Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cika babban mutum aure darajarka dakin matarka,yanzu da matarka ce sai ka kwanta a cinyarta ta Sanya ka nishadi ta lallaba ka,kefa kaka? Allah kiyashe ni cinyata tunda tayi rashin Shureim shike nan ba wani Kato da zai sake daura Kansa a kanta,Dariya Jawad yayi yace kina missing abinki kenan? Kwarai kuwa wannan uban gemun naka sai kake Kama da shi,ai na dauka ku bakwa son gemu?cewar Kaka, Inji uban wa Yara kuci gaba da ajiye gemu ni kaina a baya idan Ina ganin na Shureim sai naji na sake kaunarsa wata sabuwar kaunarsa nake ji cewar tsohuwar farar, Murmushi Jawad yayi kawai tare da gyara kwanciyarsa yayi matashi da cinyar kakarsa,kafarta ta zame tace baka Isa ba kayi aure ka kwanta a ta matarka,Ni din? Ae Kai din Mana yace Zan Kuma komawa Kano bazan sake siyo Miki fura me Dadi ba,ai nasan dole sai ka siyo min ma amma dai kwanta badan halinka ba,Dariya yayi ya kwanta abinsa sai bacci.

Muna tsakar gidan tare da Yan matan gidan Muna hira masu girki suna yi muka ji ashar ta fara tashi da bala'i a sashen Nomau,Gwamma tace Nomau kaji kunya Kai Kam kayi asara,ace Yar cikinka zaka aura wannan yarinyar me ta Isa me ta sani kamarka katon gardi ga tsufa baza ka hakura da mu ba,Nomau cikin bala'i yace dama duk Wanda ya ajiye wata a gidansa ya shiga Uku shi da baccin rana sai dai ya gani anayi gaba daya Kun maida ni banza wofi nan ya fara ashar kala kala,muna ji muna kallo.

Asif ne ya shigo palon kaka ya iske tana kallo,sallama yayi ta amsa da fara'a bayan sun gaisa tace Yana ciki dazu nan yaje samansa haurawa yayi saman ogan nasa Kuma dan Uwansa,Yana Shiga ya iske shi daure da towel ya fito a wanka,Fuska Jawad ya bata tare da furta Malam basai ka jirani a palona ba Kawai sai ka shigo min yanzu da tsirara nake fa ya furta a gajiye,Dariya Asif yayi tare da Zama a gefen bed dinsa sannan yace ai sai na Sha kallo kawai wani yace ka tube,ya ake ciki ranka ya Dade zamu je Kano din ne gobe? kamar bazai Yi magana ba ya furta Inshaallah,Man ya kamata fa kayi aure ga kudi ga komai ko ni da nake yaronka Ina da Mata sai Amarci nake Sha wallahi kayi aure kaji dadi ana ta barinka a baya,juyowa Jawad yayi Yana goge gashinsa ya furta baka da aikin yi ka taba Jin Ina ko kula wata? Wallahi da me fura ma ka aura sai Naga Kuna Kama kalli yarinya kyakyawa ta kirki wannan matar manya ce,da Alama ma tana da hankali Ni nayi maka sha'awarta Kun dace,wannan ta samu Hutu sai an kalleta cewar Asif, Jawad Yana fesa body spray yace dama naga alamar sonta kake Yi in kana so ka Kara ta biyu Malam karka dameni ni bata yi min ba, wannan yarinyar Zan aura ai Kuwa da nayi asara me ta sani me zata iya nafi marfinta sai na sata yoyon fitsari nafi karfinta,dariya Asif yake tare da cewa kasan Kuwa Mata? Wannan zaka sa yoyon fitsari? Tsaki Jawad ya ja ya furta please ka kyaleni ko ka barmin room,Shuru Asif yayi yaci gaba da kallon wani Indian series a katuwar plasma din dakin Jawad.

Jawad ma Zama yayi suna kallon film din ana zuba love budurwar tana wani fari da iya zance murmushi Jawad ya saki ya kalli Asif yace karya sai film wace zata zauna tana uban wannan love din,Asif yace kayi aure ka gani wallahi abinda yafi haka Mata nayi Jawad yace Indai zata min haka kana ganina ka kirani da Sallau wato sallamamme kenan ko ka dinga kirana da Dan bila,Bila babban bawa to nine Dansa kaga Danbila kawai,Asif ya dinga dariya kamar ba gobe

Asif yace idan ka sake ka auri Yar Kauye wacce bata waye ba to ba Kai ba Jin sweety sai dai kaji ana Kiran wasu banda Kai,Jawad Yana Murmushi yace Ina son mace me iya zance wacce zata dinga tsarani ,wannan sai Yar birni gogaggiya cewar Asif,Jawad yace wa yake zancen ta kauye na aurota haihuwa daya ta ragargaje haka zaka ga nononta da wuyanta da cikinta duk sun hade sun Zama Kai daya na kasa gane Ina nono Ina wuya Ina cikinta musamman kibarta tayi yawa bada Ni ba,nafi son wayayya Yar birni,suna ta hirarsu suna nishadi har magrib suka fita Sallah masallaci.

Washe gari da wuri suka bi flight zuwa Kano inda zasu raba kudin a kauyuka Yankin Kano ta kudu Inda Suka nufi Secretariat dake garin Takai kafin su je an gama shirya mutane da komai,Babu bata lokaci Suka Isa cikin motocinsa na alfarma da sauri ya fara sauraron matsalolin mutane Yana sallamarsu lokacin Najla suna Kauyen 'Yar Kaya kusa da Yankin Sumaila sunyi kwalliya ana ta Shan biki wata ce tazo da labarin rabon da akeyi a cikin kawaye,tace bayin Allah ana ta rabo babu mu wani me kudi ne yake fitar da zakkah duk shekara gashi wannan lokacin dama ance a jahar Kano zai yi suna Takai local gamman kuyi sauri muje,Amarya me Suna Tanoma ta zaro Ido tace Al'quran kuzo mu tafi baza a barni a baya ba, Nima idan na karbi kaso na ai hike nan ko jari na kafa,ta durma min duka a baya tare da furta hegiyas tahi muje,haka na mike Muka yafa gyalenmu duk mun Sha anko kana ganina kasan Ni daga birni na fito ba kalarsu bace,haka muka cika wata karamar mota Gulf wasu akan cinyar wasu Muka tafi.

Har inda ake rabon aka shigar da mu nan take Jawad da mutanensa Suka zubawa motar Ido Saura kadan ya gama sallamar mutane sabo da dama mutane masu matsala ake tara Masa ba kowa da kowa ba,ai kallonmu suke dukkanmu da anko muna ta dirgowa daka cikin mota,Muka biya kudin mota muka tafi gabansa da sauri Amarya tana gaba Tanoma jiki na rawa tace dan Allah ka tallafa min da jari,Jawad ya Mata wani kallon Iska ya ebeta ya watsar tare da dora idonsa a kaina mamaki ya kamashi shi wacce ya sani a birni take ba shiri yace ke ba kece ta rannan ba har Muka siyi fura a gidanku ba,nunawa nayi ban San zancen ba nace laaa ni kuma? ba ni bace gaskiya Ni sunana Fara a Kauye nake Ina da Yar uwa dai a Kano sunanta Najla

Asif ne ya matso yace ke amma ku Yan biyu ne? Da sauri na daga Masa Kai nace ae Najla a hannun Maman mu ta girma ni kuma a wajen kakannina,Asif yace ohh shi yasa naga kinfi ta birni nutsuwa amma gaki a Kauye Kamar ba Yar can ba
Gado nayi kasan mu kyawawa ne jinin mu haka muke ga farin jini Allah ya bamu duk inda muke sai an so mu sai anji kaunarmu sai shegen bala'i gare mu wannan gadon Yana damuna,Asif yayi dariya yace naji ance Fara ke sunanki ne Kuma Fara? Ae da yarenmu ne duk macen da aka haifa wacce ba baka ba Indai Fara ce to sunan Kawai za a sa Mata,kaga wannan Yar uwarmu ce ita Kuma sunanta Tanoma an haife ta ana noma,Asif yace amma maguzawa ne ku ko? Nace ae,ai Jawad kakarin amai ya fara Yana masifa dama sister dinki ba Yar Fulani bace naje na Sha furarsu? Najla tace yo wa ya kaika yanzu ai an daina tantancewa,Asif ya kalleni sosai yace kamarku tayi yawa wannan ankon fa biki kuke Yi? da sauri Tanoma tace musamman muka dinkashi sabo da zuwan Oganku me rabon kudi sabo da nuna farin cikin ganinsa,Nace in kaje kauyenmu kace ankon Jawad zaka ji ance mune Muka fitar da ankon sabo da murnar zuwansa,Kadada kanwar Amarya itama tace ai na zuwanku ne,Asif ya nisa shi dai bai yarda ba amma yayi shuru,yana Gama sallamar kowa sannan ya dawo kanmu bai ko kalle mu ba ya irka 10k ya bawa kowacce,Kadada tafi ta fara kowa a cikinmu Suka hau tafi banda Ni,Tanoma ta rangadawa Jawad guda duk Yan matan sai guda suka cika wajen da sowa da guda Ina ta kallonsu Tanoma ashariya ta duro tana irga kudi kutmar doson uwa......tace dan ubanki Kadada irga kudin kwanon masara ashirin,Kadada ma ta daga nata sama tare da furta burar.....shi Jawad ma Dariya suka bashi ya murmusa sun zagaye shi suna ta faman guda mota ya shiga abinsa Suka wuce Asif har da cewa ki gaishe min da Najla,nace zata ji Inshaallah

Cikin Kano Suka wuce direct Tahir guess palace Suka Yi masauki shi da Asif,mu Kuwa mota muka Shiga sai kauyenmu,muna komawa gida Babba wato Wanda yafi kowa tsufa a gidan ya rufe Amarya da fada sai danno ashariya dan kutmar.....Burar....yace gidan Ubanwa kuka je ana Neman ki za a Mika ki dakin mijinki,Tanoma ta bada hakuri sannan ta shirya aka dauki Amarya zuwa gidan mijinta wani bamaguje Dan uwanmu gidanta ba nisa da nasu.

Washe gari da Yamma Muka je gidan Amarya Tanoma muka isketa tana kuka
Nace Amarya lafiya Ta noma tana shesheka tace abun ba dadin ji Kawai abar kaza cikin gashinta,ashe Nasafiya Dan iska ne, dodo yayi maganinsa babu ni ba shi ni da shi mun kulla gaba sai nayi wata biyu bana magana da shi




BANA BUKATAR GODIYA SHARHI NAFI SO DAN ALLAH FANS





AsmaBaffa
10/6/22, 22:01 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA🌏

6-10

Official

By
AsmaBaffa




SADAUKARWA NE GA

ZAINAB GARBA BUTALAWA


Wannan Novel a
WOMEN 24 TV kadai za a iya samun ci gabansa

SHIN KIN SAN SHAHARARRAN GROUP ƊIN NAN DAYA SHAHARA WAJEN KAWO SHAHARARRIN FINA-FINAN DA SUKA SHAHARA WAJEN SAKA MA’ABOCIN KALLONSA A CIKIN NISHAƊI DA FARIN CIKI?
IDAN HAR BAKI SANI BA LALLAI KUWA ANA YI BABU KE!
KODA YAKE HAR YANZU AKWAI BABBAR DAMAR ZUWANKI DON A CIGABA DA DAMAWA DA KE IDAN HAR KIKA JONE DA MU!

Kuna ina ma’abota kallon shirye-shiryen Arewa24 na ƙasashen waje da suka fara ba su ƙarasa ba? Yi Maza ka garzayo wannan maƙala don ƙarasq kallon shirye-shiryen.

Kuna ina ma’abota karatun lobayya wato ma’abota karatun littafan hausa? Shin na tambayeku akwai wani novel da kuka karanta har yau baka samu karashensa ba? Ko kuwa akwai novel ɗin da kake nema ruwa a jallo ka rasa? To kaima garzayo wannan maƙala domin dacewa da haziƙan fasahan littattafai.

‘Yan gayu sam! Bamu barku ba! Kina son koyon kwalliya ɗaurin dankwali kala-kala? Yi maza ki jone da mu kin ji? In sha Allahu sai dai ki koyawa wasu, domin an tanadar muku kyawawan vedios wanda zasu taimaka ki koyi kwalliya da kanki, ki koyi ɗauri da kanki.

Anzo wajen! Wato fannin girki! Ayyuriririiiii!
Duk kyan mace sai ta iya girki ta cika sunanta kyakkyawa! Maza-maza yar’uwa ki jone da mu don kuwa muna kawo manyan-manyan girki masu daɗi da ɗanɗano wanda ba su da wuya balle ma ace sai ankashe musu kuɗi. Ke dai shigo ki ganewa idonki!

Ƙarshen-ƙarshe kenan! Wato ba anan fa aka tsaya ba akwai wani babban albishir ga masu son group ɗin, shi ne babban tanadin da akai don kawai a faranta muku! Tanadin kuwa shi ne, akwai haɗaɗɗan novel da ya haɗu iya haɗuwa ya tsaru iya tsaruwa da aka yi shi musamman dan ku, wato wanda ake sakinsa a iya group ɗin kacal, wanda wasu manyan marubuta ne ke rubuta su, duk dai sai kin antayo zaki ganewa idonki. Wannan ma na ɗaya daga cikin littafan.
Kalli katsa kaɗan!



*TSARE TSAREN WOMEN24 TV WHATSAPP DA WOMEN24 TV VIP👇🏾*

DAURE KI KARANTA DAKYAU

Akwai groups guda biyar(5) da muke tura littafi wanda marubuta keyi kyauta da kuma littafin da Sai a group ɗin zaki iya samu sannan da wasu groups ɗinda muke tura videos na makeup, daurin dan kwali, girke girke, Indian Hausa da shirye shiryen AREWA24

Group ɗin akwai na *MATA* daban sai na MAZA daban bama hada *MAZA* da MATA a group saboda tsaro

*KUDIN WOMEN24 TV VIP*
Sannan maza su *#500* zasu bada mata kuma *#500* zasu bada
Wannan group in duk littafin da kika gani a ciki toh anan kadai zaki iya samun littafin inkin gani a wani guri toh na sata ne

*KUDIN WOMEN24 TV*
*#300* na masu karamin karfi shikuma shikuma *free book* kadai muke turawa wanda koh zaki iya samu a wasu groups in

Inkin biya *#500* zan saki a dukka groups in women24 tv VIP da women24 tv


*GROUP DIN YAKASANCE KAMAR HAKA*

1.WOMEN24 TV VIP NOVELS
2.WOMEN24 TV VIP AUDIO NOVELS
3.WOMEN24 TV VIP DOCUMENTS
4.WOMEN24 TV VIP VIDEOS
A wannan group in zamu dunga tura maku Videos na Makeup, Girke Girke, Daurin dan kwali, Indian Hausa da films inda *AREWA24* sukeyi irinsu Dadin Kowa, kwana chasa'in, Rayuwata, Ajeeb Akushi da Rufi da dai sauransu

5.WOMEN24 TV VIP MUNSAN JUNA WANNAN GROUP IN NA HIRA NE
Kinajin sunan groups innan kinsan meye za'a dungayi a groups in
DARI BIYAR (#500) zaki bada insaki a dukka groups dinnan guda takwas.

Account number.


2065301650
Zubairu Hayat Iman
Uba bank.


Number waya.
09030159301





Inbaki da Bank account zaki iya turo da katin MTN

'Yan Niger ku nemi wannan number
+227 90 79 59 39

Kada kibari gara basannan ta wuceki.



Page naki ne
UMMIN SADIQ



Jawad hakimce yake a palon Yayan mahaifinsa Yana jiransa kannensa Marayu Mata da maza sai Fitowa sukeyi suna gaida shi tausayinsu ya kamashi,wata Yar karamar yarinya wacce da kyar take tafiya tana gwaranci ta fito da gudu tare da hayewa jikin Jawad ya dauke Yana Murmushi bai San hawaye yana digo Masa ba,sai Yarinyar ce tace Yaya mene? Babba Yana kuka dama? tana dariya Babba Yana kuka tana tafi,da sauri yasa handkerchief tare da goge hawayensa da sauri ya daga Meenat sama Yana Mata wasa

Duk sai kannen nasa sukai ta fitowa Mata da maza kowa yace Yaya Nima dagani sama haka ya dinga faman dagasu,Samarin masu dan hankali hannu ya basu Suka tafa da kowa

Sai bayan minti biyu Abba ya fito sanye da jallabiya ya bata rai Yana hararar kannen Jawad,duk suka mike tare da komawa dakinsu,Jawad ya dan duka tare da gaisa shi ya furta Abba gani kace kana nema na,zama Abba ya gyara sannan ya kalli Jawad yace Jawad Kai Kam me ka rasa a duniya da ka kasa yin aure komai Allah ya baka ga kyau ga kudi ba wacce zata ce bata sonka amma ka zauna shashanci ni Kuwa ko matan banza kake bi bamu sani ba?

To ka sani baka da Uwa baka da uba ga uban tarin kanne an Haifa maka an Kuma mutu an bar maka,tunda Kaine Babba ya Zama dole kayi aure ka maida yaran Nan karkashin matarka...

Ni wlh bani aka barwa ba matata tace baza ta iya rike dan wani ba kaga ba yanda zanyi Alfarma daya Zan maka kayi aure cikin gaggawa ka kwashe yaran nan su koma gidanka sannan matan babanka sun ce su gidansu zasu tafi baza su rike kowa ba aure zasu je suyi har Yan yaran nan da suke Shan Nono tsige su zasu yi su bamu su tafiya zasu yi

Jawad hankalinsa ya tashi ransa Kuma ya baci da Maganar Yayan mahaifinsa ya kalle shi yace yanzu Abba Kuma ka yarda matarka tace Haka Kuma ka amince? To ya zanyi da ita muna zaune lafiya so kake na saketa munafuki,ya za ayi a daura Mata jego ita bada haihuwa ba yaranta Uku azo a bata wahala da Yara gasu nan sunfi goma Sha,Amma Abba kasan Kaka ma ta koma Labenon ni kadai a gidan a Sai Yan aiki ya za ayi na auri mace Kuma na bata jegon Yara yarinya matashiya haba Abba,kaga Jawad nima matata baza tayi Jego ba sannan bazan bari kakarka ta wajen uwa ta rike mana Yara ba ko a kasar nan take zaune bazai yuwu ba Kayi aure ka Karo masu aiki su taya matarka raino Allah ne ya Dora ma,Nima Kaka ko tana nan bazan bata jego ba bare ta koma kasarta ma ta gado,Baki Abba ya tabe yace itaku Kuma wannan Ni ba ruwana in zakayi aure kayi na baka Yan satikai ko na Kori yaran nan daga gidana,Mahaifiyar taka kafin ta rasu wani abin arziki ta shuka, Jawad ransa ya Kara baci yace ba matsala Inshaallah Zan kwashe su dama yanzu duniya ta lalace Dan uwanka Uwa daya uba daya in ka mutu bazai iya rike maka da ba,Rayuwace shima Daddy maganinsa kenan da aure aure kayi ta haifar yara gasu nan Kuma Abba kaci Amanar zumunci wlh ya mike sanye cikin danyar shadda Yana baza kamshi ya fice,Abba yace kaji shegen yaro to bazan rike ba bani nace ya tara yara ba,farko ma dana ce Zan rikesu zafin mutuwa ne yanzu Kuwa na fasa.

Jawad Yana fita compound Hafeez dan Babba da shi yace Yaya Jawad cak ya tsaya da tafiyar da yake zuwa wajen motocinsa har Hafeez ya karaso yace ka gama tafiya zaka Yi,? Jawad yace ae Hafeez ko da matsala?Hafeez yace kudin abinci zaka Bamu Umma iya yaranta ne kadai suke ci suna koshi wallahi mu sau daya take bamu abinci Kuma shima da rana Kawai kwana muke da yunwa har su Meenal,me yasa baku fada min da wuri ba? ya school fa? Hafeez yace a taxi nake zuba kowa mu tafi motocin gidan nan Umma ta Hana driver ya kaimu sai yaranta kudin hannuna ma ya Kare jiya bamu je school ba,ni kadai naje sabo da final Exam takaici ya Kama Jawad yaji tausayinsu Nan yace Kuma baza ka kirani a waya ba Zan kwasheku very soon ku Kara hakuri kunji yace to Yaya,biyoni mota suka jera har mota ya fito da dubu dari ya bashi yace ka boye ko Mene kuyi da shi idan ya Kare ka min waya a kula dasu Meenat sune Yara ku kula da komai nasu kaji, Inshaallah Hafeez yace ya koma ciki Jawad ya Shiga motarsa driver yabawa Umarni ya wuce da shi Office .

Yana Office Asif ya shigo ya zauna a kujera Yana Masa barka da aiki Jawad ya kwashe yanda sukayi da Yayan mahaifinsa ya sanar da Asif da komai ma dake tafiya,Asif yace abinda nace maka kenan Sir kayi aure komai kankantar mace tana da amfani yanda aka maka rashi aka bar maka marayu in ya kamata ace kana da Mata duk ka kwashe yaran su koma gidanka tana kula da su tare da Yan aiki suna taimaka Mata is better basai kana sonta ba a samu me hankali ko biyanta kudi ne sai kayi a aureta ta kula da Yara Kawai ta zauna tare da yaran ko da rayuwar aure bata hadaku ba sai a dinga biyanta,Jawad yace wacce marar gata ce zata yarda a aureta sabo da bautar yaran wani,ai biyanta zaka Yi ta Fadi Nawa zaka bata gaba daya daka Kai sai ita zaku San haka,Jawad yace to wa ka hango? Asif direct yace Fara Jikar Maguzawa naga tafi Najla hankali Yarinyar da muka siyi fura a wajensu da to Yar uwarta wacce ke kauyen Fara alama tana da hankali sannan suna bukatar kudi da gudu zata amince, Jawad yace amma kaje wajen Yarinyar Kai kuyi magana idan ta Amince fine cewar Jawad,Asif ya furta an gama next week zanje Inshaallah.

Umma tana kitchen ana hada abinci tare da Yan aiki tuni iya yaranta su Uku Rayyan, Affan da Nabeela Suna Dining suna breakfast da dankalin turawa da kwai ga shayi me kauri da farfesun kaji suna breakfast shima Abba Yana palonsa a can yake karyawa da lafiyayyen abinci,Kannen Jawad Kuwa tana kitchen din ta sa an dafa musu farar taliya ko wanne ta zuba plate Yar kadan kadan ta kalli me aiki tace to asabe ni nayi na Allah muna da yaji ai sai ki soya musu manja kowa ki zuba Masa ki basu suci su tafi school Kar ki manta Kar Wanda ya bude min fridge ya dauki lemo ko ruwa uban kowa cikinsu ya Sha na pampo,Asabe tace an gama Hajiya,Umma ta fice tare da haurawa saman palon Abba a can itama ta karya da farfesun da bread ga tea hadin kauri,Yaranta Kuwa tuni driver ya tafi kaisu school,Su Meenat Kuwa taliya Suka ci yaran da kansu suka shirya kansu,akwai Nawwara,Asmau da suma da girmansu zata Kai 13yrs itace ta shirya Yan yaran ta hada kansu kaf bayan sunci taliyar irin su Meenat su dama ba a saka su a school ba sunyi kankanta su biyar ne Wanda ko maganar kirki basu iya ba a gida ake barinsu Bayan an musu wanka an shirya su cikin kayan gida sai a barsu a gidan,Hafeez kafin ya wuce School sai da ya yiwa kannensa take away abinci lafiyayye Suka tafi da shi school shi Kuma ya dawo gida ya wuce bangarensu ya bawa su Meenat Suka ci sannan ya gyara su ya samu Binta me aiki duk cikin Yan aikin gidan itace kadai me tausayinsu tare da kula da lamarinsu Yaran ma itace take kula da su a boye,Hafeez godiya ya Mata ya Kara rokonta ta kula dasu Meenat kafin su dawo tace ba matsala sannan ya fita.

Umma Kuwa suna karya wa da Abba a palonsa tace yaran nan naka basu da godiyar Allah ace wai har Taliya nake sawa a dafa musu sabo da cikinsu ya dauka idan sunje school Kar su ji yunwa amma Wai Hafeez shine zai zageni su a gidansu basu San Mai da yaji ba,nace Hafeez Lagos garin arna ne kasuwanci ne ya kawo iyayenku Kar kuce lallai ku sai rayuwar Yan garin zaku dauka bai dace ba,ai sai Kuwa Asmau ta ja min tsaki Wai ai ba gidan ubana bane nan take Hajiya Barira Umma ta fashe da kuka,Alhaji Umar Dankoli Abba ya rikice Yana bata hakuri yace kiyi hakuri Hajiya Bari su dawo daga school zanyi maganinsu

Hajiya Barira tana hawayen karya tace Alhaji ka kyalesu ba komai Zan rike yaran nan idan Jawad yayi aure Naga gidansa ya hadu ka duba gidan da ya kera kamar wani Dan kwallon kafa duniya guda me zai hana mu koma can ni da yarana ya bamu part Daya ya saka matarsa a part daya da kannensa tana kula da su kaga zai Fi yarinya karama zai aura baza ta iya tarbiyyarsu ba,Abba yace gidana Honey me kyau ne Ina samu dai dai gwargwado me zai sa na koma gidan yaro da Zama Ina Yayan mahaifinsa,Amma kasan Jawad ya fika kudi ko wallahi in ya kawo wata Bamu San azabtar da yaran nan da zata Yi ba amma idan Muna kusa shike nan kasan rayuwa sai ta mallake shi yanzu Mata mallakar Miji sukeyi suna jefa shi a bala'i da asiri,Nan take Abba yace hakane Kuma bari zamu koma gidan idan zancen auren ya taso Umma Murmushi ta saki tace Alhmdllh ko kaifa shi yasa nake sonka ka waye da yawa Dariya suka Yi gaba daya

Meenat ce tayi kashi a wando ga me dan kula dasu bata kusa Umma ta hanata shiga part din,Fitowa Meenat tayi Kashi na bin cinyoyinta Lokacin Umma ta fito taji wari ta kalli Meenat tana rakubewa a bango jikinta ya hau rawa cikin maganarta da bata iya sosai ba tace dan Allah kiyi hakuyi Umma,Umma wata uwar tsawa ta buga Mata Kashi dan ubanki Kika Yi a wandon yau Zaki ci ubanki dake kabari, cikin Yan aikinta Binta ta kwalawa Kira ta fito da sauri tace wankewa Yarinyar Kashi da kayan jikinta ki gyara ko Ina data bata sannan ki kawo min ita main Palo,Hajiya me gadi ta Kira tace tsinko min bulala lafiyayya maza ka kawo min ya fita da gudu ya samo ta bishiyar dalbejiya katuwa me kauri ga tsayi ta karba tace good tare da kwalawa Asabe Kira Tace kawo min man shanu a kitchen Asabe ta kawo da sauri Umma ta dangwali man shanu ta shafe jikin bulalar da shi tana maiko tace tafi zafi ance,Asabe maida man kitchen

Kamar yanda tace haka

Please Login or Register in order to submit comment