Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ita tareda fadin Wash Allah! Ummina sannu da gida.
Ywwa Annur ya office din.
Alhmdullh amma na gaji sosai wlh.
Sai hakuri ahankali zaka saba insha Allah karka samu damuwa kaji.
Insha Allah Ummi. Mikomai abinci tayi yahau ci suna dan hira jefi jefi.


Tana shiga dakinta ta zauna dan gabaki daya bataji dadin hakan daya faro ba.yanxu me Abba zai ce idan ya shigo.da wannan tunanin tashiga toilet danyin alwala.
Sai bayan tayi sallah sannan ta tuna da numb.Annur.
Mikewa tayi tashiga sakawa bayan tagamane tayi save da sunan sa dan batasan me zata rubutaba.tana kokarin kiransa taji Abba na kiranta.
Cikin rawar jiki ta wurga fone din karshan gado.fitowa tayi sanye da hijab a jikinta.
Abba sannu da zuwa.
Ywwa yaki inasan magana dake.
Zama yayi akan kujera yana facing dinsa.
Itama zama tayi kusa da shi.
Amal wanene wannan yaran da naganku tsaye dashi a waje.
Am! Abba dama lokacin da na kwanta a asibiti shida mamansu suke kula dani Har abinci suke bani shine yaxo yakuma dubani.
Shiru yayi nadan lokaci sannan yace da ita.
Amma baki gayamin ba nayi musu godiya ba.itama shiru tayi kanta a kasa.
Toh Allah saka musu da alkhari kinji.
Ameen tace dashi.
Lokacin ne hajiya ta sauko ta samesu a falon zaune.
Barkanku da hutawa uba da yrshi.Alh. ne yayi murmushi tareda ce barknki de.
Amal abincin yayi.
Eh tace da ita.
Ywwa bara naje nayi serving dinku.
Aa Abba kadai za'a zuvama tun dazu mukaci namu.
OK ba damuwa.
Mikewa tayi da Sauri tayi hanyar danin din.ta bude macaroni dinta sai kamshi ke tashi.
Miyar tuwon Alh.ta bude batare da kowa na ganiba ta barbada wata kawa guda daya sanan tasa hannun ta ta juwa.rufewa tayi sannan ta shiga kitchen din hannunta ta wanke tas ,sannan ta fito.
Kallon inda suke zaune tayi sannan tace Alh.kataso mana kaci abincin.
Saina dawo daga sallah insha yace da ita batare daya kalle taba yana duba mail a wayarsa.
Komawa tayi tana murmushi ta zauna tareda cin abincin ta San ranta sannan ta mike.tayi dakinta cike da farin ciki.

Amal data koma daki key tasan ya a kofar tata sanan ta koma saman gadonta takwanta tareda janyo wayarta,dan kiran Annur din.

Shikuma lokacin da Uthman yabar gidan su Amal. Annur ya kira ya shaida masa da abunda ya faru tsakaninsa da Amal din dakuma Abban ta.
Nan yaji dadi sosai kuma yayi masa godiya.
Tunda Uthman ya sanar dashi cewa Amal zata kirasa. Yashiga daki dan jiran kiranta amma shiru.Har yaje yayi sallar insha ya dawo amma bata kira ba.hakan yasa shi cikin da muwa dan yana bukatar jin muryar ta.

