Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🍓🍓PAPI NE!🍇🍇

*Second edition*


_by Noor Eemaan_📚✍️


Wattpad
@NoorEemaan


In the name of Allah most glorious, most merciful.


Wanna labarin ƙirƙirarren labari ne, ban yarɗa a juya min shi ta ƙowacce siga ɓa idan ƙunne ya ji....



Alhamdulillah dukkanin yabo sun taɓɓata ga ubangiji mai sammai da ƙassai, a ƴau gani tafe da saɓon novel har ɓiyu ƙamar haƙa *PAPI NE DA ƘƳAUTAR KODA* ban san ya zan yi muƙu ɓayanin books din ba, sai dai shaƙƙa babu zaku ji ɗadin books ɗin in sha Allah, kuɗai ku cigaba da ɓina ɗan jin ƴanda ɗoguwar tafiyar da zamuyi ɗani ɗaku zata ƙasance. Banyi alkawarin yin typing kullum ba...


Wanna Littafin Sadaukarwa ne Gabadaya ga dukkanin Maraya(orphans) Dana gidan Marayu da ma ko ina Suke a duniya...



Page1-2

*SOKOTO STATE*

Misalin k'arfe takwas na dare ne, unguwar shiru tamkar babu halittu a cikin ta, wanda hakan baya rasa nasaba da ruwan saman da ake tsulawa tamkar da bakin kwarya, mafi akasarin gine-ginen unguwar na marasa karfine domin mutum na ganin tsarin gidajen unguwanin zai tabbatar da hakan.

A hankali wani yaro mai kimanin shekaru goma sha biyar a duniya ke tafiya, duk da uban ruwan da ake tsulawa hakan bai dame shi ba, ga wurin fakewa da yawa amma bai yi hakan ba. Duk da kananun shekarun sa yana da tsayi sosai, wanda mutum zai iya tunanin ya kai irin shekaru ashirin din nan.

Wasu kod'add'un jeans da riga ne a jikinsa sai wani snickers a kafarsa, yana da k'yau, da alama idan ya zama babban saurayi za a yi k'yak'yyawan gaske da yanmmata zasu yi ruɓuɓɓin sa, yana daf da shan kwanar da zai saɗashi da layinsu ya ji kukan jariri, cigaɓa yayi da tafiyar sa ba tare da ya ko kalli inda kukan ke tashi ba...

Har ya kai kofar gidansu wanda ya kasancewa na zallan jar ƙasa, ya ji Hankalin sa ya kasa kwanciya domin tunda ya taho sautin kukan jaririn ke amsa kuwwa a kunnuwan sa.
Runtse ido yayi kana ya juya da sauri har da guɗun sa....

Abun mamaki har yanzu kukan jaririn ke tashi, A hankali ya karasa gaban kwallin da jaririn ke ciki add'ua dauke a bakinsa yayinda wani tsoro-tsoro ke k'ok'arin shigar sa, sai dai yaki ɓawa tsoron daman samun muhalli a zuciyar sa...

Har ya kai hannu cikin k'wallin da niyyar daukar babyn, sai kuma ya sauke hannun, ya fara k'ok'arin daukan k'wallin gaba daya, a tunanin sa idan yaje kofar gida ya buɗe, faduwar gaba ce ta saukar masa dai-dai lokacin da kwallin ya rabe kansa sak'amak'on ruwa daya gama jika ta yayinda k'yak'yyawan baby'n yayi gefe yana daf da shan kasa...

Cikin wani sauri da bai san yana da shi ba ya cafko ta, k'asancewar akwai cak'walli sosai a wajen yasa ya fadi kasa, runtse idanun sa yayi sak'amak'on ɓugewa da kansa yayi jikin wani dutse, sai dai ya rike baby'n gam gam a jik'in sa, yama rasa wani jinsi zai bawa wanna baby'n shin _jariri ne ko jaririya ce_ ?
Sai d'aya dauki tsawon mintuna goma kana yaji kansa ya dan daina ciwon, ya mik'e tare da baby'n a jikinsa wanda zuwa lokacin ruwan ya fara tsagaitawa kadan da kadan, Kara kallon kwallin yayi yaga ta dame da kasa saboda tsananin jikewa, bayan haka babu komai a tare da baby'n domin ko riga babu a jikinta sai jini da bai gama fita a jikin ta ba har yanzu da alama haihuwar yau ce...

Cikin tsananin tausayin baby'n dake ratsa zuciya da jikinsa ya mike ya fara tafiya bayan ya shigar da ita cikin jikin sa, a dalilin sa na son kare ta daga ruwan saman dake dukan naked body d'inta har yanzu, duk da dai babu abinda rigar tasa ta karewa baby'n domin a jike take sosai, baby'n kuwa wani damke fatar k'irjinsa sa tayi tana k'ok'arin tsotsa, wani sabon tausayin baby'n ne ya sake dirar masa...

Cikin sauri-sauri gudu- gudu yake tafiya har ya isa bakin kofar gidan nasu, tura kofar gidan yayi wanda ya kasance na zallan langa langa ne, shiga yayi kana ya sanya sakata...Dakuna biyu ne kacal a gidan sai bandaki, daga can gefe akwai wasu manya manya dutsina uku, da kuma wata tukunya akai wanda aka kwashi tuwo a ciki da alama nan ne maɗafa, tsakar gidan ba wani babban bane, kana jar kasa ce wanda ya sake ca'bewa saboda ruwan saman da aka yi, ga robobi reras a jira cike da ruwa da alama ruwan sama aka tara cikin su...

Daki dake a farko ya nufa, hadi da daga labulen ya shige... wata tsohuwa mai k'imanin shekaru hamsin da tara zaune kan gadon ta irin na bunun nan ga tudu da laushi, wani kallo ta jefa masa kana cikin fad'a ta fara cewa......



*Ya kuka ga wanna labarin? Shin in cigaba ko in dakata? yawan comment dinku ne zai sa na cigaba da suburbudo muku shi...*✍

Don't forget to share
Comment and
Vote me on wattpad @NoorEemaan


NoorEemaan na muku sahihiyar kauna🥰



🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

_by Noor Eemaan_✍️📚




Wattpad
@NoorEemaan



Tnx all naga comments dinku da yawa hakan ya bani k'arfin guiwar typing, Sannan mutane da yawa sun tambayeni cewa menene ma'anar *"PAPI NE"* ? TOH Papi dai another name ne da diya kan kira uba da shi...

Page 3-4


" Kai Nu'aymu ka fita idona in rufe fa, bazai yu kullum ka dinga tayar min da hankali ba, dana Ahamadu bai taba sani magana ba" sai kuma tasa kuka tana cewa "Allah ya jikan ka Ahamadu, albasa bata bi halin ruwa ba" ta karasa tana fyato majina...

Kallon ta ya tsaya yi yana mamakin yawan rigimar ta, domin ba wani tsufa mai yawa tayi ba amma dukkanin wata alama na rikicin tsufa ya riga ya gama bayyane kansa.

Runtse idanun sa yayi wanda hak'an ya zame masa tamkar dabi'a, kai kace wani babban saurayi ne.
"Ooh Kaka rigima, nifa ba yaro bane da kullum zaki dinga sa min ido kan lallai sai na dawo gida da wuri, sannan sunana ba Nu'aymu bane, Nu'aym nake!"

"Kai dallah rufamin baki, ina abun yake? Idan kai ba yaro bane toh meye kai dan gidan ku, yaushe ma aka yaye ka?"

Bai kara kula ta ba, saboda baby'n dake tare da shi, cikin lalluma ya fara cewa"haba matar yi haku'ri, in sha Allah zan dinga k'ok'arin dawowa gida da wuri kinji?"

Tabe baki tayi kana tace "toh Allah yasa" Nu'aym na k'ok'arin magana baby'n ta canyare k'uka, wata zabura Kaka tayi ta haye gadonta ta lafe kuriyar dakin kana cikin tsananin tsoron da rudu ta fara cewa "Nu'aymu aljana jaririya cikin gidan mu innalillahi wa innah ilaihi raju'un, mun shiga uku" ta karasa tana zaro ido hadi da sake shigewa jikin gadon.

Wata dariyar mugun ta ya saki, cak! Kaka ta tsaya da k'ukan nata tana cewa "ya rahamanu ka taimake mu, shikenan aljana ta shiga jikin Nu'aymu jikana" jikinta har wani karkarwa yake, yayind'a ta dinga karanto duk add'ua daya zo bak'inta, har add'uar shiga bandaki ta karanto, saboda tsananin rudewa.

sam bata lura da baby'n ba, saboda bata da wani girma hak'an yasa kai tsaye mutum bazai fahimci haka ba.

Gimtse fuskar sa yayi ganin bilhakki da gaske kuka take, kana a hankali ya ciro baby'n daga cikin jikin sa, wanna karon kaka ta fi shiga rudu da tsananin firgici...

Bakin ta rawa yake alamun tana son furta wata kalma, amma ya gagara, kan gadon ya kwantar da baby'n hadi da cewa "relax kaka, baby'n dan Adam ne k'amar mu, kiyi mata wanka ina zuwa" ya karasa yana ficewa domin sanyi sosai yake ji so yake yaje ya sanja kayan jikinsa...

Sai a lokacin bakin Kaka ya bud'e ta fara cewa "wallahi Nu'aymu baka isa ba, kazo ka dauk'e wanna aljanan jaririya daga kan gadona, wanna 'ya karamar diyar da wanna uban madarar kyau kace mutum ce, san...." Kukan da baby'n ta sake sanyawa mai matuk'ar taba zuciya ne ya katse mata tunanin ta.... Take wani tausayin baby'n ya fara ratsa ta, add'ua dauke a bakinta ta dauki baby'n hadi da runtse idanun ta, baby'n sai girgiza take a hannunta, sak'amak'on rawar da hannun ta ke yi...

Ta kai tsawon mintuna goma a haka kana ta bud'e idanunta ganin babu abinda ya sameta, kwantar da baby'n tayi kana ta sauko daga kan gadon tana waiwayon baby'n still cikin tsoron domin gani take tamkar halittar K'yak'yyawar baby'n zai iya sauya wa...

Sif (wardrobe) dinta da ko murfi babu kuma tsahon yayin nan ne ta nufa, wani zanin ta ta dauko ta lullube baby'n da shi kana ta janyo wata tsohuwar stove (risho) ta kunna kana ta dauko wata sabuwar tukunyar ta dake da sauran sabunta ta, saboda tsananin son da take wa tukunyar shiyasa bata dorawa a wuta, cikawa tayi da ruwa ta dora, babu jimawa ya fara tafasa, dan sirkawa tayi da ruwan sanyi kadan, kana ta dauko wani babban roba, hadi da dauko baby'n ta fara yi mata wanka da wani sabulun ta dan saba'in da take ta lallaba saboda sosai take son kamshin sabulun, sosai ta gasa wa baby'n jiki kana ta sake nada ta da zani ta kwantar da ita kan gadon, Sif dinta ta dauko wasu riga da wando masu dan kwari data siyawa diyar kawarta data haihu, kan cewa jibi zata je musu barka, daga kayan tayi tana kallon su kana ta fara cewa "sai ka biya ni kudina, domin naira na gugan naira har dari takwas na cire na siya, atoh" ta karasa Cikin fada tamk'ar Nu'aym din ne a gabanta.

Sosai yarinyar tayi kyau cikin kayan, wani zanin ta sake dauk'owa ta lullube dukkanin jikinta, kana ta cigaba da mitar Nu'aymu zai d'awo ya same ta, kawai ya dire mata 'ya ba tare da yace komai ba ya fice...

Kwantar da baby'n tayi kana ta shiga goge ruwan daya zuba a kasa, fitar da robar ruwan wank'an waje tayi ta zubar kana ta fara juye ruwan saman data tara cikin robobi cikin wata tsohuwar duro dinta, tsakar gidan ta fara sharcewa, kana ta nufi wajen rariya ta fara dauraye kafarta, wanda yayi d'aidai da sallamar da ya yi.

Amsawa kasa kasa tayi, ita ala dole fushi take dashi, bai kulata ba ya nufi dakin kakan, hak'an ya kara bak'anta ranta "wato Nu'aymu saboda ka raina ni shiyasa kayi ficewar ka batare da ka ce min komai ba, saboda ga marainiyar wayon ka ko?" Tun daga tsakar gidan take wanna maganar har ta cimmasa a daki"

"Wato ga sabuwar kamu ko, ina maka magana kayi min shiru?"

"Dan Allah kaka kiyi Shiru, zan yi miki bayani komai"

D'aidai gaban sa ta tsaya ta rike kugu tana cewa "bazan yi shiru ba, nace bazan yi shiru ba dan gidan ku, tukunna ma yar waye kace ka dauko babu ko riga a jikinta, ga ta sabuwar haihuwa"

"Zanyi miki bayanin komai kamar yadda nace, ga madara irin na yara na siyo mata sachet daya ki bata da karamin feeder na siya, ga kuma awarar ki cikin ledan nan, sai da safe" ya karasa yana ficewa...

'Ka dawo ka dauke wanna yarinyar daga kan gadona, kana nufin a nan zata kwana ban san wacece ba" ta karasa tana binsa har kofar dak'in sa, sai dai ya rufe dakin nasa, kwankwatsa dakin ta shiga yi yayi shiru a dakin yana dariyar hadi da cin tuwon sa miyar kuka hankali kwance...
Bayan ta gaji da buga kofar ta koma dak'in ta tana sababi...

Ruwan zafin daya yi ragowa ta hada mata madarar da shi, sanya wa baby'n feeder'n tayi a baki ta bata fuska taki sha, cigaba da bata tayi har ta fara tsotsan... Tas baby'n ta shanye feeder'n, ga wani gumi daya tsatsafo mata saman goshi, tausayin baby'n ya kama kaka d'omin yanzu hank'alin ta ya dan kwanta saboda babu wata alama daya nuna cewa wanna baby'n aljana ce...

Bayan ta kwantar da ita ta janyo ledar awarar ta ta fara ci tana tunanin rashin mutuncin da zata yi wa Nu'aym go'be bayan ta gama ta fita hadi da dauro alwala, kan gadon ta kwanta tana karanto add'uar kwanciya bacci, domin kaka akwai ibada...Babu jimawa bacci ya dauke ta

2:30am
Baccin su suke hankali kwance, sai kawai k'uk'an baby'n ya karade dukkanin ila'irin gidan, yamutsa fuska kaka ta yi domin ba kadan ba take jin dadin baccin ta, tashi tayi zaune ta fara lallaba baby'n, sai dai ina tamkar kara cewa cigaba da kuka take...

Yana cikin baccin sa yaji tamkar cikin kunnen sa take yinsa, mikewa yayi ya bud'e kofar dakin sa ya fita, yana zuwa ya dauk'e ta izuwa dakin sa ba tare da ya sake cewa komai ba, jijigata yake sai dai taki yin shiru, labb'ansa na kasa ya sanya mata a baki, take ta kama ta fara tsotsa, wani zafi-zafi ke ratsa kwanyar sa a sak'amak'on tsotsan da take yiwa labb'ansa, k'ok'arin zarewa yayi saboda zafi da ya ishe shi, ta tsalla kuka, saurin mayar mata yayi, ya cigaba da jure zafin har tayi bacci, sauki ajiyar zuciya yayi kana ya kwantar da ita kan gadon sa da bai fiye girma da taushi ba, kwanciya yayi shima, yana add'uar Allah yasa kar ta tashi kafin safiya...





Har yanzu bamu shiga cikin labarin ba, just bear with me habeebt's, sannan Ku yi manage wallahi nayi typing ya goge, raina a bace yake😔


SHARE✔
COMMEN✔
VOTE✔
EDIT❌

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓
Written by
Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan



This book this dedicated to all orphans in the orphanage home.

Page5-6

........Ciƙin ikon Allah kuwa bata ƙara tashi ba har gari ya waye, sai takwas na safe Nu'aym ya fito daga dak'insa baby'n dauk'e a hannun sa.

Ƙo ina tsaf tsaf alamun an gyara, gama shatin tsintsiya kwance kan jar kasar, d'aga gefen wajen mad'afa kuwa kaka ce tsukunne ta dora musu d'umammen tuwon su da yayi ragowa jiya, "my kakus ina kwana" ya fad'a cikin tsokanar ta.
Shan toka/kunu kaka tayi ba tare da ta bashi amsa ba, kan yaloluwar tabarman su ta nufa da kwanon tuwonta ta fara ci....Dariya ya saki d'omin ya san dole dama za a yi hak'an
Kan tabarman ya zauna gefen ta ya kara cewa "haba tawan kiyi haku'ri kinji"
Sai data kai wata katukar loma kana tace" k'ullum sai ka gama yin son ranka sai ka wani ce in yi haku'ri, toh baru kaji a yau sai ka fitar da yarinyar nan daga gidannan bazata sake kwana a nan gidan ba, ko tausayin ta baka ji, jaririya da ko cibiyar bai gama nuna ba ka dauko, nama rasa wacce uwa ce mara tunanin ta baka 'ya sabuwar haihuwa har ka kawo ta gidan nan cik'in ruwan sama, fisabilillah fa" kaka ta karasa maganar cik'in masifa kana cik'in daga murya.

Jikinsa yayi sanyi, d'omin d'uk rigimar su yana matuk'ar son kakar sa haka itama. Cik'in muryar daya san zata tausaya masa yace "ki gafarceni k'aka, banyi da niyyar bata miki rai ba, sannan tsananin tausayin wanna baby'n yasa na har na d'auko ta a hanyar dawowa na daga gareji Cik'in kwali...."
"Cik'in kwali kuma kuma Nu'aymu?" Kaka ta ce tana tsame hannunta daga Cik'in tuwon
"kwarai kaka Cik'in kwali ,nan ya shiga bata labarin yand'a ya tsince ta.....
K'uka mai ciwo k'aka ta fashe da shi tace " Allahumma ajirni fi musibati wa aklifni khairan minha, duniya ina zaki damu ne? Yanzu saboda rashin imani uwa ta yar da dan data haifa da cikinta, shin yaushe zamu yi hankali ne, tayaya masifu da rashin cigaba bazasu iya mana yawa ba, muna aikata manyan laifuka, yanzu meye laifin wanna jinjirar da bata san komai ba, wai saboda toshewar basira da tunani kayi cik'in da wata tara ka haifeshi tsannan ki ce zaki ji kunyar rainon dan ko yar dazai iya jikan ki a duniya, wasu na nema ido rufe wasu na yar wa, shin wanna data yar da jaririya, bata san wani hali zata shiga ba, zata rayu ko zata mutu, hannu na gari zata fada ko akasin haka, kuma mace ce fa, mace da rayuwar ta ke bukatar kulawa, sanya ido, hadi da bata tarbiyya ingantacciyar domin matukar ka tarbiyan tar da ya mace tamkar ka tarbiyarta da Al'ummah ne, shine ta yar da ita bako tsoron Allah, idan Allah ya dauki ranta wani amsa zata bawa ubangijin ta? kai jama'a mu ji tsoron Allah" kaka ta karasa cik'in amo dake nuna cewa tana matuk'ar jin haushin da tsanan wadannan halaiyan daya addabi al'ummar mu a yau...
take wani matsanancin tausayi, da son wanna jaririyar ya ratsa zuciyarta, d'omin shakka babu ta yarda da jikan ta, sannan ta san cewa bazai taba kowa abinda zai cuce ta har gida ba, kawai da farko taji tsoro ne saboda yand'a duniya ta lalace yanzu...

Ajiyar zuciya ya sauk'e maganganun kakan na ratsa zuciyar sa, duk da yana da karanci shekaru amma yana da kaifin tunani. Yana shirin yin magana baby'n ta saki wata atishawa a tare suka kai kallon su gareta
"Nu'aymu sanyi ya shiga jikin yarinyar nan, ooh yarinya Allah ya saki miki" kaka tace tana rike haban ta
Sannan ta kara cewa "in sha Allahu, da hannuna da k'arfina zan taya ka rikon wanna yar, d'omin yanzu girma ya hau kanka ka zama uba, d'omin zata taso da sanin cewa Kaine ubanta, sai a nutsu, eh sai a nutsu saboda kada yarinya ta gado rashin jin magana Allah ya raya mana ita ya taya mu riko, Allah yasa mai taimakon addinin islama ce" kaka ta karasa karshen maganar a zolaye...
"Murmushi kawai ya saki, wani girma na kara shigar sa, farincikin mara mitsaltuwa na ratsa shi jiyake tamk'ar ita din diyar sa k'amar yadda kaka tace...
Kasa kasa da muryar kaka tayi tace " yawwa wani hanzari ba gudu ba, duk wanda ya tambayi ka cewa yar waye kace diyar kanwata ne d'a ta rasu, duk da ba wanda zai tambaya, tunda bamu da abun duniya babu mai rabar mu, kawai inkas(in case) idan sun tambayeka shiyasa na fad'a, kuma koda wasa bana son wanna yarinyar tayi k'ukan uwa a duniya, don haka zamu rufa mata har duniya ta nade kaji ko?"
Jinjina kai yayi Cik'in gamsuwa, karban ta kaka tayi domin yi mata wanka, duk tattalin kaka sai gata ta fidda dari biyun ta tace "kaje kantin iliyasu ka siyo pampas(Pampers) lamba daya ka kawo min maza"
Amsar kudin yayi yace "yau yaushe kaka?"
"Yau asabar, lafiya kake tambaya Nu'aymu"
"Tab... wallahi za'a yi ruwan sama yau, kaka da kanki kika fidda kudi a siyi abu wa mutum, ina mammakon na ki ya tafi?"
"Kaji min dan bazan yaro, yo kayan jikinta ma atika kawata da diyar ta ta haihu zan kaiwa, wallahi da nace sai ka biyani amma yanzu na yafe, don inason wanna diyar sosai mai madarar kyau"
Dariya ta bashi, ficewa yayi yana jin kaunar kakarsa a ransa...


*ASALIN SU*
Malam jafaru dikko dan asalin garin katsina ne, shine da na uku wajen iyayensa kuma auta, bayan ya girma ya fara fita neman na kai, daga kano har Sokoto, wanda a nan ne ya hadu da wata yarinya mai suna zainab, tak'e ya kamu da sonta saboda tarbiyar ta, ba a dauki tsahon lok'aci ba aka daura musu aure kasancewar suna son junan su...
Kasancewar yafi dan samu kudi a sokoto ne yasa ya siyi dan karami fili yayi gininsa dai dai talaka suka ciga'ba da rayuwar su, bayan shekaru hudu zaynab ta haifi da namiji ranar suna yaro yaci suna AHAMADU wanda daga shi Allah bai kara basu haihuwa ba....


BAYAN SHEKARU ASHIRIN DA TAKWAS
A cikin tsayin shekarun nan abubuwa da dama sun faru , wasu sun mutu ciki harda malam jafaru, wanda mutuwar sa ta dakesu ba kadan ba, a cikin tsayin shekarun nan dai Ahamadu yayi aure, ya auri wata yar nan sokoto, suka ciga'ba da rufawa juna asiri cik'in kaunar juna... Bayan shekara daya matar Ahamadu mai suna Amina ta haifi yaro K'yak'yyawan gaske, ranar suna yaro yaci suna *NU'AYM* wanda duk suka dora masa son duniya, sai dai kwana arba'in da haihuwar, mahaifiyar Nu'aym ta koma ga Allah....
Sosai sukayi kukan rashin ta bare ma zainab(kaka) haka kaka ta ciga'ba da rainon sa har ya girma kuma alhamdulillah bai yi wata rigima ba. Haka ta ciga'ba da rainon sa har ya kai shekaru uku, mahaifinsa Ahamadu ya sa shi makarantar private....
Yana jss3 a makaranta Ahamadu ya rasu, sak'amak'on ciwon ciki daya yi kwana daya tal, wanna karon Nu'aym yaji mutuwar mahaifin sa kasancewar sa yaro mai wayon gaske
Haka suka haku'ri suka ciga'ba da rayuwar su cik'in rufin asirin Allah, saidai daga baya komai ya fara kare musu, ko a cik'in yan'uwa babu masu waiwayon su balle har su taimak'a musu k'asancewar yanzu zumuncin da taimkon juna yayi karanci...
Ganin halin babu da suke ciki yasa Nu'aym fara tunanin abin yi domin taimaka musu, sosai yake da tunanin tamk'ar babba, kaifin tunanin da zafin zuciyar nema...
K'asancewar yanzu an cire shi daga private school ya dawo na government saboda rashin kudi, sai yaje wani gareje dake gaba da unguwar su, ya roki ogan zai dinga zuwa koyan aiki, babu musu ogan ya amince, bai rufa wata biyu ba ya fara iya aikin domin har yan kananun gyare gyare zai iya yi, idan ya tashi ogan zai bashi dari uku, hudu haka wata rana har dari biyar....

Da wanna kudin suka dinga rufawa juna asiri har ya bawa k'aka jarin dari hudu, ta kuwa auno lalle ta fara kullawa goma goma kuma alhamdulillah ana dan siya, kullum idan ya tashi daga boko baya dawowa gida direct gareji yake tafiya, domin yana da izu arba'in a kan shi yana kuma fatan matukar abubuwa suka dan daidaita musu zai koma islamiyya, da bayan magariba yake tashi daga gareji, sai yaki dawowa gida su zauna hira shi da abokansa, har tara, goma, yana kaiwa wani zubin, babban abokinsa

Please Login or Register in order to submit comment