Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wallahi, saboda haka ni yanzu ba ya gaba na yaje ya cigaba da matar so har gaban abada.” Dahda ya saki ajiyar zuciya “A daiyi ha’kuri kada ayi masa baki idan rai ya ‘baci ba’a sob hankali ya gushe Dija na. Amma ya aka yi kika san bai kawar mata da budurci ba kin tambayeta ne?” Momma ta girgiza kai “kwananta nawa a gidan uku fa dama Dahda tace ko kallon arziki bai yi musu ba, yarda ya tsaneta bana jin zata tsole masa idon da har zai aikata wani abin da ita, ba ma zan tambayeta ba balle na sa ta jin kunya ‘karshenta ma bata san abinda zan tambaya d’in ba inje in bud’e mata wani sirrin da ya girmi kwanyar kanta in jefa mata tunani da ‘kananan shekarunta.” Dahda ya girgiza Kai “kafin yace Ai shikkenan zan dai cigaba da kiransa har zuwa sanda zan sameshi ban san inda ya tafi bane.” Momma ta ta’be baki kawai ba tace komai ba.

Dada tsohuwa tana fitowa daga d’akin da take taga Shatu zaune da su Hafsa. Baki ta kama tana taunar goro kafin tace “Muhammdu d’an Abdallah mai zan gani haka ke kuma wa yace ki fito wirjanjan haka ko yunwar ya sake barinki da ita?” “Cab Dada ai gwara yunwa akan abinda yayi mata sakinta fa yayi.” Momma ta fad’a tana fitowa daga bedroom d’inta. Sai gani su kayi Dada ta zauna da’bas akan kujera “menene saki? ko dad’in ji babu ke dai wallahi Dijah kiyi ta instingifari don bakinki ba ya fad’ar Alheri sai sharri, sharrin ma Ki rasa wa zaki yiwa sai d’anki Na cikinki auzubillahi wallahi uwarki bata yi sa’ar haihuwarki ba.” Mommah cikin takaici ta shige d’aki, tana ji Nahna na sake tabbatarwa da Dada sakin. Ji tayi ta saki kuka tana fad’in “Wallahi Dijah kin haifi tanbad’adde tunda muke a danginmu ba’a ta’ba bazawara ba sai yanzu...”.


Zainab Amarya da sauri ta sallame sallahr, ta d’au wayarta da take ta faman ringing, kamar yarda tayi hasashe kuwa Shuwa ce. Don haka cikin azama ta saka wayar a kunne tace “ke kuwa Shuwa ina kika shiga? Tun safe nake nemanki da daddad’an labari saki dai ya tabbata.” Shuwa tace “ Kai har naji dad’i, hankalina ya kwanta. Sai dai fa da wata a ‘kasa don kuwa yanzu daga wajen sa nake ya bani wani magani yace lallai a saka masa a abinci, shine ‘kiyayyarta zata dawwamawa zuciyarsa idan ba haka ba nan da lokaci kad’an komai zai iya canjawa kuma yauyau ake son a saka masa kafin wancan na jikinsa ya sake shi. Don haka ga maganin yanzu zan taho dashi.” Anty Amarya ta zaro ido “Yau kuma Shuwa ba sa fa gari, ya za’a yi yanzu?” Shuwa ta zaro ido “ki aika mata mana sai ta tura tasha a kar’ba” Zainab tace “kin san ina kuwa suka tafi? Turkey fa.” Wayar da take hannun Shuwa ce ta fad’i cikin tashin hankali tace “Wallahi to zainab akwai gagarumar matsala matu’kar wancan maganin ya sakeshi kiyi sauri ki kirata idan jirginsu bai d’aga ba ta san yarda tayi ta hana tafiyar a yau har sai ta amshi maganinnan..” zainab hannunta na rawa ta shiga danna kiran Shaheedah....

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-30


Elegant Online Writers......

Cikin hukuncin ubangiji bugu d’aya wayar ta shiga, Shaheeda tayi saurin picking call tamkar jira take dama a kira. Anty Amarya ta saki ajiyar zuciya. Shaheeda da hannunta yake sar’ke da na Imran taji Antynta tace “Hello Shaheedah ki san yarda kika yi kika ruguza tafiyar nan dan akwai babbar matsala, auren dai ya mutu amma komai zai iya faruwa Idan ba kiyi amfani da wannan maganin da Shuwa ta kawo yanzu ba.” Shaheedah da ta saki baki cikin tsananin razana tace “Ai muna cikin jirgi har mun d’aura belt, ina shirin switching wayar Off fa kika kira ni.” Zainab tace “shikkenan Shuwa kin ji sun tafi.” Shuwa ta dafe kai, sun jima zaune cikin hali na tashin hankali, kafin Shuwa ta saki ajiyar zuciya ta dubi Zainab tana mi’kewa “Shikkenan ni bari na wuce zama bai ganni ba, tunani na d’aya shiga kwazazzabonnan sam hanyar bata da kyau, shima nace masa yayi ‘ko’kari ya samu waya yace min wani baya bu’kata, yana da babbar hanyar sadarwa daga aljannu. Kema kiyi ‘ko’kari ki san hanya da kanki ki dinga zuwa kin bi kin li’ke a gida uwa a kanki aka fara aure, daga anyi magana kice kina shakkar mijinki tattabara uwar aure. Kin zauna kamar wata sokuwa har yau kin kasa kame miji.” Anty Amarya jiki a sanyaye tace “Ke dai kiyi ha’kuri Shuwa Manga waccar matar ta riga ta shanye zuciyarsa tsaf, wallahi duk asirina ta fini, don duk zaman da nayi a gidannan da asirce-asircen da nake baya tasiri a zuciyar manga, kallon arziki wannan ba yi min shi yake ba,a wajen danginmu kad’ai nake samun sau’ki don Hajja da kanta ma bani abu take tace na zuba masa a abinci, don mu had’u muyi maganin makira Dijah,amma wallahi kamar ‘kara masa ‘kaunarta ma nake yi.” Shuwa tayi tsaki “ Dai na ga ya min kayan haushi don Allah da kinje kin yiwa mutumin can bayani ai da ba haka ba, kin zauna kina jira na inyi hidimarki in yi Ta ‘yarki, shi yasa sam ni ban yarda da lamarin zaman aure ba a wani kulle ka a gida sai san da a kaso zaka fita. Idan zaki tashi tsaye ki tashi idan kuwa ba haka ba kina ji kina gani burinki zai bi iska.” Daga haka ta fice kamar guguwa ta tafi. Duk takaicin zainab na cika ta shi ys sam bata so tayi wannan auren na jaraba ba, da tun tana yarinya ta ‘kidirce sai ta auri Manga shi yasa ma ta taimaka mata, don sosai take ji da ita ta d’auketa tamkar uwa d’aya uba d’aya suke.


Ita kuwa Shaheedah tana cikin jirgi abin duniya ya isheta, tunaninta mai zaije ya dawo. Burinta na farko dai ya cika da taji an saki Shatu. Amma fargabar ta d’aya yarda lamarin zai juya, duk da ba ta haufi a al’amarin Shuwa ta san tabbas zata taimaka mata. Ta sake kwantar da kanta a kafad’ar Imran, da har I zuwa lokacin ya kasa walwala fuskar sa a had’e take kamar hadarin kaji. Ji yake kamar bai kyauta ba kamar Allah zai tambayeshi akan tsakaninsa da Mommah. Ya lumshe ido sakamakon wata ‘yar ‘kwalla da ta tarar masa. Yana ji jirgin ya lula dasu sararin samaniya alamar ya daidaita. Zuciyar Imran tayi nauyi, har wani bugu take na tashin hankali. Fatansa da burinsa Allah ya huci zuciyar Mommah, amma fa sam bai yi dana sanin sakin Shatu da yayi ba. Zuciyarsa ce ma take ‘karfafarsa akan hakan da yayi shine abinda ya dace.



