Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gantalalliya bansan ciwon kai na ba, shine bazaki iya taho min da komai ba, ai shikenan kuma wallahi sai na dauka na ci, ɗama bakincikin ɗanɗanawa kuke min" tana gama fadin haka ta wawuro springs rolls hadi da zobon ta nufi dakin ta harda saka key kana ta dan daga murya yanɗa zasu ji tace "marasa kirki, kuma sai na cinye duka zan fito"..........


(Am so sorry habibtie's for keeping you waiting, ina busy ne kwana nan, wanna ma a tsatsaye na muku shi💖)








Thank you for reading Papi ne!💞






Share
Vote
Comment


Nooreemaan
07082281566



🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*WATTPAD*
@NoorEemaan









EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌


39-40

............... Wata dariya suka sanya, Nu'aiymah har da kwallan mugun ta, kaka rigima, toh meƴe abin shiga dak'i har da sa key? Bayan Nu'aym ya gama cin egg roll din shi, ya ce ya ishe shi, kana Nu'aymah ta shiga dakin ta domin ta sanja kayanta, wasu riga da skirt na wani material mai taushi ta sanya daƴa fidda hadaddiyar surar ta, dankwalin ta yana a k'anta, domin tasan idan ma bata d'aura ba papi sai ya sa ta d'aura di'n, kasancewar bata son daura dankwali...




Turare ta fesa sama sama domin Nu'aiymah akwai son k'amshi, man zafin da take shafawa papi ta dauka kan dressing mirrow dinta ta fito, hakan yayi daidai da bud'e kofar da kaka tayi, wata dariya ce ta sake tahowa Nu'aiymah tuna abinda kaka tayi dazu, cikin tsokana tace

"kaka kin fito"

Bata rai kaka tayi tace "toh bazan fito ba? Kaji min ja'irar yarinya, bayan kin gama min rowa zaki min magana, yanzu dan baki da kirki 'yar nan akwai abin dadin nan amma bakya siyo min?".




Gimtse dariyar ta tayi, tasan idan bata amsawa kaka ba, tofah yau ta dinga mita kenan har dare, dan haka tace


"Toh kaka zan dinga siyo miki kullum kinji"


Washe baki kaka tayi kana tace "ko ke fa 'yar albarka" ta karasa tana shiga toilet.



Da kallo Nu'aym ya bi kaka yana murmushi, a ransa yana add'uar Allah ya kara wa kaka tsahon rai domin ita din farincikin su ce.....



"Papi bari na shafa maka man ka, na manta da safe"


"Ai dole ki manta da safe, baby rigima" inji Nu'aym idanun sa kafe k'anta, har yau ya kasa yarda cewa baby'nsa dake jaririya ce ta dawo budurwa mai kyawun gaske....



Boyayyen ajiyar zuciya ya sauke, ya lumshe idanun sa, kana ya ware su kan fusk'ar ta... Tana tsugunne gaban sa tana shafa masa man zafin, bud'e kofar bandakin da kaka tayi ya sanya shi dauke idanun sa... Yace "baby kinyi sallah kuwa?"

Kallon shi tayi tace "Papi nayi tun a masallacin school dinmu"

Jinjina kai yayi, ta cigaba da shafa masa man ta na zuba masa surutu, nan dai suka cigaba da Hirar su, harda da kaka dake basu labari suna ta dariya, bare ma Nu'aiymah har da kwalla, Nu'aym kam sai dai yayi murmushi.....




****** ******* ******


Bayan sati biyu Nu'aiym ya koma bakin aikinsa cike da kewar su.... Kamar koyaushe Nu'aiymah tayi kuka, hakan ke kara karya zuciyar Nu'aym.


Ɓabban burin shi yanzu ya siya musu gida a jigawan, domin su koma kusa dashi hankalin shi zai fi kwanciya idan yana ganin su tare a muhalli daya.



Bayan kwana biyar da tafiyar Nu'aym, kaka na zaune a parlour da misalin karfe sha biyu na rana tana kallon film a tashar MBC ACTION.


Wani film na fada suke haskowa, kaka fadi take "A'a a'a kai wannan mutanen baku da mutunci wallahi, sai fada kuke kuna zub da jini abu bai yi k'yau ba" wani ihu ta saki ganin an caka wa wani wuka tace

"karka kashe shi, karka kashe yi, wayyo! Kaga mutane masu zuciyar dutse kamar na firauna" abin dariya har rufe fuska kaka keyi, wai kada ta ga yanda aka cake wani da wuka...



Ringing d'in wayar ta ya dauke mata hankali daga kallon fim din da take, daukan wayar tayi, wanda yanzu Nu'aym ya sanja mata zuwa *infinix smart5* a kunne ta kara bayan ta daga tace
"assalama alaykum"

Daga dayan bangaren habib Husain ya gyara zaman sa kana cikin ladabi yace

"kaka ina wuni"

"Lafiya lau, manyan kalau? Sai dai ban shaida mai magana ba"


"Lafiya kalau kaka, sunana Habib Husain, Nu'aiymah ce ta bani number'n ki, na hadu ta ita lokacin data dawo daga makaranta, ban samu kira bane sai yau"




"Ai yo dan albarka, tabbas Nu'aiymahtou jika ta ce, Nu'aiymahtou! Nu'aiymahtou!! Kizo za a yi magana dake" kaka tace cikin daga murya fusk'ar ta a washe.



Nu'aiymah dake kitchen tana hada masu lunch(abincin rana) ta zo falon cikin sauri, a tunanin ta Papi ne, domin ita ta manta da wani shafi na Habib Husain


"Kaka Papi ne?" Tace bayan ta shigo falon

"A'a ba shine bane, karbi katinsa na tafiya a banza"


Amsa tayi ta fito waje, tana tunanin waye?
"Assalama alaykum" tace cikin zazzak'ar muryar ta.

"Wa'alaikumu salam mai kyau nah" cewar Habib Husain cikin taushin murya.



Take ta fahimci mai magana, a fili tace "ina wuni"

"Lafiya lau mai kyau nah, ya kike haba gaɓa daya kin manta dani ko? Gashi ni kin sace zuciya ta, kin hana ta sukuni, tun daga ranar dana ganki kullum cikin begen ki nake, na azabtu da rashin ko da jin muryar ki ne, amma yanzu naji sanyi a raina, fatan kina cikin koshin lafiya?" Ya fada cikin iyakar gaskiyar sa kana cikin kulawa.



Lumshe lumsasun idanunta tayi, masu kama da mai jin bacci, wani yanayi taji a jikinta, domin kalaman sa suka tsaru sosai a kunnuwan ta.

Ware idanun tayi tace "Alhamdulillah ina lafiya"

"Masha Allah naji dadi jin haƙan mai kyau nah, gaskiya naji dadi yanda kaka ta amsa gaisuwata"



Murmushi Nu'aiymah tayi, ba tare da tace komai ba.

"Ki sa min rana mai kyau nah domin in zo gareki, idanuna cike suke da kwadayin ganin ki, please and please karki ce min a'a " ya karasa cikin wani salo mai tafiya da zuciyar wacce aka yiwa.


Murmushi ya subuce mata, ba tare da sani ba, a fili tace "ni ban sani ba, duk ranar da ka so zuwa"

Cikin jin dadi Habib Husain yace "wow! Nagode da wanna damar da kika bani, in sha Allah zaki iya ganin na akodayaushe, bye take care, I Miss you" kit ya kashe kiran.


Ajiyar zuciya Nu'aiymah tana jin wani yanayi a tare da ita, kaf din rayuwar ta babu namijin data saba dashi, sannan yake gaya mata magana mai dadi sama Papi'n ta, amma yau da Habib Husain ya gaya mata kalamai, wanda ba wai tafi jin dadin na Husain din bane fiye da na papi, a'a kawai salon sa ne ya sanya kalaman suka tsaru har suka samu muhallin zama a zuciyar ta...



Falon ta koma domin mayar wa kaka wayar ta, bayan ta duba girkin ta.

"Kaka ga wayar"

Ba tare da kaka ta karbi wayar ba tace "ke! 'yar nan, dama kinyi saurayi ba labari? Oh duniya yarinyar nan akwai ki da zurfin ciki, yanzu da bai kira waya ta ba, bazan sani ba"



Turo baki Nu'aiymah tayi tace "kaka ni fa ba saurayina bane"


"Kaji min ja'ira, idan ba saurayin ki bane, meye na bashi lamba ta? Kinga banason iyayi idan ma kina so, ai ba wani abu bane, daga jin muryar yaron nasan yana da kirki, dan haƙa ina miki add'uar Allah ya tabbatar mana da alkhairi, ai wanna abin farinciki ne"


"Nifa kaka ba fa cewa yayi yana sona ba, kawai ranar nan ne, na dawo daga makaranta shine ya biyo ni, daya matsa min da yawa shine na bashi lambar ki" Nu'aiymah ta fada tana Turo bakin shagwa'ba


Dariya kaka tayi tace "yaro yaro ne, yaro man kaza"

Nu'aiymah bata fahimci maganar kaka ba hakan yasa tace "kaka kin ji wai zai zo"

"Ai ba matsala, Allah ya kawo shi lafiya, yaushe zai zo di'n"


" kaka bai fada min ba"

"Toh ai shikenan, yanmmatan kaka, wai yarinya ta girma, mun kusa samun suriki" ƙaka ta faɗa a zolaye.

"Kai kaka dan Allah faa" Nu'aiymah tace cikin kunya tana barin dakin...



Da kallo kaka ta bi ta tana Dariya, ita kam zata so Nu'aiymah tayi aure a kananun shekarun ta....


Bayan kwana uku, da magriba Nu'aiymah da kaka na zauna kan sallaya sanye da hijab da alama sallar suka gamawa iddar wa, da carbi a hannu su suna ja. Suna a haka wayar kaka ta fara ringing, alamun ana kira, kasancewar wayar na gefen Nu'aiymah ya sanya ta ga sunan mai kiran kamar yanda tayi saving da * Ya Habib Husain.....



Manage please🙏



Afuwan habibtie's in sha Allah daga yanzu ranakun posting sun dawo sau uku a sati, domin wallahi busy da nake ciki ya sanya hakan, bana da lokaci kwata kwata wallahi, ku tayani add'ua kan abinda nake yi yanzu, Allah ya bani sa'a.
ina fatan zaku min haku'ri... Ranakun posting din sune kamar haka monday, Thursday, Sunday. Amma matuk'ar na samu lokaci a sauran ranakun da ban ambata ba, toh zaku iya ganin update, amma kusa a ranku cewa ranakun dana ambata wato litinin, alhamsi, da lahadi suna ranakun da tabbas zaku ga posting.



Ngd sosai da kauna da kuke nunawa books dina, ku sani a addu'oi'n ku👏 Noor na muku sahihiyar kauna💞




#Share
#Comment
#Vote

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*WATTPAD*
@NoorEemaan











EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌



*(Assalama alaykum ya jama'a ina gaida ku my fans a ko ina kuke a duniya da Wanda na sani da wanna ban sani ba. Na fara posting din novel dina na farko mai suna *RAYUWAR FAHEEMAH* nasan wasu sun fara karantawa... dalilin daya sa na sake reposting din labarin Saboda abubuwan daya kunsa, Wanda zan so kowa ya karanta ya amfana, sannan a lokacin da nake littafin mijin Ammina ne sila nayi posting dinshi, sai dai rashin lokaci yasa nake turowa da yawa wani har readmore goma, fiye da haka ma nayi posting a lokaci d'aya, ma'ana complete din labarin na dawo dashi page 10 gaba daya kana a kwana goma. Hakan yasa bakowa ya karanta ba, Saboda yana da yawa sosai, shiyasa yanzu na sake reposting din shi, a yanda yake page by page. A cikin labarin akwai fadakarwa, wa'azantarwa, tsantsar mugunta, soyaayya mai tsafta da babu algus a ciki, da dai sauran su. Dan haka ku biyo ni comment dinku kadai nake bukata already ina da complete din novel din)*



Page 41-42

..........kaka da ta shafa add'ua ta dube ta hadi da cewa "waye ne?"

