Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya hana a kira ni, Ummiya ma amsarta jiya ita ta basu yau,Wasa Wasa Jawad ya nace fashin kwana dai dai sai yazo kano har anyi sati biyu Yana ta zuwa amma a bari mu hadu anki,Yan kannen nasa ma ya daina ta tasu waya Kuwa kullum sai mun raba dare muna waya ganin haka Baba ya kwace Wayar ba kukan da banyi ba,Jawad ya daina samuna,Hankalinsa ya sake tashi yace dole Naga matata wlh na gaji, Yana zuwa Kano yau Sunday ana zuwa daukansa ya karbi key din mota da Kansa yayi driving zuwa kofar gidan Ummiya daga can bayan gidan yayi parking ya tura yaro ya Kira Masa Kadada,Yaro yazo yayi sallama Ummiya ta amsa yace Wai ana Sallama da Kadada,Kadada dake makale da headphone tana Jin kida kasa kasa tace kaje kace tana da Saurayinta me zan ci da shi, Yaro ya dawo wajen Jawad yace tace Wai tana da Saurayinta me zata Yi da Kai,Jawad Jin amsar yasa itace yace kace Farooq ne,ya koma yace Wai yace Farooq ne,Kadada ta mike zumbur tace kace gani nan kace Ina Miko gaisuwa kafin na karaso,Yaro ya sake dawowa wajen Jawad tace gata nan Wai tana Miko gaisuwa kafin ta karaso,Jawad yayi dariya yace to ya bawa yaron dubu daya ya tafi Yana ta murna da godiya.

Motar yayo gaba yanda zata gane shi,ya ganta da Leda a Hannu ta fito tana kalle kalle,horn ya Mata ta Gane tayi wajen motar,tana zuwa ya sauke glass kasa taga Jawad tace ah Babban Yaya me Najla komai dozin an ganku jiya gashi an ganku yau gobe muke saurare,sannu ya zafin soyayyar? Ya akaji da radadin love,Jawad yace shigo mota,ta bude gaba ta shiga ta Mika Masa lemukan data taho da su harda snacks tace jiya naje Oasis yace uhm Yan gayu,Dariya tayi yace har kin karbi musuluncin ne? tace Ina nan dai na kusa Ango nake jira ya shirya,Jawad yace ai mun shirya,Dariya tayi tace Ina jinka nasan da dalilin zuwanka,Yace so nake Kawai ki San ya Zaki Yi Najla ta fito na ganta please, Kadada ta kalleshi a ranta tace dan jakar uba lips dinsa har yayi duhu Najla bata tsotse shi, a fili tace so kake dai kaga matarka ko? Yace ae ki sato min ita na ganta,Kadada tace Maganar gaskiya a Gaban Ummiya nake ta sa min Ido gani take damu aka hada baki aka auri yarta da kudi, Kuma Ni ban iya abun Muna Muna da boye boye ba,Amma ga guarantee Tahantsi kasan ta hantsi itace shugabar munafunci da boye boye da hada gidoga ta gidanmu,wannan wajen in aka Zo to kowa sai yaja baya, Sha yanzu magani yanzu Tahantsi a yanzu da Zan Mata waya nace ta taho zata zo 1hr zaka ganta a nan kasan kauyen ba nisa ne me yawa ba,yace Indai tazo dai Zan ganta? Kadada ta kwankwashi jikin mota tace ai kaga Fara an gama ko da sojoji ake tsaro, Kai da ace Tahantsi ta waye tsab zata Shiga damfara,Jawad yace Kira ta,Kadada ta latso number Tahantsi tana ringing din...din..din..ba'a daga ba tace tana can a jaka ta barta ai Tahantsi na rasa irinta,sai da aka sake Kira sannan Tahantsi ta daga waya Kadada ya akayi ne Dan kaza kazanki wannan irin Kira haka,to ki bar komai ki taho Kano,Ummiya ce ta mutu? Tahantsi ta tambaya,taci gaba da cewa wayyo Fara ta fito rana,Kadada tace ke ba itace ba Kin San dai labarin na fada Miki Fara na gida,Tahantsi tace Haka kikace na tausaya Fara an Saba da harka kullum an makale a gindin Jawad to yanzu dai ya huta,Kadada tace ke Yana jinki dai, Tahantsi tace shine Kika sa Handsfree Ina Jin kunyarsa to sai dai yayi Hakuri mu bakinmu duk su Gwamma basu gasa shi ba,Jawad har ya gaji da Jin surutunsu shi ayi a fito Masa da Fara.

Kadada tace ya kuwa Tashuka ta? Jawad yace dan Allah kiyi abinda ya kawoni, Kadada tace to ke kyale lafiyar Tashuka sai Nan gaba ayi zance yanzu ki taho fa yanzu kizo ki fito Masa da Fara ya ganta yace zai iya mutuwa,Tahantsi tace ai dole tunda an hanashi ganinta tsofaffi fa suna Wasa da soyayya,Kadada tace sun dauka zamanin da ne yanzu kisa take, Jawad yace bani Wayar ta Mika Masa yace please ki taho tace yo gani na fito ma Yaya Jawad,har kin shirya? Wa nake dashi da sai nayi kwalliya ai matsalarka tafi tawa gani nan ta kashe waya,Kadada taci gaba da Zama a motar Jawad anki kashe mota suna ta Shan ac da kamshi,tace Ina su Meenat Kuwa? Yace suna Nan lafiya tace to ya ka baro min mutumina yace yace a gaida ki,to ga lemon Nan kasha tunda rabonka ne ba kai na siyawa ba amma ka Sha in yazo Kuwa bazan asarar kudina ba ka jawo masa,Jawad Yana ta dariya ya dan samu nishadi sabo jini wani abin idan tayi sai a fisge yaga Kamar Faransa

Ai kafin 1hr ma Tahantsi ta dira a kofar gidan Ummiya Kadada ta balle mota taga Tahantsi har da jakar tafiya da alama zata dade a cikin garin, Tahantsi tace yawwa nazo,ki fito Masa da Fara ko ta halin Yaya,Tahantsi ta sake tambaya Kawai yaga Fara? Kadada tace ki dinga wayewa Tahantsi karki aure mijinki ya dinga saki a kwalaba tam,idan ta fito ki basu waje baki ga wannan karon Lips dinsa ya dan canja ba, Tahantsi ta leka ta glass tace Kuma fa haka ne,Jawad dai yaga suna kallonsa ta glass, Tahantsi tasa kayanta a bayan mota ta shiga gaba tace muje da fatan ka tanadi wurin kwana a Kano kullum kazo Zan fito ma da Fara,Jawad yaji Dadi sosai.

Bayan layin gidan Baba tasa yayi parking ta fito da Jakarta yace karki dade tace to,tana shiga gidan Baba ta ganshi da baki maza,ta gaida shi yace ah Tahantsi ce a gidan, Tahantsi tace ae naji ance Fara tana nan shi yasa nazo na Mata kwanaki,Baba dake Namiji ne ba sa Ido ba zargi yace tana ciki Shiga madalla ,Tahantsi tana shiga ta ganni a Palo ina hadawa Yara tv game,naji dadin ganin Tahantsi nace oyoyo ya akayi Kika San Ina nan, muje ciki cewar Tahantsi sai da muka Shige bedroom dina sannan tace karki Bata bakinki Kadada ta sanar min komai,ta fada min yanda Suka Yi da Jawad,nace da gaske Kuna tare nace kwarai shirya mu tafi,Muna fita nasan me zance da Baba,da murna nace dama yanzu nayi wanka, English wear ne ajikina Riga karama da skert marar nauyi Tahantsi tace ki matse ki tsuke, nace kin gani nanyi kalleni,tace Dan dada tsukewa, Tsaki Naja Hijab na saka da Nikaf nasan Jawad haka zai ce na fito jiki a waje shi yasa na saka,Tahantsi tace muje,Muna Fitowa naci Karo da Baba yace Ina zuwa? Tahantsi tace wani Kaya aka turo shine zata rakani na karba Kuma da sunanta aka turo da address din Nan Ni ban San wajen ba,Yace ba izinin mijinta zata fita? nace ai yace duk inda ya kamata naje,yace to karki dade nasan kina sonsa baza ki karya doka ba, nace to Muka fice tare da Tahantsi tace muje Muna ta sauri Muka Shiga Napep zuwa inda motar Jawad take ai Kuwa ya ganni yace Tahantsi Allah ya Kara tsawon rai ashe da amfaninsu

Tana ganin na shiga mota ta wani Shige gidan mutane bata San suwaye ba,tayi sallama aka amsa tace dan Allah zanyi Sallah Suka ce to Dake sun ganta da mayafi da doguwar Riga,ta Shige toilet tayi fitsari ta watsawa fuskarta ruwa da kafafu ta fito aka ce sallaya tana ciki ta Shige ta zauna Allah yasa ba kowa a dakin tayi luf a zaune.
Ni Kuwa motar na shiga Kawai yaja motar ya bar layin yace safe wuri zanyi parking,nace to,ya tambaya Ina wayarki? nace Baba ya kwace wani garden ya shiga Ni ban taba sanin da wajen bama, ba kowa a wajen,yace na dawo Kano da zama sabo da ke Nasha wahala Ina ta Sha ma,kullum sai nazo Ummiya taki Hakuri,nace uhm shi yasa Watarana nake Mata karya.

