Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mana ko Amal.
Ba dole nayi dariya ba Nana irin wannan rashin kunya haka.
Dallacan ya kajitafa,kina wannna maganar ahankali Allah ne kadai yasan yanda kike ruda boo dinki zakina min dariya.
Hhhhhh! Kai Nana Nide ba haka nakeba.
An gaya miki kowa irin kine Uthman yana magana yana kallan titi.
Amma de Yaya kasan Amal nada saurayi.
Tabbas ma kuwa,amma ita tanada kunya ai ba irinki bace.
Hmmm! Ya Uthman kenan gwara nayi a fili kowa ya sani da in zauna ina boye boye.
Ai saikiyita himma kina rashin kunyar.ya fada tareda yin parking kofar gidan.
Amal ce ta bude motar tareda fita tana dariya.
Amma de Yaya kaima kanka kas....
Malam Dallah fita kiba mutane gurin keko ciwo bakinki bayayi sai shegen surutu.
Haba ya Uthman toh mutun Allah yayi masa baki saiyaki magana,ni Wallahi kuna bani mamaki.
Naji jeki de
Harta shige gidan tana faman mita.
Tafdi yaga kokarin Aliyu da zai auri Nana koda yake shima ai haka yake murmushi yayi.tareda kulle motar ya nufi part dinshi dan Lokacin sallah magrib ya kusa.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
(4pm) daidai yafito daga meeting.
Office dinsa ya nufa tareda zama,wayr shice tayi kara murmushi yayi tareda dagawa.
Ahhh! Mutan Dubai ya candin.
Kaide bari ai kayi missing.
Allah ko mutumin kace kana jin ddinka.
Ai barama kaji tun dazu nake kiranka amma nasan kana meeting.
Wallahi kaide bari yanxu nan na fito.ya ake cikine.
Ai wato gidan da muka sauka kaji na gayama anan Amal dinka take.
😳haba de!!
Wallahi kuwa yanxun nan muka rabu dasu,munkai wata frnd dinta gida nida Nana. Na huce nayi sallah.
Ai malam nima nayi mamaki sosai.
Kaga yanda ta kara kyau ta yi kiba Wallahi tanajin ddi.
Allah abokina.
Wallahi da gaske baka ganta ba.ka kirata mana zata cema muna tare.
Amma fa guy kawar nan tata tayi Wallahi.
πŸ˜ƒAllh malam?
Wallahi kuwa nima nan zan shiga kaga nima nan gaba kadan nazama magidanci.
Gaskiya kuwa kaga ka huce gori.Amma nayi mamaki ko dama yr uwarku ce baka saniba.
Allah kadai ya sani.zata iya yihowa hakan,dan ba kaga yanda suke ji da itaba.
Gaskiya naji ddin hakan,ya su mum da Amarya.
Wallahi duk suna lafiya qlau.
Toh masha Allah sau anjima mayi waya bara na kira gimbiya.
Ohk toh sai anjima din.
Sannan sukayi sallama.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Suna shiga dakin alwala sukayi dan yin sallah.
Bayan sun idar,Amal tace da Nana.ina zuwa Amarya.
Murmushi Nana tayi tareda fadin saikin dawo.
Falo ta fito,bataga kowaba tasan suna daki suna hira.
Kitchen ta nufa ta Dora musu abinci marar wahala.
Nan danan tayi ta gama,tana jerawa a dinning. Anty Humairah ta fito daga dakin.
Ganin Amal harta gama abincin tace my Amal harkin gama kike nufi,
Wallahi Anty, ai maras wahalane taliyane kuma dama akwai ruwan zafi a heater.
Toh sannu da kokari Allah miki albarka ya kawo mata tagari.
Kai Antyna.ameen ta fada tareda jin kunya.
Sannan ta koma cikin daki.tana shiga ta tarda Nana na faman waya.
Toh sarkin wa 8:30pm Har tayi saiki tashi kiyi sallah issha ko?.
Dariya tayi tareda dagoma Amal hannu alama bayanxuba.
Yayi kyau shi ba sallah zaiyiba kya sani.
Ta fada tareda shigewa toilet.
Tana fitowa ta sanya hijab dinta tareda tada sallah.
Saida ta kusan idarwa sannan Nana ta yi masa sallama tareda mikewa ta sanya hijab dinta itama ta tada sallah.


πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Suna gama waya da Uthman ya fita masallaci dan yin sallah la'asr.
Bayan sun idarne sun fito kabeer yake sanar masa cewa saura 3wks bikinsa.
Ahhhh Ango kenan kace bikin ya matso Allah ya kaimu lokacin.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
Hajiya ladi kuwa yau da kanta tace zata shiga kitchen me aikin yauta huta.ita zatama Annur abinci.
Nan yahau tunanin abunda zata girka masa.
Harde ta gama yanke hukunci.kitchen din ta shiga dan duba abunda zata hada masa.
Can kuma wata zuciyar tace da ita taje ta gyara masa dakinsa inyaso saita dawo tayi masa girkin.
Dakinsa ta nufa ga mamakinta ta murda ta jishi a kulle.ta kuma murdawa amma still a kulle.tsaki taja tareda barin kofar dakin.
Falo tadawo ta zauna tana tunanin abunyi.
Danyau so take ta faran tawa Annur din rai.


πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Suna idar da salln.
Amal tace da Nana taso muje muci abinci.
Ba tareda tayi mata musu ba afalo suka tarda mum,Hakeem da Uthman da alama Anty tana kitchen.
Zuwa tayi tama uncle sannu da zuwa sannan ta koma kitchen din itama.
Aa Amarya ce uncle ya fada yana kallan Nana.
Wallahi nice uncle Hakeem inayini
Lafiya qlau kunzu lafiya ya kowa da kowa ya Ango da shirye shiryen biki.
Tana murmushi kanta akasa tace kowa lafiya lau wallahi.
Toh masha Allah.
Mum ce ta kalleta tareda fadin ja'ira Ashe kinada sauran kunya ba dika ta guduba.
Dariya duk sukayi.
Hakeem ne yace aa kode kune Baku fashimce taba.
Wata fahimta kuma Hakeem Allah bata da kunya.
Humairah ce ta fito tana dariya tareda fadin dinner is ready.
Mikewa duk sukayi kowa ya nufu dinning din dancin abincin.
Amal da Nana ne sukayi serving kowa sannan suka zauna.
Nan akahau cin abinci ana hira kowa na yaba dadin girkin Amal din.πŸ˜‹πŸ˜‹.
Saida suka kusan karewa sannan Nana taceda Uthman.
Ya yamaganar shan ice cream din.
Harararta yayi tareda fadin baza'aba uwar kwadayi.
Ammafa kayi alkawarin zaka kaimu ko Amal.
Itade Amal murmushi take batace komai ba.
Hakeem ne yace aa Ku barshi ya huta ni saina kaiku.
Mum ce tace da Hakeem aa kayi zaman ka shi zai kaisu.
Wallahi da kin rashi ya huta niba saina kaisu ba.
Allah Hakeem ba inda za kaje ba kannan shi bane ya kaisu mana.
Anty Humairah ce tace itama Nana da shegen San yawo ta hakura mana sai gone zatace sai taje wani shan ice cream saikace me ciki.
Shide Uthman be kuma cewa komai ba.
Illar sai kiyi Sauri Ku gama mu huce.
Mikewa yayi daga gurin.
Itama mikewa tayi tana dariya.ta kalli Amal, tareda fadin taso mana Amal.
Mikawa tayi tareda bin bayanta.daki suka shiga tareda dauko Vail insu sannan suka fito.
Hakeem ne yace ga kudin shan ice cream din.
Nanace tace aa ka banshi ya Hakeem mungode.
Tunda ke bazaki amshi kudina ba my Amal zoki amsa.
Murmushi Amal tayi tareda fadin mun gode uncle sannan suka fita.
A mota suka sameshi sannan suka karasa.
Nan ce ta roki Amal da tashiga gaba dan haushin ta yakeji karya daketa.
Dariya Amal din tayi sannan suka shiga.
Ba wanda ya kula cikin su yama motar key tareda fita daga gidan.


Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)

Dis page goes to you Ummie Jafar ( Autar mama😍). Allah kara basira ya barmu tareπŸ‘©β€β€οΈβ€πŸ’‹β€πŸ‘©

155-160

Waka yayi tareda fitowa towel daure a kugunsa.
Zama yayi gefen gado yana tunanin ina kuma umminshi ta nufa.tabbas har yanzu akwai sauran aiki a gabansa zaita yimata addu'a dan tana bukatar hakan.
Har kwalla yayi sabo da tausayin mahaifiyar tasa da irin wannan rayuwar da ta daukama kansa.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Washe gari Amal bata da lecture.
Koda tagama abunda zatayi.
Breakfast sukayi gaba dayansu suka nufi asibitin dubo Abba.
Sosai yaji ddin ganin su nan Amal ta gabatar mai da rose flower data siya masa.
Sunsha hira sun debemai kewa har suka dan jima sannan suka fito daga asibitin.
Uncle da Uthman gari suka shiga su kuma suka nufi kasuwa dan fara siyayya.
Sosai sukayi yawa dan gaba dayan su sun jigata.
Koda yaushe kuwa Annur cikin kiran Amal dinsa yake susha hirar su ta masoya.duk Lokacin da Annur ya kira Amal Anty Humairah na lura da hakan.
Sai kusan magrib suka dawo gidan dan ko girki baza su samu damar yiba nan Humairah ta kira Hakeem tunda su basu karaso gidan ba.dan su taho musu da abinda zasuci.
Ko wance toilet ta nufa danyin wanka.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Sai bayan la'asr hajiya bilki ta dawo gidan koda ta shigo ba kowa falo,kara tajiyo a kitchen kai tsaye kitchen din ta nufa me aiki tagani tana aiki.
Cikin girmamawa tayi mata sannu da zuwa.
Bayan ta amsa take tmbyrta ko hajiya ladi na nan.
Aa hajiya tun jiya da daddare ta fita kuma Har yanxu bata dawowa.
Ohk! Annur ya fita office ke nan.
Eh tunda safe ya fitan.
Juyawa tayi dan taji mugun ddi da hajiya ladi batanan dan tasan zata iya yaudarar Annur din.dakinta tanufa dan sauke gajiyar da takoso a unguwa.

πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”Ί
Tunda Annur ya fito daga gida office ya nufa dan yauma yana da meeting Har zuwa lokacin shiga masallacin juma'a.
Shiyasa ya fita da huri.
Yanxunma be ddi da fitowa ba.

πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±
Wednesday (3:00pmNG)%
(6:00pm Dubai)

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Annur ya Riga ya dauki break na 2wks a office dan haka sai faman shirye shirye yake mafanyi.
Da har ya matsu goban tazo dan ji yake kamar ya janyo ta.
Koda yaushe yana tareda Amal dinsa a fone ba dare ba rana gashi sunyi wani irin sabo da juna.
Ya riga ya gayama umminsa kan cewar yana da meeting a Dubai kuma sati gida zaije yayi.
Da ker ta yanda ya tafi dan sun riga sun canza magana da Maman Sara.
Ranar Sunday zasu shigo garin kanon.shiyasa bataji dadin tafiyar tasaba dan so take su saba da Sara sosai.
Shikuwa dadi yaji dan tunkafin ya hadu da ita yaji ya tsaneta ainun ko ganin ta baya sanyi ballantana asa maganar aure.
Hakanan ta yarda ba dan tana soba,saidan tana San aikin nasa kuma batasan ya samu matsala da aikinsa.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
Ita kuwa hajiya ladi data tafi gidan wata kawarta ta koma dan ta dauki shirinta Mundin ta dawo Wallahi sai ta aure Annur ko ita ko hajiya bilki.
Hakan yasa hajiya bilki jin ddin tafiyar hajiya ladi dan itama kanta saitafi jin ddi kuma tafi sakewa dama ga baki zatayi.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Lokacinne Amal ta shigo gida dan daga makarnta ta dawo.
Dan gaba daya kwanakin batanan tana makarnta, dan haka suke fita siyayya babu ita hakan baya mata ddi dande babu yanda zatayi ne.
Haka itama Nana batajin ddi in Amal din tatafi makaranta dan gidan baya mata dadi ko kadan.dan sunyi wani irin sabo kullum suna tare cikin raha.
Dan haka itama yau Amal na cikin farin ciki dan murnar gobe habibeen nata zai shigo duk da goban tana da test a skul Amma tana cikin farin ciki.

Jikin Abba kuwa yayi kyau sosai dan yanxu Har tafiya yanayi kuma abinci ko wanne yana iya ci.
Sosai su Amal na kai masa ziyara kuma hakan nayi masa dadi.
Dana Amma kusa sallamarsa dan jiki alhmdullh yayi kyau sosai.

Sakina ma na yawan zuwa gidan dan itama sun zama kamar yan uwa.
Hakanne ya bama Uthman damar bayyana mata abunda ke cikin ransa kuma tayi accepting nasa sosai suma suke zuba soyayyarsu.
Hakan yayima mum dadi data samu labari wajansu Nana.
Dan ta yaba da hankali da nutsuwa na ya rinyar.dan tana komawa zata sanarma Abban sa dama shima ya matsu dan nasa yayi aure.
Sai suje gidan su sakina su tambaya dan basa San abun yadau lokaci.

Uthman ya samu uncle Hakeem ya sanar masa bukatar Annur nasan auran Amal din kuma ya sanar masa yanda Abban Amal din ya dauki abun da kuma tsakanin Abba da ita ummin Annur din.kuma ya nuna masa yanda Annur din da kuma halayyarsa take.
Yakuma nunamai yanda suke neman taimakon sa,wajan neman auranta gun ddi.
Sosai Hakeem yaji ddi dan yanda Uthman yayi masa bayanin komai batareda ya buya masa wani abuba.kuma shima kansa yasan hajiya bilki da ladi gaba daya.
Kuma yayi masa alkawarin insha Allah zasu samu narasa.
Zaijema da Abban Amal maganar inya fito daga asibitin.

Uthman yaji ddi sosai kuma yayima uncle din godiya.
Annur ya kira duk ya shaida masa yanda sukayi da uncle Hakeem. Shima yaji ddi sosai yayi ma Allah godiya Yakuma yima Uthman din godiya daya ciki aboki na gari.

πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”Ί
Tana shigowa gidan danjin shiru tasan ba kowa daki ta nufa tayi wanka.
Kitchen ta nufa kafin ayi sallah. Girki ta dura musu sannan ta koma daki.
Bayan ta idar da sallah ne taji karar shigowar su.
Batareda ta cire hijab din jikin nata tafito falon.sannu da zuwa tayi musu sannan suka shiga da kayan dakin dasuke ajjewa.
Amal ta kalli Nana data baje akujera.sannu Amars ya hanya.
Harara ta watsa mata ta wasa tareda fadin zan kamaki shine kika boyemin wayata ko.
Ba kowa a falon sai su biyu dansu su mum sun shige daki.
Haba tawan banasan kina tafiya kina waya danna rage miki wahalama.
Pilon dake kusa da ita ta cilla mata tana dariya.
Itama dariyar takeyi ta shige cikin tana fadin sowie Aliyu's wife to be.
Hahhha Wallahi zaki shigo dakin ki sameni kuma kema yau babu waya da Annur..
Sannan ta shige dakin.
Amal dake cikin tana karasa girkinta tace lallai ma aida kin kasheni dama kina gani yau skul ta hanamu waya..

Bata jimaba ta gama girkin ta jera kan dinning sannan ta koma dakin dayin sallah issha.
Lokacin data shiga sallah Nana takeyi dan haka itama sallah ta tada.
Kusan atare suka idar.
Saida suka shafa addu'a sannan Nana ta kalli Amal da hararar wasa.
Allah Amal baki da mutunci yanzu ko wani hali kikesan Aliyu ya shiga.kuma gashi bama tareda ya Uthman balle ya kira shi.
Dariya tayi ciki ciki.tareda mikewa tana fadin haba uwargida sarautar mata gashide ki kirashi ki cinyeshi.ta dauko mata wayar daga cikin Jakarta ta mika mata tana dariya.
Nana dake zaune tana jira ta miko mata wayar.
Tana mika mata ta janyo ta tana dariya tana mata dukan wasa.

Mum ce ta turo dakin da sallama.
Daga bakin kofa ta tsaya tana kallansu.
Allah ya shiryeku kullum saikace kananun yara Ku dosa dukan juna.
Amal data janye jikinta daga na Nana tana dariya gashin kanta duk ya hargitse ta kalli mum tace Wallahi Nana ce mum.ta karashe maganar tana kallon Nanar dake zaune itama kanta ba ribbon.
Mumce tace aidama nasan sai ita.
Nana ta kalli mum kamar zatayi kuka.
Wallahi Amal cefe ta tafarmin da wayata makaranta kuma bamuyi waya da Aliyu ba.
Baki ta rike da hannunta Oo ni yrnan! kunga Ku taso kuci abincinku.
Toh mum Amal ta fada tareda gyara gashin kanta.
Ni sai nayi waya da Aliyu tukun.
Mum ce ta shigo dakin ta nufi Nana tana fadin zaki tashi ki huce kosaina ci kwal baki keda wayar..
Da gudu suka fito falon suna dariyaπŸ˜†πŸ˜†

Sai bayan sungama cin abincin sannan suka dawo falo danyin hira banda Nana data shige daki danyin waya.

Uncle Hakeem ne ya kalli Amal sannan yace da ita naji duk abunda Uthman yace dani game da yaran dayace yana sanki.
Yanzu ga Uthman, Antynki harda Maman Uthman. Zansamu Abban ki da wannan magana Amma kafin nan inasan naji da bakinki in kina kaunarsa.
Amal da kanta ke sunkuye a kasa cikin kunya kanta na can kasa.
Tace eh! Uncle!
Yauwa toh alhmdullh kinga yanxu inada confidence din magana da abban ki.
Anty Humairah da mum ma duk sunji ddi musamman ma Uthman.
Mum ce tace tabbas Amal tayi dacan miji dan Wallahi Annur yarone mai hankali da kuma kirki.dan Hausa na fadin albasa batayi halin ruwa ba.
Saide fatan Allah ya sanya alkhari aciki.
Kowa de ameen yace.
Anty Humairah ce tace,aimu zama be kamaniba zan aurar da yr guda nike zaune haka.
Dariya de suke ita kuwa Amal diki ta shige dan kunya..


Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)

160-165

Daki ta shige da sauri tana dariya itama.
Tabbas taji ddi kuma Allah yasa Abban ta ya amince.
Nida fans mukace ameen ya Allah.

Saida sukayi waya sannan suka kwanta.

πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±
Thursday morning
(7:00amNG)
(10:am Dubai)

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Annur ne yafito cikin shirinsa tsaf na tafiya afalo ya tarda umminsa zaune kan daya daga cikin kujerun dinning din.da alama shi take jira da batasan ya tafi beyi breakfast ba.
Har kasa ya durkusa tareda fadin Ummi ina kwana.
Lafiya qlau Annur harka fito ne?
Eh Wallahi Ummi.
Toh Allah ya kiyaye hanya ya saukeka lafiya,naso tare zamuyi tafiyar nan Amma nayi alkawarin bazan komaba sai bayan bikinka.
Yanxu de kafin katafi kazo kayi breakfast tukun sai muje na anjeka a airport din.
Bai musa mataba ya mike tareda zama kan kujerar,nan ta mika masa abincin Shide kawai yana cin abincinne badan yana soba.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Tana tashi da safe tayi dukkan abunda zatayi sannan ta shirya cikin shirin makarantar ta.
Dan tasan ba wanda ya tashi acikin gidan sai uncle Hakeem shima dan fita zaiyi.
Dinning ta nufa tayi breakfast dinta dan tasan uncle ya dade da fita tun 7am.
Bata dau lokaci ta gama sannan ta fice zuwa makarnta dan yau tana da test.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Yana gamawa ta dauko mayafinta da key din mota suka tafi.
Suna tafiya suna hira sama sama,dan duk hirar tata akan bikin shine da Sara.
Shikuwa hankalinsa ma baya gurinta kawai tunanin yanda Amal zatayi inya ganta.
Har suka isa airport din tana ta faman zuba ita kadai danshi bama jinta yake ba.
Basu jima ba aka fara kiran masu tafiya nan danan suka gama komai,saida suka kara sallama da Ummi sannan ya huce.
Saida jirgin su ya tashi sannan tabar airport din.
Cike da so da kauna dakuma kewarshi dazatayi.

πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±πŸ”±
(3:19pm Dubai).

Jirgin su Annur ya sauka.
Kai tsaye daga airport din hotel ya nufa nan yayi bucking din komai aka bashi dakin dazai zauna.
Nan ya haura da kayansa ya shiga dakin.
Iya haduwa dakin ya hadu komai a gyare an kayatashi sosai gwanin ban sha'awa.
Kayan shi ya anje nan ya nufi toilet dan watsa ruwa ajikinsa.
Bayan ya fito daga toilet din daure da towel a kugunsa,wayar shice da take ringing ya nufeta dan duba me kiran.
Uthman ke kiranshi murmushi yayi ya dauka.
Ya mutumin harfa na sauka,yanzuma na kama hotel yanzuma nayi wanka zan shirya na taho.
Yawwa pls kayi Sauri kaganta can tana faman jiranka.
Ohk insha Allah gani nan.
Maza yayi ya shirya cikin ka nanun kayan da suka amsheshi yayi kyau sosai ya feshe jikinsa da turare sannan ya fita.yana fitowa wani dan gurin saida gold ya tsallaka ya siyoma Amal wani zobe me kyau sosai dan karami daidai hannunta sannan ya sanya a aljihunsa.
Wayar shi ya Ciro ya turama Uthman address din hotel din sannan ya kira shi.
Pls kazo ka daukeni kaji.
Baka da damuwa gani nan zuwa.

Bai wani dau lokaci ba ya karaso wajan da Sauri ya fito sukayi hugging din juna suna murnar ganin juna.
Sannan suka shiga cikin motar.

πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”Ί
Amal kuwa tunda aka taso daga makaranta, gida ta nufo cike da murna.
Tana zuwa suka hau yimata tsiya dan kowa yasan da zuwan Annur din.
Toilet ta nufi tayi wanka ta fito.
Data dawo anan ta tarda Sakina ita da Nana suna mata tsiya Har daki suka bita.

Kwalliya ta shiga tsan tsarawa tayi kyau kamar ka saceta ka gudu.
Wani hadaddan blue green din material Anty Humairah ta dauko mata yana da adon flowers silver.
Jewelry silver tasa tayi kyau ainun sannan ta sanya silver plat shoe da mayafi silver OMG! I can't explained how pretty she look.
Su Nana dake zaune kan gado kallon ta kawai suke dan tayi mugun haduwa.
Sakina ce tace anya kuwa yau Annur bazai zauceba irin wannan haduwa haka.gaskiya Amal kinyi kyau ba karya.
Masha Allah Nana ta fada tana daukar ta photo.
Sannan suka fito falon.
Anty Humairah ce ta taso da Sauri ta rungume Amal din tana fadin tubarakallah Masha Allah.
Mum ce tace dole Ku zautamin yarona irin wannan ado haka.
Dariya suka sa gaba daya.

Lokacin ne Uthman yayi dakin a daidai kofar gidan.
Amal ce ta dafe kirjinta tare da rufe idanunta.
Nana ce ta rike hanci tareda ran gada buda.
Megida ya karaso Angon Amal ya iso.
Mum ce tace kede Nana Allah ya shiryeki.
Dariya sukayi gaba dayan su.

Annur da Uthman ne suka shigo da sallamar su.
Batare da Annur yaga Amal din ba ta shige daki da Sauri tare da rufu kofar.
Jingina tayi da kofar ta rike kirjinta tana numfashi sama sama.
Fuskar ta dauke da murmushi dan wani irin farin ciki takeji wanda bazata iya fasalta irin shiba.
Hawaye taji suna sauko mata.
Ita kanta ta rasa hawayen menene.

Zama sukayi saman kujera.
Fuskar shi dauke da murmushi ya russuna ya gaida kowa na cikin falon.
Sosai Anty Humairah taji ya burgeta.kuma taga kamala da nutsuwa a tare dashi tabbas Amal dinta tayi dace.itama kanta saida tayi kwallar farin ciki.
Bayan sundan jima ana hira sannan sukace bara su basu guri.akira masa Amal din tazo ta zuba mai abinci.
Uthman kuwa inkiya yayima sakina dasu hadu a waje.
Su mum daki suka koma.ita kuma tabishi suka fice.
Nana ce tashige dakin dan kiran Amal din.
A gaban mudubi ta ganta tana gyara fuskarta.
Oo! Ni Amal ko fuskar za'a canza.sai faman kwan kwalarta ake.
Itade murmushi tayi batare da tace komai ba.
Toh kije inji habibeen naki ba kowa

Please Login or Register in order to submit comment