Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Binta ta gama ta kawo Mata Meenat tana kuka Binta tana Jin tausayin Yarinyar ya ta iya,Meenat tuni ta fara tsaga ihu Umma ba tausayi ta cire Mata kayan da aka sa Mata Yan kanti ta bar yarinya tsirara tare da riketa Kam ta fara shafda Mata bulala tana ihu sai da ta farfasawa Meenat jiki sannan ta hankadar da ita ta Fadi bakinta ya fashe,Hajiya bulalar ta jefar sannan ta wanke hannunta tare da haurawa sama ta kwanta a makeken bed dinta bacci ya kwashe ta,Meenat tana Palo tana birgima tana ihu gashi Umma tace Kar wani me aiki ya taba ta suna ji Binta harda kuka ta fita daga part din gaba Daya sabo da tausayi.

Tana fita Jawad ya shigo gidan a motarsa ta Alfarma Fara tas yau shi ke driving Kansa sanye cikin 3qutr da t-shirt masu tsada sai shining yake Yana kamshi tun daga compound yake Jin kukan Meenat da sauri ya karaso cikin palon ya isketa tsirara jikinta yayi rudu rudu wani wajen ma ya fashe abinka da me haske ganin Jawad zumbur ta Mike tare da fadawa jikinsa tana rusa kuka,Tausayi ta bashi ya tuna matan Babansa duk da ba yaransu bane dukkan yaran sun hada sun rike babu wacce take zaluntarsu duk da kusan kowa Mamansa daban daban amma ba a samu muguwa ba kowacce Daddynsa ya aura tana rike yaran da Amana,daukan Meenat yayi Yana lallashinta

Sorry my Angel waye ya dukar min ke Haka? tana shesheka tace um..Umma ce akan nayi Kashi a wando Kuma babu me kaini toilet shi yasa,eyya sorry idan kina Jin Kashi daga yau ki fadawa me aiki kinji tace ai ban gansu ba,yace to kiyi a pow din Ayanah kinji Kai ta daga masa, ransa ya baci sosai da irin dukan da aka yiwa Meenat Yarinyar da bata San me take ba ko ba kanwarsa bace dole me Imani yaji tausayi

Yace Ina Ayanah fa? an kunna musu Cartoon let's go na gansu,dakinsu ya shiga ya iske shi kaca kaca babu me kulasu Binta ce ma take dan gyara su kullum tana kula da su duk sunyi bacci su hudu,kowacce a kasan tiles ga uban ac,Jawad Kansa ya daga sama yace dole nayi aure ko hayar Mata zanyi dole nayi,Meenat ya ajiye tare da sa Mata kayanta tace Yaya yau abinci me Dadi muka ci Yaya Hafeez ya siya Mana,Sauran yaran ne Suka tashi su ma duk Kamar Meenat suke Ayanah ce Bata kaisu ba,na kusa saku a school Kuma ai kunyi wayo murna Suka Fara suna tsalle,bedroom din ya gyara musu da Kansa ya shirya komai neat sannan ya dauki Ayanah ya Mata wanka da ruwan zafi ya ajiyeta a saman bed,ya dauki Nee'ema itama ya wanketa tas ya ajiyeta ya dauki Ameera ya Mata sannan Khairat da Meenat ya musu su biyar duk ya shirya su harda gyara musu gashi suna ta murna sunyi kyau suna ta kamshi,Binta ya Kira yace ta taho Masa da sauran a mota shi Kuma ya dauki Ayanah da Meenat ya sa su a Bayan mota,Umma ce ta fito da sauri ta karaso compound din wajen motarsa tace yanzu Jawad ka shigo baza ka tsaya mu gaisa ba sabo da Allah hakan ya dace?

Jawad ya sake daure Fuska ya ja Tsaki ko kulata baiyi ba har Binta tazo ta zuba Masa yaran a bayan mota su biyar yace da Binta Shiga gaba keda Ayanah itace karama ta Shiga Kuwa shima ya kunna mota Yaja Suka fice abinsu,Umma tace Binta Binta Zaki dawo ki sameni ku Kuma nasan bazai wuce shopping zai Kai ku ba wato ni bazai jira ya hada da yarana ba Yan guda uku sai dai iya kannensa sune Yan Uwansa zaka gani ai zaka dawo ka barsu dani wulakancin daka min a kansu Zan fanshe Dan banza marar tarbiyya duk kasar waje ta lalata shi dama dan wata sadaka yalla ne zai gaji arziki,Wai wani Yan Lebonon a gidan uban wa we shall see taja Tsaki tare da komawa part dinta.

