Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ɓa, tayi nadaman zuwan ta giɗan party dinan, gashi ta bata ran Papin ta.


Zata bud'i baki domin ba shi haku'ri idanunta suka kai kan kafarsa da hannun daya kumbura sukutum. Wani ihu ta saki tana yarfa hannu kamar a jikinta taji ciwon kana cikin karaji tace Papi! Hannun ka ya kumbura sosai, wayyo Papi nah sannu! Kana jin ciwo sosai? " ta fada tana rike dayan hannunsa mai lafiya.

"Ki bar mu dak'i" yace ido a lumshe.

"Am sorry Papi bazan sake ba, kazo muje asibiti kaji?"

"I said get out!"

kuka ta saka kana tace " Ka...ka...ta...ce kazo, ita tace na kira ka" ta faɗa murya na rawa


Duk da har yanzu yana ganin laifin kaka amma bazai iya bujirawa k'iran ta ba, cikin dauriya ya mike yana cije labb'ansa da suka yi jaaa Saboda yanda yake datse su da teeth d'insa, cikin tausayawa Nu'aiymah ke kokarin rike shi ya mata wani kallo daya sa ta tsaya, cikn dubara ya fara takawa domin barin dakin yayinda Nu'aiymah ke biye da shi a baya tana sharar hawaye....





Kuyi hkr please, wallahi bana jin dadin jikina, kuyi hkr kadan nayi, ba nan nayi niyyar tsayawa ba, gobe matuk'ar naji kwarin jik'ina zan sake yi muku update🙏




#Share
#Vote
#Comment



🍇🍇PAPI NE!🍓🍓


*WRITTEN BY*
Noor eemaan



*WATTPAD*
@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌


*pls&pls sisters kuyi following dina a Wattpad @NoorEemaan*



(Kila kuga typing error😎)

33-34

........Salati kaka ta sanya ganin yanda Nu'aiym ke jan kafafun sa, ga kumburin daya yi. "Nu'aymu hatsari kayi? yaushe haka ta faru? Ko aljanu ne suka biyo dare suke son kassara min jikana?" Kaka ta fada cikin iyakar gaskiyar ta, sannan cikin damuwa.



Bai kula ta ba, sai zama d'aya yi yana cije lebe, domin zuwa yanzu azaba iya azaba ta ishe shi.




" ''yar nan ya akayi haka ta faru? Tunda ubanki dan ganin dama ne, yaki kula ni"



Nu'aiymah dake share hawaye tace "ji...ji...ya da...ya...dau...koni...da...ga... wa...jen...pa...party...mu...ka...fadi...daga...kan...lifan" ta faɗa cikin rawar murƴa tana fashe da kuka domin yadda hannu da kafar Papi tayi dole mutum gaji tausayin sa.




"Innalillahi wa innah ilaihi raju'un" kaka tace tana tafa hannu

"Amma ''yar nan baki kyauta min ba, idan shi zuciyar dutse da shi yaki fada, ai ke kya gaya min a kira mai gyara tun a jiyan"


"Sannu! Sannu!!" Kaka tace tana dan latsa inda ya kumbura, runtse idanun sa yayi, duk da azabar dayake ji bai hana ta ba, Nu'aiymah ce ma tace "wayyo! Kaka ke daina taba masa akwai zafiiiii fa"



"Toh masu uba, ai ni bana kaunar sa ƙenan dole ki ce haka, karshen kaunar daya kamata ki nuna shine ki sanar da ni a kira mai gyara tun a jiyan, sai yanzu zaki yi min wani iyayi, toh bari kiji gojewar kashi yayi, dole aje gun mai gyara ya d'awo da kashin daya goce saiti, sannu Nu'aiymu bawan Allah, hada mana karin kumallo mu karya sai aje wajen malam Danliti, ya gyara masa "




Wasu hawayen Nu'aiymah ta share, ta fara hadawa kaka, domin tasan bata da haku'ri kan yunwar Cikin ta, sai Nu'aym da zallan black ta siyaya masa tunda baya son madara a shayi.


A sanyaye ta ce "Papi gashi"


Idanunsa a lumshe ya mika hannu ya karba.

Shiru falon ya dauka sai sautin taunar kaka dake tashi, sai data sake kai wasu chips dazai kai 10 bakinta kana ta kalli Nu'aymah tace "A'a Nu'aiymahtou ya naga bakya ci?"



A raunane tace "ba komi na koshi" domin ita damuwarta Papi ya daina fushi da ita, ko yunwar bata ji.

Kaka zata sake Magana ya bud'e idanunsa fess kan Nu'aiymah, fuska a dan daure yace "zuba, and eat up now"



Bata musu ba ta hada black tea, domin itama bata fiye son madara ba, sai chips data debi kadan tana ci tana hawaye tana kallon papi, amma sam bai kalleta ba.


Kaka data kai kofin tangaran bakin ta mai dauka da tea daya sha breavages, kofin manne a bakin ta tace "kwa ji da karyar Engilihi(English) dinku"



Babu wanda ya kula ta, har suka gama breakfast din, duk da kaka tafi kowa cika cikinta dam ƙuwa.




Bayan kaka ta saki gyatsa tace "Alhamdulillah! Nu'aymu ya kamata aje gidan malam Danliti a duba ka, domin kara tsami yake faa"


"Toh" ya amsa mata



Kaka ta kara cewa "anya zaka iya tafiya? Kodai a kira mai adaidaita sahu, domin bana jin zaka iya tuka babur lifan din nan ƙo?"


Jinjina kai yayi, domin ba ma zai ma iya tukin ba.


Nu'aiymah tayi saurin cewa "kaka na iya mashin, zan iya kai shi tunda ba nisa" (kasancewar Nu'aiym na koya mata)


"Kinga rufa ni ki saya ni, kar ayi biyu"


Amma ina Nu'aiymah tace "Allah kaka zan iya, ki tambayi Papi ma" tana fadin haka ta koma dakinsa ta d'auko key, kana ta shiga dakin ta ta sanya dogon wando baki, Saboda zaman mashin, sai rolling data yi da dankwalin k'anta kasancewar yana da girma...


Dan babur din ta haye ta kunna hadi da nufar waje, kaka ta kalli Nu'aym tace "daure ka tashi, kaga ita har ta fice, ooh wanna yarinya da zuciya take ko tsoro bata ji, ni ina zan iya tuka babur, ko hawa ma bazan iya ba, domin jina zan dinga ƴi kamar a kwalta nake shawagi".



Danne dariyar sa yayi, ya lallaba ya bar gidan, tana zaune kan babur din, kasa dauke idanun sa yayi daga gareta domin wani bala'in kyau tayi kan mashin din, har yau yana mamaƙin saurin girma ɗa ciƙa da baby'nsa tayi. Da suka hada ido kuwa ya sakar mata harara, ta tabe baki zata yi kuka, ya dauk'e kai kamar bai gani ba...



Kan Babur din ya hau, da kyar ƴana cije leben sa, da suka yi mugun jaaa kamar ya shafa jan baki.... ai fa take suka gefe luuuuu, zasu fadi, Nu'aiymah har da dan ihun ta, tama saki babur din tana jiran ta jisu a kasa...



Cikin wani k'arfi dabai san yana da ragowar sa ba, ya kama babur din ya dawo dashi ɗaiɗai, ƴana cije leben azaba, kana ya kalli Nu'aiymah yace "lazy type, dama bazaki iya ba, kika fito da mashin din?"


Shagwa'be fusk'a ta yi tace "Papi na iya faa, daka hau ne abin ya fi k'arfina"


tabe baƙi yayi yace " Wai ba munyi fada ba? Karki ma kula ni, mara jin magana kawai"


"Kukan zallan shagwa'ba ta sakar masa tace " Allah Papi na daina, please ka daina fushi da ni"


"Ohh really? Dama kina gudun bacin raina? My friend mu tafi"


Wani hawayen sakalcin ta share, amma taji dadi, tunda yayi magana mai dan tsayi da ita, da alama ya fara saukowa...



Ba musu ta fara driving din a hankali, duk inda suka gifta sai an kallesu, wasu har suna gulma a tsakanin su wai mace ta hau mashin, wasu kuma burge su sukayi, dama haka rayuwa take...



Isar su kofar gidan malam Danliti yasa ta faka mashin din, kallon ta yayi yace ta fara sauka, kana shima ya sauka cikin taka_tsantsan.



"Shiga kiyi sallama da shi" inji Nu'aym


Ba musu ta nufi cikin gidan, ta tarar da mata uku wanda da alama matan malam Danlitin ne.


Kasa tayi cikin girmamawa tace "ina kwanan ku" bayan taƴi sallama.



Hada baki sukayi wurin fadin "lafiya kalau"

"Am... malam yana nan kuwa?" Inji Nu'aiymah.


"Eh yana nan, lafiya dai 'yar nan ko?" Babbar cikin matan ta tambaya.




"Eh lafiya, mahaifina ne yayi gocewar kashi, shine muka zo ya duba shi"







"Ai yo, Allah ya kiyaye gaba" kana ta nufi dakin malam din, babu jimawa ta fito tace "gashi nan zuwa" ga kujera zauna mana" matar ta fada tana nuna mata kujera yar tsugunno.



Murmushi daya bayyanar da wushirya ta tayi kana tace "a'a nagode"


Daidai lokacin malam Danliti ya fito rike da wata babban sallaya a hannunsa, matan suka hada baki wurin fadin "barka da fitowa malam" ya amsa. Itama Nu'aiymah har kasa ta gaishe shi, ya amsa a sake, kana ya shimfud'a sallayan a soro yace Nu'aymah ta fada wa Papi ya shigo.



Fita tayi waje tace "Papi wai yace ka shigo" bai ce komai ba, ya shigo tsoron yana lafiya da kyar domin ji yake tamkar an dora masa bulu inci takwas a kafar, ga matsananci azaba da zugi......




Nasan yayi kadan, kuyi hkr pls, wallahi na gaji😓


Share fisabilillah
Comment
Vote

🍇🍇PAPI NE!🍓🍓




*Written by*
Noor eemaan





*Wattpad*
@NoorEemaan










(Assalama alaykum, kamar yadda na fada a baya cewa wattpad dina yana ɗa matsala, domin nayi kuskure wurin saka username din. Domin akwai masu cewa suna son following dina na basu Wattpad name dina, alhamdulillah yanzu dai waccan tsahon acct din an goge shi, duk da mutanen sunyi following dina.
Ina rokon ku kada ku gajiya Ku sake following and voting dina dama wadanda basu taba yi ba, saboda Allah da Manzon sa.
Ga sunan wattpad din👉 @NoorEemaan Nagode sosai da kauna da kuke nunawa novels dina💖 )




EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌


Page 35-36

Gaisawa suka yi da malam Danlitin, kana ya lallaba ya zauna yana cije lebe, shi kan shi malam Danliti sai daya jinjina kai ganin yanda hannu da kafar Nu'aiym din suka kumbura.




Mikewa malam yayi ya koma cikin gidan ya dauko masu abubuwan dazai bukata na gyaran kana ya dawo, kallon Nu'aiymah yayi

"yanmmata dawo daga gefe domin yanzu zan yi masa gyaran"


"Toh" Nu'aiymah tace a sanyaye domin wani tausayin Papi'n ne ya cika zuciyar ta.


A hankali malam Danliti ya fara murzawa hannu kamar dai yana masa tausa, yayinda yake shafa masa wani man zafi, wani mugun zafi da baki ba zai iya fasalta tashi ba, ya shiga ratsa kwanyar Nu'aym babu abinda yake sai faman cije lebe idanunsa sun kada sunyi jajur, Nu'aiymah dake kallon sa sai faman share hawaye take, domin tasan ba k'aramin zafi yake ji ba



Ba zato suka ji "kwat" Allah ya bawa malam Danliti ikon mayar da kashin hannun ƙan saiti, Maimakon Nu'aym ya saki ihun azaba, sai Nu'aiymah ce ta saki ihu tace " auchhhhh! wayyo Allah Papi! Malam ka bari, aƙwai zafi"
Nu'aym kuwa azaba iya azaba ya sha ta, sai dai yayi matuk'ar jarumta.

"Sannu! sannu!! yaro, sannu da jarumta saura na kafan"


Sosai malam Danliti ya sha wuyar dawo kashin kafar daidai, domin gwara na hannun, haka ma Nu'aym wuyar daya sha ba kadan bane, domin har kwalla sun taru a idanunsa, amma bai bari sun zubo ba, yayinda kukan Nu'aiymah ya cika kunnen su, malam sai dariya yake mata, ganin ba ita aka yiwa ba, amma sai rusar kuka take....




"Baby stop!" Nu'aym ya fada cikin wahalaliyyar murya domin sam bana son jin kukan ta ko kadan.



Shiru tayi tana sakin shesheka, amma hawaye basu daina zuba a idanun ta ba, nan malam Danliti ya bashi wasu mai yace a dinga shafa masa. Godiya sosai Nu'aym ya masa, malam Danliti sai yaba jarumtar Nu'aym yake.

"Baby je ki daga kujerar lifan akwai wasu kudi ƙi ɗauƙo" kana ya kalli malam yace
"Malam nawa zan bayar"

"A'a dan samari, duk abinda Allah ya hore ka bayar, bana fada"
Jinjina ƙai ƙawai Nu'aym ƴaƴi
Bayan Nu'aiymah ta dawo hannunta dauke da kudin ta mikawa Nu'aym, ya yi alamar ta bawa malam din.




Mika masa tayi ta hannu biyu, kana Nu'aym ya mika mata hannunsa ta kama ya mike yana dan yamutsa fuska, goɗiƴa malam ya dinga zuba wa, domin kudin da yawa bai laifi, sai murna yake yau shi da iƴalan sa zasu sha jar miya lafiyayye da shinkafa.




Kamar yadda Nu'aiymah ta tuko Babur din a zuwa, haka a yanzu da zasu koma giɗa Nu'aiymah'n ce ke tuka su....
Bayan sun iso kofar gida, Nu'aym na kokarin sauka, ɗomin taji saukin shigar da ɓaɓur din ciki, Nu'aiymah tace "Papi ka zauna zan iya shiga da kai cikin gida".


Bai musa ba, amma a ransa ƴana yaba mata kan ƙoƙarin da ta yi, duk da shi ya ƙoya mata babur bai yi tunanin zata iƴa tuki har haka ba, kasancewar kofar a bud'e take yasa ta shiga gidan kai tsaye... Kaka dake zaune tana tsumayin dawowar su da bisu da kallo har Nu'aiymah ta faka mashin di'n.




Sannu! Sannu!! Allah sarki dan Nu'aymu na, kaji jiki kam, eh kaji jiki, gocewar kashi akwai azaba, sannu Allah ya kiyaye gaba danna, zo ka zauna, ka sha iskar Allah ta ala ko ka rage zugi" kaka tace tana nuna masa kan wata babban sallaya da take zaune a kai.



Zama yayi cikin dabara yana amsawa kaka, "zo ki zauna kema kika tsaya mana aka kamar soja"


Nu'aiymah bata amsawa kaka ba, sai zama d'ata yi gefen Nu'aym tana dora k'anta a kafadar sa...



Tabe baki kaka tayi kana tace "gulma, sai me dan baki zauna kusa dani ba? Ai zai koma aikin ne ya bar ni da ke, naga jikin wa zaki raba ke mai son jikin bala'i"



Murmushi da iyakar sa lebe Nu'aym yayi, a ransa yana mamakin ko me abin wanna doguwar maganar, oh kaka kenan Ya aiyana a ransa.


*JIGAWA*
"Baba mun yanke shawarar zuwa India da Raliya domin a binciki lafiyar ta, tunda dai suna da kwararun ma'aikata a can kila a dace tunda har yanzu babu sauki abu da da gaba yake yi, mun ma yi magana da Al'ameen kan batun tafiyar, yace da kanshi zai kaita" yaya Auwal ya karasa yana kallon baba


Numfashi baba ya sauke kana yace "toh Auwal, Allah yasa a dace, Allah ya kuma yi muku albarka ɗuƙan ku"



"Ameen" duk suka amsa idanun su kafe kan Raliya dake zaune, lokaci zuwa lokaci sai ta fashe da dariya mai sautin gaske, gashi kulllum sai ta burkita gidan gaba d'aya, tayi ta daga abubuwa tana watsar wa kamar mai neman wani abu.

Wanna kenan.





*SOKOTO*
Kaka na zaune tana cin fried rice da Nu'aiymah ta girka, domin baby'n Papi ba dai iya girki kala kala ba, musamman ma na zamani...







Yayinda Nu'aiymah dake durkushe gaban Papi tana shafa masa man zafi, idanun sa a lumshe su, har ta gama shafa masa kana ta mike ta mayar da man zafin ta dawo gefen sa ta zauna, hannu sa ta kamo tana ta wasa da azurfofin hannun sa.



A hankali ƴa fara ware idanun sa ya sauke su kan ta, hakan yayi daidai da dago sleepy'n eyes dinta, dake a lumshe a kodayaushe kamar mai jin bacci. Shagwa'be fusk'a tayi, domin har yanzu bai sakar mata fusk'a ba.



Dauke kansa yayi ya basar kamar bai ganta ba, cikin sakalci da shagwa'ba tace "Allah Papi bazan sake rawa cikin mutane ba kaji kayi haku'ri please Papi nah, kaka ki bawa Papi haku'ri kinji"


Kaka dake yagar naman kaza dake kan shinkafa tace "haba kai kuwa, sai kace ba muslimi ba da aka sansu da zuciyar yafiya hadi da haƙuri ba, yau kwana nawa yarinyar nan na rokan ka, amma ka ki hakura, kai wallahi ina jin da a zamanin firauna kazo daka yi bakin hali, haba dan Allah!"




Dariya ma kaka ta bashi, yana shirin yin magana Nu'aiymah tace "kai kaka firauna fa kika ce, ni dai ki daina danganta Papi na da firauna gaskiya" ta karasa tana turo baki gaba.



"Laila a ilallahu, ni zaki yiwa haka, wato ni zaki gwale ƙo, kin ma samu ina shigar miki, sai ta ja kwafa kana tace " zamu gauraya ne, bake mai uba ba" kaka ta karasa ta cigaba da cin abincin ta, bata kara kula su ba.

Dariya ce ta jiyo Nu'aym amma ya daure, kana a fili yace "ai dama ba a shiga tsakanin * 'ya da uba* "

Kallon Nu'aiymah yayi yace "baby'n Papi na yafe miki kinjiiiiiiii, amma idan kika sake rawa a wajen biki zan yi fushi sosai dake kuma bazan hakura ba.


Rungume shi tayi da k'arfi tana murna " auchhhh! Baby" Nu'aym yace


saurin tashi Nu'aiyam tayi tana fadin "sorry Papi" ita ta ma manta da ciwon sa, saɓoɗa farinciki.


Murmushi ya saki kana ya ja kunenta a hankali, nan suka dinki a binsu ta shiga zuba masa surutu tana bashi labari abubuwan daya faru baya nan, dama bata samu fuskar gaya masa ba, amma a ka'ida tun a ranar daya zo hutun karshen mako har wajen sha biyu dare suna hira, shakuwa da tsananin son junan su ya zarta tunanin mai karatu....




Haku'rin dai sister's na barku kuna ta jira😩👏 kuyi haƙuri da wanna, ina busy ne.




Share fisabilillah
Comment
Vote


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓







Written by
Noor eemaan








Wattpad
@NoorEemaan















EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌








(Pls do vote and follow me at wattpad @NoorEemaan)




(Kila kuga typing error🤒)




37-38


.................. Haka suƙa cigaɓa da rayuwar su ciƙin farinciƙi da annushuwa, Nu'aiymah ta dage da jinyar Papi'nta bama ta bari kaka tayi. Nan fa kaka zata shiga fada wai Nu'aiymah ta hanata samun lada, da dai sauran su, kaka rikici kenan abinda bakai fada bama yi take...








*** *** *** ***





Nu'aiymah ce sanye da uniform farare kal hadi da ratsin blue, Yayinda hijab ɗin ta ya kasance medium(maɗaiɗaici) shima fari, idanunta sanye farin glass daya yi matuk'ar amsar ta, kafarta sanye da canvass farare. Kasancewar Nu'aym ya sanja mata makaranta zuwa na private (ta kudi).












Jakar goyo ce a bayanta baka, hannun ta rike da wani bakin Leda data yiwa Papi tsaraban aya, biscuit, alawa, egg roll da spring rolls sai zobo da har yanzu da sauran sanyin sa, domin mutum zai iya hango hakan ta ledar.








Sosai ake rana, daga yanda take tafiya a hankali tamkar mai tausayin kasa zaka dauka bata jin zafin ranan, sai dai ba haka bane tsananin gajiya ne, domin yau ko break ba a bari sun fita ba, Saboda karatu daya ɗau zafi...









Zumudi take, burinta taje giɗa tayi tozali da Papi'nta, tayi kewar sa tun safe, dama da kyar taje makarantar, taki tafiya sai faman kuka taƙe, wai bazata tafi ta bar shi ba, sai ɗata ga ɓacin ransa sannan ta tafi
domin har yanzu bai koma aiki ba, Saboda jikin sa bai gama warware ba, ya kuma sanar, har an turo mutane biyar ɗa suka zo duba jikin sa daga company'n nasu....












Ta sha ƙwanar layin gida ƙenan taji ana ta danna horn a bayanta, tafiyar ta ta cigaba da yi batare da ta juyo ba, sallama taji wata had'add'iyar murya tayi ta basar bata juyo ba, amma ta amsa a ranta, saɓoɗa muhimmancin ta.








Ta danyi nisa taga ansha gabanta da wata motar hummer jeep, kaucewa tayi ta cigaba da tafiya, ganin da gaske bazata tsaya ba ya sanya mamanllaƙin motar fitowa daga ciƙin motar sa.....







Hada'dden saurayi ne mai kyau hadi da kuruciya ya sha wasu had'add'un English wears, cikin sauri ya tari gabanta yace "haba mai kyau, yanayin ki ya nuna ke mai tarbiyya ce, sannan ya nuna cewa daga gidan mutunci kika fito, an kuma san duk wani mai tarbiyya da girmamawa dan Adam, tunda Allah subhana wata ala ya karrama dan Adam, ko ba komai ai kya masa mun sallama, duk da ba mutuncin mace bane a tare ta a titi, am sorry for that, amma ki bani mintuna biyar dan Allah, I know kin gaji daga school kike please mai kyau" ya karasa cikin wani salo.







"Afuwan, ina sauri ne please" Nu'aiymah ta amsa tana kokarin wucewa.




Kara shan gabanta yayi yace "dan Allah ki saurare ni, bazan bata miki lokaci ba, ni kaina ina saurin ne, amma ganin ki ya sa bazan iya barin ki ba, ba tare ɗa nayi miƙi magana ba"





Dan yamutsa fuska baby'n Papi tayi ita ala dole yanmmata(😹😜) tace "alright ina jinka"





"Nagode mai kyau da wanna damar, da farko dai sunana Habib Husain ni dan nan garin sokoto ne, ina aiki a company'n MTN, sannan ina zaune tare da iyayena ɗuka ɗai anan sokoton, ko zan iya sanin sunan ki?"




Habib ya fada yana jifan Nu'aiymah da wani kallo mai kashe sassan jiki.



Dan turo baki tayi domin ba kadan take jin ranar ba, a taikace tace " SUNANA NU'AIYMAHTOU NU'AYM AHMAD "




"Wow! Nice name, ina son sunan ki, but it seems kin gaji da yawa bani number'n ki ma yi waya"





Dan waro ido tayi kana cikin yarinta tace "Papi na baya bari na rike waya, dana kaka ma nake yin game"






Shagala yayi da kallonta, sosai yarintar ta ta tafi da hankalin sa, murmushi ya saki kana ya sanya hannunsa a aljihun wandonsa ya ciro wayar iPhone 11promax yace "ga wanna ki fara maleji(manage) kafin na sanja miki sabo, domin kin girmi wanna wayar mai kyau nah"







"Sake waro lumsasun idanunta tayi tace " a'a Papi zai yi fushi da ni bana so, ƴace ƙaɗa na ƙarbi aɓin ƙowa"









wow! irin macen da naƙe fata da muradi kenan wato mai tarbiƴa ya aiyana a ransa amma a fili "Sai kice sirikin sa ne ya baki" Husain ya fada yana son ta karbi wayar.





"A'a nagode sai anjima" inji Nu'aiymah.



"To tsaya, bani number'n kaka zan kira ki, karki ce a'a please na roke ki da Allah"







Dan Jim tayi Kana ta amsa ta sanya masa, saboda kada ya sake tsayar da ita yasa tayi gaba abinta, bata ma tsaya sauraran abinda yake cewa ba.....






Zaune ta tarar da kaka da Nu'aym suna hira jefi_jefi ɗuƙ ɗa yawancin maganar kaka ce take yin sa, domin Nu'aym hankalin sa naga baby'n sa ganin har karfe biyu bata dawo ba....






Sallamar tace ta katse masa tunani, wani sanyin dadi ya ratsa zuciyar sa, a fili sai ya balla mata hararan wasa, tabe baki tayi irin na shagwa'ba kamar zata saki kuka tace "Papi nayi laifi ne?"




"Eh mana tun d'azu ina jiran dawowar ki, amma har after 2 baki dawo ba?"



"Am sorry Papi kajiiiiiiiii"

"Toh na hakura 'yar albarka"


"Ke dai gadon bakin hali kika yi wurin ubanki, ace ki dawo daga makaranta ba zaki gaishe ni ba, ni ba mutum bace, wato nayi kankanta baki ganni ba ko, ƙo kuma ban isa ki gaishe ni ba, uhm yar ganin ɗama?"





Dafe kai Nu'aym yayi, ko yaushe baby'n ta ɗawo da zata ce bata gaisheta ba? kallon Nu'aiymah yayi yace "baby please talk to kaka, if not she won't allow us to receive fresh air" Nu'aiym ya fada da turanci gudun magana amma bai tsira ba, suka ji tace "toh meye na kiran sunan kaka a karyar Singlishi(English) idan ba tsoro ba ka fada da yaren hausa mana, gabadaya kun aro karya turancin ku, toh bari kaji baka birge ni ba ehe!, ina alfahari da yarena dama al'ada ta, amma ku yaran zamani sai kayar turanci wai ƙu boko ko...?"








"Kaka sorry kinji, ina wuni na sameku lafiya" inji Nu'aiymah ta na kumshe dariyar ta.





"Lafiya nake ras kuwa, yar ganin dama sai yanzu zaki gaishe ni?"




Nu'aiymah bata kula ta ɓa, ta kalli Nu'aym tace "Papi I bought kayan dadi for you daga school ɗinmu"




Kaka jin an kira *kayan dadi* domin shine kadai abinda ta fahimta a turancin, babu abinda take sai zube ido take taga me a ciki leɗar.........




"Really baby? Thanks 'yar gidan papi'nta" inji Nu'aym.




Murmushi Nu'aiymah tayi ta fara fito da duka kayan ta zube su gaban sa, dariya ce ta taho wa Nu'aym "ooh baby rigima ina zan kai duka tarkacen nan?"




Cikin shagwa'ba ta fara dire kafafu tace "Allah papi ka cinye duka kai na siyowa faaaaaa"



Rike kafafun da take ta buga wa a kasa ƴayi, kana yace "it's alright baby, amma ki min haku'ri ba duka zan ci ba, like this ones..." Ya nuna aya, biscuit, da alawan.

"Su ki cinye na yafe, tunɗa dama kece gwanar zaki"




"Toh Papi nah" ta fada cikin murna domin ba komai yake yarda yaci ba, musamman idan ya bai san waye ya girka ko ya hada abin ba, egg roll din ta sanya masa a baki ya gutsira, lumshe ido yayi yana girgiza kai alamun yayi dadi domin sanya ta farinciki....




Dariyar farinciki Nu'aiymah ta kyalkyalle dashi tace "da dadi ko Papi?".

" sosai ma 'yar Papi, Amma idan da ke kika yi, nasan sai na cinye leɓena Saboda tsabar dadi, I know my daughter is a good cook"




Murmushin jin dadi ta saki ganin an ƴaɓe ta.





"Uhmmmmm duniya" Kaka tace tana tafa hannu, daman ta jima tana kallon su kamar taga TV, bazata iya yin shiru ba hakan yasa tace "wato yarinyar nan ban taɓa sanin cewa bakya sona ba sai yau, ki siyawa wa ubanki abin tabawa amma ni da nake siya miki abu in naje unguwa ki kasa siyo min koda yar aya nan ce, kin manta ranan naira na gugan naira har dubu d'aya na siya miki wani dan kunne na yanmmata Saboda nasan zai miki ƙƴau, Saboda kin mai da ni

Please Login or Register in order to submit comment