Tana kiran shi badau lokaciba ya daga.
Yasan da Amal dinsace zata kirasa da sabuwar numb.
Cikin muryar ta me sanyi tayi masa sallama kamar batasan yin magana.
Nan yaji wata kasala ta saukar masa.lumshe idanun sa yayi tareda yima Allah godiya daya kayatar yakuma halicci abubuwa kyawawa masu sanya niwadi.
Shima amsa mata sallamar yayi.
Sanan shiru ya ratsa na waso yn lokuta.
Amaaal! Yakira sunan ta da wata iriyar murya.
Bata amsaba illar shirun da tayi masa.
Amal naga alama so kike ki kasheni ko?.
Aa tace dashi tareda jirjiza kanta kamar tana gabansa.
Toh kashe wayar na kira ki kinji Amal ina.
Kashe wayar tayi sanan ya kiranta.
Amal kina jina?
Eh tace dashi.
Toh meyasa bakya sona,ko wani abun nayi wanda bashi dakyau?.wlh ki gayamin duk wani Abu maras kyau da kikasan inayinsa na miki alkawarin a darannan zan gyara dan Allah Amal.
Ji tayi kamar tayi kuka dan tana mutukar tausayin Annur.
Wallahi bakamin komai ba,kuma a iya zaman da nayi dakai ban taba ganin kayi wani Abu maras kyauba.kuma nayarda dakai๐Ÿ’ฏ.
Yaji ddi sosai da irin kalamun da Amal din tayi.
Naji ddi da kika yimin irin wannan shedar.
Amma Amal meyasa baki sona dan Allah ki gayamin.
Idanunta ta rumtse da shima besan irin San datake mai bane shiyasa yake gaya mata irin wannan maganar.
Bance bana sanka bafani.kawai de baka tunanin halin da zamu shiga nan gaba.kasan su Abba baxasu yard......
Haba Amal ya katseta cikin Sauri.kinga inde kina sona shikenan ba abunda zasuyi mutukar Allah ne ya hadamu shikadaine zai iya rabamu.nide burina Amal ki furta Kalmar kina sona ko naji sanyi a raina.
Kunya taji kamar tana gabansa.murmushi ta saki sannan tace wlh kunya nakeji.
Shima murmushi yayi,nasan zakiji nauyin hakan tunda Kalmar ta kasance me tsada agareki musamman danasan yaune karo na farko dazaki fara furta ta gada namiji.
Pls Amal ki gayamin mana pls kinji.
Rufe idanunta tayi tare da furta:
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
You are the one who I can open up to. I feel so comfortable in your presence. I love you my sweetheart.
๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
Tana gama fadar haka tayi maza ta kashe wayar gaba daya.
Shikuwa Annur totally speechless. Dn beyi tsamanin haka daga gurin Amal dinba,besan lokacin da yayi wani ihun dadi ba.mutukar farinci ya bayyana aransa.dan duk wata gajiya da damuwa ya nemeta ya rasa.
Numb.tata yakuma kira.amma yajita switch up.murmushi yayi dan yasan kunyace tasanya ta yin hakan.
Mikewa yayi dan yin alwala yayi sallah rakh biyu dan nuna godiya da farin ciki wa Allah daya bashi Amal..

Ita kuwa tana gama fadar haka ta kashe wayar gaba daya tareda dorata a kirjinta.idanunta ta rufe San Annur na dda shiga cikin rainta.
Mikewa tayi dan zuwa kitchen ta dan zubo abinci.dan bataci komai ba.

Fitowa tayi cikin tsananin farin ciki.tana yo hanyar dinning. Ganin mutum kwance a kasa ya sanyata kurma ihu.
Ihun da tayine ya jawo hankalin yn gidan gabaki daya sukayo waje.
Ganin datayi kamar Abban tane ya sanyata kara sawa wajansa da gudu ta fada kansa tana kuka.

WACECE AMAL ??.

I dedicated dis Page to my lovely,cwt mum.Allah ubngiji ya karamiki lafiya da kwari yasa kigama da duniya lfy.ya cika miki burinki.
Mama ur my angle un earth.ur my life first person,I may fail to express my self about her but she is my life forever.rwwly Lov u ma mumโฃโฃ๐Ÿ˜๐Ÿ˜๐ŸŒท.

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
( Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

85-90

WACECE AMAL.??

ASALI.
Alh.muktar Sunusi dutse.shine ainahin sunan mahaifin Amal.
Su uku iyayensu suka Haifa anan garin dutse.
Hajiya Khadija itace babba,tana aure a sokoto amma tunda take Allah bai bata haihuwa.Har mujinta ya kuma south African da ita dan acan yake aiki.
Sai mace ta biyu mai suna Sadiya ita kuma Allah yayi mata rasuwa tun tana karama.bayan ta rasune aka haifi muktar shine na uku tun daga nan ba'a kara haihuwa agidanba.Har Allah yayma iyayensu rasuwa.
Sai hajiya Khadija ta dauki kaninta tun lokacin yana sokoto.ba laifi sun rike shi tsakani da Allah Har ya gama karatunsa na secondary. Bayan nan ne suka nema masa admission anan university of sokoto.nan ya karanci business administration. Sosai yana da kokari.Har Allah yasa ya kammala kara tunsa.
Bayan nan ne yashiga yin business dinsa Allah ya buda masa.
Wannan kenan dan gane da mahaifin Amal.

Mahaifiyar Amal sunan ta Zainab. Ita kadai iyayanta suka haifa.mahaifin ta da mahaifiyar ta yn asalin fulanin sokoto ne.suna nan zaune a madaidaicin gidansu dan basu da wani arziki.sana arsu shine kiwo.iyayensu ko mata sayarda nono da manshanu ne sana'arsu.Zainab ta taso cikin gata da kulawa agurin iyayenta da kuma yan rugarsu.
Dan tataso da kyau kuma tana da farin jini gurin mutane.
Lokacin da Zainabu sunan da ake kiranta kenan ta dan tasa dan bazata huce shekara 15.suna fita daga cikin rugarsu,au fito cikin gari dan saida nono ita da kawayenta.
Wata rana mahaifin ta sunfita birni dan saida shanunsu,da lokacin babbar sallah ta matso,.nan aka kawo gawarsa sunyi hatsari Allah yayi masa rasuwa.sosai mutanan kauyen sunji mutuwar sa,dan yana da mutukar kyauta da San mutane.bayan anyi arba'in itama mahaifiyar ta Allah ya amshi ranta.sosai Zainabu tayi kukan bakin ciki da rasuwar iyayenta amma haka ta rungume akdara.
Nan rukwanta ya koma hannun baffanta wan babanta.tun daga nan rayuwa ta canxa.kullum cikin tsangwama da kyara,kuma sun rike mata gadanta da iyayenta suka bari.kullum cikin kuka take.batada lokacin kanta saina tallah.Har mutane tausayin ta suke yi.

Wata rana tayi wankanta taci ado da kayansu na filani,ta dauki tallan nono ta,tare da kawayenta dan ranarce za'aci kasuwa agarin nasu.

Nanne suka hadu da muktar shima yaje siyayya.
Tunda ga wannan Lokacin suka saba dashi har soyayya ta shiga tsakaninsu.dan Har suna maganar aure.
Hakanne yasa wata rana muktar binta rigarsu dan sanarwa baffanta.
Bayan sunje yasami baffan nata harya yanda da bayanan sa.yana zuwa ya sanarda matarsa tace fir batasan zanceba wannan aure bazai taba yiwaba.hakan kuwa akayi.dan baffa ya Sanar da muktar ya hakura da Zainabu dan anyi mata miji.


Lokacin da muktar ya sanar da yayarsa batin auransa da Zainabu itama ta yarda amma taso ace yasamu yar birni kuma me ilimi ya aura,Amma tunda itama yarinyar kirki ce Allah sanya alheri tace dashi.
Nan itama ta sanarwa me gidanta.
Shima cewa yayi ae be yarda ba.yariga yagama tsara komai nanda wata guda zai aurama muktar kanwarsa maryam.
Nanfa zance ya rikice dan kuwa bazai taba yiwaba.
Sosai muktar yaji ba ddi dan baxai taba auran wata maryam ba Zainabu yake so kuma itace matarsa.
Nan Alh. Auwalu mijin yayarsa yace inde kuwa muktar bazai auri kanwarsa to dole yabarmai gidansa kuma ya maidomai aduk abunda yasan mallakinsane.
Nanfa kan muktar yakuma daurewa,hankalinsa ya tashi.
Nan yasamu Alh.auwalu ya shaida masa cewa zai auri maryam din da Zainabun shikenan.
Alh.yace besan wannan ba dan baza a hada yr uwarsa da yr talakawaba.
Nan muktar ya tattara duk abunda yasan na shine ya maidama Alh auwalu kayan sa.ya dauki sauran kudinsa Wanda zasu iya isarsa jari.
Kai tsaye rigarsu Zainabu ya nufa.nan yasamu baffan Zainabun ya bashi dukiya me tarin yawa dan yace inya kawo zai aura mai ita,amma insun tafi karsu sake su dawo.
Nankuwa aka daura musu aure muktar ya tafi da Amaryarsa Zainabu.

Nan baffanta ya sanar da mutane ai Zainabu tabi dan birni sun gudu.nan aka rinka tsine mata ana Allah wadai.tun daga lokacin basu kara jin duriyar Zainabu ba.koda dangin mahaifiyar ta sukazo suma hakan aka sanar dasu.sunyi kuka sosai na rashin ta amma haka suka hakura.

Kai tsaye jigawa ya nufa da ita.gida suka kama haya.sannan a hankali ya fara sana'arsa.Har Allah ya buda masa.ya sai gidan kasa.
Sunanan cikin farin ciki da kaunar junan su.
Har sukayi tsawan shekara 2 da aure.amma Allah bai basu haihuwa ba.
Haknna ya fara daga mata hankali amma shike kwantar mata yacemata haihuwa ta Allah ce.
Tunda suka basu danginsu basu kara waiwayarsuba.sunan cikin farin ciki dajin dadi.

Saida sukayi shekara 3 da aure sannan Allah ya bama Zainabu juna biyu.murna gurin muktar basai anfadaba.yayi farin ciki sosai.Har macca yaje dan kara godiya ga Allah.
Zainabu tana nan cikin kulawa dajin ddi.nan Alh ya sami wata bazawara take kula da ita tana kuma tayata aiki.
Sunan wannan mata laraba.
Laraba tanada mutunci da kuma amana nan ta rike Zainabu kamar yar uwa a gareta.

Ranar wata alhamis ranar da muktar bazai taba mantawa da ita aduniyaba.
Ranar ne Zainabu ta tashi da ciwon nakuda.tasha wahala sosai dan saida ta kwana biyu tana nakudu sanan Allah ya sauketa ranar alhamis din da daddare ta santalo yarta mace kyakkyauwa tana haifota tace ga garinku nan.dan muktar daya sami labari kusan binta yayi.
Sai ranar juma'at da safe akayi jana izarta.mutuwar ta girgiza laraba sosai dan sun shaku sosai.
Yarinya kuwa madara ake bata danma bata da rigima.koda yaushe tana bayan laraba.

Ranar sadakar ukune yarinya taci sunan mahaifiyar muktar Fatimatus Zahra.
Haka rayuwa taci gaba Har aka yi 40.
Muktar ya roki laraba data zauna da Amal a gidansa Har Allah ya kawo mata miji tayi aure.
Haka kuwa akayi Har Amal tayi shekara 2 .tataso cikin jin dadi da kulawa agurin laraba da Abban ta.komai idan ya gani na Amal dinsa komai ya samo Amal. Itace dan ginsa.itace komai nasa shiyasa ya dauki San duniya ya dora akanta.
Haka muktar zaiyi tafiya zuwa abroad dan saro kaya yabar su Amal agida.

Bayan shekara 5. Lokacin Amal nada shekara 7.tana primary 3.ta taso cikin wayo da kokari dakuma kyau ga surutu.kuma tanada shiga rai komai nata cikin nutsuwa take yinsa.
Lokacin ne laraba tazo masa da batun aure zatayi tasamu miji.
Sosai ya tayata murna amma yana tunanin yanda Amal zata dau al'amarin.
Haka ya shirya mata kayanta lokacin yana gaf da komawa Dubai dan haka ya sallami laraba ya kuma yimata alheri me yawa.ya mata alkawarin inya samu lokaci zai dinga kawo mata Amal.
Amal taso atafi da Auntynta amma yace mata zata biyosu daga baya murna taketa famanyi zata shiga jirgi.ta dawo tana bama frnds dinta labari.

Bayan sunje can ya nema mata makarnta anan taci gaba da zuwa.lokacin da zai dawone ya barta gidan wani amininsa da matarsa dn basu da da ko daya.sunji ddi sosai barntana Amal da take da shiga rai haka kowa ya barta Har lokacin da zata gama primary.

Sosai Amal taji ddin zama dasu,dan sun dauke ta tamkar iyayenta. Har lokacin da Abban ta yaxo tafiya da ita.nan suka rokeshi akan ya barta tayi secondary inta.hakan kuwa akayi amma da sharadin inya samu mata yayi aure zai dawo ya dauke ta.nan sukace sun yarda.


Bayan shekara 3.lokacinne Amal tayi junior graduate dinsa.na aji uku har party aka hada mata.
Lokacinne muktar ya hado da hjy ladi kuma Har sunyi aure.dan haka yaxo daukar Amal dinsa.danshi kansa ya bukatar ganin Amal dinsa.
Uncle Hakeem da Aunty Humairah basu ji dadin rabuwa da Amal ba sunsha kuka haka suka hada mata sha Tara na azziki.
Saida jirgin su ya tashi sanan suka dawo cike da kewar baby Amal.

๐Ÿ”ธ๐Ÿ”น๐Ÿ”ธ๐Ÿ”น

Lokacin da su Amal suka dawo daga Dubai. Lokacinne Amal ta shiga sabuwar rayuwa.
Abban tane ya nema mata makarnta dan cigaba da karatunta.

Farkon lokacin da Amal ta fara karatunta cikin jin dadi,kuma bata samun rashin kulawa a wajan hjy.ladi.
Saide Abu daya ne yake kona mata rai wannan ba komai bane irin San da muktar yakema Amal.mai tace tanaso burinsa yayi mata shi.bashida lokacin kowa inba na Amal ba inde yana gida.

Hakan yasa ta nemi kawarta hjy Bilki dan sanar da ita halin da take ciki.nan ta gaya mata tanan kan hanyar zuwa gidanta.

Bata dau lokaciba ta iso.nan ta tarda Alh da Amal suna kokarin fita.
Bayan sun gaisa cikin fara'a nanta dubi Amal tana dariya Amal yan mata unguwa za'a eh tace da ita tareda gaida ta amsawa tayi sanan ta shige cikin gidan.
Dakin ladi ta nufa zaune ta ganta bakin gado.zama tayi kusada ita tareda dafata.
Lfy kuwa jamila kinga yanda kika rame kuwa.
Wlh Bilki kede bari.
Gaba daya wannan yarinyar ta gama tusamin bakin ciki.
Kwata -kwata Alh.baya kulani inde suna tareda ita.komai Amal wannan wani irin bala'i ne.
Haba kawata ki kwantar da hankalin ki,sai kace ba ladin dana saniba.kar ki bani kunya mana.Har wannan yarinyar ce zaki tsaya kina damun kanki.
Hanzu ki kwantar da hankalin ki,zan San abinyi insha Allah kibani kwana biyu.nandai suka taba hira sannan tabar gidan.

Bayan ynkwanaki data dawo.a falon ta tarda hjy ladin.zama tayi suka gaisa sannan ta kalleta da murmushi.
Andace mutuniyar.yanxu nanda kwana uku zanbar kasar ,saboda haka zan tafi da Amal a boye.kinga saina sata cikin harkar da nakeyi dama akwai mutanan dake sansa buwar dauka.kinga daman gata kamar su koma yarinya.
Muktar dake tsaye yana jin duk abunda ke faruwa cikin bacin rai da fushi a fuskarsa.
Nan yahausu da bala'i da fada.Har saida sukayi kaca kaca da hjy Bilki nan ya korata da kashe din yakuma ganin jamila da Bilki wlh zasu rabu Har abada.
Tunda ga wannan rana hjy.Bilki da Alh.muktar suka bar shiri.hakan ya sanya hjy.ladi ta tsani Amal take taku ramata.
Mundin Alh.muktar baya gida toh Amal bata da kwanciyar hankali.musamman idan baya kasar.
Tana shan wahala ba karamaba.
Hakan ya sanya ta fara tambayar Abban ta inda mamanta take,abunda bata taba tambayaba tunda take arayuwata.hakan yayi mugun daga masa hankali.
Amma tambayar duniyarnan da yayi mata saitace kawai tana San ganin ta ne.
Haka de yayita kwantar mata da hankali.dan bayanda zaiyi ya tafi da ita,saboda exams zasu fara,shiyasa ya dinga lallashin ta.
Sannan ya kuma gargadin jamila kan ta kula masa da Amal.
Haka ta nuna masa ba damuwa zata kula da ita.

Tunda ga wannan lokaci Amal ke fuskantar wahala iri daban danan har suka gama exam dinsu.
Amma kullum tana fuskantar bakin ciki.
Ta dalilin hakanne ciwo ya kamata me kama da hawan jini.shine take ta fama dashi Har yayi mata babbar illah.

WANAN SHINE LABARIN AMAL!๐Ÿ’


Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

90-95

AN DAWO LABARI.

Kuka sosai Amal keyi yayin da Abban ta ke kwance a kasa daba asan wani hali yake cikiba.
Wayyo Allah Ku taimaka Abba na ya mutu.
Hjy ladi dake tsaye dan murna itama kukan take,amma na karya.
Hanyar waje Amal ta nufa tana faman kuka.gurin Baba me gadi ta nufa ko dan kwali babu a kanta.gashin kanta ya zubu Har kafadar ta.
Baba dan Allah ka taimaka.
Lafiya me yake faru.
Abbana ya mutu.
Batasan lokacin data janyo hannun hannun me gadi ba zuwa cikin gidan.Har gaban Abban ta kaishi tana kuka.
Dan Allah Baba ka taimaka min mu kaishi asibiti.
Gaba daya ta rikice kamar mahaukaciya tayi nan tayi can.
Me gadi da hanne sune suka kamawa Amal Abban ta har suka sakashi a mota.
Da gudu ta dawo cikin gidan tana kuka ta nufi wajan hjy ladi dake zaune tana faman kuka.
Dan Allah ki taso mutafi ki taimaka karya mutu.
Cikin muryar kuka tace
Amal wata mutuwa kuma bayan kina gani ko motsi bayayi.
Me kuma kikesan muyi wani saban kukan ta kuma fashewa dashi.
Toh kitaso mana muje asibitin mu duba kodai be mutu ba dan Allah ki tashi.
Kuka take sosai ranta kamar zai fita saboda kuka.lokaci daya duk ta fita hayyacinta kamar ba itaba.
Mikewa hajiyar tayi tana rufe fuska da hannu.alamun kuka.key ta dauko suka fita.da ker hanne ta sama Amal hijab dan gaba daya tana mutukar tausayin ta.
Amal baya tashiga kusa da Abban ta ,tana gaman kukan.
Hanne da hajiya sune a gaba.
Kai tsaye asibitin suka nufa,Amma yanda kasan ma driving take ba.
Amal ji take kamar ta kwace motar ta tuka dan bakin cikin irin tukin da takeyi.
Cikin zafin nama tayo kukan kura ta shako huyan hajiya dake driving tana kukan munafurci.
Cikin daga murya tace wlh Abbana ya mutu saina kasheni.
Hajiya da taji shaka kasa tokin tayi neman gurin da zatayi parking tayi.
Parking ta samu tayi tare da kwankwale hannun Amal da ker daga huyanta.
Tari ta kamayi bayan ta kwaci kanta da ker.
Bude motar tayi tareda fitowa waje.kana ganin ta kaga za rar riya.
Kan titi ta nufa kanta tsaye batare da tunanin kar wata motar ta kade taba.
Hannu ta rinka dagawa tana ihu ko wata motar zata tsaya.amma kusan minti goma ba wanda ya biyo hanyar da mota.
Hakan ya sanya Amal da da rudewa.
Da gudu tabi wata hanya tana tunanin ko zata ga mota amma shiru.
Tsungun nawa tayi agurin ta kuma fashewa da wani saban kuka.sosai take koka kamar ranta zai fita.hakan ya sa kirjinta ya kama yimata wani irin mugun ciwo dan ji take kamar zata mutu.
Hakan yasata fara ganin dishi dishi.

Hanne ce tabiyo bayanta tana faman kiranta.can ta hangota rike da kirjinta tana tsaida wata mota data taho.
Nan takuma yin gaba tana daga hannunta alamun motar ta tsaya.
Ahankali motar tayi parking mutumin ciki ne ya fito.wani dattijo suka gani ya nufosu yana tambayar lfy.
Gaba daya kasa magana tayi.kanshi tayi kamar zata fadi hanne ce ta rukota.
Ta fadi kasa.
Subhanallah mutumin ya fada tare da kara sowa kanasu.bayin Allah lafiya meya sameta.da ker ta iya cewa.
Ruh...wa ruuu..wa zansha.
Da sauri ya nufi motarsa ya bude ya dauko mata ruwan.
Sannan ya bude ya mikawa Amal.
Amal da idanunta suka fara lumshe suna budewa ahankali tana kallon su gasu nan de.
Hanne ce tana hawaye tace Amal bude bakin ga ruwan kisha kinji.
Ahankali ta bude mata bakin ta sa mata robar ruwan,saida ta shanye gaba daya.sannan ta sauke wata irin ajiyar zuciya.
Idanunta na hawaye tace hanne Abbana Ku taimaka min kar Abbana ya tafi ya barni.
Kiyi hakuri Amal Abban ki bazai mutuba kinji.kiyi hakuri tashi muje.
Mutumin ta kalla tare da fashewa da kuka ta durkushe a gabansa tana rokwansa.dan Allah baba ka taimaka min Abbana ne zai mutu ka taimaka Baba.
Aini banga kowaba anan yana ina Abban naki yake.
Mikewa tayi tana mai nuni da hannunta gashi can muje.
Toh kuyi gaba gani nan zan biyo bayanku bara na dauko motata.
Da sauri yayi gurin motar tada.key yay mata dan shima yaran sun mutukar basa tausayi.
Ga mamakinsu basu hango alamun motar awajan ba.da gudu Amal ta kuma falfalawa ixiwa gurin.
Ihu ta kurma rashin ganin motar a wajan.
Hanne ma data karaso hankali tashe itama ganin ba motar awajan.
Rungume Amal din tayi suna kuka.hanne hjy ta kashe min Abbana, dan Allah me mukayi mata me muka tsare mata ta kareshe maganar tana kukan.
Nima kaina kukan nake saboda tsananin tausayin su Amal din.
Mutumin ne ya karaso da motarsa tare da fitowa yana tambayar su ina mahaifin nasu.
Cikin kuka tajuyo dan bayyana mai abunda ya faru.
Abban ta hango kwance tsallaken titi.da gudu ta karasa tana gashinan kuzo mu sakashi a motar mu kaishi asibitin. Da Sauri suma suka karasa wajan daukar shi sukayi suka sakashi acikin motar.suka nufi asibitin dashi.

Basu wani dau lokaci ba suka isa wani babban asibiti. Nan suka fito dashi kai tsaye emergency suka nufa dashi.nan sukuma suka tsaya anan waje suna safa da marwa.
Bayan kamar 30mins likitan ya fito daga dakin sanan yace da wannan dattijo ya biyoshi office. Sannan yayi gaba.
Kallon Amal yake itama kallon shi take.
Rugawa tayi tabi likitan sai hawaye take.
Tare suka shiga office din,zama yayi kan kujera sannan itama ta zauna.
Cike da mamaki ya kalleta dan ta bashi tausayi.yn mata bake nakiraba Baban ki nakira.
Muryar ta na rawa ta ce ba babana bane maras lafiyan ne babana.bamu da alaka da wancan mutumin kawai taimakwanmu yayi ya rage mana hanya.
Toh kina nufin duk wasu baya nai da yakamta ke za'ae wama.
Girgixa kanta tashiga yi tareda furta eh.
Menene sunan ki,
Fatima muktar.
Shikuma maras lfy fa,
Muktar sunusi.
Bayan yai rubutu sannan ya kalleta da kulawa.
Yace Fatima mahaifinki yaci poison acikin abinci.
Wani kukanne ya taho mata tayi saurin toshe bakinta.
Tabbas yaci guba ,kuma tayi sana diyar lalatamai kaso 40 cikin hanjinshi.yanxu munyi masa allura nanda karfe 5:00am zamuyi masa theater. Sabo da haka zaku biya kudi 500,000k.
Ya mika mata wata takarda gashi zaki sa hannu anan.
Jikinta na rawa ta sanya hannu.
Ki kwantar da hankalin ki insha Allah Abbnki zai samu sauki.ba kuka yake bukata daga garekiba yana bukatar addu'ar ki daneman sa'a abisa aikin daza ai masa.
Cikin kuka ta furta insha Allah. Sannan yace zaki iya tafiya ki biya kudin.
A jikinta gaba daya yayi sanya,ahankali ta fito daga dakin.hanne na ganin ta tayo gurinta da sauri.ita ta taimaka mata ta zauna.
Bashewa tayi da kuka tare da rungume hanne.
Amal kiyi hakuri me likitan yace.
Cikin kuka tafara fadin hajiya ladice wlh.taya haka zata faru Nina dafawa Abbana abinci da hannuna ya akayi yaci goba taya hanne taya,tare da kara fashewa da kuka.


Ita kuwa hajiya ladi tana ganin su Amal sunbar gurin ta fito da Alh.ta yadda shi anan wajan.tayi tafiyarta.gida ta koma ta koshe duk wani abunta.sanan ta dauki abunda take so.tahau mota tanufi kano kai tsaye.dan duk a tunanin ta Alh ya mutu..

Written by Zeenaseer๐Ÿ˜˜
[12/29, 10:35 PM] Zeenaseer: ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒธ๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท
๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท๐ŸŒท

AMAL
NA
Zainab Naseer Sarki
(Zeenaseer๐Ÿ˜˜)

95-100

Har kusan 1:15am
Su Amal na nan zaune dan ko alamun bacci babu a idanunsu.
Amal ce ta dago da kanta ta kalli hanne da idanuwanta sukayi jajir duk suka kumbura saboda kuka.
Hanne ina mutumin nan daya taimakemu?.
Cewa yayi dare yayi kuma iyalansa na jiransa fone din shi na gida bare ya kirasu.Amma yace insha Allah gobe zanzo da iyalansa.
Hawaye ne yakuma zubo mata.Allah sarki.Allah ya biya shi ya saka masa da gidan aljanna.
Ameen hanne tace.

Wata nurse ce ta karaso wajan su.da Sauri Amal ta mike tsaye.
Nurse din murmushi tayi tare da cewa ki kwantar da hankalinki insha Allahu mahaifin ki zai rayu kinje kidena yawan kuka bakya tunanin zai iya zamar miki matsala.
Goge hawayen tayi tareda cewa insha Allah.
Ywwa kokefa gashi fone din mahaifin kici a aljihunsa muka gani.
Amsa tayi tareda yimata godiya.
Allah kara sauki tace da ita sannan ta juya ta tafi.
Wayar ta amsa ta kunna pic dinta ne tayi murmushi akan screen din wayar.
Wani saban kukanne ya daga kwace mata.tabbas inde abbanta ya rasu bata da wani sauran jin dadi arayuwata.
Haba Amal saikace ba musulmaba ki rinka irin wannan maganar kidau kandara mana.kidena irin wannan furuci dan Allah.
Shiru tayi tareda nazarin Wanda zata kira

Please Login or Register in order to submit comment