Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta sanarwa da abunda ya samu Abban nata.
Dasauri ta shiga contact din wayar da neman numb.uncle Hakeem dake Dubai. Cikin sa'a kuwa ta samu.
Kiranshi tashiga yi ba sassautawa.saida tayi mai kusan missed call 5 amma ba'a dagaba.
Duk da haka bata hakura taci gaba da kiran nasa.
Cikin sa'a kuwa aka dauka.
Assalamu Alaikoum!
Aka fada cikin muryar bacci.
Kuka ta fashe dashi
Wanda hakanne yayi sanadiyar sa Hakeem mikewa zaune daga kuncan da yake.
Lfy Amal ce,menene ya faru meya samu Abban naki.
Dakyar yasamu tayi shiru.cikin murya mai rawa tashiga yimasa bayanin abunda yafaru.
Humairah ce tashiga tamfayar lafiya ganin mijin nata ya tashi cikin dare yana waya kuma hankalin sa atashe.
Kinga Amal kiyi shiru kidena kuka.jeki hadani dashi Dr.din muyi magan pls tashi yi Sauri.

Mikewa tayi tashiga neman Dr.din.amma wata nurse ta gaya mata yariga ya tafi gida saide abata numb.ninshi.
Nandanan ta amsa jikinta na rawa ta turawa Hakeem din.
Kiranta yayi ta shaida masa saide ya kira Dr.ga numb.dinshi nan yatafi gida.
Nan yace mata bara ya kira Dr.din yaji yanda ta bakinsa.sannan ya kashe wayar.

Dr.na shirin kwanciya ya gama duk abunda zaiyi yaji wayar shi na ringing. Da kamar bazai dagaba ganin sabuwar numb.ne yasa shi dagawa.
Bayan sun gaisa dashi Dr. Din yayi masa bayanin shine uncle din yarinyar da takawo babanta yasha poison. Nan ya gane kuma yakuma yimasa duk bayani yanda zai gane.
Hakeem ne yace da Dr.dole sai nan da 5 din za aeyi masa aikin.ko zai iya huce hakan.
Dr.ne yace eh zai iya kaiwa 10:00am.
Hakeem yace toh Dr.munasan hada mana takardu dan Allah munasan ayi masa aikin anan Dubai. Yanxu saina turo wani aje ayi musu bucking da wuri inde ba matsala.
Yauwa gaskiya ka bada shawara mekyau yanxu ba matsala zan hada komai inyaje asibitin saiya nemu Dr.James zai bashi komai sai ya sameni a airport ayi musu bucking din.
Ywwa Dr nagode sosai Allah saka da alheri.

Cikin Lokacin dabe huce 30mins ba aka gama komai.
Nan Hakeem ya umarci Amal da tafi wani dazai aiko ya kaita gida ta dauki duk abun zata dauka kuma ta kwaso duk wani Abu me amfani na Abban nata.nanda 2:30am jirgin su zai tashi.
Nanta nufi bakin gate din itada hanne dan jiran Wanda zai dauke sun.
Amma hanne hankalinta duk ya tashi dan zasu rabu da amal din.
Suna nan tsaye saiga wani mutum ya karaso wajansu amota ya tambayesu ko sune su Amal eh suka cemasa tareda shiga motar.
Kwantancan areas sukayimasa kai tsaye ya kaisu ya gaya mata da tayi Sauri nanda wasu yn lokaci zasu tafi airport zai huce da ita.

