Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa hannu ta ‘dau wayar. Tsaf ta karance abinda ke ciki, zuciyarta ta cika da ‘bacin rai kafin ta saki murmushi “Hajiya Mama ki kwantar da hankalinki Imran zai yi abinda yafi wannan amma bakomai kansa ya cuta, yara kuma Allah ya shirya su ya bawa uwarsu lafiya shayar dasu, Insha Allah rana ita yau za’a ‘daura aurenta da Ammar shi zai maye musu gurbin uba na tabbata Ammar zai kula min dasu ko bayan raina fiye da Imran. Ta shanye hawayen tas ba tare da ta bari sun zuba ba,
Don tayi al’kawari ta daina zubar da hawayenta akan Imran, ta lura ba abinda yafi so irin wanzuwar ‘bacin ranta. Murtar Hajiya Mama a sanyaye tace “Allah ya shiryeshi, hukuncin da kika yi kuma shine abinda ya dace ubangiji ya bawa Ammar wuyan ‘dauka. Farin ciki ta cika zuciyar Ammar yaji tamkr ya tashi ya buga tsalle.




Saduwar alheri love you all. Ana tare.
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zanyi Da Ita?


38




Tsawon awoyi takwas Shatu Ta ‘dauka a kwance, kafin su shigo don ‘daga ta ayi mata wanka.

Mommah da kanta tayi mata wankar bayan nurse ‘din ta nuna mata yarda zata yi, sosai ta gasa mata jikinta da towel. Shatu ta fito da ‘kwarinta, duk da tana jin iska kamar ta ‘dauketa, ba mamaki saboda an cire abin da yake cikin.

Kafin a mayar mata da drip ‘din, Doctor ta bu’kaci a bata yaran su ‘dan zu’ki Maman saboda hakan yana da amfani a wajen jariri. Kunya ce gaba ‘daya ta dabaibaye Shatu tana jin tamkar ‘kasa ta dare ta shiga.
Mursisi tayi, tamkar bata fahimci abinda Momma ta ke gaya mata ba. sai da Mommah ta fahimci kunya take ji, sannan ta shiga lalla’bata “Haba Shatu, daure ki ba su kowa daga haka ya fara kuma kina ji aka ce hakan yana da matu’kar amfani ga lafiyar su, ko ba kya son su zamo masu kuzari?” Hawaye ne ya fara ambaliya a idanun Shatu, a zuciyarta ta raya yau fa ake yinta! Yanzu ta ya zata iya shayar da su? Wallahi kunya ba zata barta ba. musamman ga Ammar yana zaune ya tasa baby girl ‘din da kallo, ji yake tamkar ya lasheta ko don ganin tana kama da Shatu ne. Mommah ta kalli sashen da take kallo, tace “Au Ammar dama kana nan maza to ka bamu waje.” Yana murmushi ya fice a zuciyarsa yace “Kwana nawa ne zasu zama mallakina a daina yi min rowarsu.”
Yana fita Momma ta zura hannu da kanta ta zaro Maman ta ri’ko Baby ta manna maman a Bakinsa, da sauri Shatu ta runtse ido na tsananin jin kunya. Duk da babu ruwa a ciki sosai haka ya dinga zu’ka tamkar zai cire kan, da alama nan gaba Good sucker za’a yi.

Hajiya Mama dariya tayi ganin yarda Shatu take ta kawar da kai idanunta kuwa a rufe ta kasa bu’de su. “Addarsu da kin bar masa haka, kada ya kwankwa’de ita kuma ya barta, duk da ni zan fi son haka kada ta ture min gwamnati wajen Alhajina.”
Mommah tana murmushi ta mi’kawa Hajiya Mama shi kafin tace “Tun yaushe kuma kina ganin yarinya Balarabiya. Bari Alhajin ya zo ki ji mai zai ce.” Tana ri’ke da ‘yar ta sake ciro ‘daya maman ta manna mata a baki. Wani karan Kuka Shatu ta saka da ita kanta bata san dalilin kukan ba sai dai na fassara shi a na farin ciki.

Sun dai sha abinda suka sha amma ba don sun ‘koshi ba, hakan yasa da Ammar ya shigo Momma tace yaje ya tambayo Doctor ko za’a iya basu madara? Take Doctorn ya rubuta musu madarar da za’a iya basu mai kyau ta S.M.A ya siyo musu carton guda a pharmacy ‘din asibitin, sai da aka dama musu suka sha sannan suka samu barci mai nauyi ya ‘daukesu. Shatu kuwa tsananin yunwa take jin musamman jin cikinta yayi fa yau.



Sai dare Dahda ya koma gida. Da azama Zainab ta tare shi cikin kwalliya ta gani a yaba. Ga ‘kamshin humra da ta sha surkulle kala-kala da ta ba’de jikinta da ita. Ba yabo ba fallasa ya amsa gaisuwar da take masa, da
Azama kuma ta rungumeshi tsaf a ‘ko’karinta na son ya sha’ki sihirtacciyar humrar.

Abin mamaki Dahda janyeta yayi gefe, tabbacin sa’kon nata bai isa in da take so yaje ba. Fuskarsa a ha’de tamau ya shige ‘daki.

Zainab ji tayi kamar ta ‘dora hannu a kai tayi ta zunduma ihu, ta rasa wani irin mutum ne Dahda da duk ‘karfin asiri baya cinsa, duk da ta sani abin a bayyane yake Dahda baya wasa da ibada musamman sallolin dare da azimin litinin da alhamis, sallahr walaha da azkar na safe da yamma duk basa wuce shi. Sannan duk sanda zai yi barci sai ya karanta suratul mulk da suratul kafirun bayan azkar ‘din barci. Amma duk ta jingine hakan ta ‘dora laifin akan Mommah Dijah baiwar Allah gani take sihirin da take masa ne yafi nata ‘karfi.
Hawayen idonta ta ‘dauke tana tunanin Shikkenan ita kuma ta tabbata mara nasara a rayuwa, Dijah ce kullum take rinjaye a kanta. Abin ba’kin ciki haihuwar da Shatu tayi yau na ‘yan biyu, ita tata ‘yar bata jin ko ‘batan wata ta ta’ba yi.

Kamar an zungureta ta zaro wayarta ta shiga dannan kiran Shaheedah, ji take idan bata sauke duk wani takaicin ta akan ta ba yau ba zata samu salama a zuciyarta ba.

Shaheedah da ta ji kiran daga sama, a zabure Ta ‘dau wayar gabanta yana sake duka, don tun da aka sanar da ita haihuwar ta rasa sukunin zuciya. Ganin Antynta ce ta ‘daga a sanyaye. Kawai kuka ta saka mata. Zainab tayi tsaki “Ke da halla saurara min ki ji tambayar da zan miki, kina da ciki ko baki da shi?” A shagwa’be tace “Haba Anty Allah ya tsareni da haihuwa yanzu, ban shirya kwararra’bewa ba.” Wani zagi Zainab ta ‘kunduma mata kafin tace “Fahimtar dani ban gane mai kike nufi ba? Zuwa kika yi kika yi tsarin iyali ko me?” “Ni wallahi kwanaki ma na samu cikin ni nace masa bana so muka je muka cire shi.” Zainab ta zabga salati “Shikkenan Shaheedah kin kashe ni amma kuwa ke dai nayi jakar yarinya da babu tunani ko ka’dan a zuciyarki, don ubanki to ga Shatu nan ta haifa masa twins, kin ga ko yanzu ta ci gida, ke sai ki zauna kiyi ta adana jikinki shashashar banza.”
Cikin takaici ta ajiye wayar tana sake tsaki da la’antar shashashancin Shaheedah.

Ita kuwa Shaheedah ta’be baki Tayi, cikin ranta ta ce “To ni ina ruwa na ta haifi duniya ma, ko da na ‘boyewa Imran haihuwar ba don komai bane sai don kada yace lallai sai ya tafi Nigeria yanzu, idan ban da haka ni bana ba’kin cikin ta haifi ‘dari ma.


Zainab kuwa da takaicin ya gama cinta, wanka Ta ‘karawa she’kawa ta sake ambula sihirtacciyar humra, tayi shigarta cikin wata shara-sharan rigar barci ita a dole sai ta ja hankalin Dahda a wannan Daren. Ta fice bayan ta cilla chewingum a bakinta.


