Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yanzu kenan ya kakesan ayi kasande bazan taba daga bikin nan ba ko?
Gobe zan tafi koma ranar sat 2pm zata min ajigawa.zance dama wajan dinner da daurin aure ake bukata ta.
Anjiyar zuciya ta sauke tare da fadin Allah ya kiyaye bata jira me zaice ba ta fice tare da kullo mai kofar.
Wani mugun tsalle ya buga yana dariya.
Dama already ya gama hada kayansa dan yama sakasu cikin motar shi dan amota yake San tafiya.
Hahhah lallai Ummi ai kawai natafi kaikuma nextwk insha Allah.
Sannan ya dau key dinsa ya fice daga gidan.
Cikin motar sa ya nufa tare da yimata key dan yasan yanzu Amal dinsa nacan tana jiran shi.
Gate aka bude masa sannan ya fice daga cikin gidan.


๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป
Anty Humairah ce tayi waya kan azo atafi dasu.
Basufi minti 10 da saukaba mota ta iso airport da driver dan daukar su.
Abban Amal aka fara kaiwa gidan sa.dama yariga ya yawa wani yaransa waya akan a anshi key gurin me gadi abude agyara masa gidan.
Dan kullum suka kira wayar hanne akashe dan sun rasa ko lafiya.
Har kofar gida suka kawo su,mai gadi ya rinka murnar ganin uban gidan nasa nan ya shigar mai da kayansa gida.
Saida sukayi sallama da su Amal sannan ya huce.

Kai tsaye gidan Hakeem na nan aka huce dasu.suma sunsa an gyara ko ina dama kusa da gidan su Nana ne.
Cikin gidan suka shiga tare da kayansu.
Dakin da Amal zata zauna Humairah ta nuna mata sannan ta dau trolley dinta ta shige.
Wanka ta shiga tayi sannan ta fito tayi sallah la'asr.
Kayanta ta dauko atamfa Riga da skit ta sanya dinkin yayi mata kyau sosai sannan ta danyi light make-up. Tayi kyau sosai ta kara fari da kiba.
Tana fitowa falon rataye da mayafi a kafadar fone dinta na hannunta dan Anty Humairah ta kira ta akan ita gama ta fito su shiga gida.
Nana ce ta turo kofar dakin da gudu ta shigo ta rungume Amal din tana dariya itama rungume tan tayi tana dariya.
I misssss u my Amal. Dariya tayi tareda fadin nima haka my Nana.
Kunzo lafiya ya hanya,
Alhmdullh Nana ya garan biki.
Wallahi taro gashinan saima kun shiga gida.
Allah ko,ina sakina?
Wallahi yanxu muka gama waya kinsan gobe zamuje kunshi gidan da ake mana gyaran jiki.
Tafawa sukayi,Nana tace ke vakiga na canzaba.
Wallahi kuwa naga Har wani kumatu kikayi.
Hhhhhh bana San sharri kema can zamu kaiki a gyarama Annur ke.
Dariya suka kumayi.sannan tace banga ya Humairah ba ina ta shige.

Fitowa tayi itama ta gama shiryawa tayi kyau sosai tana fadin gani nan Amarya.
Gaisawa sukayi,sannan Nana ta musu ya ban gajiya.
Lafiya qlau Nana ya taru
Wallahi taro nan saima kin shiga gida.
Aiko ynzu kinsan na matsu naga yn uwa da dangi.
Aikuwa sunacan suna jiranki.
Toh maza Ku huce muje bazan kulle gidan ba Hakeem na ciki.
Sannan suka bi bayanta suka fita.

Gidan nasu suka nufa tun daga bakin gate suka fara gaisawa da mutane dan Humairah mace ce ta mutane.
Har suka shigo cikin gidan.
Kuzo kaga dangi da yan uwa sai rungumar juna ake ita kanta Amal sun burgeta sai taji inama ace dangin tane.
Itama Amal din sai gaida mutane take ana amsa mata cike da fara'a. Nana na rike da hannun amal duk inda Humairah tayi suna biye da ita.
Wani falo suka shiga duk yawan cinsu matane manya da tsofaffi acikinsa.
Nan suka durkusa anata faman gaidasu wasu su rungume Humairah suna fada mata irin kewarta da sukayi.
Wata yar dattijuwa ce me fara'a ta kalli Amal sannan ta kalli Humairah tace Aisha ina kika samo diya kamar yr gidn jikar gidan mandibbo?
Kai inna bafa yr can bace.
Allah sarki gani nayi tana min kama da Zainabu yar gidan dije Allah jikar rai.
Amal najin haka ta dago kai gabanta na faduwa ta mike tsaye.
Kowa sai kallanta yake.
Anty Humairah ce ta juyo tareda fadin lafiya Amal.
Anty ji nayi an ambaci sunan babata.nide a yanda Abbana ya bani labari.
Ya auri mamana a sokoto kuma kuma su nanta Zainabu kuma yatafi da ita tundaga ranar basu kuma komawa.
Tabbas wannan jinin sarkin fulanice.cewar dattijuwar.sannan ta kalli wato yr tsohuwa tace da ita Inno duba diyarnan dakyau bata maki kama da Dije.
Nima tunda na shigo nike kallanta.kamar Dije Allah jikan rai.
Yaki yarnan jinin gidan sarki basa buya inde tana da taban ruwa a bayanta ba makawa ko tawaddar Allah cikin ido Allah yayi masu wannan baiwa.
Nan Amal tana hawaye ta matsa gaf da matar,duba jikinta tashiga yi amma bataga taban ba.
Har ta hakura sai kuma tace muga bayanki juyawa tayi ta dage dan kwalin kanta.
Ga taban nan manne a saman huyanta kadan kafin keyarta.
Nan fa aka hau murna.Amal kuwa farin ciki kamar ya kasheta.
Sai kukan ddi take haka Nana d Humairah da wasu yan tsirari a falon.
Kinga diyata bar kuka kinji nan kamar gidan Ku yake duk nan yan uwanki ne.
Sannan tace kinga wannan ta nuna Inno yr tsuhuwa uwassu daya uban su daya da ka karki Dije Allah jikan rai.
Mukuma nan da kike gani duk kannan kakarkine Har Babar su halima(Nana). Da uwar Uthman kinsan ta ko?
Eh Amal ta fada toh duk iyayanki ne da kakanninki dan haka kibar kuka.abunda ya faruwa wa mahai fiyarki Allah zai saka mata.
Dan Lokacin da aka tura a dauko Zainabu sai cewa ake tabi saurayi ta gudu.sai daga baya gaskiya ta fito.
Sabo da haka kinga dangin mahaifiyar ki saiki godema Allah.
Kowa ya taya Amal murna sosai nan ta shaida musu sunanta .
Sunji ddi suma abinci aka zubo mata ita da Nana suka zauna sunaci sai faman hira ake da farin ciki.
Nan Humairah take shaida musu maganar bikin Amal din.
Nan fa akahau buda da wani saban farin ciki.kacede muna da biki nan kusa bayan na Nana.
Nan aka yayima Humairah godiya abisa rukun da tayima Amal.
Wallahi ba komai shiyasa koba kasan mutun ba ka taimaka mishi koda bai zama dn uwankaba wata rana zai jiknka.
Nan de akayi ta hira ana maida zance Har aka kira magrib..


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

180-185

Bayan sun idar da sallah magrib Amal ta kira Abban ta tagaya masa abinda ya faru.
Shima kansa ba karamin ddi yajiba dan bashi da buri daya huce na farin cikin Amal din.

Wayr tace tayi kara dan tana jin ringing tasan me kiranta.
Da murmushi a fuskarta ta daga tareda sallama.
Bbyna nima fa ina jigawa.
Dagaske da Har kasa na bar jin ddi dake min bazaka samu damar zuwaba.
So don't wrry beauty yanxuma kin gani dakin Uthman Ango gashi kani.
Kace masa nagode koya kira yamin ban gajiya.
Yan daga gafe yace ayi hakuri hakuri pls.
Murmushi tayi tare da fadin kasa loudspeaker zan gaya muku wani abun farin ciki.
Cikin zumudin ji Uthman ya mike daga kwancan da yake.
Muna jinki .
Yau nasamu dangin mamata.kuma Uthman pls ka gayama mum dinka.
Wow! Gaskiya mun tayiki farin ciki amma aina kuka hadu dasu cewar Annur.
Hmmm dangin su Uthman am also part of them.
Cike da mamaki suka hada baki tare da fadin da gaske?
Sosaima kuwa.toh wannan wani irin farin ciki zamu tayaki kawai Allah zamuyita gode mawa.tunda shine kadai yasan irin farin cikin da muke ciki cewar Uthman.
Dan shi Annur yama kasa magana gaba daya.
Sun tayata farin ciki sosai kuma tabbas taji ddi.sannan take kuma gode musu tukun sukayi sallama.

๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ
Washe gari tun 11am suka bar gida ita da Amal suka tafi gidan kunshi.
Can suka tanda sakina duk da suna waya da Amal din taji ddin ganin ta.
Nan aka fara gyrama amare jiki ana tsantsara musu lalle me kyau.ga gyara gashi da suka sha.

Basu suka dawo ba sai GAF da magrib suka shigo gida.
Wanka sukayi sannan sallah.
Itama sakina gida ta huce dan kawaynta duk sunzo.
Haka gidan su Nana ma ba'a magana dan ankuma cika sosai.
Kowa yaba kunshin su yake dan yayi kyau ainun.
Saida sukaci abinci sukayi sallah insha sannan Nana taja wasu kawaynta su biyu Hassana da fadila suka nufi gidan Anty Humairah dan a can suke kwana dakin Amal din.
Shima uncle Hakeem ya taya Amal murna sosai.dn yan tausayin yarinyar.

๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ
Yaune kamun amare kowa kagani yasha anko sunyi kyau sosai ansha bidiri anci ansha amare ansha kyau.

Itama gidan hajiya bilki sunyi kamu ansha shagali sosai sunsha kida da rawa kuma tayi taro sosai.

Haka biki yay ta tafiya Har ya zo ranar assabr dinner ranar da Annur yayima umminsa alkawarin dawo wo gida.tun da yayi sallah zuhr ya kashe gaba daya wayoyinsa danma kar afara ne mansa.

Har yamma tayi lokacinne amare suka gama shirin su ko wacce da kalar kayan data sanya sunyi mutukar kyau gabaki dayansu.
Haka aka aiko da motoci kala kala suka dauki amare da kawayansu zuwa hall din da zasuyi dinner din su cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Komai suna yinsa acikin natsuwa.
Amal ce ta fara bude taro da addu'a cikin harshan larabci da kuma turanci,kowa na gurin saida ta burgesa.
Musamman habibeen zuciyarta dan ji yayi kamar ya saceta ya gudu kowa sai kallanta yake Har yaji kishi ya kama shi๐Ÿ˜†๐Ÿ˜†.
Haka suka cigaba da gudanar da abubuwansu kala kala.

๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ
Can kuwa tunda akayi sallah la'asr Annur bai isoba hankalin hajiya bilki ya tashi dan tabbas tasan Annur karya yayi mata dan baya San Sara.
Dan haka ta kudiri niyar babu abunda zai hanasu party dole suyi.
Kuma washe gari dole a daura aure.

