Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ji ance wata jikarta ta Musulunta shike nan ta Fara Suma aka taru a kanta,Babba mijin Gwamma yace Gwamma tana mutuwa Zan bita mene Amfanin rayuwata ai Kuwa Gwamma ko la'asar bata kai ba Rai yayi halinsa,duk Yan gidan ba Wanda yayi kuka har yayanta dama sun gaji gashi tasha jinya sannan ta dade a duniya,bayan sun binne gawarsu yanda suke Yi a Bayan gidansu suke binne duk Wanda ya mutu dan gidan filinsu ne Guda,Ummiya taje ita da Baba da kishiyoyinta,mu Kuwa munji labari bamu je ba tunda Yan gidan basa kaunar mu gashi Ummiya tace Lallai mu shirya nida Tahantsi muje tunda ita Kadada jego take Yi.
Ana gobe suna Ummiya tazo gidan Kadada ta sauka ban ma San tazo ba sai da muka je gidan da Jawad na ganta,na Kira Jawad suka gaisa,Ummiya ta hadowa Kadada kayan Barka masu uban yawa da tsada,duk wani Abu da akeyi na alada Ummiya ta yo ta kawo,ranar Suna yaro yaci sunan baban Farooq Usman ana ce Masa Fuad,sai Bayan sati Daya Ummiya ta tafi Bayan taje sun gaisa da su Umma da Safna,gidana ma taje ta yini.

Umma Kuwa yanzu sosai muke zumunci da ita sai abinda nake so Haka yaran ma tun basa kulata suna Jin tsoro har sun saki jiki sabo da yanda take kyautata musu yanzu itama zuwa take ta kwashe min su,sosai yanzu nake hutawa,Watarana haka suke tafiya gidan Kadada ko Tahantsi dan ma Jawad ba sosai yake barin su ba,yafi barin yaran suje manya suna gida,aikin gidan nan kaf da su Asmau ake yinsa da Yan aiki sun iya komai yanzu ba abinda nakeyi sai gyara part din Jawad da nawa sai girkinsa

Cikina ya cika wata tara cif lokacin Tahantsi tana da yaron ciki na wata biyu,da kyar nake Zama nake tashi Wai Jawad bazan Haihu a kasar ba,nace kayiwa Allah ka kyaleni tunda baka ce mu tafi wata kasar ba sai Yanzu Wai dansa bazai Zama citizen na Nigeria ba,sai da na Kai kararsa wajen Abba sannan ya hakura yaji haushina Wai na Kai kararsa,Yau Sunday na tashi da nakuda misalin 5pm da asuba,Yana bacci na tashe shi yace haihuwa ce? Nace ae Ina Jin a kaini asibiti,a hargitse Jawad ya tashi da kayan baccinsa Riga da wando dogo ya daukeni nace ga kayana can ka dakko,ya sani a mota da kayan bai fadawa kowa ba sai me aiki guda daya Iya muke ce mata muka tafi asibiti,hanawa nayi nace karka Kira kowa,Muka je asibitin Ina ta Shan wahalar ciwo amma Sam ban Yi kuka ba na daure sosai,Ina ta Shan azaba har 11am ta wuce ban Haihu ba,Jawad shi Yana dakin ma kusa dani Yana min Sannu yaga yanda nake Shan wahala,sai 12pm sannan na haifo Dana Namiji Nima Kato Kamar mun hada baki da Kadada,Iya tana kula Dani har naji karfi na samu nayi wanka,in ka ganni sai kace bani na Haihu ba,daki Suka canja min na hutu,jaririn Yana hannun Jawad lokacin tuni ya sanarwa da Tahantsi da Kadada sai ga Tahantsi da abinci basket guda iri iri,Jawad Jariri ya Hana Yana hannunsa yace lallai Khadija ke ta daban ce Yanzu nake tunanin zuwa na Nemo mata abinci sai gashi kin kawo,nace yunwa nake ji a bani abinci, Tahantsi ta hada min tea me kauri ga farfesu ga chips haba na dafe Kan girki naci na koshi abina sannan Jawad ya zuba yaci shima,ba a sallame mu ba sai da aka tabbatar lafiya nake sannan,Jawad harda tambayar likita iceko Bata karu ba idan Kun San ta karu ku dinke min matata tsaf ko na dinke abata,bata karu ba sir ai da tuni mun Mata dinki,Jawad yace yawwa to sannan Muka bar asibitin,a gidana na iske Kadada da Farooq tare da dansu Fuad, Suka karbi jariri me Kama da Jawad sak,a yau ya sanarwa da su Hafeez da kakarsa,yaran gida sai Murna sukeyi da ihu abin gwanin birgewa,su Meenat cewa sukeyi kaninsu ne,Jawad yace danku dai kune kannena shi danku ne Meenat,Meenat suna ta dariya ita da Ayana Suka ce Yaya Muka ga dai Bamu Muka haife shi ba,yaushe zamu haihu mu sai mun girma ko Yaya? Jawad yace to shike nan ga Kanin naku nan yaga baza su gane ba,ranar Safna tazo Umma Kuwa sai dare tazo,Baba Yana ji ya kirani a waya Wanda a baya Baba ba ruwansa dani lallai yanzu Baba ya canja sosai da sosai ma,haka mutane Suka dinga sintiri har ana gobe suna Nima dai irin Kadadan nayi ba suna,Su Ummiya sunzo da kishiyoyinta,haka tanoma tazo da wasu Yan gidan maguzawan,munyi mamakin ganin Tashuka Babar Kadada da Babar Tahantsi Wai sunzo Mana ashe Suma sun Musulunta,yanzu da yawa gidan Maguzawa duk sun musulunta.

