Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muce zasu zo siyan kayan auran kan wata.
Wow! Kice Anty zamu sha biki,Allah yasa lokaci ba skul.
Insha Allah babu.

Wayar Humairah ce tayi kara.
Hannu tasa ta dauka dan ganin uncle ne ke kiranta.
Tana dagawa yace.
Ina Amal ta shigane ina ta faman kiran wayarta no ans.
Ka gantanan maybe tabar wayar daki.bata mana.
Ansa tayi tareda gaida shi.yauwa Amal barka,yanxu aka kirani daga asibiti Abba ya farka Har an bashi abinci.
Wani uban tsalle ta yi,tareda saukuwa daga saman gado. Tana murna.
Zagayowa tayi tareda rungume Anty Humairah,
Anty Abbana ya farka wayyo dadi Wallahi Har yaci abinci.
Ahhh! Barka Allah ya kara sauki.
Toh sarkin murna sai kici gaba da addu'a, mikawa Antynki wayr.
Da Sauri ta mikawa Anty Humairah wayar.
Yanxu suka kirani Wallahi kinga jiki ya fara samun sauki sai acigaba da addu'a Allah ya kara sauki.
Ameen ya Allah ga shinan anata faman murna.
Dariya yayi,sannan yace,ki tashi ki kaita skul in antashi saiki biya ki dauke ta Ku taho asibitin nima yanxu zanje.
Toh adubashi kafin muzo.

Amal dake tsaye tsananin farin ciki tama rasa inda rata sanya kanta dan ddi.

Anty Humairah ce ta mike tareda fadin,saiki huce na kaiki makarnta in an tashi zamu huce asibitin.
Haba cwt Anty mu fara zuwa asibitin mana.
Uncle dinki cewa yayi saikin taso,saurin me kike yine ,maza ki huce mu tafi kinga bai kamata da fara zuwa makarnta ki fara missin lectures ba.
Ba haka tasoba amma bata nunaba,toh Anty na muje.

Jakarta ta dauka da fone dinta.suka fita tareda kulle gidan.
Suna shiga motar.
Amal ta shiga kiran hanne.
Ba tadau lokaci ba ta daga kiran nata.
Hello! Amal ina kwana.
Lafiya qlau hanne,dama kiraki nayi na shaida miki Abba ya tashi.
Alhmdullh barka Allah ya kara lafiya.
Ameen hanne yanzu makarnta zan tafi innaje asibitin zan kiraki.
Nan sukayi sallama.

Suna karasawa makarnta ta sauketa,
Sauri taketa famanyi dan ta yi latti.
Kai tsaye class dinsu ta nufa dan tasan anshiga.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
1:00pm πŸ•
Suka fito daga lecture sai kuma zasu shiga ta.( 1:45 to 3:00pm).
Gauri ta samu kasan wata bishiya ta zauna tana duba wani littafi.
Wayr tace tayi kara.
Tana dauka taga Sakina ce ke kiranta.tana dauka.
Amal kina inane yanzu na fito daga lecture.
Wallahi nima yanzu na fito,ina bayan library a zaune wajan flowers din nan.
Ohk to gani nan zuwa.
Toh saikin karaso sukayi sallama.
Cigaba da abunda take tayi.

Bayan 10mins.
Sakina ta karaso wajan hannunta rake da Leda.
Itama zama tayi kusa da Amal din sunama juna murmushi.
Amal sannu da hutawa ya kikaji makarantar tamu.
Hmm! Ba magana karatu akwai huya sai an daure wlh.
Sosaima kuwa me kike karntane Amal?
Sakina ta yima Amal wannan tambayar tana kokarin fito da abunda yake cikin Leda.
Meat pie ne da lemo guda biyu ta shiya musu.
Sannan ta mikawa Amal di daya ta dau nata.
Tnkuuuuu! Ta fada,
Ina karantar medicine ne.
Yayi Allah ya bada sa'a. Sannan ta kurbi meman hannunta.
Nikuma ina karantar mass comm.ne.
Itama Amal din ci tafarayi tana kallon sakinan.wow! Kinsan nima abunda nakesan yi kenan Amma Abba ya fisan science wlh.
Gaskiya science yayi,gwara kiyi science din muzo muce Dr.Amal amana allura tafada cikeda zolaya.
Dariya itama Amal din tayi.

Sunaci suna hira Har suka kammala.
Sannan suka nufi skul mosque dan gabatar da sallah.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά

Yana zaune a office dinsa yana faman aiki wayar shi tayi kara da alama kiran sa ake.
Daukowa yayi tareda duba kowaye sanna ya kara a kunan sa dayan hannunsa rukeda paper.
Uthman ne yake kirasa.
Hello Angon Amal ya office din,Uthman ya fada yana dariya.
Shima dariyar yayi, tareda fadin lafiya qlau Wallahi.
Kai mutumin nan daga ji muryar ka kana cikin farin ciki.bani nasha mana.
Kaide bari mlm ai munyi maja da mutuniyar dan muna waya sosai.
Hhhhahha! Kace na fara shirye shiryan biki.
Shima dariyar yayi.
Amma kasan Abban ta nanan da ransa.akwai de abunda yake faruwa shiyasa sukayi hakan.
Amma de Har yanxu be farfado ba.
Ayyah Allah sarki Allah kara lafiya.
Ameen yace dashi,ya ake cikine mutumin kwana biyu.
Wallahi kaide bari abubuwa sunyi yawa.yanzuma on Thurs su mum zasu huce Dubai kasan yr gidan yayrsu za'a yima aure shine zasuyi siyayya. Toh kuma naji mum na fadin na shirya dani za'a.
Ahabade kaga nima Dana biku inasan ganin Amal ita,saide problem daya Wallahi inada meeting da wasu yn kasar Spain saide next week.
Amma mutumin kana ganin Ummi zata barka.
Kai in bata barni naga maso yiyataba ni zata aura.commot Dallah.
Ahhhhhhh Allah my guy kace Lov ba wasa.nimade zan samo wata cika najide yanda kukeji.
Dayafi de.
Dariya sukasa gaba dayansu.sannan sukayi sallama.


Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)

130-135

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Suna fitowa daga masallaci, suka rabo.
Ita Sakina gida ta tafi.
Ita kuma Amal class ta koma dan tana da wata lecture.

[3:00pm]
Daidai lokacin suka fito daga lecture.
Tunkafin su fito Anty Humairah ta fito cikin shirinta dan tafiya asibitin.
Tana fitowa daga lecture ta kira ta,nan ta gaya mata inda zasu hadu.
Cikin mota ta sameta zaune tana jiranta.
Side din da zata shiga,
Ta fude tareda sallama ta shiga.
Harkin fito?
Anty Humairah ta tambaya tana kokarin yima motarki.
Eh! Wallahi amma da alama kin dan jima anan.
Eh to bawani sosai bade.
Ya skul din.
Alhmdullh, gobema 10 nake da lecture.
Hutana frdy,sat nd sun.
Amma kullum ina zarya.
Amal kenan aishi haka karatun ya gada,saide hakuri.
Ta karashe maganar tare da shan wata corner.
Amma Anty uncle ya kiraki sunyi magana da Abba.
Eh gaskiya yade ce mini yaje jiki alhmdullh.
Allah mun godema,dan Wallahi duk atunanina Abba baxai tash.....
Fone dinta dake cikin jaka ce tayi kara.
Hannu ta zura ta dauka.
Annur ne ke kiranta,duk sai taji tanajin kunyar Anty Humairah.
Kuma bazata iya katsema hrtcontrol dinta wayaba.
Dagawa tayi tareda sallama.
Ya kk ya skul din ko Har kin dawo.
Um! Yanzu na fito daga lecture muna kan hanyar zuwa asibiti duba Abba ance ya samu sauki dan Har ya farfado.
Toh alhmdullh pls ki duba shi,in kinje,nima insha Allah nextwk zan shigo.
Bazade ka hakura da zuwanba kenan ko?

Kamar zai mata kuka yace.
Haba Amal ko bakya San gani nane,
Aa ba haka bane aikin naka fa?
Amal break zan dauka danna zo na ganki.
Kinga Uthman ma yana nan shigowa.
Insha Allah zaizoma gurin ki.
Ki gayamin me kikesan ya kawo miki.
Shiru tayi tana San tace wani Abu Amma tanajin nauyin Anty Humairah.
Zan fadama yanxu mun karaso asibitin sai anjima.
Ohk saikun dawo kinji.
Bye.

Daidai lokacin sukayi parking motarsu.
Gitowa sukayi
Anty Humairah tana kallon Amal da murmushi.
My Amal ko mun samu siriki ne?
Kai Anty ba wani siriki abokine.
Hahahah ja'ira abokinne ake kashe mai murya haka.
Itama dariyar ta bata.
Sanan ta zagaya suka nufi cikin asibitin suna hira abun aha'awa.
Elevator suka hau nan da nan suka isa.
Dakin suka nufa,
Amal ji take dan dadi kamar tayi tson tsuwa ta shiga cikin dakin.
Da sallama suka tura dakin.
Ganin Abbanta zaune wata nurse gabanshi da alama magani ta bashi.
Da sauri ta fada kansa tana kukan dadi.
Shima murmushi yayi tareda shafa kan nata.
Ita kanta nurse din sun burgeta Har murmushi tayi sannan ta fice daga dakin.
Anty Humairah ce ta karaso tadan rissina tareda gaida Abban.
Ahankali ya amsa,tareda tambayar ta ya gidan.
Lafiya qlau ya Karin sauki.
Alhmdullh yace.

Amal din Abba kukan me Nene koma kikeyi tashi ki goge hawayanki.
Dagowa tayi abunka da farin fata Har fuskn ta danyi ja.
Abbana sannu Allah ya kara sauki.
Ameen Amal dina.
Dazu na tambayi Hakeem kina ina!
Yace ai kina makarnta.
Naji ddi sosai.
Allah ya miki albarka ya baki miji na gari kinji.
Ameen Abbana, hanne tace tana gaida kai.
Ina amsawa Amal.
Bani rau insha.

Da Sauri ta juya ta dauko ruwan kan wata yr wardrobe ta dauko ruwan tareda zubawa a cup.
Matsawa tayi gaf dashi,ta bashi a baki.
Yan sha yadan kware.
Maza tayi ta anje cup din agefe ta rungumoshi kamar karamin yaro tana ahafamai baya a hankali tare da yimai sunnu.

Humairah dake gefe ita kanta sun bata tausayi koma sun burgeta Har kwalla saida ta zubar.

Tana manne jikinshi tace Abbana.
Naam Amal!
Annur yace yana gaida kai.
Amal waye kuma Annur?
Hmm zaka sanshi yacema shima zaizo ya dubaka insha Allah.
Toh Allah kawoshi.
Ameen ta fada tareda janye jikinta daga nasa tana kallon sa.
Abbana duk ka rame .
Hmmm ke kuma kinyi kibarki ba,su Humairah sun sa yarinyar ta koma yar lukuta.
Dariya sukayi gaba daya.
Humairah ce tace aikode gatanan ba wani abincin kirki take Ciba.
Abban ne yadan bata rai ya kalleta.
Kunnan ta takama tareda make kanta jikin kafadunta.
Am sowie Abbana dama saboda tuna ninkane banaci Amma tuna gashi ka warke zan dungaci sosai Wallahi.

Karar wani Abu sukaji kamar ana magana.
Mikewa Humairah tayi,tareda fadin Amal kuma saita taso mu huce Lokacin visitors ya kare.
Kamar zatayi koka ta kuma makewa jikin Abban nata,
Shima bayasan Amal din tashi tayi nesa dashi,Amma ba ynda ya'iya haka dokar asibitin yake.

Sallama sukayi masa tareda yi masa alkawarin zata dawo gobe harda yr kwallanta.
Kiranta yayi tareda goge mata hawayan.
In kika kara kuka,
Ya dubi Humairah karki kara kawota.
Murmushi tayi tareda kara rungume shi.
Insha Allah Abbana na dena.
Hannu suka rinka dagawa juna Har suka bar dakin.
Itade Humairah kallan su take famanyi da mamakin irin soyayyar da sukema juna.
Sannan suka fita tareda shiga mota saikuma gida.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Suna gama waya da Amal.
Nan ya shiga tunanin ko inyaje ya zata kaya musu da Abban Amal dukda yana tunanin bazaisha wahala wajan shawo kansaba.
Umminshi ce zata kawo matsala amma insha Allah yau zaije mata da maganar.

πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”Ί
Dakin hajiya Bilki ta nufa.ko sallama babu ta tura dakin tareda shigewa taci uwar kwalliya kamar wacca zataje gasar sarauniyar kyau.
Bilki ni zan fita saikuma na dawo.
Ba tareda ta kalli inda takeba tace saikin dawo.
Murmushi tayi tareda janyo mata kofar ta fice.
Harabar gidan ta fito tahau motarta.
Sannan ta fita.
Hajiya bilki dake tsaye bakin window tana kallonta.
Murmushi itama tayi hmm! Ki gama haukanki nan da wata biyu zuwa uku zanma Annur din aure sai naga abunda zakiyi.
In banda haukama irin naki me Annur zaiyi da mata irinki.
Tsoki taja sannan tabar wajan window.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Suna komawa gida.
Wanka amal tayi sannan tayi sallar la'asr.
Fitowa tayi dan neman abunda zata sama cikinta.
Kitchen ta nufa.
Ta dauko abinci.
Rashin ganin Humairah a falo ya sanyata binta dakin dan batasan zama ita kadai.
Da sallama ta tura dakin.

Humairah dake tsaye jikin wardrobe tana gyara wasu kaya ta jiyo ta amsa.
Zama Amal din tayi tareda bara cin abincin ta.
Anty ni kuwa yaushene in uwankun nan zasu zo.
Amal kenan kin matsu suxone?
Eh! Wallahi Anty, amma de harda amaryar zasu zo ko?.
Eh da amaryar da kanwar mamanmu sai kuma danta.
Allah ya kawo su lafiya.
Allah Anty banaso suzo ranar da ina da skul.
Aikuwa inaga ranar Thurs zasuzo,kuma exactly kina skul.
Amma ai zaki dawo ki tanda su.
Amma nide gaskiya Anty banso hakanba.
Dariya tayi mata tareda fadin Amal sarkin San mutane..
Wallahi kuwa kinga ya kama jibi ke nan.Allah de ya kaimu lafiya.
Ameen.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
Annur yau da huri ya dawo daga office yana zaune a daki yana signed din wasu files.

Umminshi tayi sallama tashigo dakin.
Zama tayi bisa gadon tana fuskantarsa.
Shima ita yake saurare dan duk ya anje komai gefe daya.
Sannu da aiki tace dashi.
Shima amsa mata yayi tareda fadin yauwa ummina ya gidan.
Lafiya qlau Annur.

Dama akan maganar da mukayi da kaine nayi maka magana Amma kayi shiru saboda haka Nina sama maka mata nanda 2months za ayi mikin.
Sara yr gidan hajiya murja da suke a Lagos sabo haka nariga na yanke hukunci kuma aure ba fashi.
Nanda 3wks zatazo gidan nan ta zauna Har Lokacin bikin naku.dan anan nakesan ayi komai.
Wallahi yarinya abar tausayi kasan babanta ya rasu tunda jimawa.
Kallonta yake da mamaki.
Sannan yace Amma Ummi ita yarinyar cewa tayi tana sona?
Eh na tura musu pic ka,sunce kayi musu.
Amma ni kinsan ina santa ko bana Santa.
Nasan Annur ko kare na kawo maka acikin gidan nan zaka soshi balle mutun sukutum,kaima dan baka ganta bane Amma nasan zaka sota.
Mikewa yayi tsaye tareda fadin toni bana Santa bana kuma kaunarta,
Wallahi ummina bazan taba San wata ya mace acikin zuciya taba inba Amal ba.
Tasssss yaji ta kasheshi da mari.
Wallahi Annur sunan tama nakuma ji acikin gidan nan saina tsine maka.
Kai wani irin mahaukacine,kanada hankali kuwa.
Ko kunya bakaji a hulakanta uwarka agabanka Amma kace still kan San hada jini da wadnnan hula kantaccin mutanan.
NA gayama kuma nakara maimaitama banasan Amal kuma bazaka taba auran taba koda hakan zaiyi silar barinka duniya.
Kuma ka shirya ba abunda zai hana auran ka da Sara,sakaran banza wanda besan mutuncin kansaba.
Sannan ta juya tabar dakin.
Murmushi yayi ko ajikinsa yasan babu abunda ya isa ya hana ikon Allah, kuma yanaji ajikinsa Amal matrsa ce.
Toilet ya shiga danyin alwala sallah insha..


Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)

135-140

Yana fitowa, masallaci ya fita dan yin sallah.
Umminshi na zaune a falo tana kallon sa Har ya fice ba tareda ta cemai komaiba.
Shima kuwa ko kallon inda take baiyiba.

Bayan an idar da sallah ya shigo gida.
Lokacin yayi daidai da fitowar hajiya ladi daga mota.da Sauri ta kulle ta karaso gaban Annur din.
Annur ta kirayi Sunansa.
Kallonta yayi samada kasa sannan yace ya akai.?
Naji sakon ka gurin mahaifiyar ka,Amma inasan ka gayamin dalilin da yasa baka sona.
Wata iriyar dariyace ta subuce masa,harda rike ciki sosai yake dariyar bashida alamun tsayawa.
Sabida bakin ciki kasa koda motsawa tayi tana ta faman kallonsa.
Cigaba da dariyar sa yayi tareda shigewa gida.dan bama zai iya sauraran haukan matar ba.
Da sallama ya shiga falon fuskar sa dauke da alamun murmushi.
Ya huce zuwa dakinsa.
Umminsa data zubamai Ido da mamakin murmushin me Annur yake.bata gama yankewa kanta hukuncin hakanba.

Hajiya ladi ta shigo fuskarnan ba alamun dariya kamar karamar yarinya.
Hakanne ya baima hajiya bilki dariya itama.
Tsayawa tayi cak!
Tareda juyowa a fusace tana kallon ta.
Wato kun maidani mahaukaciya keda danki ko,kun ajjeni agida ga joker kuna kallo.yayi muku kyau.
Ta juya fuuu! Tashige dakinta tareda banko kofar.
Hakanne ya sanya hajiya kara tuntsirewa da dariyar da tafi ta farko.
Wato shima Annur din kin bashi dariyar kenan.
Mikewa itama tayi tareda shigewa dakinta tana fadin Allah ya kyauta..


Thursday morning
[9:00am] daidai ya nuna agogan Dubai.
πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Amal ce ta fito sanye cikin shirinta na tafiya skul.
Riga da wandone ajikinta green color na Pakistan sunyi mata kyau sosai sai jacket baka data sanya saboda yanayin garin na sanyi.
Tayi rolling mayafin kayan a kanta.
Sannan ta rata jikarta.

A dining ta tarda Anty Humairah.
Zama tayi tareda gaidata.
Cikeda fara'a ta amsa mata.
Harkin fito kenan yau ba ai baccinba kenan.
Wallahi Anty Sauri nakeyi yau test ne dani Har gudu biyu,shiyasa nake Sauri danxan duba wani littafi cikin library.
Toh Allah ya bada sa'a ya kuma sa acinye gaba daya.
Ameen tace.
Tanata faman Sauri ta cinye abincin dan 10am zasu shiga lecture.nan danan ta tuttura.
Sannan ta mike dan tacema Anty Humairah zata tafi da kanta dan itama tasan gari kuma aikina take yi danyaune bakin su zasu zo.
Mikewa tayi tareda rataya jikarta sannan ta zagayo wajan Anty Humairah ta manna mata peck a kumatu.
Tareda fadin bye my Anty,in baki sun karaso asanar dasu ina gaidasu kafin na karaso.
Dariya tayi tareda fadin insha Allah my cwt hrt bye.

Sannan ta fita daga gidan tareda janyo mata kofar.
Bakin titi ta nufa sannan ta tari taxi sai makarnta.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά
[6:00am]
Daidai ya nuna a agogon Nigeria.

Kai tsaye airport na nufa.
Da alama passengers suna cikin jirgi.dan naka jirgin bai tashiba.
Maza nayi na fada cikin jirgin ina nishi saboda uban gudun danasha.
Neme neme yashiga yi.
Can nahango.
Uthman zaune shida wani saurayi da alama yanxu suka hadu dan gaisawa sukeyima.murmushi nayi nakuma matsawa.

Mum na hango zaune kusa da ita wata kyakyawar budurwace da gani shekarunta bazasu huce 19 zuwa 20 ba.ta kwanto da kanta jikin mum.
Ita kuwa mum tana ta faman mita.
Ace mutun sai shegen San jiki Allah Nana (Halimatu sunan ta shine suke kiranta da Nana).
Zanga ranar da zaki dena sai kace mage.
Nana dake faman dariya tana kara shigewa jikin mum.
Kai dan Allah Mum Uthman dayake haka suke kiranta.
Auremafa zanyi basai nazoba zn dinga zama jikinki.
Naji uwar rashin kunya daga.
Dariya tayi tareda dagata.innayi aure nasa Aliyu bai hanani kwanciya jikinshi.
Jeki kita kwanciyar maras kunyar banza.Allah yaran zamani baku da kunya.
Mum Uthman meye kum....
Kene rufemun baki sai shegen surutu kamar parrot.
Dariya taci gaba dayi tana kallon mum din.
Suna cikin hakanne jirgi ya tashi dama already sun daura belt dinsu.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
Shima Annur yau da huri ya tashi saboda yanada meeting har guda biyu.
Yanxu zai shiga 7am ya fito 11am.
Bayan nan zai shiga wani da 2pm zuwa 4pm.shiyasa baibi su Uthman din ba.
Amma yana da burin yin hakan Amma tunda 2wks zasuyi shima zai bisu yayi ko 1wk dayane inyaso saisu dawo tare.
Nan danan ya gama shirinsa.
Falo ya fito ya nufi dinning ba komai sai ruwan tea.shiya zuba yasha sannan ya fice daga gidan.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·
Koda Amal ta karasa makarnta kai tsaye library ta nufa.
Tana shiga ta shiga neman littafi da zata duba.
Ba tadau wani lokaciba ta dauko shi tashiga dubawa dan remains 15 mins su shiga test din.
Wayar tace tayi kara da Sauri ta zira hannu ta dauka tareda karawa a kunne sakina ce ke kiranta.
Amal yau bazan samu damar zuwa skul ba Amma ki gayamin lokacin da zaki fito a lecture nasan raki dubo Abba sai na zo najiraki mu huce asibitin.
2pm zan fito inyaso saiki jirani mu tafin.
OK saikin fito bye.
Ta kashe wayar.
Nan taci gaba da abunda takeyi dan Sauri take batasan lokacin yayi bata gama ba.

Bayan wasu yn mintina ta mike ta nufi class dinsu da gabatar da test din dake gabanta.

πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”Ί
Anty Humairah kuwa.sai faman aikin tarbar baki akeyi ta dora wannan ta sauke wancan.
Ta gyara gidan babu abunda yake sai kanshin girkiπŸ˜‹πŸ˜‹πŸ˜‹
Dan Anty Humairah gwanace wajan girki ta iya abinci kala daban daban.
Shiyasa take koyawa Amal.
Gata da tsafta da kwalliya.komai nata tsaf yake.
Shiyasa uncle Hakeem kejida ita suke zaman su lafiya koda basa haihuwa hakan baya daga musu hankali saide koda yaushe su kaga yaro yana burgesu.
Shiyasa suke kaunar Amal kamar yar cikin su.
Ita kanta Amal din tausayinsa takeji harta daukama kanta alkawarin inde tayi aure ta haihu zata basu first born dinta kyauta wa su dan saka musu da alkharin da sukayi mata.πŸ˜ͺ.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
(2:00pm)
Harsun sauka sun iso gidan Anty Humairah, da yake ita taje ta dauko su.
Sai yaba kyan gidan da tsarinsa suke.
Boys quoters ta kai Uthman daki mai kyau da toilet nan ya haye gado yana kallan ta.wlh nagaji Anty Humy.
Saika tashi kayi wanka kazo kaci abincinka.
Sannan ta fice daga dakin.

Dakinta takai mum Uthman da Nana. Suma zama sukayi tareda fadin gaskiya mun gaji.
Mumce ta kalli Nana dake kwance tana wani latsa fone.

Yimin shiru bayan duk akaina kikaxo yarinya sai shegen San jiki.
Allah inzamu koma baki zama kusa dani.
Dariya Humairah tayi tareda fadin Allah ko mum.
Wallahi yn nan bata da kunya karama da YAYA zata aurar da ita.
Dariya Nana ta kamayi.
Mum Uthman me nayi kuma.
Zaki min shiru ko saina kode miki baki.

Dariya Humairah ta kama sannan ta kalli Nana toh zaki zauna nan dakin ko kuwa dakin Amal zaki zauna.
Yauwa Anty ina Amal din Allah na matsu na ganta.
Ayyah zaki ganta tana makarnta sai zuwa anjima zata dawo.itama yanata faman jin ddin zuwanku Wallahi bakiga yanda take sankuba tunkan Ku zo.
Mumu ce tace Allah Sarki harkun tuna naming da wata yarinya abar tausayi itamako Amal Sunanta.
Anty nide kaini dakin Amal din na watsa ruwa can zan zauna Allah sa tana da surutu musha shagalin mu.
Mum ce ta kalleta Allah shiryaki Nana.
Dariya sukasa sannan ta dau trolley dinta Anty Humairah ta dakata dakin Amal din.
Sai kiyi maza ki shirya ki fitu kici abinci.
Toh tace da ita.

Kallan dakin ta tsaya yi komai gwanin ban sha'awa sai kanshi dakin yakeyi.
Matsawa tayi jikin wani dan karamin pic na wata yarinya kamar balarabiyya tayi kyau sosai tun tana karama ne.
Amma tabbas in wannan ce Amal din tana da kyau.toh Amma Anty tace dani su a Nigeria suke kika kawar tace balarabiya anan garin.
Da wannan tunani ta shiga toilet danyin wanka.

πŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»πŸ”ΊπŸ”»
2pm tafito daga lecture. Ta gaji sosai amma dole sai taje asibiti dan taga Abban ta.
Wayar sakina ta kira nan ta gaya mata inda take.
Nan ta karasa.kuma dauko wayar tayi ta kira Anty Humairah.

Anty Humairah nata faman hadama bakinta launch. Taji karan wayarta.
Dauka tayi tareda murmushi tasan Amal ce.
Cwt mum cwt Anty.
Murmushi tayi tareda fadin my Amal ya test din.
Alhmdullh. Nasan de baki sun iso Ade mikamin gaisawa kafin na karaso pls.
Toh bbyna.
Kin tafi asibitin ne?
Eh yanxu zamu tafi nida Sakina sanna frnd din tawa danake baki lbr.itama zata je ta duba Abban.
Toh bbyna ki gaida Abban kinji saikun dawo we Miss u bye.
Bye itama tace tareda kashe wayar.

Kara sowa tayi tareda fadin Sakina mu huce ko.
Yawwa Amal kinsan harna kosa Wallahi..



Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹


Please Login or Register in order to submit comment