Cikin gidan suka nufa.ta bawa hanne umarnin ta hado bata duk wani abunda tasan tana amfani dashi.ta kaisu cikin mota.
Upstairs ta haura da gudu ta nufi dakin Abba. Karamin trolley ta jaho,duk inda tasan yana anje wasu mahimman takardunsa da ATM dinsa.laptop da duk mukullayen sa.sanna ta kulle dakin ta sauko.nan sukaci karo da hanne ta shigo daga kai kayan Amal motar.
Yauwa hanne kinkai bara mutafi.
Haba Amal ko kaya mana kibari ki canza da Allah kawo nakai kayan ki gyara jikinki.
Mikamata mata kayan tayi tanufi dakinta da gudu,dan toilet ta nufa dan dauraye fuskarta. Sannan ta fito Riga da wando ta sanya.tayi rolling din Vail din kayan.fitowa tayi tareda janyo dakin.
A can bakin gate ta tarda hanne.rungume juna sukayi suna kuka.
Hanne yanxu ke kadai zaki zauna ko bakyjin tsoro.
Aa amal zan tafi gidan wata yr uwarmu Dana sani.inyaso inkundawo sai nadawo.Amal Allah ya bada sa'a a wannan aiki da za'ae.ameen tace da ita tareda yin hanyar waje.Amal ga wayar taki.da Sauri ta dawo aa hanne ki rike zamuna waya dake.kuma dan Allah duk wanda ya tambayeki kice masa Abbana ya rasu kinji.ki kulle gidan inzaki tafi.hannu ta zura cikin jakar hannunta,gashi kibawa me gadi wannan shima ki gaya masa yace Abba yarasu duk Wanda ya tambayeshi.dan Allah hanne ga amanar komai nan ahanun Ku.zan dinga turo muku kudi kinji.
Suna kuka suka rabu abun tausayi.
Tanaji tana gani motar su Amal ta tashi zuwa airport.

Ita kuwa hajiya ladi sai misalin 1:00am sannan ta isa kano.kai tsaye gidan su Annur ta nufa.dama sunyi waya da hajiya tana kan hanya.
Tana karasowa Me gadi ya bude mata gate.hajiya dama da tasan da shigowa gidan nasu.ita ta tarbeta suka huce dakinta.
Nan tafara gaya mata duk abunda ya faru.
Haba jamila gaskiya kinyi wawta yanxu me kike tunanin mutane zasuce.mijinki ya mutu kina wani garin gaskiya zaki bata mana plan namu.
Amma inde ya mutu ae shikenan kin cikamin burini.dani muktar yake zancan wlh.yanxu ki kwanta ki huta karkisa komai a ranki.

Lokacin dasu Amal suka iso airport din 2:25am saura mintina kalilan jirgin su ya tashi.da Sauri aka fito da kayan nasu.dama anriga ankawo Abban tun dazu.nan sukayi sallama da likitocin da mutumin kowa yana mishi bata alheri.
Daidai lokacin da aka sanya jirgi yatashi zuwa Dubai.

Saida Amal taji jirgin ya tashi hankalinta ya kwanta,sassanyar anjiyar zuciya ta sauke tareda jingina kanta jikin kujerar.lumshe idanunta tayi tana tunawa da irin rayuwarta da sukayi da Abban ta.tabbas ambanta ya mutu zatayi babban rashi.tana wannan tunanin bacci barawo ya sace ta..

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

100-105

Ba ita ta farkaba sai suka kusa sauka.
Tana tashi ido suka hada da wata budurwa.murmushi tayi mata.itama mayar mata tayi.idanun Amal har yanxu a kumbure suke saboda kukan data sha.
Gyara zamanta tayi.
Wancan budurwar tace da ita kinsha bacci.
Wlh kuwa,aiko danayi baccin harna ji ddin jikinna.
Allah Sarki ko baki da lafiya ne?
Aa wallahi lafiya ta qlau Abbana nede bashida lfyn.
Ayyah Allah ya sauwake amma da alama kuka kikayi dan ga idanunki nan duk sun kumbura.
Wallahi hankali nane ya tashi sosai.ameen na gode.
Hannu ta mika mata suka gaisa.
Ni sunana Sakina Abdulsalam.kuma ina zaune anan garin jigawa.ina karatune a Dubai amma nakusan gamawa.naxo bikin yayana ne.
Allah Sarki.
Nikuma sunana Fatima muktar. Amma ana kirana da Amal.nimade a jigawan nake.yanxu de abunda zai kaini Dubai Abba ne bashida lafiya shine za'a yimasa aiki.
Allah ubngiji ya sauwake Amal. Insha Allah inde zan kawo miki ziyara.
Toh na gode.
Nande sukaci gaba da hira.
Har lokacin saukarsu yayi.