Abin ya mana dadi sosai mutuwar Gwamma ta jawo kowa Musulunta yake musulmi sunfi maguzawan yawa a gidan,ranar Suna yaro yaci sunan Baban su Jawad wato Muhammad,su Asmau suka sa masa Prince haka kawai,haka Jawad yace a rabu dasu tunda sun sa masa Wai sabo da kyansa Suka sa Masa,Meenat kullum suna wajen Danjariri ita da Ayana,sai bayan suna su Tashuka Suka koma gida da Sha Tara ta arziki,su Kadada suna ta murna,su Hafeez dai Muna Waya,ga Abeed da Humaira sunyi wayo sosai,Iyayen yaran ma wasu sunyi aure suna zuwa ganin yaran su Watarana Kuma Jawad Yana sawa a Kai su hutu su ga iyayensu mata sannan suna zuwa ganinsu har gida harda alherinsu.

Jawad tunda nayi sati biyu sai dai iya romancing har ana gobe zanyi arba'in ranar Kuwa ko aiki bai fita ba ya Kafa ya tsare sabo da yanda na hanashi yin komai nace sai nayi arba'in,shabiyun dare 12am ranar 39 yana zaune Yana kallon agogon wayarsa yace to Alhmdllh 12am kinyi arba'in lokaci ya fada,nace sai kace wata Christmas, fa munje Kauye da wajen Ummiya ganin gida mun dawo sannan ake yin wani Abu,Jawad yace Ina wlh bazai yuwu ba,bazan iya ba ya jawoni jikinsa,Jariri ne ya fara kuka Yana bed dinsa kusa da namu,Jawad yace iyye au bazan taba uwarka ba ai Kuwa yau sai dai ka Suma ba ruwana,Dariya nayi nace Kai Honey shi yasan me kakeyi ne,Jawad yace ai muyi kukan mu tare da shi Yana Yi Ina yin nawa na dadi,abinka da an Dade ba a hadu ba Yana farawa na bada kai sabo da yanda na Sha gyara nima a kusa nake,munyi missing juna sosai yau Muka raya daren mun jiyar da juna dadi sosai Yau Jawad Kamar zai Yi hauka na samu na bashi mamaki yau,yace bai taba Jin Dadi irin na yau ba yanda na bashi kulawa na nuna Masa kauna,sai da Muka nutsu bayan munyi wanka nazo na dauki prince na bashi nono yasha sannan ya koma bacci,da asuba sai da ya kara Yi,ranar bai fita office ba Kawai moreni yake.
Sai bayan sati daya ya barni Muka je Kano Ni da su Kadada,gidan Ummiya Muka Yi 2days Kauye Muka kwana biyu gidan Maguzawa yanzu Mata da maza da yawansu musulmai ne.
Kadada har da zuwa gaida liman me sata a Addua a kauyen ta bashi dubu ashirin ranar a masallaci har jaririn Kadada yasha Addua,Jawad Kuwa yanda Abba ya Umarce shi haka ya bawa Megari dubu dari biyar ya Kara jarin noma,sannan Abba ya biyawa me gari da Sahura aikin Hajji sanadin Umma.
Daga baya tafiya ta tasowa Jawad zuwa Italy akan Business,Yana fada min na dinga kuka dole yace na shirya ya tafi dani,ya Mana Shirin tafiya nida Jariri muka cale,sai da lokacin aikin hajji yazo Muka hadu da su Kadada da Farooq a can,tare da Ummiya da Baba,ga Sahura da Megari duk inda kaga Megari Yana manne da Sahura dariya yake bamu komai Sahura,Muna zaune a wajen darul Tauheed yazo shi kadai Ina kusa da Jawad muna Shan ice cream ya ganmu ya karaso yace Baku ga Sahura ba? Jawad yace dazu na ganta ita da wata Yar Pakistan sun fara kawance ta bita, Subhannallahi inji Megari shike nan zata gurbata min rayuwar Sahura idan nayi sake sai ta shigar da ita kungiyar Yan Alkahira ko Yan Taliban masu kashe kashe kungiyar su Osama bin laden,Falau falau Megari ya Kara gaba ya tafi Neman Sahura da kyar ya ganta tare da Yar Pakistan suna ta Maganar kurame to kowa baya Jin yaren kowa Kuma kowa baya jin turanci Wai Kuma a Haka Suka Yi kawance megari yace da biyu in Ban akwai wata manufa bata Jin yarenki bakya Jin nata dukkanku Kuma bakwa Jin turanci da uban me zakuyi kawancen ya fisgo hannun Sahura ya janye a barsa yace haka Kawai a jawo min ki Fara yankani da wukar yanka albasa,muna ta dariya da Jawad Muna kallon Megari,lokacin Tahantsi ta Haifi yarta mace kyakyawa taci sunan Maman Aliyu Amina.

Sai da muka kusa shekara muna Italy sannan Muka dawo gida Nigeria lokacin su Hafeez suna final year suka Zo Hutu,subhannallah Hafeez yayi mugun girma ya Zama saurayi,Haka Ahmad ma kansu daya sunyi hankali sosai sun wani ajiye gemu da saje,suna tashi komawa aka hada su da Waleed dan level 1, Nima Jawad ya Nemo min makaranta private university Ina zuwa,su Kadada ma suna ta makarantarsu abinmu Shar damu har su Hafeez suka gama Suka dawo aka bar Waleed,shima Yana can aka Kai kannensa maza su biyu masu biye Masa,Hafeez tuni Jawad ya Dora su a wasu company nasa sun fara aiki sosai,Suna zuwa wajen iyayensu Mata Kuma suna tallafa musu.

sai da Kadada ta shekara hudu sannan ta sake haifo Mace,Ni Kuwa bani da ciki har Tahantsi ta Kara haihuwa ta biyu Namiji,sai da na Gama makaranta sannan na haifo wani namijin lokacin Asmau da Nawwara sun gama Secondary an saka su a university a nan Lagos.
Har Hafeez da Ahmad Suka fitar da Matar aure,Hafeez wata Eesha zai aura a Jigawa state take yarinya me hankali kyakyawa Wai a kusa da office dinsa Suka hadu tazo Lagos wajen Yar uwarta,shi Kuma Ahmad a makaranta Suka hadu Yar Adamawa ce,Jawad yace sai su jira a hada da Asmau da Nawwara a huta tunda yaga suna da samari dukkansu a Dangin Iyayen su mata Samarin Suka fito suna da aikin yi,Asmau Kano za'a kaita Nawwara a Kaduna,tunda sun girma Kawai ayi musu auren sa karasa makarantar a gidan mazajensu cewar Jawad.
Ai kuwa mun Sha biki sosai an Kai Amare an musu duk abinda ya dace.
Umma ma kannenta an musu aure tuni.
Haka rayuwar taci gaba da tafiya Alhmdllh komai yayi normal Bamu da matsala sai abinda ba a rasa ba.

Safna ma ta Haifi yarta mace,Ummiya Kuwa bata sake haihuwa ba,wata kiba tayi da kyau Kawai Jin Dadi takeyi farin cikinta sai a karshe yazo,gidan Maguzawa yanzu babu Arne ko Daya duk sun musulunta Banda mijin Gwamma Babba yace bazai taba Musulunta ba yanda Gwamma ta mutu Haka zai bita sai ya cika Mata burinta,ai Kuwa shima Haka ya mutu kafiri
Mu Kuwa mun Kara gogewa baza kace mun Haihu ba,kana gani kasan muna Jin dadi mun sake yin hankali mun nutsu,su Kadada duk shiriritar nan Saura kadan duk babu sai dai abin dariyarsu Wanda dama mu Haka muke baza mu daina ba Kuma sai ta Allah.
Wannan karon Jawad Dangin Mamansa yace zai kaini can kasar na Kai musu ziyara duk da cewa wasu sunzo Mana na sansu,muka shirya da yaranmu biyu Muka bi jirgi Muka ware.
Muna cikin jirgi yaro Daya prince Yana jikinsa Nima karamin Fawaz Yana hannuna, Jawad Yana tsokanata uwar maza next ma Namiji Zaki Karo min,nace Inshaallah mace Zan Haifa ta Allah ba taka ba Yana ta min dariya yace to zan gani,Nace IInshaalla mace,Yana dariya Yana ta Mana video a waya har yaran Muna nishadinmu abinmu cike da so da kaunar juna.






ALHMDLLH

Nan na kawo karshen Jikar

Ina Matukar bawa fans Hakuri na rashin posting akai akai da aka samu,a karshen novel din ne yazo min da abubuwa ne na rashin samun lokaci,duk masu karanta novel Dina sun San ba a fasa Posting Indai lafiya lafiya wannan novel din ne a karshe ban samu lokaci ba,Ayi hakuri da hakan yanayi ne na rayuwa.


Idan an samu kuskure ayi Hakuri dama baza kayi abu 100% ba dole a samu kuskure.

Masu sharhi Ina Matukar godiya na gode Allah ya hadamu a sabon novel ya kaimu da rai da lafiya

Allah ya biya muku bukatunku fans Ina godiya da Adduoinku










AsmaBaffa

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment