Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shi kam har da mikewa. "Ah ah kun san juna ne?" Wata yar'uwar su Raliya ta tambaya.



"Eh na san shi a sokoto" Nu'aiymah ta amsa.



"ikon Allah, dama kun hadu a sokoto, kuma baku san ku yan'uwan juna bane " matar ta kara fada, kana ta bawa habib Husain labarin komai a tak'aice.



Anan dai Nu'aiymah take jin cewa uwar Habib Husain a dangin su Al'ameen take. A tak'aice dai habib Husain cousin din Nu'aiymah ne, sosai ta sha mamaki kuwa, daga baya ta share, domin ita kam ta gama shan mamaki tun daga ranar da ta ji cewa papi ba shine mahaifin ta ba.






Ya kuwa jima a gidan suna hira, Habib Husain farinciki kamar ya zuba ruwa a kasa yasha, domin a ganinsa komai zai zo masa da sauki yanzu tunda Nu'aiymah dai yar'uwar sa ce...







Share fisabilillah

Comment





9:06pm



Comment dinku is needed😎



ÑõõrËêmaãñ ce😍


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓





*WATTPAD
@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




Page 73-74



......Ɓangaren Nu'aymah kuwa bata kowa komai a ranta ba, ta biye masa suka yi hira sosai, domin a tunanin ta tunda ya dauki tsahon loƙaci bai neme ta ba, domin tun ranar da papi ya kora masa warning bata kara ganin sa ɓa, ko da a waya ne hakan yasa ta dauka ya hakura da ita.




Sai ɗai ɓangaren habib husain ba haka bane, dama yana son ta, amma shaƙƙar jan kunnen papi ya sashi janyewa, sai yanzu tsohuwar zumar sa ta tashi.



Habib husain bai jima da tafiya ba, al'ameen ya ɗawo, daga kofa ya tsaya ya warewa nu'aiymah hannu, da gudu ta shige jikin sa ya rungumeta, yana jin farinciki a ransa sosai.



Raliya na gefe tana kallon su fuakar ta dauƙe da murmushi. ɓayan ta gaishe shi ta mikawa nu'aiymah fadeel ta shiga shirƴa musu dining area domin suyi dinner..




Bayan sun gama sun ɗawo falo, suka cigaba da hira, a marairaice Nu'aymah ta kalli al'ameen tace "Daddy ka kira min su papi nah muyi waya dan Allah" Murmushi Al'ameen yayi yace "Yanzu kuwa ƴar gidan papi, in sha Allah zan taho miki da waya, kema kina amfani dashi"



"a'a Daddy papi ya hana, wai sai na gama secondary school zai siƴa min, yanzu idan yaga na rike zai yi fushi ko mummy" ta karasa tana kallon Raliya.




jinjina kai Raliya tayi fuskar ta dauke da murmushi, tana kuma kara yaɓa wa namijin ƙoƙarin ɗa Nu'aym wajen kula da ƴar su, haka zaliƙa AL'AMEEN...




dama ya amshi lamɓar kaka hakan ya sa shi dialing lamɓar... ringing daya zuwa uku suka ji murƴar kaka ta rangwaɗa sallama....



Amsawa Al'ameen yayi ya gaisheta cikin girmamawa, amsawa kaka tayi sai ta fashe da kuka tace "Aminu yaushe zaku dawo mana ɗa Nu'aiymatou? kullum cikin kewar ta muke, ja'irar itama ɗaga zuwa yin kwana biyu sai tayi zaman ta" dariya Al'ameen yayi yace "kiyi hakuri kaka, tana nan dawowa gareku, ai aro kuka bamu, dan Allah ki kwantar ɗa hankalin ki, yanzu ma ita tace na kira ku gaisa"



"Toh ai shikenan, bata wayar" kaka ta fada tana jan majina



Amsa babyn papi tayi tace "kaka nayi kewar ku, ina papi nah?" ta fada muryar ta na rawa alamun tana ɗaf da sakin kuka.


"amma ƴar nan baki da kirki, uban naki kadai kike tamɓaya ko? saboɗa ni ba mutum bace ba, shi Nu'aymu da kike tamɓaya ya fini damuwa da rashin ki ne, ja'irar 'ya kawai?"



Murmushi Nu'aiymah tayi, a yau bata ɗa karfin ɓiƴewa kaka, hakan yasa ta saki murmushi daya sa idanun ta ciko da kwalla. "kiyi hakuri kaka nayi kewar ki sosai, ina wuni ya kuke?"



"toh yanzu naji batu, lafiya lau yar albarka, ya mutan jigawa"


"suna lafiya kaka" Nu'aiymah ta amsa.



"Toh masha Allah! in gayamiki 'yar nan papi'nki ya dawo wani iri, tunda kika tafi na kasa gane kansa, gabadaya kewa ya ishe ni, ga shi ko kulani baya yi, ya daina min magana sosai, daga gaisuwa shikenan, sai kace wacce muka yi damɓe yana ci_cin magani"



Sosai jikin Nu'aiymah ya kara yin sanyi kalau, "kaka ina papin yake"



"oho masa kila toh yana dakin sa" kaka ta fada.



" Toh bari na kira layin sa tunda na haddace lambar sa"


"toh shikenan" kaka ta fada.


Sai a lokacin Nu'aiymah ta lura iyayen nata basa falon, saka number'n papi tayi ta yi dialing, har ta katse bai ɗaga ba, kara kira tayi nan ma ba'a daga ba, sarkin shagwaba kuwa tuni ta saki kukan sakalci...



A Karo na uku ta sake dialing number'n sai da ta kusa sinkewa ta ji ya daga.


"papiiiii" ta ce tana sakar masa kuka.


azabure ya mike daga kwancen da yake yace "baby? ooh no please stop that, kuka kuma?"


"toh ba kai bane kaki daga wayar tun ɗazu"


"oh! sorry ban san ke bace, da tuni na daga, am sorry kinji baby"

jinjina kai tayi kamar yana gabanta, tana share hawaye, amma bata ce komai ba.


"babyyyyyy?" ya fada a dame jin bata ce komai ba.


"Na hakura papi nah"


Ajiyar zuciya ya sauke yana jin nishadi na saukar masa.


"i miss you so much baby, ki dawo gida hakan nan" ya fada.


"i miss you too papi, zan dawo kaji"


Kamar yaro dan karami yace "Toh" abin tausayi, taɓɓas ya gama fahimtar cewa raunin sa itace Nu'aiymah, tamkar da kaunar ta aka halicce shi, domin abinda yake ji a kan yar tasa ya wuce So. A yan kwanan kin nan ba karamin damuwa yake shiga ba, bacci ma baya iyawa, abun na damun shi ainun, rashin baby a kusa da shi tamkar rabuwar wani sashe ni daga jikinsa, yasan cewa idan yaje jigawa domin taho da ita babu mai hanawa, yasani cewa Al'ameen zai bashi, amma bayason suyi tunanin yana nuna iko da ita ne, tunda su ma sun cancani zama da ita, ita din jinin su ce, Allah kawai ya kaddara basu zasu raine ta ɓa.


Ajiyar zuciya ya sauke jin muryar baby na cewa "papi bacci ka yi bacci ne"


Murmushi ya saki, ooh baby kuruciya, tayaya zai iya yin bacci, suna waya.


"A'a baby idon papin ki biyu"


"toh papi ka saki ranka kaji, kaka tace yanzu baka kulata, bata rai ka ke"


Murmushi yayi yace "rabu da kaka kinji, kin san ta da rigima, wai lambar waye kika kirani dashi"



Murmushi itama tayi tace "lamɓar Daddy ce" jinjina kai yayi...

ai fa nan ta shiga bashi labarin yan jigawa, labari ya yi labari har ta sako zancen Habib Husain, ta shiga gayamasa har da dangatakar dake tsakanin su.


Sosai gaban sa ya buga, har sai daya runtse idanun sa, tuno habib husain, da irin soyaayar daya gani yana wa baby ya shiga gilmawa ta cikin idanun sa, gashi kuma yanzu yana matsayin dan'uwa a gareta.



Gashin kan sa ya shiga hargitsewa yana jin wasu alburusan kishi na caka ko wani sassa na jikin sa, sosai yayi ƙoƙarin daidaita muryar sa, yace "baby dare yayi, zan kwanta ko? gobe zan kira ki kinji na ji ya ya kuka tashi, sannan kiyi addu'a kafin ki kwanta bye" ya karasa yana katse kiran, bai ma tsaya jin me Nu'aiymah zata ce ba...


Sosai bacci ya kauracewa Nu'aym, juƴi yake yana tunanin mafita, sai gabanin asuba bacci ya sace shi. Bangaren Nu'ayimah kuwa ta shima sosai kafin bacci ya dauketa, domin papi ya sabar mata da hira har bacci ya dauke ta...



Bangaren Habib husain kuwa yana barin gidan AL'AMEEN wajen mahaifiyar sa ya nufa, bai yi wata_wata ba ya sanar da ita komai daga sanin da yayi wa Nu'aiymah da irin son da yake mata, komai dai bai ɓoƴe ba, domin ance a bari ya huce shi ke kawo rabon wani...





SHARE


COMMENT





NOOR🌟




🍇🍇PAPI NE!🍓🍓






*WATTPAD*
@NoorEemaan








EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌




page75-76



.......Sosai mahaifiyar Habib Husain ta ji dadi da batun da ɗan na ta ya fada, saboɗa a loƙacin da ta ga Nu'ayimah taji ta kwanta mata a rai, ta kuma yi wa Habib din sha'awar ta, amma bata son abinda zai sa danta yaga kamar dole ta yi masa, hakan ya sanya bata furta ba, ta yi shiru da bakinta, ashe shi yana ma sonta, wanna abu yayi dadi mata ɗaɗi kwarai.






Kallon habib husain tayi, fuskar ta ɗauke da murmushi tace "karka damu habib, in sha Allah zan yiwa AL'AMEEN magana, naji dadi sosai, Allah ya tabbatar da alkhairi"






Rungume mahaifiyar sa yayi yace "Ameen"




******************



Zaune Nu'aym yake a falo, ya hada hannunsa waje daya, sosai yayi zurfi cikin tunani, hakika labarin habib Husain da baby ta bashi ya fi komai daga masa hankali



Da sallama Kaka ta shiga falon hannun ta dauke da gyada irin na kwalbar nan tana zazzagewa tana taunawa




Ganin bai amsa sallamar ba, ya saka ta zama kusa dashi ta dafa shi, cikin sauri ya waiwayo ya kalli kaka, sai kuma ya dauke kansa yana sauƙe boyayyen ajiyar zuciya




"Dan nan! wai menene ya dame ka haka ne? Gabadaya ka kuntatawa kanka, baka da walwala uhm"



A hankali ya dago jajayen idanunsa ya sauke su cikin na kaka. Hannun kaka ya rike gam, tamkar baya son yin magana ya bud'i baki yace


" Kaka damuwa ta baby, na kasa jure rashin ta, ga kuma habib ko waye yake da suna...." nan ya shiga bawa kaka labarin dangantakar dake tsakanin Nu'aiymah da habib Husain din a yanzu.






Sosai Kaka tayi mamakin hakan, ita kam har ta manta da labarin habib Husain din.


Kallon shi tayi, so take ta bugi cikin sa taji
ainahin abinda take hangowa a idanun sa hakan yasa tace

"Nu'aymu dama dole wata rana zamu rabu da Nu'aiymahtou, ko ba komai akwai aure, idan tayi aure taje gidan miji shikenan kuma, sai dai ta kawo mana ziyara"







A zabure ya kalli kaka, har wani tashi gashin kansa yake Saboda tashin hankali da kalaman Kaka suka haddasa masa, cikin murya da amon sa ke fidda zallan tashin hankali yace "kaka ba zamu rabu da baby ba, har abada! Mutuwa ce kadai zata raba mu, kamar yadda muka rayu tare tun kuruciya haka zamu kasance, mutuwa ce zata raba mu, Bazan taba amincewa ta kasance matar wani ba, baby a matsayin 'ya ta take, amma tabbas zata kasance matata in sha Allah, Kaka kin kasa fahimta ne? Ki fahimta mana cewa zuciyata na bugawa a ko wace dakika domin ita, kaka ki fahimta cewa baby ce! zuciyata ta riga ta nutse cikin kogin son baby, I love her Kaka, Tayaya kike tunanin zan iya rayuwa babu ita, Tayaya zan bari ta auri wani bayan ni ina raye"






Kauda kai gefe kaka tayi tana sakin murmushi irin na manyan nan, duk zurfin jikinsa dai yau ya bud'e baki yayi magana, jinjina kai tayi tana jinjina wanna al'amarin d'aya shigo musu mai cike da abin mamaki, ta kuma tausaya masa sosai, dama ta da de da hango cewa wanna shakuwar tasu zai dawo wani abu mai girma.


amma Saboda rikici yayi wa kaka yawa Maimakon ta lallaba shi, amma ina sai ta fara hanlin na ta.




"Kai yanzu dan nan, dan baka da ta ido shine zaka ce kana son 'yarka! Kasan dai yarinyar nan har yanzu tana maka kallon uban ne, duk da cewa iyayenta sun bayyana, kana gotai_gotai da kai, kitika_kitika da kai zaka zauna kace kana son ta, Saboda shaukin sonta ya maka yawa har da wani cewa I lobe ha(I love her)" ta karasa tana kwaiƙwayon muryar Nu'aym din.





Mikewa yayi kamar zai tashi Sama ya bar mata gidan cikin bacin rai, shi kam yanzu ba shi da lok'acin biyewa kaka, domin abinda ya dame shi daban, mafita kawai yake nema




Ta bangaren Kaka kuwa bayan ta ga fitar sa, da kyar dai ta gano lambar Al'ameen ta kira shi, bayan sun yi doguwar gaisuwa, kaka ta shiga bashi labarin komai, Al'ameen bai yi wani mamaki ba, domin tun daga ranar daya ga Nu'aym din ya hango zunzurutun son 'yar sa a idanun sa.

Kuma gashi ya riga ya amsawa mahaifiyar habib Husain da ta zo masa da maganar dan ta yana son Nu'aiymah, amma yace Mata sai ya ji daga bakin Nu'aiymah tukunnah.




Bai boye wa kaka ba, ya sanar mata, jinjina lamarin kaka tayi, tana fatan Allah ya zaba musu abinda yafi alkhairi, da haka suka yi sallama.







Sai kuma jikin Kaka yayi sanyi, tausayin Nu'aym din ya rufe ta, har hango tashin hankali da zai yi idan baby'nsa ta zama mallakin wani, amma idan Allah yace ba tasa bace dole yayi haku'ri, da watan tunanin ta cigaba da tauna gyadar ta, amma a sanyaye sabanin dazu da har karan taunar gyaɗar bakin ta ke tashi.





Ta bangaren Al'ameen kuwa, yana zaune tare da Raliya a lokacin da kaka ta bugo waya, kallon shi tayi tace

"a gaskiya yaya hankalina yafi kwanciya da a bawa papi Nu'aiymah, Saboda sun riga sun zama abu daya, ta saba dashi matuk'a, ya kuma san komai nata, karka manta next two month zata yi clocking 17years da kuruciya a tare da ita, amma tunda shi ya san komai nata, zaman su zai fi tafiya dai_dai a shine mafita, domin Yanzu idan kace zaka bata zabi, ba lallai ta zabi shi Nu'aym din ba Saboda kuruciya, domin zata ce ai Habib Husain ya ce yana sonta, shi papin nata bai taba cewa yana mata so irin na aure ba, ka gane? So may be bayan anyi auren da habib din, sai a rasa kwanciyar hankali domin rigima zata saka tace ita wajen su papi zata koma, kullum ina lura da ita sai tayi kukan rashin su, kaga me aka yi kenan, shiyasa bana so a bata zabi saboda zata iya zabar abinda zai dame ta nan gaba, Nu'aiymah tayi kadan ta san waye take wa ainahin so, amma tabbas ina mai tabbatar maka aka aura mata papin nata zaka yi mamaki irin kaunar da suke wa juna, amma dai a ganina a kira family meeting kaji shawarar mutane" ta karasa tana kallon Al'ameen.





"Haka ne kam kanwata, nima wallahi har raina na fi kaunar bawa Nu'aym din auran Nu'aiymah, kamar yadda nace har Abada bazamu iya biyan su ba, toh wallahi ba zamu iya ba, amma idan ya mallaki 'yarmu hankalina zai kwanta, kuma zan yi amfani da shawarar ki wurin Kiran family meeting"






A WhatsApp group din su na family meeting ya sanar da meeting din.






***********




Two day's later kowa ya hallara a family house din su Al'ameen.

Babu bata lokaci ya sanar da dalilin taran su dayayi, domin yasan cewa yan'uwan sa zasu bada shawaran abinda ya dace ayi, Saboda sosai suke da hadin kai a family dinsu.





A tak'aice dai kowa ya kawo shawaran sa da hujjojin sa, inda mafi yawan mutanen wajen suke ganin dacewan a bawa papi auren Nu'aiymah, wasu kuma ke cewa a bawa habib Husain Saboda kara karfafa zumunci su...





Wanda ya kasance yaya ga Babba a familyn sannan mai fada a ji ne a Cikin dangin su, karon farko da tunda aka fara magana bai ce komai ba sai yanzu "kowa ya kwantar da hankalin sa, duk wanda Allah ya bawa 'yarmu tsakanin su biyun zamu ji a ranar auren, in da yanzu na saka ranar auren nan da sati daya, babu wasu bidi'a da za a yi, daga daurin aure, sai walima, da reception na iya maza, Allah ya tabbatar mana da alkhairi"





"Ameen" duk suka amsa, domin sun san cewa bazai taba yin abinda bai dace ba.



Aɓinci iri_iri aka tanada domin su, Nan kowa ya shiga deban abinda yake so yaci, wanda dama duk meeting din da za a yi sai anyi girki da yawa domin ahalin su ci, sosai wanna meeting din ke kara dankon zumunci a tsakanin su.





Sosai mahaifiyar habib Husain ta danne zuciyar ta, domin bata son kowa yaga rashin jin dadin ta ga abinda babban yayan nasu ya yanƙe, amma ita kam zata gaya wa Habib din ya cire rai da samun Nu'aiymah, idan Allah yayi tasa ce toh alhamdulillah! Idan kuma ya rasa ta toh sai yayi haku'ri, dama akwai wacce ya fara kulawa sama² sake ganin Nu'aiymah ne ya sa shi shashantar da maganar ita wacan yarinyar.






Al'ameen kuwa daya dawo gida, ya sanar da Raliya komai, sai taji jikin ta yayi sanyi, domin bata san waye zai zaba wa 'yar ta ta cikin su biyun a matsayin miji ba, amma ita kam har ranta tafi Son a bawa Nu'aym.





Gama managar su ke da wuya Nu'aiymah ta shigo tana turo bakin shagwa'ba, a hankali Al'ameen yace "kanwata gabadaya halin ki na shagwa'ba 'yar mu ta dauka"





Hararan wasa tayi masa kasa² tana murmushi alamun yayi shiru kada Nu'aiymah taji, dariya yayi yana Mai da kallon sa ga Nu'aiymah





Zama tayi a gefen su, bayan tayi sallama, kallon su tayi tace "tun dazu ina ta Kiran wayar papi baya dagawa, na kira kaka kuma tace wai baya gida" ta karasa Idanunta na kawo ruwan hawaye.





Cikin kulawa duk suka dawo gefe da gefen ta ya zamana tana tsakiyar su, lallaba ta suka yi da cewa kila network ne, anjima sai ta sake kira







Bayan an kwana biyu wanda bikin Nu'aiymah ya rage saura sati daya ba tare da ta sani ba.




Kaka ce ta kira Al'ameen domin jin me ake ciki, bai boye Mata komai ba ya sanar da ita, saboda bai ga amfanin boye mata ba tunda an zama d'aya.





Nu'aym da dawowar sa daga bankin kenan ya je biyan ragowar kudin gidan daya siya a jigawa, flat ne mai girma da tsari, domin furniture da sauran abubuwan bukata na gida ya zuzzuba su, Sannan duk ya rufe da manya manyan tampol saboda kura, dama mamaki yake so ya bawa su kaka rana saka yace su tafi, shine kuma Allah ya bayyana iyayen baby'n sa.






Amma yanzu da kishin Habib Husain ya rufe masa idanu ba Shiri ya biya ragowar kudin gidan wanda ya rage dubu dari ne, domin har wani gizo baby da habib Husain ke yi masa wai suna tare kullum, duk da a nan SOKOTO yake aiki, amma zuciya bata da kashi...




Yanzu a cikin satin nan yake son su koma jigawa kusa da baby'nsa hankalin sa zai fi kwanciya, ga kuma aiki ya baro baya zuwa, ya kamata ya koma hakan nan da wanna ya shige cikin gida...









Kaka da bata iya shiru da bakin ta ta kwashe komai da Al'ameen ya gaya mata ta gaya masa.





Ai fa nan Nu'aym ya haukace wa kaka tamk'ar sabon mahaukaci, har bata son kallon cikin idanun sa Saboda tashin hankali da bala'in da take hangowa a cikin su, har nadaman fara bashi labari tayi...



🍇🍇PAPI NE!🍓🍓







*WATTPAD*
@NoorEemaan













EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌





Page 77-78



.....Nu'aym kuwa K'anshi ya rufe a daki, yana jin wasu tashin hankali a jikinsa, abinda yake ji yafi zazzabi, tamk'ar aka saka aɗɗah ana daddatsa ko wani part na jikinsa, ya kasa yarda cewa baby'nsa za a yi wa aure, kuma an rasa waye mijin sai ranar auren za a sanar, Shi kam ya na cikin tsaka mai wuya...





Ta bangaren Nu'aiymah kuwa sosai ta damu da rashin kiran da papi da bai yi ma ta ba, amma da tayi magana su Al'ameen kan kwantar mata da hankali hadi da lallaɓa ta.







***************







*RANAR DAURIN AURE*

A yau ya kasance ranar da za a d'aura wa Nu'aymah aure, ko ina dangi ne a cike, duk da cewa basu gayya ci wasu mutane da yawa ba, amma hakan bai hana bikin cika ba, Saboda dangin su yawa garesu...





Da misalin karfe goma sha daya na safe, kamar a mafarki aka d'aura auren NU'AYM AHMAD TARE DA NU'AIYMAH AL'AMEEN BISA SADAKIN NAIRA DUBU DARI.



Take fusk'ar Al'ameen ta wad'atu da murmushi, dama yasan cewa babban yayan su zai yi adalci, amma rashin sanin abinda ke ransa ya sanya shi cikin damuwa da wasi'wasi.




Fidda tsadaddiyar wayar sa yayi ya dannawa Nu'aym kira wanna karon domin yi masa albishir. Domin sosai yake son Nu'aym tamkar dan cikin shi ko yace kani, domin sam baya masa kallon suruki.





Kwance yake gabadaya babu kwari a jikin sa, banda fuskar sa da mutum zai gane cewa yana cikin tarin damuwa babu abinda zai sa mutum yasan cewa akwai damuwa a tare dashi, domin bai rame ba, Saboda ginanan jikin sa, ga kewar baby'nsa daya yi masa yawa, ya ma kasa Kiran ta, abubuwa sun yi masa yawa yama rasa abun yi.




Ringing din wayar sa ya sanya shi bud'e idanunsa, har ta katse bai daga ba, kira na biyu ne ya sanya shi kallon wayar, lambar daya gani ya sanya shi bud'e idanunsa gabansa na faduwa...




Hannu na rawa ya daga kiran, cikin kamala yaji muryar Al'ameen yace "mijin Nu'aiymah Alkawarin Allah ya cika, a yau dai burin mallakar 'yarka Nu'aiymah ta cika, yanzu haka muna wajen daurin aure, an d'aura, Allah Ya tabbatar da alkhairi, ya baku zaman lafiya" yan fadin hakan ya katse Kiran, yana murmushi.




Tamk'ar gunki haka papi ya tsaya ya zubawa wayar ido, sosai yayi mamaki, take ya kara jin sautin amon muryar Al'ameen na sanar dashi ya zama mijin Nu'aiymah.
can kuma kamar an tsikare shi da allura ya kwala wani uban ihu cikin zallan farinciki...






Birgima ya shiga yi kan gadon sa, yana murna tamk'ar yaro dan shekara biyar, Kaka da ta shigo da gudu ta tsaya turus ganin abinda yake yi, ganin kaka ya sanya shi durowa daga gadon ya nufe ta, ganin haka ya sanya Kaka sarkin tsoro rugawa a waje da sauri abin Dariya, taku uku yayi ya rungumeta yace "kaka na mallaki baby, zamu rayu da baby nah kamar yadda muka fara, kaka ki yi farinciki Na zama mijin baby Nu'aiymah" ya karasa a nutse, Yayinda hawaye zallan farinciki suka zuba masa...



fadin farincikin kaka ba ta lokaci ne, sosai tayi farinciki da wanna auren, har da kukan ta. Nan dai suka shiga shirin tafiya jigawa, wani hada'dd'en farin shadda babban riga papi ya sanya, duk da ya taba sawa sau daya, amma tamk'ar sabo haka yake, hula, takalmi, agogo, duka to match ya saka, sosai yayi kyau ya kuma fito sak angon Nu'aymah sai baza kamshi yake.






Bayan ya fito da babur dinsa, suka rufe gidan hadi da kashe abubuwan wuta tunda ɓa nan kusa zasu dawo ba, Kaka da ta sha sabuwar atamfa da gyalen ta ta dane babur tana jawa papi kunne kan karya yi gudu da ita a babur da haka suka tafi, fusk'ar su fess Saboda farinciki, bare ma Nu'aym.







Ta bangaren Habib Husain kuwa kamar yadda yayi tunanin hankalin sa zai tashi sai yaga ba haka bane, duk da tabbas yaji ba dadi rasa K'yak'yyawar yarinya kamar Nu'aiymah, amma ikon Allah hankalin sa bai wani tashi ba, ya kuma sanar da mahaifiyar sa cewa aje a nema masa auren yarinyar nan daya dan shanshantar da maganar ta mai son waseelah, inda aka saka lokacin biki wata uku masu zuwa...



Wanna kenan.



***************************




Bangaren Mariya kuwa da kyar ta samu wani mai a kori_kura ya taimaka ya saka ta a bayan booth zuwa garinsu.



Sosai iyayen ta suka yi mata fada, kana sunyi fushi sosai da ita, ba kuma halin Kiran Al'ameen su roke shi tunda dai saki uku ne, haka ta cigaba da zama a gidansu tana jinyar kafar ta, gashi ta tarar gidan nasu ba kamar da ba, kullum sai sun ci tuwo gashi ita ta saba da abinci masu rai da motsi.
Ga raini wurin kannenta biyu mata da suka rage basu yi aure ba, komai dai ya lalace mata, kullum cikin nadama take, domin bata ga ribar muguntar da ta yi ba, tunda daga karshe ma itace ta kasance cikin mayuwancin hali...






*****



Sai karfe biyu na rana suka iso Jigawa, da taimakon kwantance da Al'ameen yayi musu suka isa har gidan, sosai suka tarar da gidan a cike babu masaka tsinke, Al'ameen da kanshi yayi musu iso, bayan sun gaisa sosai domin har runguman Papi Al'ameen yayi, domin tabbas yana kaunar Al'ameen kamar yadda yake kaunar 'yarsa Nu'aiymah.



A sitting room suka zauna, nan aka kawo wa su kaka abinci iri² yayinda wasu cikin dangi ke zuwa kawo gaisuwa wa kaka musamman da suka san cewa sune suka kula da Nu'aiymah har girman ta, kaka fadi take

" A kawo min Nu'aiymahtou na ganta, nayi kewar ta"
ai nan Al'ameen ke sanar da ita cewa

" kaka ai ba ta ma san cewa bikinta aka yi ba, domin babu Wanda ya sanar mata, dama jira muke idan kun zo sai a yi komai a tare" ƴa fadi haka, hadi da kiran Raliya...

"kanwata ku zo da Nu'aiymah, ga su kaka sun iso

Please Login or Register in order to submit comment