Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a haka har Muka Zo cikin Gari,ya tsaya a pharmacy ya siyo min maganin ya bani na Sha sannan aka Yi gaba zuwa hotel dinsa,yace min fito banyi musu ba na fita,yace ka mai da Tahantsi gida itace zata kular min da Baba,Binta sugar dinka Kuma kasan yanda zakayi da ita ni na gama maka sai godiya nake jira kazo Watarana ka min,Fitowa Farooq yayi tare da Jan Jawad gefe yace ka shammace ni yanzu asibitin da mukace zamuje fa a tsuma ni? Dariya sukayi harda tafawa yace sai a Lagos ya juya tare da rike hannuna Muka karasa ciki har room dinsa kafin mu shiga sai da yayi Mana order abinci,Ina Shiga na ajiye jakata a saman drawer Hijab Dina na cire na kwanta a saman gadon sabo da yanda kaina ke ciwo,wanka ya Shiga ya fito daga shi sai towel yaga na Fara gumi naji sauki sosai wuyana ya taba yace ya warke nace ae,yace je ki wanka to ko na Miki? Dariya nayi na tashi na Shiga da kayana duka,bayan nayi na dauki sabon brush nayi brush sosai Kamar yanda yayi,sannan na daura towel Dina na fito wannan towel din har yafi na gida guntu sai da naji kunya amma Kawai Fitowa nayi haka ya bini da kallo nace wanne kayan Zan sa lace din ya min nauyi,maadanar Kaya ya bude tare da furta ga kayanki na taho da su sabo da naji kala uku Kika dauka,naji Dadi na bude na dauki wata Yar Riga silk marar nauyi me siririn hannu na saka,da pant Kawai,na gyara gashina sannan nayi Sallah la'arsa Kamar yanda yayi shima,tuni an kawo abinci lafiyayye harda su Fruits,da Kansa ya dinga bani a baki har Muka koshi Muka Sha fruits sosai tare da kuskure bakinmu.

Kwanciya nayi Ina huce gajiya ya kwanta a gefena shima tare da jawoni jikinsa na rungumeshi Ina murmushi nayi missing dinsa sosai,maidani yayi kasansa na dawo Kamar Yar karama gashina me santsi yake shafawa a hankali Yana kissng saman lips Dina,jikina ya fara rawa yace ba abinda Zan Miki ni bacci na daukoki ki tayani trust me sai sanda Ummiya ta bani ke a dakina ranar to ba sauki bare rangwame na gaji da hakuri.

To muyi baccin Yamma tayi amma dai bari mu huta,ganin zai zame min rigata najuya bayana tare da dunkule jikina,hannunsa yasa ta tsakanin hannayena Ina kwacewa yace Dariya kike bani ke ganinki karfinki ne yasa in Kika janye hannuna nake cirewa,Hakuri na bashi yace ki bari tun kafin na canja mind na Miki warka warka,Dariya ya bani nace sai kace tsohuwar radio, please joke apart ya wani marairaice I miss you, Ina so na taba,me? So kike in fada Miki? tace ae a hankali ya rada Mata kyawawan nono abuna, Yana shagwaba ya sa hannayensa ta kasan nawa hakura nayi na nasan bazai hakura ba,sai da ya gama latse latsensa da tabe tabe,ya dawo Kan mazaunaina ya dinga latse su Wai massage yake musu nace na gaji





Ayi Hakuri da wannan


Maman Mujaheed Fans Muna... muna..muna
Muna da magunguna mata da supplement kaka kala na gyaran jiki da gyaran fata na Karin niima da matsi Ina uwargida da amarya da masu Shirin aure dama taku muna da kayan mata da supplement kala kala iya kudinka iya shagalin ks cikin sauki Mai kama da kyauta ba'a Nan mmn mujaheed ta tsaya ba tana yima marasa karfi adashen kayan gyara 500 duk weekly abaki kayan 5k 1k weekly abaki na 10k sai kin zabe abin kk so muna aikawa duk garinda kake

08066726866








AsmaBaffa
10/6/22, 22:03 - Buhainat: 🌏 JIKAR MAGUZAWA🌏
66-70


NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP
IN KIN GANSHI A WAJE NA SATA NE


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA


PAGE NAKU NE

Cutie
Bestynbeelat
Aidah Maman Tasnim
Maman Samha
Ummi H






Wayarsa ce tayi Kara ya dagani tare da dagawa Hello...muryar mace naji kasa kasa Yana ta faman cewa Okay...yeah..tana ta magana ban San me take cewa ba naji kishi na mike zumbur tsaye sai da ya kalleni yana wayarsa ya dade har ya gama ya kashe wayarsa,kallo na yayi tare da riko hannuna lafiya Fuska na hade tare da fisge hannu na nace mene na wani Okay baza ka bude baki kayi magana ba sabo da wato Kar na gane budurwarka ce ni Zan hanaka soyayya ne ko aure zaka Kara me na Isa nayi,wato sabo da bana gidanka shine ka fara soyayya,Jawad ya saki baki Yana kallona yace na yarda ke yarinya ce gaskiya,da sauri nace ae ai kace haka Mana tunda ka samo Babba tsohuwar banza ni dama nasan ba so na kake ba jikina kake bi,Dariya yayi kawai yace Wai da gaske kike? Raina a bace nace ae,yace tab Sannu da aiki to,ai haka kake ce min kullum yarinya yarinya na saka kuka,Jawad ya zaro Ido ya bude baki tare da furta ahhh....ke Mene haka? Yace yanzu ni wanne Mata ne ban gani ba a duniya Naga Fara,Naga baka,Naga wankan tarwada,Naga Yar lukuta,Naga siririya ke a siririya ma Naga wasu Kamar Sandar Snooker,

Naga larabawa,turawa,indiayawa duk na zagayesu nace Ina sonki,Ina son wata Zan tsaya na saurareki,ai kaji gashi Nan kace babu Kalar da baka sani ba dama kallonsu kakeyi, idan ma doguwa ce dai ka sani da wuya dogo ya zam me hankali kaje kaji wakar shata baza tayi hankali ba Indai doguwace Kuma baza ka taba samun nutsuwa ba,Dariya Jawad yayi yace to ke kenan tunda kema dai doguwa ce Kinga kin tonawa kanki asiri bana son shiririta zauna idan so kike kiji wace to a karkashina take aiki,wato har Mata kake dauka yace ae,to fire her taje ta nemi wajen aikinta,Baki Isa ba Kuma wannan bana son zargi fa ya bata rai sosai,Zauna bana son irin wannan karki sake min haka,kyaleshi nayi na koma na zauna,me yasa ku dukkanku kuke da taurin Kai ne, laaaa harda Ummiyata ko,kinji nace ita,kace dukanmu yace Ni nace ne ?ya wani Bata rai Shuru nayi na kwanta a gefensa, lokacin magriba nayi yayi Alwala tare da canja Kaya yace na tafi masallaci nace to,Yana fita na Kira su Farisa kawayena Muka gaisa Basu San Ina gida ba ban fada musu ba Nima,tashi nayi nayo Alwala tare da gabatar da Sallar magriba Ina Adduoi Jawad ya bude kofa ya Fado a guje yace ga Naroro nan,da gudu na tashi na fada toielt na kulle,Dariya ya dinga Yi yace tsokanarki nake,Fitowa nayi Ina dariya nace wlh naji tsoro su Kadada sun Musulunta ya kamamu ubanmu zaici,Sallayar hannunsa na karba na juya ashe bai saki sallayar ba ya jawo na juyo ya jawo ni na fada kirjinsa yayi huging dina nace Addua fa nake fuskata ya shafa da tafukan hannayensa Wai Ameen Inshaallah an karba ta wuce ya daukeni tare da kwantar dani saman bed.

Farooq Kuwa bayan ya sauke mu mota ya koma Kadada ta fito tare da komawa gaba Amarya,Farooq ya kalleta tace ae Amarya sai a gaban mota muje in Kuma so kake ka Zama driver to,Farooq yayi dariya yace ai hankalinki na gani da Kika dawo gaba,ya wuce da su wajen cin abinci Suka ci abinci suna ci Farooq Yana musu bayani akan Sallah da abinda ya dace mutum ya sani Wanda ya shiga musulunci,haka da Suka fito a mota ma, Tahantsi ya fara saukewa a bayan gidan Baba ta Shige gida tana shiga ta tambaya Baba ya dawo masu gadi Suka ce a'a taji dadi tare da Basu cin hanci dubu Daya Suka Yi godiya ta wuce ciki Kai tsaye,Matan Baba suna yin Tahantsi sabo da aikinta,kullum tayi ta musu aiki tana yiwa yaransu wanka,tana dawowa tayi sallama basu taba ji ba a bakinta sai yau,tace na Musulunta yau na koma Khadija ba Tahantsi ba idan ma Tala'asar ce ta fita daga bakinku daga yau na koma Khadija,Ke da gaske kike? tace fitar da nayi masallaci naje nida Yar uwata Kadada Muka musulunta,Kai amma mun tayaku murna Alhmdllh mun samu karuwa tace addinin musulunci ya samu karuwa,suna tayata murna ta koma bedroom ta fito tace ku Zo ku koya min Alwala da Sallah kafin na shiga makaranta,ai da sauri Suka shiga koyawa Tahantsi abubuwa taje zatayi alawala yanda Suka koya mata,Bata iya karatun Sallah ba,yaran gidan Yan manyan Suka dinga koya Mata karatu sai da ta iya Fatiha da kyar,da dare suka koyawa Mata suratul Iklas tafi sauki,sai tahiya da tasbihi da akeyi a sujjada da ruku'u,sai dagowa daga ruku'u ta iya sannan taje tayi Sallah tun daga wacce ta risketa Bayan ta Musulunta Tana idarwa ta bingire a wajen tana wash wahala wuyana wayyoooo..

Farooq Kuwa bayan yayi parking a kofar gidan Ummiya Kadada ta kalleshi ya juyo Yana kallonta shima fari tayi da fararen idanuwanta masu kyau Kadada ba dai kyan idanuwa ba,Farooq yace Amarya wannan Ido sai kace farin wata ,Dariya tayi tace hmm ba dai mutunci Zan maka,ana kawoni ka tabbata 10pm kana gida daga aiki sai gida bazan dauki yawace yawace da Zaman majalisa ba,sannan ba cin abinci a waje,Farooq yace Wai kece mijin ne ko matar yau naji ikon Allah, amma ai ni matarka ce Ina da iko da Kai Kamar yanda kake da iko dani,biyayyarka dai zanyi Nima zaka min 50-50,Dariya ta bawa Farooq yace Namiji yafi karfin kanki,Kai karami ba Nawa Babba ne,Farooq Yana kallonta yanda take magana direct,yace Allah ya kaimu a kawo ki gidan ki gani idan Zaki iya tankwara Ni nayi abinda banyi niyya ba,kiyayi kanka Yar gidan Tashuka ka aura,Babana Sanda ya auri Tashuka auren hadi ne Yana wani yanga harda gwada yanda Babanta yake Tashuka kike ko wa ni ba kalarki bane sai dai na lallaba dake sabo da hadin Gwamma ne amma Ni nafi karfinki,Tashukata Allah sarki Bata kaini ba lokacin shekarunta 13 baka ganta ba Yar tatsitsiya,komai yace tace to..to..to akayi aure bai sani ba ashe Tashuka Boss ce ta girmeshi a wayo shi Kam shekarun ne Kawai,har yanzu gashi ya kasa mata kishiya sai yanda tayi da shi har aka Haifeni,Taya ke Kika San zancen bayan ba a haifeki ba ma,Gwamma ce ta fada mana Kuma na yarda,Murmushi Farooq yayi yace yaushe Zan dawo to Naga Amarya na musamman a tanadi dakin zance,Kadada tace Indai zaka zo ka min waya bana son zuwan titse,okay ya furta tace ka fara bin doka kenan Murmushi yayi ta fita,yace ki gaida Ummiya sai na Zo a kiyaye dokokin aure Kar a min Wasa da igiya idan akayi min ba Dadi nima zanyi ba dadi, Kadada tace sai munyi waya Allah ya kaika gida lafiya,inye an Fara koyo,Ido daya Kadada ta kashe Masa ta juya cikin gidan Ummiya ta barshi Yana dariya,Jawad ya Kira Wai yazo ya kaishi airport ya karbi motarsa,Jawad lokacin ma Muna kasan Dan carpet a zaune ya sani tsakanin cinyoyinsa ice cream muke Sha da nama Yana bani abaki Yana ci shima shi yasa yace tab ai wlh bazan fito ba kazo ka ajiye min mota a hotel ka shiga Napep ya kaika,Haka zaka min? Wayarsa ya kashe ma haka Farooq ya dawo ya kawo motar ya shiga Napep ya wuce dare yayi dama night Flight ne shi yasa.

Tahantsi Kuwa har ta Fara bacci Baba ya dawo yaji labarin ta Musulunta dakin ya kwankwasa ganin 8pm, tashi tayi tare da bude kofa taga Baba da murna yace Ashe Kun Musulunta? tace ae sunana Khadija Kadada Kuma Fatima, Mashaallah nayi murna ubangi Allah ya dawwamar da ku a ciki har kashen rayuwa ameen tace,yace Najla tayi bacci ne? Ae yanzu dai ta Shiga bayi,Baba yace tototo so nake dama nace ta Fara shiri ko mahaifiyarta bata yarda ba ta koma dakin mijinta zaman ya Isa Haka bai Dace ba, Tahantsi tace ai sai suruki ya rainaku Baba gaskiya ku bashi matarsa wannan bai Dace ba idan ba so kuke rabo yasa a fara muku dauki dai dai ba ko a dauke ka ko Ummiya gwara ku hakura,Baba yaji tsoro yace hakane gaskiya Kar mutuwa ta riske mu,tana Ina in fada Mata ta koma, Tahantsi tace dama karya nake Baba tana can tare da mijinta a hotel,Baki Baba ya bude tare da furta hotel? Na saduda na hakura baza ku daina karya ba Allah ya shiryeku Kawai, Tahantsi ta Fara dariya tace dama duk fitar Nan da muke muce munje siyayya ko munje karbo Sako duk karya ce Baba wajen mijinta take zuwa Ni dalilin zuwana gidan nan kenan,Baba yace uhm Yan banza makaryata to ta koma wlh tun kafin matsala ta afku a gidana ya juya ya tafi.

Kadada Kuwa tana Shiga gidan Ummiya da murna ta tareta tace Ina murna,Dariya tayi tace sai azo a koyi karatu a fara Sallah Kadada tace ai nasan mura sai ta kamani sabo da yawan taba ruwa,in shiga tsarki inyi Alwala kullum sau biyar,ga wankan tsarki kwaduwa Kawai Ummiya Bari na huta, ta Shiga daki ta cire kayan jikinta tare da shiga wanka tana Fitowa Ummiya ta koya Mata Alwala,Kadada wani facal facal ana dan shafa ruwa kadan,kisa ruwa in Zaki saka mene Haka? Uhm uhm Mura Ummiya,garin shakar hanci ta ja ruwa da yawa a hancita ta fatalar da buta sabo da azaba sai da ta dade Ummiya tace sai ancanja sabuwa wannan bata Yi ba,aka sake sabuwa facal facal hancin ma Sai dan gefen kafar aka shafawa ruwa Taki ta canja sai haka aka kyaleta,Karatuma haka aka Sha fama kafin ta iya,Ummiya tace Addini sai da Hakuri da Dangana,Kadada ta harari Ummiya,Dan ubanki mene sa'arki ce? to ni me nace amma ai kin San sunan Surukina ne,Danganan? Kadada ta Dora hannaye a Kai gashi Nan kin Kara fada Kamar zata Yi kuka,Dariya ma ta bawa Ummiya tace amma ai sunan ubanki da uwarki fada kike har a gabansu da gaban kowa,sai a Kan suruki Dan ance Dangana sunansa daban abinda muke nufi daban, ya sunansa complete? Kadada tace tab ni na fada bada ni ba,Amma ai kin San sunan me shagon kofar gidan Nan ko? Ummiya tace Ibrahim? Da sauri Kadada tace ae sai ki hada da sunan Hakuri da Kika fada,Ibrahim Dangana cewar? Ummiya a zuciyarki nace ki fada fa Ummiya Dariya Ummiya tayi tace to Shikenan matar Farooq Ibrahim Dangana duk an kwashe Mana ku kunyi Lagos Saura Tahantsi ta dawo nan in kin tafi,da Tahantsi zamu tafi tayi min zaman daki cewar Kadada,Ummiya tace baki da hankali katuwa ta hantsi ce zata Miki zaman daki Tahantsi da take da son girma Allah ya kawota ki fada a gabanta kya Sha ashariya,Dariya Kadada tayi ta dauki Wayarta tace Ummiya kije Daddy ya dawo kin barshi shi kadai kuyi soyayyarku ta dattijai,sai naci ubanki Ummiya ta juyo tare tallafewa Kadada keya Yar Iska fitsararriya,Ummiya sorry ai na zaci Kun tsufa Kun hakura sai mu Ashe....baki ta gwabe Mata tashi Yar Iska ki tada Sallah Ina gani ai na koya miki,Kadada ta zumbula hijab ta Fara Sallah gata Nan dai raka'ar farko ta Fara lankwashe kafa bata taba Yi ba ihu ta saki wayyo kafafuna zasu balle Ummiya tace Sallah sabuwa ta lalace ta farko kinyi magana,Ummi ta koya Mata yanda zata lallaba tayi,Kadada tace ai sai kice zaman rakumi kafata ballewa zata Yi Ummiya,kafar dama zakisa ta danne ta hagu Kinga gani kalli aka koya Mata tana ta ihu Kashi na sai Daddy ya fito yace Kai lafiya yaga ashe duk koyon Sallah ne ya koma ciki, sai kyaleta akayi tayi yanda zata iya har tayi sallolinta,Ummiya tashi tayi ta ta Mata sai da safe tace in Zaki ci abinci Yana kitchen tace to

Kadada Wayarta ta jawo tare da Kiran Tahantsi tana dagawa su irin musulmai harda salamu alaikun, Tahantsi tace ke Binta Alaikum aka ce to naji idan za a kaini mu tafi Mana dake ki min zaman daki, Tahantsi ta kutuntumo ashar tafi goma kin Raina min hankali sa'arku ce ni,sai naci ubanku wlh ke da Fara haka tace dazu na bita to bazan je ba Ina gidan Ummiya,Kadada ta kyalkyale da dariya tace ko soyayya Kya kalla ki koya Tahantsi Muje Nana Khadija,Bazan je ba ki wuce turaka ana ta kwalwaleki ni Ina can tsuru bada Ni ba wannan Farooq din naki idonsa a tsakar kai wani Hakuri zai iya, Tahantsi tace dazu fa Ina kallonsa Yana kallon kirjina Ina tuna nin ma Hannu zai Kai na hade rai sabo da Ni ba Fara bace, Tahantsi tace keee Na saduda da Farooq na tsinke da lamarinsa,kwana nan labbaki zasu koma yellow Dan naki inaga sai dai yellow ba ja ba ko suyi kore kore,Wayyo Vamfire Kawai cewar Kadada,na Fara tausayin kaina Blue sai su dawo ma, Tahantsi tana ta dariya tace can Kuwa Ma'aikatar shike nan sai ta Allah ,Kadada ta saka kuka tace gwara na Fara tun yanzu,Ummiya nasan gobe zata Fara gyaraki tace tuni ma dazu ma ta bani wani Abu na Sha Wai na infection,Kadada na tausaya Miki kin Shiga Uku har Tashuka sai kin nemo,Kadada tace abinda Kuwa Kika ga yasa na koma Kauye wajen Iyaye to ba karami bane,bari na Kira Fara ta koya min dabaru kare Kai tun kafin, Tahantsi tace tana wajen terrorist dinta ki kiyayi Jawad ba karamin criminal bane terror ne na kirki,Suka kyalkyale da dariya har da dura ashar amma sai kiga Fara a Fuska shar kullum wani kyau take karawa da haske Tahantsi tace yo ta samu collagen din jikinsa ba dole ba,Tahantsi akwai daukan darasi ko ya taga Abu ko taji ta rike,Kadada tace bari na bashi haushi na dinga surfa Mata kira ta kashe waya ta Kira Ni

Lokacin ma Yana zaune a gefen bed Yana aiki da system Ina kwance a saman bed kaina Yana saitin bayansa nayi sama da kafafuna na Dora su jikin fuskar bed Ina ta Masa tafiyar tsutsa a baya Watarana yayi dariya ya noke jiki Watarana ya shareni,waya ce rike a hannunsa ana fada Masa Abu Yana shigarwa,Kadada ta addabeni da kira yace daga please bana Jin me ake cewa,a hankali nayi magana Kadada lfy,Ki bude murya mana Fara Hira na bugo muyi ki Kira Farooq mana,to ni da Yar uwata zanyi in Kuma bakya so na to,to Ina jinki Ina Terror dinki,wa? Terror Jawad dariya ta bani nace Zan fada Masa ai Yana ji,
Jawadiririya Dan tsako da yaji bikin Iya sai fakat Kadada ta rero wakar da su Gwamma suke wa Yara,nace Farooq Kika yiwa back to sender,Jawad ne ya juyo yace bana ji fa kiyi ki gama,katse wayar nayi yaci gaba da tasa.

Farooq bayan ya sauka yayi wanka tare da Shirin bacci,Farooq fari ne Amma ba Kar ba Dan fari fari dai Haka,dogo ne har ya danfi Jawad tsayi da kyauri kadan,Iyayensa su biyu Suka Haifa rak shi da kanwarsa Na'ima wacce tuni an Mata aure da yaranta biyu,Babansa me kudi ne sosai shi,sannan aiki Babba yake a Nnpc Lagos,asalinsu Yan Katsina state ne da Mamansa Hajiya Marwa da Babansa Ibrahim Dangana,sabo da hakurin Babansa tun Yana yaro Iyayensa Suka sa Masa Dangana,Basu da wata matsala daga uwar Farooq har ubansa.
Sai da yayi Shirin bacci sannan ya Kira Kadada,sai da tayi ringing har ta katse tana kallo tana kwance itama tayi Shirin baccinta,sake Kira yayi sai data kusa katsewa ta daga da wata iriyar murya an wani narke an shagwabe,Farooq yaji tsigar jikinsa ta tashi yarrrrr sau da dama yakan ji haka idan Kadada tayi magana da salo,Bai San Sanda yace my Binta sugar...My Shugar...Kadada aka ji wani dadi aka Kara shagwaba Kan ta baya tun yaushe kaje gida sai yanzu zaka kirani Ina ta tunanin ko kaje lafiya uhmm....aka karasa da wani da jaaaa shi Kansa Farooq sai da yayi dariya a boye, yace to kiyi hakuri ai gashi na kira mene labari? Tsaya ai ban Gama ba ya lafiyar iyayena? Wai surukanta Kadada an iya duniyanci,Farooq har da Jin dadi yace suna nan lafiya,na kusa dai nazo na dinga zuwa Ina gaisheta Allah yasa gida Daya zamu zauna na dinga Tayata aiki itama ta huta,Farooq shi kam iyayin Kadada Dariya yake bashi sai kace bazawa irin Wanda sun San Kan tsiya,ba shiri ya Danna recording sabo da ya dinga kamowa Yana ji Yana dariya,Yace ai tana da Yan aiki,Wa yake ta Yan aiki ga surukarta,Farooq Yana ta dariya kasa kasa,yace to ai gidanki daban sai dai Watarana na dinga kaiki,to shikenan cewar Kadada a ranta tace gwara da ba gida Daya zamu zauna ba nazo na samu suruka irin Umma Watarana na saki layi Tasha ashariya Allah ya taimakeni surukan yanzu masu shegen son da ga kishi da matar da a dinga bin kwakwafi idan Allah yayi tana cikin na kirki shike nan,Haka ta dinga Iyayi Yana ta Jin Dadi Yana Kara sonta bai sani ba har Suka gama waya Bai San dare ya ja da yawa ba sabo da iya hira ta Kadada.

Umma yau kaca kaca sukayi da Abba sakamakon asara da yayi a Harkar kasuwancinsa Rabin jarinsa kaf babu Kuma Umma ta nace sai ya Bata million biyar zata cika ta sai fili,Fitowa yayi cikin Fushi yana bin steps ta fito cikin Fushi ta cakumo rigarsa ta baya ba inda zakaje sai ka bani wallahi,cikin Fushi Abba ya juyo ya dinga kashe Umma da Mari har sai da taje kasa sannan ya hau jibgarta Kamar zai kasheta sai da ya Mata ligif sannan yace na sake,Igiyarki dama Saura Daya na karasheta,Umma ta kurma ihu wayyo na shiga Uku Saura Daya dama ka karasa,Nasiru ka tuna soyayyar mu ka rufa asiri muci gaba da zamanmu ba tare da kowa ya sani ba,Alhaji Nasir Yana mugun son matarsa Yana sakinta sai Kuma abin duniya ya cunkushe Masa kwakwalwa,Allah yasa yaran basa nan ba kowa a kusa sai ya fashe da kuka yace kin cuceni Ina sonki kin San na karasa igiyar data rage bazan iya jure ki auri wani kiyi auren kisan wuta ba,babu kyau mun sani muci gaba da Zaman mu ba Wanda ya sani amma Kar mu bari wani abu ya shiga tsakaninmu,Umma tana kuka duk iskancinta tace nasan akwai da yawa yanzu wallahi babu aure a tsakaninsu mazajen sun sakesu Amma so yasa sun kasa fadawa kowa baza ta iya wani aure ta fito ba sunyi Shuru sunci gaba da rayuwarsu suna ta ci gaba da haihuwa da yaransu duk Yayan Zina,Ni bazan iya ba dole mu hakura da juna ka biya kudi na samu wani gara Nan gaba na aura sati yayi yawa ya sakeni sai na dawo a daura Mana aure,Abba ya yarda yace tabbas ba kyau Amma kije ki auri na kauyenku gwara Yan Kauye da basu waye ba Kinga da wuri zai sallamo min ke,Umma tace Inshaallah tana goge hawaye,Abba yace Ashe Maman Najla tazo ta dauke yarta wai? Umma Ina yanzu ta kanta take ta daina ta wata Najla tace kowa yaji da matsalarsa Nima gashi gobe Zan tafi kauyenmu da saki ta rushe da kuka,shima Abba ya zauna a step ya fashe da kuka Suka dinga yi babu me lallashin wani

Bangaren kannen Jawad ma duk da cewar ba abinda Suka Nema suka rasa basa Jin Dadi Sam sabo da rashin Najla,ga Jawad ma tunda ta tafi baya Zama Yana Kano ya tare sai dai kullum su kirashi suna cewa dan Allah ya dawo musu da Aunty sai dai yace musu to Kawai,Maman Hafeez Kuwa dama tunda ta sheka taga ba kwaya ta hakura ta gudu gida taga Harkar Umma sai ita





AsmaBaffa
10/6/22, 22:04 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
71-75


NA KUDI NE MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP


Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA


Page naku ne

Maman Afrah
Binta Idris
Hafsa Abdullahi
@jinddah
Auntyn Khairat
Maryam Bello
Maryam T Baliya









Umma ko da yaranta Suka da dawo daga school karya ta musu tace zata tafi kauye ganin gida amma zata Dade bata dawo ba sai dai a dinga Kai

Please Login or Register in order to submit comment