Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motsa daga cikin kwalin ba, hakan yasa hankalin na kwanciya, ina sauka a tasha naga ruwan sama ya fara sosai, kwalin cikin hijab dina, cikin sauri na shiga ratsa unguwar har nazo wajen da babu jama'a na ajiye kwalin mai dauke da jaririyar na tafi da mugun sauri, duk da ana ruwa ban tausaya mata ba, domin kiyayyar da nake wa Raliya ya shafe ta.


Tabbas wanna diyar Raliya ce, domin a ɗaiɗai wajen, ranar, da kwanan watan, da shekarar, duka iri daya ne da wanda yaron nan(Nu'aym) ya fada, toh a ranar na raba Raliya da 'yarta.

Bayan na dawo gida sai na fara kukan karya da kiran Al'ameen da sauran mutane, ina sanar dasu batan Raliyan ina kuka sosai, sanar dasu nayi cewa Raliyan ta dage zata zo gidan su, ni kuma a lokacin ina girki, tace in zauna inyi musu girkin yanzu zata dawo, wanna karyar na shiga gayawa mutane ina kuka, kasancewar akwai alaka mai k'yau tsanakin mu ɗa ita, hakan yasa babu wanda ya zarge ni, bayan an kwana biyu, zuwa lokacin har Al'ameen ya dawo, na faki ido na fita zuwa gidan dana ajiye Raliya, sosai ta shiga wari da tsami domin babu wanka, ga kuma jinin haihuwa, hayar mota nayi saboɗa tsaro kana na jata na saka ta a ciki, daidai kofar gidan su na wullar da ita kana na bar unguwar a guje, a lokacin da malam baba ya kira cewa an ga Raliya yashe a kofar gidan, na nuna ban sani ba, har da kuka na, sosai nake Jin tausayin mijina Al'ameen kan halin da yake ciki, a dalilin rashin 'yarsa da rashin lafiyar Raliya, amma ina bazan iya taimakon sa ba, domin bana son ko wacce mace ta rabi mijina, ina tunanin zan yi rayuwa ta ni kadai tare da mijina babu kishiya, domin a tunanin na har Raliya ta koma ga Allah bazata warke ba, tunda ance sai in ta ga 'yarta ne zata samu sauki, ashe diyar ta na raye ban sani ba, wayyo Allah na shiga uku " Mariya ta kai karshen maganar tana birgima a kasa...


Sannan ta dora da ba su labarin yanda aka yi ta saci ADEEL, da kamata da Nu'aym yayi, har kawota police, ta kuma ce a ranar da na sace jaririn nan daka duba dakina da baka ganni ba, domin da hannuna naje na sato wanna yaron....
.


Ai fa nan maganganun suka Shiga tashi kala² kowa na fadin albarkin bakin sa, masu zafi na yi,...

"Allahu akbar kabiran! yau ga Nu'aymah ga iyayen ta, komai yazo karshe, amma domin a tabbatar sai a je a gwada jinin ku(DNA TEST) " kaka ta fada tana jinjina girman al'amarin, yayin da take share hawaye...



Kallon papi Nu'aiymah tayi, sai ta saka dariya mai hade da kuka tace "PAPI kana jinsu? wai ni 'yar su ce? papi ka gaya musu kai ne ubana mahaifi, ni ban taɓa ganin su ba, papi ka....." Kasa karasa maganar ta yi sak'amak'on wani duhu daya gilma ta idanun ta, sosai wanna labarin ya yi wa k'wak'walwarta yawa da nauyi, domin akwai sarƙaƙiya cikin labarin da zallan mamaki, kunnuwan ta sun gaza daukar su, nan ta fada jikin Nu'aym ta suma, Cikin sauri Al'ameen ya tari jaririn dake hannunta ya rungume...

Yayinda Nu'aiym ya rungumeta cikin zafin nama yace "Babyyyyyyyyyyyyy!" cikin fitar hayyaci da diriricewa....





Share fisabilillah



Comment


Noor😚


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*WATTPAD*
@NoorEemaan







EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




Page 69-70

...........Amma ina baby'n Papi bata motsa ba, sosai hankalin su ya tashi, bare ma Nu'aym, kara jijjiga ta yayi yace "please baby wake up! Nine mahaifin ki, nine komai naki, ki tashi please karki min haka, kaka kin ga abinda kika janyo ko? Miye amfanin fadin gaskiyar? ga halin da gaskiyar ya jefa baby nah a ciki" ya karasa yana jijjiga ta ɗa ƙarfi, jiyoyin kansa sun mike sunyi rudu² alamun tashin hankali da bacin rai...




"Na shiga uku ni zainabu, Nu'aiymahtou ki tashi dan Allah karki mana haka, wayyo dana sani ban tona sirrin boye ba" kaka ta fada tana sharban hawaye da majina...



Cikin zafin nama Nu'aym ya dauke ta ya dora kan kafadun sa ya nufi hanyar waje da ita cikin tashin hankali, Al'ameen da Raliya dake sharban hawaye da kowa dai suka mara wa Nu'aym baya, bayan Al'ameen yace a mayar da Mariya a rufe har su dawo, larai kuwa ta tasa keyar ta tana hadawa da bugun ta har cikin guide room....




Wajen gate din Nu'aym ya nufa, duk kiran da kaka take masa bai amsa ba, burin shi kawai ya sada Nu'aiymah da hospital...

Mota Al'ameen yace kaka ta shiga su cimma Nu'aym a waje, ai kuwa ta shiga, haka ma sauran yan'uwan kowa ya faɗa mota.
fitar su ke da wuya suka ga Nu'aym ya tari keke napep har ya shige, hakan yasa su bin bayan shi....



Basu wani jima ba suka isa babban asibitin private, Sallamar mai napep Nu'aym yayi ba tare da ya tsaya amsar sanji ba ya nufi asibitin cikin gudu....





Ganin emergency ya sanya nurse suka turo gadon nan na marasa lafiya zuwa gaban Nu'aym, kwantar da ita yayi, kana cikin sauri ya shiga turo keken bai ma bari nurses din sunyi aikin su ba, domin a ganin sa baza su yi sauri ba.



Sai da ya shigar da ita emergency ward kana babban doctor din ya bukaci ya fita domin suyi aikin su, ba dan yazo ba, ya fita waje ya zauna yana dafe kan sa dake mugun Sara masa, hakika bai taba tunanin zuwan wanna ranar ba, bai taba tunanin zai ga wanna tashin hankalin ba...


Haka su kaka suka zauna a reception suna jiran doctor ya fito, Yayinda Nu'aiym ke bakin kofar dakin da take kwance yana jiran doctor ya fito, yaji halin da baby'n sa take ciki....



Tun Nu'aym yana kirga mintuna, ya dawo awanin, sosai hankali shi ya tashi, haka ma na su Al'ameen, kaka kuwa tun tana kuka muryar ta na fita har ya d'awo baya fita...


Sai bayan awa hudu likita ya fito yana share gumi, cikin sauri Nu'aiym ya nufi shi yana tambayar wani hali take ciki? Haka ma su kaka suka marmatso gaban likita suna jiran ya basu amsa, ajiyar zuciya likita ya sauke kana yace a biyo shi office....



Ai fa Nu'aym ne a gaba, bayan sun shige office din, Amma yayi musu kadan Saboda yawan su, hakan yasa wasu ke a waje, cire glass doctor yayi yace "ku kwantar da hankalin ku, shock ne ya kamata hakan yasa zuciyar ta bugawa da karfi, amma zata iya farfado wa a ko wani lokaci in sha Allah" ajiyar zuciya mai sauti Nu'aym ya sauke, wanda yasa su jin tausayin sa...




********


A tak'aice dai, kwanan Nu'aiymah biyu kana ta farfado da sunan papi a bakin ta, nurse da ta zo duba ko ruwan da ake mata ya kare, tayi saurin fita domin sanar da Doctor, a tare suka dawo da Doctor'n nan ya duba ya ga lafiyar ta kalau, sai rashin kwarin jiki.....




"P...pa..pi" likita yaji muryar Nu'aiymah ta daki dodon kunnen sa, a hankali.



"Sorry patient bari a kira miki shi ko" Idanunta a rufe ta jinjina masa kai, Yayinda hawaye yake zuba ta kunnen ta.



Fita likita da nurse suka yi, ai kuwa suka yi kicibis da Nu'aym "kaine papi ko?" Likita ya tambaya yana kallon Nu'aym ɗin.


"Eh nine" nu'aym ya fada cikin rawar baki.


"Sunan ka kadai take ta ....." Ai bai tsaya jin karashin ba, ya fada dakin, girgiza kai likita Yayi yana mamakin wanna shakuwar dake tsakanin su...



Taran likita su Al'ameen sukayi suka hada baki wurin fadin

"likita zamu iya shiga?"



"Eh toh! Amma banda hayaniya dan Allah" ya fadi haka suka Shiga wani daki da nurse, ɗomin duba marasa lafiya...

Bakin gadon Nu'aiym ya karasa da sauri, hannun ta ya riko cikin nasa, Yayinda yake shafa kanta yace "b...ba..by, how are you feeling now?"


Sosai abubuwan da suka faru suka dawo k'wak'walwarta, kuka ta fashe da shi tace "pa..pi am not fine, zuciyata ba dadi, papi is that true? Gaskiya ne cewa ba kaine ubana na ba? Na san karya ne ko papi nah?, dan Allah kace karya ne, bani da kowa sai kai da kaka ko? Tayaya yanzu zaku ce ba kune ahalina ba, shin kun gaji da zama da ni ne....."




"Shhhhh! Baby stop that" Nu'aym ya fada yana dora hannun sa kan labb'an Nu'aiymah yayinda idanunsa suka yi jajur kana ruwan hawaye ya cika cikin su taf...



"To gayamin papi, ina mahaifiyata? Duk lokacin dana tambaye ka bacin rai kake nunawa? Shin wacece mahaifiyata, ko bata duniya ne papi, dan Allah ka fadamin, a yau ka warware min komai papiiiiiiiiiiiiii" ta fada cikin kuka har wani sama² numfashin ta yake, duk da ta gama sanin komai dangane da rayuwar ta, amma brain dinta ya toshe, tamk'ar wacce bata fahimtar komai haka ta dawo...



"Nice mahaifiyar ki" suka ji muryar Raliya ya daki dodon kunnen su.

a zubure Nu'aymah ta juya, soaai ta kurawa Raliya dake kuka ido, ƴayinda ta kasa magana.



"Yanzu wata gaskiyar ko nace shaida zai bayyana kan shi" Al'ameen ya fita da sauri, basu fahimci inda kalaman sa suka dosa ba, hakan yasa suka bishi da kallon..



Mintuna biyar suka d'awo tare da likita, jinin Al'ameen da Nu'aiymah ya dauka domin ayi musu DNA TEST.



Bayan awa d'aya da rabi result ya fito, likita ya kawo, result kuwa ya nuna NU'AIYMAH JININ AL'AMEEN CE...



Ai nan wasu sabon ƙoke_ƙoke ya fara, cikin kuka Raliya tace " my daugther come, please come to me, come to your biological mother (ƴata zo gareni, dan Allah ki zo gareki, kizo ga mahaifiyar ki ta asali)" tamkar status haka Nu'aiymah ta tsaya.



Nu'aym ya mikar da ta, hannun ta riko har gaban Raliya dake sharar hawaye, kallon juna suka yi na yan mintuna kana Nu'aiymah tayi saurin fadawa jikin ta, wani yanayi mai dadi da bazai mitsaltu ba ya shiga ratsa ta, sosai wani dumin dadi da iska na musamman ya shiga kada Nu'aiyamah, tabbas uwa daban take, yanayin ne na musamman, Sosai suka k'amk'ame juna suna kuka, a yanda suke manne da juna zaka dauka yan biyu ne masu matuk'ar kama da juna (identical) shekaru kawai Raliya ta fi Nu'aiymah.




Sun jima a haka, Nu'aiym dauke kanshi Yayi, bai san yanda zai kasance ba, in har ace za a raba shi da baby'n shi...


Shima Al'ameen dake sharar hawaye tamkar mace Saboda tausayi ya nufe su, ya rungume Nu'aiymah a jikin sa yana jin raɗaɗɗin bakin cikin shekara sha shida ya kau, wani zunzurutun son 'yar sa ƴa shiga ratsa shi, daga karshe ma rungume su ukun Yayi cikin farinciki, haka sauran dangin aƙa shiga rungume Nu'aiymah kowa na Nuna farinciki sa...



Al'ameen da kan shi ya rungume Nu'aiym, sosai ya shiga godiya da nuna farincikin sa, hadi da Kyawawan addu'a agare shi, haka zalika kaka har kasa Al'ameen da Raliya suka duka a gaban ta suna godiya ga kaka hadi da add'uar fatan alkhairi, haka sauran dangin kowa yayi godiya a garesu, domin add'ua kadai zasu iya musu, amma duk wata Kalmar godiya tayi kadai, haka zalika baza su iya biyan su dawainiyyar da suka yi Nu'aiymah ɓa, sai dai suyi musu add'uar fatan alkhairi kawai...




Sun jima suna hira sosai, tamk'ar sun saba, Nu'aiymah zaune jikin Raliya da Al'ameen, da dangi ta ko ina, meya fi wanna farinciki? Fuskar Al'ameen tamkar farin wata dan farinciki, kowa dai ka gani yana cikin farinciki, nan aka shiga kiran yan'uwa na nesa dana kusa cewa anga 'yar raliya da aka sace shekaru sha shida da suka wuce, sannan an ga sabon ɗan da ta haifa, kuma ikon Allah sai ya da kani suka hadu, sannan mutumin daya sinci yayar(Nu'aiymah) shine ya tsince kanin (Adeel) wanna ba komai bane face ikon Allah, sun kuma yi mamakin jin cewa Mariya ce mai wanna rashin imanin, wani karin farinciki kuma Raliya ta warke. Ai fa nan labari ya shiga zaga dangi na nesa dana kusa, Sannan kowa yace dole zai so domin ganin Nu'aiymah...



ADEEL ne ya katse musu hira da kukan sa, mika wa Raliya kaka tayi tace "'yar nan, bashi ya sha, acici mala'ikun tauna ya fara, ya ma yi kokari tun shekaran jiya madara yake sha, bayan ga uwar sa" dariya suka yi jin kaka tace acici mala'ikun tauna...



"Baby zo ki ƴi sallar da ake bin ki kinji, na siya miki MacLean da brush" ya fada yana zura hannu a aljihu, ya matso MacLean din a brush kana ya mika mata, bata fuska tayi tace "PAPI ni sai ka raka ni"



"your wish is my command 'yar papi" ya fada yana riko hannunta.



"Kai Nu'aiymahtou yanzu har bandakin sai ya kara ki saboɗa sharri, wanna iyayin har ina, kai ma Allah ya kara, ba kai ka gama shagwa'ba ta ba" kaka ta fada.



Take kuwa Nu'aym ya gwaleta, ai fa nan yan dakin suka sanya dariya, domin draman ya burge su ainun.



Da Kallo su Al'ameen suka bi su Nu'aiymah, basu damu ba, domin sun sa Nu'aiymah ta riga ta saba da papi ta yanda rabuwar su abu ne Mai wahalar gaske, kuma zai dauki lokaci kafin ta daina masa kallon uba.



Nan kaka baki ya bud'e, ta shiga basu labarin draman su, da gwaletan da suke yi, da shakuwar su, hadi da yarintar Nu'aiymah. Sosai su Raliya suka sha dariya Kuwa, duk da sunyi mamakin tsananin shakuwar su, domin wasu ma tare da uban su na ainahi suke, amma basu yi irin wanna shakuwar ba, sun kuma ji dadi da Nu'aym ya taka rawar matsayin uba agareta, ya bata tarbiya, domin za a iya cewa Nu'aiymah rainon papi ce! Tarbiyan papi ce!! amma kaka ma ta taka muhimmiyar rawa a rayuwar 'yar tasu, take Nu'aym ya samu matsayi mai girman gaske a zukatan su, bare ma Al'ameen da Raliya...



Har Nu'aymah ta gama rama salolin dake kanta hajiya kaka bata daina basu labari ba, ganin jikin Nu'aiymah garau yasa doctor ya basu sallama...



Su Al'ameen sun so tafiya jigawa a yau, amma kaka tace su tafi gida wajensu su kwana idan yaso gobe sai su tafi, tunda yamma ya fara yi, basu musa ba, domin suma zasu so su ga muhallin da yar tasu ta rayu tsahon shekaru masu yawa, bayan duk sun biya charges din asibitin kana kowa ya shiga mota suka nufi gidan....





Share fisabilillah

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*WATTPAD*
@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌

71-72


...........Su Raliya suka saki jiki a gidan, wanda hakan yayi wa kaka dadi, nan fa Nu'aymah da kanta ta shiga kitchen tayi wa iyayen ta girki tare da taimakon Papi'n ta, sosai su Al'ameen suka yi mamakin shakuwar ɗaƙe tsakanin papi da babyn'sa.
Kaka kuwa tana gefe tana basu nishadi hadi da labaran ban dariya...




Bayan ta gama, ta zubawa kowa nasa a kyakyawan plate, k'asancewar dining ɗin zai yi musu kadan, hakan yasa suka shimfud'a tabarma babba suka zauna a farfajiyar gidan...




sun yaba da girkin na Nu'aiymah, domin duk ƙanƙanatar shekarun ta, ta iya girki sosai, wanɗa kaka ce ta koƴa Mata, gashi kuma Allah ya yo ta a mace mai son yin girki, mai kuma son koyan girki kala² amma da an biyewa ta Nu'aym da ko indomie bazai bari ta dafa ba, a Cewar shi tayi kankanta da Shiga kitchen...




Nu'aiymah dai yau tare da mahaifiyarta Raliya ta kwana, jikin ta ta shige, tana jin dumin uwa na ratsa ta, sosai suka yi hira, ta dinga b'awa Nu'aiymah labari irin murnan da son da Al'ameen ya dorawa cikin ta da sauran su.
Adeel kuwa wajen kaka ya kwana, domin dai Raliya tace ita bazata kwana dashi ba, domin kada ya hana ta hira da 'yarta, dariya kaka tayi ta kuwa dauke shi suka kwana tare, tunda akwai madarar sa ma da sauki...



Sai karfe biyun dare bacci barawo ya dauke su. Washegari da safe duk sukayi wanka, suka karya, Yayinda su Al'ameen da suka kasance maza suka kwanta a garejin gidan, brush da wanke kafafu kawai suka yi, domin a cewar su baza su shiga bandakin cikin gidan ba, idan sun je gida sayi wankan. Nu'aiymah da kanta ta kaiwa su Al'ameen abinci a garejin wajen gidan, sosai kuwa Al'ameen ya zaunar da 'yar shi kusa ɗashi ya dinga janta da hira, manager da Abba suna gefe suna kallon su da murmushi, sai da zasu fara cin abinci ta basu waje...




Nu'aiymah, kaka, papi, kamar kullum a tray daya suka ci abinci, wanda wanna karon Raliya ta saka hannun ta domin su ci tare, saboda ji tayi sun burge ta, haka sauran mutanen falon.




Bayan duk sun gama, sun yi shirin tafiya, Al'ameen ya kira Raliya yace tayi wa kaka magana zasu shigo, ai kai tsaye kaka tace su shigo.
Bayan duk sun shigo an sake sabon gaisuwa, nan Al'ameen yayi gyaran murya alamun akwai magana mai muhimmanci da zai yi, hakan yasa falon daukan shiru....



"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Godiya ta gabbata ga Allah mai kowa mai komai, daya nuna mana wanna ranar mai dumbin farinciki, domin na ga 'yata da ta bata lokaci masu tsayin gaske, da kuma bayyanar jaririna na, kuma abin farinciki a hannun mutane masu dattako da mutunci suke, ina kara godiya a gareku Sosai Nu'aym da kaka.


Ina son kowa ya shaida, na mallakawa Nu'aym company nah wanda yake aiki a yanzu, duniya da lahira, bawai na biyaka hidimtawa 'yata da dana daka yi ba, har Abada bazan iya biyan ka ko da kwatan hallacin ka gareni, dama ahalin ba" Al'ameen ya fada yana kallon Nu'aym.




Cikin girmamawa Nu'aym yace


" A'a bazan karba ba, nagode sosai "

"A'a Nu'aym kar muyi haka da kai, kaka ki sa baki, na sani cewa ban isa in biya shi ba, idan kuma bai karba ɓa, wallahi bazan ji dadi" Al'ameen ya fada yana kallon kaka...




Murmushi kaka tayi, tabbas alheri danko ne, a yau Nu'aym zai mallaki company Saboda kula da ragamar rayuwar Nu'aiymah da yayi fisabilillah, shin da ta nuna wa Nu'ayimah tsana da wani ido zata kalli iyayenta masu mutunci a yau.



Kallon Nu'aym tayi tace "Nu'aiymu jikana, ka karba kaji, mayar da hannun kyauta baya babu k'yau"




Bai musa wa kaka ba, yayi godiya sosai ga Al'ameen.



"Sannan muna neman alfarma, ku bamu aron Nu'aiymah tayi kwana biyu, domin ta gana da dangina da na mahaifiyarta"



Jinjina kai kaka tayi tace "toh shikenan, babu matsala, hakan ma yayi k'yau"




Allah sarki Nu'aym gabansa yayi wani mugun hargitsewa, sosai yaji wani abu ya soki zuciyar sa, kenan baby'n sa zata tafi ta barshi, wani kewar tane ya fara kama shi, bai bari sun hada ido da kowa ba, domin kada a fahimci yanayin sa.




Mikewa sukayi, domin tafiya, nan Al'ameen yace kada Nu'aiymah ta dauki kaya ko daya, komai na buk'atar ta akwai a can.
A sanyaye ta mike ta zo gaban Nu'aiym, habarsa ta dago tace "papi na! Mu tafi tare kajiiii" ta fada tana fashewa da kuka hadi da fadawa jikin sa.




Runtse jajayen idanunsa yayi, yana jin kukan ta har kasan zuciyar sa, sosai tausayin su ya kama kowa, haka zalika Al'ameen saurin dauke kansa yayi, domin sam bayaso ya cigaba da kallon su, hakan zai iya sawa ya ce ta zauna tare da su, amma ina bazai iya ba, su ma suna da bukatar ta a Jigawa.



Ganin kukan na ta yaki karewa ne ya saka Nu'aiym dago ta yace "baby yi Shiru kinji, da kaina zan zo in tafi dake kinji Amma sai ki daina kuka ok"





Abin tausayi tace " na daina papi" ta karasa tana share hawayen fuskar ta.



Hannun ta ya riko suka nufi waje, hakan yasaka sauran take musu baya, mota duk suka shiga, ai fa ganin baby'nsa cikin mota ya saka shi jin wasu kwalla sun cika masa ido, amma Saboda tsananin jarumta da dakewa bai bari hawayen ya zubo ba, da sauri² ya shige cikin giɗan Yayinda kaka ta fara sharban kuka ganin da gaske yau bayan shekaru goma sha shida Nu'aiymah zata yi nesa da ita.



"Allah ya tsare Nu'aiymahtou, Allah ya kiyaye hanya, ya kaddara saduwar mu, ki dawo da wuri kinji, zamu yi kewar ki sosai" kaka ta fada cikin kuka tana nufar cikin gidan da sauri domin tsayuwar ta a wajen kara karya mata zuciya yake.




Sosai jikin su Al'ameen ya yi sanyi, a ransu suna jinjina kaunar da su papi ke yiwa Nu'aiymah.



Da kyar Raliya ta lallaba Nu'aiymah tayi Shiru, sai sauke ajiyar zuciya take yi, police station suka nufa, amma Al'ameen kadai ne ya shiga, babu bata lokaci Al'ameen ya bukaci a fito masa da Mariya, ai fa ta kara shan duka gabadaya ta ɗawo babu kyau gani, Kallo daya Al'ameen yayi mata ya dauke kansa, shi kam sai yanzu ma yake ganin munin ta.



Takarda ya rubuta mata saki uku, yace daga police station din nan ta nufi gidan su... ya kuma umarci larai da ta sake ta, kana ya basu kudade masu yawa ya fice..., sosai Mariya ta shiga zunduma ihu tana kuka, Kira take "Alameen kada ka min haka, wallahi ina sonka, sonka ne ya kai ni yin wadannan abubuwan dana aikata, wayyo Allah saki uku ka min" birgima ta shiga yi a kasa, gabadaya muryar ta ke tashi a police station din, ai fa nan larai ta kora ta waje, ta kuma bi motar su Al'ameen da gudu, amma ina sunyi nisa, nan ya sanar da yan cikin motar hukuncin daya yanke a kanta, ai kuwa babu wanda yaji komai a ransa, domin bakin halin ta yaja Mata...



Sun yi tafiya mai tsaho kafin su ka isa Jigawa, gidan su Al'ameen aka wuce da Nu'aiymah domin ta fara ganin dangin ubanta, kana sauran motocin suka kai su Raliya gida.



Sosai Nu'aiymah taga gata, kowa ya dinga haba² da ita, kallon daya za a mata asan jinin Raliya da Al'ameen ce! Nu'aiymah kuwa ta saki ciki da su, duk da kewar kaka da Nu'aym yana nukurkusanta ba, ai kuwa da kyar bacci ya dauke ta a ranar Saboda KEWA.




Har washegari dangi nata zuwa ganin Nu'aiymah, Ana musu barka, Mariya kuwa zagi da tsinuwa ta sha shi a bakin mutane kam.




Kwanata biyu a gidan su Al'ameen kana aka kaita gidan su Raliya, kamar yadda ta ga gata da kulawa a dangin su Al'ameen haka ta gani ana su Raliya Sosai, kwanan ta biyu a gidan kana al'ameen ya kwashi y'ay'an sa da matar sa zuwa gidan sa.




A lokacin da Nu'aiymah tayi tozali da daki na musaman wanɗa aka ware domin ta tun kafin to zo duniƴa, an zuba kayan wasa, na jarirai iri daban² ba karamin tausayawa iyayen ta tayi ba, ta kuma jinina kauna da suke mata.



Duk da har yau mamakin bai gama barin ta ba, ta yanda ko mai ya juye ya sanja cikin kankanin lokaci, hakika samun mutane kamar Papi'n ta da wahalar gaske ta aiyana a ranta...




***********



Zaune Habib Husain yake a office din sa, mahaifiyar sa ta bugo masa waya ƙan cewa yazo Jigawa idan ya samu lokaci, domin Allah ya bayyana diyar Raliya da ta bata tsahon shekaru, sannan Raliya ta warke, nan dai ta bashi labari a taikace...

ya kuwa ce zai zo cikin satinan domin ganin cousin dinsa da ta bata, ya kuma jinjina muguntar Mariya, domin babu wanda yayi tunanin tana da wanna mugun hali haka....




Lumshe idanunsa yayi, sak'amak'on tuno Nu'aiymah da yayi, ko wani hali take ciki yanzu Allah masani, abu daya ya sani cewa yana son Nu'aiymah sosai, amma tuna irin warning da papi yayi masa ya ke sanyaye masa guiwa.
Gashi kuma yaga Nu'aiymah bata neme shi ba, hakan na nufin tana jin maganar ubanta ko kuma yana da matsayi mai girma a ranta, domin shi dai bai yarda cewa NU'AYM shine uban Nu'aiymah ba, domin akwai kuruciya a tare dashi kam. Ɗuka wadanan maganganun a ransa yake yin sa.



Bayan kwana uku da gama wayarsu, ya nufi jigawa, direct gidan Al'ameen ya fara zuwa, nan ya tarar da wasu yan'uwa sun zo barka, zama yayi aka gaisa da yan'uwa, cikin farinciki da raha...

Kallon shi Raliya tayi tace "dama san kanwar ka, ka kazo gani, domin kai dai kam baka ziyara, sallah take bari ta fito" dariya yayi, yana Sosa keya.



Bayan mintuna goma kuwa Nu'aymah ta fito, da fuskar habib Husain ta fara tozali, zaro ido tayi sosai cikin zallan mamaki, haka ma Habib Husain,

Please Login or Register in order to submit comment