Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace mashaallah ta fuskanci basa so su fada Mata wani abun tunda taga Sanda Kadada ta bigi Tahantsi,kyalesu tayi Kawai tana tunanin yanda zata San komai,abinda na siya Mata Suka bata dana Daddy sai nasu da kayan sarinsu Ummiya tace aiki ya ganku yanzu yaushe zaku je kauyen? Tahantsi tace sai jibi zamuje

Bayan su Kadada sun tafi masu aiki sun gyara ko ina,Nima na gyara ko Ina Nawa sannan na wuce part dinsa Palo na gyara Yana kamshi,sai kitchen da sauran wurarensa,sai bedroom na kalkale toilet na dawo dakin sai dana gyara ko Mai Kawai bed ne ban gyara ba sabo da Yana ta baccinsa,tashi yayi sabo da yanda nake ta tabe tabe a dakin,Mika yayi tare da cewa ya Allah ke dai baza ki taba bari mutum ya huta ba harda tsaki, daga shi sai garen wando ya cire bargon tare da tashi ya sauko kasa yace gyara bed din na koma baccina,bance Masa komai ba na hau gyara bed din yace tsaya,tsayawa nayi na juyo Ina kallonsa yace Wai tunda aka kawoki gidan nan kin taba gaishe ni Kuwa? Ni kaina sai yanzu na tuna ana wata gaisuwa da safe Dake kowa gaisheni yake a gidan,Murmushi nayi nace Hadisi ko Aya kawo ta wacce tace mace ta gaida Miji,yace baki San ladabine ba ka gaida Wanda ya girmeka ba,tunda nayi hatsari sau daya Kika taba cewa ya ka tashi da jiki,ki dinga bincikata fa tam,nace to malamin tarbiyya naci gaba da gyara na,hararata yayi ya zauna a wata resting chair, har na gama nace to zanyi turaren hayaki ka koma Palo,dama har hayaki kike sa min a daki sai an zuba min asiri na shaka ban sani ba,Ni dama Ina da ja tunda naga nayi tunaninki nayi hatsari nasan ba lafiya Allah ya toni asirinki karki sake min turaren hayaki a room shi yasa kullum naji turaren Aljanu a room dina ashe su kike ta turo min.

Haushi naji nace me zanwa asiri anan na Masa kallon sama da kasa nace karka manta dalilin zuwana gidan nan,Allah ka rabani da yiwa Namiji asiri ya soni,Allah karka bani mijin da sai na Masa asiri zai so ni in baka bani takarda taba Allah ya konani,Allah kasa Wanda zaizo dan Kansa yace Yana son mu shi zamu aura Kuma irinsa Zan aura nan gaba,kwanciya yayi abinsa Yana kallona Ina ta masifa har na gama yace Jikar Maguzawa ke dai ki fadi gaskiya ko an biya ta wajen Kakanni an kaiwa dodo sunana,Dariya ma ya bani nayi Murmushi na gama gyara ko Ina nace muje wanka to,tashi yayi Muka shiga toilet ya zauna daram,nace yau da hammata zamu Fara sai na Kara aske ta tas karangiya ta fara Fitowa,Jawad yace Nima gobe ku hadu dasu Kadada ku zage min tawa iyayenku ma baku barsu ba sai ni,Shuru na Masa nace yau bana Jin magana dan Allah ka tsaya Wai Mene ma ban sani ba,hannayensa na dage sama yayi Kara yace ciwo na fa Zaki karasa min hannu,Sorry to shaving soap na fesawa wajen na aske da shaver,Almakashi na dauka wani dan mitsil nace tsaya gemunka wani gashin a ciki sun wuce wasu tsayi baka je aski ba,bai hana ba na daidata su dass, Maganar zucinsa ce ta fito fili kaga Yar yarinya gaskiya nayi asara Jawad tabewa ta sameka, Dariya na tsaya Ina ta Yi yace kin fiye Dariya ni kin dameni harda hararata,wanka na Fara Masa ya isheni da kunnena ruwa zai shiga,sai da na gama nace to na gama nawa sai ka wanke Kaciyar taka ka fito, yace sai na ballaki Watarana baki da kunya ko,fita nayi na barshi sai da ya gama abinsa ya fito ya dan daura towel din Kamar zai fado sabo da hannunsa bai da karfi, Zama yayi Yana huce gajiya Wai bazan shafa Masa Mai ba sai in nayi wanka,wanka nayi haka na fito da towel dina na tsaya jikin mirror

Na dakko mayuka sai kallona yake nace kai Wai lafiya? fuskewa yayi ya wani hade rai yace bani maina na shafa bana son naki yau,nace sauki ka ji,maida na fasa shafawa yau,a ransa yace wannan shegen towel Wai shi baya subucewa,Miko Miko min wannan shaving oil din Wanda idan anyi shaving ake shafawa, dakkowa nayi na Mikasa na juya Zan tafi ba zato ya fige towel dina Wai sorry eyya Ashe ba hannunki na riko ba ungo daura abinki,duk na dirirce na rasa Ina Zan shiga Kuma naki juyowa yace to ni dai Ina ta kallon Duwawu,kunya naji na juyo da sauri,na rufe Ido Kam tare da Mika Masa hannu nace Dan Allah ka bani ka rufa min asiri,yace to ana ta baki kinki karba kin rufe Ido kin juyo min kirji abu haka,na sake rudewa Jin yace Yana ganin kirjina na juya baya again yace nace na gani tubarakalla ki rufe sai ki sake juyo min baya na gani kina da baya Kuma ban siya ba,da sauri na sake juyowa idona a rufe na Mika Masa hannaye biyu ya bani towel,yace a'a Ni banzan iya rungumeki ba bada ni ba nace ban siya ba Allah,ihu na saki na durkusa a kasa,ya sake cewa harda roko karki hadani da Allah ma

Kuka na saki ya Dora min towel din a kaina yace ki dinga daurewa da kyau daga yau karki Bari na sake gamo da wanna halitar taki,a zaunen na daura towel dina nace Kuma wuta bal bal,na saka Hijab dina zanyi waje yace ashe dai a Dan kwai,a jikin kofa na tsaya nayi tafi nace ka dai ga wuta Kuma ba wani a dan a kwai, akwai chasssss nake yau sai mafarki Allah ya tsare katifa ta shiga Uku ka jawa kanka yau Ina Nan a nan Zan kwana sai na tabbatar.
Dariya Jawad yayi Ina fita yace Allah ya kawoki

Kayan da aka zuba musu manja na kwashe aka dinga wankesu a washing machine ana shanyawa duk Wanda ya bushe a goge su tass,Wanda aka yanka wannan sai kaiwa akayi inda ake Kai Mama ta mutu in an samu na zaba to su Suka sani,akwai Wanda ba a musu komai ba dogayen riguna da kayan bacci da Inners tattarawa nayi akwati uku na maida dakin Jawad sai da Muka gyara komai Zakiyatu itace tayi girkin Yara,Suka dawo yau ba Islamiyya Jawad yazo har palona ya zauna suna ta hira dasu Meenat suna Wasa da dariya,Bangaren Nawwara da Waleed ko wanne yayi gidan uwarsa ,Waleed Uwarsa ta koma Kauye cikin sokoto,Nawwara tana nan a Lagos don uwarta a nan aka ganta aka aura, Babar Nawwara ita dai bata so Nawwara ta koma wajenta ba,tace Yar nan kina can cikin daula kina karatunki kina zamanki lafiya amma ki dakko Kaya kice kin dawo wajena,Nawwara harda kuka ita tafi son wajen uwarta,Babarta tace ai Kuwa kyaci ubanki duk da ban yarda da gallazawar da Kika ce ana muku ba sai ki zauna ki sani babu kwandalata a cikin kararunki sai ki dauki tallan Lemo dama shi nake siyarwa Wanda na aura ba kudine da shi ba,Ina ta dana sanin barin gidan Mahaifinku da nayi amma kin dawo to ai shike nan sai kiyi talla kisha lemo kiyi dif ai nasan Jawad din ba mahaukaci bane zaizo har gida zanji komai Kuma wallahi idan karya kike yi sai na Miki jina jina, Nawwara tayi Shuru ita gaskiya ta fada.

Bangaren Waleed kuwa Mamansa harda murna tace Danbaba ashe kayi hankali, haka ake gallaza muku kayi kokari ma da baku lakada Mata duka ba,Waleed yace ai Saura kadan wallahi yasan a ransa karya yake Najla baza ta maru ba,tace kazo a dai dai dama shekaran jiya aka gama raba mana gado Ina da gonaki uku,ga kudi dubu Hamsim sai ka dinga kula da gonar tunda kaga ka girma Da me dadi ba abinda baza ka iya ba,Waleed ya zaci noma Wasa ne harda Jin dadi,ta ebo dubu Hamsim din duka tace dama kaga kudin nan Ina ta so inyi shawara to gaka yanzu dubu Hamsim din Nan me ya kamata ayi da ita,Waleed ya Saba da kudi ya bude baki yace yanzu dubu Hamsim har sai anyi shawara a kanta aiki sai kauye ai ni ko sati baza ta min ba Kinga wayata ta fa Mama dubu dari Yaya ya siya Mana,Maman Waleed harda guda tace ashe kadara ce da Kai haka ah Dan nawa ya girma,yanzu a sikandire aji nawa kake? Yace karshe exam zamu zana Nan gaba,Yaya Hafeez Kuma University zai tafi turai,tace Kai Kam ai baza ka shekara biyu ba tunda kana wajena sai aure,Waleed ya bude baki tace ae mu a Nan garin har Wanda basu kaika ba aure ne da su, Waleed yinin ranar in banda gyada babu abinda ya iya ci a kauyen,Mamansa Nan take tasa aka damko wata katuwar kazarta ta yankawa Waleed aka soye Masa ita tace ya ebi kudi ya siya abinda yake so,ya ebi dubu ashirin ya fice gari idan yayi yawo ya dawo ya bude kwano yaci Kaza ya fice,washe gari ma aka yanka zabo aka Masa farfesu ga kudi a aljihu yaro da hauka shi gani yake gata ne duk dadin da yake samu a Gaban Jawad bai Masa ba shi yasa akace a yaran ma akwai marasa tunani sosai

Yau da dare ni kuwa bayan na gama da Yara na musu Assignment Asmau ganin ba Nawwara ta dan sakko kadan har ita na yiwa Assignment na koya musu karatun Islamiyya,sai dai yaran su kwana a wajen masu aiki sabo da ba yanda za ayi a bar yaro su kadai,Meenat da kyar ta yarda ta kwanta can
Wanka nayi da brush nayi Shirin bacci na cikin kayan bacci wando ko gwiwa bai Kai ba da riga Yar karama me siririn hannu wasu masu laushi dark green and orange,Ina Fitowa Allah yasa da hijab dina dogo Hafeez ya shigo yace Aunty dan Allah indomie nace Wai Waleed bai dawo ba? Yace dan Allah ki fadawa Yaya Kar ya dawo da yaron nan ya rabu da su Kawai tunda basu da hankali, nace ai bazai yuwu ba kasan yaro da shirme gwara aje aji idan aka tattabar gidan Suka je shike nan,Okay Aunty Indomie din Dan Allah su Bintu sunyi bacci,to bari in na gama Zan kiraka a waya,sharp sharp na dafa Masa indomie tasha hadi na kirashi a waya ya dauka na kashe komai na wuce part din oga.

Ina Shiga naji Yana ta wayyo ya lulluba Yana ta rawar sanyi Yana nishi,Yana kaina kaina zai fashe ohhhh.....saman bed din na haura nace lafiya yace zazzabi da ciwon Kai Miko min paracetamol,na dakko Masa magani da ruwa hannunsa Yana karkarwa ya Sha ya koma ya kwanta harda cewa na Karo Masa bargo dama shi Yana yawan Yin ciwon Kai musamman idan yaje aiki ,Na sake lulluba Masa bargo na zauna a gefensa can naji yayi shuru Wai har ya sauka zazzabin ya bude bargo ya hada uban zufa harda galla min harara nace me nayi? Haka ake jinyar me zazzabi? Murmushi nayi yace Karo min ac mutum ba tausayi, ac na Karo sosai na kwanta can gefen bed yayi kwanciyarsa,da wuri nayi bacci Yana zaune sai da ya gaji dan Kansa dake na kashe light Kawai ya kwanta,gaf dani ya kwanta ya leka fuskata yaga Ina ta bacci yatsansa yasa a kunnena kadan banyi ko motsi ba,gashi na ya ja kadan Shuru,wuyana ya shafa na dan motsa kadan ya zare hannunsa da sauri ya sake jira,sannan ya jawoni tsakiyar bed kaina na sosa,Ina cire hannun a hankali yace bari a sosa Miki,ya Sosa wajen yaga ban farka ba yace sai kace gawa,girgizani yayi yaga shuru,ya daukeni cak ya maidani kusa da shi sosai yaga ban farka ba,yatsu yasa ya dallar min wuya,a gigice na farka na kalli inda nake nace waye ya kawoni Nan? Kinzo nan sai manne min kike,nace sorry na koma can inda na Saba kwana,sai da ya bari na koma bacci na ya daga kafata daya sama ya jawo ni,na farka yace Asuba tayi,zumbur na mike nayi hanyar toilet Yana kallo Dan mugunta har nayi Alwala nayi Sallah sannan yace ashe 12pm na zaci 5pm ma yanzu, wani takaici ya kamani na koma resting chair na kwanta abina sai bacci,bacci na yana nisa ya dawo ya dauke ni harda min shillo ya kwantar dani ni a bacci naji Kamar an daukeni ban iya tunawa ba sai da nayi bacci ya kwanta a jikina kuka na saki Ina dukansa a hannu wajen ciwonsa,zafi yaji ya koma gefe can inda yake,sai da baccinsa yazo sannan bai San ma yayi bacci ba,harda makara sai dana farka na ganni inda nake kwanciya ina tashi nayi brush da Alwala na fito sannan na tashe shi nace mun makara,tashi yayi shima yayi brush da Alwala dake yanzu kwana Uku Yana yin abinsa da kansa

Kadada Kuwa ranar da Suka dira a Kauye Yan Gida suna ta murna ana ta zuwa Sannu da zuwa Yara har sun waye sun Zama Yan birni,Ashariya ce Kawai ke tashi ba ga yaran baga manyan maza da Mata kowa narkota yake,Kadada tace har nayi Ja haba Kuna cikin bala'i,Tahantsi ana ta kallon gashinta Wai yasha kyau ana ta yabawa,Gwamma tazo tace wannan ai Iskanci kuka koyo,Kadada haushi ya kamata dama Gwamma kakar kowa ce sune tsofaffin gidan,tace Dan Allah kwashi gashin Hammatarki ki Kara gaba Gwamma haba gashi kinyi daura kirji jibi fa gashin hammatarki sai kace anyi adon allurai a jikin banko cako cako, Tahantsi tace baza fa su waye ba,Gwamma ta duro ashariyar tace me kuka kawo Mana Kadada data Hantsi Suka kalli juna Suka ce dama sai da Muka Yi gulmarki a jirgi,Nan fa kowa ya gigice su Tahantsi sun hau jirgi azo a gansu aka yanyamesu a gidan Wai ga bakin jirgi asha kallo ana ta washe baki ana kallon su Kadada Kamar sababbin amare akan Kawai sun hau jirgi sai da aka nutsu su Kadada aka bude tsaraba ko wanne waje garin kwaki gongoni Daya da yankan sabulu Daya da kullun omo,danginsu Kauyen sai da aka aika gida gida tsarabar Lagos,Tanoma aka sa wuka aka yanko Mata sabulu da dan tsayinsa aka hada Mata harda takalmi flat na roba Suka tafi da kansu da daddare za a Kai Mata.

Suna shiga Tanoma ta shararo ashar tace yayi mutanena ah'ah wannan kyau haka,Suka hau tafawa duk magana sai an duro ashar,Tanoma tace kunyi kyau Ina kuka baro min mutuniyar Fara? Ke Fara me farar aniya Fara anci gaba kije kiga Fara yanzu ai yanzu take farar ba da ba,Tanoma aka rike baki da cikinta a gaba,tace ya soyyaya da dan birni? Kadada tace tana can tana cin ubanta tana ta soyuwa har tayi rumus,ai mutuniyar taki anji dadin Namiji mayyar kullum tanacan wajensa Wai kula take da shi ga kudi duk son kudin Fara haka take fal fal fal da kudi Tahantsi ta gwada tana shafe tafin hannunta

Kadada tace zamu tafi ban fada Miki ba nayi katon Goshi,goshina ya girma yayo kwal gaba na samo abokin Jawad,Tanoma tace Kadada Musulmi ne? Kadada tace ae,ai Kuwa su Tashuka baza su yarda ba kin sani karki dakko bacin rai, tab wa ya Isa dani sai in bana sonsa har iyayena sai na bijire musu zaku gani,yo Ni wa nake tsoro ai sai dai kuji kallamar shahada a katuwar speaker ta masallacin garin Nan,bazan Musulunta a gidan Ummiya ba a kauyen Nan Zan Musulunta ranar juma'a sai an sa min speaker a baki kowa yaji a garin nan sannan na zabi suna Fatima daga ranar na koma Fatima Binta Sugar, kowa daga ranar idan bai kirani da Binta Sugar ba a garin nan sai ya gane kurensa ke kin sani kaf garin Nan musulmi sunfi yawa mu dama bamu da yawa, tashi mu tafi Tahantsi me Sunan lokacin Sallar walaha ,Tanoma tace au har Sallar walaha kin sani? Kadada tace ai Muna ji musulmai suna fadan komai Muna gani dole na rike Suka Yi waje,kwana daya zance ya watsa Kauye Kadada ta kusa Musulunta,musulmai a Kauye ana Sallah bayan an idar Liman harda cewa wannan yarinya Kadada da take kaunar musulunci Allah ya karkato da hankalinta Allah ya shiryeta ta karbi kalmar shahada, dama liman yasan Kadada tasha dura Masa ashiriya tafi a irga har gidansa take zuwa ta zazzageshi ta fito musamman lokacin azumin Ramadan Wai ya hanasu bacci da Sallar dare sai taje har gida tayi sallama da shi ta kutuntuma Masa ashariya ta tafi, Haka ladan ma har tare Masa hanya take yi ta antaya Masa zagi

Su Kuma limaman Kauye ga shiga sharo ba shanu har sai an zake ko cuta wani yake a kauyen su Kadada sai sun Kira sunan me cutar wane wane Allah ya bashi lafiya,ko haihuwa akayi sai liman yayiwa jariri Addua a speaker haka za ayi ta jero masu matsala a gari ana musu Addua,barawo idan aka ji an shiga gidan wani sai kowa yaji a masallaci ana addua ko Kuma sai cikin dare kowa na bacci 2pm suzo su kunna karatun Qur'ani,wani idan ya farka shi da bacci shike nan akan haka Kadada take Tawaye,Kafin Kadada ta koma wajen Ummiya har Binta Sugar ya yada gari duk musulmai Ina Binta Sugar

Bayan kwanaki Farooq ya kira Kadada a waya harda gaida shi Ina yini,yace lafiya Alhmdllh Yana dariya kadada tace bafa nason rashin mutunci zamu bata mene na wani dariya na daina gaisheka,yace sorry to afwan,Kadada tace Kai ice ko baka kule kulen Mata naga Kamar idonka a tangare yake Anya kuwa baka dan aeee.....Farooq yace Ina dake ni na isa ba ruwana ni,yawwa yanzu a Ina Muka kwana da aure kazo ko da aurere? Yace ni na isa nazo da wasa,Kadada tace to na kusa komawa Binta Sugar nan gaba idan na gama shawara da zuciyata Zan Musulunta Kai zaka Zo Kauye ka karbi speaker ka musuluntar dani Kuma duk randa ka shirya aure musuluntata sadakin aurenka tunda naji Fara tana ta karanto ko kissar musulunci ko hadisi ko me to dasu zanyi koyi abin ya birgeni naga Kuma Dan kaza kazan da zai ce aure bai dauru ba Farooq yaji Abu Kamar a mafarki shi har ga Allah bai gama tantancewa zai auri Kadada ba yarinya tsagera taje Watarana ta zagi uwarsa,gashi tsoronta yake ji ta Kar taje ta hanshi sukuni,Bayan sun gama waya ya Kira Jawad ya fada Masa Jawad ya dinga dariya yace ka shirya jihadi wallahi lada Babba Farooq, albarkacin musulunci ni gaskiya Ina jinta a Raina amma ba can ba tazo dai tayi ta zama,Jawad yace wallahi a ka'ida gobe zamuje mutum zai Musulunta ayi gaggawa sabo da mutuwa rayuwa ba tabbas,baza ta mutu ba Inshaallah karka kawo Mana zancen mutuwa ana zaune kalau ai tace sai ta gama shawara ya kashe wayarsa Farooq yace daga Wasa yaushe nace Zan aureta ni gaskiya auren dole za ayi min

Wasa Wasa Jawad ya Kai wata guda da yin accident Ina Masa abubuwa da ma kullum ciwo ba sauki Kuma sai yaje office ya dawo gida ya narke idan na daina zuwa tayashi kwana sai ya tsiri zuwa asibiti kullum yace ya tafi asibiti Wai ance yayi bugun ciki cikinsa sai ya dinga ciwo Wai jini ne ya daskare a cikinsa inji karyar Jawwad,,munyi mugun sabawa da juna sabo yawan mu'amula tare ko Ni yanzu bana son na kwana ba shi a gefe duk da ba abinda yake hadamu amma dadin hakan nake ji,ga yaran gaba daya mun shaku,Hafeez ana ta Masa shirye shiryen tafiya turai shi da Ahmad za a hada Kawai duk da Hafeez ya riga Ahmad gamawa sai yace ya jira Ahmad sai su tafi tare,Ni Kuwa batun karatu har an siya mun form Yan Yara duk mun Saba da juna,Tunda nazo gidansa watana uku kenan bai taba barina na fita ba ko bakin gate tunda nabi su Kadada sau daya ya dinga masifa ko nace ya barni naje ko shopping ne shi bazai yarda ba sai dai na rubuta a bayar a siyo,makwafta sunzo min sau nawa yaki bari naje har sun daina zuwa, yau yara kaf Yan manyan yace Hafeez ya tattara su ya kaisu yawo amma Ni banda ni,shiryawa nayi harda yin shigar musulunci ko zai barni nasa hijab na yayi masu kyau har kasa me hannu nasa nikaf, sannan na je part dinsa na iske Yana ta rubuce rubucensa Yana shigarwa Yana fitarwa Yana ta lissafi

Sabo da Ina so a barni nace dan kasuwa dan kasuwa Allah ya Kara ma lfy Allah yasa bugun cikin nan ya warke sai lokacin ya kalleni tunda yaga haka yasan ma dalili bayansa zai Sosa nace tsaya na Sosa ma,harda cewa Yi sauri kaikayi,Dariya nayi na Sosa masa na sarkafo hannayena biyu ta wuyan na kwanta a bayansa duk ba bamu taba haka ba sai yau nace naje dan Allah? Murmushi yayi yace ki dinga kaunar Allah dai ni na San ba banza ba kuje tunda kinyi shigar musulunci haka ake so ki dinga fahimtar Allah kullum ana doraki a Hanya bakya ganewa jiya ko gaishe ni baki yi ba,sabo da murna na jijjiga wuyansa da karfi gefe ya turar dani kije Saura kije ki ta yake baki kina Hafeez Hafeez harda da gwada yake bakin da hakora kina washare baki a gaban kannen Miji dama Ina ciki dake naji Sanda Ahmad ya tsokaneki kin iya girki Aunty, harda Dariya ke ga gwana ta gwanaye me tuwo ba gari jeki dan Allah kafin kisa na fasa barinki kina Abu Kamar zamanin fir'auna Kika Zo raino ko na dakkowa kaina raino,Tafiya nayi Ina dariya nidai tunda an barni shike nan nabi su Hafeez Muka ware,ko 30mnt bamuyi ba ya dinga sambado min Kira naki dagawa ya koma Kiran Hafeez yasan mitar Jawad ya daga yace kai wannan dadewarfa kwana kuke so kuyi ne,Hafeez yace haba Yaya yanzu ma fa ko 3mnt bamuyi ba,Ni kakewa musu ka rainani ko to a fasa ku dawo gida,Hafeez yace to ya kashe wayarsa

Nace dan Allah rabu dashi Muka ci gaba da harkokinmu duk munga kiransa Muka ki dagawa,ya gama kulewa sai wurin 11pm na dare Muka koma gida, ai a compound na ganshi a zaune a wata kujera,nace Kar kowa yayi magana,Ina Fitowa na fito da takalmana a hannu ya bude baki zaiyi magana nace ka godewa Allah da Muka dawo gida a raye,Jawad sai yayi slow yace lafiya nace ai da yanzu mota tayi filla filla da namanmu motar ma Sai da Muka tsaya gyara yaran nan ma takeaway Muka musu Kar a barsu haka yaro bazai ji dadi ba,Sai masifa ta koma Kan Hafeez Zan kwace Motata Zan hanaka driving baka da hankali zaka kashe min kanne,Hafeez Yana ta dariya a ransa ya wuce ciki,na bawa Yara nasu nace Masa muje Ina cewa ai Hafeez yau munga basirarsa shi ya goce abin bai faru ba

Sai da Muka shiga ciki yace anya ba karya kike ba? Nace hmm Kawai na cire hijab dina da Nikaf na kwanta a saman bed nace ga naka take away din yau bazan iya girki ba,dama ni nace ki dafa min abinci ko kinji bakina nace wance Yi min girki,me yasa yanzu ka koyi fada ne da mita? Ke Kika koya min kullum na dakkowa kaina raino,sai da yaci abinda Muka siyo yaje yayi wanka tare da Shirin bacci yace wankan fa? nace dazu fa nayi da magriba sai kace agwagwa Ina laifi kullum Ina Yi sau biyu Watarana sau uku ma,baza ki kwana a dakina ba nace tafi nono fari na mike zanyi gaba.

Yace ni kike cewa tafi nono fari? Kal ma kuwa na fada na fice,harda cewa Iyyeeeeee ae ba laifin glob bane batir ne,Ni na jawa kaina ya mike ya sawa kofarsa key yayi kwanciyarsa ya kasa bacci,sai yaji ya dawo gwauro yace Kai ya naji Kamar lokacin Ina gwauro na,Tsaki yaja yace dole ma nayi bacci na,ya kasa bacci ya tashi yayi nafilar tsakar dare har sai

Please Login or Register in order to submit comment