Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yana zaman jiran su, fuskarsa na bayyanar da damuwar da yake ciki. Yanzu kam ya ha’kka’kewa kansa ba ‘karamin son Shatu bane ya kama shi. Tunda ta taho idanunsa yake zube a kanta.
Da sauri ya mi’ke yana tambayar Mommahn ya ake ciki? Mai likitan yace? Mommah ba tayi masa magana ba illa jan ajiyar zuciya da take yi akai-akai. Tsaf tunani ya cunkushe mata zuciya burinta suje gida ta titsiye Shatu ta ji gaskiyar batun.

Ammar hankalinsa a tashe yake driving, don haka tu’kinnasa ya zama rough sosai, bai san me ya canja Mommah, burinsa d’aya Allah yasa ba wani mugun ciwo bane ya kama Shatunsa, da lamarin ya gigita hankalin Mommah. Suna parking Mommah ta fice da sauri, ta kuma tasa ‘keyar Shatu zuwa cikin gida. Basu tsaya ko ina ba sai cikin bedroom d’inta. Ammar duk da bai iya la’be ba ranar kam ya koya. Suna shiga Mommah ta mayar da ‘kofa ta rufe. Idanunta ta zuba cikin na Shatu “Gaya min Kun had’a shimfid’a da Imran ne kafin ya sake ki?” Gaba d’aya kunya tayi wa Shatu dabaibayi ta shiga wasa da yatsun hannunta bata ta’ba jin kunyar wani mahaluki ba kamar yarda ta Mommah yau tayi mata dirar mikiya “Ki fito fili ki gaya min, ki ture batun ni mahaifiyar Imran ce ya saka ni a mizanin mahaifiyarki, ki d’ago ki gaya min kun had’a shimfid’a nace.” Idanun Shatu a runtse, cikin wani yanayi ta d’aga kai. Mommah ta saka salati kafin tace “Shatu bud’e idonki kiyi mini bayani idan ba so kike zuciyata ta buga ba, shin bai sameki cikakkiyar budurwa bane shi yasa ya sake ki a kashe gari ko ya aka yi? Don ni dai abin ya bani mamaki ganin tafiyarki ko canjawa ba tayi ba, bai same ki a budurwa bane?” Da sauri ta girgiza kai kafin ta sake runtse ido murya na rawa tace “Wallahi Mommah ya sameni don zanin gadon ma ya ‘baci da jini, kuma naji a ‘kauyenmu ance idan aka ga haka shine mace ta kai budurcinta. Don yar gidan maigari ma da akayi mata aure sai da ta bamu labari.” Mommah ta saki wata nauyayyiyar ajiyar zuciya hankalinta kam yanzu ya kwanta. Ta tabbatar rashin mutunci ne kawai ya sa Imran ya ketawa ‘yarta haddi ya kuma tsallake ta barta. Ai kuwa wallahi sai ta shayar dashi ruwan mamaki. Ta sake jin haushin Imran ya dabaibayeta sosai.
“Zan ja kunnenki kada ki sake ki gaya wa kowa kina da ciki, kafin na san shawarar da zan yanke akan cikin naki, don bana son karatun ki ya samu tasgaro.”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-32


Elegant Online Writers.....


Momma ta sake gyara zamanta, tana kallon Shatu “Kada ko da wasa ki gayawa kowa kina da ciki, idan nace kowa ina nufin kowa, yanzu tunda hutu kuke jibi insha Allah zan wuce dake Abuja a can zaki haihu, idan yaso a samo miki malamin addini da wanda zai dinga koya miki karatun boko, kafin ki haihu mu san mai za’a yi.” Shatu ta d’aga kai cikin ‘karfin hali jikinta duk a sanyaye yake, ta mi’ke ta fita bayan Mommahn tayi mata umarni.

Ko da ta isa d’aki tsayawa tayi cak a gaban mudubi, ta d’aga rigarta hannunta akan shafaffan cikin da ko alamar da nuna zaunuwar ciki bai yi ba.sai dai motsin da cikinnata yake yi ne ya tabbatar mata da akwai cikin, lokaci d’aya ta saki hawaye sai kuma murmushi kamar wata zautacciya, a fili ta furta oh ni Shatu nice zan zama Mama”. Ta saka tsalle cikin tsananin murna saboda dama Allah ya sawa Shatu jarabar son yarinya. Tayi sak kuma cikin tsoro tana tunanin Innaji kada dai itama ta mutu kamar yarda Innaji ta mutu. Zama tayi gefen gadon hannu bibbiyu tayi tagumi tana tunanin Innajinta. Take hawaye ya gauraye idanunta cikin tsananin kewar Innajinta.



———————————-
Ammar tunda ya shiga d’akinsa ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai struggling a d’akin zuciyarsa cike da tunanin abubuwan da yaji suna tattaunawa. Shatu da ciki? Kuma cikin Imran, hankalinsa kam ya tashi duk d’okinsa na Shatu ta gama idda ya sanar da ita abinda yake kwana yake tashi dashi, da gaske yake son Shatu, zai iya cewa tun ba yanzu ba ya fara sonta, tun kafin ayi bikinsu da Imran, lokacin da aka yi auren hankalinsa ya tashi sosai, sai dai da ya tuna Imran ba sonta yake ba hankalinsa ya kwanta, ya tabbatar ko mu dad’e ko mu jima zai rabu da ita a taurin kai irin na Imran ya san ba zai zauna da ita ba, sai dai kash burinsa bai cika ba ashe Imran ya gama da Shatu. Amma duk da hakan ba zai fasa ba, ba zai daina jumirin Jiran Shatu ba har zuwa sanda zata haife ta gama idda. Idan ya so tana haihuwar sai ya fitar da abinda yake cikin ransa a d’aura musu aure. Da wannan tunanin ya mi’ke ya nufi d’akin Mommah.

A zaune ya samu Mommah da alama tayi zurfi a tunani, jin sallamarsa ne ya sata saurin d’agowa tana amsa masa sallamarsa bayan sakin gwauron ajiyar zuciya.
Ammar ya ‘karasa ya zaune a gefenta, hannunta ya kama a hankali yace “Mommah kiyi ha’kuri kada ki dinga d’aga hankalinki akan Imran addu’a kawai zaki yi masa nima kuma zan taya ki, sannan cikin Shatu ba zai hana ni aurenta ba idan ta haihu.” Da sauri Mommah ta d’ago tana kallonsa, kafin tace “ya aka yi kasan tana da ciki?” Murmushi Ammar yayi kafin yace “Duk naji hirarku d’azu, Na biyo ku da magungunanta da kuka manta a mota na samu kuna zancen.” Mommah ta saki ajiyar zuciya kafin ta kalleshi tace “Ammar ina son wannan ya zama sirri tsakanina da kai pls, bana son kowa ya san da zaman cikin nan, hankalina ya fi kwanciya da hakan ina son na bawa mutane da dama mamaki, ka kuma kwantar da hankalinka Shatu tamkar ka aureta ka gama in dai ina raye, saboda na lura da abubuwa da dama tun farko da kai Shatu ta dace ba da Imran ba, saboda haka a ranar da ta haihu ranar suna za’a d’aura aurenku, saboda bana son yaron ko yarinyar suyi maraicin uba, sannan bana son su ri’ki Imran a matsayin Babansu.” Ammar farin ciki ya cika zuciyarsa, burinsa zai cika a lokacin da ya cire tsammani da tabbatuwar hakan. Shatu burin ran sa zata zamo matarsa, ai ji yayi kamar Mommah ta tsundumashi a aljannah, ya shiga furta “Nagode Mommah ubangiji ya ‘kara girma, amma kuma ya za’a yi da karatunta?” Mommah tace “Idan mu kaje Abuja zan samar mata fitattun malamai zan kuma basu ko nawa ne su dinga yi mata lesson a gida, tana haihuwa sai ta zana S.S.C.E, burina a yanzu bai wuce ayi auren ba, ko don na cusawa Imran ba’kin cikin da ya cusa min, Na san tabbas nan gaba sai yayi da na sani in dai dangin Abbanku ne.” Ammar ya mi’ke farin ciki fal zuciyarsa tare da tunanin Shatu ta zama tasa confirmed.




—————
Da daddare kuwa bayan Dahda ya dawo ya ci abinci ya gama duk wasu al’adu da yake yi kafin ya kwanta, Mommah ta kawo masa zancen son tafiyarta Abuja, sai dai ta ‘boye masa musabbabin tafiyar tata ta dai sanar dashi tana son zuwa kai Shatu hutu. Bai kawo komai a ransa ba yace “Allah ya kaimu gobe zan saka Ammar yayi muku booking flight, hakan yayi kyau ko bakomai ai sunyi miki kara kuma na tabbata suna son ganin jikarsu.” Murmushi kawai Mommah tayi alamar ta jin dad’in barinta da yayi.

Kashegari kuwa wuni guda su kayi cur suna ta shirye-shriyen tafiya, duk wasu kayan da zata bu’kata Ammar ya siyo mata irinsu turare bulgari da mayukanta na Neutrogena zuwa ‘yan dogayen riguna sakakku da zasu yiwa masu cikin dad’in sawa, kaya dai cikin Akwati babba tamkar shine uban d’an duk da ba kayan babies bane, sai dai kayan babies d’in ma tuni yace Mommah tayi masa list akwai tafiyar da zai yi zuwa Qatar zai siyo su a can. Mommah tace “Don zumud’i Baban Baby” yayi murmushi yana jin dad’in sunan da aka kira shi dashi. Jin d’an yake kamar nasa.


——————-
Flight d’in Azman Air na 7:30am suka bi zuwa Abuja, su Shatu an maze wai ita a dole ba za ta nuna lokacin ta fara hawa jirgi ba. sai dai lokacin da jirgin ya fara tashi ta ji wani iri ga kunnuwanta sun toshe tuni ta ru’kun’kume Mommah cikin tashin hankali, tana kiran sunan Allah idanunta a runtse, Mommah a hankali ta rungumeta tana murmushi tace “A’a Shatu ya da haka Kuma? Ai da kin cigaba da mazewar.” Shatu ina bata nutsu ba duk jikinta rawa yake har sai da taga jirgin ya daidaita ya daina jirkitawa. Sannan ta bud’e ido tana kallon Mommah, ita kanta dariya abin ya bata. Ta shafa cikinta da taji yana mata ‘kugi sannan ta kalli Mommah tace “Mommah cikina wallahi kamar zan yi bayan gida.” Mommah tace “To tashi ga toilet can ki shiga.” Da sauri ta zaro ido tace “In mi’ke tsaye anan? Ai wallahi ba zan iya ba.” Mommah ta ‘kunshe dariyar da take cinta tace “Sai ki ri’ke abinki kafin mu isa, minti nawa ne.”




——————
Suna isa airport d’in na Abuja, suka tarar Drivern Hajiya Mama yana jiransu.

‘Karfe 🕤 kuwa a ‘kofar gidan su Mommah tayi musu dake unguwar Gwarimfa a Garin na Abuja. Gidane mai girman gaske wanda da ka ganshi zaka san mazauna cikinsa ba ‘karamin kud’i suka tara ba, wanda za kayi mamaki ‘kwarai Idan aka ce maka ahalinsu Mommah ne a ciki saboda mutanene da basu d’au duniya da zafi ba, ba su da girman kai ko kad’an kuma, ba kamar yarda wasu masu kud’in suke ba.

Duk girman gidan Hajiya Mama ce kad’ai, sai masu mata aiki su biyu mata da biyu maza da ta ajiye. Su Nahna da Hafsa tuni suka koma karatu, shi kuma Hisham ba kasafai yake zaman Nigeria ya fi zama a uk a can yawancin business d’insa yake, sai dai yana yawan zuwa akai-akai.


Hajiya Mama cikin farin ciki da murnar ganinsu ta taresu, musamman Shatu da bata ta’ba kawo mata ziyara ba.

Sai da suka ci abinci suka huta sannan Mommah ta dubi Shatu “sai ki shiga ciki da bedroom d’in su Hafsa kiyi amfani dashi yafi kusa da na Hajiya Maman.” Shatu ta mi’ke da sauri don dama ta gaji burinta kawai ta mi’ke ta kwanta.

Sai da ta shige sannan Mommah tace da Hajiya Mama “Sai ki ganmu kwatsam.” Hajiya Mama tace “Hutu na san kika kawota.” Mommah ta girgiza kai “Hutu ba Hutu ba, Shatu dai ciki ne da ita.” Wata irin fad’uwar gaba ce lokaci d’aya ta riski Hajiya Mama tace “Ciki Kuma? Wani irin ciki ko dad’in ji babu cikin na wanene?” Mommah ta saki murmushin takaici tana girgiza kai tace “cikin Imran, Mama ashe sai da ya riga ya kusanci ‘yar nan sannan ya tsallake ya bar ta.” Hawaye ya kawo idon Mommah alamar ita kad’ai ta san rad’ad’in da take ji. Hajiya Mama tayi salati ta sanar da ubangiji kafin tace “cab wannan fa shine ana wata ga wata, yanzu ya za’ayi shekaru sha biyar yarinyar nan ta iya haife cikinnan ina tsoron lamarinnan in dai ba tiyata za’a yi mata ba,kuma shi Imran d’in ya san da cikin?” Mommah ta girgiza kai “Bai sani ba, don ba ma zan gaya masa ba, don ni tunda ya tafi magana ma ta fatat baki bata had’a ni dashi ba, kuma kema Hajiya Mama please bana son ki fad’awa kowa zancennan shi yasa ma na tattara na dawo da ita Nan,don haka ma tun jiya kika ji ina tambayar ki Dada tana nan kikace ta tafi, don bana son surutunta, kin san mutanennan ba hankali ne da tunani dasu ba sai abin su ya koma kan cikin don haka zan ‘boye zancen Baba kawai na yarda ki gayawa.” Hajiya Mama ta saki ajiyar zuciya kafin tace “Eeh to kema kin kawo shawara abar dubawa, yanzu mutum kam abin tsoro ne sai kana takatsantsan da addu’oi da azkar, Allah yasa mu dace ya kuma raba ta da cikin lafiya amma tabbas kam sai dai ayi mata c.s, kuma ya za’a yi da zancen karatunta?” Mommah tace “Ai kafin na tafi zan saka a samo mata ‘kwararrun malamai Insha Allah ldan ta haihu kuma lokacin ta dad’a gogewa sai ta jarraba zana ssce, saboda Shatu akwai sharp brain masha Allah.” Hajiya Mama tace “sai ‘kiriniya kuma ba da rashin iya girki.” Mommah dariya kawai tayi tana duban Hajiya Mama da tace “Maganar ba kwa waya da Imran ba mafita bace, duk da ba’ace idan d’a yayi wa uwa laifi laifi ne ta ‘kaurace masa ba, amma a gareni ni ban ga fa’ida a cikin haka ba. Fushin uwa ga d’anta ba ‘karamar masifa bace gareshi, idan har ya kira ki nan gaba ki amsa idan ba haka ba kina sake nisanta soyayya da sha’kuwar da take tsakaninku, su yaran yanzu addu’a suka fi bu’kata fiye da fushi, da yawa iyaye su suke lalata yaransu da bakunansu, idan yaro yayi maka laifi madadin addu’ar shiriya sai zagi da masifa iri-iri, don haka ki jajirce da yi masa addu’a nima kuma ina kanyi ba zan kuma fasa ba har sai naga abinda ya turewa buzu nad’i Allah yayi muku albarka da ku da zuri’arku baki d’aya.” Mommah tace “Ameen insha Allah zan sake dagewa Hajiya Mama.”

Koda Babansu ya dawo Hajiya Mama ta sanar masa ba ‘karamin dad’i yaji da samuwar cikin ba, saboda ko bakomai suna son ‘karin yara a cikin zuri’arsu kasancewar ba su da yawa.


—————————————
Mutanen turkey, zamannasu ya zamo ba yabo ba fallasa wata rana a sha zuma wata rana a sha mad’aci, kamar yarda dai hausawa kance zo mu zauna zo mu sa’ba.

Yau ma kamar kullum ya dawo daga office a gajiye, sai dai yana shigowa yaga gidan kaca-kaca kamar yarda ya barshi, mamaki ya kama shi don ya san Shaheeda dai ba ‘kazama bace tana da tsaftar ta iya iyawarta. Ya ‘karasa cikin bedroom d’in kamar yarda yayi hasashe kuwa ya sameta du’kun’kune a gado sai rawar d’ari take. Da sauri ya ‘karasa ya yaye blanket d’in yana furta “Me ya sameki haka?” Murya a cunkushe tace “Bani da lafiya” ya mi’ka mata hannu “oya tashi mu tafi Asibiti.”

Tun a hanya take kwara amai, duk da hankalisa a tashe yake amma farin ciki bai bar zuciyarsa ba. burinsa yaje hospital a tabbatar da zarginsa na cewa Shaheedahn ciki ne da ita saboda Allah ya saka masa son yara.

Suna zuwa kuwa aka yi test da scanning bayan likitan ya tambayeta yanayin da take ji. Da murmushi Doctorn ya dubeshi “Congratulations she is pregnant.” Wani sanyin dad’i ya ratsa zuciyar Imran, yayin da Shaheedah taji labarin yazo mata kamar dirar mikiya take annurin da yake fuskarta ya ‘bace ‘bat.



Am sorry for the late posting..

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-33

Elegant Online Writers.


Mamaki ya cika zuciyar Imran har bai san sanda yace mata “Madam Lafiya?” Ba tare da ta amsa ba ta mi’ke tayi hanyar fita, hakan yasa shima dole ya mi’ke yabi bayanta.

Tun a mota yake jero mata tambayoyi amma tayi d’if da ita, ‘karshe ma runtse ido tayi tana tunanin zuci, har bata san zancen da take d’arsawa a zuciyarta ya fito fili ba “Ina ni ina ciki yanzu, wallahi ban shirya ba, ban shirya wata haihuwa yanzu ba, shikkenan duk na bi na lalace jikina ya susuce, bayan yanzu ne na san na fara sanin dad’in duniya sannan wani baby can ya rusa min shi, ban shirya haihuwa ba gaskiya, don haka kayi ha’kuri cire cikinnan zanyi.” Wani kallon da bai shirya ba ya watsa mata, saboda yarda ta ha’ki’kance take magana ba ko shayin idanunsa yaga alamar kuma zancen nata daga ‘kasan zuciyarta yake. Bai mata magana ba har suka isa gida.

Sai da suka zo kwanciyar barci yace mata, bayan ya gaji da kuka da ro’kon da take masa akan a zubda cikin. “Meye dalilinki na rashin son haihuwa yanzu?” Ta mi’ke tana sake murza idonta da share hawayenta tace “Kai kanka idan kaji hujja ta sai kafi ni son a zubar da cikin, na farko dai na san baka son mace mai ‘kiba ka sha kuma fad’a min hakan, to wallahi haihuwa da wuri shi yake saka mace ta bud’e ta zama kamar uwar mata. Sannan duk wata ni’imar ta raguwa za tayi breast, hips d’ina da komai ma sai nayi loosing d’insu, don haka please Habibi mu bari nan da ten years haka sai muyi shirin haihuwa, kana ga dai yarda matar khalil abokinka ta zama lutiya, to wallahi haka zan zama.” Shiru Imran yayi ya fad’a dogon nazari a hankali yace “Idan haka ne zan bi ra’ayinki on one condition amma idan likita yace ba matsala idan aka cire cikin, ba kuma matsala tattare da yin planning d’in.” Cikin farin ciki ta rungumeshi “Insha Allah Habibi bakomai ma.” Yayi smilling yana lakuce mata hanci “kin ci sa’a bana son ‘katuwar mace kuma kince saurin haihuwa na sa mace ta bud’e, idan ban da haka da ba zan yarda ba wallahi, to ni d’in ma dai bana son zama Daddy soon, amma fa ina da son yara.”


———————————
Kwanan Mommah uku a Abuja ta tattara ta tafi ta bar Shatu da tsananin kewarta, don da kuwa gaba d’ayansu suka tafi, har abin yada dinga bawa Hajiya Mama tausayi ta jinjinawa girman sha’kuwar Shatu da Mommanta.
Amma haka suna ji suna gani suka rabu da juna.

Bayan tafiyar Mommah Hajiya Mama gaba d’aya ta mayar da kulawarta akan Shatu da abinda yake cikinta. Cima mai kyau da Abin sha mai kyau da zai ‘kara mata lafiya da ta jaririn da yake cikinta. Tayi ‘bul’bul da ita gwanin sha’awa kamar ka ta’ba jini yada fito. Kullum Ammar sai ya kira ta yaji lafiyarta ya kuma tambayeta bata da wata matsala? Kiran nan uku a rana ya zame masa tamkar tilas a gareshi, ita bata kawo komai sam a ranta ba har a yanzu a matsayin d’an uwa mafi kusanci ta ajiye shi. Kullum Mommah tana kiranta taji ya yanayin jikinta da karatunta? Tana jin dad’in ganin yarda take samun Improvement a karatun, both islamic da boko ta san ba zata bata kunya ba.

Ko da aka koma school Dahda ya ishi Mommah da zancen dawowar Shatu, direct tace Hajiya Mama ta ri’keta zuwa shekara d’aya zata dawo. Dahda sam bai kawo komai a ransa ba, yace Allah ya nuna mana amma dai ba fishi su kayi da sakin da Imran yayi mata ba ko?” Mommah ta girgiza kai “Ko d’aya ai sun yarda da ‘kaddara.” Bayan haka da kwana biyu Mommah tasa Shatu ta dinga kiran Dahdan tana gaisheshi.

Sanda tafiya ta kama Ammar zuwa Qatar a can yaof siyo duk wani kayan baby da za’a bu’kata, komai unisex duk da a lokacin cikinnata bai fi wata shidda ba.



———————
Bikin ‘yar gidan falamata ‘kanwar Dahda, hakan yasa su Mommah suka fara shirin tafiya bikin, duk da bata son zuwa amma Hajiya Mama tace taje duk kuma abinda aka yi mata kada ta tanka ta kawo ido ta zuba. Kada tace ‘kala. Hakan yasa dole ta shirya ta bi Dahda da zai tafi. Don ita zainab sune ‘kirjin biki tuni na ta tafi.

Dahda yana da gida a maiduguri don haka a can suka sauka, sai da tayi wanka ta shirya sannan ta tafi gidan Hajjan. Mota cike da kayan gudumawa.
Gidan dan’kam da jama’a ta samu. Babu mai yi mata kallon arziki kowa wani irin duba yake mata, ‘kalilan ne masu murmushin da bai kai ciki ba. Gefe ta samu ta zauna ita da Basirah mai aikinta kasancewar Hajjan na cikin bedroom d’inta, kuma bata bata fuskar shigar mata d’aki ba. Tsawon lokaci tana zaune Hajja bata fito ba, jama’ar wajen kuwa ba wanda yake ta tata, hakan yasa ta zauna tana dannan wayarta.

Tafi Awa d’aya da zuwa kafin Hajja ta fito daga d’akin ‘yan koranta na bayanta alamar an san da zuwanta, don duk fuska ba walwala suka fito. Mommah na ganinta ta dur’kusa har ‘kasa ta gaisheta, tamkar ba zata amsa sai kuma ta amsa cikin ginshira.
Basirah ta jawo babbar ghana must go ta kayan da suka kawo ta dire a gaban Hajjan, daga haka ta fice daga parlourn ranta a ‘bace da kallon rainin da ake yiwa uwar d’akinta, matar da take mata kallon mahaifiya don kuwa Mommah tayi musu ri’ko na fisabilillah da ko a gidajen iyayensu ba zasu samu irn kular da take ba su ba.

She’ke’ke Hajja ta dubi kayan, ba Ta kuma ko bud’e ba tace “An Gode.” “Hajja ai ba ita zaki godewa ba Ya manga za’a godewa don na tabbatar shi ya bada kud’in.” Mommah ta zuba mata hameedah da tayi maganar ido saboda yarda ranta ya ‘baci don kosun ficikar Dahda babu a cikin kayannan, amma da yake ba sa sonta balle ace tayi alheri dole suce Haka, wannan ta guda tace ba zata zo bikin ba gashinan tunda ga yanzu ta fara riskar takaici. Hajja ta gyara zama “Alhamdulillah dama ina ta son ganinki, ya kika ji da ‘bacin ran sakamakonki tun yanzu kuma ashe kin fara girbar abinda kika shuka, Imran kuma ya saki ‘yar taki, ko bakomai ya nuna miki baki isa ba, ina isar taki da kike tin’kaho da ita? Ai dama Na san ko mu dad’e ko mu jima sai tarihi ya maimaita kansa, yarda kika hana d’ana yi min biyayya kema sai kin riski sakamakonki gashi nan kuwa dahir kin gani. Kwana uku da aure ya sako miki ita.” Gaba d’aya gurin suka saka dariya Idanun Mommah suka kawo ‘kwalla, har zata tanka musu sai kuma taa tuna umarnin Hajiya Mama, don haka dole tayi shiru tana jan addu’oi a zuciyarta, ko bakomai Imran ne ya jawo mata, mi’kewa kawai tayi ta fice daga gidan don bata son zubar da hawaye a gabansu. Hannun Basirah ta ja suka bar gidan tana sake jiyo sanda Hameedah tace “Aikin banza gayyar tsiya kawai ta bi ta mallake mana d’an uwa.”

Ko da ta shiga motarr driving d’in kawai take ba cikin nutsuwa ba, yarda zuciyarta take tafarfasa tamkar ta fasa ‘kirjinta ta fito hakan yasa ta samu gefen titi tayi parking hannunta dafe da ‘kirjinta ta shiga kiran layin Dahda don ba zata iya cigaba da driving d’in ba, da kyar ta sameshi ta gaya masa halin da take ciki. Basirah kuwa hankali tashe take tofa mata duk addu’ar da tazo bakin Ta.

Cikin mintuna ‘kalilan Dahda ya bayyana a wajen cikin tashin hankali ya d’aukota cak daga cikin motar numfashinta yana fisga da ‘karfi, da sauri ya sata a seat d’in baya kanta saman cinyar Basirah yaja motar da wani irin mahaukacin speed. Suna isa asibitin dama tuni yayi waya don haka suka tarar da wheel bed aka yi saurin d’orata akai aka turata a guje don numfashinnata gaba d’aya yana shirin d’aukewa.



—————
Wani irin mugun mafarki da Shatu tayi sakamakon kwanciyar da tayi barcin rana shi ya farkar da ita a razane, cikin firgita take kiran “please Mommah kada ki mutu bana son na rasa uwa a karo na
Biyu.” Da sauri Hajiya Mama ta kamata don itama tun safe gabanta yake fad’uwa ba wai tana jin dad’in jikinta bane. Idan kuwa ta shiga irin wannan yanayin zahiran mutuwa ce babu tantama. “Kiyi addu’a ba’a son tashin hankalin mai ciki.” Hajiya Mama ta fad’a cikin ‘karfin hali da dauriya. Da sauri Shatu ta rungumeta “Hajiya Mama don Allah ki kaini wajen Mommah. Mafarki nayi ta mutu.” Wani irin tashin hankali ya riski Hajiya Mama don bata san sanda ta dafe ‘kirjinta da yake bugawa ba ta kama Shatu ta rungume kawai ba tare da tayi magana ba, ‘kirjinta yana bugu fat-fat.



———————

Dai-dai wannan lokacin shi kuma Imran suna gaban Doctor shi da Shaheedah. Bayan rattabawa Doctor bu’katar su ta zubda ciki da kuma son tsarin iyali Doctor ya tabbatar musu ba wata matsala. Har ya sake ‘karfafa musu gwiwa abinda ya dace kenan it’s too early ace sunyi aure ko shekara ba

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment