Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fita da ‘bera” daniel ya zaro ido “‘bera kace mai kyau you mean rat?” Tsaki taja “kayi sauri ka tsaya kana surutu sai ya shige wani wajen” yana shiga ta rufo ‘kofar da key “idan ka cireshi ka gaya min sai na bud’e.” Ta bud’e peppe soup ta tara yawu a bakinta ta tottofa ta mayar ta rufe tana dariya, sannan ta ciro wata leda a jakarta ta tsiyaya ruwan cikin shayin dariya take sosai “yau zamu ga ‘karsheb tsafta zaka sha yawuna ka sha kuma ruwan hammata ta.” Da sauri ta bud’e daniel jin Imran na’kwala masa kira.” Kaga ‘Beran?” Ta wurga masa tambayar bayan ta lura yana kallonta “ban ganta ba” ficewa tayi tana cewa “ta gudu kenan bagware wai ban gan taba sai kace ‘beran macece?”



Not edited.....



*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-14



Tun da ta ganshi a parlourn hakan yasa ta zama don taga ko zaici abincin,shi kuwa yana dinning a zaune ya had’a tea ba tare da ya dubeta ba da alama sauri yake don haka da azama ya d’aga cup d’in tea d’in ya kur’ba ya kuma bud’e bowl d’in peppe soup d’in ta zuba a plate ya kai baki yana kur’ba dad’in peppe soup d’in ya ratsa har kwanyarsa ya lumshe ido yana sake zu’ka. Dariyar da shatu ta saka ce yasa shi saurin bud’e idonsa sai kuma ya had’e ransa yana dubanta tana ta she’ka dariya har da tuntsirawa,jikinsa ne ya bashi tabbas akwai dalilin dariyar tata don haka da sauri ya ture plate yace”ke zo nan” tana ‘kunshe baki ta fara shirin guduwa “wallahi kika d’aga ‘kafa daga wajennan ko da one step ne zaki ga abinda zan miki zo nan nace.” Hantar cikinta ne ya d’uri ruwa har ta juya zata wuce ba tare da taje d’in ba taji ya dam’keta ta baya gashinta yaja taji zafi sosai don haka ta runtse ido.”Don Allah ka sakar min gashi akwai zafi fa to wai mai ma nayi maka?” Tayi maganar cikin muryar shagwaba bai mata magana ba ya jata zuwa part d’insu a parlour ya wurgata saman kujera”gaya min uban me kike wa dariya ko na baki wahala nan dai ba mai cetonki balle kice wallahi idan baki gaya min ba ko school d’in da kike zumud’in zuwa ba inda zaki”Jin yace ba zata school ba ne hankalinta ya tashi duk d’okinta da takeyi zai ruguza mata shiri ta fara rawar baki”kada ki sake kiyi min ‘karya ina da abinda zan saka a jikinki in gano gaskiya don fad’a min gaskiya kafin na gano da gaskiya.” Ya fad’a cikin’kara tsare gira. Hakan ne ya sake razana ta tayi saurin cewa “idan na gaya maka gaskiyar zaka barni in wuce school?” “Fad’i ina jinki” ya fad’a yana tsareta da ido. Ajiyar zuciya ta saki sannan tace “Don Allah kayi ha’kuri a cikin peppe soup ne na zuba yawu na a tea kuma na zuba maka ruwan hamma.....” da sauri taga yayi toilet yana kakarin amai hakan yasa ta suri school bag d’inta tayi waje a guje. Ya dad’e yana amai kamar ya amayar da kayan cikinsa ‘karshe ya fito har wani jiri yake ji kamar ya kifa haka ya kwanta akan gado yana maida numfashi har ga Allah yarinyar nan ta cuceshi cuta bata wasa ji yake kamar ya fito da kayan cikinsa ya sauyasu ha’koransa kuwa da harshensa ya dirje su yafi sau nawa har rad’ad’i suke masa zazzafi mai zafi ya kamashi haka ya ‘kudunduna a gado duk da yana da important issue haka ya ha’kura da fitar.


A school an kar’beta ko da suka gwadata suka ga gwara kawai su kaita primary five tunda tana da sharp brain idan yaso a gida a samar mata lesson teacher.


Da ta dawo kuwa samu tayi duk gidan suna part d’insu Imran wai bashi da lafiya ta’be baki tayi ta samu abinci kawai ta fara ci ita ina ruwanta da ciwonsa mutum sai shegiyar tsaftar tsiya har da wani amai da ciwo. Taci ta ‘koshi sannan tayi wanka ta zira da wando tana fitowa ta tarar da mommah ta shigo. Mommah ta bud’e mata hannu tana welcoming d’inta tare da furta”oyoyo autar mommah ya school d’in” ta d’aga kai “
Ba laifi mommah amma fa sai an jawa ‘yan class d’in kunne bana son rashin kunya don naji suna ce min wai ra’kumi a cikin ‘yan tsaki to yau dai nayi musu na ba’kunta gobe kuwa wallahi na jaki zasu ci” Mommah murmushi tayi ta dafa ta “ba’a fad’a a makaranta baby na kada ki kula kowa kin ji’yar albarka kiyi karatunki kawai ki koma gida shine abinda ya kaiki kinji?” Murmushi tayi ta d’aga kai shigowar nahna ce yasa mommah ta tuna ruwan tea zata dafawa Imran kuma ya ro’keta don Allah da kansa zata kawo masa don yanzu tsoron ta’ba komai na gidan yake da zai iya ma da kansa zai shiga kitchen d’in ya dafa to jiri yake ji saboda tun safe ba abinda ya shiga cikinsa.Momma ta girgiza kai “kinga kuwa nahna shaf na manta abinda nazo yi bari in tashi” Nahna tana dariya tace “ya kuwa ce da kanki yakeso ki dafa masa kuma kina juyewa in kawo masa ni ban san me ya sameshi ba” mommah tace “mhmn rabu da Imran haka yake idan yana cuta sangarta ce dashi zan ga yarda matarsa zata yi da ‘kyan’kyaminsa wallahi abin yana damuna sai kace wani mai cutar tsafta.” Da kanta ta dafa tea d’in ta bawa Nahna ta kai masa.

Yana ganinta ya mi’ke zaune da kyar yana ri’ke kansa ya jingina da bangon gadon a hankali ya motsa bakinsa muryarsa ta fito “please mommah ce ta dafa kuma kina tsaye a wajen? Ibilishiyar yarinyar nan kuma bata wajen ko?” Nahna ta girgiza kai tana dariya ta tabbatar masa mommah ce ta dafa da kanta. Ta zuba ta mi’ka masa yana sipping a hankali. Lokacin shaheeda ta murd’a ‘kofa ta shigo kallo d’aya tayiwa nahna ta d’auke kai hannunta d’auke da cooler ta nufi gefen gadon ta zauna cike da kwainane sai zabga ‘kamshi take ta zauna a gefensa tana jan yatsun ‘kafarsa “am sorry Habibi ya jikin?” Nahna ta kai idonta kan hannun sai kuma ta ta’be bakinta da sauri ta fice tana mamakin rashin kunya irinta ‘yan matan yanzu sam basa iya tsare mutuncin kansu shi yasa ko auren aka yi mazan basa ganin mutunci su.shaheeda ta sake kallonsa tana murmushi “ Habibi in zuba maka abincin?” Da sauri ya girgiza kai, ta kuwa had’e rai a hankali tace “kai habibi I cooked it with my own hand fa please kaci kaji?” Cikin muryar shagwa’ba take gaya masa hakan ya sake narkar da zuciyarsa yana jifanta da wani kallo ya matsu ya matsu sosai ya auri shaheeda shi kad’ai irin son ta da yake dan’kare a zuciyarsa yana jiran lokacin da Zai amayar dashi.ta zuba a plate ta zauna tana bashi a hankali cikin sigar jan hankali.



Mommah ce ta tilasta shatu sai taje dubashi, ta mi’ke tana zun’bura baki a zuciyarta take tunanin ita mommah bata san itace silar ciwon bane ta tabbata yanzu idan taje sai ya huce haushin abinda tayi masa. Hafsa ce cikin fad’a tace “Ba zaki tashi kije ba sai na ‘bata miki rai baki san d’an uwanki bane shi duk duniya baki da kamarsa fa shi da Ammar.” Mi’kewa tayi ta fita niyyarta idan ta fita ta la’be ta dawo tace taje, sai dai a rashin sa’arta Nahna ta mi’ke tace “Bari muje na san halinta yanzu ta ‘buya tace taje.” Ta tura ‘kofar bed room d’in a hankali bayan ta shiga parlourn hakan yasa Nahna saurin juyawa ta koma. Ita kuwa shatu mummunan gamo tayi shaheeda ce a gefen Imran tana ta shafa masa fuska wai tausa take masa ta shige jikinsa sosai kamar me. Da sauri shatu ta runtse ido tayi saurin juyawa shi kuwa Imran motsin da yaji ne yasa shi saurin mi’kewa sai yaga fitar shatu da sauri ya janye jikinsa yana wa shaheeda wani irin kallo “sau nawa zan gaya miki bana son irin wad’annan abubuwan bafa wayewa bace yanzu kinsa yarinya ‘karama ta gammu a haku me kikeso tace mai kike so tayi zargi a zuciyarta?” Shaheeda marairaice masa fuska tayi “Haba habibi meye a cikin hakan kawai fa tausa ne amma tunda baka so insha Allah na daina Allah ya kaimu lokacin da zaka zama halal d’ina in nuna maka pure love da ba surki amma waccen yarinyar mai take zuwa yi har bed room d’inka?” Runtse ido yayi yana tunanin lamarin yarinyar baya ko son ganin fuskarta tsoronta lamarinsa yake bashi don haka dole ya samarwa kansa lafiya ya fita sabgarta kafin tayi abinda zai kaishi lahira burinsa ma lokacin bikinsa yayi ya tattara ya bar gidan ba sai ta ganshi bama balle ta hukunta shi da ‘kazantarta.



A ranar Dahda ya dawo amarya aka shiga giringid’ishin kama miji mommah dai ko gurinsa bata jeba balle taga abinda zai ‘bata mata rai, sai da ya gaji da kansa ya shiga part d’inta tana zaune da kwalliyarta ta tsadaddiyar atamfa ta kashe d’auri parlorn nan sai ‘kamshin turaren wuta yake yi. Murmushi ya sakar mata “uwargida ran gida barka da hutawa ni nazo gaisheki tunda ba’a nemansa” murmushin ta saki itama bayan ta gama saurararsa tace “hakan da kayi shine abinda ya kamata ka bi cikakkiyar sunnar manzon Allah ya hanya?” “Alhamdulillah” ya furta yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya ya tabbata da itace da girki da tuni ta kai masa ruwan wanka ta kuma taimaka masa da tausa da lafiyayyen girkinta tana zuba masa tana murmushi ba dole dijah ta sace zuciyarsa shi kad’ai ya san wacece dijah ya kuma tabbatar ba zai samu kofa kwafinta bane balle wacce ta kaita. “Na biya wajen hajja wai me ya faru ne ta tabbatar min da aljannu a cikin gidannan wai ba zata sake zuwa ba” yana murmushi ya fad’a mommah ma dariyar tayi tace”Ba mamaki da aljannun a d’akin da take sauka amma mu dai bamu ta’ba gani ba” “Ni na sani na san rigimar hajja ce yanzu ba ma wannanba ta rigime min sai anyi bikin Imran nan da wata d’aya da Rabi” mommah ta saki murmushi kafin tace “Masha Allah Allah ya nuna mana me yayi saura ai ya gama gininsa Allah yasa albarka yasa abokiyar arzikinsa ce yana d’akima ba lafiya” Dahda ya mi’ke “ai naje na duba shi ina shigowa zainabu ta fad’a min Allah ya bashi lafiya yace min stress ne yayi masa yawa Imran ne akwai son kud’i baya son hutawa” mommah tana dariya tace “kyan d’a ya gaji ubansa”



*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-15



*****
Tun daga lokacin Imran ya tattara shatu ya watsar a gefe baya shiga shirginta sam ko a waje ya ganta baya zama idan kuwa yana waje tazo da sauri yake barin wajen. Hakan da yake yi kuma sosai ya fara damun zuciyar shatu bata so ba sam bata so ya daina shiga lamarinta ba haka kawai take son ta dinga ganinsa tana jin muryarsa da kuma kyakykyawan murmushinsa, hakan yasa ko da yaushe take zama a main parlour kawai don yas shigo ta ganshi taji’kamshinsa ta kuma ga kyakykyawan takunsa da yake yi tamkar a cikin izza bata san daliliba haka kawai IMRAN AHMAD MANGA yake burgeta. Ba wai soyayya take nufi ba tunda har a lokacin bata san so ba kawai dai burgeta yake tsaftarsa kallonsa tafiyarsa maganarsa komai Imran manga yayi burge shatu yake sosai har cikin zuciyarta ba mamaki hakan yana da ala’ka da zamowarsa d’an uwanta kuma jininta wanda duk duniya bata da na biyunsu. Ganin ya daina shiga shirginta itama ta tattarshi ta watsar ta kama Ammar abinta da uncle d’inta Hisham da kullum suke tare indai suna gidan.

Tuni ta mayar da hankalinta akan karatunta both islamic da boko bata wasa burinta ta zama mai ilimi ta kuma iya english kamar yarda taga su Anty hafsa suna yarawa abin yana burgeta yana sata nishad’i, hakan yasa take damun mommah da zancen ita kuma mommah ta dafa kanta tace “sha kuruminki shatun mommah zaki iya turanci da ko bature england sai ya sara miki” hakan da mommah take fad’a shi yake ‘kara mata ho’b’basa taji tana so tana kuma zakwad’i da karsashin son zamowa baturiya mai yara english ba gargada ko tuntu’ben harshe. Sosai take dagewa lamarin har tsoro yake bawa mommah ganin yarda ta mayar da karatu abokinta ko da yaushe zaka sameta da littafi na islamiyya da na boko. Tsoron mommah d’aya kada karatu ya sa ‘kwalwarta ta’buwa don haka sau tari take ‘kwace littafin ta saka mata kallo ko tace tayi barci ko na rabin sa’a ne kwanyarta ta samu hutu.

Tuni su hafsa suka tattara suka koma Abuja saboda yawan damunsu da hajiya mama take da yawa akan hutun ya isa, kullum fad’a take tana ‘karawa “ Ba hauka bane abin ku tattaro komatsanku ku dawo nima ina bu’katarku idan bikin yazo kwa koma tunda dai bata da wasu sha’ki’kan da suka wuce ku” hakan yasa dole suka tafi zuciyarsu cike da tausayin mommah ganin yarda kishiya da dangin miji suka sakata gaba. Koda suka gayawa hajiya maa murmushi kawai tayi kafin tace “haka rayuwar ta gada ba yarda bawa zai zauna ‘kalau bai jarrabeka ba idan kaga Allah baya jarrabarka ma ka binciki kanka balle d’iya mace a gidan miji taya kuke zaton zata samu aljanna a ‘bagas ai dole ne a jarrabeta ko ta’bangaren kishiya uwar miji ko dangin miji, ‘ya’yansa ko d’ungurungum mijin ma gaba d’aya babu wata mace da zata ce salin Alin tana rayuwarta ‘kalau tsakanin bawa da ubangiji godiya kawai a duk yanayin da ya tsinci kansa don haka ta godewa Allah tunda mijinta na sonta saura kuma ta barwa Allah ta sha mamakin hukuncinsa ai hukumullahi la ajabun.”