Taci sa’a kuwa ta samu ‘kofar a bu’de, cikin farin ciki ta danna kai bedroom muryarta cike da kwainane tayi Sallama. Kamar wata zararriya ta saki zani da hijabin da ta shigo dasu tana jifan Manga da wani shu’umin murmushi, idanununta cikin nasa. Shi kuwa sak yayi yana yi mata kallon mamaki da tunanin ko ta fara samun motsuwar kwanya. Farinciki ya cika zuciyarta a tunaninta kallon tsananin bu’kata yake jifanta da shi. Ganin bai ta’ba tsayawa yayi mata wannan kallon.
Takaici ya gume Dahda, da sauri ya mi’ke idanunta zube Cikin shamulallen ‘kirjinta da kyautatuwa yayi a ‘boyesu saboda rashin kyan ganinsu, ba a bayyana ba. ko Mommah da nata suke cas gwanin sha’awa bata tayyara su haka a fili.

Tsaki ya zabga ganin tana tunkaro shi yayi saurin dakatar da ita da hannunsa fuska a ha’de yace “Saurara am not in the mood, kuma Abuja zan tafi da sassafe na san ai kina da labarin kinyi Jikoki ko?” Ranta ya ‘baci da salon wula’kancinsa, tunda aka yi aurensu bai ta’ba bu’katar ta ba kullum ita take kawo kanta idan bu’katar hakan ta ciyota, murya a sha’ke tace “Tabbas naji labari, amma ina tantama idan jikokin namu ne, kwananta uku da tarewa fa ya saketa, yaushe har ya sadu da ita ta samu ciki.....” “Ke! Dakata bana son sakarcin banza kada ki sake ki sheganta min jikoki, ko kwana ‘daya tayi ya saketa,
Hakan ba yana nufin ba zai kasa tarawa da ita ba, kuma ‘ya’ya na sane don haka kada na sake jin wannan banzar maganar mara kan gado.” Daga haka ya ja duvet ya rufe jikinsa idanunsa a lumshe yace “Idan kin tashi fita pls off the light asuba ta gari.” Tsananin takaici ne ya rufe Zainab bata san sanda ta kai kanta bakin ‘kofa tana takaicin asarar ku’din humra da tayi. (Haka lamarin yake wanda bai ji bari ba zai ji hoho!)




—————

Takwas na safe a cikin asibitin tayi wa Dahda, tuni y kira Ammar ya tambayi ‘dakin da suke, don fushi yake da Mommah ba zai iya kiranta ba, duk da tun jiya yake ganin kiran ta amma yayi burus ya ‘ki ‘Dauka, so yake ya nuna mata abin da tayi ‘din zahiran bai ji da’di ba kuma bata kyauta ba.