—————————-
Shatu a kwance kan Gadon ta na ainahi na gidansu, idanunta kulle kamar mai barci sai dai ba barcin take ba, sa’banin haka tunani ne ya cika zuciyarta fal, tunanin Imran da moment d’in da suka yi spending a first Night d’insu na daren jiya, shine abinda ya hana ta sukuni, ya kuma yi tsaye a zuciyarta kamar me. Da zarar ta lumshe ido hakan take gani. Imran dai Imran dai, kunnuwanta kuwa sun kasa toshewa da jiyo tarin za’ka’kan kalaman da yake furta mata a kunnuwanta cikin zallar so da alfahari da kasancewarta matarsa. Ashe hakan duk sun wani salon yaudara ne na maza da suke aiwatar wa idan suna bu’katar matansu, tabbas Imran ya bar mata tabon da ba zai ta’ba gogewa ba, ya d’arsa mata ‘kaunarsa a zuciyarta ta yarda ko nan gaba bata jin zata samu wanda zai maye gurbin tarin ‘kaunarsa a cikin ran Ta. Ya cuce ta tun daga ran da ta samu kanta a matsayin matarsa take jin dad’i da farincikin samun miji kamar sa. Ashe lamarin zai zama tamkar dangwaliliya ne a wajenta. Ta share ‘yar guntuwar ‘kwallar da ta taru a saman idonta, kafin ta mi’ke ta shige toilet, gwara tayi alwala ta fuskanci rabbil hikimati ko zai yaye mata damuwarta.


Da safe tsaf ta tashi, ‘kasanta ma da yake mata ciwo tuni ta nemi ciwon ta rasa, ras take jin kanta duk Wani ‘bacin rai ma ya gushe daga ‘kirjinta har wani annashuwa da walwala ne suka ‘karar mata. Wannan yana daga cikin sirrin ‘kiyamallaili in dai zaka lazimci yin ta to fa cikin hikimar ubangiji kun yi hannun riga da ‘bacin rai. Allah ka bamu iko. Tayi shirin ta tsaf cikin uniform d’in ta tana ji a yanzu ne za ta d’aura d’amarar karatu. Sai ta bawa Imran mamaki da yake mata kallon bagidajiya.

A kitchen ta tarar da Mommah tana aiki, ta baya ta rungume Mommah cike da Nishad’i take furta. “Morning sweety” cikin farin ciki Mommah ta rungumeta ita ma, ta ji dad’i sosai da yarda Shatu ta saki jikinta, itace dai ko barci ba ta samu ta rintsa ba, saboda tunanin da yayi mata dabaibayi.
Hannunta akan Shatu tana shafawa tace “Masha Allah daughter na, hope everything is alright?” Shatu ta d’aga kai tana kar’bar wu’kar da Mommah take yanka cake da ta gasa mata a oven. Saboda ita tayi wannan sammakon idan ban da haka ba itace da girki ba. ba abinda zai fito da ita da Asuba haka. Suna aiki Mommah tana sake yi mata nasiha a fakaice “Ki dage da karatu kin ji daughter na both ilimi nake nufi boko da islamiyya, ina so kuma ki ajiye wauta da shiririta you are now a matured ki zama ‘yar gayun da za’a dinga kwatance dake, kin ji?” Shatu ta d’aga kai, alamar amsawa duk da dama ko Mommah bata fad’a ba ta ci burin hakan a cikin ranta. So take ta zama so silent irin mutanennan da magana ma sai a dole suke yin ta. Wanda dai ake kira masu aji.