********

Wata d’aya ya rage biki a kuma lokacin ne ‘kannen Ahmad manga mata masu ji da kansu suka iso gidan d’an uwansu da set d’in akwatinan lefe za’a wuce dasu dangin uban shaheeda da suke Abuja.

Mamaki ne ya hana momma magana da suka samu a sashenta suka ce taje taga lefen da Imran ya had’a. Baki sake take kallonsu kafin ta furta “shi Imran d’inne ya had’a lefe ba tare da sanina ba saboda bai mayar dani uwa ba ko mai?” Tsaki hameedah tayi tana tauna chewingum sai kuma ta tintsiro d’ankwalinta gaban goshi tana watsawa momman kallon raini tace “yo da ke har wata tsiya kike d’aukan kanki d’a dai kin haifa amma baki isa kice zaki juya shi ba wannan kam sai yarda muka ga dama kin dai juya ubansa mun’kyale ki yanzu kam the table

Don haka muka saka dole ya auri shaheeda mu juya shi son ranmu kema ki d’and’ani rad’ad’in da mu kaji da kike juya yaya manga ki taso kiga lefe idan kinga zaki iya idan kuma ba haka ba kya gani a jikin surikarki kuma ‘yar kishiyarki shaheedah.” Ran mommah ne ya ‘baci har ta gagara ‘ko’karta furta ko kalma d’aya ce ga hameedah yarinya ‘yar cikinta da take tsaye take mata fitsara. Suma duka sauran ba wanda bai furta albarkacin bakinsa ba sannan suka juya suka tafi suna dariya da shewa burinsu ya cika sun ‘batawa mommah baiwar Allah zuciya. Tsahon lokaci tana zaune a wajen ta kasa mi’kewa tufka take a ranta kawai da warwara tabbas idan ba’a yi wasa ta bari a kayi aurennan zasu ci galaba a kanta za kuma suyi duk abinda suka ga dama hawan jini suke neman cusa mata da ciwon zuciya,ita bata ga abinda tayi musu a zahirance da bad’inance kawai dai ‘kiyayya ce suke mata su kansu da basu san asalinta ba balle tushenta. Ya zama dole tayiwa tufkar hanci lefe dai ba zata je ta gani ba kuma Imran zai zo ya sameta zata nuna masa ita d’in nan dai itace wacce ta haifeshi ta d’au cikinsa wata tara ta kuma shayar dashi nononta na tsawon watanni sha takwas.


Tsawon lokaci mommah na zaune a parlournta ranta a matu’kar ‘bace ta gaji ta gaji da tozartawa da wulakancin dangin miji, mafita kawai take nema tun daga parlournnata tana jiyo su tana jiyo ba’ka’ken maganganu da suke jefo mata masu kama da gugar zana hakan ya ‘kara hassala zuciyarta taji kuma zata iya komai don ‘kwatowa kanta ‘yancinta ciki kuwa har da samowa Imran aure ko da a cikin d’iyoyin friends d’inta zata nuna musu tana da iko da d’anta kuma ba wata shegiya da zata yi mata tin’kaho da d’anta alhali sanda tayi na’kudarsa ko wacce cikinsu tana can shanye da baki tana barci.lokaci yayi da zata farka daga barcin da take ta amshe matsayinta na uwar d’a mai cikakken iko akansa fiye da kowa a duniya.