Bayan Knocking na minti ‘daya ya tura ‘kofar bakinsa ‘dauke da sallama ya shiga. Momma cikin farinciki ta amsa masa, ya ‘dauke kai kamar bai ganta ba direct ‘bangaren da Hajiya Mama ya isa har ‘kasa ya dur’kusa ya gaisheta. Cikin kunyar surukuta take amsawa tare da yi masa murnar haihuwar da aka yi masa. Ya amsa shima ‘din idanunsa a ‘kasa, yana wasa da hannunsa, ya dubi Shatu da take ‘ko’karin mi’kewa zaune yace “A’a Shatu yi kwanciyarki ke da baki da lafiya.” A kwancen ta saki murmushin kunya ta gaida shi, ya amsa fuskarsa ‘dauke da tausayinta yarinya ‘karama ‘yar shekara sha shidda da haihuwar ‘yan biyu, gani yake kamar lamarin yayi mata girma. A hankali yace “Ya jikin naki?” “Da sau’ki Dahda” ta fa’da murya a sanyaye. Yace Masha Allah” yana kar’bar baby boy ‘din da Mommah take mi’ka masa tana gaisheshi. Ya amsa ba tare da ya kalleta ba. Mamaki ya kama shi ganin yaron a hannunsa yana tuno sanda aka haifi Imran haka yake kwabo da kwabo kamar yayi kaki. “Masha Allah ubangiji ya raya ka. Amma ba kai ya kamata na fara ‘dauka ba amaryata ya kamata na fara ‘dauka.” Ya fa’da yana ajiye shi a makwancinsa, ya ‘dauki Baby Girl ‘din yana bin Hajiya Mama da kallo da ta kama Shatu “Mi’ke maza muje ki tattaka, sun ce ki dinga tattakawa kada wajen yayi tsami.” Daga haka ta kama ta tana takawa a hankali suka fita. Dahda yayi murmushi don ya san hakan wata dabara ce ta dattijan mutane masu nagarta irin dai surukarsa Hajiya Mama. Suna fita Mommah ta kama shi suka zauna, kanta ta ‘dora a kafa’darsa suna kallon babies ‘din tare. Muryarta ta kwantar sosai kafin tace “Yalla’bai am very sorry please naga fushi kake dani sosai, Don Allah ka yafe min, wallahi jiya ko kyakykyawan barci ban yi ba tunda nayi ta kiran wayarka ka’ki ‘dagawa hankalina ya tashi please ka yafe min!” Cikin sauyin muryar da ta san tana narkar da zuciyarsa ta fa’da, tuni kuwa ya lumshe idonsa cikin sake godiya ga rabbi da ya azurta shi da mata ta gari mai amsa laifinta, ba kuma ta girman kai wajen bashi ha’kuri. Cikin wasa ya shafa kumatunta “Na yafe miki Deejah na, da kam nayi fushi sosai tunanina ba ki mayar dani wata tsiya ba, amma yanzu da naga zanka’de’diyar amarya ta duk wani ‘bacin rai ya tafi. An gayawa Imran ni na kira wayarsa bana samun sa I don’t know why?” Mommah wani murmushin takaici tayi kafin tace na gaya masa ga kuma amsar da ya bayar.” Ta mi’ka masa wayar bayan ta bu’de text ‘din da Imran ‘din ya turo. Dahda cikin ‘bacin rai ya ke mi’ka mata wayar cikin fushi yace Allah ya kyauta amma kuwa zai sha mamaki na a lokacin da yazo zaiyi iko da ‘ya’yan nan.” Mommah ta kama hannunsa tana matsawa a hankali tace “Ai ni na riga na yanke hukunci, hukuncin da na tabbata sai ya kusa buga zuciyarsa daga Shatu har ‘ya’yan na mallakawa Ammar rana ita yau za’a ‘daura musu aure......”
[10/2, 7:01 PM] +234 803 800 7509: Me Zan yi da ita?


39



‘Kuri dahda yayi mata ido cike da mamakin furucinta fuskarsa a ‘daure yace “Allah ya sanya alheri.” Ya dire mata yaran a gefe yayi hanyar fita. Da sauri ta sha gabansa ta ri’ke duka hannayensa biyu idanunta cikin nasa race “Dahda Why? Me yasa na hango tamkar ba kayi farin ciki da abinda na yanke ba?” Matsar da fuskarsa yayi gefe, ya ‘ki cewa komai sai jan numfashi yake, tabbas ko a mafarki bai yi zaton Dijansa zata riki’de ta koma haka ba. Zartar da hukunci a duk lokacin da taga dama sa’banin da da sai ta nemi yardarsa Kafin aiwatar da komai. “Please yalla’bai say something mana bana jin da’din wannan fuskar da kake arowa ka sawa kanka.” “Kamar yarda bana jin da’din wannan Dijahn mai yanke hukunci bisa son zuciyarta ba tare da tunani ko tsinkaye ba.” Ya furta fuskarsa na sake tamkewa. Gaba ‘daya ta ha’de hannunta ta dun’kule kafin tace “Am sorry ba nufina zartar da hukunci ba, da ma yanzun ma shawararka na nema kuma duk abinda kace dashi za’a yi aiki, don haka please zauna, ka kwantar da hankalinka ina nan a Dijanka ta da mai bin umarninka cikin son rai ko akasin haka.” Ya zauna ‘din kamar yarda ta bu’kata, sai dai bai saki fuskar ba yace “Me yasa tunaninki ya baki wannan abin da zaki ha’da ya dace? Ban hana Ammar auren Shatu ba amma not now it’s too early ki sake aurar da Aysha, Na zata ko wani kika ga zai aurar da ita a yanzu sai inda ‘kardinki ya ‘kare wajen ganin kin hana shi sai gashi da kanki kike son aurar da ita sati guda kacal da haihuwa tamkar kina neman kai da ita. Bance lallai sai kin mayarwa da Imran ita ba, ko ka’dan bai cancanta da Shatu ba tunda baya sonta kada a koma ‘yar gidan jiya, Amman ‘din ya dace da ita amma shima ba yanzu ba sai ta goge ta yi karatu ta yarda zata iya fafatawa da kowace matsala a rayuwar aure, ta kuma solver ta ba tare da ta tunkari wani da zancen ba. Da C.s a jikinta sati guda ko gama farfa’dowa ba tayi ba taji za’a yi mata aure, ai sai ki jefa zargi a zuciyarta, ta zata kin fi son farin cikin ‘ya’yanki fiye da nata marainiya. Don haka ki sake tunani.”

Mommah tayi shiru tana gasgata zantuttukan Dahda a zuciyarta, tabbas zancensa dutse zata iya kam jefa tunani a zuciyar Shatu Allah ya sota Dahda ya ankarar da ita kuskuren da taso tafkawa. Da sauri ta dinga yi masa godiya,
Dahda murmushi yayi kawai ya ja hancinta “Sarauniyar ‘yan gaggawa, ki ri’ke a kanki duk mai gaggawa yana cikin aikin dana sani kullu yaumin, kina girma tunaninki na yara. Bari in yi sauri in tafi kada Hajiya Mama taga rashin hankali na na san saboda ni ta fita.” Mommah murmushi kawai tayi tana masa rakiya zuwa ba’kin ‘kofa.


Koda Hajiya Mama ta Shigo, Mommah tayi mata bayani akan maganar da suka yi da Dahda. Hajiya Mama murmushi tayi kafin tace “Nagode Allah da ya fahimtar dake kika gane, Allah ya nuna mana lokacin, ya ha’da kawunansu” Mommah ta amsa da ameen. Yayin da Shatu ta lumshe ido, zuciyarta na dakan uku-uku tunani take yi a zuciyarta, shin da gaske ne zancen auren ta ake yi da Ammar, hawaye ne yake shirin fito mata zuciyarta cike da fargaba tace wannan fa shine ana wata ga wata, tabbas ba za ta iya yiwa ammar butulci ba, mutumin da ya tsaya mata tsayin daka yake nuna mata ‘kauna ta fisabilillah. Idan ban da haka sam bata da burin sake aure anan kusa ta fiso ta zurfafa iliminta, bata sa a ranta ko nan da shekaru goma zata sake aure ba, da so samu ne da sai ta rufa shekaru talatin cif, amma kana taka Allah na tasa ga yarda lamarin ubangiji ya juya, ba zata iya bijerewa muradin Momma ba na aure Ammar.


——————————-
Kwanan su hu’du aka sallamesu, cike da ‘koshin lafiya yara sai ‘kara kyau sukeyi kamar ka suresu ka sace. Kaf dangin Imran babu wanda yayi waya yayi barka, balle Allah ya raya, abinda ya hassala zuciyar Mommah, musamman Imran ‘din da bai sake kiran ta a waya ba, hakan yass cikin fushi tayi blocking ‘dinsa a wayarta, da wayoyoyin su Hajiya Mama.

A ranar kuma su Nahna da Hafsa jirginsu ya dirga Nigeria sun zo hutu. Zuciyarsu fal da farin cikin ‘karuwar da suka samu. Har rige-rigen shiga gidan suke. Suka ‘dauki yaran suna sakin Murmushi, su ‘dinma bayan sun ci abinci suka tambayeta Imran ya sani? Take Mimmah ta basu amsa ta kuma sanar dasu cin mutuncin da ya turo, “Don haka ina ro’kon ku kuma kuyi blocking ‘dinsa in dai na isa daku. Cikin matu’kar jinjina girman lamarin suka dinga jajantawa da fa’din bai kyauta ba. A take kuma suka cikawa Mommah burinta na blocking ‘dinsa.

