Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kuka.itama hawayen take saboda tsabar tausayin ta.
Dakar suka lallasheta. Suma suna hawayen. Dan duk Wanda ya gansa sai yayi tunanin bazai kara tashiba dan ko zai tashi za'a dau lokaci.
Sunanan zaune har 4pm tayi.lokacinne suka lokacin tafiyar visitors. Dama 1 to 4:pm ake rufe ziyara.
Amal ji take kamar abanta tareda Abban ta ko bataje wajan shi ta dunga hangoshi.
Haka suka tafi jikin kowa a sanyaye suka koma gida.


Lokacin da Uthman ya karaso gidan su Amal. Me gadi ya samu zaune yana alwala yin sallah la'asr.
Bayan sun gaisa yake tambayar sa Ashe me gidan Allah yayimai rasu.
Shide me gadi eh yace dashi dan haka aka umarceshi yace.
Amma saiyace da Uthman ba'anan suke zaman makokinba.
Nande shima Uthman yayi sallah sannan ya tafi.

Ahanyar komawarshi office ya kira Annur ya sanar masa hakanne Amma ba'a nan ake zaman makokin ba.sannan sukayi sallama.

Annur dake zaune kan kujera cike da tunani kala kala.to Amma ya akayi haka.
Koda yake ba zaman makoki tunda hanne tace Amal din na Dubai.
Gashin kansa ya hargitsa tareda shingidawa jikin kujerar yana nazarin abinyi.


Tunda suka dawo gida Amal ta shiga daki tana faman kuka,dan gani take kamar Abban ta baxai kuma tashiba.sosai hankalinta ya tashi.

Humairah ce ta turo kofar dakin da sallmarta.zama tayi kusa da Amal din tana kallon ta.
Rungumota tayi jikinta tana lallashinta.
Haba Amal sai kace bakya kaunar Abban naki.ko kukankine zai saya warke.Amal addu'a yake bukata.kina mishi addu'a koda yaushe zai warke.zai tashi kamar da.zai cigaba da rayuwa dake kamar yanda kke bukata.
Ko gaya masa akayi bakya sakin jikinki kina walwala Wallahi bazaiji dadi ba.
Yanxu kitashi kiyi sallah la'asr na tambata bakyiba.dan tunda muka dawo kike Kuka.
Oya maza kije kiyi ki fito kici abincinki.


Ana tashi daga aiki.Annur gida ya nufo dan yana bukatar hutu.yana shigowa parking din motarshi yayi.sallah ya farayi kamar yanda ya saba kamin yashiga gida.
Da sallama ya tura kofar dakin.
Mutuwar tsaye yayi ganin hjy.ladi xaune suna hira da umminshi.

Annur sannu da zuwa harka dawo.Ummi ta fada dauke da murmushi a fuskarta.
Bai kula taba.ya huce dakinsa.
Yana shiga yayima door din key.dan baya San damuwa.
Tabbas kenan Abban Amal ya rasu.toh Amma ita da aka yima mutuwa akanme zata dawo gidan mutane ta zauna.
Shifa harga Allah baya kaunar Matan nan Har cikin xuciyarsa.
Saman gadanshi ya haye yana tunanin barkatai.
Da ker yamike ya shiga toilet dan watsa ruwa ajikinsa ko yaji sanyi.
Bai jimaba ya fito tareda alwalansa.
Jallabiya yasaka sannan ya fito dan tafiya masallaci.
Inda ya barsu da zai shigo anan yakuma taddasu.
Bai kula suba yanufi hanyar fita daga falon.
Annur umminshi ta kirashi.
Bai jiyoba yace da ita an kusa tada sallah.
Be jira mezataceba ya fice daga falon.


Hajiya ladi dake zaune ta kalli Bilki tareda kama baki.
Kina nufin kema Annur haka yake miki.
Uhhhm! Kede bari haka yake wlh.wannan shegen halin nasa yana kona min rai bansan ranar dazai denaba.
Allah ya kyauta de.


Abunda yakuma bata masa rai shine,yanxunma suna nan.kenan basuyi sallah ba.
Dakinsa ya nufa dan baya San ganin fuskar hjy.ladi.

Cikin fusata hjy.ladi ta mike tareda dakama Annur tsawa.
Annur dakata,banasan iskanci,ya za ae kamaidani kamar kanwarka.ina ma magana kana wani tafiya.
Dama kasan da tamu dakai kafice a gidan nan bakayi breakfast ba kuma yanxu kadawo shima na daran me kake nufi.

Ummi nif.....
Anan zaka yimin magan.kadawo nan ka zauna mana.

Hajiya ladi itade kallon Annur kawai take.ji take kamar ta hadiye shi.

Ba asan ranshi ya dawo ya zauna kan kujera yana kallon TV.
Ina jinka tace tareda zama.
Na koshi,banacin abincin a koshe nake.

Kaji mahaifin Amal ya rasu.
Toh Allah ya jikansa!
Kawai ya mike ya nufi dakinsa.

Kallon juna sukayi tareda kwashewa da dariya.
Kinga yaro ya ganu gaskiya ya rabu da ita.wallahi ko ajikinsa.

Shikuwa Annur saboda hajiya ladi yayi haka.dan kardu kuma ta kuma Amal dinsa.

Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)

115-120

Suna fita daga asibitin, kasuwa suka nufa.
Nan suka hau yawa daga wannan shago zuwa sannan.
Siyayya sosai sukayima Amal din.
Harda waya suka saimata sabuwa,kaya kuwa ba'a magana.
Dan ita kanta tayi mamakin irin wannan siyayya da sukayi mata.
Sai kace bada kudi sukeyintaba.
Haka aka jigo musu kaya cikin mota.
Sai kusan 2pm.sukabar lasuwa.
Gidan wata kawar Anty Humairah suka nufa.

Ta tarfesu da fara'a gata ga barkwanci.
Sunan ta Asma'u.sosai itama taji Amal ta shiga ranta.saida sukayi sallah suka ci abinci.
Sannan sukayi mata sallama dan salon suke san zuwa.Har waje ta rakosu.tabama Amal turarurruka masu tsada da kamshi.sannan suka tafi.

Salon suka nufa,nan aka wanke musu Kansu aka gyara musu.
Danma basu jima anan ba,sannan suka nufi gida.dan 5pm ta kusa.


Tunda Annur ya dawo daga sallah azhr.yake kiran numb.Amal ko ince hanne, Amma bata dagaba.dan harya fara jin haushinta.

Sai yanxu daya dawo daga sallar la'asr sannan ta daga.
Bayan sun gaisa yace da ita ke menene amfanin rike wayarki.
Tun dazo ana kira Amma baki dagaba lafiya de ko.
Lafiya kalau tace dashi.
Tareda fadin Wallahi ita ba wanda yake kiranta shiyasa take anjeta kawai.sai yanxu taga kiran nasa.

Dama ba wani Abu bane tambayar ki zanyi ko Amal ta kiraki.

Wallahi nima Har yanxu shiru.

Toh pls karfa ki manta tana kiranki ki turomin kinji.

Toh tace dashi insha Allah zan turo maka.

Sannan sukayi sallama.



Ana tashi daga office gida ya nufo.bayan yayi sallar magrib. Ya shigo da sallama.
Yanxu ba kowa cikin falon hakan yai masa ddi sosai.
Dakin shi ya nufa yayi wanka.
Laptop dinsa ya dauko dan tura mail.

Umminshi ce tashigo dakinsa da sallama.
Amsa mata sallamar yayi.tareda nuna mata gurin zama.zama tayi tana kallon sa.

Yauma daka anjemin breakfast ni kakesan in ciye kenan.

Ummi pls ba haka nake nufiba wlh.
Yau na fita late ne shiya.ku ma yanxu inna dawo daga sallah zan zo naci nawa.

Toh naji yanxu,
Dama magana nakeso muyi dakai.

Laptop din tashi ya ture gefe daya,tareda maida hankalinsa kanta.ina jinkii Ummi.

Yawwa! Kaga yanda nadau dawainiyarka tunda kana karamin kawo eyanzu.kayi karatu kuma yanxu gashi kana aikinka,yanxu aurene kawai ya zagema.

Da Sauri ya dago kansa yana kallonta.

Kai ta daga mai alamun hakan take nufi.
Tabbas aure nakesan kayi Annur.
Kasamo mata ayi maka aure.
Nabaka nan da wata daya.
Inkuma baka kawo ba nixan nema maka da kaina.

Cikin wata iriyar murya daya shiga cikin tashin hankali ya dubeta.
Haba ummina kinsan de yanxu neman mata azamanin na da kakeso akwai huya.kumani inasan auran macemai nutsuwa da hankali.

Kowa ni da fatansa kenan, kuma ai ba duka aka zama dayaba.sabo da haka Nide na gayama,kuma ba sha wararka nake nemaba umarni nake baka inhar na isa dakai.

Bata jira mai zaiceba ta fice daga dakin tareda kullo masa kofar.

Kanshi ya dafe da yake bara zanar tsagewa.
Wannan wani irin bala'i ne.
Ya zai iya solving din matsalar dake tsakanin umminshi da dangin Amal.acikin wata daya.
Ga aikinsa yauashema yake da lokacin yin hakan.koda yaushe yana busy.
Inna lillahi waa inna ihaihir raji unn.!
Yaketa furtawa.
Ahankali ya farajin sauki acikin zuciyar shi.
Yanji anata faman kiran sallah Amma bazai iya zuwaba.
Tabbas so babbar cutace,yanxu menene mafita.
Da ker yamike yashiga toilet.
Alwala ya dauro.abun sallah ya shinfida,dan bayajin zai iya fita masallaci.
A daddafe yayi sallah, dan wani irin Ciwan kai dayake ji.yan idarwa ko sallayr bai dauke ba ya haye gadon ya kwanta tareda lumshe ida nunsa.


Suna shiga gidan suka hau shiga da kayan har suka gama.
Wanka duk sukayi.
Tare suka shiga kitchen danyin girki,
Sunayi suna hira kamar ya da kanwa.
Har suka gama.

Ana kiran magriba, uncle ya shigo gidan.
Dakin shi ya huce shima.
Saida sukayi sallah sannan suka fito falon.
Amal ce ta fara fito.
Sai Anty Humairah. Can kuma saiga uncle din yafito.
Nan suka yimai sannu da zuwa.sannan shima ya musu ya gajiyan kasuwa.
Hira sukahau na kasuwan suna dariya.
Sunan Har akai insha'i.
Shine yajasu sukayi sallah.
Sai Bayan sun idar,suka nufi dinning.
Sosai sunji ddin abincin.
Anaci ana hira suna dariya. Har suka kammala.
Amal ce duk ta tattara kayan ta kai kitchen din.
Sannan suka dauko masa kayan.
Nan yayita yaba kayan.
Nan Anty Humairah ta dauko fone din da tasiyama Amal.

Nima ga abunda na siyama yar tawa.nan ya amsa tareda yimata godiya.
Bude wayar yayi.harda kyautar layi aciki.
Nan ya hada mata komai.ya sanya mata numb.dinshi dana Humairah.
Sannan ya kira.ankuwa yi sa'a da kudi aciki.
Saina yayi mata setting din komai sannan ya mika mata tareda fadin aje asanya caji.

Daki ta nufa cike da murna.ta saka cajin.
Sannan ta dawo falon kayan ta dinga dauka tana kaiwa dakinta.
Nan Anty Humairah ta nemi tayata tace Aa ta barshi.

Tana gamawa ta koma falon tayi musu sallama dan baxata kuma fitowa ba saboda gyaran kayanta zatayi.

Auuu! Yau ba hira kenan Amal din Abba.
Dariya tayi uncle kayana zan gyara saida safe.sannan suma suka yi mata saida safan ta koma daki.


Nan tashiga gyara kayan nata tana shirya su cikin wardrobe. Tanayi tana murna tana karasu ajikinta.
Har tagama gaba daya.

Saida tayi shirin baccinta duka sannan ta koma kan gadanta.
Wayar Abban ta ,tadauko tareda kofar wasu numbs.cikin wayarta sannan ta mai da ta sanya wayarta a caji.
Tayi addu'o'in data saba inzata kwanta bacci.sannan ta kashe wutar dakin ta kwanta.


TWO WEEKS LATER πŸ’

Monday morning🌝
7:00amπŸ•–
Lokacin Amal ta gama hada musu breakfast, dama already tayi wanka.
Nan dannan ta shirya ta fito.
A dining ta samu su uncle nan tagaida su dan ranarne zata fara zuwa makarnta.
Itama breakfast din tayi sannan suka fito tareda uncle sanshi zai dinga anjeta a makarnta in tanada lecture. Anty Humairah Har motar ta rakosu tana cema Amal yau ita kadai zata bari cikin gida.
Uncle yayi dariya tareda fadin kozaki bitane.suna dariya,hakde Har suka fice da gidan sannan ta koma cikin gida.


Shikuwa Annur tunda umminshi tayi masa wannan magana Har yanxu bai dawo lafiya ba.duk yabi ya rame kamar bashiba.
Gashi kullum sukayi waya da hanne sai tace Amal bata kira taba.
Abu goma da ashrin ya hade masa.
Dan ko a office bashi da nutsuwa duk wanda ya tambayeshi saiyace bashi da lfy.
Hakanne ogansu ya umarceshi da in cutar nashi yayi tsanani ya dauki break mana yaga likita.
Saiya cemasa zai dauka amma ba yanxu ba.
Kuma Har yanxu wata magana bata taba hadusu da hjy ladi ba.

Itama kanta Ummi tashi shiga wani hali ganindan nata kwana biyu duk ya wani fita daga haiyacinsa.
Gashi ita baxata janye maganar aurensaba.
Dan sotake ayi auran sannan ta kuma taci gaba da sana'ar ta hankali kwance.

Ita kuwa hajiya ladi jin shirin yayi yawa,yasa zata yima hajiya maganar taji ina zancan yake.

Itama hanne ta shiga damuwa ganin Har yanxu Amal din bata kiraba,ga Annur nata faman damaunta.
Nan tashiga tunanin ko Abban ne ya mutu hankalin ta ya tashi sosai.
Dande Gwaggo na dan tausasa mata zuciya.


Amal yau anshiga makarnta kuma tabbas taji ddin makarnta balaifi.
Musamman yanda taga kowa yana abunda ke gabansa ba tareda wani ya sanya masa idoba.

Zaune take kan wata kujera tana kallon yanda mutanan gurin ke rayuwarsu.hakan yana mutukar birgeta.
Dan basu dadi da fitowa daga lecture ba.
Lokaci lokaci takan duba wayarta.
Hanne ce ta fado mata arai.nan danan ta shiga neman numb.dinta cikin contact dinta.amma bata ganiba,hakan yasa tadau alkawarin tana komawa gida zata kiranta.
Wata ta hango kamar wanda suka hadu cikin jirgi.da sauri ta dauki Jakarta tabi bayanta tana dan Sauri.
Harta cimmata.
Ammm! Excuse me ta fada.
Juyawa tayi ta kalli Amal.
Laaah! Amal ko,kace anan?
Hannunta taja suka zauna.Ashe zamu kara haduwa inata tunanin indazan ganki.
Amal daketa faman murmushi tace Allah Sarki. Ya kk ya karutu.
Lafiya qlau wallahi ya jikin Abban naki.
Da sauki tace.

Toh yanxu kinga lecture zan shiga kibani numb.dinki inna fito saina nemeki.

Nan ta amshi fone din sakina ta sanya mata numb.din sannan ta mika mata.

Ywwa Amal na gode saimun sake haduwa.
Sannan tabar wajan.

Ta jima anan zaune kafin su shiga lecture suma.


Jikin Abba da sauki.
Amma Har yanxu be farkaba.Amma sun cireshi daga glass din.
Kusan kullum sukaje in Amal batayi Kuka ba to zatayi hawaye.


Yauma kamar kullum suna zaune shida kabeer bayan sun fito daga sallar la'asr yake shaida masa ai ankusa bikinsa.
Sosai Annur ya tayashi murna.

Kabeer ne ya kalli Annur yace dashi nikuwa Annur kaje kaga likitan kuwa.
Naga kamar kana wasa da rayuwarka kamarma baka damu da cutarkanba.

Hmm! Kabeer kenan ba haka bane,kawai de nasan cutar bata likita bace.

Ohh! Kenan kaima auran kke bukata.

Kabeer bazaka gane bane.wato akwai wata yarinya danakeso.kuma andan samu matsala ne.kuma inasan nayi solving matsala.
Kaini bama hakaba,Dubai nakesan zuwa.

Dubai kuma Annur, kai kuwa me zakai a Dubai.

Inasan ganin yarinyar ne,kuma bansan ta inda zan faraba.

Tafdi! Kace kai cutar taka ta so ce.
Toh Allah ya taimaka ya bada sa'a.

Ameen yace tareda mikewa tsaye.toh saika tashi ka koma dan ankusa tashima.
Sannan suka rabu.


4:30pm.
Amal ta fito daga lecture.
Wayar ta taduba taga missed call din sakina.
Itama kiranta tayi.
Bata jimaba ta dauka.

Hello Amal na fito inata kiarnki baki dagaba.

Pls kiyi hakuri na shiga lecture ne.

Ohk Nina tafi gida sai gobe ma hadu kinji.
Tamm nagode sai anjima ta katse.

Da kanta tadawo gida.da mamakinta Humairah taga,Amal.

Aa! En makarnta Har an dawo?.
Zama tayi kan kujera dan agajiye ta ke.ruwa ta dauko cikin fridge tasha sannan tace.

Anty sannu da gida,karatu akwai wuya Anty yanda ka kasan anmin duka.

Aidama sai hakuri.
Bayan wuya sai ddi.
Sai kije ki watsa ruwa ki huta.

Toh tafada tareda mikewa.ta nufi dakin,da ker ta cire kayan ta shiga toilet din .
Saidata gasa jikinta sannan ta fito.
Gado ta fada tareda, lumshe Ido.
Nandanan bacci ya dauke ta.

Ba ita ta farkaba,saida magrib. Mikewa tayi tanufi toilet tayi alwala danyin sallah.
Saida ta sanya kayanta sannan tayi sallah tana idarwa ta dauko wayar Abban ta dan kiran hanne.


Annur na zaune a office yana aiki.
Fareeda ta shigo.
Sir kana da baki.
Nan yabata iznin su shigo.
Tana fita suka shigo su biyu ne.


Hanne na zaune itada Gwaggo suna hira.taji wayar na kara.dan tunda Annur ya mata magana akan tadena barin waya nesa da ita.

Tsoro taji Lokacin dataga wata irin numb.da bazata dagaba harta kusa tsinkewa Gwaggo tace da ita ta daga mana kar ta katse.

Da sallama ta daga.
Amal cikin farin ciki ko amsa sallamar batayiba.
Tace hanne Amal cee! .


Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer😘)

120-125

Cikin murna hanne ta mike tsaye sabo da tsananin farin cikin jin muryar Amal din.

Cikeda zumudi hanne tace.ya Dubai din ya kowa da kowa ya kuma jikin Abban.

Wallahi kowa lafiya qlau,Abba kuma jiki da sauki za'a,amma Har yanxu be farfadoba,saide kullum muna cikin addu'a.

Toh Allah ya bashi lafiya. Yakuma tashi kafadunsa.

Ameen Amal tace,tareda cewa ya en gidan da kike zaune suma qlau ko?

Lafiya lau muke wallahi suma suna gaida ke kuma suna yima Abba ya jiki.

Yana amsawa.hanne harna fara karatu anan fa.

Da gaske Amal. Kice hankalin ki ya kwanta to Allah ya taimaka.

Tashi tayi daga gaban Gwaggo ta shige daki.
Sannan ta Amal.
Hmmm in gaya miki har nayi saban saurayi dan gidan Gwaggo ne,kuma tsakani da Allah yake sona aurena ma zaiyi.

DA gaske hanne. Allah ya sanya alkhari na tayaki murna,
Amma de yana da aikin yi ko.

Nagode, eh yana Sana'a ba laifi yana da rufin airinshi sosai dan Har mota gareshi.matar shice ta rasu shekara 3 da suka huce.
Shine zai kara aure.dan harya sanar da Gwaggo.
Itama taji ddi sosai.
Shine ta ce masa yabari iyayen gidana su dawo.

Gaskiya naji ddi.Amma yanxu hanne Har kyajira Abba ya warke.

To menene Amal. Nimafa kamar uba yake a gurina kede kawai kiyi fatan Allah bashi lafiya.

Ameen thumma ameen, babude wata matsala ko.

Babu komai.Yawwa Amal wannan mutumin yanata kiranki,yanxu yacema inkin kirani na tura masa numb.dinki.
Ywwa Annur.

Allah Sarki dan Allah ashe yana kiranki.toh ki tura masa.

Toh. Yanxu kinga na dawo daga makaranta.zanci abinci na kwanta na huta sai kuma na kuma kiranki.
Ywwa baki gayan sunan yayan nawaba.kuma ki gaida shi.

Hmmm! Sunansa Ahmad.
Saida safe ki gaida su dan Allah kuma ki duba jikin Abba nabarki lafiya.

Sannan ta kashe wayar.
Nan ta nemi gajiya ta rasa.dan taji ddin waya da hanne sosai.
Tanasan hanne itama tana kaunar ta.shiyasa take kewarta.

Wardrobe dinta tabude ta dauko kayan bacci ta sanya.
Sannan ta saka hijab dinta tare da fita falo dan yinwa takeji.

A falo ta tarda su uncle suna hira.
Amal idanki biyu dama.aena dauka gajiyan makarntar ne yasaki bcci.
Cewar uncle yana kallonta.

Wallahi na danyi baccinma,Amma wayama mukayi da hanne me aikin gidnmu.
Wallahi tana da kirki so sai kuma tana kaunarmu.
Tacema tana gaida Ku.

Masha Allah, muma muna amsawa.Anty Humairah ta fada.
Maza ga abinci kije kici nasan kina jin yinwa.

Abincin ta dauko ta dawo falo ta zauna.
Tanaci suna hirar makarnta, tana basu lavarin abubuwa daban daban.
Wani suyi mata dariya wani kuma su gyara mata.

Amma fa uncle sun iya lecture, kamarba larabawa ba.dan wallahi ana gane turancinsu sosai.

Eh hakane kinsan akwai turawa acikin su.kede ki Dage.dan karatun medicine ba karamin Abu bane.
Allah de yabada sa'a.

ameen suka fada itada Anty Humairah.

Tanci suna hira harta kammala ta maida plate din kitchen tasha ruwa sannan ta dawo falon.Sunanan Har akayi insha'i sannan ta shiga daki ta sako alwala ta dawo falon sukayi jam'i.


5:55pm

Ya baro office din.
Yana cikin driving a mota yaji message ya shigo fone dinshi.
Be damu da koma wayeba.dan baya da bukatar sanin akanme aka turo shiba.
Burinshi be huce hanne ta kirasa ta shaida masa sunyi waya da Amal.


Ita kuwa hanne. Bayan sun gama waya da Amal.
Wayrta ta duba ko akwai kudin dazata kira Annur.
Saura #4.
Dan haka ta yanke shawaran tura masa da numb.


Nan danan ya karaso gida.saida yyi sallah magriba ka'ida kenan yake shiga gida.
Danko yadwo ba'ayiba saiya jira Har yayi sannan.

Da sallam ya shigo cikin gidan.yauma ba kowa cikin falon.da Sauri ya nufi dakinsa dan yau bayasan haduwa da kowa.
Yana shiga yayima kofar key.
Wanka ya fara shiga kamar ynda ya saba danyau ko sallah insha'i a gida zaiyi.
Bayan ya gama duk abunda zaiyi.
Har sallah, sannan yayi shirin kwanciya dan bacci yakeji.wayarshi ya janyo da duba sakonni.
Sakon hanne ya fara gani dan ya canza sunan tun tuni.
Jikinshi Har rawa yake ya buda.
Kamar haka yaga an rubuta.

ASSALAMU ALAIKOUM.
ANNUR GA NUMB.DIN
AMAL NAN.BA KUDI A
WAYAR DANA KIRA KA.
HANNE.


Nan daran ya danna kira a numb.kuma ya shiga harta fara ring.

Ita kuwa Amal dan gajiyar makaranta da tayi,ya sanya bata tsaya kallo ba ta musu sallama ta nufi daki danyin bacci.

Tana shiga daki hijab din ta cire ta haye gado tareda kashe wutr dakin.
Tana nan kwance Har baccnta yayi nisa dan ta gaji.
Dayake bata da nauyin bacci taji kamar karan wayar ta.
Mikewa tayi ta dauka tareda karawa a kunne.
Cikin muryar bacci tayi sallama,ba tare da ta duba numb.me kiraba.

Amsa sallamar yayi tareda fadin.
Amal! Annur nefa.
Da Sauri ta gama watsakewa.

Da farkode ya hakuri.
Da mamaki tace hakuri kuma.
Shima mamakinne ya rufe shi.
Tabbas kuwa haka nace dan an shaidamun cewa Abban ki ya rasu.

Abbana bai rasuba illade yana kwance dan haryanxu bamusan amatsayin da yakeba,nasa afadi hakanne saboda wata manufata daban.Amma kaima inasan ka dauka a hakan.

OK insha Allah.
Amm! Amma kinsan Allah zai sakamin saboda irin huran da soyayyarki take yimin.
Kullum fa cikin tunaninki nake.
Wallahi da Dubai din zan taho.

Murmushi tayi mai sauti,wanda shima kansa yaji.
Dubai din zaka taho?

Eh mana ko kina mamaki ne.kuma Har yanxun ban janye ra'a yinaba.
Zanzo na duba Abba kuma naga masoyiyata.

Murmushin takuma yi.Amma kasan Ummi bazata taba yar daba.

Na sani,amma kuma sai naxoba.
Ko korata kikesabyine.

Nina isa nidaba kasa taba.Allah ya kawoka lafiya.
Ameen.

Yanzu de bacci nakeji saide da safe.
Auuu! Koratama kikeyi my heart princess πŸ‘‘.

Nina isa na koreka.
Toh najide bansan ina takura miki,sai goban kinji my one nd onlyπŸ‘ŒπŸ».

Hmmm! Toh Allah ya kaimu tace dashi.

Too I Lov u❣
Kema ki fada pls.
En dariya tayi tareda rufe idanu sabo da kunya.
Zata fada kenan yace
Dakata!
Saura inkin fada ki kashe wayr kisa zuciya ta tabuga.tunda wancanma haka kikayi
Saiyau Allah ya kara bani ikon jin muryarki.

Insha Allah.
I Lov u tooπŸ’•
Mutukar ddi Annur ya jishi.
Kamar karsu rabu da juna da kr sukayi sallama.

Kowannan su kasa anje wayr yyi tana ruke da su.
Suna tunanin ynda rayiwar dayansu zata kasance batareda dan uwan taba.

Sosai Amal tana jin Annur cikin zuciyar ta.dan Har tana da burin kara ganin kyakkyawar fuskarsa.
Lallai in Abban ta ya warke zata gaya masa tana San Annur Har cikin ranta.

Shikuwa gogan ba'a magana.dn a fadin duniyar nan aka cire umminshi, bbu wanca yakeso sama da Amal.

Kowannan su da tunanin dan uwansa yayi bacci.


πŸ”ΊπŸ”ΊπŸ”ΊπŸ”ΊπŸ”ΊπŸ”ΊπŸ”Ί
πŸ”»πŸ”»πŸ”»πŸ”»πŸ”»πŸ”»πŸ”»
Pls dearest kuyi hakuri bnyi page din nan da yawaba,yankewa nayi a hannu.
Did page also goes to u my fans lovs u ba'a dadiπŸ’πŸ’

😘😘



Written by Zeenaseer😘
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: 🌹🌹🌹🌸🌹🌹🌹
🌷🌷🌷
🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer😘)

125-130

Yau Amal 10am take da lecture dan haka bata tashi dahuriba.
Tana kwance saman gado tanata sharar baccinta hankali kwance.taji wayarta na faman ringing.
Mikewa tayi ta dauko wayar.

Assalamu Alaikoum
Habibtee!
Tana jin haka tasan Annur ne ya kiranta.

Kara shigewa cikin blanket din tayi.tareda amsa sallamar tasa.

Yanaji muryar taki haka ko baki tashiba.
Wallahi bantashiba sai zuwa anjima tukun.
Kina hutawa ba haka nakesun ki kasance koda yaushe cikin jin ddi da kwanciyar hankali.
Hmmm! Kaima ae kana hutawan.
Amal ina wani Hutu,kinsan na fara aiki yanxuma ina office kinga kuwa banida wani sauran Hutu.
Nima ai hutun nawa na wani dan lokaci ne,zuwa anjima zan shiga lecture kasan na fara karatu.
Alhmdullh dama nima burina kenan kayi karatu Amal kizama wani Abu.me kike karantane.
Medicine nakeyi inasan nazama likita arayuwata.
Toh Allah ubngiji ya bada sa'a yasa agama lafiya.
Amen ta fada.
Yauwa saiki samin rana yaushe zan shigo Dubai din.
Aa kayi zamanka mana,kanasan janyowa kanka matsane,kasan Ummi bata sona taya zakace zaka taho gurina.
Amal kenan ya kikesan nayi,bani da burin daya huce nazo na ganki Amal ina kaunar ki da yawa.
Nasani Annur Amma kasan halin mahaifiyar ka,banasan abunda zai sakata kara tsanata.
Ba komai insha Allah komai yazo kareshe insha Allah babu abunda zai kuma faruwa sai alkhari.
Toh nagode sai anjima.
Toh my bby San mun kuma waya.

πŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”ΆπŸ”Ά

Zaune hajiya ladi take a falo tana faman shan kanshi dan tagaji da giran gawan shanu.
Hajiya bilki ke ta sauko daga upstairs tana faman yauki.
Karasowa cikin falon tayi tareda zama kan kujera.
Dukkan su babu wanda ya kula wani tsawan lokaci.
Bilki! Hajiya ladi ta kira sunan ta,A gaskiya na gaji da irin wannan abun da kikemin.
Kin maidani kamar wanda tazo cin abincin a gidan nan,saide ki bani abinci ki barni kara zube.
Jamila me kikesan nayi miki.ina baki ci da sha da gurin kwana.toh kuma bayan wannan wani Abu kekisan da namiki.
Dakata aiba haka mukayi dakeba,ina maganar aurena da Annur?
Haka zakice dani kenan, jamila nayima Annur magana yace baya kaunar ki,baya sanki kuma inna takura masa yace zai bar gidan.kinga yanzu saiki hakur....
Cikin fishi ta mike tsaye,dakata Bilki, ba haka mukayi dakeba munriga munyi magana dake yanxu kuma da bukatarki ta biya zaki watsa min kasa a Ido. Kince inde Annur dankine toh zaki sashi ya aureni.kenan yanxu ba danki bane.Wallahi kin bani mamaki Bilki ban taba tsammanin haka agareki ba.
Nagode sosai kuma kinsan koni wacece.
Waboda haka Wallahi ko kina so ko bakya so saina auri Annur Wallahi kinji na rantse.
Feeeee tanufi hanyar shiga dakinta dan barin gidan zatayi.
Jamila itama takirata tareda mikewa.
Hjy ladi tsayawa tayi ba tareda tajuyo ba.
Kiyi hakuri dan Allah. Insha Allah zan San yanda zanyi,ki kwantar da hankalinki,inde ni na haifi Annur zai auri jamila.
Murmushi hjy ladi tayi tareda shigewa cikin dakin.
Ajjiyar zuciya tayi tareda zama kan kujera.tabbas tasan halin jamila bata da mutunci,dan haka dole tadau mataki akanta.

πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·πŸ”·

Tana gama waya da Annur, mikewa tayi tareda gyara dakinta tas.sannan ta shiga wanka.
Saida ta gama wanka ta shirya tsaf,sannan ta fito cikin shirinta na makarnta.
Dogowar riga ta sanya light blue, ta sanya bby hijab white.
Sannan ta sanya takalminta ta dau hand bag dinta da fone dinta ta fito.
Bata ga Anty Humairah a faloba,dining ta huce ta ci abinci,sannan ta mufi dakin Anty Humairah.
Da sallama ta shiga cikin dakin.
Kwance ta ganta saman gado tana waya.
Zama tayi kusa da gadon tana kallon ta harta gama wayr.
Matsowa tayi kusa da ita.
Antyna inakwna ina fitowa naga banganki faloba.
Lafiya lau my Amal, ina gama aikina na shigo daki ina waya da gida,kanwar Maman

Please Login or Register in order to submit comment