.” Da sauri ta girgiza kai “Ka siyo kawai, zan turo maka sizes ‘din ta whatsapp, amma don Allah kayi ha’kuri da abinda ka gani ba wani abu muke ba....” Da sauri ya dakatar da ita “Ban shirya jin komai ba, na fahimci abin da yake nufi shi yasa ma zan fara shirin bikin gadan-gadan, don ya fahimci da gaske nake ba gudu ba ja da baya, idan ma tunaninsa zan ha’kura na bar masa ke, ba zai yiwu ba.”

Shatu kasa cewa komai tayi illa cigaba da jan zaren mayafinta da Tayi, har a zuciyarta ba haka ta so ba so tayi Ammar ya janye ya ha’kura. Amma ba yarda ta iya dole ta mi’ke ta fita daga bedroom ‘din Ammar ya bita da kallo yana sakin ajiyar zuciya.



——————-

A ranar Imran ya juya zuwa kano so yake ya je ya think tsiye Shaheedah ya gano gaskiyar lamari, idan kuwa ya tabbatar ita ce ta ha’da kitimurmurar nan tabbas zai gwada mata zahirinsa. Ta jirgi yabi kuma tare da Akram da ya ma’kale masa ya tafi, ita kuwa Ikram ko kallonsa ba ta yi.



Ba tare da ya sanar mata zai dawo ba, zuwan da ake kira zuwan ba zata. Suna zaune ba je da kayayyakin da Shuwa ta kar’bo musu wajen yawon bin malamansu, ya tura ‘kofar side ‘din Anty Amaryar ya shiga. Ganin yarda suka razana ne daga ganinsa ya tabbatar masa akwai wani abu da basa so ya gani. Yana shigowa idanunsa ya sauka akan wata laya da aka gar’kamawa kwa’do (padlock). Gabansa ya fa’di, yayi excusing ‘din su bai kuma fasa shiga ba.

Zama yayi akan kujerar da take fuskantar Anty Amarya, idanunsa cikin na shuwa da take shirin juya tunaninsa “Kina ji ko Shaheedah dole sai an tashi tsaye, wannan ramar taki akwai mutanen ‘boye don haka na kar’bo miki magungunan nan kada ki sake ki yi wasa dasu.” Imran cikin mamakin matar ya zura hannu a aljihu yana mi’kewa kamar zai wuce sai kuma ya saka hannu ya ‘debe tarkacen da suke gaban Shuwa. Gaba ‘daya ji su kayi kamar su zunduma ihu, yana murmushin rainin hankali yace “Bari ni zan adana mata su,
na san ta sarai da wasa da magani ni kaina ramar tata tana damuna ashe mutanen ‘boye ne?” Daga haka yasa kai ya fice ‘dauke da Akram a kafa’da.

Ba Anty Amarya ba har ta Shuwa sai da ‘yan hanjinta suka ka’da saboda gaba ‘daya magungunan da bayaninsu a ciki, gudun kada ta manta yasa ta rubuta, da kuma sunayen mutanen da maganin zai yiwa aiki, hakan yana nufin Imran yana gani zai san inda maganin ya nufa. Shaheedah kawai hawaye ta ji yana zubo mata ta tabbata ta ta ta ‘kare.

Shuwa da sauri ta dubeta “Ki mi’ke kije tun kafin ya bu’de ki san dabarar da kika yi masa kika kwashe. Ai kuwa ba shiri Shaheedah ta mi’ke har da gudunta.



Sai dai ina addu’arta bata amsu ba, wannan ranar, yau dai kam Allah ya toni asirin su.

A parlourn ta tarar dashi hannunsa ‘dauke da layar nan da sunanta da nasa ya fito ‘baro-‘baro. A takardar kuma an rubuta yarda za tayi amfani dashi ta mallaki zuciyarsa. Saura duk kayan ‘kazanta ne har da wanda da jinin haila zata ha’da. Wata irin tsanarta ta ziyarci Imran fiye da wacce yake mata. Ya runtse idanunsa yana son ‘daukar action amma yana tunanin gwara ya bari ya gama ‘kunsa musu takaici, bari ya nuna musu bai fahimci komai ba, ya ga iya gudun ruwansu. Ajiye kayan yayi a gefe yana jifan ta da murmushin da na dole ne ya aro ya yafa a fuskarsa. Ya tura mata kayan yana ta’be baki “Zo nan ki kwashi kayannan ki adana su amma please kada kiyi wasa dasu kin ji ance maganin jinnu ne.”

Wata kyakkyawar ajiyar zuciya Shaheedah ta saki tana hamdala a zuciyarta da bai gane ko meye ba da sauri ta ‘debe kayan, ta kai su ta adana su. Sannan ta dawo gefensa ta samu ta zauna, ya ji kamar ta jona masa wuta, amma haka nan ya daure yana kallon Akram da ya fara alamar barci ko yunwa. Itama ido ta zubawa Akram ‘din kafin tace “Wai a ina ka samo mana yaro mai kama da kai?” Mamaki ya kusa kashe Imran daga zaune, na zallar rainin hankalin Shaheedah nufinta bata son ‘Dansa bane ko me? Direct ya amsa mata da “Jikan Mommah ne.” Jikin ta ne ya sanyi, tsoron kada ya jefo mata tambaya ya sata saurin mi’kewa “Allah ya raya shi, bari in je in samo maka abinci.” Har ta kai ‘kofa ta ji yace “Ki bar abincin nan za muje eatery mu ci nagode.” Jikinta a salu’be ta fita jin yace ba zai ci abincin ba, ta fara tunanin ko dai ya ganeta ne ya bagarar da zancen, amma anya kuwa da ya ganeta ai ba zai ‘kyaleta ba, da tuni ya ‘dau mummunar hukunci.

Tana shiga Shuwa ta tarbeta “Yaya? Allah yasa dai bai gane ba.” Shaheedah ta ta’be baki “Gaulan babu abinda ya gane. Ya ma bani magungunan na kwashe abi na, kuma a yau zan fara amfani da su.” Suka saki ajiyar zuciya gaba ‘daya. Shuwa ta ‘dauko ‘dayan maganin Ta mi’kawa Zainab “Kin ga wannan maganin shi ake kira manta uwa, na farra’ku ne tsakanin Hajja da ‘danta don kuwa mutumin nan ya tabbatar min matu’kar ba farra’ku aka yi musu ba aikin da ake son ya kama manga ba zai kama shi ba,
Sai an cusa wa Hajja tsanar Manga ta daina tunawa da shi a addu’a sannan zai ci shi. Don haka ki kula, cikin dare ake so ki fita da ‘daurin ‘kirji ki yi ha’ka ki birne kina yi kina ambatan sunan mijinnaki da na uwarsa.” Zainab cikin farin ciki ta amsa tana zabgawa Shuwa godiya, gani take ko uwar da ta kawo ta duniya bata sonta kamar yarda shuwa take son ta, ta yarda da hakan har cikin ranta.



——————————

Kashe garin sadakar bakwai suka dawo, nan fa Ammar ya fara sakin ku’di ana ha’dawa Shatu lefe, a tsukun wannan lokacin sam Imran hankalinsa ba a kwance yake ba, dauriya kawai yake da ‘karfin hali, ga shi ya tsaurara bincike akan Shaheedah da iyayenta musamman Shuwa, duk wani takun ta ya sani, burinsa ya samu hanyar da za su tonawa junansu asiri da kansu, ba tare da wani ya shiga cikin lamarin ba.


Yau ma bai gaji ba a bedroom ya samu Mommah, da niyyar sake bata ha’kuri kamar yarda ya ‘kwallafawa kan sa kullum. Mommah Ta ‘dago ido tana kallonsa “Ba zan gaji da ce maka na ha’kura ba, amma batun na sake aure maka shatu ne babu shi, Shatu bata da miji sai Ammar don haka kada ka sake zuwa min da wannan zancen na gaya maka.”

Idanunsa jazir ya mi’ke ya tafi ‘d’aki zuciyarsa cike da ‘kunci ya zauna dafe da kansa yana tunanin mafita, idan baiyi wasa ba wankin hula na neman kai shi dare, a yarda ya ji suna shirye-shirye auren ba zai fi sati uku ba, hakan na nufin yana ji yana gani Ammar zai yi winning a kansa. Ina! Ba zai yiwu ba.


Da sauri ya ‘dau wayarsa ya shiga danna kiran Ammar, murya a cunkushe yace “Kana ina?” Ammar sai da yayi jim sannan yace “Ina tare da Shatu, wani abu ne?” “Ka sameni a bedroom ‘dina akwai maganar da za mu yi da Kai.” Ammar shima murya a cunkushe yace “Okey” ya ja gwauron numfashi yana duban Shatu “Ina zuwa ki shiga gida idan na dawo za muyi magana.”



A tsaye ya sameshi yana struggling a bedroom ‘din nasa. Ammar yayi sallama a karo na uku kafin ya amsa da alama yayi nisan kiwo a tunani.

