Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibiti a canja min bandage,Tsaki ya ja yace to hatsari guda ma yarinya mirsisi ko kwalla bare nasa ran zanga hawayenta,haushi ya sake ji yace sabo da taga Allah ya jarabceni ita ke taimaka min dama idan ka laru da danadam ka shiga uku,Tsaki yaja yayi zuciya yace ko hannun zai balle ya balle ai sunyi asara, yayi Fushi ya jawo wata longslip shirt sharara arsh me colar ya saka Yana ta Kara Wai hannunsa, ko Gaban rigar bai kulle ba yace haka Zan tafi ba ruwana, wandonsa Jean black pencil yayi kyau Kamar ba daga bacci ya tashi ba,Driver yayiwa magana ya fito Yana takama Wayar ma bai iya riketa sosai yace Allah yasa na hadu da Ladies Yan Mata gani nan ku tarbeni tunda matar bata so.

Mota ya shiga harda duba Hanya ko zaiyi Karo da wata lady din,Bai ga kowa ba sai arna, motar mu Kuwa open and close Hafeez ya dauka su Kadada Suka ce sai an Mana ta yan India Hafeez ya bude mota Dake unguwarmu kaf ba layin jaga jaga bane,Kadada ta hango Usir na busa kwallo tace mu siyawa Yara nace so kike su hanamu bacci da busa ba me siya to ni a tsaya zanyi sari na dinga siyarwa a Kauye, Hafeez yace to ai sai muje inda ake sauke Kaya a araha Zaki samu,ba inda akace muje ba sai tafiya sarin Kaya nace yawwa idan naga wani Abu Zan siya na baku ku dinga siyarwa a can Kuna turo kudi mu raba riba a sake sarar wasu a tura,ba wani shopping da Muka je Kadada tace kar mu wani kashewa Yan gidanmu kudi mu siya musu garin kwakwi dan Lagos da manja da sabulu me Sanda Sanda sai omo kowacce a gwada mata gongoni Daya da yankan sabulu daya,Ummiya Kuma Ni me za a siya Mata ne,Kadada tace ga lace masu araha ga kyau ga atamfofi Nima a siya min na kaiwa gyatimata data Hantsi tunda dai ai wata kusan tafi wata kusan,nace Ummiyata tafi karfin haka Kadada ki duba mijin da nake aure,ai Zaki bada kudi a bata ga tsaraba nace to.

Wajen Sarin Kaya Muka wuce yanda Muka tsara haka Muka siyi komai na tsaraba,sai dai ni na siyawa Ummiya takalma masu tsada kala Uku da mayafai Atamfa masu tsada kala Uku lace kala biyu ga wani materials,sai omo masu kyau da sabulai Suma su Kadada iyayensu sun musu siyayya dai dai musali haka Yan Gida ma,na bada turaruka masu kyau kala biyu nace a kaiwa Daddy,Kadada tace Babanki fa nace ke rabu da shi,Kadada tace uhm uhm Najla kome iyaye sukayi iyaye ne wlh karki wulakanta daya baza ki ga dai dai ba,watakil ma shi yasa Umma ta tsaneki, nace kin manta abinda Baba ya yiwa Ummiya a gabanmu muma haka tab a kyale zancen Kawai Kuma wlh ban wulakanta shi ba Kawai dai ni bana Shiga sabgarsa,koma mene lafazinki a kansa ba Dadi ki daina ki barshi a ranki,muci gaba da gashi Bari na siyawa Babana gajeren wando na Shan Iska tunda na rasa me ya kamace shi cewar Kadada Muka dinga dariya,Kadada tace ya kaga kaurin Babana a gajeren wando, Tahantsi tace sai kace sandar bishiya kiyi a hankali kin San Babanki Kadada wargajewa yake a tsakar gida ya kwana jikin bishiya Karki silar da da kunama ko miciji zasu Shige Masa wando mudai ba ruwanmu ato,Kadada tace sai na siya Masa yaji dadin shuka a gona, Gaban wani Igbo taje tace Kai Hafeez ka fada Masa sunan mazantakarka a waje da turanci,Hafeez yace Mene haka Yana dariya,tace gajeren wando buje na manya ai sunansa kenan kana yin sake za aga komai a waje faro, Nace Kadada ke da kin koma wajen Ummiya,ai daga Nan Kauye zamu wuce sai naje ganin gida Zan koma birni,Hafeez ya tsaya ya siyo Wanda Kadada ta nuna kala biyu,aka siyawa ta hantsi sai da muka gama sarin mu sannan aka jibge Mana Kaya a wani katon buhu jumbo me L aka nannade aka sa a mota Muka biya kudi, Muna tafiya Hafeez ya kaimu wani hadadden wajen cin abinci da shakatawa,Muna zuwa Tahantsi tace inzo Lagos banci dodon kodi da tsutsar ruwa ba ai nayi asara,Kadada tace a kawo Kai Hafeez ko Mene Indai da Snail a kawo nace ni dai Banda Ni,baza ki waye ba ai ke cewar Kadada.

Hafeez yasa aka kawo musu shiryeyyen abinci yasha snail wata Miya da wata yellow rice taji kayan lambu,Ni Kuwa Banda Snail nawa,Hafeez ma me Snail ya Saba,Kadada tayi Loma Daya ta dafa min kafada tace baki iya komai ba Dan uwarki shegiyar miyarki sai kace faten garin masara,nace wallahi zamu hadu gobe Zaki bayani,Tahantsi tace rufe Mana baki rannan Haka Kika Mana miyar kubewa Kamar yawun Dan Iska sai kace an wanke Kan dan akuya,Hafeez Yana cin nasa Yana ta dariya yace dan Allah karku tafi gobe,nace zaka Kara kawo mu nan wajen? Yace ae,Kadada tace na yarda da Aljanna gaskiya kukeyi su Fara tunda aka samu irin wajen Nan a duniya ai na yarda a can ma akwai Aljanna,Kuma tunda aka samu Kauye da wahalar rayuwa akwai wuta a can ke Fara karya gwamma take tace Wai bacci akeyi a kabari Kawai a tashi ba hisabi,Allah Ina zuwa sai na nuna Gwamma da yatsa nace karya take tayi magana Kuma na kutuntumata ashar,Tunani tayi tace kai ba yanzu ba sai na sake tabbatarwa, Tahantsi tace karki jawo a tsine miki nace Kuma haka ne ba ruwana kuje da dadin girkinku Fara.

Ni nasan Kadada karya take dan da Tahantsi ce ta fada Zan yarda tafi saukin Kai Kuma da za a samu Kadada ta shiga musulunci da gidan nan sun shiga Uku sai an samu da yawa sun Musulunta sabo da yanda suke sonta sabo da fitsararta da rashin Kunya ko wani aka yiwa Abu a gidan Kadada za a iya turata taje ko Gaban uban waye yasha ashar ba ruwanta,Shi yasa Sam duk haushi suke ji ta zauna a wajen Ummiya amma ba Wanda zai iya Mata dole sai ta koma Kauye nan gani nan bari,shi yasa Ummiya ta janyeta.

Wuri uku Hafeez ya kaimu har dare bayan Isha bamu dawo ba sai 9 pm Muka shigo gida,Muna shigowa Jawad shima motarsa ta shigo bude masa akayi ya fito ya bata rai ko kallonmu baiyi ba ya wuce part dinsa,me aiki zamu sa ya Kai Kaya,Kadada tace matsa ta daga kayan nan zata Yi ciki da shi,Sai ga Farooq ya shigo da motarsa Yana Fitowa yace banyi Niyyar zuwa gidan Nan yau ba sai Kadada tace gobe zasu tafi ko?

Kadada ta jefar da kayan tace Kai irin wannan dirar mikiya haka ba sanarwa Muna can mun tafi cin kayan dadi, Farooq karasowa yayi kusa da mu,ji nayi anyi fito Kamar an busa usur na kalli can inda naji sound din Ido biyu nayi da Jawad yatsansa daya ya daga sama Wai Allah na kallona,Ni Daya na gani dariya nayi na kalleshi,Hafeez ya gani ya kalli Jawad ai sai ya zageshi da Hannu ya Masa dakuwa, wajen ya bari,Ni da Tahantsi ma tafiya Muka yi,Kadada da Farooq Muka bari Kadada tace gobe fa tafiya zamuyi dole Ummiya tana ta fada bai dace ba, Farooq yace to muje mota na baki tsaraba gobe bana gari,tace wasu Yan iskan Samarin Kuwa tab ai ko biyar din rake baza su baka ba,sai zancen banza hauka nake kazo sau Uku na fito ba komai ai Kuwa da yaga harara in ya gallabeni yaji Mari,Farooq ya firgita yace marin saurayin? Fess Kuwa Nawa na mara ai ni duk Samarin da nayi ba Wanda bai tafi gida da yatsuna biyar a fuskarsa ba,Farooq a ransa yace duk zuwa dole na tafi da kyauta wannan jarabar yarinya na rasa me yasa nake nemanta,yace Nima Zaki iya marina? Kadada tace ban gama tantanceka ba tukun amma Kai ai na kyaleka kamshinka yasa na kasa shi yasa ban iya ba amma haushin da ka bani rannan da tuni ban warwareka ba,Kuma yanzu har salo nake a Marin na Marin mutum nace Yi gidan tsohuwarka na juya Ina taku dai dai.

Farooq a ransa yace Allah ya tsare ni tab ,Waya ya dakko guda biyu iri daya amma kowa Kalar tata daban Android din Infinix masu kyau da Leda na kayan sawa kowacce nata daban,baiyi Niyyar bani kudi ba ya irgo dubu ashirin yace gashi kusha ruwa,godiya na dinga Yi nace na gode na gode,ka Dade kayi karko,yayi Murmushi yace golden din ce taki Zaki ga number ta,Kadada ta dura ashar tace samari sai birni Allah idan naje Kauye wani ya kalleni in ba sai naci kaza kazansa Allah yasa ma na koma unguwar su Najla,kamewa tayi ta Sara Masa yanda sojoji suke Yi tace Saura fareti Nan gaba zai biyo baya sai na gama tantanceka,Farooq Yana ta dariya suka yi sallama ya tafi ko ciki bai shigo ba ya wuce abunsa.

Can su Kadada Suka kaure gida da murnar waya,wanka na shiga a room dina lokacin Yara duk sunyi bacci,na iske toilet dina faca faca da jini,raina ya baci matuka nasan Asmau ce ko shakka babu wulakanci ne,Kamar na fashe da kuka haka na danne zuciyata na wanke komai Kal ko su Kadada ban fada musu ba,bayan nayi wanka na fito na Fara shiryawa akwati na bude cikin kayan lefena gaba daya an sharara musu manja,har na ledar an fito da su an zuba,da sauri na bude sauran akwatunan Naga wasu kayan duk an yayyanka su da almakashi wani rigar wani skert din wani wandon,Su Bintu na Kira na tambayesu ko sun ga wani Suka ce basu ga kowa ya shiga ba dake basa zama a part din aiki ke kawo su su tafi,Su Kadada na nunawa Suka ce ki fadawa mijinji mu yanzu wa Muka San yayi da har zamu fara tuhuma,Muka zauna Muna ta alajabi,part din Jawad na tafi da sauri

Ina zuwa part dinsa ban San komai ba ya dauke ni da Mari,sai da idona ya dauke,ciwonsa ya fama tare muka saki ihun,idonsa har ya Kada yayi jajir sabo da tsabar masifar da yake ji,yace ubanwa Kika tambaya da Kika fita? na baki uzini ki fita baki San aure ba? Baki da Ilimin Addini,hannayena na Dora a ka Kar ya sake marina,amma ko kuka banyi ba nace Kaine kace muje fa,kaina yayo da masifa yace ni nace kije? Karya ziki min?