Jawad Kuwa yawo ya kaisu suka je wuraren shakatawa da yaran tare da Binta Yar aiki 2pm suka Yi lunch a wani Eatery sannan ya musu shopping na kayan ciye ciye na Yara suka dawo gida suna parking a mota ya iske dukkan kannensa sun dawo daga school ga Salamatu matar Babansa da Aziza itama Amaryar Babansa ce Yara ne matasa Salamatu shekararta ashirin da takwas da yaronta data yaye Abeed while Aziza 24yrs take da yarinyarta Humaira itama nono take Sha amma an kusa yayeta
A Palo ya iskesu dukkan kannensa suka dinga fitowa Mata da maza suna gaisar da shi yana amsawa mazan Kuwa Hannu ya basu suna ta tafawa tsarabarsu ya basu sannan suka gaisa da matan Babansa Ya zauna Ayanah tana jikinsa Aziza tace dama wajen Abba da Kai muka zo duk da cewa kullum kana zuwa gida Kuma komai na Abinci da sutura babu abinda ka Gaza mana Alhmdllh mun gode,Jawad ya kallesu yace amma fa Kuna takaba ai da Kiran mu kuka Yi gidan,Salamatu tace a'a dole ce taso mu,Suna Haka sai ga Abba ya shigo palon

Karasowa yayi ya zauna bayan an gaisa yace Salamatu lafiya dai ko Kuna takaba zaku fito bai dace ba wallahi yanzu ana Wasa da addini ana Wasa da takaba ko Idda wanne irin abu ne zaisa sai kunzo nan,Yara ne munga sun muku yawa a halin da kuke ciki na rashi duk da nasan dan uwan nawa baza ku shekara biyu a gidansa ba tare da ya sakeku ya auro wasu kamar yanda ya Saba,ana baku ci da sha me kuke nema? Allah yasa ba kudi kuka Zo Nema ba daga mutuwa an tara muku kudin sadaka mene sai Kun dakko kafa Kun taho gidana to ku sani bani da kudin da zan baku kuci ku koshi ku zauna lafiya ga gida nan tangameme sai nan gaba za a raba muku gado..

Aziza baki ta tabe tace Allah sarki ai dai ka bari kaji me ya kawo mu ko,Umma ce ta fito tasha wanka cikin lace fari tayi kyau dama gata kyakyawa Zama tayi kusa da mijinta tana Jin zance,Aziza tace dama mun yanke hukunci kowacce gidan Iyayenta zata tafi mu karasa takaba a can,gida mu kadai kamar mayu baza mu iya ba kowa tana da iyaye gabansu zamu koma ya halatta idan da dalili me karfi mace ta fita ta karasa Takaba a gidan Iyayenta ko Yan uwanta sabo da Haka duk mun yaye Yara har Humaira na tsigeta a Shan nono zamu ajiye muku idan mun gama takaba Aure zamu Yi.

Nan take Hajiya Barira tace wallahi bazanyi jego ba bazan karba ba yawwa ba dai a part Dina ba wancan ma yaran masu girma sun isheni Allah ya gani,Abba yace to Kai Jawad kaji baza ta iya ba ya za kayi kaifa aka mutu aka barwa ka shiga Uku da kazo a Da na farko babba,Jawad cike da bacin rai yace ba damuwa ku ajiye yaran kuje,Umma Zan kawo Nanny Guda biyu masu kula da yaran kafin nayi auren, duk da haka Umma Fuska ta bata tace kayi sauri gaskiya bana son Jin kukan yaro wannan ma sun isheni mutunci Kawai nake muku,Salamatu ce ta ajiye Abeed itama Aziza ta ajiye Humaira yaran suka hau ihun kuka sabo da kiwa amma haka su Aziza suka fice tare da barin gidan abinsu duk da cewa a ransu son yaransu da tausayinsu sun cika musu zuciya amma hakan bai hanasu tafiya ba,Abba yace Kai wannan Yara da kukan tsiya suke yaja Tsaki ya tashi tare da haurawa sama abinsa,Umma ma mikewa tayi tare da kallon Humaira data Fadi sabo da kuka tana Mika Hannu inda taga mamanta ta bi,Tsaki Umma taja tace yarinya ki dinga kuka haka sai kace ana yankaki shegen Kai kamar na kwado,Jawad ka sani ko ka dauki Nanny dole fa sai kayi aure sabo da Nanny akwai mugun hali ni dai bazan iya ba amma Kai dai ka sani tana fadar haka ta wuce sashen mijinta aka bar Jawad da Yara suna uban kuka a palo.

Binta me aiki ya kwalawa Kira tare da daukan Abeed ya lallashe shi tare da mikawa Binta shi ya dauki Humaira,yace Zan biyaki kudi masu yawa duk runtsi ki kular min da kannena,Binta tace zanyi kokari duk da cewa Watarana Umma tana hanani Shiga dakin yaran,kiyi kokari dai please tace Inshaallah,dubu talatin ya bata ta karba tana godiya fita yayi direct Office ya wuce...
Hadadden Building dinsa yaje Wanda ke Lekki Lagos yana zuwa ya sallami kaf ma'aikatansa sannan ya Shiga lift zuwa Hawa na hudu inda Office dinsa yake.

Ba karamin haduwa Building din yayi ba komai glass da glass office dinsa Kuma komi na ciki fari ne kal ko Ina kamshi da sanyi ke tashi,Office dinsa katon gaske harda Palo da bedroom tare da toilet,wasu takardu ya kwashe Kawai sannan ya fito ya bar Office zuwa gidansa dake Banana Island Lagos unguwace ta sai Wanda ya Isa ya gagara,Yana driving Yana Magana shi kadai,Ido ya lumshe tare da furta Wai aure zanyi? Jawad da aure duk adana jikina da nake Tsaki ya ja kawai sannan yace ko na dakko Nanny ba Kamar matar gida ba,matar gida itace me sa Ido me Nanny zata musu haka ya dinga zance shi Daya har ya Isa katafaren sabon gidansa Da ya gama tsara shi Yana zuwa duba gidan yayi kafin ya zuba furniture ya fito
Ya Shiga mota me gadi ya bude Masa gate ya fita ya koma Ikeja GRA inda yake zaune a hadadden gidansa yan aikin gidan dukkansu maza ne me girkinsa ce kawai mace yare ce me suna Dina Yana Shiga ya iske ta shirya Masa abinci dining ya wuce Bayan yaci lafiyayyen Abinci samansa ya haura tare da sheka wanka ya dauro Alwala ya shirya cikin jallabiyya sky ya wuce masallaci sabo da magriba ta gabato.

Najla tuni na bar kauyen Kakanni na na koma cikin Kano gidanmu har munyi nisa ma da Fara Zana ssce exam.
Yau Friday bamu da Exam Ina zaune Ummiya ta fita unguwa Daddy Yana wurin aiki sai ga Kawata Farisa da Hamziyya sunyi sallama sun shugo,Ina murnar ganinsu nace daga Ina haka mu shiga Palo,Farisa tace ke dakata kiji Jawad me sadakar kudi a company dinsa dake kano gobe za ayiwa mutane interview zai dauki ma'aikata masu degree da NCE,kinsan abin farin cikin? Nace Yi sauri dan Allah ki fada min dama Ina Neman kudi Ido rufe,Farisa tace abincin Yan gayu ake bayarwa a ciki duk abinda mutum yake so kyauta zai karba Indai interview yaje,Naman kaza kala kala,kwai,zabi,friedrice,sakwara,snacks ke abinci dai ance a reception din cikin building din ba abinda babu Kuma Indai kaje interview kyauta zaka ci ko Mene,Hamziyya tace baza taje ba tsoro take ji ko secondary Exam Bamu gama ba da me zamuje interview.

Dariya na saki Ina murna nace kin tabbatar kyauta ne? Yayana yaje fa last year shi ya bani labari,yaushe za a fara? Monday 9am,nace ki zabo kayan Sallah mu shirya muje kin tabbatar abincin Yan gayu ne kuma har da nama? tace ae,Hamziyya tana kallonmu tace Allah ya shiryeku nace Ameen,Kinga Farisa Ni zanje Interview da takardu ,ke ki dauki Certificate dinki ko ma na Mene mu samu file me kyau mu zuba muje,sannan mu dau wanka sabo da raini nan muka gama shirye shiryenmu Hamzy sai dariya take Mana.

Ko da Ummiya ta dawo ban fada Mata ba Allah yasa satin kaf bamu da Exam,ranar Monday da wuri na gama aikin gida naci wanka na shirya cikin wata Atamfata sabuwa dinkin riga da skert maroon and black color nasa takalmi da jaka black da mayafi na ebo takardu biyu na zuba a file dina,Ummiya bata da teaching ranar, Kallo na tayi tace Ina zuwa haka? nace makaranta zamuje za a Mana wani lesson mantawa nayi ban fada Miki jiya su Farisa suka zo Suka fada min,Ummiya ta yarda da ni tace a dawo lfy nace Ameen ta bani dari biyar kudin Napep dana abinci na karba na fita,ban tsaya ko Ina ba sai gidan su Farisa.

Ina zuwa na ganta ta fito ma ta Sha lace dinta itama tayi kyau ta dakko takardu a file nace wanne takardu kika dakko ke? tayi dariya tace Jssce certificate na dakko da Indigene form sai birth certificate,Nace Ni Kuma commern Entrance ne sai birth certificate da state Indegene,Dariya Muka sheke nace shi yasa yau banci komai ba zamu ci kaji,tafawa mukayi sannan muka tafi tare da Shiga Napep.

Muna zuwa muka iske
Mutane dukkansu maza ne ba Mata sai mu sun cika bakin gate securities basu bari sun Shiga ba,ya hadu wajen sosai muna tsaye muma ka rantse takardun arziki Muka ebo mazan har wani magana ake Mana Kuma interview kuka Zo?nace ae wlh gashi ma Naga ba a bude ba Allah yasa Kar a barmu jira,suka ce haba ai oga Yana zuwa za a bude Mana Allah yasa muka ce,Bamu dade ba sai ga wata mota me rai da motsi ta yanko ciki ana cewa ga Oga nan haka aka wangale Masa gate driver dake driving ya shiga da mota,Bayan 15mnt aka Bude Mana gate tare da cewa masu interview su shiga,muka Shige ciki wani hanya aka bi damu Muka haura sama mutane ko Hamsim bamu Kai ba,sama aka hau damu muna ta kallo Farisa tace ko yanzu kasuwa ta tashi Dankoli yaci riba munsha kallo,wani wajen cin abinci aka kaimu akace kowa ya karya,Farin ciki ya kamani,Muka zazzauna katon wajene hadadden restaurant kujeru da Table hadaddu ma'aikatan suka Zo suna tambayar kowa abinda za a kawo masa,suna zuwa kanmu nace Kai bawan Allah ka tattabar akwai lunch? Yana Murmushi yace sosai ma Kuwa nace kawo Mana komai na wajen

Baki bude yace komai? nace ae komai da ake ci kowacce ka zuba Mata a gefe,to yace ya tafi ba a dauki lokaci ba sai gashi ya dawo da katon plate kowacce shake da abinci iri iri,Chips a gefe,yam and Egg with souce a gefe,ga wani pepper chicken, wani snack kala biyu a gefe ya ajiye Mana ya koma ya shako wasu plate din da abin ci iri iri ya ajiye Mana,ya koma ya kawo wani plate din na farfarun Naman rago daban, yace an gama Hajiya ya juya zai tafi Farisa tace tea din fa? yace sorry ya koma ya kawo Mana,nace Juice da karfi,ya kawo Juice da ruwa,sai kallonmu akeyi ana gulmar mu muna ta washe baki nace Farisa mu Fara? tace tsaya a irga uku tace 1,2,3 start muka Fara duri da Bismillah nace muyi Adduar abinci,Allah kasa abinci ya zauna lafiya a cikinmu,ya Mana amfani sai muka shiga ci ba ji ba gani,Ina cin kaza nace Kar mu bar komai sai munyi kara'i muci yanda ko tunawa muka Yi said mun dinga Jin dadi

Farisa tace ai gyatsa ma idan nayi sai naji kamshin Naman Nan,banza ta fadi naji ance sai yayi sati Yana interview kullum sai munzo don irin wannan abinci, Muna ta ci na kalli daya daga cikin ma'aikatan nace Karo Mana ac,ya Kuwa Karo karfinta,muci wannan muci wancan sai da Muka cinye komai tas Muka shanye komai ruwa ne kawai bamu sha ba, toothpick na dauka Ina sakace hakorana na kuskure bakina da ruwa sannan muka zauna Muna hutawa,cikin mazan suna ta Mana Dariya mun lashe komai wasu suna ta mamaki,sai da Muka huta sosai sannan nace a kawo Fruits salat na kwala da karfi masu bada abinci Suka sake kawo Mana,Farisa tace mene ya rage bamu ci ba? nace Coffee,Nan Tace a kawo Coffee Suka kawo Muna korawa a hankali yayinda tuni an tafi wajen interview, fitsari tuni ya fara kamani Amma na daure abina Muka tafi inda ake Kiran mutane suna shiga sharp sharp ya gama da mutane Suka tafi yin lunch sai mu kadai akace mu shiga,Farisa tace wlh bazan iya Shiga ba ai abin kunya ne dama Ni girki ne ya kawoni nace tab ai Ni sai na shiga ko banza na bata Masa lokaci na tsani naga me kudi Yana hutawa, Farisa dariya tayi na mike na Shige da takardun primary dina

Sallama nayi tuni tsaruwar office din kamshi da sanyi sun ratsani har wani bacci na Fara ji,Yana hakimce yasha wata shadda sky ya zuba kyau sai sheki yake ban San Sanda nace Jawad Fariyar Shadda, ya ganeni tsab ya nuna bai Sanni ba har gaban table dinsa na karasa Yana zaune a kujera tana jujjuyawa, tsugunawa nayi nace Ina kwana mun ga abinci kala kala mun gode Allah ya biya ka ci da marainiya Allah ne yasan irin ladan daka samu yau,wlh baka ji farfesun Nan ba dadi har yanzu shinshina hannuna nakeyi Ina Jin kamshinsa,Dan Allah wannan kajin amma daga kasar waje kasa aka kawo,ko kulani baiyi ba Yana ta rubuce rubucensa,nace an gode shayinma ice ko da Madarar Dano aka Yi sa ai kasan dano ta kasar Denmark ko? Hannu ya Miko min yace sit ga sit nan Miko min documents naki

Mika Masa nayi nace Allah yasa ka bani babban matsayi a nan,bai min magana ba ya duba file dina tunaninsa ma NCE nayi lokaci guda Naga ya dago ya kalleni a fusace tsoro ya kamani fitsari na ya fara damuna dama matsewa nayi nan take nace zanyi fitsari dan Allah,bai kulani ba nace dan girman Allah,takarduna ya watso min yace get out,rokon sa na Fara na mike tsaye Ina matse kafafuna nace Dan Allah zanyi fitsari a wando dan Allah,takalmana na cire sabo da yanzu Saura kadan na Fara Yi a wando tsalle na fara Ina Kai kawo a office din nace wayyo Kawai na hango wata kofa a Office din da sauri naje na Murda handle na shiga sai Naga bedroom komai yaji,na duba naga wata kofar na bude Ina shiga Naga lafiyayyar toilet sai kamshi ke tashi komai clean kofa na kulle da sauri nayi fitsari na a nutse nayi tsarki da ruwa me dumi sannan na shirya kaina nayi flushing tare da wanke hannuna na fito,Karo naci da shi a room din tsoro naji yace koma ki wanke min toilet,nace ban bata ma ba bani da Infection, wani kallo ya min ba shiri na koma ciki komai a kwai haka na wanke Masa sannan na fito nace angode na fice da gudu na kwashi takarduna na fice Ina haki na manta da Farisa sai data rike ni sannan na tsaya cak nace wayyo muje dan Allah,tace Naga kin dade nace muje wajen lunch first Zan Baki labari, Sallah Muka je mukayi ta azahar lokacin har 2pm tayi,

Sai da Muka koma wajen lunch mutane har sun gama sun tafi Muka je aka kawo Mana friedrice taji Hadi ga Rabin kaza kowa,juice da ruwa aka kawo Mana wani irin girki na Yan gayu haba nan ma muka Fara duri sai da Muka cinye Muna hutawa Nan na bawa Farisa labarin komai tana ta min Dariya,daga nan nace da masu abinci su zuba Mana take away,Ina fada sai ga Jawad ya fito cikin takunsa na kasaita Farisa ta rude da haduwarsa aka zuba Mana take away sai Naga Jawad an zuba Masa wani Kalar lemo na Apple Nan take aka Masa nace laaaaaaaaaa da karfi sai da kowa ya juyo sun zaci wani Abu ne har Jawad sai da ya juyo nace dama akwai irin juice din Oga Nima a hada min irinsa,Nan take wani ya dinga masifa yace tunda kuka Zo komai sai kunci to irin wannan na Oga ne ba a bawa kowa,nace to jaraba munji karka damemu,Farisa tace muje gida,nace Kinga oga Yana Sha ki tsaya ko zai rage na Sha irin nasa,wani waje na daban ya zauna Yana Sha Yana latsa waya.

Wayo nayi nace bari na dan taka ko Zan samu cikina ya samu space na fara dan zagawa a wajen da wayo har naje kusa da Jawad,idan Naga zai ganeni sai na juya naci gaba da tafiya haka na dinga yawo a wajen a dole dan motsa jiki nakeyi,Tsaki Yaja ya tashi ya bar abin da yake Sha ya fita Yana waya na zaci ya gama Sha ya tafi na dauke na kwankwade na ajiye Masa cup din,Ina juyowa Zan tafi nagan shi a bayana ya dawo, tsoro da kunya yasa na arce da gudu nace Farisa muje Muka kwashi take away dinmu nace dan Allah kayi hakuri Kai masu aiki ku hada Masa sabo me yawa yafi na baya Dadi,na kalleshi nace sorry sir zasu maka wani Wanda yafi na da Dadi da kauri Yi hakuri kaji bazan sake Sha maka abinka ba.

Jawad shi Dariya ma na bashi na maida shi yaro Tsaki yaja Kawai ya Kira driver yace su wuce Airport,mu Kuwa Muna fita Napep muka shiga Muna ta tafawa nace wallahi dole mu dinga zuwa duk ranar Interview har Muka rabu Muna Jin dadin girkin mu,Ina komawa gida na bawa Ummiya take away nace a wajen me makarantar mu yazo ya raba mana tace to mashaallah ke baza kici ba? Nace naci acan Kawai kici

yau Saturday bani da Exam Ummiya ta fita teaching da takeyi a private school nice a gidan nake ta aikina komai sai dana gama na hada furar siyarwa sannan na hau keken dinki ina taya Ummiya dinkin mata,Sallamar Daddy naji ya shigo mikewa nayi tare da amsawa nace Daddy Sannu da zuwa ashe yau zaka dawo,yace yawwa Najla ya aiki ya makaranta? Nace lfy Alhmdllh Maman naki tana makarantar ne? nace ae na mike na karbi ledar hannunsa da jaka ta kai masa daki ta kawo Masa ruwa da lemo,me Kika dafa ne? Nace shinkafa da Miya da salat bari na kawo maka,da sauri na shiga kitchen na hado Masa na kawo Masa Palo yace Allah ya Miki Albarka na amsa da Ameen sannan na koma naci gaba da aikina,Kira ya kwala min na tashi na koma yace na manta kinyi bako Yana kofar gida,mamaki ne ya kamani Wai bako ni inyi bako sabo da kwar jinin Daddy mayafin doguwar rigata maroon na yafa sannan na fita

Ina fita naga mota baka mamaki ya kamani sabo da nidai duk kyau na ban taba samun saurayi me Mota ba tunda mu talakawa ne a unguwar Talakawa na taso haka na karasa jikin motar Ina zuwa naga ya bude kofar motar ya fito Asif na gani Nan take nayi Murmushi tare da furta Barka da rana ya aiki? Alhmdllh ya gida ya su Mama? Lfy suke yace good,Nace Ina Ogan naku? Yana garinsu Lagos,Ido na zaro na tambaya dama dan Lagos ne? ae mana nace Masha Allah,Furar kazo siya ne? Ya kalleni ya saki Murmushi yace wlh sabo da Yar uwarki ta Kauye nazo tun daga Lagos har nan,sai lokacin na tuna karyar da nayi musu a Kauye nace ba nice Najla ba Yar uwarta ce a Kauye sunana Fara,Allah yasa lafiya? Yace hmmm abinda nazo da shi deal zamuyi a biyata kudi,baki na washe nace kudi za a bani ka tabbatar? Yace bafa ke ba kanwarki Fara ta kauye me hankali,nace oh to,fada min ko Mene ai yanzu Maganar kudi ita ake ji duk na rude na gigice nace ai yanzu harka Indai da kudi Kuma ba kisan Kai bace ai ita Fara Shar da ita, Asif ya saki dariya yace be calming down please You have to calm down,nace wace calm down ai nutsuwa ta Kare Ina jinka wanne deal ne?

Ogana Jawad....dakatar da shi nayi da Hannu nace Wai.... Wai ma da Jawad zasu yi deal din? Yace kwarai,me kudin fa? Ae Mana yace,nace angama dama naga Yana da hankali mutumin kirki ne ga hakuri ba ruwansa da duniya duk kudinsa,Asif ya sheke da dariya yace farko fa cewa Kika

Please Login or Register in order to submit comment