Tana zaune a dinning tana break-fast, Ammar ya shigo fuskarsa da alamun rashin walwala a tare dashi. Tun jiya da Dahda ya sanar dashi ko runtsawa bai yi ba tunaninsa d’aya da ya tsaya masa, shine mai ya shiga yan yayannasa? Da yake son saka mahaifiyarsu a matsala, kullum ba shi da buri sai saka mata ‘bacin rai, sai ya jawo mata wani ciwon ya cucesu. Da wannan tunanin ya shigo don a jiyan bai samu ganin Mommahn ba, ba zai iya ba tasirin da tausayinta yayi a cikin ransa mai girma ne, don ya dad’e bai samu abinda yasa shi zubar da hawaye ba sai jiyan da ya riski wannan ba’kin labarin.
Shatu cikin fara’a ta d’ago tana kallonsa, kafin tace “ Yaya Ammar ina kwana?” Murmushin ‘karfin hali ya sakar mata sannan yace “lafiya Shatu, irin wannan loda abinci haka ina zaki kai shi?” Murmushi ta sakar masa tana nuna cikinta. Ya gyad’a kai “maza kije ki zama lutiya, wallahi ba kyau za kiyi ba.” Ya zauna gefen Mommah yana gaisheta, hankalinsa ya kwanta ganin Shatun Ta saki ranta. Mommah ta amsa masa cike da kulawa “Yaushe ka dawo daga kadunan? Don jiya har na kwanta baka shigo ba, hope tafiya tayi nasara an samu abinda aka je nema?” Murmushi ya sakar mata “Wallahi Mommah Alhamdulillah” yayi saurin fad’a yana mi’kewa “Bari na sauketa a school na dawo.” Mommah ta bi bayansu da kallo, tana ji da ta sani ma da Ammar ta had’a Shatun ta san da zai yi mata kyakkyawan ri’ko. Ba ka tara sani ga Allah, sannan lamarin ubangiji ya wuce nan ba mamaki shine dalilin da yasa bai sanya mata wannan tunaninba sai yanzu da lokaci ya riga ya shige.

Sai da ya sauketa a school ya sake dawowa wajen Mommah, so yake ya taushi zuciyarta sannan ya sanar da ita abinda ya kwana dashi a zuciyarsa. Har sannan Mommah tana saka turaren wuta a sashennata da yake ta bad’a ‘kamshin turare da ‘kamshin Girki kasancewar Mommahn ‘kwararriyar chef ce ta ainahi kuma karatun da tayi kenan. Ya zauna yana had’a tea. Mommahn ma sai da ta ‘karasa sannan ta dawo ta zauna kusa da kujerar da yake a saman dinning d’in. “Gwara da ka dawo dama ina son nace ka yiwa su Nahna booking flight na Abuja, har Dada ma tun jiya take tijarar ba zata zauna gidansu Imran ba tunda ba shi da zuciyar musulunci. Kuka fa ta dinga yi a gidannan.”
Ammar ya tsayar da zuba peppe soup d’in da yake yi, yace “Mommah ai bai kyauta ba wallahi nima Dahda da ya fad’a min kasa barci nayi wallahi, na ji zafin abin sosai a raina.” Momma ta saki ajiyar zuciya kafin tace “ai lamarin Hammanka sai addu’a, Allah ya shiryeshi.” Ta fad’a tana ‘ko’karin kawar da ‘bacin ran da yake son dabaibayarta. Ammar ya ajiye cokalin yana fuskantar ta, cikin muryar lallashi da ‘ko’karin kwantar mata da hankali yace “Addu’ar da za muyi tayi masa Kenan, ki kuma cire abin a ranki kada damuwa ta kama mana ke, sannan insha Allah ni zan share miki hawaye idan Shatu ta gama karatu zan maye gurbin Ya Imran.” Wani farin ciki ya ziyarci zuciyar Mommah cikin murmushi take cewa “Idan kayi min haka Imran ka share min ba’kin ciki Allah yayi maka albarka ya nuna mana lokacin.” Shima yana murmushin ya mi’ke, ko yanzu burinsa ya cika da yaga murmushin farin ciki a fuskar Mommah. Ya bata side hug ya fice. Bin shi tayi da kallo tana tuno Imran d’inta na da mai son farin cikinta da walwalarta amma gaba d’aya ya juye mata tamkar an canza mata zuciyarsa.

‘Karfe 5:00 dai-dai Na asuba jirgin mutanen turkey yayi landing a yotel air international airport. Istanbul suka Isa, dama tuni yayi musu booking a five star hotel. Suna zuwa motar da zata d’aukesu zuwa hotel d’in ta iso. Gaba d’aya Shaheedah Ta ru’kun’kumeshi saboda sanyin da taji yana ratsa mata ga’bo’bin jikinta. Har suka isa zuciyar Imran a cunkushe take ji yake tamkarma ya koma Nigeria.

Suna shiga apartment d’in da ya kama a hotel d’in, toilet kawai ya shiga, burinsa kawai ya watsa ruwa yayi wanka yayi sallah. Har ya fito ya tarar da Shaheedah zaune ta zabga tagumi, sai ya ji tausayinta ya kama shi don tunda suka taho bai bi ta kanta ba. ya zauna a gefenta, cikin cunkushasshiyat murya yace “kije kiyi wanka madam.” Ta saki ajiyar zuciya tana mi’kewa, ko bakomai yanzu hankalinta ya d’an kwanta da taji yayi mata magana cikin Kulawa.
Har ya shafa mai ya zira kaya, bata fito ba hakan yasa ya zauna a gefen gado yana jiran ta fito suyi jam’i. Wayar Shaheedan ya bud’e da yake ya san password d’inta. Kamar jira ake text d’in Anty nta ya shigo “Shaheedah ki saurare ni da kyau.....,,,”

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-31

Elegant Online Writers.....

Tsaki kawai ya ja, yayi keeping wayar a side, ba ya son duba sirrin mutum sam, hakan ba d’abiarsa bace. Yana zaune har ta gama shiryawa kafin ya mi’ke su tada jam’in sallar.


——————————-
Bayan wata uku..

Kafin nan abububuwa sun fara da dama, wasu masa dad’i wasu sa’banin hakan. Shatu ta koma school kuma sosai ta mayar da hankalinta akan karatunta, gayu kam iya gayu yanzu Shatu ta zama ‘yar gayu bugawa a jarida. Momma ta mayar da ita classic baby, koman ta mai tsada ake siya mata kayan cosmetics da kayan sawa duka masu tsada sosai take using. Girki ma Mommah ta dage sosai waken koya mata, tana kuma dagewa sosai da yake ta saka abin a ranta. Tuni suka manta da Batun Imran, da tun bayan tafiyarsa ya kasa kiran Mommahn, sau tari yana son kiranta sai dai yana tsoron fad’anta. Hakan yasa sai dai yawan turo mata text messages akai-akai, ita kuma ko ta karanta bata bashi amsa.wani lokacin ma ba ta karantawa take barinsa.

A yanzu kam Imran suna yawan samun sa’bani da Shaheeda, don haka kawai wata rana sai yaji ya tsaneta baya ko san ganinta. Wata rana kuma sai yaji ba wacce zai iya so bayanta. Sau tari tunanin Shatu yana damun zuciyarsa, har yaji ya d’okantu da son ganinta, amma kuma sai yaji take ya ‘kara tsanarta. Don haka Shaheedah suka ‘kara dagewa duk da ba su samu wanda zai kai mata sa’kon ba, suna matu’kar ‘ko’kari wajen kawar da hankalinsa, ko da na lokaci kad’an ne. Suka kuma kawar da hankalinsa daga tunanin zuwa Nigeria yaji sam ya tsani zuwa Nigerian sosai kuwa, lamarin dai sai addu’a.


Gefe d’aya Ammar yana ta dakon jiran lokacin da Shatu zata gama idda don ya bayyana mata abinda yake ransa, ya kuma kafa kansa a zuciyarta. Duk da Mommah tace ya bari ta gama karatu amma yarda soyayyarta tayi ‘karfi a zuciyarta baya zaton zai iya hakan. Don haka duk san da yayi tafiya tsarabarta daban take daga kayan sawa har kayan makeup ya d’aukewa Mommah su shi yake yi mata, har waya ya siyo mata Iphone 13 ya kuma koya mata yarda ake amfani da ita. Zuwa lokacin yana ta lissafi ta gama iddar ya fayyace mata sirrin zuciyarsa.


Yauma da wuri ta dawo daga Islamiyya saboda ciwon mara da ya addabeta. Tana shigowa direct bedroom d’inta ta wuce ta cire uniform ta fad’a toilet. Kamar yarda tayi hasashe period d’inta ne yazo wanda daga shi ta gama idda. Bayan tayi wanka ta kintsa kan ta sannan ta fice parlour.