Fuskar Ammar a ‘daure yace “Ga ni.” Imran ya ja numfashi kafin yace “Na gan ka, yanzu Ammar kana tunanin abinda kayi, kayi min adalci a matsayi na na brother ‘din ka ciki ‘daya? We are siblings fa.” Ammar ransa a ‘bace yace “Me nayi na rashin adalci?” “Auren matar da ‘dan uwanka ya saki.” Ya ba shi amsa a zafafe. Shima a masifen yace “Hakan ya haramta ne?” Cikin takaici da kallon baka da hankali Imran yace “Idan bai haramta ba, ka san dai ana barin halak don kunya, kai yanzu ba zaka ji kunyar su Akram su girma suga ka aurewa uban su mata ba, da wani ido zaka kallesu? Ina raye ka aure min mata saboda son zuciya. To I warn you for the last time ka fita daga harkar mata ta.” “Idan na ‘ki fa?” Wani murmushin takaici Imran yayi kafin yace “Dole ma zaka yi ko da tsiya ko da arziki, ka bawa Mommah shawara kada ta ‘kulla gabar da ba’a san ‘karshenta ba. Me Za ku sanar da ‘ya’yan da zaku haifa, na baka shawara idan kunne ya ji jiki ya tsira.” Ammar ya ta’be baki kafin yace “Sai dai idan kashe ni zaka saka ayi, amma ba zan bar ta ba ni na saka ka sake ta?”
“Okey kada ka sake ta je ka ka aureta.” Ya fa’da yana sakin murmushin takaici.
Ammar ya juya ya fice a zafafe.




————————-


‘Karfe 3:00 na daren ta mi’ke daga gadonta, bayan ta yi ‘daurin ‘kirji ta fito a hankali daga ‘d’akinta. Ta bu’de ‘kofar da zata sada ka da baya ta cikin parlournta.

Tana isa wajen da sauri ta hau waige-waige, ganin ba wanda ya ganta ya sata ‘ko’karin ha’ka ramin da zata burne layar, tana gama ha’kawa ta ciro layar tana ambata suna da ‘dan ‘karfi ta zura layar a ramin. Dai-dai lokacin da hasken flasherr waya ya dallareta da sauri ta juyo, lokaci ‘daya ta razana zata saka ihu. Cikin wata irin murya yace “Kada ki fara Zainab, Yau Allah ya toni asirinki, ha’ko abinda kika birne.......



Ga masu son biyan ku’din vip group inda za ku dinga samun posting biyu a rana ga account number.


2118666253 U B A


Sai tura shaidar biya ta wannan layin

08033748387

Nagode da ‘kaunar da kuka nuna min jiya kam na ga masoya na!
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me zan yi da ita?


45


Gabanta ya shiga dukan Tara-tara, bayan Ta d’ago ta yi arba da Dahda a tsaye idanunsa cikin nata, ran sa a matu’kar ‘bace yana mata wani irin Kallo. Ya zura wayarsa a aljihu bayan ya yi saving vedionta da ya d’auka. Bai ce mata komai ba ya juya ya bar wajen.

Ji ta yi kamar ta dur’kushe a wajen ta saka ihu, shikkenan dubunta ta cika bata da wata hujja da zata kare kanta.



Dahda kuwa tunda ya koma bedroom ya kasa barci,hakan ya saka shi tashin Mommah ya ce ta d’auro alwala su yi sallah. Mommah ba tare da ta san dalili ba ta cika umarninsa kasancewar dama ta saba irin wannan lokacin sallahr ta ke yi.


Dahda ya da’de a sujjada ya na godiya ga Allah da ya bayyana masa wacece Zainab. A kuma daren ya rubuta mata takardar saki cikotan guda biyun da suka rage, ya tura vedion cikin system ‘dinsa saboda ya zama shaida a wajen Hajja, duk da ba yanzu zai gaya mata ba sai ya sake ‘kwakkwaran bincike akan lamarin Zainab.


Tun a daren Zainab ta ke kuka, ta shiga kiran Shuwa domin ta sanar mata aiki ya riga ya kwa’be, amma Shuwa bata d’aga ba tana can ta na sharholiyarta, duk da ta ga kiran tsaki ma ta ja ta kife wayar ta na cigaba da aikata bad’ala, a zuciyarta fad’i take na gaji da matsalarki zainab ba akan ki zan ‘kare ba, ina ga ma yanzu na daina miki wani aiki kud’inki zan fara ci haba ina dalili?



———————————

Mommah ganin Dahda sukuku ya tashi

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment