Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jin dukkanin hirar dake tashi a dakin, wanda na yan'uwan sa ne da na Raliya.



Suna cikin hirar su yaji wayar sa ta fara ringing, amma bai da alamar dauka, har wayar ta sinke, wani kiran ya sake shigowa.... Hakan ya janyo hankalin yan dakin suka yi shiru, cikin sauri kanin sa mai Suna Abba ya daga kiran hadi da sakawa a hands free ya ajiye kan gadon da yake kwance, wajan kunnensa domin yasan ba bacci yake ba.



Take muryar 'yar sandan nan ya karade ila'irin dakin... "Hello ƴallabai sunana larai Usman jami'ar yan sanda, ina kira ne daga sokoto, ga wata mata ta bani lambar ka, wacce aka kama ta 'yar da jariri sabon haihuwa...."



A zabure Al'ameen ya miki, jin abinda 'yar sandan nan ta fada, fisge Karin ruwan da ake masa yayi, hannun, jiki, da bakinsa na rawa yace "wa....wa...ce...ce?"


Ɗaga dayan bangaren yar sanda nan wani mugun kallo ta watsawa wa matar tace "ya sunan ki?"


Shiru matar tayi tana zaro ido, ran yar sandan nan ya baci, wani mugun mahangurɓa ta bata a fuska, Saboda tsananin azaba, ga jikin ta yayi tsami dama, hakan yasa ta saki wata rikitaciyyar kara....



"Nace ya sunan ki? Ko bakya jini ne?" ɗomin sosai larai taji ta tsani matar.

A zabure Al'ameen dama sauran yan dakin suka mike, domin muryar wacce tayi ihun yayi musu kama dana wacce suka sani, cikin rawar baki Al'ameen yace "ki...ki... barta har mu zu, yanzu zamu taho, ki turomin address din wajen" kit Al'ameen ya koma ya zauna, gabadaya k'wak'walwar sa ta toshe, yama rasa tunanin yi, a hankali ya koma dabas ya zauna kan gadon


Kallon Al'ameen mahaifiyar sa tayi tace "Aminu! Ya da zama kuma? Ka mike mu tafi, karfafa jikin ka, kaji dan nan"


Gabadaya suka Mike, yaya Auwal, ya usman, su malam baba da mama, da dai sauran yan'uwan, da manager'n Al'ameen na company'n sa, daya zo duba jikin shi, har da Raliya malam baba yace a biya gida a taho da ita Saboda ba mamaki yan sandan su bukaci ganin ta, hakan kuwa aka yi, gabadaya kan su ya daure, so suke suje su ga mamallakiyar muryar da ta yi ihu, domin muryar yayi musu kama da na wacce suka sani, motocin ɓiƴar suka shiga, duka kirar sienna.



Karfe Shida na yamma suka isa wajen, ganin yamma tayi, yasa mahaifiyar Al'ameen ta kawo shawaran a kama hotel su kwana, idan ya so gobe sai su je police station din, hakan kuwa akayi, amma Al'ameen bai so ba, domin a k'age yake...

*********************


WASHEGARI da misalin karfe tara na safe, direct address di'n da larai ta tura musu suka dinga bi, hadi da tambaya har suka iso police station din, babu bata lokaci duk suka fito daga cikin motacin suka nufi cikin station din.



Suna shiga suka yi kicibis da Larai ta fito daga office din DPO fuskar nan a murtuke da alama aiki ya dau zafi, kai yayi chaji.

Hada idanu tayi dasu Al'ameen da shigowar su kenan, haka kawai jikinta ya bata Al'ameen shine mutumin da suka yi waya dashi jiya.



Domin ta kara tabbatar wa sai tayi dialling number'n sa, take kuwa wayar ta ta dauki kara, cikin sauri Al'ameen ya nufe ta yace "ni...ni...ne wanda muka yi waya, ina matar take? Wacece ita? Ina jaririn?" Ya jero tambayar ɗuƙ a rikice.



"Calmdown ranka ya dade, zaka ganta, ku zauna ina zuwa, zan fito da ita yanzu" daga kansa Al'ameen ƴayi tamkar jariri ya koma da baya da baya ya zauna dabas kan benchi, haka sauran duk suka zauna, kasancewar akwai abun zama wadatacce....


Sun kusan mintuna goma a zaune, larai ta tasa keyar matar nan ta nufi wajen su Al'ameen, babu abinda take sai faman jan kafa, kasancewar kafar tata tayi tsami sosai, domin ba k'aramin buga ta ke sha wajen larai ba...



Da kallo duk suka bita, kasancewa kanta na kasa hakan yasa basu ga fuskar ta ba, wani dundu larai ta maka mata a baya tace " dago kanki" a kausashe

A hankali ta dago kumburarran fusk'ar ta ta sauke su fess kan na Alameen, a kidimie Al'ameen ya nufe ta yace "mariyaaaaaaaaaaa! Kice? miya kawo ki SOKOTO yaushe kika zo?"




kallon larai yayi cikin fushi yace "me tayi muku? Me matata ta muku? Miyasa kuka mata wanna dukan kawo mutuwar?"


Wani murmushi takaice Larai tayi tace "matar ka fa kace? dama wanna ita ce matarka? Amma tir baka yi sa'ar mata ba, wanna munafukar mai fuska biyun da kake gani ita ce aka kama ta yar da jariri sabon haihuwa"....



Gabadaya dakin ya dauki Salati, kowa ya shiga tofah albarka cin bakinsa, ga Mariya tayi kasa ta kanta, cikin rashin gaskiya ta ma kasa yarda ta hada ido da kowa, Al'ameen kuwa Sam baya son tunaninsa ya tabbata, amma yanzu da larai tayi maganar nan ya kara hargitsa tunanin sa, tamkar gunki haka ya tsaya, can wani jiri ya debe shi, luuuuuuuu ya tafi zai fadi, Abba kaninsa yayi saurin taro shi ya zaunar dashi yana bashi baki, Yayinda gabadaya sauran yan wajen kansu ya kulle, domin abinda basu taba zata ko tunani suka gani yanzu a zahiri, dama labari aka basu, tabbas da sun Karyata...




Cikin fitar hayyaci Al'ameen ya kalle ta yace " ma...ri...ri...ya wani jaririn ki ka yar? nawa jaririn d'aya bata ne?, innalillahi wa innah ilaihi raju'un" ya karasa cikin rawar baki, gabadaya yama rasa abin cewa, domin bai taba tunanin hakan ba, koda a mafarki ne.




Cikin wani fushi maman Al'ameen tace "ke Mariya! ba tambayar ki ake ba, bazaki yi magana ba?"



Sosai gaban Mariya ya sake bugawa domin wanna shine karon farko da surukar ta yi mata magana cikin fada da fushi, gabadaya kamar ta nitse a awajen, domin ji tayi ta muzan ta, da kallo da shiga bin kowa, yayinda su ma suke binta da kallon zallan mamaki, wasu har tsana take hangowa a idanun su, Raliya kuwa bata ma san abinda ake yi ba, sai faman abubuwan ta take irin na masu ciwon hauka, amma babu wanda ya kalleta, domin sun san lalurar ta....



Wani duka larai ta nada mata a baya, sak'amak'on shirun data yi, ihu ta tsala tace "e....eh...shi...ne .....jaririn ka ne, nina Sato shi" ta fada a rikice ɗomin ba k'aramin tsoron larai take ba, har bata son ta taba jikinta da suna duka...



" mahammadur rasulilillah! Mariya kece?" gabadayan su suka fada cikin madaukakiƴar mamaki, sosai hayaniya ke tashi a wajen, kowa fadin albarkacin bakinsa yake, hadi da aibata Mariya.




Ai fa nan jikin Al'ameen ya shiga rawa, ya shiga kokawa da numfashin sa, sosai Al'ameen yake kallon Mariya cikin zallan mamaki, dama makashin sa na kusa dashi bai sani ba? Matar sa, uwar gidan sa, abin son so itace dama ta sace masa jariri? Kenan cikin Raliya na farko tana da masaniya kan batan cikin da haukacewar ta? ya ilahi! K'wak'walwar sa ta gagara daukar wanna abin mai matuk'ar ban mamaki da al'ajabi.






Sai da larai tace "silent please, hayaniyar tayi yawa, dan Allah kuyi Shiru"

Kallon Al'ameen tayi tace "yallabai ina mahaifiyar jaririn, akwai tambayoyin da nake son mata".



Maman Al'ameen ce tayi saurin cewa " Yallabiya kin ganta nan, ai bata da lafiya"



Kallon Raliya, larai tayi, a kallo daya ta hango alamun cutar hauka a tare da ita.


Sai a lokacin bakin Al'ameen ya bud'e yace wa larai "ina dana yake? Dan Allah ku bani shi ko zan samu saukin abinda yake damuna"

gabadaya yan wajen sun tausaya masa, ace babban mutum na kuka, cikin girmamawa larai tace "yallabai, wani saurayi ne mai suna Nu'aym ne ya tsinci jaririn a lokacin da Mariyar take k'ok'arin yar da jaririn, yanzu haka yaron yana tare da su, ya kuma yi alkawarin zai cigaba da kula da yaron har iyayen sa sun bayyana, har....."


Cikin sauri Al'ameen ya katse ta da cewa "please ki kaini wajen su, kai gidan su yaron, domin in ga gudan jinin na dan Allah" sosai tausayin sa ya kama kowa.


"Ai yallabai bamu da address din yaron, sai dai a kira shi yazo" ta fada tana latsa tsadaddiyar wayar ta, dama ta karbi number'n Nu'aym wajen wani dan sandan.



*****

Zaune suke gabadaya a falo, Hajiya kaka na basu nishadi kamar kullum, yayinda Nu'aiymah ke bawa ADEEL abincin sa, sai faman tsotsan feeder yake, an shirya shi cikin kaya masu k'yau, yaron yayi bul_bul gwanin burgewa da sha'awa saboda sosai yake da shan madara, ga kuma kulawa yana samu, kullum kamanin sa da Nu'aiymah Kara bayyana yake, tun abin na basu mamaki har suka basar, ga wani mugu_mugun son yaron dake ratsa jijiya da bargon jikin Nu'aiymah a kullum.



Tsagaitawa Nu'aiymah tayi da dariyar sak'amak'on kiran wayar Papi da aka yi, mika masa tayi domin wayar na kusa da ita, amsa papi yayi ya latsa Kore hadi da karawa a kunnen sa, take yaji muryar larai na sanar dashi cewa " barkan ka dai malam nu'aym an samu iyayen jaririn wajen ka fa, domin ita Mariya ce ta bani number'n mijin ta, bayan taji wuya, ashe dan mijin ta ne, ba lokacin bayani, kazo station please yanzu, duk suna jira" kit ta kashe wayar...




Sosai gaban Papi ya fadi, haka kawai yake ji tamk'ar wani al'amari mai girma zai faru a yau.


"Dan nan lafiya?" Kaka ta fada tana kallon sa.


"Kaka an samu iyayen jaririn nan..." Nan dai yayi musu bayani kamar yadda larai tayi.



"Yo ai wanna abin farincikin ne, maza ku shirya muje, domin wallahi sai na kara zagin mai fuskar tubani can(in ji darma😂)"

a sanyaye ya mike, ya nufi dakin sa, dama kayan shan iska ne a jikinsu duka, amma duk sunyi wanka.

hakan yasa ko wannen su ya nufi daki domin ya Sanja kayan.


Nu'aym ya sanja kayan zuwa dagon wandon jeans da yellow'n riga, sai takalmi sau ciki baki, sosai yayi wani lafiyayyen k'yau.

Nu'aiymah kuwa abaya mai yalwar stone blue color ta saka, wanda ya sa hasken ta kara fitowa tayi das da ita, itama sau ciki mai k'yau black irin na mata ta saka, tayi rolling da mayafi.



Hajiya kaka kuwa atamfar ta mai k'yau ta saka super holland da hijab pitch color ya dan dara guiwar ta kadan, ADEEL Nu'aiymah ta rungume a kafadar ta, sai ta rufe shi da towel din babies saboda iska da hasken rana...



Kaka ce ta kalli Nu'aiymah tace " ke 'yar nan maza dauko yar jakar nan ki saka madaran Adeel da karamin flask da feeder'n sa, domin kada ya ji yunwa, kin san yaron nan acici ne, atoh kada ya cinye mu da kukan sa"


Dariya Nu'aiymah tayi, ta shiga daki ta dauko komai kamar yadda kaka tace, karban jakar kaka tayi ta rataya, Nu'aym na jin su amma babu halin dariya domin sosai yake jin faduwar gaba...




Rufe gidan Nu'aym yayi suka fito, a yanda suka jero sai kayi tunanin mata da miji ne, nu'aym da nu'aiymah da dansu, kaka kuma mahaifiyar papi, haka da yawa mutanen da suke kallon su, musamman wadanda basu san su ba suka dauka.



Keke napep suka tara suka shiga, bayan Nu'aym ya fadi inda zai sauke su, gabadaya wata muguwar faduwar gaba ke riskan shi, amma bai bari su kaka sun sani ba....



Bayan sun isa bakin gate din station din, Nu'aym ya biya mai keke kudinsa, kana suka nufi cikin asibitin...


Nu'aym ne ya fara shiga cikin wajen, followed ba kaka, sai Nu'aiymah da ta kasance ta karshe...

Da Kallo su Al'ameen suka bi su kaka, kowa da lugudin da zuciyar sa ke yi, yayinda babu inda idanun Nu'aiymah ya sauka sai kan Raliya...



Kura mata ido Raliya tayi, Yayinda ta mike a zabure ta nufi Nu'aiymah...mutuwar tsaye Nu'aiymah tayi sakamakon hango photocopy ta sak ta nufo ta, haka zalika su kaka da su Al'ameen haka suka yi, kowa ya kasa motsi, Raliya na daf da isowa wajen Nu'aiymah dake kallon ta bata ko kiftawa, ta zube kasa kana ta saki wata gigitaciyar kara ta suma....


A kuma daidai lokacin ne, cikin tsananin rudewa da ganin komai zai lalace mata Mariya tayi subutar wata kalma daya Kara hargitsa kwanyar su kamar haka.....





Muje zuwa habibtie's😍🔥
Sai lahadi, idan mai kowa da komai ya ara mana rai.




Noor😍


🍇🍇PAPI NE!🍓🍓



*WATTPAD*
@NoorEemaan






EDITING IS NOT ALLOWED❌❌❌



Page 67-68


(NOT EDITED)

......... "Na shiga uku na! dama boka na kan tudu yace duk ranar da Raliya ta ga 'yarta zata warke, da a dalilin hakan ne yasa na hauka ta ta, na kuma raba su tun ranar da ta haife ta, bana tamtama wanna yar ta ce, wayyo Allah meyasa komai zai faru yanzu" mariya ta fada cikin fitar hayyaci, rikicewa, gigicewa, hadi da tsantsar tashin hankali.



Ai nan wuri yayi tsit tamkar ruwa ya cinye su, kowa ya zura ido ga mariya cikin tsantsar al'ajabi...


Muhammadur rasulillah! fadin tashin mutanen wurin bata lokaci ne, babu wanda ya fi shiga tashin hankali sama da PAPI, sai Nu'aiymah da k'wak'walwarta ya gaza daukar maganganun da mariya ke yi, ga gabanta dake mahaukacin bugu data rasa dalilin hakan, sosai ta rike jaririn domin har wani juyi Idanunta keyi, fahimtar hakan yasa Nu'aym saurin riketa zuwa jikinsa ta baya, wasu tagwayen ajiyar zuciya ta sauke tace "papi nah dan Allah mu tafi, mu bar nan wajen, zuciyata zata bare k'irjin na ta fito, ka taba kaji yanda take bugawa papi, please" ta karasa tana sakin kuka.




Fadin tashin hankali Nu'aym bata lokaci ne, ya ma kasa yi mata magana. Yayinda Al'ameen ya tsurawa Nu'aiymah ido baya ko kiftawa, tabbas wanna K'yak'yyawar matashiyar tayi matuk'ar yin kama da Raliyan'sa... wani abu mai girman gaske da bazai iya furtawa ba, yake ji a kanta ....



Mahaifiyar sa ce katse masa tunani da cewa "kai Aminullahi baka ga halin da matar ka take ciki ba, nemo ruwa, maza nemo ruwa Aminu a yayyafa mata, suma tayi" ta fada tana zuwa gaban Raliya ta shiga girgiza ta, cikin rikice wa Al'ameen ya fita wajen ya samu shigon masu siyar da pure water, Leda daya ya siya, ya mika wa mai shagon one thousand, mai shago fadi yake yallabai ga sanjin ka...
Amma ina Al'ameen ko juyowa bai yi ba, a 360 ya koma cikin police station...




Ledar ya yaga ya fasa ruwa daya ya sheka mata, shiru babu motsi, kowa yayi cirko² hankali a tashe, wani ledan ya fasa ya sake sheka mata, Shiru kake ji, a karo na uku ya fasa wata Leda ya sheka mata, wata doguwar ajiyar zuciya ta sauke kana ta mike a hankali cikin nutsuwa, ji tayi kanta na sara mata, dafe kan tayi na yan mintuna kana ta mike a hankali ta kalli Al'ameen tace " wayyo yaya kaina ciwo" sai kuma ta shafa cikinta ganin shi a shafe tace

"yaya ina ciki na yake?"



Ai wani kuka Al'ameen ya fasa ya rungumeta ganin ta dawo hayyacin ta, sosai ya rungumeta, duk da mayuwancin halin da yake ciki hakan bai hana shi jin dadin ganin matar sa cikin haƴƴacin ta ba...



Kabbara hadi da hamdala mutanen suka Shiga fadi cikin mamaki da farinciki, bayan shekaru goma sha shida, finally Raliya ta dawo cikin hank'ali da nutsuwar ta...





Mariya kuwa kara ta fasa ganin Al'ameen rungume da Raliya, tamkar ruwan zafi aka watsa mata, haka taji sanda Al'ameen ya bata Raliya tight hug, ga kuma alama ya nuna ta samu lafiya, birgima ta shiga yi a kasa tana fadin "na shiga uku nah ni Mariya wanna tashin hankalin har ina?"





Raba jikinsu Raliya tayi cikin kunya, kara kallon shi tayi tace "yaya meya faru? Ina cikina yake ka yi Shiru"



Zai yi magana kenan manager'n sa na wajen yace "'ah ah, Nu'aym dama kaine? sam ban lura ba sai yanzu"



Cikin sanyin jiki shima Nu'aym yace "manager nima ban ganka ba wallahi sai yanzu"



Mamaki ne ya kama Al'ameen kallon manager'n yayi yace "dama ka san shi ne?"


"Kwarai yallabai, shine director din company'n ka na Jigawa" manager'n ya fada ba tare da mamaki ba, domin dama ba duka ma'aikatan sa ya sani ba...

Jinjina kai kawai Al'ameen Yayi, shi kanshi Nu'aym yayi mamakin ganin Al'ameen shine mai company'n da yake wa aiki, ikon Allah kuma basu taba haduwa ba...
dama ba wai Al'ameen yana yawan zuwa bane, domin akwai wasu harkoki da yake tabawa, komai ya damkawa manager'n sa, sai da Nu'aym ya fara aiki shima manager ya samu saukin aikin, domin abubuwa na masa yawa...




Ganin ihun Mariya ya yi yawa ne, ya sanya larai yi mata duka mai k'yau da Sandar hannunta kana ta nutsu...


Nu'aiymah dake cikin wani yanayi tace "papi mutafi, kaka kiyi masa magana mu tafi gida zuciyata na bugawa...



Kaka ajiyar zuciya ta ja, babu bakin magana, tun dazu ta kasa magana sak'amak'on wasu abubuwan da take hangowa kan su Al'ameen ɗin.



Nu'aym kuwa abinda yake muradi kenan su tafi gida, amma ji yayi kafar sa tayi masa nauyi, sam bai shirya zuwan wanna ranar ba, yaya baby'n sa zata ji? Wani hali zata shiga idan ta san gaskiya.




Jin muryar Nu'aiymah yasa Raliya mikewa ta nufi wajen ta, kamo fusk'ar Nu'aiymah tayi tace " yaya wacece wanna mai kama dani, meyasa nake jin wani abu mai girma a tare da wanna ran?"

Nu'aiymah kuwa runtse idanun tayi, sak'amak'on wani mugun sanyi daya shiga ratsa ta tun daga yatsar kafar ta, har izuwa tsakiyar brain dinta...


Kasa magana Al'ameen Yayi, Kuka tasa kamar Karaman yarinya tace "kayi Shiru, kowa ya min Shiru, nace ina cikina babu amsa, please wani ya min magana? Ko na rasa cikin ne? Abinda na haifa ya rasu ne ko?" Ta karasa tana jijjiga hannun Al'ameen din...




Sosai tausayin Raliya ya kama kaka, cikin tabbaci ɗa son kawo karshen komai tace "baiwar Allah ga 'yarki nan, shakka babu Nu'aiymahtou 'yarki ce, Nu'aiymahtou kiyi hakuri maganar boye² ya kare, yau dole siririn boye ya bayyana kansa"
.



"Noooooo kakaaaaaaaaaaaa" Nu'aym ya fada cikin karaji yana dukan Garu da k'arfin sa....






"Bar ni dannan! Ka barni, har zuwa yaushe zamu cigaba da boye mata, kana ganin hakan daidai ne?" Itama kaka ta fada hawaye na zuba mata, domin irin ranar da take tsoro kenan..






"Bamu gane ba, baaaba kiyi mana bayani, kin samu a duhu, dan Allah" mahaifiyar Al'ameen ta fada, cikin rikice wa...



" Zan sanar daku, amma tabbas zan so jikana ya fara fadin yadda ya tsince ta, domin hausawa sunce waka a bakin mai ita tafi dadi, sauran bayani kuma zanyi muku shi"...




" dan Allah, dan darajar Manzon rahama, ɗan nan! Ka taimaka ka warware mana wanna kulalliyar" wanna karon malam baba ne yayi magana...




Kasa yin musu papi yayiwa malam baba, domin dattijon yayi masa k'warjini ainun...


Runtse jajayen idanun sa yayi da k'arfi, kana ya ware su kan Nu'aiymah, wani Kallo yaga ta na masa mai dauke da abubuwa masu yawa, saurin dauke kansa yayi, kana yace "ranar da bazan taba mantawa da ita ce 01-10-2003. Ranar ta kasance laraba ce, da misalin karfe takwas na dare, ruwan sama ake mai k'arfin gaske, a lokacin ina da shekara goma sha biyar, na dawo daga gareji cikin ruwan saman, ina daf da shan kwanar layin gidan mu naji kukan jaririya Kwance take cikin kwali ruwan saman yana mata duka, domin har kwalin ya jike sosai......




Nan Nu'aym ya shiga basu labarin komai, tiryan tiryan, kamar yanda yake a page 1 din littafin nan...



Babu abinda mutanen wajen su ke yi sai kuka, saboda tsantsar rashin imanin da Mariya tayi, in ka dauke papi, sai mariya dake ta zaro ido jin Nu'aym ya fadi shekara, kwanan wata, hadi da RANAR da ta yar da diyar Raliya ta farko.....


Nan itama hajiya kaka ta shiga bada labari tiryan_tiryan har zuwa girman Nu'aiymah...
sai ta kara umartan Nu'aym ya kara fadin yanda ya kama Mariya a lokacin da take kokarin ajiye ADEEL....

Ai fa nan mutane suka shiga sakin Salati, sosai kansu ya d'aure, musamman da a waje daya Raliya take ajiye jariran da take daukowa, kowa kuka yake, bare ma Raliya da sai yanzu ta fara fahimtar komai, domin a tunanin ta bacci tayi ta farka, ashe har anyi shekaru goma sha shida bata sani ba.....




"Mariya miyesa? Mena miki? Meyasa kika zabi ki cuce ni? Shin na taba yi miki wani abu ne? Da a kan y'ay'an da nake haifa zaki dauki fansa? Ina bukatar amsoshin nan, mena miki?" Al'ameen ya fada yana nufar ta, jikin sa har wata bari take?...



Cikin sauri Abba kanin shi ya rike shi, domin ya fahimci halin da Al'ameen din yake ciki zai iya kashe mariyar bai sani ba...



Dama larai kiris take jira, hakan yasa ta daga katakon nan ta maka bata a cinya, da baya, "Arrrrrrrrrrrrrrrrhhhhhh wayyo! Na shiga uku, zan fada, wallahi zan fada" Mariya ta fada cikin azaba.


"Toh maza ki fada" yar sanda larai ta fada cikin sautin amo


"baka taba min laifi ba, domin kai mutumin kirki ne, *HAUKAN KISHI NE YA JANYO MIN" majina ta face kana ta cigaba...

Kamar yadda kawo ya sani ni haifafiyyar garin taraba ce, Sannan iyayena masu hali ne domin komai akwai a wadace a gidan mu... Tabbas auren soyyaya muka yi da Al'ameen, bayan shekaru masu yawa Allah bai nufe ni da haihuwa ba, amma ban damu ba, domin Al'ameen baya nuna damuwar sa, a cewar sa haihu ta Allah ce...



BAYAN TSAYIN WANI LOKACI

Kwatsam ya kawo min zancen yaga kanwar aminin sa Auwal yana so...
Hankalina ya tashi irin sosai dinan, a ranar ban yi bacci ba, Saboda ZAFIN KISHI, idan baka manta ba, da farko na tayar da hankalina Sosai, babu kwanciyar hankali a gidan ka, daga baya sai na sanja salo a zuwan na hakura, amma ba k'aramin daurewa nayi ba, domin har ga raina na tsani Raliya duk da ban taba ganin ta ba a loƙacin..



Sosai kaji dadin ganin na sakko, bayan watanin biyu aka d'aura maku aure still ban nuna komai ba, amma araina tsanar ta ne fal, sosai na shiga shige_shigen wurin bokaye da malamai domin raba ku amma ban dace ba...


Watan Raliya takwas a gidan ciki ya bayyana, a ranar tashin hankali dana shiga bazai mitsaltu ba, amma ganin hakan ba mafita bace yasa na sanja salo, ban kuma nuna wa kowa komai ba....


Kulawa sosai na shiga bawa Raliya, amma kasan raina haushin da tsanar ta fall cikin ta, kowa sha"awar mu yake, ganin kishiyoyi masu hadin kai, amma basu san abinda na minne a raina ba....



Bayan na san cikin ta ya isa haihuwa, a kuma lokacin ne wata tafiya ta kama Al'ameen ta kwana hudu duk bai so tafiya ba saboda cikin Raliya daya tsufa, hakan ya min daidai, gun bokan dana dade ina jin labarin sa na nufa, ya kuwa tabbatar min bukata ta zata biya kafin gari ya waye, ai nan nace so nake a haukatar da Raliya, domin ta manta ta san wani Al'ameen a duniya, a tunanin na ma Al'ameen zaka guje ta, amma sai na ga akasin haka...



Ba musu boka na kan tudu yace aiki kam an gama, amma da sharadi duk ranar da Raliya ta ga 'yarta zata dawo hayyacin ta, hankalina ya dan tashi, amma daga baya nayi tunanin ta yaya ma zasu hadu? Hakan ya kara min k'arfin guiwa, bayan na dawo gida nayi abinci mai rai da lafiya, abincin da na zubawa raliya na barbaɗa maganin da boka ya bani, ai kuwa ta shiga ci da zuciya daya muna hira, bayan awa biyu naga ta fara wasu alamu na masu ciwon hauka, murmushin samun nasara nayi...


Hannunta na rike, babu musu ta shiga bina, mota na shigar da ita cikin dabara ta yanda ma'aikatan gidan ba za su lura ba, na kuwa ci sa'a basa farfajiyar gidan...
.



Wani k'aramin daki da na kama hayar sa na kai ta, na rufe ta da kwado, na dawo gida na kwanta ina jin zuciyata wasai, fari kal,...



WASHEGARI

da misalin karfe uku na yamma na koma gidan dana ajiye ta, nan na tarar da ita zaune cikin jini da K'yak'yyawar yarta a gefen ta, ashe nakuɗa ce tazo ta haihu ɗa kan ta... cikin sauri na dauki wani tsohon kwali dake dakin na saka jaririyar kana na sake rufe dakin na fita....



Tunanin zuwa SOKOTO shine abu na farko ɗaya zo raina, domin a tunanin na bazaa su san cewa a waje mai kusa na yar da jaririyar ba, zasu yi tunanin waje mai nisa ne, hakan Yasa naje tasha na tari motar SOKOTO na kuwa samu cikon mutum daya dama suke jira, kuma har na sauka jaririyar bata

Please Login or Register in order to submit comment