Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hankalinta, hakan yasa ta sak shi a gaba da tambaya, jan ajiyar numfashi ya ke yana fad’in bakomai ki bari akwai lokacin da za ki ji, tabbas Lamarin d’an adam abin tsoro ne a dai tsukun lokacinnan ki dage da addu’a da azkar kawai shine abinda zan ce miki.” Shiru ta yi tana kallon cikin ‘kwayar idonsa tace “Allah ya jishshemu alheri, dama zancen gidan Ammar zan maka ya ce muje mu gani an kammala gini. Kuma ka ga bikin ‘karatowa ya ke ya kamata na shiga Abuja akwai shirye-shiryen da za mu yi, Hajiya Mama ta ce na mayar da Shatun can saboda a had’ata da ‘yan uwanta a fara musu gyaran aure.” Dahda ya ce “Ni kuwa da ina son mu yi shawara, ko dai Ammar zai jan ye ya barwa d’an uwansa matarsa wallahi Dijah bana son rabuwar kan yarannan su biyu fa kad’ai Allah ya bamu.” Mommah ta girgiza kai “Kada mu yi haka da kai Dahda, ka bari na koyawa Imran hankali, idan za ku yi la’akari da abubuwan da ya aikata bai fa kamata ku goyi bayansa ba, kun ce gaba ma ya sake yi kenan, yara kuwa ba su kad’ai Allah ya bamu ba ga Ikram da Akram nan an haifa mana.” Dahda ya girgiza kai “Allah ya sanya alheri yasa kuma za’a yi damu, kin tabbatar ita yarinyar ta amince da za’bin na ki?” Momma ta jinjina kai “Ta amince tuni shine ma dalilin da yasa na zo maka da zancen ka yi musu addu’ar fatan alheri kawai.” “Allah ya tabbatar da alheri.” Dahda yace yana mi’kewa da key a hannunsa “Bari na je na ga gidannasa, idan akwai abin da bai yi ba a gyara tun wuri, sai ki yi wa masu furniture d’inta da aka bawa su siyar da nata na gidan Imran magana, su samo mata latest design idan da ciko sai ayi musu.” Cikin farin ciki Mommah ta ce Allah ya saka da alheri Dahda ya ‘kara arziki.” Ya amsa da ameen yana ficewa da sauri.


A bakin part d’in ta ya ganta a tsaye da sauri ta sha gabansa ta dad’e ta na dakon jiran fitowarsa. Yana ganinta ya d’aure fuska tamau ya ce “Zainab matsa na wuce ba na son rashin arziki.” Kuka sosai ta sakar masa ta na jan hannunsa zuwa cikin part d’insa.

Gaba d’aya ta zube a gabansa “please Dahda ka yi ha’kuri wallahi sharrin shaid’an ne.” Cikin masifa ya ce “Shi shaid’an dama kullum a cikin sharri ya ke ai, ki tashi tsaye in dai nine ba abinda zan miki na bar ki da duniya ta koya miki hankali.” Wani fariciki ya ratsa ta ashe dai da gaske Shuwa ta ke da ta ce ba da abinda zai iya yi, an riga an kulle bakinsa. Farin ciki ya sata su’butar baki da cewa “Aikin ki ya na kyau Shuwa.” Da sauri ta toshe bakinta ta na kallon Alhajin da sarai ta san ya ji abinda ta ce, amma ga mamakinta sai bai ce komai ba, alamar ya zama mijin ta ce d’in dai da gaske.
Juyawa ya yi ya fice a ransa ya na mata dariyar mugunta saboda shi kad’ai ya san gadar da ya shirya mata. Ita kuwa tsalle ta sa ka har da juyi cikin ‘karaji ta ke kiran Shuwa ta na fad’in “Alherin ubangiji ya kai miki aminiya ta gari.” (Allah ya shiryi ma su hali irin na wad’annan bayin Allahn, Rabbi ya kare mu daga tarkon su)



———————-

Bayan kwana biyu, da zancen da Mommah su ka yi da Dahda, tuni ta shirya tafiya da Shatu Abuja ita da su Nahna da suka gama hutun su.

