Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kaka tayi, yasan cewa babu aibu a maganar ta, amma hakan nan yaji haushin su...





Ba tare da ya kalle ta ba yace "k'aka meye laifi dan na saka mata safa? Ina jin duk wani aikin gida baby na k'ok'arin yi duk da tana da karancin shekaru"




" nidai gaskiya na fada, atoh tunda baka son laifinta, ka gama shagwa'ba yarinya komai kayi mata, kabarta tana wasu abubuwan da kanta mana"




Bai sake kulata ba ya sanya mata takalmin ya dauk'i jakar ta ya rataya hadi da riko hannunta, Kallo kaka yayi yace "sai mun dawo"
"Toh a d'awo lafiya dan albarka, ke kuma kada Allah yasa ki min sallama dan nayi wa ubanki fada" kara turo baki Nu'aiymah tayi ba tare da ta amsa mata ba...




Da misalin karfe daya da rabi na rana, Nu'aym tsaye cikin haraban makarantar su baby'n sa, yana jiran fitowar ta, can ya ga ta taho da gudu tana k'iran
"papi nah!"
Murmushi kawai yake sakar mata hannu sa sanye cikin aljihu.

Tana daf da karasowa wajen Nu'aym, wata budurwa dake tsaye ta kira ta da alama malamar makarantar ce, "Nu'aiymahtou Ahmad Nu'aym zo, wancan waye?"

Dan kallo Nu'aym tayi tace "Papi na ne"

Cikin dan daurewar kai Anty'n mai suna maryam tace "meye ma'anar Papi?"

"Mahaifina" Nu'aiymah ta amsa cikin kosawa domin so take taje wajen Papi anty ta tsayar da ita.

Cikin zunzurutun mamaki Anty Maryam tace "what! Kina nufin wancan shine ya haife ki?"

"Eh shine Anty" Nu'aiymah ta sake amsawa.



"Wow! So amazing" ( wow! abin burgewa) Anty maryam ta fada a hankali, Kana ta dafa Nu'aiymah tace "kina da.... Sai kuma tayi shiru tace jeki kawai kinji"
ta ki karasa maganar ne saboda wani tunani data barwa zuciyar ta sani...




Ai da gudu ta sake kwasa ta nufi Nu'aym hadi da rungumeshi, sosai shima ya tallafe ta, kana ya sauke ta, hadi da tsugunnawa gaban ta ya riko kafadunta. Kumatun ta daya ya rike a tausashe yace "bakya jin magana ko baby? Bana hanaki gudu ba?"



Cikin muryar shagwa'ba tace "kayi haku'ri Papi bazan shake (sake) ba"




Murmushi ya saki domin har yau bata iya furta *sake* ba sai dai tace *shake* a fili yace Good girl" hadi da bubbuga kumatun ta a hankali.




"Meye wancan take gaya miki" ya fada yana dan satar kallon anty maryam dake tsaye har yanzu tana kallon su cikin so da birgewa.





Turo dan tsut din bakin ta tayi ta fara cewa "wai, wai, wai cewa take waye kai shine nace mata Papi na ne kai, shine tace wai kina da.... Sai kuma ta yi shiru tace wai inje" Nu'aiymah ta karasa cikin kwaikwayon muryar anty maryam din.





Girgiza kai yayi hadi da mik'ewa ya d'auki Nu'aiymah, suka fara tafiya, tsaf ya karanci yanayin Anty maryam din. Domin ya sha ganin mata masu nuna son da suke masa baro_baro a fili, haka cikin *camp* mata da yawa na zuwar masa da maganar soyaayya sai dai sam basa samun fusk'a, hakan yasa ake masa kallon mai girman kai, domin baya shiga harkan kowa....





Ranar lahadi da misalin karfe biyu na rana ya shirya domin komawa, har karfe biyu lallaba Nu'aiymah yake, sannan ta hakur'a musamman d'aya gaya mata cewa kullum sai ya kira wayar kaka domin yaji muryar ta. Da wanna ya tafi, tana ta faman rusar kuka, jiki da zuciyar sa ba dadi haka ya tafi ba dan yaso ba.
Kaka ta kama aikin lallashin.....✍️







#share fisabilillah
#comment
#vote


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓





Story and written by
*Noor Eemaan





Wattpad
@noorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌



Page 25-26


(Not edited)

..….......................... Bayan Kwana biyar da tafiyar Nu'aym.
Da misalin karfe biyu ya kira wayar kaka, da kyar kaka ta nagane wurin amsawa, ta danna hadi da kara wa kunne ta.

Bayan sun gama gaisawa yace "kaka ina baby?"

"Tana daki kayan islamiyya take sanjawa, Nu'aiymahtou! Nu'aiymahtou!! Nu'aiymahtou!!! Kizo ubanki ke kira"


Nu'aiymah dake daki ta fito da gudu ta amshi wayar cikin zallan farinciki tace "Papi nah!"

Nu'aym dake ta sakin murmushi sak'amak'on uban k'iran daya ji kaka nayi tamkar wacce take wajen gidan yace "My beautiful daughter, ya kike ya school?"

"All fine Papi, ina wuni"


"Lafiya lou baby'n Papi"


"Papi yaushe zaka dawo?" Ta karasa cikin sanyin da muryar shagwa'ba.

Murmushi ya kara saki kana yace " na kusan dawowa gida in sha Allah kinji 'yar Papi?"


"Toh papi nah, kadawo da wuri ina kewar ka kaji, yawwa Papi ka tuna wanna anty'n daka gani ranar daka zo daukana a makarantaaaaa' ta ja karshen maganar


Daga bangaren Nu'aym kuwa runtse idanun sa yayi kana yace " eh na tuna ta"


"Jiya tazo ajinmu tace wai na bata lambar (number) ka, dama na haddace a wayar kaka na bata"


Kara runtse idanun sa yayi yace " baby meyasa kika bata? Da ce mata kika yi Daddy'n ki bai da waya, amma karki sake kinji" ya karasa a tausashe.


"Toh papi bazan sake ba".



" Good girl, yanzu dai kinci abinci?"


"A'a"


"Toh maza kice ki tafi islamiyya karki makara kinji Papi loves you"
.
"I Love you too my Papi bye"


Kaka ce ta karbe wayar ta tace "iyayen gulma wato sai da kuka karar mun da katin waya kai da ubanki ki ko?"



Dariya Nu'aiymah tasa tace "kai kaka papi ne fa ya bugo ai kudinsa zasu cire ba taki ba" amma ina kaka taki yarda ita ala dole su Nu'aiymah sun karar mata da Katin waya...

Nu'aiymah na cin abinci tana yayiwa kaka dariya.


Haka suka cigaba da rayuwar su cikin kauna da kewar Nu'aym, haka zalika shima ta bangaren sa, dan dai da waya hakan yasa suke samun saukin kewar tasa.
Duk watan duniya Nu'aym sai ya dawo yayi musu kwana biyu kana ya koma. Cikin watanin biyar da kudin da yake tarawa na yan bautar kasa ya gyara duka gidan zuwa na siminti tsabanin da da yake na jar kasa. Haka zalika bango sai da aka yi plasta aka yi fentin dark blue da light blue wanda yayi kyau daidai rufin asiri. Kana yasaka a fidda dan karamin kicin(kitchen) daga wajen madafa.
Toilet dinsu yasa aka dawo da shi na zamani(water system) tsabanin da da yake na gargajiya (pit toilet).



*** *** *** ***



Kwance yake a Corpers Lodge di'n su, idanunsa na kallon saman silin yayinda yake bin dan madaidaicin fankan da kallo, a zahiri zaka dauka cewa kallon fankar yake, sai dai ba haka bane, duniyar tunanin kewar Baby Nu'aiymah ya fada. Wayar sa dake saman cikinsa tayi kara, ta d'auki sakon sitti tana ringing kana ya daga k'iran ba tare da ya kalli lambar daya yi k'iran ba...

"Assalama alaykum, aminci Allah ya tabbata agareka"


Dan bata rai yayi sakamakon jin wata murya, haushi ya kama shi, sam ya tsani mace ta dinga make murya nan, yafi son mutum yayi magana da natural voice din shi"

"Murya a daure yace "wa'alaiki salam"


Daga dayan bangaren wani yanayi ne ya ratsa zuciyar anty Maryam, sak'amak'on dadi da gardin muryar Nu'aym tace "ina fatan kana lafiya, ya 'yata take?"


Wani killer smile Nu'aym yasaki wato har da tambayar 'yar sa Saboda iyayi da neman shiga. A fili yace "tana lafiya"


"Naji ji dadin jin hakan, nasan baka shaida ni ba, Maryam ce anty'n su Nu'aiymah"

Sarai yasan itace a fili yace "ohh"

"Am dan Allah idan bazaka damu ba ina son muyi wata magana da kai, my handsome "

Wani takaici yasake kama Nu'aym jin ta kira shi da "handsome" a fili ya furta "ina busy, may be wani lokaci" yana fadin haka ya katse k'iran, take ya maka ta a black list, sam ya tsani rashin aji arayuwarsa...



Daga bangaren anty Maryam kuwa ta dan ji ba dadi ganin ya katse k'iran, amma ta wani bangaren taji dadin jin muryar sa. A afili tace " in sha Allah, zaka zamo mallakina" ta fada tana bin lafiyar gadon ta ta kwanta.







*BAYAN WATA SHIDA*
A yau Allah ya nufa su Nu'aym suka gama bautar kasar su, haka dai yayi sallama da garin *Jigawa* tare da wadanda yayi zaman mutunci dazu, bai bar garin ba sai da ya yi submitting CV d'insa a masa'anta masu yawa, kana yayi tsaraba wa baby'n sa da kaka ya nufi *Sokoto*....



Bayan sun iso kofar gida a tasi (taxi) tare da mai tasi din suka fito, ya taya Nu'aym fito da kayan dake booth yana sauke su kasa.



Wasu yara dake ta wasa a kofar gidan suka shiga kai kayan cikin gidan, sallamar mai taxi yayi, hadi da bawa yaran kudi suka hau tsallen murna, murmushi yayi ya nufi cikin gidan...


Sallama yayi yaji shiru, ya dan yi mamaki ganin ba kowa a tsakar gidan.
Dakin kaka ya leka yaga bata nan, ga bandaki a bud'e. A dakinsa ya fara jin tashin kuka kasa _kasa a tamanin ya nufi dakin....

Nu'aiymah ya hango kwance kan katifarsa tana ta murkususu, cikin sauri ya nufi gadon hadi da tallafo ta jikinsa, cikin zallan damuwa dake shimfud'e a fusk'ar sa, riko fusk'ar ta yayi yace "baby! Mike damunki? Talk to your father, gaya min mike damunki" ya fada cikin damuwa da tausayinta.

Ta kasa magana sai kuka take, cikin dauriya tace "Papi!"

"Na'am baby gayamin meke damun ki?" Yafada kamar shima zai saki kukan.

Kasa magana tayi sai hannunsa data kamo ta doro kan cikinta, dake mugun yi mata ciwo, tama rasa takamamme inda take jin ciwon


"Sorry kinji, cikin ke ciwo, muje a baki magana ya fada yana kokarin tashi da ita a jikinsa.


Daidai lokacin yazaro ido cikin madaukakin mamaki, bata tare da yasan maganar ta fito fili ba yace "jini"

Gaba d'aya zanin gadon ya baci da jini, take ya fahimci cewa jinin al'ada ta fara, "my daughter is now matured('yata ta girma yanzu)" ya fada a ransa da murmushi a fusk'ar ta, duk da yayi mamakin ganin ta fara period a wanna shekarun nata, sai dai ba abin mamaki bane ikon Allah kenan .


Sai a lokacin itama ta ga jinin d'aya bata zanin gadon, wani ihu hadi da kuka ta saki tana cewa " Papi jinina zai kare, jinina yoyo yake papi, ka sayar da jinin kaji kada ya kare" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta da yarinta.


Da ace bai matse dariyar sa ba, babu abinda zai hana shi dariya duk da matsanancin tausayin ta dake ratsa shi. Afili yace "Baby yi shiru kinji, jinin ki bazai Kare ba, yanzu muje in hada miki ruwa ki yi wanka...


Tana d'auke a jikinsa har tsakar gida, ya sauke ta, ruwa ya cika bokiti(bucket) da shi ya mika mata toilet, wani zani d'aya gani a shanye kan igiya ya mika mata, yace " baby shiga wank'a ina zuwa"

A sanyaye ta nufi toilet din tana k'uka, sai daya ga ta rufe bandakin kana ya fice zuwa kanti domin siyo mata *sanitary pad* (kunzugu).



Manage please na gaji da yawa😔



#Share
#Comment
#Vote


Please Follow and vote on wattpad @NoorEemaan

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓



*Written by*
Noor iman



*wattpad*
@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌



(Pls sister's👏 vote and follow me on wattpad @NoorEemaan)











27-28


(Not edited)

............ Ɓayan yaje kantin ya siyo sanitary pad mai suna MOLPED. Ƴa dawo gidan yaga har yanzu bata fito ba, sai kukan ta dake tashi kadan_kadan a bandakin.



Dakin kaka ya shige yana mamakin ina taje haka, pant din Nu'aiymah ya dauko ya ajiye kan gadon kaka kana ya zauna yana jiran shigowar ta...


Bayan kamar mintuna goma da zaman nasa ta fito idanunta jajur, tana tafiya a hankali tamkar mai koyan tafiya, kafe ta yayi da ido, tausayin ta fall zuciyar sa, kawar da kansa yayi hadi da cewa "gashi ki kimtsa jikin ki..." Ya karasa ya nufi hanyar waje


"Papi nah!" Ta kira sunan shi a raunane


Cak! Ya tsaya batare da ya juyo ba.


Ganin ya juya yasa tace "Papi kaga jinin har yanzu yana zuba da yawa ko kuma ni mezan yi da wanna abun" tace tana nuna sanitary pad din.


Tausayin ta mai yawa ne ya darsu a ransa, hakika ita din karamar yarinya ce bata san kan abun ba.


A hankali ya juyo yace "Baby ki saka pad din a jikin ki, ina waje"


"Papi ni ban iya sawa ba"


"Ooh God! Baby nima ban iya ba, ki..." Sai kuma yayi shiru ya dawo gadon ya zauna.



Pad din ya dauko ya kurawa ledar ido yana karanta bayanin da suka yi hadi da hoton da aka zana mai d'auke da yanda mutum zai saita pad din a jikin pant, tare da awanin daya dace mutum ya cire Saboda kiyayye lafiya.



Bayan ya gama saita mata, ya bata yace "saka shi, ki saka kaya, ina waje"


"Toh papi" tace tana kokarin cire zanin data d'aura.




Zanin gadon sa daya baci da jini ya cire hadi da kayan ta. Amo ya jika da ruwa cikin babban roba, kana ya daga zanin gadon da nufin fara wankewa, hakan yayi daidai da sallamar kaka....




Salati ta sanya ganin jini a jiki zanin gado, cikin tsoro tace "dan nan ina ka samu jini? Ciwo ko kaza ka yanka mana?" Ta fada tana dube_dube, idanun ta suka hango mata kayan fadeelah a kasa, take ta fahimci abinda ya faru. Cikin sauri ta nufi daki ta hango Fadeel na kokarin sanya wando.



_"ya rasulillahi manzon Allah, Ohh duniya"_
Kaka tace cikin mamaki tana kallon Nu'aiymah.



Da gudu Nu'aiymah ta fito ta rungume Nu'aym ta baya tana cewa "Papi kana jin kaka ko? Kace ta daina, tana sani kunya" ta fada cikin iyakar gaskiyar ta tana boye fuskarta, yayinda take kuka.



Juyo da ita yayi ya rungume, yana bubbuga bayanta alamun rarrashi, cikin son kwantar mata da hankali yace "yi shiru kinji, daina kuka you see jikin ki ya yi zafi"




Hannunta ya riko suka dawo kan tabarma yace ta zauna kana ya cigaba da wankin sa, batare da ya kula kaka dake ta salallami ba.



Bayan ya gama ya shanya kayan hadi wanke hannunsa ya dawo kan tabarma ya zauna hadi da dora kan baby Nu'aiymah kan cinyar sa yana dan bubbuga bayanta...



"Yayi muku kyau uba da 'ya, gabadaya kun share ni"



"Ohh! Kaka a enough please, kin tafi ki bar min Baby cikin mayuwancin hali, da ban dawo ba fa?"




'Kaga malam karka isheni da wani turacin karyan ka, har da wani enop(enough) unguwa naje dubiya, kafin na tafi kuma lafiya lau na barta, gata gabanka ka tambayeta, Nu'aiymahtou ba lafiya lau na tafi na barki ba, har kika ce na siyo miki cakulat(chocolate)? " ta dawo da maganar kan Nu'aiymah cikin tsigar tambaya.



Turo baki Nu'aiymah tayi hadi da cewa "Eh"



"Toh kaji dai da kunnenka, da za ka fara min wani kumbure_kumburen ka na banza, wai kai mai 'ya ko"



"Toh naji, ya isa kakus" ya fada cikin gajiyawa da maganar ta.



"Yawwa 'yar nan bud'e kunnen ki, ki ji abinda zan gaya miki, daga yau kin girma fa, babu ke babu wasa da namiji ko kula wani namiji, idan kika bari namiji ya taba ko da yatsan ki ne, shikenan zaki samu ciki, ki nutsi ki daina tsalle_tsalle, ki kula da gyara jikin ki idan ba haka ba wari zaki na yi, da kin shiga mutane zasu fara gudun ki idan bakya kula da tsaftar jikin ki..."



Kukan Nu'aiymah ne ya katse Mata sauran maganar ta, ita babu abinda yafi sa ta kuka kamar cewa da kaka tayi za a dinga gudun ta.



Runtse idanun sa yayi kana ya ware su kan kaka yace "kaka! kaka!! kaka!!! Please ya isa, tayaya baby zata iya daukan duka wadannan kalaman naki? Sun yi mata tsauri dayawa, domin har yanzu yarinya ce karama, kin sani cewa bata zuwa ko ina, daga makaranta sai gida, ni ki daina sa min ta kuka"




"Toh ka fini son ta ne? nace ka fini son ta ne? nima ina son ta ai, shiyasa ma na zauna ina gaya mata abinda ya dace, tunda kai uban zamani ne baka gaya mata ba, kuma da kake cewa ba ta zuwa ko ina, ai na fika sanin Nu'aiymahtou mai nutsuwa ce, amma dan yau ne ka haife shi baka haifi halin sa ba, a toh ka barni in gaya mata, kina jina Nu'aiymahtou ko? rabu da Papi'n ki....." Haka dai kaka ta cigaba da yiwa Nu'aiymah nasiha, Nu'aym kuwa tagumi ya buga yana kallon kaka...




*** *** *** ***



*BAYAN KWANA HUDU*
A yau jinin Nu'aiymah ya d'auke, tayi wanka, kasancewar ta san yanda ake wakan jinin haila domin a islamiyya ana koya musu.



Bayan tayi wanka ta fito ta sanya kaya, kaka tace ta zauna ayi mata kitso ko hudu ne yayi bushe da wuri kasancewar tana da cikar gashi hadi da tsayi. Ai ana fara taje gashin ta fara matso hawaye, kaka sai mita take "dole ki so kitso yarinya, tunda kin zo a mace, idan kuma ba haka ba sai a aske gashin kowa ya huta"



Ana haka Nu'aym ya dawo daga gareji, kasancewar bai samu aiki har yanzu ba, ya sanyi shi ke zuwa garejin.




Tun kafin ya karaso Nu'aiymah ta kara sautin k'ukan ta, zama yayi ya shiga lallashin ta, amma inaa sai juya kai take, jikin sa ya sanya ta ya shiga lallaba ta, har aka yi kitso zane guda hudu...





Ana gama wa kuma ta shiga nunawa Papi kitson daga sauka har wajen mazaunan ta, shafa kan yayi yace "kitson yayi kyau Sosai Baby na"





Washegari da misalin shida da rabi na sanyin safiya, Nu'aymah ke tsugunne cikin kitchen gaban murhu sanye da kayan Nu'aym na bautar kasar sa da aka rubuta NYSC da manyan haruffa sai hula p-cap, kana ta d'aura zani, ita ala dole tasa kayan Papi, domin sosai take son kayan, ita bata ki kullum ta sa kayan ba, Nu'aym har dariya yake mata idan ta saka, domin kayan yayi mata yawa.



Doya hadi da kwai da Nu'aym ya kawo jiya, wanda yau kaka zata yi musu karin kumallo dashi ta d'auko, dakyar take iya fere doyan domin rinjayar ta yake, haka ta fere wani wajen har da bawon doyan a jiki, ga jikin ta daya fara yi mata kaikaiyi sak'amak'on taba jikin ta da ta yi da hannu da take fere doyar, still dai bata hakur'a ba, ta fara datsa doyar, kasancewar wukar mai kaifi ce yasa bata sha wahalar datsar ba.




Bayan ta gama ta wanke doyar, sai ta fasa kwai nan guda shida, a wani kwano karami, dama wuta ya huru har ya gaji da ci, domin shine abu na farko data fara yi.



Wata tukunya da kaka ke suya akai ta dora a wuta, hadi da zambada mai da suke tattalawa cikin tukunyar, doyar nan a danyar sa haka ta tsoma shi cikin kwan da ko Maggi mai samu ba, ta sanya cikin man daya dau zafi, ganin kwan yana kama jikin doyar yasa ta saki yar karar murnan a fili ta furta "yau papi da kaka zasu ci girkina, Papi zai ji girkina yafi na kaka dadi"


Haka dai ta gama suyar da ko wani wajen mai bai taba doyar ba, ta kwashe a wani faranti mai murfi tana jin wani dadi na ratsa ta, gamawar ta keda wuya kaka ta fito Salati sauke a bakin ta, ganin har rana ta fito bata dora musu karin kumallo ba...

"Amma 'yar nan baki da kirki, dama kin tashi baki tashi ni ba, in dora mana girki"



murmushi murna tayi hadi da cewa "ai na yi mana girki kaka" tace tana nuna farantin da hannun ta


"Kinyi me?" Kaka tace cikin daga murya yayinda ta kwalalo ido.

"Na soya mana doya da kwai" ta kara fada murmushi d'auke a fuskar ta.



"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" shikenan kinyi mana bakin cikin cin kayan dadi, kika san yanda nake ta zumudi gari ya waye kin soya mana, wa ya aike ki ni zainabu?"




Nu'aym dake tsaye bakin kofar dakin sa, sai gimtse dariyar sa yake, domin kaka ta bashi dariya.



"Toh kaka ki ci d'aya kiji akwai dadi, wallahi na fika iya girki" Nu'aiymah tace tana kara sakin murmushi irin na alfahari da kanta dinnan




Gaban Nu'aiymah kaka taje, daya ta dauko ta sanya a baki, furzar wa tayi sak'amak'on wani karnin kwai, ga doyar danye.



"Amma kin gama da mu wallahi, dan nan, dandana kaci ko tafasa doyar bata yi ba" kaka ta fada tana ansar faranti daga hannun Nu'aiymah ta mikawa Nu'aym.



Wani murmushi ya saki, kana ya dauki daya, idanunsa kafe kan na Nu'aiymah dake ta sakar masa murmushi, ita tasan ubanta zai yabi girkin ta, haka ta aiyana aranta.




Tauna daya yayi ya kasa hadiye wa, Saboda wani dandano mara dadi daya ziyarce harshen sa, dan bata fusk'a yayi ya furzar da doyar a bakin rariya ya kuskure bakinsa ya dawo gaban Nu'aiymah data fara matso hawaye, kaka sai cewa take "kaji abinda naji ko nu'aymu, abu salam ba armashi" amma bai kulata ba.



kafadun baby'n sa ya riko yace "My baby ta girma har ta ita girki, kinyi kokari sosai kinji"



Turo baki tayi tace "toh meyasa ba ka ci ba Papi?"



Dan murmushi ya sakar mata yana share mata hawayen yace "ki bari anjima zan gaya miki kuskuren ki, sai ki gyara nan gaba kinji ko"



Murmushi ta sakar masa tace "Papi jikina kaikaiyi yake min"



"Ai dole baby, doya fa kika fere, bari na zuba miki ruwa kiyi Wanka"



Kaka data saki baki tana kallon su tace "amma baka yi ba, ina jira kayi wa 'ya fada, amma ka kama wani iyayi wai kai nunawa 'ya soyaayya ko? Ai shikenan sai mu zauna ba karin safe"





Bayan Nu'aiymah ta fito ta sanya kayanta, har lokacin kaka mita take, Allah yasa yana da dan kudi a hannun sa, ya siyo musu biredi(bread) dan dari biyu da hamshi, sai kayan shayi na dari biyu da ya siyo musu sukayi karin safe(breakfast) amma inaa har yanzu mitar kaka bai kare ba, fadi take Nu'aymah tayi musu asara da bakincikin cin kwai da doya...







(Gobe ma zan yi kokarin yi muku update, am so sorry habibtie's, wutar mu ce ta lalace, sai jiya da magrib aka gyara. Nagode sosai da kauna
Noor loves you too)



#Share
#Comment



🍇🍇PAPI NE🍓🍓




Written by
Noor Eemaan






Wattpad
@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌















page 29-30

(Not edited)

BAYAN SHEKARA DAYA

Nu'aym ne ke tsaye cikin shigar kananun kaya, hannun sa soke cikin aljihun wandon sa, yayinda fuskar sa ke fidda murmushin farinciki Wanda baya rasa nasaba da wayar da yake.



Ajiyar zuciya ya sauke, kana ya mai da duban sa ga su kaka da Nu'aiymah dake jiran ya musu bayani.


"Kaka na samu aiki, a wani babban masa'anta dake Jigawa, sannan sun sanar dani cewa albashi na dubu dari uku"

Ai ihun kaka da na Nu'aiymah ne ya karade ila'irin gidan, yayinda Nu'aiymah ta daka tsalle ta fada jikinsa tana murna.


Murmushi k'awai yake saki, yana shafa bayan Nu'aiymah, hakika duk wani tsanani yana tare da sauki, a yau shi ya samu aiki da har za'a biya shi dubu dari uku bayan tarin wahalhalun da suka sha, idanunsa sun dan tara ruwan hawaye daga gefen idanun sa, na zallan farinciki.


Haku'ri hadi da add'ua ne suka kawo shi matakin da yake kai yanzu, domin da wuya a samu Wanda yake da kwalin degree ace kuma yana zuwa aikin gareji. domin girman kai da wasu suka d'aura wa kansu. Gashi d'aya yi haku'ri, Allah ya musanya masa da mafi alkhairi.


Managar Kaka ya katse masa tunanin sa, "d'an nan zo zauna ka bani labari, kai alhamdulillah Allah mun gode maka, na ma rikice Nu'aymu, dubu dari uku nawa kenan?"



Wani murmushin ya sake yi, sauke Nu'aiymah daga jikin sa yayi suka zauna kan tabarma yace "kaka dubu dari sau uku, sannan sun ce ranar litinin zan fara aikin, amma ni ranar lahadi zan tafi nan da kwana hudu kenan".

Kuka kaka ta fashe da shi tana cewa " Alhamdulillahi ala kulla halin, Allah abin godiya, yanzu da wata ya kare ɗan nan zaƙa rike dubu dari har sau uku " ta fada ta na gwada uku da yatsun ta. Kana ta cigaba "yanzu ɗan nan, zamu ɗawo cin kaza, dankalin bature, doya da kwai, ɗa shayin madara mai kauri kamar ƙoƙo, ohh! Allah ya nuna mana karshin watan lafiya"

Dariya Nu'aiymah da Papi suka sanya, harda tafawar su, domin yanayin yadda kaka tayi maganar har da hadiyan yawu dole mutum yayi ɗariya.


Ɗan bata fusƙa ƙaƙa tayi tace "

Please Login or Register in order to submit comment