Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shine Abdul -hafeex, domin Abdulhafeex na son abota da Nu'aym, amma Nu'aym bai fiye sake masa sosai, k'asancewar Abdul-hafeex dan masu kudi ne...
Kullum haka kaka ke fama da shi kan dawowa gida da wuri, wani zubin har fad'a suke, domin kaka akwai rikici duk da haka dai suna da matuk'ar son junansu wanna kenan...

*CIGA'BAN LABARI*
Zaune suke a dakin kaka, tana shirya baby'n cik'in wasu kaya masu kananun kudi domin baza su fi dari hudu ba, ba laifi baby'n ta rage k'uka domin k'ullum Cikin dare sai ta tashi tana kuka sai dai Nu'aym na daukar ta zata yi shiru ta ciga'ba da baccin ta har mamakin hak'an yake, duk ranar da bai samu kudi masu yawa a gareji na siya mata madarar yara ba, sai ya siya mata nono na saba'in haka wurin masu fura kuma alhamdulillah tana karba ta sha.

Bayan kaka ta gama shirya ta ya karbeta ya rungumeta a jik'in sa, murmushi kaka ta yi tace "toh mai 'ya wani suna ka zaba mata ne?"
Lumshe idanun sa yayi kana ya ware su kan baby'n yace "BABY NU'AYMAH"
Dan tabe baki kaka tayi tace "meye wani bebi (baby) kuma sai kace wata yar tsana"
Murmushi yayi yace "toh NU'AIYMAH nake nufi"
"Yawwa yanzu naji batu, Allah ya raya mana Nu'aiymah, sai kayi mata hudu ba ko?" Take kuwa ya yi mata, "Allah ya raya ta" kaka ta kara cewa
"Ameen ya Allah kaka" yace yana kara kamkame ta a jikinsa, shi dai yana jin wani abu da bai san ma'anar sa ba a jikin sa...
"Sai dai dole mu yanka mata ragon nan nawa a sunan ta, tunda ina da guda daya Allah ya hore min, idan yaso sai a dinga siya mata madarar yara har Allah yasa ta kai minzanin cin abinci..
Dariya yayi yana mamakin yawan sakin hannun ta a yanzu yace" hak'an yayi dai dai kaka" Allah ya kara miki lafiya da Nisan kwana"
"Ameen dan jikana".....tace cik'in farincikin.


Share✔
Comment✔
Vote✔
Edit❌

🍇🍇PAPI NE🍓🍓
Story and written by
Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan



This book is dedicated to all orphans in the orphanage home.

Page 7-8

.......haka suka cigaba da rainon baby Nu'aiymah cikin k'ulawa da tattalin, k'amar yadda kaka tayi alkawari ranar da Nu'aiymah tayi k'wana bak'wai cur da haihuwa aka yank'a mata ragon kaka k'waya daya da take ta adanawa shekara da shek'aru....basu gayyaci ko da mutum d'aya ba saboda dalilai masu yawa, na farko saboda abinda mutanen zasu ce game da baby Nu'aiymah da kuma rashin kudi, d'omin idan suka gayyaci mutane me zasu basu? domin ko kudin mai suyar naman b'ab'u, sai tafasa wa k'awai suka
yi....


*** *** *** *** *** ***

Kullum cik'in dare Nu'aiymah sai ta tashi da kuka, da zarar Nu'aym ya d'auke ta kuma sai tayi shiru, wani lok'acin idan madararta ta kare labb'ansa yake sanya mata ta tsotsa domin ka Kodan baya son jin k'ukan ta, hak'an yasa k'od'ayaushe labb'ansa ke yin jaa hadi da kumburi, har ya saba da lokacin da tak'e fark'awa cik'in daren, da lokacin yayi sai ya tashi, wata sabawa tayi dashi mai ban mamak'i, domin idan zai tafi makaranta da safe sai ta fara k'uka, shima idanun sa sai su ciko da k'walla ya dawo ya zauna yace yafasa zuwa, sai k'aka tayi masa jan ido yak'e tashi ya tafi har da k'wallan sa..., kuma matuk'ar yaje makaranta sai ya siyo mata su manta gida, goriba, carbin malama, tsami gaye, alawan madara, gullisuwa, illoka da dai sauran abubuwa, duk da dai ba wani iya ci tayi ba...
A lokacin data yi shekara daya da rabi ta fara kiran sa "PAPI" a ranar yayi matuk'ar mamaki hadi da tsananin farinciki domin har ransa sunan yamasa dadi ya kuma ratsa zuciya da jinin jikinsa...



BAYAN SHEKARU BIYAR
Wata K'yak'yyawar farar yar yarinya mai kimanin shekaru shida zaune kan wata tabarma d'aya gama fita a kamanin sa, sanye da uniform light blue riga da wando hadi da karamin farin hijab, koko ne a gabanta da biscuit dan ashiri tana ci, kokon kuwa sai wasa take da shi taki sha...
A gaban ta Nu'aym ne zaune kan wata kujera yar tsukunno, gaba daya ya sanja cik'in shek'aru shida, ya yi wani girma na ban mamak'i bawai yayi kiba ba, ko dan bata wata alamar kiba a jikin sa, amma gaba daya jikinsa ya dawo wani a mumurde tamkar mai yin gyming ko nace training, duk inda ake neman giant namiji ya kai, domin wani dan shekara talatin baya da irin kirar jik'insa shi mai shekaru ashirin da d'aya a duniya, sanjan sa kwance luf luf, daya karawa fusk'arsa k'warjini da kyau, K'yak'yyawa ne sosai chocolate color mai dauke da manyan idanuwa, digon hancin dan madaidaicin baki, da dimples masu lo'bawa a d'uk sa'ilin d'aya motsa bakin sa...
A hank'ali muryar sa ta cik'akk'un maza ta ratsa cikin kunnen wanna yarinyar yace "baby Nu'aiymah, kiyi sauri mu tafi mana kin kusa makara zuwa school fa" ya kara sa yana kallon ta.



Turo dan bakinta tayi tace "Papi nah! ni bazan sha koko ba, tea zan sha" ta k'arasa tana share k'walla.
Ai karaf kaka dake wanke wanke tace "kaji min ja'irar yarinya, yo idan baki sha koko ba uban me zaki sha, kedai iyayi ne dake na bugawa a jarida, kina yar idan malam shehu kice wani wai shayi"


Runtse idanun sa yayi, kana ya ware su ya kalli kaka dake ta sababi ita kadai, yanzu rikicin ta sai abinda ya karu, akodayaushe yana gode wa Allah, amma matuk'ar Nu'aiymah ta nemi wani abu ta rasa hak'an na matuk'ar taba zuciyar sa, sai ya dinga ganin ya gaza a kan k'ok'arin da yake na wadata su da abinda yake da shi.
Yana shirin yin magana yaji Nu'aiymah tace "Papi kaga kaka ko" ta k'arasa tana fashewa da k'ukan shagwa'ba, domin sosai Nu'aym ya gama shagwa'bata, sam baya son bacin ranta, amma matuk'ar tayi abu mara k'yau huk'unci mai tsanani yake mata, wata rana har rokon sa k'aka ke yi idan ta ga huk'unci yayi yawa, amma hak'an baya hana su kuma dinkewa abinsu, domin shak'uwar da son junansu baki bazai iya furtawa ba, sai dai Nu'aym akwai zafin zuciya da saurin fushi...
Ai kafin ya bawa Nu'aiymah amsa k'aka ta cafe da cewa "sai kisa ya dake ni ai, masu uba, nace kisa ya dake ni kuga abinda zan muku daga ke har uban baki"


Girgiza kai yayi yace "yanzu fisabilillah kaka da baby kike wanna masifar sai kace wata babba?"
Kara arzuk'owa kaka tayi tace "babo ba baby ba, nace babo ba baby ba, tunda baka son laifin ta, to ni sai nayi magana ehe, ba tsoron ku nake ji ba"


"Kaka ki daina yiwa Papi nah fada bana so" Nu'aiymah tace tana kara turo bakin ta.
"Eye! To sannu masu uba"
riko fuskar ta Nu'aym yayi yace "baby nah, rabu da kaka kinji, kiyi haku'ri ki daure ki sha k'ok'on I promise idan na d'awo daga gareji zan siyo miki chocolate da kayan tea ki min add'ua a kawo aiki gareji, kinga idan na siya miki tea yanzu bazan samu kudin motar zuwa school ba, ko baki son naje makaranta?" Ya k'arasa cik'in sigar tambaya.(kasancewar Nu'aym ya fara zuwa b.u.k, domin lokacin da suka zana jarabawar qualify a ss2 yaci jarabawar aka biya masa NECO kadai, bayan sun zana NECO'N ya k'asance daya daga cikin daliban da suka samu scholarship kyauta zuwa jami'an bayero wato b.u.k, kasancewar komai kyauta ne kawai kudin mota yake, kuma har yanzu yana zuwa gareji matuk'ar ba shi da lectures, idan ma akwai lectures d'aya d'awo zai zo garejin, da wanna kudin suke rufawa juna asiri)



Jinjina kai tayi ta dauk'i k'ok'on ta fara sha tace "ina so Papi" murmushi yayi yace "that's my daughter"
bata sha da yawa ba ta dire kofin, ta mike, daukar ta yayi ya saba ta a k'afada yana cewa "mun tafi kaka"
"Ku dawo lafiya" tace tana cigaba da aikin ta, ita ala dole fushi take, shi abin ma dariya ya bashi domin yasan fushin ta na yan mintuna ne ta sauko, ya kuma san zata yi magana ne... ganin har sun kusa fita daga gidan Nu'aiymah bata kula ta ba tace "yayi miki kyau, ko sallama babu ko, saboda nayi wa ubanki fad'a" dariya duk ta basu domin kaka na matuk'ar basu nishadi duk da akwai ta da fad'a amma k'ullum cikin farincikin da kaunar juna suke, cikin dan daga murya Nu'aiymah tace "kaka na tafi bye" hadi da daga mata hannu, itama kaka hannun ta daga mata tana cewa "ayi karatu da kyau yar albarka" da haka suka fice....

Har cikin makarantar ya kai ta Wanda ya kasance na government ne inda ya kara sa karatun sa, kudi ya ciro naira ashirin yace "baby'n Papi'nta ga wanna ki kashe a break"



Amsa tayi cikin murna "thank you Papi nah" tace cikin zazzakar muryar ta ta yara, tsukunnawa yayi d'aid'ai tsayinta ya sumbace goshin ta hadi da cewa "bye baby ki kulamin da kan ki, Sannan kiyi karatu, idan an tashi zan zo in dauk'e ki ki jirani(kasancewar shi ke zuwa daukar ta, domin koda yana da lecture sai ya bar makarantar ya dawo school dinsu ya kai ta gida bai yarda ta dinga tafiya gida ita kadai ba acewar sa tayi kankanta da yawa)
" toh Papi nah" tace tana rugawa cikin makarantar hadi da waiwayon sa tana daga masa hannu, shima daga mata hannun yake har ta bace wa ganinsa, murmushi kan fusk'ar sa ya fice daga makarantar...
Daya da rabi d'aid'ai ya dawo makarantar, ya tsaya d'aid'ai inda ya saba tsayuwa, sai dai duk masu hucewa bai ga ko mai kama da Nu'aiymah'nsa ba, tun yana dauk'an abun wasa wasa har gabansa ya fara fad'uwa, duk da haka bai sare ba har sai da gaba daya yan makarantar suka gama fitowa, har ana k'ok'arin rufe gate din makarantar, a dari ya nufi gida... Isar sa gida yasa gaban sa sake wata mahauk'aciyar bugawa adalilin amsar da kaka ta bashi cewa "NU'AIHMAH BATA DAWO GIDA BA...."



A haukace ya sake barin gidan kaka na kiran sa ko kulata bai yi ba...duk inda yake tunanin zai same ta ya duba amma ko mai kama da ita bai gani ba, ga shi bata da kawa ko daya balle yace gidansu taje, gaba daya ya burkice sai tafiyar yake ba batare da yako sare ba....



bangaren Nu'aiymah kuwa, bayan an tashe su daga makaranta wata yar ajinsu tace tazo su je gidansu can kwanar ne babu nisa, abunka da yarinya ba musu ta bi bayan ta kan cewa zata dawo kafin Papi'nta ya dawo, da isarsu gidan su yarinyar mai suna hassana kuwa mahaifiyarta ta tarbe su k'asancewar ta mai faram faram, har abinci ta zuba su Nu'aiymah taki ci tace ita wajen Papi zata, matar ta lallaba ta tace taci sai ta tafi, ba musu ta ci bayan ta gama ta mike, matar ta bata naira hamsin tace ta siyi biscuit kin amsa tayi domin tasan matuk'ar Papi ya gani sai ya dake ta domin ya hana ta karban abu a hannun mutane, ganin taki karba yasa matar cewa toh zata gane hanya? Cikin sauri Nu'aiymah ta gyada kai tana dagawa hassana hannu ta fice...


Maimakon ta nufi hanyar dazai fitar da ita titi, sai
ta nufi hanyar daya sake nutsar da ita ciki-cikin unguwar, gabadaya kanta ya k'ulle ta rasa hanya, tun tana tafiyar wanda kara batar da ita yake har ta fara k'uka tana kiran "Papi"....


Misalin karfe bakwai na daren ranar yana zaune kan tabarma jingine da kaka dawowar sa daga neman Nu'aiymah kenan, idanun nan sunyi ja k'aka kuwa idanunta sunyi luhu luhu alamun ta sha kuka ta gaji, cikin muryar wanda ya sha k'uka ya koshi yace" kaka ina zan ga baby? Kalli kafata kiga yadda ta datti saboda neman ta, na rasa ya zanyi, a wani hali tace ciki? Shin tama ci abinci? Kuka take yanzu na sani k'uka take, jikina yana bani hak'an kaka" ya kara sa yana sake fashe da k'uka tamkar yaro dan shekara 5 itama hajiya kaka kuka ta wiwi gwanin tausayi, shafa kansa kawai take alamun rarrashi domin ta k'asa magana, mikewa zubur yayi kamar an mintsile shi ya kara fita daga gidan....✍️


kusan is not easy gaskiya two book nake a lokacin daya so brain dina na buk'atar hutu, shiyasa zaku ga ba lallai bane na dinga posting k'ullum.... Son so nake muku my Beautiful people😍

Please do Follow me on wattpad @NoorEemaan.

Share saboda Allah

Comment

Vote

Editing is not allowed❌


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by
Noor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan





Page 9-10
...........Tafiya k'awai yak'e yana kalle kalle yayinda zuciyar sa keyi masa wani suya, ji yake k'amar ya k"urma ihu ko zai ji sanyi a ransa... Har sha daya na dare Nu'aym bai dawo gida ba, hankalin kaka ya sake tashi domin itama ta karade ila'irin unguwar tasu har gidan mai unguwa taje ta gaya masa batan Nu'aiymah sai da kafarta ya fara ciwo ta lallaba ta dawo gida, amma ta tarar Nu'aym bai dawo balle ta sa ran ganin Nu'aiymah....



Sai misalin karfe daya na dare ya shigo cik'in gidan jiki a sanyaye, kaka ya hango zaunen a tsakar gida tana gyangyadi, tausayin ta ya kama shi, yau gaba daya babu wanda yayi tunanin cin abinci. Motsin da kaka taji ne yasa ta tashi a firgice tace "Nu'aymu yaya an dace?"



Bai iya bata amsa ba, sai kansa daya girgiza wasu zafaffan hawaye na k'waryo masa, take kaka ta fashe da k'uka tana karanta duk add'uar daya zo bak'inta.



Yanda suka ga rana haka suka ga dare, yana iddar da sallar asuba ya sake fita neman ta, sai dai har 9 na safe bai ga mai kama da ita ba.



Gida ya dawo ya yi wanka saboda yanda ya dawo bututu da shi, kaka na yi masa maganar karin kumallo bai amsa ba ya fice, domin Zuciyar sa a kusa take zai iya aikata komai ba tare da yasan ya aikatan ba.


Mak'arantar su yaje direct office din headmaster ya nufa ya gaya masa batan Nu'aiymah, take hankalin headmaster ya tashi, nan yace su je ajinsu a tambaya... gaba daya yaran sai wasan su suke domin babu malami ajinsu, suna ganin headmaster suka nutsu hadi da gaishe shi bai tsaya amsawar ba yace "shin Nu'aiymahtou Ahmad Nu'aym tazo makaranta jiya?"



Tak'e duka yaran suka hada baki wurin fadin "eh tazo"

Nu'aym k'uwa sai raba ido yake a ajin, ji yake kamar zai ganta tsaye a gabansa tana k'iransa sunan daya fi komai yi masa dadi a duniya.


Headmaster na shirin yin magana muryar hassana ya katse tasa tace "jiya bayan mun tashi a makaranta, shine muka tafi gidan mu tare" yarinya ta fada babu wata alamar damuwa a tare da ita.



"What!?" Nu'aym yace kana ya isa gaban yarinyar, habar ta ya riko ya tsare ta da da manyan rikitattun idanunsa yace "yanzu tana gidan ku!" Jikinsa har wani rawa yake ...


Cikin muryar tsoro yarinyar tace "A'a, tun jiya ta tafi, ummana tace ta san hanya tace eh"... Domin sosai hassanar ta tsorata da yanayin Nu'aym din.



Kan teburi(table) da yara kan dora littafin domin rubutu ya buga da dukkanin k'arfina sa, hakan ya sa sauran yaran firgicewa, take sumarsa da bai samu ko brush ba yau hadi da gargasan jikinsa suka mimmike, bai kara cewa komai ba ya fita daga ajin a haukace ko sauraran maganar headmaster bai yi ba domin yanzu kowa ma mai laifi yake daukansa idan yace zai tsaya tofah zai iya zubar wa da headmaster dukkanin hakoransa....



Ya danyi nisa da gate din makarantar ya hango wata tamkar baby'n sa, gaba daya uniform dinta yayi dukun dukun, yana iya hango yanda ta sanya hannunta a baki tana tsotsa yayinda take kuka ta na bin motoci da ke ta wucewa da kallo, murza idanun sa yayi, still ita yake hangowa daga nesa, domin ya gasgasta ya sa shi bud'e murya yace "Baby Nu'aiymah!"



Cikin sauri fara kalle kalle jin muryar Papi'n ta, ta kuwa hangon shi tsaye daga nesa cikin daga murya itama tace "Papi na!"


Wani zallan farinciki ne ya bayyana a fusk'ar sa cikin gudu ya fara k'ok'arin isa gareta, itama Nu'aiymah cikin gudu ta nufesa, a lok'aci daya suka cimma ma juna. Sama ya daga ta cak! hadi da rungume ta yana fashewa da k'ukan farincik'i itama k'uk'an take....
K'asa ya sauk'e ta ya tsugunna gabanta kana ya bata wani lafiyayyen mari daya sa ta ganin wasu taurari sun gilma ta idanun ta, kara ta fasa abin tausayi sai ta fada jikin sa yana sakin k'uka har da sheshek'a....


Fusk'ar ta daya yi jaa sosai ya riko, cikin fada yace "ina kika je? Me na gaya miki? So kike ki kasheni da raina ko? bana ce miki kullum kina jirana ba? Meyasa kika je gidan su yar ajinku? Tambayar ki nake ya k'arasa a tsawace!"


Gaba daya ya sake rude ta, jikin sa ta shige tana cukwuikwuye rigar jikinsa "Na daina Papi, bazan shake (sake) ba" ta fada cikin maganar yara kana cikin sheshek'a


Jikinsa yaji yayi sanyi, da kallo yabi jik'inta gaba daya uniform din ya dawo baki, ga cizon sauro da yayi rudu rudu a jikinta abunka da farar fata, cikin wani sabon tausayin ta yace "ina kika kwana?"


"Ban shan (san) wurin bah, a k'alk'ashin (k'ark'ashin) wata bishiya na kwana, duk wanda nace ya kaini wajen Papi ba sa k'allona, shine wani baba ya ganni yau da safe ina k'uka yace ina ne gidan mu, nace ban shani (sani) ba shine ya ce ya sunan babana nace masa Papi wai yace bai shani (sani) ba, sai dai ya kaini titi sai na nemi gidan mu, a buumm (haka take kiran mashin da buumm) din shi ya d'ora ni shine ya kawo ni titi, ina ta neman ka, Papi ka taba cik'ina kaji kuululu yake min yunwa ina ji" ta k'arasa tana dora hannun sa kan dan karami cikin ta...


Wasu hawaye ne suka zubo masa yayi saurin sharewa domin baya so ta gani, "kina jina daga yau kada ki kara bin koma wacece gidansu, idan na ba haka ba, babu ruwana da dake, bazan juri rasa ki, ko kina so na mutu?"

Kuka tasa tana girgiza kanta hadi da cewa "kayi haku'ri Papi na daina"

"Toh ya isa yi shiru" take tayi shirun tana kallon sa, fusk'ar ta ya gani chaba chaba da hawaye da majina, tun tana karama sai dai ya zuke mata majina da bakin sa domin ya taba kwada face mata da handkerchief taji ciwo a hanci, saboda wani mugun sulbi hadi da laushi ne da fatar ta. K'yak'yyawan bakinsa ya rufe kan hancin ta ya zuko majinan ya zubar, kana ya sanya hannu ya shiga share mata hawayen daya fara bushewa a fusk'ar ta, Jakar makarantar ta irin na buhun nan ya amsa a hannunta ya rataya a k'afadarsa, kana ya sumbaci goshinta yace "muje gida kiyi wanka sai mu ci abinci, gaba d'aya kin tayar min da hank'ali kaka"

Sai ya d'auke ta kan kafadar sa suka fara tafiya "Papi tamamina(takalmina) ya fadi a kasha(kasa)"

dakatawa yayi da tafiya, kana ya sukunya ya dauki slippers din a kasa, haka ta kwantar da kanta a k'irjinsa tana bashi labari, wani yayi dariya wani yayi murmushi domin Nu'aiymah ak'wai surutu kam...


Kaka dake shara a sanyaye domin tun jiya gidan bai ga gyara ba tayi saurin yada tsuntsiyar ganin Nu'aiymah rungume jikin Nu'aym tana mata murmushi, saurin karbe ta tayi a hannun sa ta rungumeta tana cewa haba Nu'aiymahtou ina kika shigane? Karki Kara tafiya ki barmu kinjiiiiiiii, ki tayar mana da hankali " kaka tace cikin kuka tana ta tatttaba jikinta

Nu'aiymah banda jinjina kai alamun "eh" bata komai, kallon Nu'aym kaka tayi tace "ina ka ganta dannan?"

Ajiyar zuciya ya sauk'e ya fara bata labari a taikace, "Allah ya kara tsare gaba, kada ki sake bin kowa jikata, ki jira papi'n ya zo ya d'auke ki kinji ko?"

Jinjina kai tayi tana tsotsar hannu, wani kallo da Nu'aym ya jefa mata yasa tayi saurin cire hannu tana tabe baki alamun zata yi kuka, bai kulata ba ya samu kujera ya zauna yana mammatse kafafun sa da sai yanzu ya fara jin ciwon da suke masa...

"Maza tube kayan jikin ki muje in miki wanka" Cewar k'aka

Make kafada tayi tana cewa "ni Papi ne zai mun wanka"

"Toh yar ganin dama kin dawo kenan ai zamu fara, saboda ke dubi idanuna sai yaji suke saboda kuka amma dan baki da karki kice bazan miki wanka ba, an ma daina kuka saboda ke..."

Ai dariyar Nu'aym ce ta katse mata sauran maganar ta, har ya daina mamak'in rikicin kaka, shekaru shida baya tana yi balle yanzu, itama Nu'aiymah jin Papi'nta na dariya sai itama ta fara kyakyalle dariya....sosai kaka ta zo wuya ganin daga yar har uban suna mata dariya, sharesu tayi ta cigaba da sharar ta tana mita.

Mikewa yayi ya fara janyo ruwa a rijiya yana zubawa a bukiti(bucket), sai daya cika bucket din ya kalli Nu'aym dake k'ok'awan cire riga yace "ki barshi zan cire miki, dauko kwandon wanka, ba musu ta kawo, rigar ya cire mata ya fara wanke mata dogon gashin ta da duk ta zuba kasa a kai, sai ihu take ruwan yayi sanyi gashi sam bata son a taba kan ta, daya gama yi mata wank'a kana ya dauraye kafafunsa da ragowan ruwan ya riko hannunta zasu shiga daki domin Sanya mata kaya yaji kaka tace " ga kayan ta da basilin(Vaseline) nan na dauko muku ba dan halin ku ba" murmushi kawai ya saki ya dawo ya zauna yayinda Nu'aiymah ke tsaye gaban Nu'aym yana shafa mata basilin din, bayan ya gama ya dauko wasu riga da wando na gwanjo ya sanya mata, kallonta yayi yace "my beautiful daughter, data fi k'aka kyau, muaah kinyi kyau" ya k'arasa cikin salon tsokana yana bata light kiss a kumatun ta...

"Ai karyar ka ta sha karya yaro, ni din nan da kake gani ina budurwar har layi ake a kofar gidanmu, kuma kaf unguwar mu babu mai kyawuna, in gaya maka ehe!"

Matse dariyar sa yayi domin ya san daman zata tanka. "Ni kam ku taho mu ji abinci domin y'ay'an hanjina sun fara juyawa atoh, tun jiya da safe rabona da abinci sai dai kawai idan nazo alwala na dan kwankwandi ruwan buta"

Girgiza kai yayi yana murmushi, indai kaka ce sai cikin mutum ya fashe dan dariya, gaba d'aya tare suka ci abincin wacce ta kasance taliya yar murji ce mai da yaji, bayan sun gama sun sha ruwa, yace "baby yau ba islamiyya time ya kure, ki kwanta kiyi bacci, ni zan je gaereji"

"Toh Papi ka siyo min sweet da chocolate kajiii" ta ce tana riko fusk'ar sa cikin yan guntayen hannayenta.

Murmushi yayi yana cewa "An gama my baby, kaka saina dawo"

"A dawo lafiya dan nan, Allah ya bada sa'a"

Da "Ameen" ya amsa yana ficewa....


*JIGAWA STATE*

Zaune wasu dattijan ma'aurata mata da miji kan wasu had'add'un kujerun kirar Italy, gefensu wani mutum ne mai kimanin shekaru40 sai wata mata mai kimanin shekaru35 a gefen wanna mutumin, cikin laluma hadi da damuwa wanna mutumin mai kimanin shekaru 40 yace "baba dan Allah ka yi min rai, inason Raliya, kabari ta koma dak'in ta"

"Hmmm Alameen kenan, nasan kana son yata Raliya amma baza ta koma gidan ka yanzu ba, saboda wasu dalilai masu yawa, bawai rabaku zanyi ba, a'a ko daya, kawai bazan iya barin ta gidan miji da wanna lalurar ba tunda bazai yu ka tsaya kula da ita ba dole zaka fita nema, ka dai ga halin da take ciki ko?" Baba ya fada yana nuna wata matashiyar budurwa mai kimanin shekaru 25, sai faman yaga littafi take, kansa ya dafa na tsahon yan mintuna yayinda matar dake gefensa sai wani yatsine fusk'a take alamun ta kosa da zaman...

Cikin tausayawa dattijuwar tace "sai haku'ri fa Alameeen, bawa baya huce kaddarar sa, Allah ya shige mana gaba"...✍️




Share saboda Allah
Comment please

Editing is not allowed❌❌❌

Please sister's follow and vote me on
wattpad
@NoorEemaan


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by
NoorEemaan
07082281566

Follow and vote me on wattpad fisabilillah
@NoorEemaan


Congratulations once again sweetheart nimcy luv Allah Ya kara basira da daukaka. 🥳💃🎉










Page11-12
K'amar wani k'aramin yaro haka Alameen ya share hawaye kana yace "nagode mama, sai ya

Please Login or Register in order to submit comment