Haka suka ci gaba da shirinsu Har Lokacin tafiya yayi haka zalika itama Amarya ba damuwar ta bace itade burinta ta aureshi ta kuntata masa tunda ya hulakantata ya kuma nuna baya kaunar ta.
Itama cikin ado ita da kawayenta yn duniya da kuma kawayan hajiya bilki da na mamata.
Tabbas ciki ya cika manyan mata sun halacci bikin nan.
Motoci suka dinga hawa suka isa hall din basu jima da fara abunda ya kawo suba.
Masu video da pic anata famanyi.
Can sai aka dinga ganin kartin maza suna shigowa cikin hall ko wanne da makamai a hannunsu sun kai kimanin su 30 ko wanne ba imani atare dashi.
Ko wacce acikin gurin hankalinta atashe yake.
Cikin takun kasaita ta shigo Hall din tana tafi.
Tabbas yau ni NA cika yr halak kuma zan nuna muku bani da hankali bani kuka dokaba zakuga duka.
Ta kalli wannan kartin tace kada Ku ragama ko da yaroni cikin su so nake duk wanda ta zo dinner en nan karta manta da ita a rayuwa sa.jikin ko wace shegiya ya gaya mata.
Nan aka hau duka babu tausayi gaba daya guri ya kaure da hayaniya ko wa takanta take.
Hajiya bilki kuwa da Sara da Mamanta masu dukansu daban kuma da gora.
Duka yake ba tausayi duk inda ya samu saida ya musu lilis saida ko wacce a gurin ko motsin kirki batayi.
Amarya kuwa suma tayi su hajiya bilki jikinta duk yayi tsami tayi nadamar sanin hajiya ladi arayuwata.
Kuka sosai ta zauna tana yi,wannna kadan ta fara gani kenan tun aduniya ta fara ganin irin wannan ina ga ta mutu.
Da alama hannun ta yama karye.
Sara kuwa karaya 2 aleg 1 acinya.
Gatanan kwance kamar matacciya.
Mamanta sai faman kuka take.
Cikin en party kuwa wanda yaga zai iya mikewa ya mike wanda bai iyawa ya kira atafi dashi.

Ita kuwa hajiya ladi dama ta riga ta sallama yn iskan data hayo.
Suna fitowa babban cikisu yace hajiya baki cika mana kudin bada.
Duka nawane za'a cika muku kudin banza ni kar Ku batamin rai wlh.
Bafa haka mukai da keba gaskiya muna ganin mutuncin ki Wallahi.
Banzaye en iska Ku harwani mutunci kuka sani,to na cinye kuma bazan biya ba.
Wani daya dake tsaye abayan ta ya buga mata sanda akai nan yayi mata dukan tsiya.sannan ogansu yayi mata fyade.
Suka dauke motarta da jakarta daga ita sai kayan jikinta.kanta ko dan kwali babu ga tsinannan dukkan da tasha ko motsi bata iyawa.
Karan motar yansanda najiyo da alama kan titin suka biyo.
Ganin mutun kan hanya ya sanyasu dakata wa tareda duba ko lafiya.
Suna fito wani mutun medan hake ya kuma haska fuskarta tareda kallan photo hannusa.
Da Sauri yace yallabai ai itace wanda muke nema duba dakyau kagani
Hajiya kece jamila ahankali ta daga kanta tace nice dan Allah Ku taimaka min karna mutu.
Yauwa isa Ku sakota cikin mota mu tafi.ba musu suka sanya hajiya ladi cikin mota suka kuma hucewa suna jiniya..

Biki yayi ddi sosai cikinfarin ciki suka tashi aka maida kowa gida lafiya.

Sannan washe gari da safe aka daura auran.HALIMA ABUBAKAR
DA
ALIYU ISA RINGIN.

AND

SAKINA ABDUL'S SALAM
DA
UTHMAN ABBA DUTSE

Taro yayi albarka manyan mutane an uwa da abokan arziki duk sun halacci wannan biki mai albarka.

Yamma nayi ko wace Amarya aka mikata gidan mijinta.
Alhmdullh biki ya kare.

๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ
Biki ya kare kowa ya kuma gidansa lafiya saikuma na Amal kowa haka yake fadi.
Rayuwa ta dawowa Amal sabuwa ta kuma saman wani saban gatan wajan dangin mahaifiyar ta.
Ga kuma Abba ta da yake kula da ita shima sosai.

Yaune ranar da Annur zai koma gida sunyi sallama da juna shida ita da fatan kuma sai sun sake haduwa dan zasuje south African ita da Abba sai kuma sun dawo.haka suka rabu badan suna so ba.

(9:00pm)
Annur ya isa gida gabansa na faman faduwa yanxu shikenan an aura masa wannan mahaukaciya Wallahi sakinta zaiyi dan bazai yima Amal kishiya ba.
Da sallama ya shiga cikin falo zaune kan kujera ya tanda umminshi.
Gabansa na faduwa ya karasa wajanta tareda fadin.
Dan Allah dan annabi kiyi hakuri ummina nasan ban m.....
Ya isa Annur, ni ba kamin komai ba nagode kwarai da Allah yabani yaro kamarka.
Kuka sosai takeyi.Annur nice zan roki yafiyarka ka yafemin kaji Dana.
Cikin mamaki yace Ummi wai meke faruwa ne dan Allah.
Nan ta kwashe duk abunda ya faru ta gaya masa.
Nan yace Wallahi sai yadau mataki akan hajiya ladi.
Rabuda ita Annur kaji inde duniyace taje zata gani.
Yanzu ya hannun naki.kinga likita.
Eh dasauki harma nasha magani kuma an Dora.
Toh Allah ya kiyaye gaba.
Ameen tace dashi.
Sannan ya mike ya nufi dakinsa.
Gaskiya yayi mamakin yanda ummin ta canza Lokaci daya.
Allah ya kiyaye de...


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

190-195

ONE WEEK LATER๐ŸŒธ
Annur da Amal suna cikin jin ddi dakuma tsantsar soyayya da sukema junansu.
Burin kowanne acikinsu ya sanya dan uwansa farin ciki.
Yauma sun shirya da yamma da zuwa kaima hajiya bilki ziyara.
Taji dadi mutuka kuma tayi farincikin ganunsu.rasa inda zata sanya amal tayi dan murna.
A gurinta suka samu lbrn ankama hajiya ladi da hodar iblis koma ta yima wani mutun sa'a kuma harda kisan kai.
Yanxude an yanke mata hukuncin daurin rai da rai.
Suntausaya mata sosai kuma suka yi mata fatan Allah ya yafe mata.
Basu jimaba sukayi mata sallama.


Rayuwar su Annur abin sha'awa abin burgewa sunyi kyau abun su sun kara fari.
Yau tunda suka waye gari suka nufi jigawa dan yima su Anty bangajiya da kuma sallama dan zasu koma.
Da huri soka isa Anty taji ddin ganin yr tata yanda tayi kyau hankalin ta kwance.
Sannan ta shiga gida gurin yaya( Maman Nana). Itama tayi murnar ganin amal din kuma takuma yimata nasiya sosai.

Ranar de sunsha yawo Har gidan sakina da Nana sukaje sunsha hira.
Kwana su biyu a jigawa saida uncle suka tafi sannan suma suka dawo gida.

Lokacin aikin hajji na zuwa bayan wata biyu da auran su Annur ya biya musu su tafi da suka gama aikin su suka biya ta dubi nan ma sunji ddin ziyarar tasu kwanan su biyar a Dubai suka nufi sokoto nan ma sunyi yawo gidan dangin Amal da sosai sannan suka dawo lokacinne Amal ta fara laulayin ciki.
Murna wajan yan uwa ba magana musamman Abban Amal da su uncle nan Annur yaci gaba da tattalin matarsa da dansu Har zuwa Lokacin da Allah zai sauketa.
Gaba daya Anty Humairah ta taso daga Dubai ta taho tayima Amal zaman jego.
Kwana Humairah uku da zuwa Amal ta santalo jaririnta kyakyawa me kama da Annur.
Kowa yayi murna sosai lokacin su sakina duk sun haihu suma.
Annur ma yayi murna sosai yaran yaci sunan baban Annur Shu'aeb suke kiransa da ARIF.
Anty Humairah tana kula da Amal da Arif Har lokacin da sukayi 40 sannan ta koma gidan ta da murnar alkawarin da Annur da Amal sukayi mata ana yayi Arif zasu kawo musu sun basu halak malak.


AFTER 3 YEARS๐ŸŒธ๐ŸŒธ
Amal da Annur sun Dada girma sunzama mum nd dad.
Dan yanxu haka ma Amal ta kuma haihuwa Amma wannan karan mace ta Haifa.
Suka Samara Zainab amma suke kiranta da AMNA.duka yrnyr batafi wata biyu ba.
Kyakyawa sak Amal Har suman kan nata.

Ko wanne gida suna cikin jin ddi da annashuwa kuma suna zumunci sosai.
Sun hade kansu gadaya.


Shikuma Arif yana Dubai gurin Anty Humairah yayi kiba yayi kyau kamar dan larabawa komai yake so shi suke yimasa.
Yana jin ddi sosai yana San Anty Humairah da uncle Hakeem sosai dan yama zata sune iyayansa.

ENDโœ…



Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

185-190

BAYAN KWANA BIYU
Annur na zaune dayake wkend ne yana duba wasu files.
Da sallama ta shigo dakin nashi tare da zama bisa gado.
Ummina harkin tashi? Ina kwana.
Lafiya qlau Annur katashi lafiya ya aiki.
Alhmdullh Ummi ya saukin hannun.
Hannuda sauki sosai Wallahi.
Amm Annur dama abunda ke tafe dani shine.tunda naga kana kaunar Amal kuma kaga yarinyar kirki ce mezai hana muje abama iyayenta hakuri su baka ka aura.
Hmm Ummi kenan dama anriga ambani Amal, kice ban gaya waba dan naga bakya santa.yanxu nan da sati uku za ayi bikinmu insha Allah.
Baki tarike da mamaki tana kallan Annur din.kace daban zo ma da maganar ba da yanzu shikenan saide naga Amarya.
Murmushi yake tare da dan Sosa kai.
Toh Alhmdullh tunda Allah yasa mun gane gaskiya yanxu ka shirya.zamuje na bama dangin mahaifin ka hakuri akan abunda nayi musu kuma na nuna maka au insha Allah.
Cikin tsananin dadi ya mike yana murna dan danan ya shirya suka fita.

Cikin ikon Allah duk ta gane gida Jan.
Nan ta dinga bi daya bayan daya tana neman yafiyarta koma Masha Allah kodan darajar Annur sun amshe su hannu bibiyu kuma sunji ddi sosai.
Nan ta shaida musu da auran Annur din kuma ajigawa zama ayi bikin sun nuna farin cikin su kuma insha Allah duk zasuje biki.

๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ๐Ÿ”ป๐Ÿ”บ
Alhmdullh itama Amarya sunje south African ita da Abban ta sun sulhunta shida yayarsa kuma ya dawo gida ya daidaita da dukkan in uwa harda wadanda be saniba.
Kuma duk sun tarbesu musamman amal yrsu.kuma ya shaida musu bikin Amal din suma.
Alhmdullh komai ya daidai ta kuma kowa ya samu nutsuwa acikin zukatansu.

Amare su sakina da Nana koda yaushe suna waya da Amal kuma dukkan nunsu suna jin ddi agidan mazajan nasu.

Har yanxu Amal taba gurin Anty Humairah dan tariketa ta hana kowa ita dan tadau alkawarin ita zata aurar da ita.

Biki ya kan kama saura sati daya.
Gaba daya sun tattaro sun dawo gidan Abban Amal din.duk wanda zaizo nan yake sauka.
Sannan ummin Annur tazo Har gida ta nemi yafiyar Amal da Abban ta kuma sunyafe mata Har Abba ke shaida mata sakin hajiya ladi da yayi.

Gida kuwa yacika ba masaka tsinke yn uwa da abokan arziki Amarya tasha gyara ta koma tamkar sarauniyar sai faman kayalli take tana zuba kamshi.
Dangin Annur sun kawo lefe har akwati dozon biyu,da mukullin mota.anyi musu tarba ta mutunci an karramasu kuma suma sunji dadin hakan.


Yaune yakama aka fara bikin Amal, baaaina tsaya ina gaya muku irin haduwar da bikin yayi ba'a magana.
Kudi kuwa sunyi kuka an kashe kudi sosai.
Hanne ma tazo itama tayi aurenta dan lokacinma cikine da ita karami.

Biki yaci sunan sa biki duk inda ake neman hadaddan biki toh wannan biki yakai.
Kamar yanda aka tsara ranar lahadi mutane suka tazu kofar gidan Alhaji muktar dan daurin auran yarsa Amal.
Manyan mutane sun halacci wannan biki,bayan an gama daurin aure uncle Hakeem ya shirya musu hadaddiyar walima anci ansha kuma angode Allah.
Saide fatan Allah ubngiji ya sanya alkhari ya kawo yaya nagari

Please Login or Register in order to submit comment