Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya sha fiye da rabi yace
"sorry my baby stop crying kinji zan d'awo soon aiki ne ya min yawa, ok? Suprise zan miki, me kike so na kawo miki, ɓa zan kawo wa kaka komai ba, hakan yayi miki uhm baby?"




"Yeeeeeehhhy! Eh Papi kada ka kawo mata komai, irin chocolate din ranna nake so, sai *Nutella, da Nutella b ready* nake so kajiiiiii Papi nah" ta ƙarasa ciƙin shagwaɓan daya zame mata jiki.



"An gama baby nah mai bakin shan zaki, ki kular min da kanki ok, zamu yi waya anjima, Papi loves you bye"


"Allah sarki mu, wato mu ba mutane bane, da ba za a ce mu kula da kanmu ba, mu daga Sama muka fado kenan ko?



wanna son kan yayi yawa, komai 'yar ka ko? Har da cewa ba za ka siyo min komai ba, to wallahi baku isa ba, daga uban har 'yar idan ba so kake nayi mata kwancen tsaraban ba, to wallahi ka siyo min nawa, nasan kana jina kama jini da kyau"





Nu'aym dariya yayi hadi da katse kiran, oh kaka rigima ya aiyana a ransa yana cigaba da aikin sa, kewar su fall ransa...









Share

Comment

Vote






Thanks for reading Papi ne! Yanzu aka soma🔥🔥🔥




Nooreemaan
07082281566


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓






*WATTPAD*
@NoorEemaan

















EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌





*ina matuƙar jinjina kokarin ki wurin yi min comment kullum, dan haka na baƙi ƙƴautar wanna page din My DARMA kiyi yanɗa kike so dashi*



Page 45-46



........... "Kaka ga wayar ki, nima idan Papi ya dawo zance ya siya min waya, ya daina ma kira a naki, bana so kina yi masa fada"
Nu'aiymah ta fada cikin yarinta da Turo baki.







Tabe baki kaka tayi tace "ai baki birge ni ba, sai na ga ya siya miki company'n wayar da masu yin wayar tuƙunna, kaji min yarinya da iyayi baza a yi masa fada ba, babu dama in fadi gaskiya" kaka ta fada cikin rikicin tsufa.






Turo baki Nu'aiymah ta sake yi, wanɗa ya kasance dabi'a a gare ta, tace "ni wallahi Papi ma ya dawo idan zai koma tare zamu koma jigawan, na barki ke kadai"





"La'ilah! Amma 'yar nan baki da kirki, yanzu aka ce ki barni, ki bi uban ki sai kiyi? Ai shikenan nasan zaman dazan yi dake cikin gidan nan wallahi"


Kaka ta karasa tana bata rai irin tayi fushin nan, yand'a tayi fuska sai abin ya bawa Nu'aiymah dariya sosai, rungume kaka tayi tace "haba kakus tawa, wallahi bazan iya barin ki ba, domin ko unguwa na kwana daya bazan iya tafiƴa ba tare da na saƙa ki cikin idanuna ba, wasa nake kinjiiiiiiii" ta ja karshen maganar a shagwa'be.





Washe baki kaka tayi tace "yauwa 'yar albarka ta, dama nasan baza ki iya ba"...




Nan dai suka dinke abinsu suka dinga hira gwanin burgewa domin dama duk fadan su na yan mintuna ne sun shirya kansa....




*****************************



Bangaren su Raliya kuwa tana samun kulawa daga bangaren iyayen ta, yayyenta, dama mijinta Al'ameen.



Kamar yau da safe a gidan Al'ameen yana shirya wa a dakin sa, a hankali Mariya ta tura kofar dakin ta shiga tana Kallon sa da murmushi, domin a yanda Al'ameen din ke son gayu da iya daukar wanka zaka yi tunanin matashi ne dan shekara ashirin da biyar zuwa da talatin.




A jikinsa yaji ana kallon sa, hakan yasa ya ajiye kwalbar turaren sa mai suna *FOGG INTENSE OUD* domin yana matuk'ar Son turaren su, dama body spray dinsu da bashi da gas ƙo kadan a cikin sa.




Murmushi ya sakar mata, martani ta mayar masa kana ta karasa gareshi, hular ƙanshi ta gƴara masa.




Gyaran murya yayi yace "dama inaso idan na gama shirya wa nazo muyi magana dake, domin akwai labari mai dadi da nake son sanar dake"



Fadada murmushin ta tayi tace "Toh gani ina jinka"...



Hannun ta ya riko yace "ki tayani farinciki Allah ya sake azurtamu da samun ciki a karo na biyu, ina nufin kanwarki Raliya na da juna biyu"...





"Yeeeeeeehy! gaskiya nayi farinciki sosai mijina, Allah ya raya ya sauke ta lafiya, in Sha Allah gobe idan zaƙa fita tare zamu je domin in duba ta"





Cikin so da ganin girmanta yace "Allah ya kaimu uwar gidana, ina kaunar ki"




Wani far tayi da ido kamar yar shekara 16 tace "love you too mijina muje In raka ka"





Ba musu yayi gaba tana biye dashi a baya, sai data ga motar sa ya bar haraban gidan kana ta koma ciki.

Al'ameen kuwa sai daya fara zuwa gidan su Raliya ya duba lafiyar ta, wanda ya dauki kusan awa daya wanɗa da kyar ya tafi, domin babu abinda yake so yake kuma muradin gani kamar Raliya da cikin jikinta, wanda ya fara tasawa..





*SOKOTO*



Bayan sati uku, Papi ya dira a garin yau da yammaci, yana zuwa kofar gidan ya danna horn ji ƙaƙe pimmmmm! Pim...pimmmm!!

Ai da gudu Nu'aiymah ta fito daga cikin gidan, sanye da doguwar riga mai tashi na material hadi da dan mayafin sa, cikin sauri Nu'aiym yayi parking ya taro ta yana rungume ta, sai tsallen murna take a jikin sa, runtse idanun sa yayi yace "my baby nayi missing dinki sosai"



"Nima Papi nayi kewarka fa sosai, ƙa dinga tafiya da ni kajiiii"




"Da na fi kowa jin dadin hakan baby, sai dai hakan bazai yu ba yanzu" ya aiyana a ransa, a fili kuwa Murmushi yasaki ganin yanda tayi maganar kamar zata saki kuka, hannun ta ya kamo bayan ya raba jikinsa da nata suka nufi cikin gidan.....





Kaka suƙa tarar bakin kitchen tana ta fada, cewa take "kaga yarinyar nan, sai kace guduwa zai yi, ki bar girki, ni kuma tsoron wanna abin nake(gas cooker) shiyasa ma ban shiga ba, da a ce gawaye ko kalanzir ko ice ne da tuni na karasa girkin"





Da murmushi Nu'aym ke binta, a fili yace "oh my kakus bakya gajiya da magana always?"




"Yo ina zan gaji da magana bayan 'yarka kullum cikin sani magana take, ko da yake ba fada zaka mata ba, Dan haka babu amfanin gaya maka, domin bakwa son laifin juna, ƙuma ƙa daina ce min always, ni ba gunzugu(PAD) ɓace ba atoh"




Wani murmushi ya sake yi, Nu'aymah kuwa kitchen ta nufa tana ɗariya, tama manta da wani girki data d'aura, murnan ganin Papi'n ta yasa ta manta, nan suka gaisa da kaka bayan ta gama mitar, bayan Nu'aiymah ta gama girki ta zuba a flask ta wanke kayan data bata kana ta dawo ta zauna a cinyar Nu'aym tana bashi labari, murmushi kawai yake yana sauraran ta farinciki ya cika zuciyar sa, ganin shi kusa da baby'n sa.





Nan ya fito da tsarabr su daga cikin jakar sa ta goyo, ya bawa Nu'aiymah na ta, wanda duka kayan zaki ne, dayar ledar kuwa kaka ya bawa, nan ta hau murna ta bud'e ledar ta fara ci....




Haka dai suka cigaba da hira, da d'addare tare suka ci abincin a plate daya kamar yadda suka saba matuk'ar su ukun na tare, kana suka shiga hira har karfe sha daya na ɗare basu yi bacci ba, amma banda Nu'aiymah dake zube a jik'in sa tayi bacci.






*BAYAN KWANA UKU*



Da misalin karfe hudu da rabi na yamma, Nu'aym ya fito sanye da shadda brown daya sha dinkin zamani ya sha hula gwanin kyau, kafarsa sanye da *palm sandals*
Daya dace da kayan jikinsa.




Agogo ya d'aura kana ya nufi parlour, kaka ya gani, tana kallon wani India movie duk da ba wai fahimta take ba



Sallama yayi kaka ta amsa, Nu'aiymah kam tana faman buga game a wayarsa, bata san ya shigo ba, da kallo kaka ta bishi tace "ohh Dan nan wanna wankan fa? Ko dai zance zaka je?"





"Zance kuma kaka? A'a gidan abokina Abdul-Hafiz zan je, ya fiƴe korafi bana neman sa" ya fada idanun sa kan Nu'aiymah.




"Eh da gaskiyar sa, gaskiya yaron yana da zumunci sosai, ya kamata kaje masa, sai ka dawo"



"Toh kaka" yace ya nufi wajen Nu'aiymah, a hankali yasa hannu ya zari wayar, shagwa'be fusk'a tayi tace " wayyo! Papi za a ci ni faaaa Dan Allah ka kawo kaji in ci wanna"




'Naki di'n baki ma san na shigo ba ko" inji NU'AYM.


"kayi haku'ri Papi ban ji ba"



"Hmmm Nu'aymu kaga wanna 'yar taka, wallahi idan ka siya mata waya na kanta, zata iya d'aura girki ta manta ta haddasa gobara mu shigesu, amma ba fata nake mana ba, a toh, gaskiƴa na faɗa"





Turo dan tsut din bakin ta tayi tana bata rai. ganin haƙan yasa papi cewa "Rabu da ita babyna, in Sha Allah da kin gama secondary school zan siya miki waya, babba daya fi na kaka sau dubu kinji, yanzu so nake kiyi karatu sosai kinji?, yanzu ga wayar ki cigaba da yin game sai ki samin caji idan kin gama ok"....





Murmushi ta saki tace " toh Papi nah"




"Sai me dan an gwale ni? Toh ban ji haushi ba ehe! Idan ma dan ka kunsa min kayi, kama siya mata company'n ɗin wayar gaba daya mana"...




Da murmushi ya fita, yana danne dariyar sa, dama ya fada ne saboda yaji ta bakin ta.






Ganin ya fita yasa ta cigaba da kallon film din ta, an hasko wata budurwa da gashinta yayi daidai da tsayin ta, hakan yasa ƙaƙa ta buɗe baki kana ta kalli Nu'aiymah tace " Nu'aiymahtou anya mutanen nan ba gashin doki suke karawa ba? Kalli kiga ace gashin mutum har jan kasa yake, tayani gani yar nan mamaki".







"A'a fa kaka gashin ta ne" Nu'aiymah ta fada idanun ta na kan game din da taƙe yi.






"Kaji min ja'irar yarinya, ke da baki kalla ba, bare ki gani sai ki wani yanke hukunci, toh indai gashin ta ne, tofah ba tamtama bamutum bace, aljanar cikin ruwa ce" kaka ta fada cikin iyakar gaskiyar ta.




Dariya Nu'aiymah ta fara yi, kana ta tsagaita tana shirin bata amsa, wayar kaka ya fara ringing, mikewa Nu'aiymah tayi ta nufi wayar dake chaji, dan zaro ido ta yi ganin wanda ke Kira.......















Share


Comment


Vote


Nooreemaan
07082281566


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*WATTPAD*
@NoorEemaan










EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




47-48




.......... *Habib Husain* ta gani a rubuce, unplugging wayar tayi kana ta kara a kunne ta, cikin sweet voice dinta mai cike da kuruciya tace


"Assalama alaykum"


'Wa'alaiki salam, da fatan mai kyau na ta wuni lafiya?"



Dan runtse lumsasun idanun ta yi, kamar yadda papi ke yi kana tace


" lafiya Alhamdulillah"



"Toh haka nake son ji, ina kofar gidan fa"


Dan Jim tayi kana tace "Toh gani nan zuwa"


ware Idanunta tayi ta kalli kaka data kafe ta da ido tace

"kaka ya Habib Husain ne yazo"


"Toh maza je ki sai kin dawo, amma ƙarki ɗaɗe"



Mayar da wayar caji tayi kana ta shiga dakin ta, wani hada'dden abaya pink mai yalwa stone ta saka, tayi rolling da mayafin abayar daya k'asance dark pink. Turare a fesa hadi da body spray, wani uban kyau mai tafiya da hank'ali duk wani lafiyayyen namiji tayi, wani black snicker's ɗa ya kara fito da haske kafar ta ta sanya kana ta fito cikin takun nutsuwar ta....


Tsaye yake jikin motar sa, ya sha k'yau cikin kananun kaya, ga tsadaddiyar wayar sa a hannu yana latsawa, tun kafin ta karaso k'amshin turaren ta ya riga ta isowa, take ya dago k'ansa ya sauke su fess ƙan fusƙar ta, wani mugun kyau yaga tayi masa fiye da na k'ullum, Yayinda soyaayar ta mai zafi ya sake ratsa zuciƴar sa.


Aljihu ya mayar da wayar yana jefan ta da wani lafiyayyen murmushi, martani ta mayar masa, hakan yayi daidai da isowar ta wajen shi.



A kunyace tace "Assalama alaykum"


"Wa'alaiki salam, barka da fitowa kyakyyawa da babu kamar ta a duniya"



Murmushi mai dan sauti ta saki, domin babu wanda baya son a yabe shi...



"Ya kaka take, ya kuma school?" Ƴa sake tambaya a tausashe.


"All fine Alhamdulillah" ta bashi amsa.


"That's Good!" ya faɗa


Shiru wajen ya dauko na tsahon mintuna biyar babu wanda ya kara cewa komai, sai ma Habib Husain daya kafe ta da idanu baya ko kiftawa, Yayinda Nu'aiymah ta kawar da kanta gefe saboda kunyar sa....



Ajiyar zuciya mai tafe da murmushi ya saki, kana yace "na san kin gaji ko? Ko mu shiga mota, domin sam bana so ki wahala"




Murmushi ta saki, domin bayan Papi da kaka shine mutum na uku dake nuna kulawar sa a kanta irin sosai dinan....



Girgiza kai tayi kana tace "A'a ban gaji ba, nan ma yayi thanks"




"Don't mentioned mai kyau nah, kin cancanci fiye da haka"



Wani murmushin dai baby'n Papi tayi, bata ce komai ba.



"Yaushe zaki gama school ne? am eager na ga kin zama matata" Habib Husain ya fada, so yake ya jata ɗa hira domin ta saba dashi sosai...



ciƙin kunƴa tace "Na gaba kadan in Sha Allah" Nu'aiymah ta bashi amsa.



"Good! Mai kyau nah, sosai kika kara kyau fiye da ranar dana zo, na lura kullum sabon kyau kike karawa, gayamin miye siririn? Me kaka ke baki ki ke ci ne?"



Murmushi daya bayyana white teeth d'inta mai dauke da open teeth (wushirya) tayi tace


"babu kome fa?"


"Da gaske ya kara fada?"



"Eh da gaske nake" Nu'aiymah ta bashi amsa.



"Toh yayi kyau, ya maganar mu? Ina son jin amsa na yanzu".....



*********

Nu'aym daya taho tun daga nesa ya hango kamar baby'n sa ce ke tsaya, domin bai yarda ita din bace, yana kara kusanto shi yana kara ganin fusk'ar Nu'aiymah d'insa na sakin murmushi da wani saurayi da baya iya ganin kamanin sa sosai, domin ya dan bashi baya...




Fadin tashin hankali d'aya fara riskan K'anshi aciki ba mai sauki bane, duk saurin da yake yi, gani yake tamkar ba sauri yake ba...



Gaba daya jikinsa tafasa yake Saboda zallan tashin hankali da bacin rai, idanun sa sun sanja launi sosai cikin seconds kalilan...



Yana daf da isowa kofar gidan, a daidai lokacin ne Nu'aiymah ta budi baki zata bashi amsar sa, sai dai hango papi ya sanya ta fasa, kana murmushin fusk'ar ta ya yawaita, ba tare da ta bashi amsar ba tace " kaga Papi nah!" Ta fada a hankali


"Ban fahimta ba, kina nufin ƴaƴanki?" Shima ya furta a hankali, idanun sa ƙan Nu'aym daƙe tahowa.


"A'a faaa ba ƴaƴa na ba ne, Papi nah nace, ubana mahaifi da ya haife ni" Nu'aiymah ta bashi amsa.



Dan waro ido Habib Husain yayi, cikin madaukakin mamaki.
Ta ya ya wanna saurayin da baya ko tamtama ya san zai girme shi ya haifi Nu'aiymah, abin da mamaki matuk'a kana da d'aure kai.



Dauke idanun sa yayi daga kan Nu'aym da bai riga ya karaso ba yace " What! are you serious? Kina nufin wanna shine mahaifin ki, I mean you biological father?"



"Wallahi Allah shine" Nu'aymah ta kara fada tana murmushi ita kam bata kawo komai a ranta ba, daidai lokacin Nu'aym ya karo sa wajen...




"Papi nah! Ka dawo?"

Nu'aiymah ta fada tana nufar wajen sa, sai dai inaaaa bacin ran ɗa ƴaƙe ciƙi bai sa ya ji abinda take cewa.



Duk da habib Husain yasan cewa ya girmewa NU'AYM amma dole ya nuna girmamawa a gare shi tunda yana son 'yarsa, duk da har yanzu yana cikin mamak'i ganin wanna matashin saurayin ya haifi kamar Nu'aiymah.


Rissinawa yayi cikin girmamawa yace "ina wuni Papi ka dawo lafiya?"





Wani sabon tak'aici ne ya kara kama Nu'aym babu abinda yake sai faman murza yatsun sa yake, shagwa'ba fuska Nu'aymah tayi tace

"Papi! ya Habib Husain na gaishe ka faaaaa"


Idanunsa masu fidda zallan tashin hankali ya kafawa Nu'aiymah yana hararar ta, yana mamakin nawa take ta har ta fara zance? Sosai yayi controlling temper d'insa (fushi) yace


"baby go inside"


Kara shagwa'be fusk'a tayi tace " Papiiiiii......"


Cikin fushi da murya mai sautin amo yace

"I said ki shiga ciki, before I lose my temper"

Tabe baki tayi irin na shagwa'ba, hawaye har sun ciƙa Idanunta ta shige gidan da gudu....


Dawo da kallonsa kan habib Husain yayi, da har yanzu bai Mike ba kamar wanɗa aƙa ɗasa, rage tsahon sa yayi, ya dora hannunwansa duka biyun kan guiwowinsa, Yayinda ya kafa masa jajayen idanunsa, ga jijiyoyin kansa da suka mike suka fito radu² Saboda tashin hankali har wani ruwan hawaye na zallan bacin rai ya taru a gefen idanun sa.



Cikin wani irin murya yace "Habibu ko what so ever sunan ƙa yake, ina maka gargadi da babban murya, daga yau sai yau kada na kara ganinka kusa da 'YATA! domin bazan mata aure yanzu ba, yata karatu take...."



Share fisabilillah


Comment



Vote


Thank you for reading my novel Papi ne!


NoorEemaan ce🔥


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓



*WATTPAD*
@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌


Page 49-50


........Cikin sauri kana cikin girmamawa Habib Husain ya ƙatse shi ɗa cewa "kayi haku'ri Papi, wallahi da gaske ina son ƴarka da aure, kuma zan iya jira ta gama karatun sai ayi auren mu dan Allah ka amin....."





Tamk'ar saukar dalma haka yaji kalaman Habib Husain din, cikin kakausar murya yace "zan maimaitawa maka a karo na biyu, stay away from my daughter, bazan baka ita ba, idan na sake ganin ka a kofar gidanan or anywhere close to my daughter wallahi bazaka taba manta abinda zan maka ba"



Nu'aym na gama fadin haka ya shige cikin gidan a haukace...



Nu'aiymah na tsaye a dan haraban gidan tana sharan hawaye, Yayinda idanun ta ke fa kan gate din shigowa....



Ga kaka nata tambayar ta meya faru amma ta kasa magana sai hawaye da take ta faman share wa, a yanayin da ta ga Papi ya shigo ya kara tsoratata, cikin sauri ta nufi bayan kaka tana kara sautin k'ukan ta, domin a tunanin ta dukan ta zai yi.....



"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un! Miye haka wai? Kai Nu'aymu aljanu ne suka shige ƙa ne? Ka wani shigo kamar zaka tashi gidan gaba daya" kaka ta fada cikin dakewa amma tsoro ne fall cikin ta, domin duk wanda yaga yanayin Nu'aym din dole ya tsorata.



Bai kula kaka ba, ya zo har bayanta ya zaro Nu'aiymah data makalkale kakan, Sosai ta kara sautin kukan ta, abinka da farar mace gaba daya fuskar ta ta dawo jajur kamar tumatir...



Da hannu daya ya rike ta, kana ya daga dayan hannu zai wanke mata mari, sai kuma ya tsaya Cak! da hannun sa yana Murza wa

Nu'aiymah kuwa kamkame jikinta tayi hadi da runtse idanun ta, tana jiran saukan mari, ganin bai mareta ba, ya sanya ta fara bude Idanunta masu cike da hawaye, hade ido tayi dashi ta ƴi saurin sauke Idanunta kasa, sak'amak'on wani tashin hankali da take hangowa a idanun Papi'n nata....




Cikin fitar hayyaci ya dora hannunwan sa ɗuƙa kan kafadunta ya girgiza ta da karfi, idanunsa ya sanya cikin nata yace

"Waye shi!" a kausashe

Shiru tayi tana kuka kasa² kara jijigata yayi yace

"nace waye shi?"

Maimakon ta bashi amsa sai ta karo sautin k'ukan ta, hannunsa daya ya cire kan kafadunta, ya hade babban dan yatsar sa data tsakiya ya dan harbe ta a kumatu, kifkifta Idanunta tayi, tana sakin shesheka kukan...



Nace "waye shi?" Ya kara tambayar ta.

Cikin rawar murya murya tace "y...ya Habib Husain ne?"


Wanna karon labb'anta ya harba yace "Idan kika ƙara ce masa yaya sai na zane ki"


"Nace waye shi? Kuma karki mun kuka"


"Ha....Ha...bib...Hu...sain ne" tace tana danne kukan ta.




"Good! Meya zo yi wajen ki?"



"Wai wai yace yana sona ne " ta fada gwanin tausayi.


Wani uban kishi ne ya tokare shi, cikin wata murya yace

"uhm! Kina son sa kema?"

Shiru tayi Hawaye na zuba a Idanunta.

"I said kema kina son shi ne?" Ya kara fada cikin daga murya...

"A.....a....a'a" ta fada cikin wata murya dake rawa sosai kana a cakude da kuka.



"Baby tell me nawa kike da har zaki fara zance? As small as you are kin fara sauraran namiji? Huh! Me nace miki kwanaki?" Ya fada cikin zallan kishi daya bayyana a muryar sa, sai dai Nu'aiymah sam bata fahimta, domin akwai ƴarinta a tare da ita.



"Cewa kayi karatu kake so inyi" ta fada gwanin tausayi.



"Kenan kin daina jin magana ta shiyasa kika fara bijirewa umarnin na, gayamin"



Nu'aiymah zata yi magana kaka dake gefe tun dazu ta kafa musu ido kamar ta samu Tv tace "yau naga ikon Allah! Miye yake damun ka ne d'an nan? Yanzu Nu'aiymahtou'n ce bata isa zance ba, ko a kauye irinta na da 'ya'ya uku ma, miye dan tayi zancen ko kana nufin har abada bazata yi aure ba? anan zata zauna, ko wani uba idan 'yarsa ta kai minzanin auren ya kuma samu suruki na gari abin farinciki ne, amma banda kai, yaron nan dan kirki ne har nan yazo ya tsugunna ya gaishe ni, wanna abin farincikin ne, ace 'yarka ta samu abokin rayuwa na gari"



Tamkar saukan tafashashen ruwa a jikin sa haka ya ji saukar kalaman kaka, wanda ya ƴi nuni da cewa ba yau ɓane farkon zuwan Husain din ba....



Ganin kaka kara bata masa rai take yasanya shi cewa " A enough please kaka! a enough! Baby 'yata ce, na kuma ce bana son tayi zance yanzu, karatu zata yi, sannan nan ba kauye bane da zaki je sa'aninta sunyi aure, bana son ganin baby da ko wani da namiji! Nace bana so! Idan bazaki iya kular min da ita ba, idan kuma bazaki iya hanata sauraran ko wani da namiji ba, toh wallahi zan bayar da ita Jigawa, zan tafi da ita Jigawa domin na kula da 'yata".....



Ya fada cikin rawar murya kana ya ɓar gidan, domin baya son ya taba jikin Nu'aiymah ko kadan, idan ba fita yayi ba, zai iya dukan ta, wanda zai yi nadama mai tarin yawa...




Zubewa Nu'aiymah tayi a kasa tana kuka sosai, idan akwai abinda tafi tsoro a duniya toh fushin Papi'n ta ne, sam bata kaunar bacin ransa...



A hankali kaka ta karaso wajen Nu'aiymah ta daga ta suka shige falo, kan kujera suka zauna Yayinda Nu'aiymah ta kwantar da kanta kan cinyar kaka tana cigaba da rera kukanta.



Kaka an nutsu, yau kam ba rikici, sosai ta ke fassara kalaman Nu'aym din kashi² a matsayin ta na babba ta fahimci wasu abubuwan daga kalaman Nu'aym din, ita kam ba zata so Nu'aiymah tayi kukan maraici ba, sam bata so Nu'aiymah ta san cewa su din ba ahalin ta bane, bazata so farinciki su ya yanke ɓa, sai dai ta lura Nu'aym ya dauko hanyar da zai sa Nu'aiymah ta fahimci cewa ba shi ne ubanta, ba tare da yasan cewa ya fara yin hakan ba, bubbuga bayan Nu'aymah ta fara yi alamun lallashin, da tunanin idan Nu'aym din ya dawo zasu yi magana.....




Bangaren Nu'aym kuwa wani wajen shakatawa ya nufa, VIP ya nufa domin baya son hayaniya a halin da yake ciki, sosai yake kokarin controlling temper d'insa, wanda kaso arba'in na cikin fushi da damuwar sa ya gushe, sai ɗai daya runtse idanun sa babu abinda yake hangowa sai baby'n sa tare da Husain tana sakar masa ƙƴaƙƴawawan murmushin ta....


Sai karfe tara ya bar wajen ya nufi gida, a keke napep ya tafi, dama bai fito da lifan din sa ba, babu jimawa ya iso gidan....




Zaune ya tarar dasu kan sallaya a dan farfajiyar gidan sunyi shiru, wani tausayin su ne ya dake sa, domin yasan cewa rashin dawowar sa ya sanya su shiga wanna yanayin.



Dauke kai yayi kamar bai gan su ba ya nufi dakin sa... Kuka Nu'aiymah ta fashe dashi, ganin bai kula su ba...



Kaka tace "yi Shiru abin ki, zai sauko kinji, tafi dak'i ki kwanta, tunda ya dawo Alhamdulillah, zuwa gobe zai sauko kinji ƙo" kaka ta fada cikin lallashi ta nufi dakin ta, duk da tasan muyuwan ci ne Nu'aym ya hakura a gobe, tabbas ta san halin jikan nata, ba shida hakuri idan ransa ya baci....



Zaman wajen Nu'aiymah ta cigaba tayi tana hawaye Yayinda take tunanin yanda zata je wajen Papi domin tsoro take ji, can ta tuna da wayar sa daya bata dazu da ƴamma, mikewa tayi ta linke sallayan kana ta nufi parlour, ajiye sallayan tayi kan kujera kana ta dauki wayar ta fita.... ta zo daidai dakin Nu'aym Nepa suka dawo da wuta, a hankali ta murda kofar dakin ta shige bakin ta dauke da sallama da amon sa ke cike da kuka......




Zaune yake daga shi sai wando 3quarter na jeans, hadi da bakin singlet da alama wanka yayi, cikin dar²

tace "p...pa...pi ga wayar ka"



Wani uban harara ya jefa mata kana ya haura gadon yana mai juya mata baya, kuka sosai ta

Please Login or Register in order to submit comment