A kitchen Ta samu Mommah, sakwara take da mitar egusi, gefe d’aya baseerah mai aiki tana wanke kwanu kan daga aka ‘bata. A sanyaye ta shiga kitchen d’in ta zauna a d’aya daga cikin kujerun da suke working space na kichen d’in. Mommah cikin kulawa ta kai kallonta kanta tana murmushi “Ya aka yi lazyn Mommah gajiya ko yunwa? Don na san yanzu kin zama acici.” Mommah ta fad’a tana murmushi. Basirah tayi dariya tace “Wallahi kuwa Mommah har cikin dare fa tashi take cin abinci.” Mommah tace “Mhmn basira rabu da ita ai gashi nan sai uwar ‘kiba take ta bud’e ko ta ina girmanta ya wuce shekarunta, yanzu fa idan tace shekarunta sha takwas ba sha biyar ba ba wanda ba zai yarda ba, yarinya ta zama uwar mata, wallahi ki rage cin nan, duk halittunki sun bud’e.” Shatu ta turo baki kamar za tayi kuka, ta hau buga ‘kafa tana kallon Basirah da take mata dariya. Cikin muryar shagwa’ba tace “Mommah wallahi kiyi mata magana ba ta fini ‘kiba bama ni fa ba ‘kiba nake ba cinyoyina ne suke ‘kara girma don duk wanduna na sun yi min kad’an, sai kuma riguna na daga ‘kirji wallahi duk sun matse ni.” Mommah tayi dariya tace “Ai dama ba ‘kiba kike ba bud’ewarce take bani mamaki, sai dai na godewa Allah da ya bani yarinya mai cikakken diri son kowa ‘kin wanda ya rasa masha Allah.” Shatu tana murmushi tace “Amma to me yasa Ya Imran ba ya so na?” Tuni annurin fuskar Mommah ya ‘bace ‘bat, sai kuma ta kalli Shatu tace “Ya period ya zo kuwa don a lissafina yau ko gobe ne.” Shatu ta d’aga kai “Wallahi yazo shine abinda yasa ma na gudo gida da wuri, wannan zuwan ma sai da na samu pain.” Mommah tace “Allah yasa kin gama a sa’a ubangiji ya tsare min mutuncinki ‘yar albarka.” Shatu tace “Ameen” jikinta a sanyaye.



A tsawon sati d’aya Shatu ta sake bud’ewa lamarin da ya dinga bawa Mommah mamaki ga cin abinci babu iyaka, har Mommah ta fara tunanin ko ba ‘kalau ba. Ta kuma yi jajir da ita kamar ka dangwali fatarta jini ya fito, ga she’ki da shinning da take abin sai dai ace tubarakallah. Sam Mommah bata kawo komaiba a ranta tafi danganta hakan da kwanciyar hankalin da Shatun Ta samu da mayukan da take using masu tsada.

Yau aka yi musu hutu, aka kuma yi speech and price giving day, Shatu ta fita zakka a cikin classmates d’inta, don tayi ‘ko’kari sosai duk da tafi ‘yan ajin girma, hakan yasa principal tace zata iya joining ‘yan S.S one tunda yanzu ba karatun da bata ganewa. Zata karanta kuma zata fahimta, sai a samar mata lesson teacher da zai dinga sake koya mata a gida. Mommah taji dad’i sosai har farin cikinta ya kasa ‘boyuwa, tana hasashen tabbas Shatu zata cika mata burinta. Gashi ta samu farin jini gurin malamai da student duk inda ta zaga zaka ji ana Shatu Mujittafa.


A ranar cikin dare cikinta ya fara ‘kugin yunwa da sauri ta tashi neman abinci. Ta shiga kitchen Ta lodo abinci a plate, don yanzu an saba ma dole ake ajiye mata abincin saboda yunwar dare. Tana fara cin abincin ta ji cikinta yana harbawa alamar motsi sosai ta zaro ido, ta kai hannu ta dafa wajen da taji motsin sai taji ya sake harbawa. Da sauri ta mi’ke cikin matu’kar tashin hankali a fili tace na shiga uku meye a ciki na,
Sosai kuwa ya cigaba da harbawa kamar tana tunzira shi, ai ba shiri ta zunduma da gudu sai ‘kofar d’akin Mommah, ta shiga nocking tana ‘kwala kiran sunan Mommah.