6:00am
Lokacinne jirgin nasu ya sauka anan Dubai.kai tsaye asibitin suka nufa dashi.anan suka tarda uncle Hakeem da Aunty Humairah. Da gudu tayi gurin su tana kuka.lallashinta suka shiga yi.
Hakeem asibitin ya bisu.
Itakuma Aunty Humairah kayan duk suka sanya a mota sannan suka nufi gida.

Ana isa dashi asibitin dama Hakeem ya Riga yayi duk abunda yakamata yayi.nan da nan likitocin suka amshe shi,kai tsaye theatre sukayi dashi dan ceto ransa.
Nan suka umarci Hakeem daya tafi tunda ya saka numb.dinsa in suka gama zasu neme shi.danshi ko jinya ba'ayi ko kwana saide kuxo kuga patient Ku tafi.komai daya kamata anayi yiwa mutun.
Haka Hakeem ya nufo gida.badan yaso ba saide dan yabi dokar asibiti.

Suna isa gidan.komai suka fito dashi.
Dakin aka nuna mata.dan baxata taba mancewa da dakin da tayi rayuwa acikisaba.komai yananan.saide yn gyare gyaran daya sha.
Trolley dinta ta anje tare dana Abba.
Kayanta ta tube ta nufi toilet danyi wanka ko taji ddin jikinta.koda ta shiga zama tayi cikin ruwan dumi tana jin dadin hakan.

Shikuwa Annur bayan ya idar da sallah daranshi.gadansa ya haye dan yana cikin farin ciki.bacci yasha harda munshari.
Saida asbah tayi sanna ya tashi danyin sallah.
Yana tashi wayar shi ya dauka dan tashin Amal tayi sallah.
kiranta ya shigayi amma shiru ba'a dagaba.
Saiya yi tunanin ko sallah take yi. Sai kawai yayi alwala ya nufi masallaci.
Bayan ya dawo daga masallaci nanma yashiga kiran layin nata amma har lokacin bata dagaba.
Damuwa ya fara shiga dan ji yake kamar ya tashi yayi tsuntsuwa yaje gurinnata ya ganta.yana nan zaune har 6am tayi.
Mikewa yayi dan yin wanka yatafi office..

Ita kuwa hanne tunda ta koma cikin gidan kuka tayi sosai dan bakin cikin rabuwa dasu Amal,har saida tayi mai isarta.sannan ta mike tayo alwala tayi sallah dan taya Amal addu'ar Neman waraka wa Abban ta.
Bayan ta idar tana nan zaune tana jan casbahha,bacci ya dauke ta.
Dama ga hanne da nauyin bacci.
Nan ta anje wayar kan gado tareda kudin.
Har Lokacin da Annur yaketa kira amma hanne batajiba saboda baccin da takeyi.

Haka bangaran su hjy ladi.tunda suka kwanta bacci basu farka ba,dama sallah ba damunsu tayi ba.bare ta asvah.
Daki guda hajiya bilki ta bama ladi ta yi zaman ta aciki.


Bayan Amal ta fito daga toilet din wanka tayi tare da dauro alwala dan gabatar da sallah ta ta asbah.
Tana fitowa.zani ta daura tareda sanya hijab dinta.
Saida ta idar da sallah sannan ta zauna tana ta mikawa Allah kukanta akan ya baima Abban ta lafiya.
Tadau tsawan lokaci tana faman addu'a.
Sannan ta mike.mai ta shafa.sannan ta gyara gashinta.doguwar Riga ta sanya me gyau ta English wears daga sama tadan kamata kadan milk color. Tayi mata kyau sosai duk da batayi wani Makeup ba harta dan fada kwana daya gal.murmushi tayi tana kallon kanta a mu dubi.
Kayanta ta yi musu ma'ajya sannan tadan shigida kadan nan danan wani saban bancin yakuma dauke ta.
Bata dau lokaci dayin bacci ba Aunty Humairah ta shigo dakin da sallama.
Ganin ta kwance kan gado tana bacci ya bata tausayi.
Karasowa tayi cikin dakin Har bakin gadon da take kwance.
Gyara mata kwanciyar tayi, tare da ja mata blanket din Har wajan kirjinta.
Tsayawa tayi tana karema fuskarta kallo. Tana mutukar kaunar Amal da kuma tausayinta.daga karshe fitowa tayi ta barta dan tana bukatar Hutu sosai.
Fitowa tayi tare da jawo mata kofar dakin.
Ganin Hakeem zaune kan kujera yayi tagumi yasanya ta kara sowa wajansa.
Lafiya ya jikin nasa.tafada tare da zama kusa da shi.
Yanxu de aiki za'ae masa,bamu da tacewa saide mu tayashi da addu'a dan ko motsi bayayi wallahi yanda kikasan gawa.nicewama nayi anya be mutuba.
Haba kaima yazakace haka ae inya mutu baza su baka wahala da tun a can Nigeria za'a ce dasu ya mutun.
Toh komade yayane Allah ne masani.Allah ubangiji ya tashi kafadunsa.
Ameen tace.
Yawwa ina Amal din take?
Wallahi tayi bacci.bakaga yanda hankalin ta yayi mugun tashiba.
Wallahi nima naga hakan,gwara da tasamu tayi baccin ko ta samu saukin jikin nata.
Dan kwanaki ya fadamun itama ba cikakkiyar lafiya gareta ba.
Allah de ya sauwake..

7:00am

Annur yabar gida zuwa office dan duk hankali sa yagama tashi kasan cewar Amal taki daukar wayarsa.hakan ya sanya ko abinci be Ciba ya fita.dan bayasan yayi latti.
Yana tafiya yana kuma kiran nata amma Har yanxu shiru.
Ahaka Har ya isa.kai tsaye office ya nufa,koda ya shiga kasa zama yayi yanata trying din numb.tata.
Rigarsa ta sama ya cire tareda gayara tie dinsa.
Yana cikin wannan Abu na tsawan lokaci sannan Fareeda ta shigo bayan sun gaisane ta bashi wasu files.sannan ta sanar masa yana da meeting 1 to 3:00pm.da wasu mutanan kasar Uganda.
OK ba matsala yace da ita.sannan ya hakura da kiran nata ya tambata inde taga missed call dinsa zata kira shi.nan ya shiga aikin abansa.

Karfe 10am,akayi sa'ar gamawa Alh muktar operation. Yanxu haka yana dakin da aka bashi.
Yana nan kwance kan gado.ga na'urori nan kala kala acikin dakin.
An sanya masa robar oxygen a hancinsa.
Amma ko motsi bayayi kawai gashinan de kwance amma yana numfashi .
Ita kuwa hanne sai bakwai saura ta barka.
Sallati ta fara,mikewa tayi tanufi toilet tayi alwala ta dawo ta tada sallah. Bayan ta idar mikewa tayi tanufi kitchen da hada abunda zataci.
Kayan wanke wanke tafa hadawa nan taga abincin da Abba yace yazama yellow shar.nan ta saka plate din da auran abinci takai shara.sanna ta wanke kwanikan tas ta gyrara kitchen din.
Sannan ta hada abunda zata karya.
Nan tashiga gyara gidan dan batasan ta barshi bata gyaraba.
Tasha aiki sosai sai wajan 11 sannan ta gama.
Toilet ta nufa danyin wanka saida ta gama shirinta tsaf.sannan tahau hada kayanta.
Suma ta dibi daidai wa daida sannan ta dauki abunda zata bukata.
Bayan ta gamane.tanufi kitchen ta kwashe duk wani abunda zai lalace kamar su nama,lemo etc.
Tahadasu guri guda sanan ta kullo kitchen din.tabi ta kashe duk wani socket gudun gobara.

Saida tayi sallar karfe daya sannan ta hado kayanta dan tafiya.
Harta kai bakin kofa zata fita.saita hango wayar da Amal ta bata da Sauri ta karasa bakin gadon ta dauka tare da dannawa.
Agogon wayar ne ya nuna 1:34.
Lokacinne taga missed call din Annur guda 41.
Ido ta zaro wannan yaushe ya kira,toh karde ace tana bacci.nan dannan tabi numb.amma shi ba'a dauka ba.saida ta kira kusan sau biyar amma no answer.
Sanya wayar tayi cikin jakar hannunta sannan ta fice daga gidan.
Bakin gate tagamu da mai gadi.
Bayan sun gaisa nan tamai bayanin komai.kuma tace yacigaba da gardin sa zatana kawo mai kudi akan lokaci.
Kudi ta mikamai tace ga wannan yana cin abinci dasu.nan ma godiya yay tayi sannan yayima Alh.addu'a.
Itade hanne ameen kawai take cewa.
Sannan tayi mai sallama ta tafi.


11:10am
Shine daidai lokacin da Amal ta farka daga bacci.da sallati ta farka.sannan ta mike tare da gyara Vail din kanta.
Falo ta fito ta nufi kan kujera ta zauna ganin ba kowa a ciki.
Humairah ce tafito daga kicin.ganin Amal zaune kan kujera yasa ta karaso wajan tana murmushi,Amal kin tashi?.
Eh Anty ina yini barka da gida.
Lfylau Amal ya jikin Abban.
Insha Allah Anty da sauki.
Toh Allah yasa Amal. Yanxu kije ki wanke bakinki a breakfast nan kan dinning kije kici.
Yanxu uncle dinki yamin waya,Har anjima Abban naki aikin kuma anyi sa'a yanxu inya dawo zamuje.yafita ba dadewa zaiyi ba kintashi kinji.
Cike da farin ciki Amal tanufi daki dan yin brush taci abinci.

Suma su hajiya ladin sai kusan 11 din suka tashi.ko wacce fitowa tayi cikin ado da takunta na kasaita.
Bayan sun gaisa dining suka nufa danyin breakfast.
Wato Annur yau kokaryawa baiba yafita office, zai dawo ya same ni.
Auu! Har Annur ya fara aiki.
Wlh ya fara aiki.kinga ko yaro ya girma sai kuma aure.
Murmushi hjy ladi tayi danjin an ambaci aure.
Tasan inta auri Annur ba karamin dacewa tayiba.
Ita kuwa hajiya bilki murmushi mugunta tayi tana kallon ladi amatsayin jaka.danko karan haukane ya cijeta bazata aurama Annur hjy.ladi ba saide ya mutu ba aure.

MUJE ZUWA๐Ÿ˜œ๐Ÿ˜œ

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

110-115

Sunan zaune suna hira suna ta faman dariya kamar mahaukata.

Ita kuwa Amal,bayan ta idar da sallah falon ta fito.
Bata tarda kowa ba dan haka dinning din ta nufa dan cin abinci.
Zama tayi tareda zuba dan kadan,kawai zataci abincinne badan tanajin yinwaba.
Nan ta zauna tanaci tana tunane tunanan data saba.
Har Humairah ta fito ta zauna kusa da ita amma bata saniba.

Amal! Takirayi Sunanta tareda kamo hannunta.
Kici abincin ki koshi dukda nasan ba wani cin abinci kikeba.
Amma ya kamata ki dinga ci.
Inkin gama uncle dinki na kiranki.
Toh Anty bara nagama zanxo.

Mikewa Humairah tayi takoma falon.
Ita kuwa Amal dan danan tagama cin abincin dan gani take za'a yima ta wata magana ne Dan gane da Abban ta.

Falon ta shiga tareda sallama sannan ta zauna kusa da kafafun Humairah akan carpet din dakin.

Amal kinci abinci?
Gyada mai kai tayi tareda cewa eh! Kanta a kasa tana wasa da yatsun hannunta.
Yauwa magana nakesan yi dake.
Kinga yanda jikin Abban ki yake.
Kuma nasan ya Samar dake cewar,zai taho dake nan dan cigaban karatunki.munyi maganar nan dashi kafin koma warsa.
Kuma anyi duk abunda yakamata.
Kuma a Lokacin da aka dauka 15th of dis month zaki fara zuwa.
Kuma yau kinga firsts.
Dan haka komai zai tafi daidai yanda Abban ki yake so insha Allah.
Gobe in Allah ya kaimu zamu kaiki ki siya duk kan abunda kk bukata na karatunki.
Tunda ga kan kayan sawa,takalma,jaka,dade sauran su.
Ki kwantar da hankalin ki.
Ki nutsu kiyi karatunki kamar kina gaban Abban ki.
Na tambata shima zaiyi alfari da hakan.
Kina jina ?.

Kai tagyada masa tareda fadin,
Insha Allah uncle zan kasance me kula da duk abunda kafada kuma zanyi karatu kamar yanda Abbana yake bukata insha Allah nadau wannan alkawarin.

Yauwa Amal,ko kefa Allah yayi miki albarka cewar Anty Humairah tare da shafa kan Amal din.

Sun jima nan zaune suna hira.Har Amal ta fara jin bacci sannan tayi musu sallama ta nufi dakin ta.

Nan suma suka ci gaba da yanda zasu kula da ita Har zuwa warkewar Abban nata.


10:00am

Shine tymdin da Amal ta tashi daga bcci bayan ta koma daga sallar asbh da tayi.
Tana farkawa dakinta ta gyara tsaf.sannan ta shiga toilet tayi wanka.
Bayan tagama shirinta cikin bakin jeans da top White me photo babie doll pink a gaban rigar.
Gashinta takama ta daure da bakin ribbon.
Karamin bakin Vail ta daure kanta dashi gashinta ya zubo Har bayanta.

Tana fitowa daga dakin.kai tsaye wani dan corridor ta nufa da zai sadata da dakin Anty Humairah dan bata ganta a falo ba,kuma bataji duriyarta a kitchen ba.

Tana karasawa tayi knocking amma ba'a bata iznin shigaba.
Hakan ya sanya tayi zatan ko tana toilet.
Da sallama ta shiga.
Jin karan ruwa a toilet ya tabbata mata da wanka take.

Hakanne ya bata daman,gyaramata dakin duk da ba wani dirty yayiba dan Anty Humairah akwai tsafta.
Har tagama amma bata fitoba.

Fita tayi tanufi dining dan yinwa takeji.
Zama tayi ta shiga cin abinci.
Tunda bataga uncle ba tasan ya fita aiki.
Cikin konciyar hankalin take cin abincin ta.
Tanan zaune Anty Humairah ta fito.cikin shirinta na fita unguwa.
Zama tayi kan kujera tareda sakamma Amal din murmushi.
Itama murmushi tayi mata tareda fadin Anty ina kwana.
Lfylau Amal.
Dama tunda na fito naga angyaramin dakin nasan kin tashi.

Kai Anty dakin daba wani dirty gareshiba.
Eh! Kinga kuwa ai kin sa yakuma yimin kyau.
Lallai Anty kema de,dan nadan gyara miki daki.
Eh! Wallahi kam na gode.
Dariya tayi sosai, ta kuma tuna irin uban aikin da take sha agidan.

Kiyi maxa kigama zamuje asibitin daga nan kuma zamu huce masu.
Tun dazu uncle dinki ya tafi shima office

Toh Anty!tace da ita.
Nan danan ta karasa cin abincin ta kwashe kwanikan.
Daki tanufa ta dora black Cort ajikinta.tareda rolling black Vail.ta dauki jakarta karama baka.
Sannan tasa takalminta mekyau plat me igiyoyi.tayi kyau sosai.
Fitowa tayi tare da janyo kofar,
Sannan suka fita.

Yauma Annur banyi breakfast ba ya fita office. Dan gaba daya hankalin sa na kan Amal. Shi tunanin yanda zai tafi Dubai din yake.ga office ga kuma umminshi sune suka tukareshi.
Yana zaune kan kujera a cikin office dinsa kanshi duk yadau caji.
Kabeer ne yayi sallama tare da shigowa office din.
Kara sowa yayi da murmushi a fuskarsa yana kallon abokin nasa.
Zama yayi kan kujerar yana mamakin abokin nasa da ko amsamai sallmarsa beyiba saboda duniyar tunanin daya tafi.
Table din gabansa ya buga yana kiran sunan sa.
A firgice ya dawo daidai.

Kabeer dake masa kallon tuhuma.yace Annur lafiyarka kuwa.kace baka da aure Amma meke damaunka Har kake irin wannan tunani haka.
Dama kwana biyun nan ina lura dakai kana cikin damuwa sosai.

Ammm! Kabeer kenan tabbas ina cikin damuwa Amma insha Allah zanci gaba dayin addu'a kamar yanda na saba.
Ya ake ciki nifa yinwa nakeji danyau late na fito ko breakfast ban samu nayiba.

Ohk! To Allah ya kauta.
Mikewa yayi tareda fadin sauka taso muje kaci abincin.

Shima mikewan yayi tareda daukar fone dinshi.sannan suka fito.
Fareeda ya sama ya sanar da ita duk Wanda yaxo yajira shi.
Sanan suka huce,zuwa cin abinci.


Tana zuwa dinning din dancin abinci,
Yauma still Annur baiyi breakfast ba ya fita.toh me yake nufi lallai yarannan ya rainani.
Zai dawo ya sameni.

Gurin hajiya ladi ta koma falo ta zauna.tana kallonta.

Hajiya ladi ce ta gyara zama tare da kallan hjy.Bilki.
Nifa Har yanxu naga shiru baki sanar dani matsayina agurinkiba.

Kallan ta tayi da mamaki.haba jamila bakya ganin raina abace yake.
Kuma duka duka kwana nawa da mutuwar mijin naki.
Mikewa tayi tabar gurin dan ta bata mata rai.

Murmushi tayi ta kuma gyara zamanta saman kujera. Ai gwara ki gayamin dan bansan Abun yadau lokaci. Tabbas saina auri Annur inkuma anki asiri ya tonu kowa ya huta.ta fada tareda mikewa tabar falon ita.

Hajiya bilki data labe dan taji abbunta zata fada.ta tsaya tareda rike baki.
Lallai ma yarinyar nan,ni zaki tunama asiri kice barin duniyar kike sha'awar yi.


Suna fita daga gida asibitin suka nufa.parking din motar ta tayi sannan suka shiga.
Already sunsan dakin.elevator suka hau dan suyi saurin shiga.dan dakin a third floor yake.
Nan danan suka karasa.
Dakin suka bude tareda shiga.yauma kwance yake yanda suka tardashi jiya.
Saide an rage wasu na'urorin ba kamar jiyaba.
Amal ce takuma matsawa kusada Glass din dayake ciki.
Hawaye ne ya shiga bin kumatunta.
Muryar ta na rawa tashiga fadin Allah ya baka lafiya Abbana.
Addu'a tashiga yimasa.
Sosai ta jima agurin.kafin ta juyo ga Anty Humairah.
Mutafi Anty.
Mikewa tayi tareda fadin yauma kukan kikayi ko.
Da Sauri ta guge wata sabuwar kallon data fito mata.
Insha Allah bazan karaba pls karki gayama uncle.

Murmushi ta kuma sakar mata.tareda rungume ta.bazan gayamaiba kinji Amal.

Hannunta taruko sannan suka fito daga asibitin...


I dedicated did page to u all my fans.wallahi nima ina kaunar Ku kamar yanda kuke kaunata.Allah ubngiji ya barmu tare.
I rwwly lovs u to d moon nd bck.๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐ŸŒน


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

105-110

Suna cin abincin suna taba hira Har suka gama.

Lokacin da Annur ya fito daga meeting.kai tsaye office dinshi ya nufa dan gaba daya hankalin sa yana gurin Amal dinsa.Allah Allah yake kar ta ga missed call dinshi kuma ta kira shi suna meeting.
Yana shiga fone din tashi ya nufa dake anje kan sofa din office din.
Salati ya saki ganin 5 missed call na Amal.
Jikinshi Har rawa yakedan burinshi ya kirata..

Ita kuwa hanne tana isa can gidan da zata je.
Bata sha wahalan gane gidan ba.amma ta dade bata jeba.
Da sallamarta tashiga cikin gidan ba'a amsa mataba.hakan yasa ta zauna kan wani dan turmi a tsakar gidan.
Batafi minti biyuba da zama wata dattijuwa ta fito daga bandaki hannunta rike da buta.
Tsayawa tayi tana karema hanne kallo.
Wanake gani haka kamar hanne.
Hanne da murmushi a fuskarta ta durkasa kasa tareda fadin nice Gwaggo.
Anya hanne ba batan hanya kikayi,shikenan haka zumunci yace daga Inno ta rasu sai kibar zumunci.wlh baki da kirki.
Wallahi ina nan,nasameku lafiya.
Lafiya muke ya kowada kuwa hanne lafiya wallahi.
Toh bismillh shigo mana.
Tayata daukar kayan tayi tareda shiga cikin dakin.
Abakin gado suka zauna.kuma gaisawa sukayi sannan ta dauko mata abinci da ruwa.
Bayan taci ta koshi.nan tashiga bawa Gwaggo labarin komai dan bazata boye mataba.kawar kakartace sosai.
Dantane yasamu kudi shine ya maidota cikin gari.
Sosai Gwaggo ta tausayama Amal da Abban ta.kuma ta cewa hanne ba komai ta zauna Har Lokacin da wowarsu.nan hanne ta dauko duk abunda ta taho da shi tabama Gwaggo, sosai tayi mata godiya.

Tana zaune a dakin,ita kuma Gwaggo ta fita tsakar gida.
Wayar ce tahau ringing da Sauri ta dauka ganin an rubuta Annur ta yi saurin daga.tare da sallama.

Anjiyar zuciya ya anje jin an daga wayar.
Haba Amal me kuma yayi zafi tun dazu ina faman kiranki baki daga ba.
Kayi hakuri ba Amal din bace hanne ce.

Ohk! Hanne ce.ina Amal din bata waya pls.
Kayi hakuri Amal batanan sun tafi Dubai.

Wani saban gumine ya keto masa.besan Lokacin daya zauna ba.
Dubai kuma lafiya de ko.

Abban tane ya rasu shine,yn uwansu suka tafi da ita.
Innalillahi wa inna ilaihir raji'un.
Yaushe hakan ya faru.

Jiya da safe.
Allah ubngiji ya jikansa.Amma insha Allah gobe da safe zan shigo jigawan.

Aa bama saika zoba,dan basu yi zaman makokiba.gidanma an rufeshi.nima bana gidan nakoma gidan mu.

Toh yanzu hanne dan Allah ya zansamu numb.din Amal ki taimaka min.gaskiya nima bata kirani ba tunda taje Amma inta kira saina baka.

Toh nagode hanne sai anjima.bai jira me zataceba ya kashe wayar dan gaba daya kansa ya kwance.taya haka amma bara ya kira Uthman naji.
Yana karinsa ya dauka.
Bayan sun gaisa yake gaya masa Abban Amal ya rasu.
Shima kansa yaji mutuwar.
Yaushe ya tambaya.
Wallahi yanxunnan yar aikin nan tasu take gayamin.
Pls kaje gidan nasu kadubamin dan Allah.
Ohk ba dumuwa insha Allah.
Sannan sukayi sallama.


Tana gama breakfast dinta suka dawo falon suka zauna itada Anty Humairah. Dan ita burinta uncle Hakeem ya dawo taje taga Abbanta.
Sunanan zaune sukaji karan bell en kofa.
Da Sauri Amal ta mike dan bude kofar.
Tana budewa ya Sakar mata murmushi.
Kunya tadanji sannan ta gaida shi.
Yar gidan Abba har an tashi daga bacci.
Eh.to ai yanzu zamuje adubo shi.maxa kije ki shirya.
Uncle aina shirya kai muke jira.
Toh ina Humairah. Itama fitowa tayi tareda cewa gani nan nima sai mu huce.
Yanda tayi maganar da barkwanci.
Hakan yasa dukansu sauka sanya dariya.
Duk suna yin hakanne dan Amal ta samu kwanciyar hankali.
Dukansu suka dunguma cikin motar uncle din suka tafi asibitin.

Basu lokaci ba suka iso asibitin sunata barkwanci a motar.
Parking uncle yayi da motar sannan suka fito dukkansu.
Cikin asibitin suka shiga,kai tsaye bangaran marassa lafiya suka nufa.
Fone dinshi ya dauko dan duba numb room din da yake.
Basu dau lokaci ba suka samu dakin.
Ciki suka shiga.Amma ba'a bari a karasa inda yake saide su hangoshi ta cikin wani glass da aka sakashi,likitocin ne kawai ke shiga.
Amal na ganin Abban a cikin wannan hali ta fada jikin Humairah

Please Login or Register in order to submit comment