Shigowar shatu ne ya farkar da ita dogon tunanin da ta tafi, shatu da hanzari ta ‘karasa wajenta ta dafa takanta ganinta cikin damuwa, tana son mommah jinta take tamkar innaji don haka sam bata son ‘bacin ranta kuma zata iya gogawa da kowa idan har yace zai shiga gonar mommah.murya can ‘kasa tace “Mommah menene meye ya sameki? Wad’ancan mutanen ne ko?” Momma ta girgiza kai tana janyo shatu jikinta “Bakomai shatu yau naji ina burin dama ke budurwa ce da ma ke kin kai muzalin aure da ba abinda zai hanani aurawa Imran ke da nayi alfahari da haka”shatu ta zaro ido “aure mommah ai nayi ‘karama” Murmushi mommah tayi kafin ta furta “shi yasa a zancena kika ji nace dama, duk da haka ba matsala insha Allah ba zan rasa wacce zan ‘karawa Imran a matsayin mata ta biyu ko da hakan yana nufin za’a yi tashin hankalin da ba’a ta’ba yi ba da wad’ancan mutanen” shatu ta ja ajiyar zuciya tana kallon mommah da hawaye yaso zubo mata ta kuma tabbatar na zallar’bacin raine. A zuciyarta ta ‘kudurce tabbas sai tayi maganin mutanennan a yau kuwa ba sai gobe ba taji itama a zuciyarta dama ita d’in budurwace a aura mata Imran da kuwa tayi sa’a kuma sai taci uban shegiyar shaheedan mai goshi kamar fitilar jirgi dama ta tsaneta tunda sanda ta ganta a kanainaye a jikin Imran. Shigowar Imran ne da ‘kamshin turarensa ya sata kai idonta kansa yayi kyau sosai cikin wani black yard african attire d’inkin zamani bai kai gwiwaba haka nan hannunsa gajerene kuma rigar tad’an kama shi kad’an an yi masa ratsin light brown daga gefen aljihun da kuma rigar ta lura yana son irin kayan yawanci shigarsa kenan yayi kyau sosai duk da kansa ba hula. Bai ko kalli sashen da take ba ya ‘karasa inda mommah take fuskarta a had’e sosai. Zama yayi sosai kusa da ita yana dafa kafad’arta had’e da zubawa shatu harara, kafin ma yayi magana ta mi’ke don ta san ma’anar hararar tasa ta shige bedroom d’inta murya can ‘kasa tace kyau kamar aljanni sai zallar ba’kin hali”.

“Please mommah na mai ya faru ne naga fuskarki ba walwala? Kuma su anty fannah sunce kije kiga lefe kin ‘ki why mommah?” Kallonsa tayi kallon cikin ido kallone da tun suna yara suka san tana yi musu idan sunyi mata babban laifi. Da sauri ya rusinar da idonsa baya jurewa wannan kallon baya son sa yana razana shi ya kuma san duk sa’in da mommah tayi shi ranta ya kai ‘kololuwa a ‘baci “ please mommah am sorry duk da ban san laifina ba” “ sorry for what Imran? You are sorry because ka wula’kanta ni ka nunawa duniya bani da amfani a wajenka ka nunawa duniya dani da babu ni you can make decisions about anything aurenka Imran ace sai dai ace nazo naga lefe? Ana yar min da magana baka neman albarkata baka damu da farincikina ba ko da yaushe sai ‘bacin raina nagode kaje ka yi aurenka kaje mutanen da kake tunanin zasu baka farin ciki su baka fiye da wanda ni zan baka Allah ya sanya albarka a aurennaka but put this in your mind bani ba ‘yan uwana a bikinka ba zamu zauna muga ‘baci rai ba.” Daga haka ta mi’ke ta shige d’aki jikin Imran ne yayi sanyi ji yake kamar yace ya fasa baya son ‘bacin ran mahifiyarsa bai san me yasa zuciyarsa ta kasa ha’kura da shaheedah ba, tsawon lokaci yana zaune kafin shatu ta fito tana ‘yar wa’karta ta “uwa tana da girma mahaifiya tai mini komai” da sauri ya kalleta gani yake kamar da shi take da shi d’in kuwa shatu take amma ya kasa ta’buka komai yana juya kalaman wa’kar shatu a zuciyarsa.