A razane Mommah ta farka cikin barci, jin Shatun na kiran sunanta da sauri ta sauko daga Gadon, ta nufi ‘kofa don bud’ewa.

Ganin Shatu a firgice yasa ‘kirjin Mommah ya buga da ‘karfi tana kallonta, tana nan waige-waigen ganin ko wani mugun abinne ya samu Shatun. Da sauri ta ri’ke hannunta suka shige bedroom d’in Mommahn. Bayan ta zaunar da ita a gefen Gado ta kalleta tace “Menene?” Shatu hawaye sha’be-sha’be tace “Mommah cikina wallahi ina jin micijin ciki ne ya girma har ya fara motsi a cikina tun d’azu yake watsalniya.” Mommah ta ware ido tana sake ‘karewa Shatun kallo banda ita shaida ce tayi period har uku, a gobe ko jibi suke saka ran na hud’u da sai tace ciki ne da ita don duk alamomin juna biyu sun bayyana ga Shatun. Mommah tagumi kawai ta zuba bayan ta rasa tudun dafawa. Fatan ta Allah yasa ba wani mugun ciwon bane zai kama Shatun.

Da kyar ta bari Asuba tayi, ta tayar da Shatu da take kwance saman gadon ta tana barcinta hankali kwance, ba abinda ya dameta, duk da cikin yana ta harbawa.
Sai da suka yi Sallah, sannan Mommah ta kira wayar Ammar don ya kaisu asibiti. Ta turawa Dahda text msg. Suka fice da sauri duk hankalinta ya gaza kwanciya.

Suna zuwa asibitin, bayan tambayoyi likita ya tabbatar ta ta’ba aure, sannan ya rubuta musu gwale-gwajen da zata je ayi mata a laboratory. Zaman jugum su kayi kafin result ya fito aka kaiwa Doctor d’in.

Murmushin da Mommah taga ya saki ne hankalinta ya kwanta ta san tabbas da wani mummunan ciwo me, da ba zai yi murmushi ba. Ya d’ago yana sake kallon Shatu, a ganin farko dama da yayi mata ya san hakan ce zata faru. “Alhamdulillah ba wani abin damuwa bane, she is pregnant.” Da sauri Mommah ta d’ago tana kallonsa “Ciki fa kace Doctor?” Ya d’aga kai “Yes off course akwai abin damuwa ne ko bata da aure ne?” Mommah ta saki ajiyar zuciya tare da cewa “Bakomai, amma abin da mamaki duba da ko last month tayi period.” Doctor ya girgiza kai “wannan ba abin damuwa bane, ba kowace bace don tana da ciki take daina period, wasu sai cikin ma ya girma suke dainawa, wasu kuwa har su isa haihuwa ma, ya danganta ga yanayin mahaifar mace, amma yanzu for confirmation bari muyi mata scan don mu san tsawon lokacin cikin.” Ita dai Mommah jin sa kawai take, amma hankalinta kam a tashe yake Allah yasa dai cikin nan na Imran ne shine fatanta.

Ana yin scanning kuwa ciki ya tabbata sati goma sha shidda wata hud’u cif-cif, watannin cikin watannin aurenta, hakan ya kwantr da hankalin Mommah tunaninta d’aya yanzu, ko dai Imran ba virgin ya sameta ba shi yasa ya saketa idan kuwa ba haka ba mai yasa zai sakar mata ‘ya bayan ya tare da ita. Ta shiga addu’ar kada Allah ya tabbatar da tunaninta, lamarin fa sosai ya d’aurewa Mommah kai har ta kai bata wani fahimtar dogon bayanin da likitan yake mata.
Ya rubuta mata magunguna suka mi’ke suka fito. A reception suka samu Ammar

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment