Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

miki.
Toh meye aciki iya kaci kace kasakeni saime kaikadaine namiji,zance kasan kowace ladi! ,dan haka wlh baxaka takuraniba.
Upstairs ta haye warta,batare da takara kallon inda yake ba.
Gaba daya kansa ya daure,tabbas yasan Amal baxata taba yin abunda aka fadaba.yanxu ina ma zai fara Neman ta,yasan duk inda take tana cikin tashin hankali.
Dakin hanne ya nufa dan yasan zata san inda Amal in take.

Hanne da tun tafiyar Amal bata cikin jin dadi.kofar dakinta taji ana bugawa.mikewa tayi ,ta bude dakin.ganin Alh. Tsaye bakin kofa yasanyata saurin risisnawa tana gaidashi.bayan ya amsa mata.
Yace dan Allh hanne kinsan inda Amal dita take?
Har saida kwallah ta zubo mata ,tagayamai duk abunda ya faru.mamaki yashiga yi,waye wannan da zai shigo har cikin gidanshi ya marar mai iyalinsa.
Cikin fishi shima ya nufi hanyar upstairs in.
Kwance ya sameta saman gado.Jamila yani dan iskane yashigomai gida hada dukan mai iyali.
Gabanta ne ya fadi.ba magana nake mikiba.
Dama dan gidan hajiya bilkine,yauwa kice biri yayi kama da mutun ban rabaki da wannan yr iskar matarba harxaki jahomin danta cikin gidana,kice kawai kun hadashi da yata yatafi da ita ko?
Wallahi aa dama bata da lfyne shine ya kaita asibiti kuma aka kwantar da ita.
Wani asibiti ne? Ji tayi kamar tayi fitsari a Wanda.
Wallahi nima ban saniba.hmmm! Jamila ni zaki maida karamin yaro,wlh duk abunda ya sami yata court ce zata rabani daku.
Be kuma cewa komai ba yabar dakin.
Hankalinta atashe tashiga Neman layin hjy.bilki harta gama ringing ba'a dagaba,sake kiranta tayi,wannan karanne ta dauka.
Wlh hjy Annur zai jawo mana bala'i,kinga Abban amal ya dawo,gashi sai fada yake harda court ce zata rabamu dashi.
Dallahcan rufemun baki kina babbar mace amma baki iyada gidan kiba,Har namiji ya zauna yana gaya miki magan,gobe zan shigo kasar.zansan yadda zamuyi.shikuma Annur wlh ko zai mutu wallahi bazai aure Amal ba.kashe wayar tayi.hjy ladi taji dadin hakan dan tasan kawar ba wasa..

Bayan su hajiya suntafine aka kawo musu abinci.shikuwa Annur ko kadan bayajin zai iya saka wani Abu acikin sa.
Har Amal ta farka amma be saniba yana can yana faman tunani.
Kallan shi ta tsaya yi cike da tausayinsa.sai yanxu ta gane ba halinsa daya da Babar saba.

WANE NE ANNUR?.......

Written by zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

45-50

I dedicated dis page to ma sistoo Maryam Naseer nd sis fareederh.Lov u to d Moon nd bck.Allah ja daranku ameen๐Ÿ‘„๐ŸŒน๐Ÿ˜˜


WANE NE ANNUR?

Asalin sunan sa shine Annur Shu'aeb Abubakar. Mahaifinsa dan garin jigawa ne,mahaifiyar sa kuma yr kano ce.sunan mahaifiyar sa hjy.Bilki.sunyi auran soyayya ita da me gidanta Shu'aeb.
Shide bawani me kudi bane amma yana da rufin asiri.
Shekarar su uku da aure amma ko batan wata bata taba yiba.shikuwa Alh. Shu'aeb yana da mutukar San yara.hakanne yasanyashi karin aure.ya auri wata mata mai suna Hauwa.hayan Hauwa taxo ba dadewa,hjy.Bilki ta samu ciki,murna wajan Alh. Ba'a cewa komai.
Amma ita hjy.bilki ta dauki kishin duniya ta Dora kan Hauwa.duk da hauwan batajin ddin abunda take yimata,kasancewa mace ce me hakuri bata nunawa.
Har Allah ya sauki hjy.bilki lafiya,ranar suna data yaci suna Annur.
Sosai yasamu kulawa wajan iyayen sa,da Hauwa na kaunarsa kuma tana San tarinka daukarsa,amma fir hjy.bilki bata bari ko kofar dakinta yaje.inde ba babansa bane yaje dashi.
Har Annur yafara tafiya amma Hauwa ko bantan wata bata taba yiba.hakan na mutakar tayar mata da hankali.amma ta fauwalawa Allah lamuranta.

Bayan shekara 10 da haihuwar Annur tun daga lokacin haihuwa ta tsaya a gidan Alh.Shu'aeb. Saiya ci gaba da godewa Allah daya bashi tillon dansa,tamkar dubu.dan yaran ataso cikin gata da kulawa,gashi da kokari makarta.haka kuma duk lokacin dabai gane wani abunba yakanje gurin antynsa Hauwa ta koyamai.
Saboda ita hjy.bilki bata yawan zaman gidan kullum tana yawan kasuwancinta.na kayayyakin sawa Dana amfanin gida.
Shiyasa Annur yafi sabawa da Hauwa.
Haka rayuwa taci gaba cikin gidan Alh.Shu'aeb.

Wata ranar laraba da misalin karfe 6:15pm,Alh.sunje kano ziyara shida matansa da dansa,suna kan hanyar dawo warsu zuwa kafuna.sukayi hatsari.nan take Alh.Shu'aeb Allah ya mai rasuwa.ita kuwa Hauwa abun sai Wanda yagani,dan ko numfashi da kr take iyawa.Annur kuwa karaya biyu yayi a kafar sa.amma hjy.bilki da ikon Allah ko ciwo batajiba.
Haka aka dauke gawar Alh.Shu'aeb akayi masa jana'iza.
Nan aka dauki Annur da Hauwa akayi asibiti dasu.
Bayan kwana uku da rasuwar Alh.Shu'aeb. Allah yayima Hauwa rasuwa.sosai Annur yaji mutuwar iyayensa guda biyu.ita kuwa hjy.bilki ko a jikinta dan gani take dabarar tace tasa bata ji ko kwarxane ba a accident in da sukayi.
Haka akaci gaba da zaman makwaki Har aka gama.

Bayan anyi sadakar 40 ,lokacin Annur ya samu sauke sosai dan haryama koma makaranta.
Dama anriga da abbata gadansu.nan ta xubasu cikin business inta.hankali kwance takuma bunkasa.
Lokacin da Annur yakai zai shiga jss1,sai hjy.bilki ta kaisa boarding sch.dan aganinta zatafi samun kwanciyar hankali.tunda so take tafara fita kasashan waje tana gama takaba.

Akwana atashi ba huya gurin Allah yau ne Annur yayi graduate a makarantar su.yanxu kuwa hajiya bilki tazama babbar antajira.dan tabar garin jigawa gaba daya ta koma,kano ta gina tanka memen gidan ta.
Business take sosai kasashe ba inda bata zuwa.takuma gogewa tayi kyau tana samun kudi sosai.

Bayan Annur yagama secondary sch.dinsa sai hjy.bilki ta turasa London dan cigavan karatunsa.
Tun bayan tafiyarsa London hankali ta,takuma kwanciya,sosai tana kula dashi dan komai yakeso tana yimasa shi.kuma lokaci lokaci tana kaimai ziyara.dan tana mutukar kaunar sa kuma shima yana mata biyayya sosai.

Annur yasataso cikin gata da kuma kulawa gurin mahaifiyar sa,amma duk da hakan besa ya lalaceba,shi ko mata basa birgeshi bare shaye shaye.Yakama karatunsa sosai na Art and design. Gashi yana da kokari shiyasa yake da farin jini a makarntar.kowa kaji suna kiransa young ASA. Bashi da buri arayuwar sa da yahuce ya gama karatunsa ya zama babban Artist. Shiyasa ya maida hankali akan abunda yasa gaba.

Hajiya bilki kuwa an kama kasa.kullum cikin shiga ta alfarma ta zama kamar wata budurwa sai cin duniyarta take da tsinke.
A yawanta na fita abroad, tagamu da hjy ladi a Dubai. Hjy ladi cikakkeyar yr duniyace,ita sana arta shine Neman maxa,da kuma business din kaya.tunda take bata taba aureba.kullum suna yawan gantali,shiyasa ta tara abun duniya.sosai.gidan ta yananan a garin jigawa amma iyayenta yn yobe state ne.
Nan suka kulla alaka da hajiya bilki, taxama aminiyarta sosai harta dorata akan harkar banxan da takeyi.sosai hajiya Bilki taji dadin hakan dan arxiki yaci uban Nada.

Wata rana taje Dubai ta hadu da wani mai kudi Alh.muktar ta aureshi.amma tamai karyar ita baxawara ce,mijinta ya mutu.haka ya yarda ,akasha biki sosai danshi Allah ya sakamai San hajiya ladi wato Jamila. Amma da sharadin zataci gaba da business inta,haka ya yarda,nanfa tasamu damar cigaba da iskancinta a boye.

Bayan shekara 4 .
Yaune Annur yagama kara tunsa gabaki daya.dan haka yana cike da tsananin murna.sunyi shagali sosai a sch dnsu.
Haka umminsa ta shiryamai party hadadde anan London din dan tayashi murna.naira tayi kuka ranar.tun daga ranar yagane umminshi ta canxa,tana tareda Mayan mata da maxa wanda basu dace da itaba.ya yi bakin ciki sosai amma ba yanda ya iya.haka kuma yasamu kaututtuka sosai daga mutane.dan Har wani company sunce suna San aiki dashi duk lokacin daya shirya.

Bayan wasu yn kwanaki da gama karatunsa.yaune ranar da,sukayi da umminshi zai dawo gida,saide ta gaya masa,bata kasar.ya zauna gidan hajiya ladi kawar ta....

Muje zuwa!๐Ÿ˜œ

Written by zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

50-55

AN DAWO LABARI!

Ajikinshine yaji tabbas ana kallonsa,a hankali ya dago suka hada ido dashi,kasa dauke kanta tayi,taci gaba da kallan sa batasan lokaci da ta sakar masa murmushi ba,shima tsintar kansa yayi cikin yi mata murmushi.
Zamansa ya gyara ya kirayi sunan ta! Bata amsa masaba illa cigaba da kallan sa da tayi.
Amal yanxu babu inda yake miki ciwo,daga kanta tayi a hankali tace babu.toh Allah ya baki lfy,ameen tace tare da juya kanta dayan bangaran.
Tabbas Annur yana da tausayi kuma mutumin kirkine.
Abbntane yafado mata aranta,ko mezaice idan yadawo bata gida,kallace ta zubo mata,lallai tasan hjy.ladi zata iya bata mata suna a wajansa.Allah ka taimakeni,abunda ta furta kenan.
Amal kuka keki,juyo da kanta tayi side din da yake.kallon fuskarta da yayi hawaye na bin kuncinta.hakanne yasa shi rashin jin dadi.
Haba Amal kinsan baki da ki kakkiyar lfy amma kike sa damuwa a ranki,kinsan ko wani mutum yana da kandararsa.kuma mumine anasan a yanda da kandarar data sameshi mekyau ko marar kyau.
Kiyi hakuri kidena damun kanki.kinji insha Allah bayan huya sai dadi.
Taji dadi sosai da kalamansa.kuma tana dada godiya ga Allah daya barta da ranta.
Yanxu kitashi kici abinci sannan kisha magani.
Mikewa tayi ahankali, toilet ta shiga bata jimaba ta dawo ta zauna.
Kallan ta yayi,kafin yace na hada miki tea kisha.kai ta gyada mai,da kanshe ya hada tea en,ya mika mata,sannan ya xubo mata ruwan semo miyna danyar kubewa Tasha kifi daman shanu.shima din mika mata yayi.
Tea in tafara shanyewa gaba daya.sannan ta shiga cin tuwon ahankali Har ta cikinye gaba daya.
Ita kanta tayi mamaki dan rabanta da cin abinci ta koshi harta manta.
Shima mamakin yadda ta cinye yake.kawo a kara miki.Aa nakoshi,mikewa tayi taje toilet ta wanke hannuwanta.sannan ta dawo.
Magani ya mika mata,anshi ki shanye sai kikuma jin dadin jikin naki.ba musu ta hadiye maganin tare da korawa da ruwa.mikamai ruwan tayi.ta juya zata kwanta.
Aa kibari abincin ya gama bin jikinki,ni zantafi sai gobe da safe zan dawo.kina bukatar wani abunne.aa bana San komai nagode.
Shikenan banasan godiynki Allah zaki godewa tunda shiya hadamu dake.tattara kayan yayi,sannan ya zaro waya daga cikin aljihunsa, gashi inkina bukatar wani abun ki kara num.in ciki ita kadaice aciki kinji.
Toh kawai tace.saida safe yace tareda jamata kofar.
Juyawa tayi tana mamakin irin kulawa ta wannan bawan Allah. Tabbas ya cancanci ko wata irin sakayya ta alkhari daga agereta.amma magana ta gaskiya baxata taba iya hada jini da hajiya bilki ba.koda kuwa Annur zai mutu itama zata mutu akan San juna.da wannan tunani aranta bacci ya dauke ta.

Hajiya bilki da zuciyar ta kifaman tafasa burinta shine taganta a gida Nigeria. Abun bakin ciki shine tun daxo take kiran num.Annur amma gaba daya yaki dagawa.lallai tana da aiki a gabanta.
Dandanan tayi Bucking din jirgin safe,gobe insha Allah 10:00am nasafe tana gida.da kr ta samu bcci ya dauke ta.

Shima Abban Amal kasa baccin yayi burinshi Allah ya hadashi da wannan tsinannan yaran daya daukar masa yrsa.
Wani hawayen bakin cikine suka zubomai.mudun aka lalata rayuwar yrsa saiya dau munmunan bataki.Abbunda yake ta gudu yau gashi ya faru.wannan wani irin bakin cikine,Allah ya tsinema hajiya ladi.gashi yarasa meyasa baya iya musu da ita,baze iya sakin taba.

Shima haka ta kasance ga Annur din,dan kokadan wani Abu me suna bacci ya kaurace a idonsa.wallahi koda za'a kashe shi baze iya rayuwa babu Amal ba.lokaci daya Allah ya jarabceshi da Santa.
Bandaki yatshi ya shiga,alwala ya dauro,ya shiga yin nafilla yana kaima Allah kukansa.


10:00am๐Ÿ•™
Shine lokacinda mum,Uthman da Annur suka iso asibiti dauke da kayan breakfast.room din da aka kwantar da Amal suka nufa.zaune take akan gado tayi wankanta tayi kyau kamar ba itaba harta danyi kumari.turo dakin sukayi da sallama. Cike da jin dadin ganinsu ta amsa musu.mumce ta zauna kusa da ita tana kallonta, kaga patient ae ta warware Allah kara sauki.
Sunkuwar dakai tayi cikeda kunya,tana gaidada mum din.
Lfylau jikin Amal?
Da sauke,Allah kara sauke.sannan ta gaida Annur da Uthman suma duk cikin fara'a suka amsa.
Abincin suka shiga zuba mata.sannan mum ta mika mata.
Wainar masa ce,da miyan ganye tasha kayan cikin ragu sai kamshi take.ga kuma kunun gyada me kauri.
Ahankali tashiga cin abincin, tana San kunun harta ci ta koshi.
Kofar akayi knocking, sannan aka shigo,wannan likitanci mai kirki.bayan sun gaisa dasu mum.sannan taima Amal ya jiki.
Duba Amal din tashiga yi,Alhmdullh jiki yayi kyau ta fada,zaku iya tafiyama yau,Allah kara sauki.ameen suka amsa.harxata fita tajuyo tace yawwa sunana Dr.Fatima Ibrahim labaran.amma anfi saninada Dr.shaheeda.hannu ta zira ta dauko musu card dinta a aljihunsa rigarta.gashinan full address in gidanane da kuma num.koda zaku nemeni nagode.tajuya ta fita.
Sunji dadi sosai da karamcin da tayi musu.sosai matar tashiga ran Amal. Har tanajin dama su kasance tare.mum ce ta yimata mgn ta dawo daga tunanin da take.kitashi ki muje mu saukeki a gida.ba musu ta mike ta sanya hijab inta.kwaso kwanikan da duk abubuwanta akayi suka fito dan tafiya gida.

Gaba daya tunda garin Allah ya waye Annur baya jin ddin jikinsa,dan yaune ranar da zai rabu da mafi soyuwa agareshi.tabbas koda yabi umarni umminshi, saiya dawo ga Amal insa.

Zaune yake a daya daga cikin kujerun falon.dan yana tunani irin na sakacin da yayi nakin tafiya da Amal dinsa.maganganun hjy ladi yake tunuwa lokacin da ya nuna,zai tafi da Amal en China.
(Haba Alh. Danni ban haifaba,kabarta mana agurina,tudda nima kamar uwa take agurina,zan kula da ita,kuma zatana debemin kewa)
Wani bakin cikine yakuma ziyartar zuciyarsa.tabbas baxai kara barintaba.dama gata ba cikakkiyar lfy ba.

A daidai kofar gidan sukayi parking da motar,da mum tace baxata shigaba tayi Latin zuwa wajan aiki amma insha Allah zatana zagayowa tana dubata.
Ita da Annur aka sauke dan shima daga nan kano zai huce.sannan sukayi sallama da Uthman suka huce.

Ahankali suka turo kofar dakin,Amal na gaba Annur na binta abaya dauke da kayanta,danshi nashima awajan me gadi ya anje dan ba dadewa zaiyi ba.
Yana zaune a inda yake yaji sallamar Amal kamar a mafarki.

Da hanxarinshi ya mike,tare da tahowa gunta.Annur ya gani tsaye abayanta,nan danan annurin fuskarsa ya kau.ya bata rai.Amal dake tsa dan murnar ganin Abban ta.tama kasa cewa komai.

Cikin fishi ya cakuma wuyan rigarsa,wanda sanadin hakan kayan dake hannunsa suka zube a kasa.
Kaine marar mutuncin daka daukarmin yata ko,wlh saika gayamin gidan ubanda ka kaita.
Cikin murya me ban tausayi Annur yace,Abba dan Allah kayi hakuri wlh ban cutar maka da yrkaba gata nan ka tambayeta,ni bana nufinku da sharri da alkhari nake nuf...
Tasss tasss!
Nizaka maida mahaukaci,yayi maganar yana nuna kansa da hannun sa.wani alherine kake nufi da ita zaka rabata da gida harna tsawan kwana uku.

Kuka sosai take,tareda durkusawa agaban Abban nata,Abba wlh da gaske yake ka tsaya ka saurareni.
Nan danan ta kwashe duk abunda ya faro,tun daga lokacin data fara rashin lafiyar harkawo I yanxu.jikin Abbane yayi sanyi,amma saiyaki nunawa.
Yakalli Annur dake tsaye kansa a kasa,zuciyar sa na masa kona.yaji Abba yace nawane kudin da kakashe.?.
Dago da jajayan idanunsa yayi,da kyar ya yiya bude bekinsa yace Abba nidan Allah nayi.kuma ina Neman wata alfarma a gurin ka, ahankali ya karaso har gabansa ya durkusa kusa da Amal...

Ita kuwa hajiya ladi tun lokacin shigwar su Amal tana labe tana jin meke faruwa.dan ita a tsorace take.

Hajiya Bilki kuwa,tana sauka a garin kano.bucking takumayi,ta hau jirgin dazai kaita jigawa.cikin lokaci kadan ta Iso kai tsaye gidan hjy.ladi ta nufa.tana isowa taba wa mai taxi din kudinsa.ta banko gate din ta shige.dama hjy ladi ta sanar da ita Annur na gidan.

Abba dan girman Allah ka taimaka min kabani auran Amal, nayi maka alkawarin rike ta tsakani da Allah har karshen rayuwata...
Banko kofar dakin da akayine ya sanya su mikewa tsaye gaba day an su.ga mamakin Annur umminshi ya gani tsaye ba alamun wasa ko wani Abu fara'a atare da ita.
Cikin karfin hali ya ambaci Sunan ta can kasan makoshinsa.
Um....um.mi.!
Kware rai kuwa nice,tunda ni ban isa da kaiba,to naxo da kaina na tafi dakai.banxa marar hankali.

Abban Amal ne yakalleta,cikin fusata kekuma waya baki iznin shigo min gidana.
Sannu me gida kaihar kana tunanin nan gidane.inbanda kandara me Dana zaiyi da wannna jakar yr taka.
Kece jaka bilki!
Kificemin a gida tunkafin nasa ayimin waje dake.
Annur inde nonona kasha ka girma kaxo ka huce mu tafi.kuma da yahuna wlh baxaka auri Amal ba.saide in bana Raye.
Haka zalika koda Amal zata mutu batayi aureba,baxata aure dankaba.

Hjy.ladi dake tsaye najin bala'i.kasa cewa komai tayi.dan itama Neman hanyar rabuwa da Alh take.

Ummina dan Allah kiyi hakuri wallahi bazan iya rayuwa in babu itaba.
Wallahi zan tsine maka inde kabari narigaka fita.
Zuciyar shi dake mai zafi da,kanshi dake bara zanar tsagewa.
Dakyar ya iya daka kafarsa ya fice daga falon.
Amal kuwa da ta dade da shigewa daki saboda kukan dayaci karfinta.

Kaikuma Alh.Muktar,tanunashi da yatsa,wallahi nidakai gaba Har a lahira.kuma zakasan Wanda ka hulakanta.
Dama in banda ke jahilace,yaushema zaki ganni a lahira.yrtace nace baxan badaba koma danki koda zai mutu akan Amal baxan aura masa itaba wallahi nagaya miki.kuma duk sanda na kuma ganinku a gidan nan saina illataku......

I dedicated dis page to u my lovly Aunty sa'a,ur d bested Aunty ever.I rwwly appreciate ur Lov nd care to me.Lov u to d moon nd bck.Allah raya miki yarnki ameen๐Ÿ™๐Ÿป๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

I dedicated dis page to my Aunty's Angeles, maryam,hameederh nd cwt Asy.may gud bless u,rwwly lovs u dearest๐Ÿ˜˜๐ŸŒธ๐Ÿ˜˜.

55-60

Ko kallan sa batayi ba.ta fice daga gidan tare da banko musu kofar.
Lokacin data fito waje ko kadan bata ga Annur ba,bakin gate in tanufa.
Can nesa ta hango sa,cikin Sauri gudu gudu ta isa gareshi.
Annur kanka kalau.kana da hankali kuwa,kana gani nan fa,hanyar motoci na hucewa yanxu inda tsautsayi mota abige kafa
Cikin murya kuka ya ja da baya tareda yarfe hannunsa.
Na mutu mana,ni yanxu mutawata tafiyemun komai tunda kika rabani da Amal. Wlh Ummi gwara na mutu.
Durkushe yayi awajan.tare da dafe kansa yana kuka.
Tabbas tana kaunar danta.amma koda zata rabashi baxata taba barinshi ya auri Amal ba.ko wace mata yakeso adoran kasa zata aura mai ita amma banda Amal.
Tashi mutafi kana batama kanka lokaci,koda mutuwa nayi Annur ban yarda ka auti Amal ba.in kaga dama ka mutu awajan,kuma wlh kabari Babar gurin nan batare da kaiba.toh kaje bani bakai.
Cikin kuka,idanunsa sunyi jajir kamar huta.
Ahankali ya kamo hannunta. Ummina nayi miki alkawari aduniyarnan bazan taba ketare umarnin kiba.amma dan Allah kidena fadin Kalmar rabuwa tsaka Nina dake.
Taimaka masa tayi ya mike tsaya.tabbas Annur kacika dan halak.muje Allah yayi maka albarka.ameen ya furta tare dabin bayan ta.

Shikuwa Alh. Saboda bakin ciki rasama abunyi yayi.kai tsaye dakinsa ya nufa.amma Sam ya kasa samun sukuni a zuciyar sa.
Dakin amna ya shiga,kwance ya tanda ta saman gado,tana faman koka.
Magana gaskiya yana kaunar yarsa aenun,amma yakasa share mata hawayenta.
Amal! Yakira Sunanan ta,dagowa tayi da idanunta da suka rune sukayi jajir saboda tsabar kuka,dan furkar ta harta kumbura.
Kema kinasan yaronne Amal shine kika zauna kina min kuka Amal.
Ahankali kali ta karaso gabansa,jikinsa ta fada tareda fashewa da wani saban kukan.
Abbana meyasa banida sa'a a rayuwata,tunda na taso bana samun kwanciyar hankali daidai da kwana daya.kullum cikin fargava da tsoro nake.
Abbana shin ko wace yarinya haka take fuskanta a rayuwa, kokuwa danni bani da uwane.Abbana me yasa baka kaunata kaima.
Sake matseta yayi ajikin sa,shima hawayen yake saboda tausashin tilon yar tasa.
Abbana banasan Annur, nima bana kaunarsa kamar yadda baka sansa.Abbana banasan kara wata rayuwa me tsayi acikin gidan nan,kawai kamin aure koma da waye,kona samu kwanciyar hankali.
Amal kiyi hakuri nayi miki alkawarin kasancewa dake Har abada.zan tafi dake,kije kisamu ilimi mai kyau da gata irin na kowace ya.kidena sa damuwa a ranki Abban ki na tare dake.
Insha Allah karshan watannan zamu bar kasarnan dake kinji.kai kawai ta daka mai.
Yauwa yr babanta.yanxu ki kwanta ki huta kinji,in anjima kiyi wanka ki shirya zamu fita kinji.toh tace mai.sannan suka bar dakin.

Kai tsaye airport suka nufa danyi bucking din jirgin da zai kasu kano.
Amma basu samuba dan sai 5:30pm zai tashi.
Restaurant suka nufa dan yinwar da takeji.bayan sun zauna aka tambayesu abunda suke bukata.
Shide Annur ruwa kawai yake bukata, ana kawo musu yadauki ruwan tunda ya kafa kanshi saida ya shanye tas.sannan ya anje.
Itama kanta mamaki take.gaskiya Allah ya isa tsakaninta da Amal, ta mayar mata da jarimin danta zuwa karamin yaro.
Annur bakajin yinwa ne.banaji kawai yace.
Mikewa yayi tare da cewa ina zuwa.wani dan guri ya samu,yanayin gurin yayi masa kyau,ga iska mai ddi.dan kishiggidawa yayi tare da lumshe idanunsa.
Tabbas yana axaftuwa da San Amal.dole yabi umminsa ahankali, inta yarda da shi.ya saiya dawo ya roki Abban Amal dan yaga mutunne mai sanyi.ya auramai Amal din yabar kasar da ita.murmushi yayi dan harya hangoshi tare da Amal dinsa da yaransu,
Da wannan tunanin bacci ya dauke shi.

Lokacin da hajiya bilki ta gama cin abincin ta, Neman Annur tashiga yi,can ta hangoshi yana faman baccinshi hankali kwance.taji mutukar ddi ganin yanda ya kwantar da hankalin sa Har yake bacci.Neman guri tayi kusa dashi.ta zauna.tana kallon sa,ta lura da yanda lokaci kadan ya fada.tausayinsa ne ya kuma rufe ta.

Hjy ladi, hankalinta yayi mutukar tashi,dan gani take kamar hajiya bilki tayi fishi da ita,kartaje ta rasa Annur rabun ranta. Ahankali ta janyo wayar ta,gabanta na faduwa ta kira num.din hjy bilki, ringing daya biyu ta daga.

Hmmmm! Jamila kenan wallahi kina bani mamaki,wai yanxu muktarne zai rabani dake,saboda ba amana.toh bara kiji,mundin kina San mukasance tare dolene ka dauki dukkan shawarar Dana baki.yanxu kare 5,zamu tashi, inasan kafin mutafi kano mu hadu dan inasan magana dake,duk yanda zakiyi ki fito,inkinxu airport ki kirani.
Insha Allah yanxu zanxo bara na shirya.
Katse wayar tayi.
Kiran sallah aka farayi na azzahar da 12:30pm tayi.Annur ne yafara motsawa.mikewa yayi tareda hamdalah ga ubangiji, gaskiya bccinnan da yayi yaji zuciyar sa tayi sanyi.murmushi ya sakarma ummin nasa.
Itama mayarme tayi da murmushin.sannan ya mike batare da yace mata komai ba ya mike da alama alwala zayi.
Saida aka tada sallah sannan ya dawo dan zuwa yin sallah.

Tana nan zaune kiran hjy ladi ya shigo wayarta.nan tayi mata kwatancan inda take.
Bata dau wani lokaciba,ta risketa nan zaune.
Karasowa tayi ta zauna tare da gaisawa.amsawa tayi ba yabo ba fallasa.

Jamila! Nasan kin ddi kinasan nasan badan kinsan muktar kika aureshiba,kuma kina Neman hanyar da zaku rabu,ki samu dukiyarsa.tabbas yanxu dama ta samu.
Wlh kika hi duk abunda zan gaya miki,nasan Annur kike so tona bakishi duniya da lahira mundin kika kawar min da muktar daga doran kasa shine bukatata kawai.
Mikewa tsaye tayi,tare d kallon hjy bilki da mamaki.haba bilki kinsan duk,abuna da barikina ban taba kisan kaiba.kuma bamakya tuananin police su kamani.
Hmmmm jamila kenan karki manta koni wacece.inkika kasheshe yrsa zamu kalawa,kinga shiya mutu,Amal na gidan yari,ga tarin dukiya,ga kuma angonki Annur.
Wata irin dariya ta saki gaskiya bakida dama.tafawa sukayi suna dariya....


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

I dedicated dis page to oll ma fans nd y lovs once. Especially my Preety queen nd my Bestie Ummie Jafar. Allah Ubangiji ya saka mukuda alkhair,takuma bar xumunci da lobayya.much Lov for u dearest๐ŸŒธ๐ŸŒธ๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜.

60-65

Annur tunda yaje yayi sallah a masallaci,zama yayi be fitoba.Har saida akayi la'asar.sannan ya fito.
Lokacin da ya fito wajan umminshi ya nufa,daya karaso be tarda hjy ladi awajan ba.dan haka zama yayi batare da yace mata komai ba.
Annur yakamata muje muci abinci,dan inmun koma gida inada abinyi,inkuma zakaje restaurant kaci acandin to!.
Shide be tanka mataba,
Annur dakai nake magna fa!
Ummi naji,nifa ba karamin yaro bane,in inajin yinwa zanje naci mana.
Baki ta tabe batare da takuma kallon inda yakeba.
Basu jima a gurin ba.ya mike tsaye tare da kallon agogon hannun sa.
Yakamata mu huce da 5 din takusa.bai jira cewar taba yabar gurin.
Itama kallon shi tayi,tare da yin Murmushi yaro kenan,abunda ta furta kenan tareda mikewa dabinshi.
Kamar yanda aka sanar da sudin 5:30pm daidai jirginsu ya tashi zuwa garin kano.

Doguwar abaya tasaka baka mai adon Golding din Stone a gaban huyan rigar da kasan hannuwan.light make up tayi,tare da rolling din dankwalin abayar.tayi kyau sosai, kamar ka saceta ka gudu.sak kama da larabawa tayi.jikinta ta feshe da turaruka masu kanshi,Wanda baxakiji kanshinba inba a kusa da ita kake ba.
Fitowan ta daga dakin yayi daidai da sakkowan Abban ta daga stairs. Murmushi ya sakar mata.
Tama shi tamayar masa.yaji dadin yadda ta saki ranta tayi kyau sosai.masha Allah ya fada tare da karaso wa wajan ta.
Abba barka da hutawa.barka yar Abba.
Taho mu huce ko.
Ba musu tabi bayansa,
Har zuwa bakin motar sa.

Lokacinne me gadi ya budema hjy ladi gate,ko kallon inda take Alh. Beyiba,budema Amal gaban motar yayi.cikin jin dadin yanda Abban nata yake kula da ita,ta shiga ya kullo mata.
Zagayawa yayi shima ya shiga side din driver.
Suna tafiya suna hira,Har suka isa wani babban communication center.
Ciki suka shiga cike dajin dadi.ya dubeta tana ta faman kallan wajan.
Amal ina,ki zabi laptop, fone me kyau da kuma camera kinji yar Baba.
Bakinta kin rufuwa yayi tsananin farin ciki.komai ta zabi mekyau,cike da farin cikin.tana ta faman yima Abban nata godiya,suka fito daga shagon.daga nan boutique

Please Login or Register in order to submit comment