Ko da ta fita bata zame ko ina ba sai wajen mai gadi, da murmushi y tareta don yana son shatu musamman yarda take girmamashi ga kyauta akai akai “uwata ta kaina ya aka yi?” Ya fad’a yana mata murumushi shatu tayi ‘kasa da muryarta “Baba taimako zaka yi mi please amma bana son kowa ya sani” ya girgiza kai “ shatu danger yau kuma wa ya takaloki?” Dariya tayi kafin murya can ‘kasa tace “wasu ‘kadangarun bariki zanyi magani ga dubu biyu ‘kai’kayi zaka siyo min don Allah” Baba ya ware ido “Aa fa shatu’kai’kayi kuma mai zaki yi dashi?” Ta had’e rai idan ba zaka taimakeni ba shikkenan bara na tafi” ganin tayi fushi yasa yace “zo uwata zan taimakeki ai ba zan’ki mai taimakona ba” ta mi’ka masa kud’in tana dariya.

*🤍ME ZAN YI DA ITA?*🤍



NAZEEFAH SABO NASHE


FREE📚
08033748387
-16


ELEGANT ONLINE WRITERS.....


Baba murmushi ya saki “ko waye ya shiga gonar uwata? Ko ma dai waye ya jawowa kansa yau” Baba mai gadi ya furta a hankali yana jinjina girman al’amarin shatun.


Tun yamma ta dinga zagaye gidan har ta tabbatar da windown ko wane d’aki sannan hankalinta ya kwanta taje ta ‘boye ‘kai’kayinta a ma’ajiyar da ta tabbatar babu mai ganinsa,sannan ta cigaba da harkokinta tamkar babu komai a zuciyarta.


Tana general kitchen ita da masu aikin gidan amaryar Imran ta shigo sai wani iyayi take da rawar ‘kafa.shatu ta zabgawa harara kafin ta bud’e fridge tana duban masu aiki “Imran yace kuyi masa abinci ne?” Ta tambayesu cikin kallon raini. Saratu ta girgiza kai “ai dama bamu muke masa abinci ba daniel ne kuma tun wancan satin ma ya dakatar da daniel ko ruwan tea zai sha naga a kitchen d’in mommah yake dafawa da kansa.” Kallon one by one tayi musu tana yatsine fuska “Ba dole ba,ba dole ya daina cin abincin gidannan ba gida duk an tara gayyar ‘kazamai dama zuwa nayi inyi warning d’inku kada wacce ta sake yi masa abinci ni da kaina zan dinga yiwa mijina abinci bana son ya dinga cin na kowani ‘kazami.” Shatu tsayawa tayi tana kallonta sai kuma ta tuntsire da dariya ta kalli saratu tace “saratu bani aron muciyarku akwai abinda zan gwada da ita” ta fad’a tana yiwa shaheedah kallon sama da ‘kasa ita bata ga abinda Imran ya gani a jikin wannan ba ‘kafafu kamar sillan kara. Shaheedah ranta yayi ‘kololuwar ‘baci da sauri ta cafko shatu ta fara wanketa da mari shatu ta daka tsalle ta rama sannan ta shiga ‘kar’kashinta ta tad’eta ta fad’i hakan yasa shaheedah ‘kwalla ‘kara ina shatu bata saurara mata ba ta hau kanta ta shiga lugude a ruwan cikinta. Masu aiki suna gefe sai dariya suke sun ‘ki rabawa saratu a zuciyarta fad’i take dai-dai kenan shegiya mai girman kan tsiya. Ihun shaheedah ne ya karad’e gidan hakan yasa duk mutanen gidan suka yiyo general kitchen d’in ban da mommah da take wanka. Da sauri su kayi kan shatu suka fara jibgarta tun tana ihu har muryarta ta dashe gefen bakinta da goshinta ya kumbura suntum. Ihun shatu ne ya fito da momma daga toilet riga kawai ta zira ta fito a guje dai-dai lokacin Imran ya dawo kenan shima ya juyo ihun yayi yo cikin gidan da sauri yabi bayan mommah. Momma ta tarar dasu har a lokacin dukanta suke sun mata jina-jina su saratu sai ihu suke suna fad’in zasu kasheta. Da sauri momma tayi kukan kura ta ‘kwaceta bayan ta dubesu

1 Comments On ME ZANYI DA ITA
avatar
hafsat-bello

1 year ago

Reply

Complete

Please Login or Register in order to submit comment