Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu sauki kudi kwaya uku.




"Allah ya sauwake maka, gaba daya ka koya mata shan zaki, kadai yi a hankali 'ya mace ce dai ehe..."



Nama balangun daya ajiye a tsakiyan su yasa ta yi shiru da sauran maganar ta kana ta hadiye miyau tace "A'a dan nan, yau dai kace dadi zamu ci, da alama aiki yayi kyau"




Dariya sa ya boye yace "Alhamdulillah kaka, yau kam na samu dubu biyu sak'amak'on wani aiki dana yiwa wani mutun ya bani kyauta" Nu'aym fada yana sanya wa Nu'aiymah nama yanka daya a bakinta.




"Masha Allah, Allah yayi masa Albarka, kaima Allah ya bud'a maka yanda kake k'ok'arin faranta mana, hakika baka baro komai daga cikin halaiyan mahaifin ka, kuma dana Ahmadu ba Allah ya jikan shi " kaka tace tana kai nama yanka har hudu bakinta.




"Kai papi kaga kaka tasa nama da yawa a baki"
Dariyar da yake k'ok'arin rikewa ce ta subuce masa, kullum kaka da salon datake yi wurin basu dariya.




Bakin kaka cike da nama tace "kaji min jar'irar 'ya daya siyo miki kayan yan gayun ki nayi magana ne? Shine yanzu kike mun sa ido, toh yanda kike takamar ubanki ne toh nima jika na ne, kin ga k'uwa dole naci iya son raina"



"Kaka! Kaka!!Kaka!!!" Nu'aym ya kira ta sau uku cikin gajiyawa da maganar ta.



"Meye toh, wato kada nayi magana ko, ita data yi magana meka ce?" Tace tana sake kai wani naman bakin ta.




"Ji yanda kikewa Baby magana kamar wata babba fa, yarinyar ce ki dinga yi mata a hankali banason bacin ranta"



"Iyeeh sannu uban zamanin, toh wallahi sai dai superglue zaka manna min a baki amma matuk'ar na gani sai na tanka yawwa" tace tana tura daurin ta gaban goshi.... Haka dai suka cigaba da hirar har suka cinye naman wanda yanka d'aya ya samu yaci, bai kuma damu ba domin Saboda farincikin su ya siya.....



*BAYAN SHEKARU HUDU*
Zuwa yanzu baby Nu'aiymah nada shekaru goma cif a duniya ba laifi ta dan yi wayo da girma kadan, wanda yayi daidai da gama karatun Nu'aym har an tura su serving (bautar kasa) inda gobe zai tafi sai dai basu yi maganar gaban Nu'aiymah ba, domin matuk'ar taji tofah bazasu yi bacci yau ba...




Daddare suna zaune kan tabarman Nu'aiymah na kwance a jikin sa, domin tana da sauri bacci idan tayi dadewar duniya to ta kai tara bata yi bacci ba. Nasiha hadi da add'uar kaka ke masa yana amsawa,...



ajiyar zuciya ya sauk'e yace "kaka ki lallaba min Baby please, nasan zata sha kuka idan taga bana nan gobe, dole zan yi fitar asuba domin bazan juri ganin tana kuka ba....





Murmushi kaka tayi tace " in sha Allah zan kula da ita karka ji komai, kuka kam dole ne zata yi shi, amma da an kwana biyu zata saba ne, ni dai fatana ka kula ka rike addinin ka kaji ko?"
"In sha Allah kaka zan kula nagode "



Haka suka cigaba da hira kewar juna har karfe goma sha d'aya na dare kana ya d'auki Nu'aiymah ya kaita dakin kaka a hank'ali domin tunda takai shekaru goma suka daina kwana tare, duk da cikin wayo yake samu ya gudo nasa dakin kasancewar har yanzu bata yarda, sai yayi kamar a dakin kaka zai kwana sai tayi nisa a bacci sai ya lallaba ya fito



Idan ta farka da asuba bata ganshi ba daya dawo daga sallar asuba tayi masa korafin bata gan shi ba, sai yayi mata wayon masallaci ya tafi...




Haka ya koma dakinsa ya kwanta tunani hadi da kewar su baby'nsa har ya fara kama shi, karshe dai ya hakur'a yana lumshe ido fatan sa bacci ya d'auke shi Saboda ya tashi da wuri....✍️





Kuyi haku'ri ya jama'a, wallahi duk yanda naso baku pages masu yawa akan bai samu ba sakamakon uzirori dasuka min yawa, in sha Allah a page 19-20 zan baku masu yawa both papi ne da kyautar koda.


Comment✔

Share✔

Vote✔

Edit❌

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by
NoorEemaan


*Wattpad*
NoorEemaan

ELEGANT ONLINE WRITER'S📚🖊




Page 19-20

(Note edited)

...........................k'iran sallar farko kan kunnensa, a nutse ya mike add'uar tashi daga bacci dauke a bakinsa, wanka hadi hadi alwala yayi, komai yana yi a hankali gudun kada ya tashi Nu'aiymah.




Bayan ya iddar da sallar'n, ya cire jallabiyan jikinsa ya shirya cikin wasu riga da wando na gwanjo(second hand) masu sauki kudi, duk da cewa kayan masu araha ne, amma sosai suka karbi jikin sa, wata jaka ta goya ya rataya a bayan sa kana ya yagi paper yayi rubutu ya ajiye kan yar kafitar sa sannan ya fito daga dakin...




Kamar ya shiga dakin kaka haka ya dinga shi, kasa hak'uri yayi ya leka, ya k'uwa hango kaka zaune tana lazimi da alama sallah ta idar, yayinda Nu'aiymah ke kwance tayi dai_dai akan gadon kaka tana bacci, kura mata ido yayi, zuciyar sa na ingiza shi kan ya shiga... Wani juyi da ta yi yasa shi barin kofar dakin cikin sauri ya fice daga gidan gaba daya.....





*Karfe tara na safe*
zaunen Nu'aiymah take kan kujera yar tsugunno tana wanke_wanke yayinda kaka ke k'ok'arin dumama musu ragowar taliyan jiya.
Cire hannunta tayi daga cikin ruwan wanke_wanken tace "kaka tun safe fa ban ga Papi ba ina yaje? Ko yaje gareji ne?"





Shiru kaka tayi tana tunanin amsar bata, can ta bud'i baki tace "eh, wani aiki zai yi shiyasa yayi sammako"




Shiru tayi tana jin ba dadi, turo baki tayi tace "shine papi bai bari na ganshi ba ya tafi ko".





Shiru kaka tayi ta cigaba da aikinta, a zuciyar ta fadi take "wanna bata ran naki zai dawo kuka, idan kika ji cewa yayi nesa da unguwar dama garin gaba daya"






Bayan ta gama wanke_wanken ta share gidan saf tamk'ar wata babbar budurwa, lokuta da dama kaka kan yaba mata, domin a kananun shekarun nan nata idan tayi aiki sai kayi zaton babba ce tayi....





kaka ta zuba musu dumamen a faranti d'aya kamar yadda suka saba ci a tare, tsakura take tana yatsine fusk'a kamar madaci take ci, a sanyaye ta dago kanta yayinda idanun ta suka kawo ruwan hawaye tace " kaka ni bazan ci ba, babu dadi abincin Saboda babu Papi nah".





Gaban kaka ne ya dan bada dam! Ita har tsoron rikicin da Nu'aiymah zata mata take, cikin son lallaba ta tace "haba Nu'aiymahtou daure kici abincin nan kinji, kinga idan uban naki ya dawo yaga baki ci ba, ai bazai je dadi ba ko"




Kara turo baki tayi tace "ni bazan ci ba, sai ya dawo, sai mu ci tare"



Kaka tayi saurin tarar numfashinta da cewa "idan abincin nan ya kai koda karfe sha daya ne zai iya lalacewa"




"Toh zamu ji na rana tare ko na dare, nidai bazan ci ba Papi ba"



Shiru kaka tayi aranta cewa take " ai kaji irinta, yaro gabadaya ya sabar wa yarinya komai suyi tare"

Haka kaka ta karasa cin nata abincin itama jikin a sanyaye, domin ta fara kewar Nu'aym d'in, ko ba komai da yanzu yana jan ta da tsokana...




Mik'ewa Nu'aiymah ta yi, kallonta kaka tayi tace "zaki je?".
" zan yiwa Papi gyaran daki" tana gama fadin haka ta shige dakin add'ua kaka take a ranta Allah yasa kada ta ga wata alama dazai nuna cewa tafiya yayi
domin ita kam bata shirya wa rikicin Nu'aiymah ba...





Tana shiga dakin ta lumshe ido, duk da karanci shekarun ta amma ta fuskanci Papi'nta na matuk'ar son kamshi, duk da ba turaren mai tsad'a yake amfani dashi ba, hakan yasa itama ke kaunar k'amshi domin Papi ya sabar mata sosai.





Dan yololuwar katifar ta fara dagawa, take takardan ta fado, sai dai sam bata lura ba, tsintsiyar laushi ta dauko ta fara shara, bayan ta gama tazo sauk'e katifar kasa, idanunta suka gano mata farar takarda yashe gefen katifa.
Durkusa tayi ta dauko, hada'dd'en rubutun Papi'nta ta gani, fara karantawa tayi kamar haka:


_zuwa ga K'yak'yyawar yata_
_ina fatan my baby ta tashi lafiya, kisani cewa ina matuk'ar kewar ki, tafiyar ta zame mun dole ce shiyasa nayi nesa daku, kiyiwa Papi'nki add'ua, sannan banda rashin ji, duk da nasan cewa K'yak'yyawar 'yata mai jin magana ce. Ki ci abincin da yawa kidawo yar lukuta na dawo na kasa daukar ki.(sai yasa alaman dariya) Sannan ki min alkawarin baza kiyi kuka ba, matuk'ar kika zubar da hawaye toh tabbas zan ji a jikina, ba kuma zan ji dadi ba, nasan dai Nu'aiymah'n papi na jin Maganar Papi'n ta ko, sai na dawo ki kula da kanki kinjiii papi loves you so Much_



Ai wani kara ta saki hadi da zubewa kan katifa ta shiga rusa k'uka, duk da dama hawaye ke ta zuba a idanunta tun lokacin data fara karanta takardan....


Ai da gudu kaka ta shigo dakin, sak'amak'on ihun kukan Nu'aiymah ta da ji, kwance ta ganta sai birgima take hadi da shure kafa tana kuka sosai tamk'ar ana yankanta da wuka ne

yayinda ta rike takardan gam a hannunta, take kaka ta fahimci komai, ta shiga aikin lallashi... sai dai duk lallashin da kaka keyi ta tamk'ar cewa take cigaba da kuka Nu'aiymah, domin taki shiru.

Da kaka ta gaji da lallashin sai ta koma waje ta cigaba da aikinta, yayinda itama taji hawaye ya zubo mata, ba karya da bahaushe yace *sabo tirken wawa* dole ne suyi kewar Nu'aym, domin yafi kaunar farincikin su fiye da shi, wasu lokutan idan yasan cewa abinci bazai ishe su ba, sai yayi karyan ya koshi, domin su ci... Abubuwa da dama ya sadaukar musu domin suyi farinciki.



Haka duk su ka kasancewa jiki a sanyaye, yayinda zazafan zazzabi ya rufe Nu'aiymah, gashi taki yin shiru sai kuka take ta na k'iran "papi nah ka dawo" ai ranar kaka taga tashin hankali, abu goma da ashirin ya hade mata, itama sai tasa kuka. Domin sosai Nu'aiymah ta rikici mata, sai data fita waje ta siyo mata paracetamol ta sha kana ta samu bacci ya d'auke ta.....



Bangaren Nu'aym k'uwa tun daya je bai zauna ba Saboda abubuwa, amma duk abinda yake baby'n sa na makale a ransa, yasan tayi kuka sosai, gashi babu waya balle yaji muryar ta. Duk abinda yake k'arfin hali kawai yake nuna wa. Sai wajen 8 na dare ya samu ya kwanta kewar gida na nuk'urk'usan shi.... Yan dakin sai surutun su suke, daga masu danna waya, sai masu hira, shi k'uwa tunanin 'yarsa da kewar ta ke cinsa, bai taba tunanin zai yi kewar ta har hak'a ba, domin dukkanin wani motsin da yayi da toh da tunanin ta ne....


Sai wajen karfe biyun dare ya lumshe idanun sa, burinsa yayi bacci, domin yaji yan dakin na hirar karfe hudu ake zuwa tashin mutanen domin su fita wajen horo, wanda zasu dauki tsahon kwanaki ana musu training nan cikin camp din, kafin ayi posting din kowannensu inda zai fara aikin daya kawo shi....




*WASHEGARI*
Gaba d'ayan matasan corper daga matan har mazan sanye suke da farar T-shirt hadi da farin wando, sai canvass farare, cikin kwarewa ake basu horo, sun dauki tsahon lokaci ana basu horo kana aka sallamesu. Sosai Nu'aym yayi kyau cikin shigar, yayinda kirar sa ta karfaffan maza ya sake bayyana sakamakon rigar ta dame shi, babu mai cewa Nu'aym dan shekara ashirin da biyar ne, Saboda kirar sa.

Bayan duk an basu karin kumallo, ya kurawa lafiyayyen abincin ido, yakasa koda kaiwa bakin sa ne, tunaninsa ko su kaka sun ji sun koshi? Duk da cewa duk wani kudin sa sai daya siya musu yan kayan abinci da zai iya kai musu kwana ashirin. Haka yayi ta tunani da kewar su daya adaddabi zuciyar sa....




Manage please idan sun kawo nepa zan fara typing, zaku iya ganin posting ako wani lokaci. Nagode muku sosai da addu'oi'nku gareni💖


#share
#comment
#vote

Editing is not allowed❌❌❌

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

Written by
NoorNoor Eemaan

Wattpad
@NoorEemaan


Page 21-22

(Not edited)

........................ karshe ɗai barin abincin yayi ba tare da yaci ba. ruwa kadai ya sha ya mike ya koma dakin su. Haka ya takure a gadon cikin kewar Nu'aiymah'n sa.





*** *** ***



Bangaren su Nu'aiymah k'uwa, ta dawo shiru _shiru, kullum tana dakin papi a kwance tana aikin kuka, tun kaka na lallashen har ta zuba mata ido.


Kamar yau ma kwance take a dakin Nu'aym hawaye na zuba daga idanunta, kewar sa mai yawa ke damunta, komai ta saba tare suke, amma yau kwana bakwai kenan ba ta ga Papi'nta ba.



Muryar kaka taji ta kwala mata kira, shiru bata amsa ba. A karo na biyu kaka ta kara k'iran
"Nu'aiymahtou!" Nan ma shiru.
"Ke ko bacci kike ne? Nu'aiymahtou!"



Turo baki tayi kana ta fito a hank'ali ta tsaya daidai bakin kofar dakin tace "kaka gani"

Kallonta kaka tayi har da zata mata fada sai tace "ga abincin ki nan, kizo kici"

Ai sai tasa kukan zallan sakalci tace "ni bana ci"





Wani haushi ne ya kama kaka, cikin fada ta fara cewa "bazai yu ba, bazai yu ki daina cin abinci ba, salon ubanki ya dawo ya sani a gaba da fada kin rame, kwana nawa yau ina lallaba ki, amma kamar tunzara ki nake..." Sai kuma tayi shiru jin sautin kukan ta na tashi sosai, tuno abinda Nu'aym yace mata karshe yasa ta sausauta murya tace "kiyi haku'ri Nu'aiymahtou ta papi'nta, ki daure ki ci abincin nan kin ji ko? Saboda idan ya dawo yaga kin rame bazai ji dadi ba"




Share hawaye tayi kana tace "toh yaushe zai dawo?"

Dan Jim kaka tayi kana tace "nan da yan kwanaki" ita kanta kakar fada k'awai tayi domin Nu'aym bai sanar da ita ranar dazai dawo ba.

Kara kallon Nu'aiymah tayi tace "yawwa yar gidan papi, zauna kici ko" da haka dai ta lallaba Nu'aiymah taci fara cin abinci...




*JIGAWA*
Bangaren Raliya k'uwa har ila yau jikinta na nan yadda yake, babu ciga'ba. Amma sosai take samun kulawa daga yayyenta, iyayenta, hadi da mijin ta Al'ameen kullum tsaf da ita kamar mai lafiya.




Gaba daya yanzu d'uk sun fawwalawa Allah komai, domin sunyi iya k'ok'arin su amma babu wani sauki sai wajen Allah.




Bangaren Al'ameen k'uwa tsaye yake a wani hada'dden daki, yana bin dakin da kallo yayinda wani abu mai daci ya tsaya masa a wuya. Kallo uban kayan wasan yara dake cike a daki iri daban _daban yake, sosai idanun sa suka ciko da kwalla sakamakon tuno wata rayuwa da suka yi a baya shi da Raliyar sa a wanna dakin.




Tsaye take da katon cikinta dazai kai watanin 7, duk da girman cikin nata hakan bai hana ta kawata fusk'ar ta da make up mai kyau da tsari ba. Daga bayanta taji an rungume ta, murmushi tasaki kana tace "Yaya"
"Na'am farincikina kanwata, ya jikin? Ya kuma baby na?"

Dan bata rai tayi kana tace "baby na lafiya, sai rashin ji".
Dariyar dabai shirya yi ba ya fashe da shi kana tace " rashin ji fa kika ce"?

"Eh yaya, baby'n baya zama waje daya, sai juyi yake tun dazu" ta karasa cikin dariyar itama.

Murmushi yasaki, hannun sa ya kai yana shafa cikinta kana yace "sorry, ai kin kusan hutuwa in sha Allah, saura kadan fatana Allah ya sauk'e ki lafiya"




"Hmm Ameen yaya, amma wani iri nake ji, cikin tsoro yake bani, jinake k'amar bazan rayu da abinda zan haifa ba"




"Shhh! Kada kice haka, in sha zaki haihu lafiya, sannan mu raini baby'n mu tare kinji ko...."?
A daidai lokacin Al'ameen ya dawo daga duniyar tunanin daya fada, hakan yayi daidai da zubar wasu hawaye masu zafi a idanunsa..




*BAYAN WATA DAYA*
A gobe Nu'aym ya gama shirya tafiya gida, domin kewar baby Nu'aiymah na barazana ga nutsuwar sa Duk wani abu dazai hada ya gama hadawa, kudin da aka biyasu na yan bautar kasa wato *alawee* ya shiga kasuwar garin ya yi musu tsaraba, har da wayoyi biyu ya siya masu saukin kudi, yar techno ce karama camon, sai vivo daya siya wa kaka hadi da layika. Allah _Allah yake gobe tayi har mamakin zumudin sa yake...


Washegari da safe ya bar garin ya nufi tasha, babu jimawa motar su ta tashi... Bayan wasu awanin suka isa sokoto, aka sauk'e shi, a titi ya tsaya ya tari keke napep saboda kayan dake hannun sa nada yawa.




Babu jimawa suka iso, daidai kofar gidan yace mai napep ya tsaya, wani sanyi ke ratsa shi sak'amak'on ganin ji a kofar gidansu, biyan mai napep hakkin sa yayi kana ya kwashi kayan ya nufi cikin gidan, murmushi fall fusk'ar sa.......


Manage🙏




Gobe ma zanyi k'ok'arin yi muku sabon update matuk'ar naga comments dinku.



#Share
SVote
#Comment

Editing is not allowed❌❌❌


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓

*written by*
*Noor Eemaan*
07082281566


*wattpad*
@NoorEemaan














*EDITING IS NOT ALLOWED*❌







Page 23-24


.......................... Sallamar sace ta katse wa kaka draman da take yi da Nu'aiymah. Shiru duk suka yi, sak'amak'on murya da suka ji kamar ta Nu'aym.



Wani sallama ya sake yi, wanda yayi daidai da bayyanar shi tsakar gidan. Wani ihun murna Nu'aiymah ta saki ta nufe shi a guje, tun kafin ta karaso Nu'aym ya saki kayan hannunsa duka...



Wani uban tsalle tayi sai gata kwance a k'irjinsa, hakan yasa suka tafi luuuuuuuuu suka zube gabadaya a kasa sakamakon taka daya daga cikin Ledojin mai d'auke da ayaba.



Sam bai damu ba, bai kuma ji ciwon buguwar da yayi a keyar sa ba, sai ma wani zallan farinciki dake shimfud'e kan K'yak'yyawar fusk'ar sa.


Kukan murna da shagwa'ba Nu'aiymah ta sakar masa tana cewa "Papi I miss you, kada ka sake tafiya ka barni kajiiiiiiiiiiiiiiii"



Wani irin zafi da yanayi ne ya shiga ratsa shi, sam bai kaunar kukan ta ko da wasa ne, hannunsa yasa ya shiga shafa yalwataccen gashinta hadi bubbuga bayanta yace "stop crying(daina kuka) my beautiful baby, am sorry bazan sake ba, Papi ne ko?" Sai ta jinjina kai... yana k'ok'arin sake magana kaka tace "ikon sai rabbul sammawati, yanzu ka markada ayaba har uku da takalmin kafarka amma ko a jikin ka, a wanna tsadar rayuwar?"



Runtse idanun sa yayi k'amar dai yadda ya zame masa dabi'a, kana ya mike tare da Nu'aiymah a jikin sa, Saboda farincikin ganinta yama manta cewa a kasa suke kwance tun dazu.



Tana manne a jikinsa har kan tabarma, taki sakin sa, domin gani take tana barin shi zai sake tafiya ya barta.



Sai da kaka ta gama kwashe kayan tsaraban kana ta dawo ta zauna kusa dashi, murmushi d'auke kan fusk'ar sa yace
"my kakus mun sameku lafiya? ina wuni"
Itama kaka murmushi d'auke kan fusk'ar ta tace "lafiya lau alhamdulillah dan albarka sannu da zuwa".


Ajiyar zuciya ya sauk'e, hakika babu inda ya kai gida dadi, komai lalacewar sa kuwa, tun da ya tafi sai yau ya samu nutsuwar zuciya...



Murmushi yake saki akai_akai, domin Nu'aiymah sai taba takalmin sa take irin dai na yan bauta kasa, sai ta cire hular sa ta sanya, shi da kaka suka yi murmushi.


Wani juya ido tayi tace irin dai yanda yara keyi tace " Papi nayi kyau?".



Tsad'add'en murmushin sa ya sakar mata kana yace "akodayaushe 'yata K'yak'yyawa ce. Kyan da kike yi bazai mitsaltu ba"



Duk da bata fahimce duka hausar ba, amma tayi murmushin jin dadi hadi da cewa "Papi ka bar min hular please, har da wanna takalmin ta sojoji".


Dariyar dabai shirya yi ba ya saki kana yace " baby waya gaya miki takalmin sojoji ne? Wanna takalmin na yan bautar kasa ne (corper) sannan ina gamawa ke zan bawa duka har rigar da wandon kina so?".



Saurin gyad'a kanta tayi, murmushi d'auke a fuskar ta.



"Dan nan ina kasamu kudi haka kayi wanna uban tsarabar?"



Bai bata amsa ba, sai wayoyin daya fito dasu ya ajiye kan cinyar ta, kara rudewa kaka tayi tace "Nu'aymu ina kasamu kudi haka?"

"Relax kaka zan yi miki bayani"

"Toh maza yi min bayani hankalina ya kwanta"..



" kin san duk wani dan bautar kasa (corper) ana biyan su kudi duk watan duniya har iya tsahon shekara dayan da zamuyi" ya kai karshe yana kallonta..



Kukan farincikin ta saka tace "Alhamdulillah! Allah abin godiya, hakika boko tayi rana, yau gamu da wayoyi har biyu, Allah yayi maka albarka, ya jikan mahaifanka, ya raya ka tare da 'yarka"



Idanunsa a lumshe ya amsa da "Ameen" kana ya sake cewa "kaka wanna itace taki" ya fada yana mike mata waya kirar vivo. Amsa tayi cikin farinciki tana shi masa Albarka....



Tsarabar kaka ta shiga fito dasu d'aya bayan d'aya daga cikin ledojin... kayan itatuwa(fruits) iri daban _daban ne, sai man shafawa na kaka d'aya, na Nu'aiymah d'aya, sai toothpaste (man goge baki) kwaya hudu, hadi da sabulu sinki biyu, sai takalmi makaranta, jaka, hadi da sababbin exercise book guda goma, hadi da fararen safa kala uku.



Albarka kaka ta shiga shi masa cikin farinciki, Nu'aiymah sai tsallan murna take, musamman ganin tayi sabuwar jaka, ita da a jakar buhu take zuwa makaranta, amma yau tasamu jakar goya.

Kaka ce ta kalleta da murmushi a fuskarsa tace "ka ga ja'ira godiya zaki yi ba tsalle ba"

Dariya Nu'aiymah tayi ta fada jikinsa hadi da cewa "thank you so much Papi nah, I love you"

"Love you too my beautiful daughter (ina sonki nima K'yak'yyawar 'yata)"
Kana ya kalli kaka yace "k'aka ya fama da maleji? Abinci na isar ku k'uwa?"



"Hmmmm dan nan, sai godiyar Allah, akwai ragowa kadan, domin 'yar ka dai bata son ji abinci da kyar nake lallaba ta take tsakura...." Nan ta shiga bawa Nu'aym labarin irin rikici da rigimar da Nu'aiymah take mata...



Idanunsa kafe kan fusk'ar Nu'aiymah dake ta faman danne_danne a wayarsa kirar canon.
Jin kaka yake k'awai yana murmushi.



Bayan wasu mintuna ya mike hadi da cewa "kaka bari na siyo mana yan kayan abinci".

" Toh dan Albarka, sannu Allah ya saka maka da Alkhairi "




"Papi zan bi ka"
Tsayawa yayi hadi da cewa "toh dauko hijab dinki"
Da gudu ta shige dakin kaka ta dauko kana ta mike Masa, amsa yayi ya sanya mata hadi da kama hannunta suka fita...



Kantin dake kusa da gida suka nufa, ya siya musu shinkafa yar hausa kwano biyar, taliya leda goma sha biyar haka zalika macaroni, sai man kuli kwalba uku, garin tuwo kwano d'aya da rabi, Maggi Leda uku...
Sannan a gefen kantin ana siyar da kayan miya, nan ya siyi na dari takwas, albasan dari hadi da salak da tumarin na dari biyu, hadi da kifi guda d'aya babba.
Wasu yara biyu almajirai suka taya shi dauko kayan har cikin gida... Dari biyar ya bawa yaran su raba, suka yi godiya cike da murna.



Sosai kaka ta shiga kuka da shi masa Albarka, domin Nu'aym yayi namijin kokari kullum burinsa ya faranta musu kallon sa tayi cikin kaunan jikanta tace "Nu'aymu ka kashe kudi da yawa, kana da kudin motar dazaka koma k'uwa?"




Murmushi yayi kana yace "ai kudin mota na ware shi daban, kuyi hakuri da wanna kayan abincin, ku lalllaba har wata ya kare, zan sake zuwa sai a siyi wasu kayan abincin"




Albarka k'uwa Nu'aym ya sha ta ba babu iyaka, maimaitawa take tunda Ahmad danta (mahaifin Nu'aym) ke raye rabunsu da ganin cimma na yan gayu sai yau... Nu'aiymah da papi'nta sai dariya suke mata...





babu bata lokaci kaka ta hada miyar stew (dage _dage) sai tashin kamshi yake, sai ta dora musu shinkafa, bayan ta sauke, ta yanka musu salak tumatir da albasa. bayan duk ta gama hada komai ta zuba musu a faranti d'aya k'amar yadda suka saba kana ta sa kifi uku, kowa daya_daya.




Sosai suke ci abincin dukkansu, domin bayan tafiyar Nu'aym babu wanda ya sake jin dadi cin abinci irin na yau ba. Haka suka cinye zuciyoyin su cike da nishadi...




*WASHEGARI*
Yau ta kasance juma'a, bayan sun gama karin kumallo, suna zaune shi da kaka suna hira, tana tambayar sa yaushe zai koma ya sanar da ita ranar lahadi. Daidai lokacin Nu'aiymah ta fito sanye da kayan makarantar ta. Safa ta mika Nu'aym wai ya sa mata

Kaka da bata gani tayi shiru tace "sabon salo da, da baya nan, wake saka miki?"

" Papi kana jin kaka ko?"

"Rabu da kaka, bata taba saka safa ba, safar ma fara, shiyasa take kishin ki" ya fada hadi da kamo lallausan farar kafarta ya fara zura mata safar, yana gimtse dariyar sa jin kaka nata maganganun.



"Yarinya dai macece, kuma gidan wani za'a kaita, idan bata saba abubuwa da kanta ba, kai zaka bita gidan auren kayi mata?"




Take fusk'ar ta ta sanja sakamakon karshe managar

Please Login or Register in order to submit comment