Ammar ya fahimci Dahda bayan yayi masa bayani, ya amince tabbas Shatu yanzu tana bu’katar nutsuwa, da kula da yaranta sannnan da gamsashshen ilimi, hakan yasa dole ya fara shirin kokawarsa Qatar, yanda yake kasuwancinsa. Bayan ya bu’dewa Shatu account, ya samar mata makarantar da zata zana waec


Ranar suna da kansa ya ro’ki Dahda da Alhaji Baba akan cewa a saka sunan iyayen Shatu. Maryama da Mujittaba haka kuwa aka yi, har ila yau da kansa yayi musu inkiya da Ikram da Akram.


——————
A daren ranar da zai tafi ya shiga bedroom ‘din Shatu don suyi sallama ya kuma fallasa mata sirrin zuciyarsa.

Yaci sa’a kuwa Ba kowa sai ita ka’dai Ikram da Akaram suna wajen
Mommah dama shan Nono ne yake ha’da ta dasu saboda matu’kar kunyar su take ji.


Kasancewar sanyi ake bedroom ‘din ya ‘dau ‘dumin heater sosai, Shatu na zaune ta sha wanka sai zabga ‘kamshi take. Kallo take a t.v taji sallamarsa da sha’kar dadda’dan turarensa na companyn lulu. Yayi dressing mai matu’kar burgewa, shi dama ya fi saka ‘kananan kaya sa’banin Imran da ya fi son African Attire. Idanunsa a cikin nata ya isa side bed drawer ya zauna. Gaban Shatu ne ya dinga bugawa ras-ras wanda da mutum zai zuba ido zai hango yarda yake ‘dagawa. Tsoro take ji sosai bata son ya furta abinda yake ransa, don ba zata iya musa masa zata ji matu’kar kunya.

Yana murmushi yake amsa gaisuwarta, tana yi tana wasa da yatsun hannnunta, idanunta a ‘kasa. Cikin wata irin murya yace “Shatun Mommah ya jikin?” “Da sau’ki” ta furta bakinta ne kawai ya motsa ban da haka da ba zai ji muryarta Ba.

Ya ja fasali kafin yace “kin san abinda ya kawo ni?” Tayi saurin girgiza kai bugun zuciyarta na ‘karuwa. “ yauwa ina son ki gaya min gaskiya Idan kin amince to Idan ma baki amince ba duk ina son ji, kin yarda?” Da sauri ta ‘daga kai, cikin zullumi da abinda zai fito daga bakinsa. “Shatu so nake na maye gurnin Yaya na idan kin amince, duk da dai ba yanzu za’ayi ba, amma dai hausawa na cewa a bari ya huce shi yake kawo rabon wani, zan tafi Qatar yau jirgin dare zan bi, mai kika ce kin Amince?” Da sauri ta ‘daga kai bayan ta runtse idanunta tana ji zuciyarta na wani irin bugu. Hawaye yana son zubo mata tayi saurin mayar dasu. Ya zama dole duk soyayyar da take yiwa Imran ta mayar dashi akan Ammar ko don ta saka halacci da halacci. Murmushi ya saki a hankali yace “Alhamdulillah nagode sosai, yau kuma na san zanyi kwanan farin cikin samun amsarki, buri na ya cika.” Ya zaro waya a aljihunsa sabuwa ‘kal ‘kirar Iphone 12 ya fara nuna mata yarda za tayi amfani da ita. Sannan ya ciro atm card ya bata “Na saka miki ku’di a ciki ina yi miki addu’ar samun nasara a karatunki and I really love you.” Da sauri ta rufe idanunta tana sake jaddada masa kalaman godiya.

Tana gani ya fice suna waving juna, ji yake tamkar ya dawo ya rungumeta. Yana tunanin yarda zai jure tsawon lokaci bai ganta ba.




———After One year( Bayan shekara ‘daya.......)



Cikin shekarar al’amura da dama sun faru wasu masu da’di wasu akasin haka.
Cikin masu da’din har da fara karatun Shatu a jami’a, da gogewarta sosai ta zama ‘yar gayu ta bugawa a jarida, duk inda ta wuce dole idanuwa su bi kanta. Fatarta ta murje sosai kamar larabawan Habasha ga diri cikakken hips da tsukakken ciki, uwa uba cikowar mamanta da suke cas dasu a cikin Riga. Hatta da idanunsa sun ‘kara haske tamkar madara.


Har wannan lokacin Imran bai zo ba, saboda al’amura sun caku’de masa, yana yawan kiran Wayoyinsu baya samunsu. Sai dai ya kira maigadi ya ce ya kaiwa Mommah. Sosai take receiving sai dai ko sau ‘daya bai ta’ba tambayar ‘ya’yansa da bai san da su ba. Haka nan ita ma bata ta’ba cewa mai yasa bai tambayesu ba. Addu’a ce dai bata fasa yin ta ba.


Sosai tunanin Shatu ya bun’kasa a zuciyarsa, wata irin soyayyarta ce mai zafi take huda dukka sassan jikinsa, burinsa ya gan ta, sai dai yana jin kunyar tunkarar Mommah da zancen, ya san abin da kunya. Don haka yake dauriyar shanye abin a cikin ransa. Yana niyyar ya samu hutu yaje yayi ya’ki a bashi matarsa.

Tuni asirin ya fara barin jikin sa an kai tajallin da yake zama ya dinga tuna moment ‘dinsu da Shatu.
Wani al’amari da Ba zai iya mantawa da shi ba. Zuciyarsa tana jin zafin sakin da yayi mata, ashe zai zo yayi da na sani, ashe da wannan halin da yake ciki har gwara ace ya zauna da ita yaji kunyar abokannasa, da duk wanda ma zai masa dariya.



——————-

Gabatowar bikin su Hafsa da Nahna ne ya sa Ammar dawowa Nigeria, don ya ro’ki alfarmar a ha’da da na shi da na Shatu.

Ranar da ya iso ya samu Mommah da maganar, tayi na’am da maganar sai dai tana tsoron zartar da hukunci kai tsaye tace ya bari zata samu Dahda da umarninsa zata yi aiki.


Da daddare kuwa ta Samu Dahda da zancen, ya dubi kyawawan jikokinsa da suke gefensa suna wasa tamkar ba ‘yan shekara ‘daya Ba, sun yi girma na ban mamaki kamar Akram ta sake bayyana sosai da mahaifinsa, haka nan macen da Shatu take kama sak da sak. Dudubniyarsu suke akan kakannasu da ‘ko’karin son ‘kwace alawar da yake ba su. Tunani ya shiga yi sosai kusan duk burin Shatu yanzu ya cika yarannan kuma dama bata saba dasu ba Mommah ce take hidima da su, ko anyi auren kuma Ba bata su za’ayi ba. Ga shi ta fara karatunta, tunda bikin su Hafsan sai nan da wata biyu zai iya amincewa ayi. Musamman da na Hisham za’a ha’da, shi yin wancan da yake ta dakon dawowarsa bai dawo ba balle ayi tunanin kome. Don haka direct yace “Shikkenan yayi shirye-shiryennasa ayi bikin dashi amma anan zai barta sai ta gama school.”
Farin ciki ya cika zuciyar Mommah burinta a karo na biyu zai cika. Da murna ta fita ta sanar da Ammar amincewar Dahdan.


Ammar yayi murna da farin cikin da har ba zan iya fasalta muku shi Ba. Yayi sujudusshukur ha’de da sake godiya ga Mommah sannan da sauri ya nufi ‘dakin Shatu.



—————————
Jirgin ‘karfe 8:00 na dare ne ya sauke su Hisham a airport. Ya kira wayar Imran ya sanar masa ya zo ya ‘dauke shi.

Farin ciki ya cika zuciyar Imran na ganin Hisham ya san ba mamaki ‘karshen matsalolinsa sun zo.

Tun a hanya Hisham yake son tambayar sa ko ya san da haihuwar yaransa amma ya kasa zuwa ya gansu tsawon shekara guda? Sai dai yaja bakinsa yayi shiru tunda Mommah

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment