Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka nufa nan ma kaya masu kyau da tsada ya siyo mata,ta dauki takalma da cosmetic, komai intace tanaso baya hanata dauka.siyayya sosai yayi mata.harda kayan ciye ciye.
Lokacin da suka shigo cikin harbar gidan ana kiran sallar magrib.yana yin parking kai tsaye masallaci ya nufa.ita kuma kayan tashiga dauka tana kaiwa daki Har tagama ga baki daya.

Tun da motar su Amal tsaya,hjy ladi take lekensu ta window dakin ta,tana murmushin mugunta.
Sannan ta koma ciki.

Tana shiga daki toilet ta nufa ta dauro alwala,ta saka hijab dinta danyin sallah.
Bayan ta idar tayi addu'o'in ta,kayan gaba daya ta dauka dan ta nunawa hanne.
Dakin ta tura da sallama.sallah itama take amma bata idar ba,bakin gadan tasamu ta zauna dan jiranta.
Batadau lokaciba tayi sallama. Kallonta tayi fuskarta da murmushi. Amal ya kayin sauki,da sauki dama kinga kayan da Abbana ya siyomin.Aa tubara kalla kaya sunyi kyau.sosai ta tayata murna,sannan ta bata abunda ta siya mata.
Godiya tayi sosai dan taji dadi.sannan ta rakata suka kai kayan dakinta.fone enta da laptop danan ta Adana sauran kayan.
Kaya ta canja zuwa marasa nauyi.kitchen ta nufa dan yima musu abincin dare.


Lokacin da suka sauka anyi sallar magriba.dan haka kai tsaye suka mufi gidan su dake sharada. Suna sauka,Annur masallaci ya nufa danyin sallah. Ita kuwa hajiya gida tashiga.dakinta tanufa dan wanka kawai take bukatar yi,mutukar gajiya ta yi mata lilis.
Kayanta ta anje,tashiga toilet ta sakanma kanta ruwa.

Saida yayi sallar insha sannan ya shigo gidan.
A falo yasameta azaune tana kallon TV,amma hankalinta ba akan kallon yakeba.
Sallamar shike tamaidata daga tunanin da takeyi.dakinsa ya nufa dan yana mukatar yay wanka ya huta.
Annur! ,tsayawa yay cak tareda rufe idanunsa.
Dawo ka zauna nan inasan magana dakai.
Badan yaso ba ya dawo ya zauna tareda kallan TV.
Inasan kabani hankalinka nan,banasan kasaka damuwa akanka,saboda kwanannan zaka fara aiki.dan haka nemo nutsuwa agareka yaxama dole.
Batare daya kalletaba ya amsa.insha Allah Ummi. Saida safe kawai yace sannan ya mike ya shige dakinsa.
Toilet shima ya shiga saida yay wankan sannan yayi shirin bacci.
Wayar shi ya dauko dan kiran Uthman, saida yayi trying din num.sau uku sannan aka daga.
Ya ASA,har kakoma kanan kenan yanxu nake shirin kiranka ansauka lfy.
Lfy qlau. Amma kasan akwai babbar matsala kuwa.
Subhanallah! Mekuma ya faru?
Nan ya kwashe duk abunda yafaru ya gaya mai.sosai ya tausayama abokin nasa.kuma zaitayi masa addu'ar Neman sa'a.
Amma kasan menake so dakai kuwa.dan Allah gobe kaje gidan su Amal, kasamu wannan me gadin nasu,ka gayameshi kace Nina turoka,kanasan ganin Amal cikin sirri,inkasamu damar ganin ta saika kira ni pls bruh...
Ba komai insha Allah, Allah kaimu goban.ka gaida Ummi.ohk nyt.
Sanan ya kashe.idanunsa ya rufe tareda hurar da iska mai zafi.lallai akwai aiki agabansa.

Jallof in taliya ta dafa musu tasha kifi da kayan lanbo.kan dinning ta anje tareda komawa kitchen din tayi dan gyara gurin data bata.bayan ta gama duk abunda zatayi.Abban ta ne yashigo falon tareda sallama. Amsawa tayi.
Abba barka da dawowa.barka de yar Abba. Sannuda kokarin Allah yayimiki albarka .
Ameen Abbana. Ga abin cinan nagama kazo kaci nasan kana jin yinwa.yauwa mamana.kamarko kinsan nayi missing din girkinki.dariya tayi tareda gyaramai kujerar da yake zama,zama tayi tareda jin dadin yanda take nunamai kulawa sosai.
Zubamai tashiga yi suna dn taba hira.
Yawwa haka ya isheni zauna kema ki zuba kici kinji.toh abbana zama tayi kusa da kujerar sa,tazuba.haba mamana saikace wata yar tsana. Maxa ki kara karnayi fishi dake.wlh Abba na koshi,kamanta kaika cikamin cikina da kayan ciye ciye.
Dariya yayi toh naji,amma ki dunga cin abinci ko kyayi kumari.in sha Allah.

Hajiya ladi kuwa tunda taga Alh.sunfita da Amal ranta yayi mugun baci.dan tasan kudi zai je ya kaso mata.haka nan de,ta huce cikin gida,tana babbamin bala'i.hanne takira dan ta gyara mata dakinta.sannan ta huce garden ko taji dadi a ranta.
Tunanin plan din dazata hada dan cimma burinta,tabbas zata samu farin ciki na Har abada inde ta mallaki Annur...


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

65-70

Bayan Amal tagama cin abincin tare da Abban ta cike da farin ciki da nishadi sallama yayi mata yanufi dakinsa.
Ita kuwa abincin hanne ta diba ta nufi dakin ta dan ta kaima ta.
Kwance tasameta saman gado.tana ganin Amal ta shigo dauki da plate din abinci,mikewa tayi daga kishingidan da tayi,dama muguwar yinwa takeji.
Hanne ga abinci kici.
Ywwa Amal wlh kamar kinsan yinwar nakeji dan najima banci abinciba.
Murmushi tayi,ai gashi saikici ki koshi ki kwanta.mika mata tayi,nantasa spoon ta hau ci,tanaci suna dan taba hira,Har ta kammala.
Tare suka fito,Amal taimata saida safe ta nufi dakinta,ita kuma kitchen ta nufa dan maida kwano ta kuma sha ruwa.

8:00am
Amal tagama hada musu breakfast ta gera komai a dinning.
Daki tanufa dan yin wanka.

Zaune yake saman gadansa dan har yayi wanka yana binciki cikin laptop dinsa.amma hankali sa,yana can kan tunanin Amal. Dan gaba daya,so yake yaji muryar ta.
Wayar shi ya jawo dan kiran Uthman.
Har tagama ringing ba'a dagaba.yasan shima kansa yanxu bacci Uthman yake be tashiba.
Maida wayar yay ya ange,dan tabbas inya tashi yaga kiransa zai biyo kiran nasa.

Tunda safe hajiya Bilki ta tashi ta hadamusu breakfast.ta gaji sosai dan rabanta da girki ta jima.
Tana gamawa wanka tayi sannan ta dauki wayarta dan kiran wata mata ko zata samu yar aiki.
Kira daya biyu,ta dauka.
Sallama alaikoum hajiya antayi lafiya.
Lafiya lau talatu,dama yarinya nakeso kinsan ina gari,zata rinka yimin girki da sauran aikin gida inzan samu.
Eh! Zaki samu amma saide zuwa anjima insha Allah.
OK! Tam ba damuwa Allah kaimu anjiman.
Katsa wayar tayi,tanufi dakin Annur. Da sallama ta tura dakin.zaune ta gansa saman gado ga laptop agabansa ya dora waya saman cikinsa da earpiece a kunnan sa ya jingina a jikin pilo.da alama waka yakeji,idanunsa a rufe ko shigowarta bejiba.
Karasowa tayi Har gabansa,sannan ta dafashi.
Ahankali ya bude idanunsa yana kallon ummin tasa.zare earpiece din yake tare da mikewa zaune.
INA kwana ummina.
Katashi lfy son.
Lfylau.
Ywwa tashi muje kayi breakfast.
Ba musu ya mike tareda tartare kayansa zuwa wani side in.
Sannan ta mike yabi bayanta.
Dinning din tanufa yana biye da ita.zama yayi yana jiranta.nan danan ta shiga zuba masa.chips ne da kwai ,sai farfesun ragon ruwa,da tea.
Bayan ta gama zuba mai itama zubawa tayi.sannan ta zauna kujerar da take facing dinsa.
Sosai ya shiga cin abincin saida yaci ya koshi duk tana faman kallonsa.sannan ya mike dan barin gurin.
Bata tanka masaba,dakinsa ya nufa,be jimaba ya fito dauke da waya a hannunsa.
Key din mota ya dauka,tare da hanyar fita daga falon.
Sai kuma ina? Tafada batare da ta dubeshiba taci gaba dacin abincin ta.
Juyowa yayi sannan yace zan shiga garine,be jira cewar taba ya fita daga dakin.
Tanan zaune taji karan fitarshi da mota.


Tana fitowa daga wanka,kayanta tasanya,atamfa tasaka Riga da skirt, me red da yellow, sunyi mata kyau sosai kamar ba Mara lfyba.gashinta ta gyara,sannan ta daura dan kwalinta.tayi kyau sosai ta feshe jikinta da turare.
Tana fitowa daga falon.Abban ta tagani zaune yana amsa kira.
Zama tayi akusa da kafafunsa,tana jiran yagama wayar.bata jima da zamaba yayi sallama da Wanda suke kiran.
Mamana! Yakirata.
Naam Abba ina kwana.
Lafiya qlau kintashi lfy,ya krn saukin jikin.
Hmmm! Abba aina warke sosai.
Toh dama haka ake bukata.
Abbana nagama hada breakfast kataso muje kayi.ywwa yr albarka sannuda kokari.
Je ki kira mamanki,sai muyi breakfast din tare ko?
Toh Abba tanike ta nufi upstair. Dakin hjy.ladi tanufa.knocking kintayi sau biyu,sannan aka bata iznin shigowa.
Da sallama ta shiga tareda turkusa Har kasa tana gaidata.da mamakin ta tiji ta amsa cike da fara'arta.dago da kanta tayi dan tabbatarwa idanta,abunda kunnanta yajiye mata.
Murmushi ta sakar mata.sunkuyar dakan takumayi tana mamaki.
Amma!hjy dama angama hada breakfast shine nazo nagaya miki.
Toh Amal gani nan zuwa.
Ficewa tayi tareda janyo mata kofar.
Aa to meyasami hjy.kode tamanta nice Amal din da bata kiran Sunanta,saide shegiya,mayya,munafuka etc.amma yau harda yimin murmushi.
Da wannan tunanin ta karasa dining din.
Zamatayi dan jiranta.Abba da ya lurada ita tun saukowarta,shine yay kokarin cewa mamana lfy ko cewa tayi baxata zoba.
Murmushi dole ta nemo ,Aa gatanan abunda takuma cewa kenan.
Yana kokarin sake mgn,hjy.ta karaso cikeda tfyrta ta yanga tana faman rangwada.
Saida ta zauna sannan cikin kissa ta gaida Alh.ba yabo ba fallasa ya amsa.dan Har lokacin fishi yake da ita.
Amal ce mike dan yin serving insu.
Aa Amal banshi bara na yi,kede sanninki da kokari.daga Abban Har Amal in kawai kallon ta sukeyi.haka tayi served din kowa sannan itama ta zuba nata.sukahauci.kowa da abinda ke sakawa cikin ransa.hakade Har suka gama cin abinci.Abba ne yafara tashi dan yana da gurin zuwa.sai ka dawo sukace dashi.sannan hjy.dan itama tana da gurin zuwa.
Amal de duk ta tsargu da abinda hjyn takeyi.kwanukan ta kwashe tayi kitchen dasu.tana kokarin fitowa suka gamu da hanne.bayan sun gaisane,take gaya mata inda abincin ta yake.
Sannan tayi dakinta.fone dinta ta dauko tareda saka sim en da Abba ya bata.
Bayan ta kunna ne,tana ta faman dubata,dan tayi mata kyau sosai.

Yana gama shirinsa zai fita,ya dauko wayarsa ya kunna dan kiran Annur, missed call insa yagani,murmushi yayi tareda bin kiran nasa.
Daga can bangarenne Annur yace,ina kashige inata faman ke ranka shiru.
Wlh km kaima kasan ban mantaba Angon Amal yafada cike da xolaya.dariyar jin ddin sunanda Uthman ya kirayeshi dashi yake.
Yauwa guy Ade taimaka.
Ba damuwa yanxu mum ce ta aikeni amma ina dawowa zan je .ohk sai munyi waya.OK ba damuwa ya katse kiran.

Shikuwa Annur can cikin gari ya nufa dan baya jin dadin zaman gidan.

4:45pm
Uthman yayi parking din motarsa can nesa da gidan su Amal kadan.sannan ya fito ya nufi gidan kai tsaye.
Tura kofar yayi tareda sallama. Gurin zama Baba me gadi ya basa.tareda amsa sallamar.bayan sun gaisane.
Yake sheda masa sakon Annur, yakuma fito da kudi ya bashi dan duk ya ji ddin kira masa ita.dadi yaji sosai dan yana San Annur shima.
Mikewa yayi yanufi cikin gidan.
Sallama ya shiga yi,yayi sa'a kuwa Amal dince ta amsa,tareda fitowa,sanye take da hijab dinta.
Aa Baba ne ina yini ya aiki.lfy lau.
Sannan ya sanar mata da sakon Uthman. Cike da mamaki tace nikuma.tabbas fa.toh Baba kace gani nan zuwa.
Cikin gidan ta koma tana sake sake aranta

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

70-75

Lokacin data fito bata hanyar gate din ta nufa,ga mamakinta ba kowa sai baba me gadi.
Aa Baba ina bakwan nawa tafa tana dube dube.
Yawwa gashi can waje cikin mota,yace kisameshi can gudun kr Abban ki,ya gnku tsaye nan.
Ba musu ta bude kofar gate din,tahau dube dube ta hanyar dazata hangoshi.can nesa da gidan su.
Hanyar tabi hata cimma motar inda ta motar take.yana cike,ya bude kofar ya zuro kafarsa guda.yana jin waka.
Cikin sallama ta isa wajan,da fara'arsa ya amsa mata.sannan ya mata ya jikin.
Itama amsamai tayi.tare da tabayr mum.
Mum na lafiya tace tana gaida ke kuma yaushe zaki kawo mata ziyara?
Inde Abba ya barni insha Allah zanxo.toh Allah kawoki Amal yn mata.dariya ta danyi tari da boye furkarta cikin hijab.
Ywwa inba damuwa ki shigo ki zauna dan inasan magana dake kuma be kamata ki tsaya hakaba ko.
Ba musu ta zagaya ta shiga dayan side din.bayan ta shigone ta zauna.yake gaya mata cewan Annur ne ya aikoshi koma yace inkin samu damar fitowa a hadaku a waya,ba damuwa na kirashi.
Itama kanta sai taji tanasan jin muryar Annur din.kai ta daga mishi.
Nan take yakira shi,yana dauka yace,toh gani ga Amal de,cike da murna Annur yace ywwa bro bata mana mika mata wayar yayi tareda cewa bara nabaku waje.sannan ya fita.
Tsawan lokaci bawanda yace da kowa komai.sainda shirun yayi yawa,sannan tayi karfin halin yin sallama.
Lumshe idanun sa yayi sakamakon jin muryar ta da yayi,sai yaji kamar an wankemai duk wata damuwa dake cikin zuciyar shi.
Shima amsa sallamar yayi.
Amaaal! Yakira sunan sa da wata irin murya meban tausayi.nasan bakya sona ko Amal?
Shiru tayi idanunta a rufe.nasani Amal ni kadai nake wahala akanki,amma dan Allah ki tausayamin kinji!
Wallahi kin kasance wani bangare a jikin tun lokacin Dana fara jin muryarki.
Har lokacin kasa bude idanunta tayi kamar akusa da ita yake maganar.
Na kasance ina me fegenki dare da rana Amal! Inaji ajiki komin daran dadewa bazan iya dena tunaninkiba. Amal pls ki tausayamin zan iya rasa komai arayuwata in bana tare dake.
Amal kice wani Abu dan Allah, kice kina sona ko zanji sanyi a raina.
Tunda ya fara maganar ya katse mata komai,jikinta yayi mugun sanyi,gaba daya tausayinsa da kaunarsa ya tsarga mata zuciyarta.
Amma tabbas tasan koda zata mutu Abba baze taba aura mata shiba,tasan halin Abban ta sarai.kanme zata yaudari zuciyarta ta amince da soyayyarsa karshe ta kamu da ciwon zuciya ta mutu.
Amal dan Allah kiyi magana ko zanji sanyi a taina.wani irin kukane ya kwace mata.yarda wayar tayi tareda fita daga motar da gudu tayi hanyar gida.
Uthman dake zaune saman wani dakali,ya mike yana kwalla mata kira,amma ina harta shige gida.
Cikin sauri ya shiga motar,wayar ya gani yashe saman kujera.dauka yayi tareda karawa a kunan sa.
Annur lfy?
Annur da hawaye kibin kuncinsa ya kasa magana.haba Annur wallahi kana bani mamaki,sai kace ba namiji ka rinka dauriya mana.
Uthman inasan Amal wallahi inji ajikina San Amal zai iya kasheni.
Ya isa haka naji pls.sai munyi waya.kashe wayarsa yayi tareda shigewa motar sa yayi gida.

Jingina yayi da kujerar motarsa,tabbas so wani babban al'amarine mu samma ga Wanda be taba yiba.
Yanasan Amal amma besan yanda zaiyi ya shawo kan matsalr iyayensu.wata iska ya hurar me zafi,tabbas inde beyi da gaske ba,ba makawo zai kamu da ciwon zuciya.
Wayar shice tayi kara,da kamar baze dauka ba,sai kuma ya dauka.umminshi ce.karawa yayi a kunne tare dayin sallama.
Annur kana inane,?
Ina cikin gari ummina lafy.
Kadawo gida inasan ganinka.ohk gani nan kan hanya.
Motar yyma key yanufi hanyar gida.

Da gudu ta shige gidan,dakinta tanufa ta fada kan gado tareda fashewa da wani saban kukan.tabbas baxata yima zuciyarta karya ba tana son Annur. Amma ya hakan ya faru,taya tabari San Annur ya shiga zuciyarta.taya haka ya faru,wani saban kukan tashiga rerawa,saida tayi mai isarta sannan ta mike dan gabatar da sallah magrib.


Yana shiga gate din gidan yayi park en motar.alwala yayi a nan,ya huce masallaci.
Bayan ya dawo ne,ya shigo gidan da sallama baiga umminshi a falon ba,kai tsaye dakin ya nufa.da yashiga karar tuwa yaji a toilet, saiya jawo dakin ya dawo falo.
Kan kujera ya zauna yana kallon film din da akeyi.amma azahiri ba kallon yakeba tunanin mafita yake yanda zai shawo kan matsalar iyayensu.
Ya jima nan kafin ummin ta fito.nan kan kujera itama ta zauna tana kallo sa.
Yanxu Annur tun safe kabar gidanan amma sainace kadwo sanan zaka dawo?
Haba ummina kinsan ai bazan kwana a titiba,na Dade banyi yawa a garinnan ba shiya sanya na fita ganin gare kuma nadnje wajan frnds ina.
Toh yayi! Dama company da nake nemama aeki sun dauke ka on Monday zaka fara aiki,saika zauna cikin kari.ya nuna murna sosai kuma yakuma kara godema Allah da Ummin tashi.
Yanxu katashi kaje kaci abincin ka mana.
Aa ummina a koshe nake.toh ai shikenan.
Kallon suka cigaba dayi kuma suna dan taba hira jefi jefi.Har aka kira insha,ya mike dan tafiya masallaci.


Bayan ta idar da salln magrib din kitchen ta nufa dan hada musu dinner. Amma kana ganin ta kamar maras lafiya.haka tayi musu girkin ta gama jikinta duk baya mata ddi.
Ana kiran insha lokacin ta gama hada musu komai,bayan ta gama jerawa saman dining. Daki tanufa dan yin sallah.sannan tadan shingida kafin Abban ta yadawo......

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

Bata jima da kwan ciyaba Abban ya dawo.
Kai tsaye dakinsa ya huce dan watsa ruwa ajikinsa yaji sanyi.bayan ya gama duk abun da zaiye.
Falon ya sauko amma ba kowa,wayar shi ya Ciro dan kiran ta.
Tana nan kwance kan abun sallar da Har bancinta ya bara nauyi,
Karan da wayar tata ke famanyi ne ya tasheta.ga mamaki ta dauko dantasn batasa num.din kowa cikin wayarsa.Abbana taga ansa.murmushi tayi tasan shine yasa num.din tasa yayi mata saving.
Da sallama ta daga,tareda gaisheshi da yimai sannu da zuwa.Amal abbanki na falor yinwa zata zautashi a taimaka mai da abinci.
Dariya tayi tare da cewa toh gani nan.
Cikin murmushi ta fito daga dakin.zaune ta sameshi a daya daga cikin kujerun dinning din.Aa lallai Abba yinwa kk ji harka karaso nan din.shima dariyan yayi.
Yinwa nakeji Amal a taimaka.
Zuwa tayidanta zuba masa abinci sai bayan sunci sun koshi. Sannan ta mike ta tattara kwanikan.
Ywwa Abbana tunda yanxu kaci ka koshi naje na dauko laptop dina kanan koyamin kayimin settings in wasu abubuwan.
Toh jeki dauko yr Abba.
Mikewa tayi tadauko laptop din kasa suka zauna yana ta faman gyara mata tana gani.
Ga games kala kala.sosai taji dadi koba komai zasuna abe mata kewa.
Nan suka zauna sunata hira da raha.yanata bata labarai kala kala.tana ta faman dariya.
Hjy ladi ce ta iskesu zaune sunata faman dariya.nan ta nemi guri ta zauna tana kalansu,barkanku da hutawa.ywwa Abba yace da ita.
Hjy ga abincinki can kan dinning.aww! Ku harkunci kenan Wlh nima bccine ya daukeni.bara naje naci,bade wanda yace da ita komai ta mike ta nufi dinning in.
Nan suka cigaba da abunda sukeyi,sosai Amal ta gane duk abunda Abban ke koya mata cike da farinci...

Annur ne kwance saman gadan sa,yana kokarin kiran Uthman din.
Uthman dinne ya kirasa.
Ya yanxu nima nake kokarin kiranka,ywwa ya kaje gida.lafiya qlau.
Ywwa pls Uthman ya za'ai maganar Amal so nake ka kuma komawa wajanta.ka kaimata waya kaga kaima ba sai kana shan wahalar zuwaba kagane.
Kaga Annur gaskiya ba inda zani,haka ake yarinya kawai ta tafi ta barni ko sallama babu koma ina kiranta ta yimin banza.
Pls frnd karka min haka mana,kasan yanda nakesan yarinyar be kamata kana min irin wannan ba.pls ka taimaka.ni ummice matsalata amma da goben zan shig jigawan.
Kaga nasan dama ta zautaka! Zani basai kaxoba kasan halin Ummi karka jama kanka wata matsalar.goban zan shiga insha Allah.
Ywwa frnd na gode,ohk nyt ka gaida ummin.sannan sukayi sallama.


Monday mrng 7:00am.

Annur ne yafito cikin shirin dinsa na office yayi mutukar kyau.sanye yake cikin black suet, ta amsheshi sosai.rataye da briefcase dan hucewa gurin aiki.
Dining ya nufa danyin breakfast.Har gama amma umminshi bata fitoba.yasan bacci take dan haka dakinta yanufa kai tsaye saida yayi knocking sai uku amma shiru ana hudunne aka bashi iznin shiga dakin.
Zaune ya ganta saman gado ta shigida da pilo a bayanta,ta rufe rabin jikinta da blanket.
Kusa da ita ya zauna,cikin sakin fuska ya gaidata.amsa mai tayi tareda fadin harka gama shiryawa sai tafiya,eh Ummi .
Ywwa dan albarka kadeyi breakfast dinka ko, dan bansan kana tafiya da yinwa,shiyasa na samo mana kuku.
Ohk! Nide zan huce saina dawo.
Adawo lfy Allah badan sa'a.
Ameen yace da ita tare da kullo mata kofar.
Parking side ya nufa tare da shiga car din dazai fita da ita,key yayi mata nan me gadi ya bude masa gate.hancin motar ya tura waje bayan sun gaisa da me gadi.
Office ya nufa cikin kwanciyar hankali.ahankali yake driving din yar ya isa enterprises din su.nan yay parking din motar sa inda aka tanada dan hakan.bayan ya fito tareda rufe motan ciki ya nufa inde naga an rubuta da manyan baki a saman building fin.AREWA ENTERPRISE NG.LTD.
Nan yashiga da yake kansan da zuwansa nan mutane suka fara tarbarsa cikin kulawa da yake shine saban manager en su.shima cike da farin ciki da sakin fuska yake amsawa Har office dinsa suka rakashe sannan kowa ya watse.
Bayan kamar minti biyar da faruwar hakan,sakatariyarsa ta shigo dan bashi duk wasu documents daya kamata ta bashi ta kuma sauran bayanan da zatayi masa.
Da sallama tashigo office din bayan ta dauki permission din shugowar.zaune yake kan kujera yana duba wasu files daya tarar agurin.batare da ya kalletaba ya amsa mata sallamar da tayi.
Gud mrng sir!
Tafada cikin muryar yanga da yayi bala'in burgeta.
Mrng yafada tareda nuna mata gurin zama.
Zama tayi tareda cewa tnkuuu sir.my name is Fareeda Mahammad nice sakatariyar ka.nakawoma duk wasu documents da sauran files da yakamata na baka.
OK tnkuuu fareeda nagode.sannan ta hau yimasa bayanan komai dalla dallah,harta gama sannan yayi mata godiya.
Bayan ta fitane,ya janyo files din yahau dubawa.
Aiki sosai yashiga yi yanda ya kamata.
Har lokacin sallah yayi sannan ya fita dan yin sallah da cin abinci.


Yau Abban Amal bai fitaba dan haka tun safiyar yau suna tare,saida lokacin sallah yayi sannan ya fita masallaci.itama dakin ta tafi danyin sallah.

A masallacinne dayaje sallah suka hadu da wani saurayi shima anan yake aiki Har sukayi musayar num.da Annur din bayan kowa ya sanar da kowa sunan sa.
Abokin nasa mai suna kabeer ne,yajashi Har zuwa wani restaurant nan kusa dasu sukaci suka koshi sunata faman hira Har suka gama.kabeer din ne yabiya kudin baki daya sannan suka fito.


Lokacin da Abba ya dawo daga masallaci be tarda Amal a falon ba,dan haka key dinsa ya dauka dan yanasan fita cikin gari.
Bayan ya fitane,bada jimawaba Amal din ta fito rike da fone dinta tanufi dakin hanne dan Sudan taba hira dan taji karan fitar Abbana.

Hjy ladi ce ke saukowa daga kan steps cikin yanga harta gama saikowa,dakin Amal in ta shiga amma batanan kwala mata kira tashiga yi.

Amal dake kwance kan gadon hanne tana nunawa hanne pics din da sukayi itada Abban ta sunyi kyau sosai ko wanne sunyi murmushi.
Hanne ce ta dubi Amal. Anya kuwa ba kiranka akeba naji kamar ana kiranki ko bakijiba.
Saurarawa itama tayi sannan sukaji muryar hjyn.
Da Sauri ta fito Har tana kokarin faduwa dan Sauri.a tsakiyar bafo ta taradda da ita. Tsugunnawa tayi Har kasa ta gaidata kanta a kasa.
Ywwa dan Allah yau mezaki dafama Abban naki.dago da kanta tayi tareda gyara hannun rigarta.
Tuwan alkama da miyan danyan kubewa.
OK! Pls macaroni Nikum nakeso ko hanne sai kisa ta tayaki dan Ku gama da huri banajin dadin jikina kinji.
Ba komai Allah ya sauwake.nagode zaki zaki iya tafiya.
Mikewa tayi tana taba baki ta nufi dakin hanne.
Hmmmm! Yarinya ke nan Har wani wasa da dariya kuke yima mutane kida wannan banxan uban naki.toh yau zanga karahen iskanci.dariya takumayi tare da juyawa ta bi hanyar upstairs.....

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

80-85

Dakin hanne ta tura ta shiga,bakin gadan ta koma ta zauna.
Hanne nikuwa kin san wani abu,wlh gani nayi hjy duk ta canza anya ba wani abun bane kuwa.
Lallai Amal kema saukace yau kuka fara rayuwa da hjyr.wata kila dan taga Abban ki gida shiya sanya take sassauta maki wani abun.
Toh koma menene Allah ya kyauta.amma cewa tayimin wai batajin ddi,na girka mata abincin ta daban ba batare Dana gidaba.
Toh! Sai kiyi matan saiki muyi tare na tayaki,nan suka cigaba da hira.....

5:50pm
Shine lokacin da Uthman yay parking kofar gidan su Amal. Gaisawa sukayi da Me gadi sannan yakuma rokonsa daya kira masa Amal din.
Babu matsala dan Alh. Ya kusan dawo wa.
Babu matsala insha Allah, dan ba jimawa zanba sako kawai zan bata,
Toh shikenan bara inkira maka ita.
Be wani dau lokaci ba yadawo tareda ce masa gata nan zuwa.
Komawa ciki yayi ya zauna.
Ba dau lokaci ba tafito daga cikin gidan dan itama tabbas tana missing din Annur ba karya.
Sallam tayi mai tareda gaida shi.
Beyi mata maganar jiyaba dan sauri yake be dadi da tasowa daga office ba.
Ywwa Annur ne yace akawo miki waya dan kuna gaisawa.
Shiru tayi nadan lokaci ,sanan tace Abba ya saimin waya daya dawo,saide kabani number din shi danni ban rike tawaba.
Ohk! Ba damuwa.pen ya dauko da memo karami ,nan ya saka mata numb.Annur din sannan ya mika mata.
Nan tayi masa godiya tareda cewa ya gaida mata mum.bata gama gaya masa ba.motar Abba ta riske su.
Rasa abin bafa tayi dan gaba daya ta tsorata.dan batayi tsammanin ganin sa a wannan Lokacin ba.
Uthman ne ya gaidashi cike da fara'a ya amsa masa sannan ya ja motarsa yabar kofar gidan.
Nan Amal itama ta shige gidan jikinta a sanyaye duk da taga yanayin furkar Abban nata ba ta nuna damuwar hakanba.
Abanne ya shigo da motarsa cikin gidan sannan ya huce masallaci.

6:00pm.
Shine time en da Annur ke tashi daga office.
Kai tsaye gida ya nufa dan yayi mutukar gajiya.
Badau lokaci ba ya iso gidan parking yayi dan Har anfara sallah. Haka ya daure ya nufi masallaci dan bayasan jam'i ya huce shi.
Sai bayan idar da sallah ya cikin gida be tarda ummin sa a falon ba.dakin sa ya nufa da watsa ruwa.
Yana shiga ya tube kayansa ya daura towel sannan ya shiga wankan.
Be jimaba ya fito bayan ya gama shafe shafan da zaiyi.
Ya sanya brown din wando 3quarter da White T.shirt.sannan ya fito falo dan cin abinci.
Zaune yaganta tana jiransa dan suci abincin tare.
Zama yayi kusa da

Please Login or Register in order to submit comment