Da sauri nace wayyo Ummiyata karya nake baka ce naje ba Kayi hakuri na rike damatsansa biyu da hannayena biyu Muna facing juna banyi Niyyar bashi hakuri ba amma zuciyata ta kasa dole nace kayi hakuri na fashe da kuka, sai lokacin naji yayi shuru a hankali yace bana son irin wannan ki daina daukan auren nan da wasa addini ba a wasa da shi na fada miki ki daina tunanin lallai sabo da Yara na auro ki,bani da hankali an fada Miki,kin San ba komai nake iyawa ba kin sani in kin San baza ki iya ba ki fada min mana,how dear you da Zaki tafi baza ki fada min ba,ance bazan barki kije bane,sai kin fita baki fada min ba ko ban Isa ki fada min ba,zamana kike ko zaman wasu,Ido na tsira Masa Ina kallon masifa da ruwa ruwanta,nasan nayi laifi nice bani da gaskiya,yatsa ya nuna min wannan ya Zama last warning da Zan miki,da shagwaba Ina dire diren kafafu Kuma Ina rike da damatsansa nace to kayi Hakuri,a raina nace kinyi asara Najla kaddara ta kawoki kowa ubanki yake ci,a garaki ta nan wannan ya garonki ta can na jawa kaina.

Wankan fa yace bana so ya fisge hannayensa yayi tafiyarsa saman bed ya kwanta dake yayi Sallar Isha dinsa,Shuru nayi bai min magana ba Nima ban Masa ba,na gaji da tsaiwa na juya Zan tafi cikin Fushi yace Mene ne Kika shigo da gudu? nace dama zuwa nayi na fada maka kayana na lefe duk an yayyanka rabi wasu an zuba musu manja gashi Nan dai,Yace laifinki ne Allah ne yayi Fushi dake kin fita baki tambayi miji ba shi yasa har wani ya samu dama ya iya shiga ya Miki haka,da kin zauna za a samu a Shiga Kuma wa yace ki bar kofarki a bude Watarana sai anzo an jefa Miki wata masifar a dakinki duniya yanzu ba tsoron Allah ko waye Allah zai tona asirinsa Watarana,Zan siya Miki wasu,sannan kina can Waleed ya bar gidan Nan ya tafi dangin uwarsa masu gadi ne Suka fada min Uwarsa tazo ta dauke shi,nace tab rabu da shi ai wuya ba shegiya bace da ubanta,har Nawwara ta tafi zanje har can na dawo da su idan Suka sake tafiya ba abinda ya dameni,can ma Asif ya ganshi a bayan school shi da Yan iskan abokai suna shaye shaye

Baki na bude nace Allah ya shirya yace ameen ya sake kallona Jawad da naci yace harda yin kwalliya ki shafa su jambaki ke ga kwalluwa ko gashi nan sai zunubi kike tara min Allah ya shiryeki,Dariya nayi ya bata rai yace wannan ba abin dariya bane Zaki jani wutar jahannama ban San hawa ba ban San sauka ba,mutum ko kuka baya Yi sai iskancin banza ya tashi ga abin tausayi baza a tausaya Masa ba,Katuwar mota tayi kuli kuli Dan Niger dani ke Dadi ma Kika ji na mutu ki huta,wallahi ki kiyayi Allah,Dariya na sake yi yaja Tsaki yace in Kinga dama kinyi Niyyar samun lada sai kizo ai kiyi aikinki,Nace ka huce kenan? Ina nan da zafi na turiri nake ma.

Nace Shaddata Fara shike nan, Atamfata wata ja Ina sonta itama an yanka ta,an fama ciwo na yau har kuka nayi gyaran kashin ma Sai da aka sake karya shi aka Dora,nace sannu Allah sarki ni kam lafaya lace Dina idan na tuna sai naji hawaye,Jawad yace a ransa wannan Sam bata tausayina a kasa Zan kwanciyata yau, yace a ransa, bayan na Masa Wanka mun fito nazo Ina shafa Masa Mai Yana lumshe Ido yace hannunki zafi kiyi a hankali sai kace bakya shafa lotion,nasan Kawai fada yayi,a zuciyarsa Kuwa haka yake cewa wayyo wayyo dadi, har ya fito fili nace naji kace wayyo Dadi da sauri ya bude idonsa da ya canja yace wayyo zafi nace ke bakya jin dai dai,kirjinsa nake shafawa na tabo nipples dinsa wani zullo yayi yace zafi wajen ya bugu,,sitiyari ne ya bugi wajen nace sannu yace dakko man zafin can kiyi massaging wajen nan a hankali,ban gane ba na dako nazo na dinga lailaye masa kirji har nipple sai shidewa yake yace zafi.... wayyoooooo zafi....nace tunda wuya kake Sha a bari Mana yace ai bazai warke ba so nake na koma office,Ina ta Abu Daya Yana sheke dadinsa ban sani ba,Ina tayi Yana ta sani Ina wani murjeshi Ina gabansa sai Sannu nake cewa harda hawayen tausayi,ya kusa releasing ban sani ba Naga ya haukace gaba daya duk na rude na zaci ciwon ne yace bani hannunki bani hannunki Yana Shan yaji........Zan mutu Zan mutu Kawai ya damki Boobs dina sabo da rashin wayona nace Yaya ba hannu bane ungo hannuna na Mika Masa ko kulani baiyi ba ya dinga lagude min boobs yace rikeni....rikeni.....Kuma yaki ya bar kirjina ya huta,ni na rude Ina tausayi sai da ya gama kawowa sannan yace Ina hannun? Yaci gaba da rudewarsa na karya,ya rike hannayena na rasa Ina ya samo karfi nace Sannu kasha wahala Yana ta min Dariya a ransa,Yace lullubeni da bedsheet zazzabi nake ji,na lulluba Masa Kansa ne kawai a waje yace dole na koma asibiti gobe a duba,nace gaskiya Sannu Yaya Jawad yau duk kafi bani tausayi yace ashe kina da Imani haka? naji dadi ya yabeni nace Yaya ba Hannu ka rike ba,Yace dan Allah? Wai Ina na rike? Nace kunya nake ji,dama kina da kunya,fuskata na rufe gaba daya,yace to nuna min na gani me na rike idan ba Hannu ba? da gudu na fice Ina ihu wayyoo,Dariya yayi sosai ya sawa kofarsa key ya shige toilet yanzu lafiyarsa ta gudu da kyar yayi wankan tsarki tare da tsarkake jikinsa ya fito Yana ta smiling.

Da na koma bedroom dina na wuce ko su Kadada ban kula ba na wuce na kwanta har bacci ya saceni ban sani ba.
Da sassafe naje part din Jawad Yana ta bacci,na Dan tasheshi ya bude Ido kadan nace su Kadada sun shirya tafiya,da muryar bacci yace da sassafe haka kamar ana korarsu,nace Ummiya tana ta musu waya,yace to bari Asif zaizo ya sasu a jirgi,nace Allah? yace ban sani ba Ina ta murna,jaka ya nuna min me kyau da yake ajiye kudade yace ki Basu dubu dari,Baki na bude yace ae nace to an gode Allah ya Kara budi na dauka naje na basu suka Yi sallama da kowa Hafeez da Ahmad sun Kara musu kyauta,Asif yayi musu komai da kayansu Niki niki suka Isa Kano.

Kafin su Kadada su je gida ma Umma taje wajen Ummiya taje a mutuniyar kirki harda bawa Ummiya hakuri akan farkon zuwanta lokacin kawo lefe,Zama tayi sosai sai da Ummiya ta saki jiki da Umma sannan ta kitsawa Ummiya karya da gaskiya,karshe harda cewa muna godiya wlh yarinya tana reno yanda ya kamata ai bamu taba zato akwai wacce zata iya amincewa a aureta a Bata millions of Naira Kuma a raino,gaskiya kinwa yarki tarbiyya Yara suna can wlh ta musu wanka wanki komai itace ,Munafuki akace idan ya rigaka shiga dakin uwarka sai kaga canji,Ummiya tunani ta lula tana tuna abubuwa da gaggawar auren Yarta da boye boye da ta dinga Yi aka rasa gane Ina ta nufa a Kan auren,Ummiya ranta ya baci wato ni Najla zata yiwa karya,duk abinda nake Mata bata gani,yaran zamani sai a barsu,to Ni na haifeta wannan zaman auren bautar baza tayi shi ba,nikam nayi nawa ya Kare bazan bari a kassara min rayuwar ya ba tunda Najla yarinya ce me ta sani ai Kuwa Bari su Kadada su dawo ai suna hanya Zan bigi cikinsu har can zanje na ganewa idona Kuma na taso yata a gaba, Inshaallah Najla baza ta Kara wata uku a gidan Jawad ba yanzu dai tayi wata biyu bari nayi bincike a nutse lokacin da na gama Zan dakko abata Ina ai Sam baza ta sabu ba bari na fadawa mahaifinta shima yayi bincike haka Ummiya ta Gama sake sakenta,Umma tasan ma tayi nasara sallama tayi tace zata koma dama gidan kawarta tazo ta biyo a gaisa ai an zama daya.
Umma na tafiya Ummiya tace a hankali zanyi bincike ba gaggawa muje zuwa.





Nan na kawo karshen Free pages dina Wanda Suka siya ku jira Update dinku


Masu Sharhi Ina Matukar godiya,a yafeni Wanda Basu da ikon siyen novel Kuma suna min comments amma ban basu kyautar pages ba abin ne sai a hankali
Na gode







AsmaBaffa
08033933642
10/6/22, 22:03 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
51-55


NA KUDI NE

MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP
IN KIN GANSHI A WAJE NA SATA NE.



Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA


Page naku ne

Ummin Najwa
Nafee




Su Kadada har jirgi sai da Asif yaga shigarsu jirgi sannan ya tafi sabo da yanda yasan ba taba shiga sukayi ba gwara ma Kadada an kawo Amarya da ita,Tahantsi Ido ta runtse aka yi aka Yi ta zauna a kujera taki Zama tace Ina Naga ta Zama ni Kuwa Ina daga tsaye,Kadada tace Niko bacci harda munshari,wani matashi wankan tarwada handsome yana ta Danna iPhone dinsa Yana pics Tahantsi tace shegiya karya yanzu sai ka sa a yanar gizo kace ka tafi amurka ashe Kano zaka je,dama ance haka kuke dan hada kudi ku shiga jirgi Kawai dan kuyi hoto ace ku masu kudi sai cuta ta kamaku ayi ta Neman tallafi a gidajen radio,ba a gane Baku da sisi sai cuta ta kamaku ayi ta sanarwa a yanar gizo sabo da duniya ta sanku a hada muku kudin asibiti a haka gaka kirar kudi Kamar mutumin kirki, ku dinga sanin ya kamata,mutane har yau Kun kasa ganewa kayi gaskiya kaga gaskiya

Yana jinta ta tsaya a kansa taki Zama sai leka Masa kujera take,Kadada tace duniya yanzu ai ta lalace mutane duk sun koma Yan kutuma.......ta shararo ashar, Wanda suke ji sai da aka kalle su ana ta dariya Yara tsageru suna ta tsige bawan Allah,bai kulasu ba shi Wanda sukewa tsiyar, gasunan kansu ba dankwali Kuma kana Nan Kaya Suka saka kowa yasan ba musulmai bane,kana Nan kayan ma sababbi,Kadada ansha farin Jean pencil da top ja,ita Kuma Tahantsi harda saka wani shegen wando pela daga sama ya dame kasa ya bude Wanda yanzu aka kara dawo da yayinsa,Tahantsi ta ware kitson attach dinta dama gashi bai da tsayi ta gyara shi harda zuwa wajen aski aka Mata zikza a gefe a dole ta waye taje Lagos an dawo ,ba me cewa Yan Kauye ne,Saurayin da suke ta tsigewa baiyi tunanin suna Jin hausa Haka ba,sai yaji sunfi shi iya hausa ma, labari Suka koma na duniya lokacin da jirgi ya daga ba shiri Tahantsi ta zauna,sai da ya daidaita sannan ta sake tashi tsaye ta leka Wayar saurayin taga Yana ta kallon hotunan wayarsa harda sababbin daya dauka tace kayi Kuwa kyau amma camera ta gyara ka a fili mu ba haka muke ganinka ba,wata dattijuwa ya kamo Yana gani baka wuluk, Tahantsi tace ba dai babarka bace wannan? ai sai ace satoka tayi kaga hancinta sai kace karamin yatsan kafar Babana,Kadada ta sheke da dariya tace kut ta cuceka ta gama dakai da kasan Kalar yatsan da sai ka suma,Yana jinsu Yana dariya a ransa wayarsa ya maida aljihu.

Tahantsi ta harari Kadada tace kin cuceni Ina ta Shan kallo gashi Nan kin jawo ya boye wayarsa, Zama Tahantsi tayi tace Ni na tsani Gwamman gidanmu yanzu Muna zuwa zata damemu me Muka siyo komai sai an dameka Kamar za a cinyeka a lasheka a huta,Kadada tace eiiii abin haushi su Naroro ya wani cangalo kafa hakora sai kace katangar kwalabe, ana jinsu ana ta dariya har jirgi ya sauka,Kadada tace munzo, Tahantsi tace au har anzo? Jarabar jos dadin har ya Kare nasan haka abin yake ma ai Zama zanyi,me hawa mota ya shiga Uku,ki duba Sanda Muka je a mota duwawaikanmu duk sai da Suka kumbura Suka dinga Fushi,Kadada tace Eiii ashe kema kin gani na dade Ina kallo a bandaki,har na Fara murna sun karu gari na wayewa na kalla naga sun koma yanda suke nace to shikenan suje tunda ba muciya da zani bace ai da sauki.

Ah mu ai duk danginmu babu Sanda kowa mulmul,Saurayin ne ya mike zai dauki jakarsa karama ya kalli Tahantsi shi gashin nata ne ya birgeshi askin ya Mata kyau irin na shegun arna marasa ji
suna fita Suka dauki shirgin kayansu da uban yawa da jirgi ya sauke,sun fito zasu shiga taxi dake airport saurayin shi anzo daukansa a mota me kyau da wani me Kama da shi maybe kaninsa ne,ya wuce su a tsaye Yana mota abinsa,taxi Suka Shiga zuwa gidan Ummiya,Lokacin Umma bata dade da barin gidan Ummiya ba,suna shiga da uban Kaya Ummiya ta rike baki tace ku Kuma wannan kayan fa? Dan Iskanci shine ke Tahantsi Kika yo wannan shegen askin ana so ku shiryu amma Kuna sake lalacewa jiki duk a waje,ai mu bamu da addini Ummiya ko Kun manta harara ta watsa musu Suka Yi shuru,tace to ya Najlan ya taji da yaran dan nasan yanzu dole tasha wahala raino ba sauki,Tahantsi tace Wai kema kin sani dama?Kadada ce ta bigi Tahantsi Wai tayi Shuru ance karsu fada, Tahantsi sai ta waske tace suna Nan lafiya ai Yana da kudi baki ga yanda Fara take Jin dadi ba tayi kiba ta koma wata baturiya yaran ma ai da masu aiki sunfi kula da su,Ummiya

Please Login or Register in order to submit comment