"Kaka ya Habib Husain ne" ta fada tana nuna wa kaka fusk'ar wayar.

Kaka da ba a iya mata tace "yau naga ikon Allah, toh ni iya karatun ku na boko nayi ne da zaki nuna min fusk'ar wayan? sannan kin bar bawan Allah yana ta kira ana ta ja masa kudi, fisabilillah fa"

Dariya da Nu'aiymah bata shirya yi ba ya subuce mata, "ooh kaka ta ya ya za a ja masa kudi bayan ban daga kiran ba" Nu'aiymah ta karasa tana daga kiran.

"Assalama alaykum" tace cikin sanyin murya

"Wa'alaikumu salam, mai kyau nah kin yini lafiya?" Inji Habib Husain

"Alhamdulillah" Nu'aiymah ta amsa.

"Masha Allah, ina bakin gate dinku"


Gabanta ne ya dan fadi, Saboda yau ne karo na farko da wani da namiji zai zo wajen ta, ba tare da ta bashi amsa ba, ta kashe wayar ta kalli kaka hadi da cewa

"wai yace yana waje kaka"

"Toh ki tashi kije ko?"

Da hijab d'in jikinta ta fita, tsaye ta hango shi jikin motar sa yana danna waya sanye yake da shadda blue color, da ya sha dinkin zamani, tun kafin Nu'aiymah ta karaso wajen, k'amshin turaren sa ya kaiwa hancin ta ziyara, wani lumshe ido tayi, domin k'amshin yayi mata dadi sosai.



Jin takun tafiyar ta yasa shi dago kansa yana sakin murmushi, kana ya mayar da wayar sa aljihu yana jiran isowar ta.



"Assalama alaykum ina wuni" tace kanta na kallon wani gefen

"Wa'alaikumu salam, lafiya lau mai kyau nah, ya gida?"

"Lafiya lau" ta amsa

"Ya kuma kaka?" Husain ya sake tambaya

"Tana lafiya" Nu'aiymah ta amsa

"Mu shiga mota ko? Saboda kada ki gaji a tsaye"

"A'a nan ma yayi"

ta amsa masa, wani yanayi mai kama da bakunta take jin kanta a ciki, domin yau shine karo na farko da ta tsaya gaban wani da namiji bisa radin kanta, Papi'nta shine namiji da ta fi sabawa da shi a duniya, a yau da take tsaye gaban wani da namiji sai take jin wani yanayi a tare da ita.




"Ok yanda mai kyau nah tace haka za a yi" Habib Husain ya fada cikin salon daukar hankali.



Murmushi kawai Nu'aiymah ta sakar masa ba tare da tace komai ba.


Gyaran murya Habib Husain yayi yace "am fadeelah ina so ki bani nutsuwa da hankalin ki please kinji?"


"Toh" ta amsa.



"Maganar gaskiya ina son ki, so bana wasa ba, ba kuma nazo da niyyar yin wasa da rayuwar ki bane, ina so ki bani dama na shigo cikin rayuwar ki domin na nuna miki tsantsar kauna da nake miki"



Shiru tayi kamar ruwa ya cinye ta, k'wak'walwarta ya toshe ta ma rasa tunani da amsar bashi, sun kai mintuna biyar a haka....



ya fahimce ta, domin ita din karamar yarinya ce bata san komai a fagen soyaaya ba, hakan yasa yace
"babu amsa ko? Na fahimce ki, zan baki lokaci kiyi tunani zan d'awo domin jin amsa ta, ki je gida gashi ma ana kiran isha, ki gaida kaka I love you"



Dummm taji Kalmar a brain dinta, take Papi ya fado mata a rai domin shi ke yawan gaya mata wanna Kalmar ita ma ta gaya masa, bata bashi amsa ba ta shige gida abin ta....



Da murmushi Husain Habib ya bita da shi, sai da ya ga shigar ta cikin gidan kana ya saki ajiyar zuciya a fili yace "ki Saba dani a hankali mai kyau nah" ya na fadin haka ya bud'e motar sa ya shige...




****** ******* *******



*JIGAWA*

Bangaren su Raliya kuwa sun je India wanda kusan watan su uku a can, kwararrun likitoci sunyi iya bakin kokarin su gurin ganin cewa an gano matsalar dake damunta sai dai result ya nuna babu wata matsala, gashi kuma a zahiri tana da cutar tabin k'wak'walwa, asibiti kusan 3 Al'ameen ya Sanja domin a tabattar sai dai duk amsar daya ce, sosai kan Al'ameen ya d'aure, kenan meke damun Raliyar sa?




Haka suka d'awo gida jikin Al'ameen a sanyaye, lokacin daya sanar da su baba abinda ya faru sosai jikinsu ya yi sanyi, nan take baba ya d'ora ayar tambaya kan cutar yar tasa...



****** ******* *******

Kimanin wata biyu kenan har yanzu dai babu wani sauki daga cutar Raliya, gabadaya hankalin Al'ameen ya sake tashi, saidai uwar gidan shi Mariya na matuk'ar kokari wurin kwantar masa da hankali....



Kamar yau Raliya na zaune a falo, sai faman hargitse falon take Yayinda Mama da baba na zaune suna tattaunawa kan maganar cutar Raliyan.....

Kawai suka ga ta fara amai gaba daya ta bata jikinta, cikin damuwa mama tace "malam ni fa ban gane wa jik'in Raliya ba , domin haka shekaran jiya tayi aman nan, ga jikinta duk ya sanja, malam bana ko tamtama yarinyar nan na da shigar ciki.......




please Manage🙏 banda lokaci ne, a tsatsaye nayi wanna Saboda cika alkawari, zan sake Baku update ranar lahadi kamar yadda nace.


Share fisabilillah


Comment


Thank you for reading my novel
Papi ne!



NoorEemaan
07082281566


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓



*WATTPAD*
@NoorEemaan







EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




_my people a page din daya gabata nayi mistake, a inda Habib Husain ya zo wurin Nu'aiymah, Maimakon in saka Nu'aiymah sai na sa Fadeelah, toh ayi min afuwan typing error ne, duk da na gyara a lokacin ta Nafessah Aleeyu (sweetheart) ta fada min, amma still wasu sun karanta, toh karku rikice Nu'aiymah zan saka, Thank you so much my feenah for the correction Allah ya bar kauna_







Page 43-44


............... Cikin tsananin mamaki malam baba ya kalli mama yace "anya kuwa? ta yaya hakan zai yu?"



Murmushi mama tayi domin ta fahimci cewa baba bai yarda ɗa zancen ta ba, a fili tace "malam bana tamtama tafiyar su India duba lafiyar ta hakan ta faru"




Shiru malam baba yayi yana juya maganar mama, a ransa yana jinjina kokarin irin na Alameen, "oh yaran zamani sai dai a barsu, basu da haku'ri" baba ya fada a fili



Murmushi mama ta kara yi, ita farincikin ta tunda da aure tsakanin su ai da sauki, kara kallon baba tayi tace


" ya kamata a sanar da shi yaron nan Al'ameen yasan da maganar ko?"


Jinjina kai malam yayi cikin gamsuwa kana yace "haka ne, amma kafin nan zamu kira likita ya duba ta, ba dan ban yarda da maganar ki ba, a'a sai dan mu ƙara tabbatar wa"



"Toh hakan ma daidai ne malam" Mama tace tana sake maida idanun ta kan 'yarta tausayin ta fall ranta...




Babu jimawa doctor yazo wanda shine family doctor din su, bayan ya gama yi mata gwaje_gwajen daya dace ya tafi, yace zuwa yamma idan ya tashi daga hospital zai kawo sak'amak'o....



Nan mama ta kai ta toilet ta gyara mata jikinta hadi da yi mata wanka, nan mama ta kara tabbatar da cewa shigar cikin gare 'yarta domin komai na jik'in ta ya sanja, gashi ta ƙara uban hasƙe.





***** ***** *****


Da yamma kamar yadda likita yayi alkawarin dawowa ya kuwa zo da result din, bayan yan gaishe gaishe ya shiga sanar da su malam cewa Raliyan na da shigar ciki na wata hudu.... Nan ya rubuta magani hadi da abubuwan daya dace ta dinga ci, godiya su malam baba suka yi masa kana yayi musu sallama ya tafi.




"Malam kaji ko? Ni fa na san yarinyar nan ciki tare ta, amma sam ban san cewa ya kai har wata hudu ba, ya kamata a sanar da yaran duka har Al'ameen ɗin" inji mama




Murmushi malam baba yayi kana yace "dole za a sanar dasu, yanzu zan kira 'ya'yyenta, amma banda Al'ameen a bari sai gobe, domin yanzu yana cikin iyalin sa, babu dacewa a sanar dashi gudun shiga hakkin ita Mariya (uwar gidan Al'ameen) a bari gobe da safe sai a sanar dashi"



"Toh" mama ta amsa wa mijin nata, domin tun a zamanin kuruciya bata taba yi masa musu ba, bare yanzu.




Nan baba ya shiga kiran y'ay'an nasa ya sanar dasu, gaba daya sunyi farinciki, sai dai sunyi mamakin ta yanda Al'ameen ya iya kusantar ta duk da bata a hayyacin ta, sai ɗai ba abin mamaki ɓane iɗan aka yi ɗuba da irin tarin soyaayar da yaƙe mata...






*WASHEGARI*
Da misalin karfe goman safe baba ya kira wayar Al'ameen...
Al'ameen dake hanyar zuwa office din shi ya ga kiran ɓaɓa, domin girmamawa surukin sa ya yi parking motar a gefen titi kana ya yi picking call din...

"Assalama alaykum, barka da safiya baba"



Cikin muryar dattako baba yace "yawwa Al'ameen ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah baba"

"Toh masha Allah, nace idan baka wani uzuri kazo ina neman ka yanzu"

"Toh toh baba gani nan" ya fada yana katse kiran Yayinda yaji gaban sa ya dan fadi domin baba bai taba yi masa irin wanna kiran ba.

A fili ƴace "Allah ƴasa lafiƴa"


Take ya juyo akalar motar zuwa hanyar gidan, kasa da mintuna sha biyar ya isa, bai shigar da motar cikin gidan ba, sai a waje da yayi parking.


Zaune ƴa tarar ɗa baba, mama, dama Raliya dake ta barnan ta, hadi da yan kananun maganganun da ba a fahimtar abinda take cewa.
Har kasa ya tsugunna ya gaida surukan nasa, kana ya yi kasa da kansa yana dan satar kallon Raliya da bata san ma yana yi ba.



Gyaran murya malam baba yayi yace "Al'ameen shin kana da masaniya kan cewa Raliya na da shigar ciki, domin sai jiya muka taɓɓatar sak'amak'on amai da take yi, muka kira likita ya yi gwaji ya kuma tabbatar mana da tana cewa cikin ya kai ƙimanin wata hudu yanzu, ga sak'amaƙon gwajen nan"



Hannu Al'ameen yasa ya karbi takardan, Bata tare da ya ankara ba, murmushi ya subuce masa, kenan making love da yayi da Ita a India Allah ya bashi sa a ta samu ciki, farincikin da yake ji a zuciyar sa bazai mitsaltu ba, kunyar ganin idon surukan sa ne, ya hana shi kasa nuna farincikin sa muraran...



Cikin ladabi yace "bana da masaniya sai yanzu, amma nayi farinciki sosai baba, kuyi hakuri dan Allah..."



"Kul Al'ameen, baka yi mana komai ɓa, dama so muke mu ji daga bakin ka, Allah ya raba lafiya" ɓaɓa ya fadi haka yana mikewa, Yayinda Mama ma ta bi bayan shi...



Yana ganin fitar su yayi saurin dawowa wajen Raliya hadi da bata wata K'yak'yyawar runguma, ihu tasa tana ƙoƙarin guɗuwa, yayi saurin rufe mata baki yana girgiza mata kai, Turo baki tayi kamar 'yar yarinya kana ta kafe shi da ido kamar mai son tuno wani abu.

Murmushi al'ameen yayi tuno lokacin da ya aure ta, sosai take da shagwaba wanda hakan na burgeshi sosai... tsam ya kara rungume ta yana jin farinciki a ransa, take kuma hawaye suka zubo masa tuno da gudan jinin sa da har yau ba a san a wani duniya take ciki ba, kila tana raye ko tana Mace Allahu masani.


Cikin ta da ya dan tasa ƙaɗan, ya ke shafawa yana jin farinciki mara mitsaltuwa a ransa.


Ya jima sosai a gidan har sai da tayi bacci ya ƙwantar ɗa ita kana ya tafi da niyyar da yamma zai d'awo.



Da yamma ya dawo cike da kayan marmari hadi da Duk abinda yasan zata bukata, malam baba ya shiga fada kan kayan sunyi yawa, haku'ri ya shiga bawa baba, a ransa ƴana ƴaɓa kyawun halin surukin nasa, domin sam bai ɗamu da duniya ba, a kuma wanna turɓan ya dora ƴaƴƴen sa a ƙai, sai karfe takwas ya bar gidan cike da kewar Raliya'nsa da abinda ke cikin ta.



*SOKOTO*

Kwance baby'n Papi take a kan gadon ta, sanye da pencil trouser sai vest white color Yayinda kanta ke sanye cikin hula, sosai take tunanin kan maganar Habib Husain, tama rasa wani irin amsa ya dace ta bashi idan yazo jin amsar sa, ga kullum cikin kiran waya yake yana kashe ta da kalaman sa masu rikitata.
A ranta dai bata jin son so, sai dai kulawar sa gareta ya sanya ta fara tunanin shi, hadi da kokarin koyawa kanta ta yanda zata so shi.
Domin soyaayyar mutane biyu kadai take ji a ranta, da kuma shi ta girma, ma'ana PAPI da KAKA....




Tana cikin wanna tunanin ta ji kiran kaka, a hankali ta sauke ƙyawawan kafafun ta kasa kana ta fito, bata ga kaka a waje ba, haka ma falo, hakan yasa ta nufi dakin ta, zaune ta tarar da ita tana jin ayaba ga waya makale a kunnen ta, zama tayi kusa da kaka tace


"gani kaka"



"Yawwa Nu'aymu gata nan, ubanki ke kira" ta fada tana mikawa Nu'aiymah wayar




Cikin farinciki Nu'aiymah ta amsa tace "Assalama alaykum Papi nah!"




Daga bangaren Nu'aym kuwa yana zaune a office d'insa, lumshe ido yayi jin muryar ta, a fili yace "wa'alaiki salam, baby nah kina lafiya, meyasa naji voice dinki so cool haka, oya gayamin maza wa ya taɓa min ƙe"




Kaka dake jin su tabe baki tayi hadi da cewa "karshen kulawa kayi tsuntsu daga can kazo nan yanzu in ba tsoro ba, yarinya gabadaya ka gama shagwa'ba ta, sai aukin iyayi ta iya"




Kukan shagwa'ba Nu'aiymah ta sanya har dirdire kafafu tace "papi kaji kaka ko? Ni ka dawo please, I have missed you a lot, ka dade wanda karon sosai papi"





Wani yanayi da ba zai mitsaltu ba ya shiga ratsa kwanyar sa, sosai yanayin shagwa'bar ta na ƴanzu ya tafi da shi fiye da na ko yaushe, gudun kada yayi abin kunya da 'yar tasa Zata fahimta ya sashi gyaran muryar, kana ya dauki ruwan gora dake gaban sa

Please Login or Register in order to submit comment