Imran bai san da tafiyar ba ya na zaune a parlour abin duniya yayi masa zafi ya rasa yarda zai yi, ya ji Mommah na yiwa Ammar magana ya samo musu ticket na Abuja a kashegarin ranar za su tafi.

Lumshe idonsa ya yi ya na jin sautin bugawar zuciyarsa yana sauyawa, da gaske dai idan bai yi wasa ba wankin hula ya na nema ya kai shi dare, Shatu na neman kufce masa. Tunda a kwana biyunnan Mommah ta hana ta ma ganinsa, kullum ta na ma’kale da ita, ya sha aika Akram da short note amma yaron ya dawo cikin gwarancinsa ya ce Mommah ta yaga.

Da kyar ya mi’ke yana layi ya nufi d’akinsa. A can d’in ma ba ta sauya zani ba mafitar dai ya ke nema, zuciyarsa ta yi cak tare da tunani, ba ‘bata lokaci ya amince da shawarar da zuciyarsa ta ba shi, idan ba hakan ya yi ba, Mommah ba zata san annabi ya fakuba.



Cikin daren ya mi’ke, bayan ya tabbatar zuwa wannan lokacin kowa yayi barci, ya nufi bedroom d’in Shatu, ya kuwa ci sa’a ‘kofar a bud’e take. Da sauri Shatu Ta d’ago ta na kallonsa dama kasa barci ta yi tunaninsa ya bun’kasa a zuciyarta. Ware ido ta yi ta na
Masa kallon mamaki “Ya Imran mai ka zo yi min cikin darennan? Past 2:00 fa?” Wani kallo ya hurgeta da shi Allah yasa da hijab a jikinta don kuwa daga ita sai satin sleeping dress, muryarsa a cunkushe ya ce “Sace ki na zo yi.” Ya hau gadon gadan-gadan cikin wani irin yanayi Shatu ta so saka ‘kara, tuni ya dam’keta “Wallahi ki ka yi min ‘kara anan zan aikata koma me na yi niyya. Kina ji kina gani ana shirin raba mu alhali na san kema kina so na kunya da kawaici ya hanaki fad’a kika bar bi ni kad’ai ina ya’ki, to ki bud’e kunnenki ki ji, sharad’i zan baki guda uku! Na d’aya ki amince mu je wani wajen a d’aura mana aure mu gudu mu bar gida, ko kuma a yanzu na aikata zina dake idan ya so naga uban da zai d’aura miki aure ba ki yi istibra’i ba........” wata irin fad’uwar gaba ta riski Shatu a zafafe tace “Idan na ‘ki fa?” “Dole ma ki amince don a shirye na zo ba ta yarda za’a yi ina ji ina gani a d’aura miki aure da wani ba ni ba za’bi ya rage na ki....”




Saduwar alheri lahadi insha Allah kun san bana typing asabar ina godiya mutanena na vip. Allah ya bar so da amana.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita


46.


Wata irin bugawa zuciya ce ta risketa, lokacin da ta ji ana buga ‘kofar d’akin, shi kansa bai san sanda ya bud’e ido ba, da azama ya mi’ke yana neman wajen ‘buya.

Shatu da sauri ta ja hannunsa jin ana sake buga ‘kofar wannan karan da d’an ‘karfi, toilet ta tura shi ta jawo ‘kofar da sauri, zuwa lokacin har wani gumi ya yanko mata duk da sanyin a’cn da yake d’akin.

Tana bud’ewa taga Hafsa a tsaye ri’ke da kanta, Ta d’an matsar da ita gefe “Matsa Shatu barci nake ji kamar na kifa, waccan ‘yar rainin hankalin ta hanani barci, wallahi Nahna akwai ba’kar muguwa.” Cikin wata iriyar razana Shatu tace “Tashin hankali anan za ki kwana?” Da sauri Hafsa ta kalleta, tana nazarinta sai ta lura kamar tana ‘boye wani abu saboda yanayin yarda fuskarta ta nuna, Hafsa ta ce “Anan zan kwana is there any thing wrong?” Da sauri Shatu ta girgiza kai cikin matu’kar firgita, ta bata hanya ta wuce.

Jikinta a sanyaye ita ma ta bi bayanta hantar cikinta na kad’awa da kuma fargaba da tsoron kada Hafsa tayi katari da shi bata san wace iriyar amsa za ta bata.


Allah-Allah ta ke barci ya kwashe Hafsa ta samu ta bud’eshi ya fito,
Sai dai har zuwa lokacin Hafsan ba tayi barci ba tana dai kwance kanta yana sara mata.



Shi kansa da yake cikin toilet d’in hankalinsa a tashe ya ke, duk wani sound d’in maganarsu a kunnensa suka yi shi, it means kenan kwanan toilet ya kama shi, ya juya ya dubi toilet d’in duk da neat yake and clean ba ya jin zai iya kwana sur a cikinsa. Idanunsa ya kai kan windown toilet d’in ya ga ‘karami ne sosai ba ta yarda za’ayi ya iya fita ta cikinsa. Tsaki ya ja sosai ya tabbatar da maganar hausawa da suka ce idan ba ka iya mugunta ba ba ka yiwa kanka ba yanzu ya zai yi ya ku’buta daga tarkon da ya tsunduma kansa. Tur’kashi! Ace Mommah ta wayi gari a ganshi a bedroom d’in Shatu ai shikkenan kashinsa ya bushe ya kad’e kuma har ganyen sa.


Hafsa na daga kwancen ta zaro waya ta duba lokaci past 2:00 am, ido ta zubawa Shatu kafin ta ce “Ke me ya hanaki barci?” Shatu da ta lula duniyar tunani bata ji me Hafsan ta ce ba har sai da ta ta’bo ta kuma ta sake maimaita mata, a murya a d’ashe ta ce “Dama ina samun sleepless ban san me yasa Ba.” Hafsa ta ta’be baki kafin ta ce “Saboda kina tunanin Imran mana kin kuma kasa fitowa ki gayawa Mommah gaskiya, ke mijin ki kike so kin bari kuna wahala da soyayyar juna, ni wallahi ban ga dalilin wannan kwamacala da Mommah ta ke shirin had’awa ba na yi mata magana ta kasa fahinmta, na kuma lura Nahna ce ta ke zuga Ta.” Shatu shiru ta yi mata kawai, saboda ita ba wannan zancen ta ke so ba, so ta ke Hafsan ta yi barci Imran ya samu ya fito daga toilet. “Ta shi ki yi light off bana iya barci da haske, kema kuma ki kwanta ki runtse idon ki kina karatu a zuciyarki za kiyi barci.” Shatu ta bi yarda tace ta kwanta ta runtse idon ta tana saurarar karatun da Hafsan ta saka mata, cikin hukuncin ubangiji barcin mai nauyi ya d’auketa. Hafsa ta bita da kallo zuciyarta cike da tausayinta ta tabbatar soyayyyar Imran ce ta ke d’awainiya da ita. Har ta rufe ido za ta yi barcin sai ta ga kuma gwara ta yi alwala ta yi sallah ta ro’ka musu Allah sassauci a zuciyar Mommah.


Direct toilet d’in ta nufa, Ba tare da wani sound na tafiya ba, saboda kada ta tashi Shatu, shi yasa Imran bai ji tahowarta ba balle ya yi locking toilet d’in. Ta murd’a da sauri kawai ta afka kanta ciki.


A tare wata irin fad’uwar gaba ta riskesu, Hafsa da Imran, har Shatu da ta farka jin sound d’in bud’e toilet, da sauri ta d’ora hannu a kai, shi kuwa Imran runtse idanunsa ya yi cikin wani irin takaici da dana sanin biyewa son zuciyarsa. Yanzu mai zai cewa Hafsa ta fahimci ba abinda ta ke zargi suke aikatawa ba? Babu! Direct zuciyarsa ta bashi amsa.

Hafsa kuwa wani irin sanyin jikine ya rufeta da tashin hankali lokaci guda. Kafin ta ja jiki ta jingina da bango sabods jirin da ta ji yana neman kada ita, cikin wata iriyar murya tace “Innalillahi wa inna ilaihirrajiuna! Imran mai zan gani haka?”

Hannunsa na rawa ya kama hannunta cikin ‘karfin hali ya ce “Look Hafsa Ba abinda ki ke tunani bane, wallahi ba abinda mu ke aikatawa.” Cikin takaicinsa ta watsa masa kallon banza kafin ta ce “Kada ka gaya min maganar banza Imran, ban gane ba abinda ku ke aikatawa ba, me ka ke yi a toilet d’inta? Kuma tun wani lokaci ku ke aikata bad’alar?” “Hafsa kada ki saka zato a ran ki, zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ne, wallahi ki yarda ba abinda mu ke aikatawa.” Tsaki ta ja “Ko Qur’ani za ka bani na dafa ba zan yarda da wannan tatsuniyar ba, wallahi ka bani mamaki Shatu ce fa ‘kanwarka marainyar Allah ita kake lalata da ita a cikin gidanku, matar da d’an uwan ka ya ke shirin aura shin ka yi masa adalci? Dole Mommah ta sani saboda dole sai ta yi istibra’i kafin a d’aura mata aure.” Ganin Shatu kawai ta yi a gabanta “Don Allah Anty Hafsa ki rufa mana asiri wallahi ba abinda ki ke zato bane magana muke da ya ji knocking mun zata Mommah ce shine ya shige toilet.” “Rufe min baki kafin na doke bakin ki, magana ku ke? Magana cikin tsakiyar dare kuma a d’akin ki? To maganar me kuke, ko ‘karamar yarinya ce ta ganku a haka ba zata yarda da wad’annan tatsuniyoyinnaku ba, ina shigowa na ga alamar rashin gaskiya a tare da ke, dama ance rana dubu ta ‘barawo, Yau Allah ya toni asirinku, kuma wallahi ba zan rufa muku asiri ba.” Hawaye ne ya ‘ballewa Shatu bata san sanda ta kalli Imran ba cikin kuka ta ce “Ka cuce ni Ya Imran.” ‘Bacin ran sa ya bayyana ‘karara da har kana iya gani akan fuskarsa, ya zubawa Hafsa wani kallo kafin ya fice da sauri daga d’akin.


Ai kuwa yana fita Hafsa ta juya kan Shatu ta shiga surfe ta “Namijin ki ka bawa yarda har haka, kin cuci kanki Shatu, Shi duk abinda ya yi ado ne sa’banin ke da zai goga miki ba’kin paint, ki sanar da ni gaskiya me ya yi miki da ya shigo?” Kuka ta ke sosai tace “Bakomai Anty Hafsa.” Wani banzan kallo ta yi mata tace tatsuniya kenan kada ki fad’a bari na tara muku jama’a tukunna sai ki magantu Allah ya kaimu safe.” Zubewa Shatu kawai ta yi akan tiles d’in da yake toilet d’in ta ri’ke kanta da ya ke matu’kar sara mata ta rasa dalilin da yasa Hafsa ta kasa mata uzuri ta kuma yarda da cewar ba abinda suke aikatawa. Yanzu gobe mai zata ce da Mommah da sauran mutanen da Hafsa ta ke i’kirarin sai ta gayawa? Take zuciyarta ta bata amsa fa Babu! Ba wanda zai yarda ba abinda suka aikata, a fili ta furta “Hasbunallah!”


Har asuba barci ya gagare su ba ita ba Hafsa ba ba shi kansa Imran da yake d’akinsa ba, zuciyarsa cike da matsanancin tashin hankali, shi ba ya jin takansa mutuncin Shatu kawai yake yi wa, don ta shi bai ‘ki hakan ya faru ba idan ya so ayi uwar watsi dole a bashi matarsa idan Mommah ta ji yana bin d’akinta cikin dare. Don shi kam a nasa tunanin gaba ta kaishi matu’kar wannan ne dalilin da za’a dawo masa da matarsa.



Da sassafe suka yi shirin tafiya Abuja, Shatu wanka ta yi kawai ta zira riga idanunta sun kumbura alamar bata samu barci ba, ga kuma kukan da ta sha.


A dinning suka zauna don su yi breakfast su wuce, tana fitowa Mommah ta zuba mata ido tana mata kallon tuhuma “Shatu lafiyarki kuwa? Kin kalli idonki a mudubi?” Ammar ya d’ago yana dubanta, cikin tashin hankali yace “Me ya same ki?” Hawayen da ya zubo mata ta saka handkerchief ta d’auke, ta amsa musu da muryar ta da ta dashe “Bakomai bana jin dad’i ne.” Mommah ta girgiza kai tana mamakin zuciya irin ta Shatu
Da ta ke manta sharri ta sani sarai soyayyar Imran ce ke wahalar da ita, sai dai ita ba zata amince ta komawa Imran ba tunda ita bata san ciwon kanta ba ita Ta sani. “Allah yasa bakomai d’in, sai ki hanzarta ki sha tea kada muyi missing flight.” A hankali tace “Azimi nake” idanunta akan Hafsa da tayi kicin-kicin da Fuska. Mommah murmushi ta saki tace “Allah ya bada ladan azimi ya sanya a mizani, amma shi azimin na menene? Da ake yinsa ranar talata.” Hafsa tace “Kika sani ko zunubi ta tafka ta ke neman yafiyar ubangiji, wani zunubin ai saboda girmansa sai an had’a da azimi domin neman yafiyar ubangiji.” Wayar da ta ke hannun Shatu ce ta zame ta fad’i, dalilin yanayi jikinta da ya hau ‘bari jin Hafsa na niyyar tona musu asiri. Fitowa Imran ce yasa suka yi shiru. Mommah ta dubeshi shima dai idanunnasa irin na Shatun duk sun kumbura dalilin rashin barci. Ta amsa gaisuwarsa tana ta’be baki, a zuciyarta tace kad’an ma ka gani sai kaji ana gud’a ana an d’aura sannan ne zaka san ka yi rashi kaje ka ji da ‘kanjamammiyar matarka. “Ku tashi mu je Imran ya saukemu tunda ya fito.” Ta fad’a tana kallon Ammar don dashi za’a tafi. Suka mi’ke kuwa gaba d’aya sai ji tayi Imran yace “Ni ma Abujar za ni.” Mommah ta juyo tana masa wani duba kamar ta yi dariya sai kuma tace “Ni fa bana son shashanci shikkenan ita kuma matar taka sai ka tsallake ka barta, dama yau-yau ku shirya ku koma gidan ku, ban ga dalilin da zaku tare mana a gida ba, tunda kun bar turkeyn.” Mommah ta fad’a a zafafe. “Aiki an je yi.” Ya fad’a yana jan trolley. Har ya kai ‘kofa Mommah tace sai ka tsaya ka sha ko tea ai.” Direct yace “Azimi nake.” Dariya ta kama Mommah ta guntse ta tace “Allah ya bada lada.” Nahna kuwa dariyar ta tayi sosai ta ce “To ko dai yau d’in wani special day ne a islam da ake azimi mu ba mu sani ba.” Ji suka yi kawai Ammar ya saki wani dogon tsaki.



—————————-

A parlour duk suka zube bayan isarsu Abujan,banda Imran da ya shige part d’in Hisham saboda kansa da yaji yana sarawa, musamman ganin an fito da lefe ana ta kallo ciki har dana Shatu da na Ammar, alamar da gaske dai an yi masa fashin mata ‘kiri-‘kiri, ya zama dole ya nemi malamin musulunci ya kai ‘kara.
Nan aka shiga tsare-tsaren Biki, banda Hafsa da ta ja gefe cikin tashin hankali, tana tunanin ta yarda zata fara gayawa iyayenta abin da ta ci karo da shi a daren jiya, tabbas gwara ta gaya musu don a san abin yi.


‘Karfe takwas na dare suke zaman cin abince har da Alhaji Baba, Imran ma ya fito, don burinsa yaga Shatu ko zuciyarsa za tayi sanyi daga tafasar da take masa.

Fuskarsa ba annuri ya zauna a gefen Alhaji Baba.


Sai da aka gama cin abincin sannan Hafsa Ta d’ago kanta ta gyara zama tace “Assalamu alaikum, don Allah ina son ku bani hankalinku akwai maganar da zan yi dangane da abinda ya faru a daren jiya.........
Shatu da Imran suka zubawa juna ido cikin tsananin bugun zuciya.




Saduwar alheri



Masu son vip group inda nake posting safe da dare su biya 500 kacal ta wannan account d’in....

2118666253 U B A


Idan an saka sai a tura shaidar biya ta wannan numberr


08033748387.

Nagode biya ka huta takaicin ka samun postin akan kari safe da dare.



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment