Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nifa shiyasa muke batawa daku wani lokacin, meye dan na fadi ra'ayi na? Talauci abun so ne? Wallahi idan muka fara jin dadi zaka ga yanda zan d'awo nayi frish(fresh) wanna 'yar taka ma zata d'awo kamar ka taba jiƙin ta jini ya fito, kai ma zaka ƙara haske, hmmmm yaro_yaro ne kuna wasa, baku san dadi ba, ku bari Allah ɗai ya kaimu ƙarshen watan lafiƴa"



Haka dai suka cigaba da hira da kaka tana basu nishadi suna dariya, ranar lahadi da yamma kuwa ya tafi jigawan. Ɓayan sun gama shan ɗaru da Nu'aiymah kan lalle sai ya tafi da ita Haka dai da wayo ya lallaba ya baro ta duk zuciyar sa ba dadi.




*JIGAWA*
Safiyar litinin ne mai cike da cunkosa ababen hawa, domin yan makaranta, yan kasuwa, ma'aikatan gwanmnati ke ciƙe a titi domin samun abun hawa.
Nu'aiym na ɗaƴa ɗaga cikin waɗannan tarin al'ummah, babu jimawa ƙuwa ya samu abin hawa hadi da yi masa kwantance company'n kamar yadda aka turo masa address di'n ta email d'insa.



Ɓayan mintuna talatin suka isa wajen ya sauka, bayan ya biya matukin napep din hakkin sa ya nufi cikin wajen.
Tun daga haraban company zaka san cewa ba karamin company bane, isar sa cikin wajen ƙuwa yaga ma'aikata ko wanne sanye da uniform white and black, ɗaga yanda suke duganar da aikin su zai tabattar maka da cewa sun san makamin aikinsu.



Wajen wani matashi dake reception Nu'aym ya nufa, hannu ya bashi suka yi musabaha kana ya tambayeshi ina ne office din manager ba bata lokaci matashin ya masa kwantance office din.


Murmushi da iyakar sa lips d'insa ya sakar wa matashin alamun godiya kana ya nufi inda ya masa kwantancen...


Zaune manager yake ciƙin office d'insa sa haɗaɗɗe, magidanci mutum ne domin zai kai 45Years, babu bata lokaci yayi wa Nu'aym bayanin komai game da tsarin aiki, godiya Nu'aym yayi yana jin farinciki a ransa.


Magidancin mutumin yace "bakomai, ai ka godewa Allah Nu'aym ko?" Jinjina kai Nu'aym yayi.
"Wato nayi mamaki sosai da CEO na company nan yace a baka aiki, domin akwai wadanda suka fika matsayin karatu, ko ni dana dade tare da shi bai bani wanna matsayin ba, amma ya zabe ka, batare da ya ganka ba, gaskiya am Happy for you, congratulations" murmushi Nu'aym yayi kawai, musabaha suka yi kana suka nufi office din da zai zauna.


Nu'aiymah ke tsaye cikin office d'insa bayan manager ya nuna masa yanda zai fara aikinsa. Ga ɗan wani kyakyyawan allo dake ajiye kan table an rubuta sunan shi da wani abu mai kyalli kamar haka "DIRECTOR NU'AYM AHMAD".


Hannun sa ya dora kan kugunsa. Yana kallon hada'dden office din sa, yana mamakin wai shi ke da wanna ƙatafaran office din, bayan gwagwarmayan daya sha, gashi komai ya zama labari. " Alhamdulillah" ya furta cikin murya da amon sa ke fidda farinciki.



Zama yayi kan kujera, yana dan juyi akai, wayar sa ya ciro daga alihun sa, number kaka ya buga... Daga can bangaren kuwa Nu'aiymah dake kallo wani film cikin wayar tayi saurin daga k'iran ganin sunan Papi'n ta.
Cikin zumudi tace "Papi!"
" yes! 'yar albarka ta, yakike?" Nu'aym yace fusk'ar sa dauke da murmushi.


"Lafiya lau Papi, ya aiki ka fara?"


Wani murmushi ya saki yace "eh na fara baby, gani nan cikin office dina"


"Yeeeeeeeeeeh mun zama yan gayu" Nu'aiymah tace cikin ƙuruciya haɗi da ƙaramar muryar ta mai dadi.



Ɗan girgiza kai yayi da murmushi d'auke a fuskar sa yace " baby ɓari na fara aiki zamu yi magana anjima ok? Papi loves you" kit ya kashe wayar yana dan gimtse dariyar sa, sak'amak'on muryar kaka daya ji tana cewa "Saboda bakin hali ni ba za a bani waya muyi magana ba, shima uban naki zai dawo ya same ni ne ehe!"



A fili ya furta "kaka! Kaka!! rikici kenan"




*BAYAN SHEKARU HUDU*






A cikin shekarun nan abubuwa masu yawa sun faru, ciki har da rushe gidan su da Nu'aym yayi.
Flat house (gida mara bene) ne mai kyau, ginin zaman domin yanzu dakuna hudu ne a gidan, sai toilet, kitchen dinsu mai girma hadi da famfo dake gefen wajen rariya. Komai dai ba laifi gwanin kyau. Duk wata Nu'aym na zuwa gida yayi kwana uku kana ya koma Jigawa, ya sanja wa baby'n sa maƙaranta zuwa na private. ɗuƙ in ɗa mai karatu ke tunanin shakuwa hadi da tsananin so na uba ɗa ƴar ke wa junan su ya wace tunanin mai tunani wato dai Nu'aym da Nu'aiymah.







*** *** *** ***




Tsaye wata K'yak'yyawar budurwa take mai kimanin shekaru16 a wani madaidaicin daki tana kokarin sanya kaya da alama wanka ta yi, fara ce sosai mai faffadar kugu hadi da madaidaitan boobs da suka dace da tsarin jik'in ta.

Ɗogo hadi da ciƙaƙƙen gashin ta daya sauka har wajen mazaunanta fake da wani jan ribbon. Zagayayyen fuska gareta mai d'auke da dara _daran idanuwa masu dan lumshewa, dogon hanci, karamin baki, dogayen eyelashes, sai girar ta da bai fiye cika ba, amma a saite suƙe, ƴa yi matuƙar ƙawata fuskar ta. Bata da kiba haka zalika bata da rama domin a murje jik'in ta yake, sannan tsayin ta daidai misali, domin bata sahun gajeru haka zalika ba doguwa bace can.


Wani orange atamfa da black ta sanya dinƙin boubou(buba) daya sha adon zamani, dauri mai V shape kana mai hawa_hawa tayi, wani takalmi mai dan tudu baki hadi da veil(mayafi) baki ta yafa, turare ta fesa a jikin ta, wani dan kunne mai zagaye (round) din nan babba golden color ta sanya a kunnenta sai wani dan hand bag karami mai kyau baki ta dauka.



Daga yanda take shiryawa zai tabbatar wa mutum ɗa cewa ita din ma'abociyar son gayu hadi da tsafta ce.


Kallon kanta tayi a madubi wani murmushi mai taushi tasaki daya bayyana ƙyawawan fararen hakoranta mai d'auke da wushirya a tsakiya, duk da babu ko digon makeup a fusk'ar ta amma tayi wani mugun kyau mai tafiya da hankali d'uk wani lafiyayyen namiji.


Daga waje muryar wata dattijuwa tace "Nu'aiymahtou! Bazaki zo ki tafi ba, kinga dare nayi ko?"



Turo baki tayi irin na shagwaba kana Cikin wani cool voice tace "Gani nan Kaka" tana fadin haka ta bar dakin ta cikin sauri....


Babban sakar gidan dake malale da marbles ta hango kaka tsaye tana cin meatpie ɗata yi ɗazu.


Turo baki tayi tace "kaiii! kaka zaki cinye min duka fa"

"makiyan ubanki Nu'aymu, na cinye din, ba ga filawa( flour)ba, sai ki yi wani, kika bata min rai ma, sai na cinye duka, in yaso kije har Jigawa ki taho da ubanki ya dake ni ehe! Dama kun saba min taron dangi.
Kuma kika yi wasa sai na hana ki zuwa party'n tunda kin san idan Papi'nki yana nan baki isa kije party ba, atoh dan ma zan rufa miki asiri" kaka tace tana cigaba da taunar meatpie dinta.


"D'auko yar jakata na baki kudin adaidaita sahu ki tafi kinga har shida tayi"


Ba musu ta shiga dakin ta d'auko purse din kaka ta mika mata, Dari biyar kaka ta mika mata hadi da cewa "ki kula kinji ko, karki dade, kafin ishaq ki taho, Allah ya kiyaye"




Murmushi ta saki saɓanin ɗazu da take ta bata fusk'a, dama dramar su da Kaka sai abinda ya karu, ƙasancewar rikicin kaka ya karu domin shekaru sun dan ja, kuma abin sha'awa basa daukan mintuna sun shirya.


Nu'aiymah tace "Toh my kaka na tafi" kaka na shirya yin magana wata budurwa da a shekaru zata yi daya da Nu'aiymah ta shigo
wacce ta kasance 'yar makotan su ce, itama cikin kwalliya, tamk'ar ita ce amaryar saboda heavy make up din fusk'arta.


"A'a Baheejja ce?" Kaka tace tana kallon ta.
"Eh kaka, tun dazu nake ta jiran baby ɓata zo ba" (yadda Nu'aym ke kiranta, haka wasu ma ke kiranta da shi)


Tabe baki kaka tayi kana tace "ai wanna da kike gani nawa gareta, sai son jiki bala'i sai kace mage"
Dariya Baheejja tayi yayinda Nu'aiymah ta turo dan karamin bakin ta.
"Maza ku tafi, Allah ya tsare" da Ameen suka amsa kana suka fice suna taku daya_daya bare ma Nu'aiymah dake tafiya tamkar mai tausayin kasa.



7:00pm
Ɗaidai ƙofar gidan ya tsaya da lifan ɗin shi, horn ya shiga danna wa a dalilin sa na son Nu'aiymah ta fito domin matuk'ar taji horn d'insa zata fito da gudu, a karo na shida ya sake dannawa, amma shiru cikin gidan ya shiga da lifan din, yana mamakin rashin fitowar baby'nsa domin ya shirya yi musu bazata shiyasa bai sanar dasu zuwan sa...



Nu'aym kenan ƙyaƙyyawan kana lafiyayyen matashi mai ji da kyau da kuruciya dan kimanin shekaru 31a ɗuniya. Farin sa mai duhu ne, domin za a iya k'iran sa da chocolate color mai dan haske kamar dai kalar yan Ethiopia. Yana da faffadar k'irjin, dogo ne sosai(idan baku manta tun Nu'aym nada shekaru 15 dogo ne bare yanzu) hancin sa bai fiye tsini ba, idanunsa masu dan girma ne, kana lips d'insa madaidaici ne masu kyau da taushi.
Bashi da saje ko daya a fusk'ar sa sai dan madaidaicin gemun sa d'aya kara masa kyau, gashin k'ansa mai dan yawa ya dace da yanayin tsarin fusk'ar sa.



Sallama yayi bayan ya daidaita parking din lifan d'insa, shiru yaji, sai gyaran muryar kaka daya nuna cewa tana sallah. Dakin Nu'aiymah ya nufa yaga wayam, bata nan sai turaren ta da k'amshin ya kama dakin.



Kan wani kujeran roba ya zauna, yana Allah_Allah kaka ta iddar yaji ina baby'n sa take?
Kaka data iddar ta sallah tun dazu a hankali tace "innalillahi, kun ji min ja'irin yaro, babu sanar wa ya antayo, ga 'yar tasa bata nan, nikam na shige su yau" ta fada tana fitowa add'ua take a bakin ta. Domin ita kam bata son rikicin Nu'aym kasancewar shi mai sauri fushi musamman idan akan abinda ya bawa muhimmanci ne.




Sallaya ta shimfud'a a kasa marbles din daya sha gyara kana tace "dan nan dama kana tafe babu ko sanar wa"


"Wallahi kaka, haka kawai naji hankalina ya dawo nan gida, ina wuni na sameku lafiya?"


"Alhamdulillah dan albarka, ya aikin?"

"Lafiya kaka, ina baby ban ganta ba?"

"Eh... uhmm... eh... toh...wato...taje party, na 'yar gidan lami, tun bikin saura sati biyu suka kawo IB ( IV) suka roke ni kan na bar Nu'aiymahtou taje musu....."

"What!?" Ya katse kaka kana ya cigaba "baby ta je Party? kaka tayaya kika bari ta je party, kin san bana so! Bana so tana fita a k'od'ayaushe, baby yarinya ce karama har yanzu, da ranar wuni ne, sai taje musu can gidan tun da ba nisa, amma ki bar ta zuwa party, ga maza a wajen damn it!" Nu'aym yafada cikin murya da amon sa ke fidda zallan fushi da yake ciki yana buga bango da k'arfi da hannunsa.





K'ansa ya rike na yan mintuna kana ya mike zuwa bakin famfo ya kunna kana yayi alwala, sallar yayi ganin har an fara k'iran ishaq.


jin kaka yayi tana cewa "amma yarinyar nan baki kyauta min ba, kin san dai ubanki bashi da haku'ri a kanki, maimaita miki nake 'yar nan, kada ki kai isha'i gashi har an fara kira" ta fada kamar Nu'aiymah'n na gaban ta.



Bayan ya iddar, ya kalli kaka cikin daurewar fusk'ar yace "ya sunan wajen party'n?"


Ba bata lokaci ta sanar dashi, Mik'ewa yayi daga kan sallaya, lifan d'insa ya hau ya fara kokarin fita daga gidan, ko kula kaka dake magana bai yi ba, ya bar gidan hadi da bawa lifan d'insa wuta.



Hall ne mai girma, domin zai iya cinye mutane dari uku, kowa ka gani cikin kwalliya hadi da shiga na alfarma yake. shirye_shirye masu kayatar wa suke yi, wakoki kala _kala ke tashi, Nu'aiymah mazari jikinta har tsuma yake, domin ta kasance ma'abociyar son waka da rawa.



Sosai samari masu ji da kansu suka fada tarkon son Nu'aymah, domin sosai ta tafi da imanin mafi yawan mazan wurin, har da wasu mata sai da suka yaba wa kyawun ta.


Ana cikin haka DJ yasanar da duk Wanda yake da niyyar rawa ya fito domin za a saka waka yanzu. Nan aka sanya waka na Abdul d one mai taken "tani da manu"


Ai Nu'aymah bata san lokacin data tashi ba ta nufi filin rawa, dama Baheejja tun dazu ta isa filin rawan.


Wani irin rawa Nu'aiymah keyi mai burgewa, nan fa samari suka fito, daga masu lika mata dari biyar _biyar sai masu lika mata dubu d'aya _d'aya nan fa kallo ya dawo kan Nu'aiymah, ta burge wasu, yayinda wasu yan matan suka jin haushin ta musamman ganin yanda samarin ke mata barin kudi, Nu'aiymah kuwa rawar ta kawai take, tama manta da cewa kaka tace ta dawo kafin isha, haka samarin suka cigaba da yi mata Barin kudi, tamkar basu san ciwon sa ba.



Daidai lokacin Nu'aym ya shigo wajen. Tun daga nesa Ya hango baby'n sa da tarin wasu samari na yi mata liki, zuciyar sa ce ta buga da k'arfin gaske, runtse idanun sa yayi da k'arfi, wani abu mai daci ya kawo wa makogwaron sa ziyara, wani irin abu ya dinga ji a jikin sa daya kasa gane ko menene...


A hankali ya bud'e idanun sa da suka sanja kala kan fusk'ar baby dake tsakiyar filin har yanzu. Cikin wani sauri ya shiga ratsa ta cikin mutanen yana jin zuciyar sa na tafarfarsa...


Nu'aiymah na cikin rawar taji an cafke hannun ta, cak! ta tsaya a razana ta kalli hannun, take gaban ta ya fadi domin ko shakka babu hannun Papi'n ta ne wanna, domin ga azurfofin sa kala biyu nan irin na maza mai bakin dutse da jan dutse.



Idanunta ne suka kawo ruwan hawaye tun kafin ta kai ga kallon shi, a hankali ta dago kanta ta sauke su kan na Papi, da idanun sa ke fidda zallan fushi da yake ciki, sunyi mintuna biyu idanunsu sarke dana juna, ita tayi saurin sauke idanunta kasa gabanta na bugawa da k'arfin, domin sosai idon sa yayi jaaa....



Cikin wani irin zafin nama ya sake riko hannunta da kyau suka shiga ratsa mutane, Nu'aiymah gaba d'aya jikin rawa yake, kallon Papi'n ta take yayinda yake janta domin bata da kuzarin tafiyar ma...



Suna zuwa wajen hall din ta tsaya kana ta fashe da k'uka tace "Papi" sai kuma ta kasa cigaba da maganar Saboda kukan daya ji k'arfin ta.


Jajaye idanun sa ya zuba mata, hannu ya daga da nufin marinta sai kuma ya tsaya da hannun na sa da ke rawa cak! Yana kokarin controlling temper(fushi) d'insa.


Nu'aiymah kuwa kif_kifta ido ta shiga yi, tana k'amk'ame cikin ta domin gani take kamar zata ji saukar marin.



Jikinsa ta shiga tana matsar kwalla, ya kai mintuna biyar yana sauraran yanda take kuka, duk da yanda yake jin dacin kukan ta bai hana shi ture ta ba.


Lifan d'insa ya nufa yana lalubar mukullin a aljihun sa, sai dai bai gani ba, can ya hango key jikin lifan din, domin ya manta dazu bai cire ba. Dafa kan sa yayi kana ya haye saman lifan din yana furzar da huci mai zafin gaske.



Kamar wanda kwai ya fashe wa ciki ta shiga takawa zuwa garesa, tana share hawaye, duk da uban tsoron da take yiwa babur lifan bai hanata hawa ba, domin tashin hankali data gani a idanun Papi yafi komai daga mata hankali, ta sani cewa son da Papi ke mata bana wasa bane, amma matuk'ar tayi laifi tana ji a jikin ta kafin ya sauko.


Wani kamkame shi tayi saboda mugun gudun da yake shararawa a titi, kuka mai sauti ta saki domin a tsorace take. Wani burki ya ja kiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiiii batare da ya juya ba yace "idan baki rufe min bakin kukan nan ba, sai na fasa shi, baby zan miki hauka, ki kiyaye ni fa" ya fada yana jan kwafa.



Kallon hannu ta dake zagaye da cikinsa yayi yace "cire min wanna hannu naki a jikina" kuka tasa tace

"wayyo! Papi bazan sake ba"

Bai kara cewa komai ba, wuta ya sake bawa lifan din yana jin ciwon kan sa na kokarin motsawa wanda a ranar daya tsinci Nu'aiymah da ya buge da dutse, lokaci zuwa lokaci ciwon kan na damunsa sosai, musamman idan Yana cikin damuwa, ga kukan Nu'aiymah dake sake burkita masa tunanin sa.


Take idanunsa ya fara ganin jira, yana jin wani yanayi mai wuyar fassaruwa na ratsawa shi, batare da ya sani ba lifan din ya kwace daga hannunsa.... Taga_taga suka fara yi a titi, wani ihun kuka Nu'aymah ta saki sak'amak'on faduwa da suka yi daga kan lifan din suka zube warwas kan kwalta....




Vote and follow me on wattpad fisabilillah @NoorEemaan



#Share
#Vote
#Comment


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓






Story/written by
Noor eemaan





Wattpad
@NoorEemaan









EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌





(Kila ku ga typing error🤒)




Page 31-32


.............. Ciƙin zafin nama ƴa ƴi saurin mirginawa ɗa ita, ƴa sanya ta a jiƙin sa domin baya son k'anta ya buge da wani ƙaton dutse ɗake gefen titin. Saƙamaƙon haka kafarsa da hannun sa na nama ya buge jik'in dutsen. ji kake kassssss kasss kakasssssssss alamun yayi gocewar kashi. Runtse idanunsa yayi wani azaba na ratsa kwanyar sa. Baya ko tantama yayi gocewar kashi....



A rud'e Nu'aiymah tashi a jikinsa, domin taji karar, amma ta rasa daga wani sashe na jiƙinsa ƙarar ya fito.


Wasu mutanen da abin ya faru a idanunsa suƙa yi saurin zuwa wajen, Salati suka sanya, kana suƙa hade ɓaƙi wurin furta "sannu bawan Allah".


Sam Nu'aym ba zai iya misalta halin da yake jin kansa a ciki, baya jin zafi hatsarin da yayi kamar yadda zuciyar sa ke masa zafi.


Ciƙin ƙuƙa Nu'aiymah ƙe cewa "Wayyo Papi nah! Kayi hakuri na tuba, Dan Allah ka tashi ina ne kaji ciwo naji wani kara kaasssssss(😹) " ta karasa cikin yarinta da iyakar gaskiyar ta.



Shiru yayi bai kulata ba, duk da zafin da yake ji sak'amak'on kukan ta, abinda yafi tsana yaji ƙo ya ga zubar hawayen ta, amma dole ne ya hukun ta ta.


Wasu samari ne suƙa ce "sannu bawan Allah, zaka iya tashi mu kai ka asibiti, ko mu dauke ka?"


Cikin dauriya Nu'aym yace "a'a abokaina nagode sosai, zan iya tashi, ku dai daga min lifan din"



"Toh normal ne ai, Allah ya ƙara kiyaye gaɓa" samarin suka fada suka cigaba da tafiyar su, bayan sun gama daga masa lifan din.



Cikin dauriya ya mike zaune yana cije tattausan labb'ansa, harara ya ballawa Nu'aiymah dake tsaye tana kuka kana ya mika mata hannun sa, alamun ta ƙama ya tashi, hawaye ta share kana ta mike masa yan siraran hannunta ta kamo nannauyan hannunsa irin sa maza masu kirar k'arfi, da kyar take iya daga hannunsa tana sakin nishi, hannunsa ya zare daga nata, domin ɓazata iƴa ɓa, kana ya mike da kyar...




Kan lifan din ya hau, idanun sa sun kara rinewa domin ba k'aramin jarumta yayi ba wurin taka kafar sa, a sanyaye ta hau lifan din "auchhh" yace kasan makoshi sak'amak'on dafe kafaɗunsa da tayi wurin hawan lifan din, domin tun daga kafadunsa zuwa hannun daman sa yake jin zafin.



Wani luuuuuu lifan ɗin ya tafi, ɗomin ba shida wani kuzari, hakan yasa lifan din ke neman fin karfin ta ba. Ganin da gaske zasu kai kasa ne yasa ya rike babur din da sauri, sosai Nu'aiymah ta k'amk'ame shi tsoro mai yawa ya bayyana a fusk'ar ta, ajiyar zuciya ta sauke ganin basu kai kasan ba.


A hankali yake tuka lifan din da hannu ɗaƴa har suka karaso madaidaicin bakin gate dinsu, sauka Nu'aiymah tayi still hawaye basu daina zuba a idanunta ba.


"Bace me da gani" yace a dan kausashe


Da mugun gudu ta nufi cikin gidan tana kuka, da kallo ya bita har ta bace wa ganinsa, numfashi ya sauke yana furzar da zafaffan huci daga bakinsa, da kyar dai ya shiga cikin gidan ya faka lifan din sa kana ya tafi dakinsa ya murza key.



Kaka na zaune a falo, Nu'aiymah ta fada jikinta tana sakin kuka, "kaka ki bawa Papi haku'ri yana fushi dani kinjiiiiiiii?"


"Ke ni daga ni, shegen iyayinki da rawar kanki ne ya ja miki, da kin dawo da wuri salin alin ba ta yanda zai san kin fita, asirin mu a rufe"


Kukan sakalci ta fasa harda birgema a jikin kaka.


"Kinga ni tashi ki yi sallah"


Tana kuka haka ta fita waje bakin famfo tayi alwala, dakin ta ta shiga ta shimfud'a sallaya kana ta kabbara sallah. Bayan ta iddar ta mayar da sallayar inda yake kana ta fito waje, ɓaƙin dakin papi ta tsaya ta tura taji ya rufe, "Papi please ka bud'e min, wallahi bazan sake ba, kaji" dam! Dam!! Dam!!! Haka ta cigaba da buga kofar, amma shiru bai amsa ba, nan ta sulale kasa tana k'iran sa tana kuka, tun kaka na share ta har ta zo bakin kofar ta rike hannu ta suka koma dakin ta, ta shiga aikin lallashi....


Idanunsa ya zuba wa bakin kofar, yana sauraran duk abinda take cewa, Sosai kukan ta ke daga masa hankali amma yayi shiru kamar bai ji ba, ga hannu da kafarsa da ke masa zugi sosai.


Haka dai Papi da baby'n sa suka kwana rai babu dadi, domin sun jima basuyi bacci ba, gwara ma Nu'aiymah ta dan runtsa.


~~~~~~~~~~~~~~~~~~~
WASHEGARI

Nu'aym na kwance a dakinsa zugi da azaba sun ishe shi, sallar asuba ma da kyar yayi a dakinsa, kana a zaune.


Nu'aiymah ke tsaye ciƙin ƙicin(Kitchen) gaban gas ta na hada breakfast, sanye take da doguwar riga maroon color daya dan kama jikinta, bata tufke gashin ta ba, sai dankwali data d'aura baƙi wanna ya sanya long full hair dinta baje a bayanta da ma gefe da gefen wuyan ya sauka har kasan k'irjin ta.


Chips take soyawa cikin mutuwar jiki, yayinda idanun ta suka yi luhu_luhu alamun ta sha ƙuka ta ƙoshi, duk da haka amma kyawun ta ya fito sosai, Bayan ta gama ta soya musu kwai, already ta dafa ruwan tea daya sha kayan k'amshi, bayan ta gama ta kashe gas hadi da zuzzuba komai a cooler ta jera cikin babban tray ta nufi falo ta ajiye kan dan madaidaicin dinning table dinsu.


"Sannu 'yar albarka, Allah ya yiwa rayuwar ki albarka, ya kawo miji na gari" kaka dake zaune a kan kujera tana jan carbi ta fada.

"Ameen" Nu'aiymah ta amsa a hankali.


"Mahaifin naki bai fito ba? Tara ƴa wuce fa, ya kamata mu karya"


"Bai fito ba kaka" Nu'aiymah tace tana Turo baki yayinda wani siririn hawaye ya zubo mata.


"Toh jike ki kira shi" kaka ta fada.


"Kaka fa bazai kula ni ba, kinga fushi yake dani" ta fada tana sakin kuka da iyakar gaskiyar ta


"Kaji min wani fi'ili, kinsan da hakan kiƙa yi masa laifi? kuma kin san dai baya iya fushi dake mai tsayi, kije ki kira shi, kice in ji ni, domin y'ay'an hanjina sun fara yamutsa wa, in ɓa haka ba nayi nawa karin kumallo"



Ba musu ta nufi dakinsa gabanta na fadu'wa...
cikin dauriya Nu'aym ke fitowa daga toilet d'insa dake manne da ɗakin da alama wanka yayi, ɗaƙƴar ƴake taƙa kafar sak'amak'on mugun kumburar dayayi ga azaba, haka ma hannunsa. Zama yayi kan gado yana runtse idanun sa, 3quarter da armless Jersey ɗa ya fito da shi kafin ya shiga wanka.


A zaune ya shafa mai sama~sama kana ya zira kayan duk a zaunen, dayan hannun sa mai lafiya ya mika kan mirror ya janyo turaren sa ya fesa. Hakika Nu'aym ya cika jarumi domin gojewar kashi nada azaba mai yawa bare nashi daya kwana ya riga yayi tsami.



Daidai lokacin Nu'aiymah tazo bakin kofar sa tana knocking hadi da yin sallama....
Ya dau kusan minti biyar yana jin ta, kana ya ce "bismillah" murƴa a ɗaure.



A sanyaye ta tura kofar idanunta taf da ruwan hawaye, gabansa ta je ta tsugunna hadi da dora k'anta kan cinyar sa cikin sweet voice dinta daƴa haɗu da ƴanaƴin sanyin da taƙe ciki tace

"Papi Good morning?"

Shiru yayi mata, dago k'anta tayi idanunsu suka sarke dana juna, ƴa balla mata harara, hawaye suka biyo kuncin ta, sosai take jin ba dadi idan Papi'n ya na hararar ta, aɓinɗa ɓai taɓa mata

Please Login or Register in order to submit comment