Sai da ya daidaita parking sannan ya kalleni yace to cire nikaf din mana,cirewa nayi yasa hannu tare da dago habata sama yace ya Naga idonki duk ya zuge? nace ba komai na cire hannunsa,dagowa nayi na kalleshi Naga Ni yake ta kallo nace daina kallo na,yace abinda ya kawoni kenan naga matata,duk Yana fada min a waya na San da gaske yake Yana so na,yace kin san bana karya I love you Fara, Dadi naji nace hmm,yace sau Nawa Zan fada baki taba amsawa ba sai hmm hmm harda marairaicewa, Shuru nayi harda shagwabar samun waje nace ni da kace yarinya ce,to kiyi Hakuri I'm sorry babbace ai na sani,Hannu yasa a kumatuna yanda akewa Yara Yar fara faratu white angel Dariya nayi ba shiri na duke shi kadan a kirji,yace ga abincin Kadada data bani na duba nayi Dariya ya bani labarin komai da zuwan Tahantsi,yace har Tahantsi tasa nayi Mana booking Hotel tace bakya Sha min lips gasu nan sun tashi daga ja,na kalleshi Ina dariya nace karya suke Nima tana zuwa haka tace Wai lebena ya koma na Yan sigari baka sha,Dariya mukayi yace muje yawo,nace Tahantsi fa? Kyale Tahantsi tasan aikinta, to nace

Sai da muka tafi yawonmu ya kaini Arab restaurant parking yayi yace Hajiya Sa Nikaf na saka Muka fito hannunsa cikin nawa a nan mukaci abinci Muna nishadi Muka fito muna Fitowa Muka wuce ShopRite hannunsa cikin nawa,Sai da na zabi abinda nake so sannan Muka dawo inda Tahantsi take,Muna jira mu Kira muji Ina take Muka hangota da Leda Wai siyayya ta tafi,tace har Kun dawo ai baku Dade ba,Jawad ya zaro Ido yace ai sabo dake,laaa ku daina ji na ai ni sai na kwana a kwararo Indai a birni ne ko Ina haske ga mutane haske kadai sai yasa gari ya waye ban sani ba,daga yau ku dinga tafiya sha'aninku,Dariya mukayi ta kalleni tace muje to Muka kwashi Kaya Muka tafi Jawad ya Shiga mota ya koma hotel hankali kwance harda bani Yar karamar waya da Zan boye.

Tahantsi tace har kin dawo hayyacinki ga labbanki duk sun tasa ki dinga shafa Vaseline Jawad bai San kadan ba,Ke Fara ki Fara gyara karku hadu a hotel gwara ya sake jinki daban kin sake canjawa,ki dai Sha ko Dan hadin zuma ne yanda zaiji zakwai karki jawowa kanki yaji ki wata gasara gasara ko Kamar sirkin Farau farau,Ina ta dariya nace Zan ci ubanku wlh Kun dameni ke da Kadada tam, Danbashananan fa bai Kare ba na taho da wani na Mata banza
Muna komawa gida Baba ya tafi masallaci Sallar Isha.






AsmaBaffa
10/6/22, 22:03 - Buhainat: 🌏 JIKAR MAGUZAWA 🌏

61-65

NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP
IN GANSHI A WANI GROUP NA SATA NE


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA



PAGE NAKU NE

Ummu Umayma
Mamma
Nana Firdausi
Mmn Muniba
Fancy Honey








Baba Yana shigowa ni ya fara tambaya Najla Kuwa sun dawo matarsa Sara tana tabe baki tare da gatsinawa Baba fuska tace sun dawo,Hajiya Sarah bata kaunata Kar mu'amula ta dinga hada Baba da Ummiya Kar Watarana ta dawo,shi yasa ita da kishiyarta basa so Baba ya dinga kulani ko kannena da muke Uwa daya su mu hudu, Baba yace Allah ya shiryeki ya wuce ciki abinsa,yau na samu waya haka muka raba dare muna waya,washe gari Kuwa 11am Farooq yazo zance wajen Kadada, Jawad ya Kira a waya yace gani na shigo kazo mu koma biko,tsabar nacin Jawad wanka yayi ya shirya cikin Shadda fara Yar gaske harda coka hula za aje gidan surukai,Farooq ne ya dauke shi a mota daga hotel din Suka wuce gidan Ummiya,sun kusa da gidan Suka hango Kadada tana ta sauri yau ma da Hijab,Jawad yace mutuniyar fa an dage kusa da ita Farooq yayi slow tare da sauke glass yace Yan Mata Ina zuwa Haka ne,Kadada taga sune tayi Murmushi tace Kauye Zan tafi Jakata ce haihu,Jaka dana sani Kadada tace ae Donkey ba ta macen da kudina na siyeta tun tana karama,duk raguna da tinkiyoyi awakai basu Miki ba sai Jaka Zaki siya,ai tafi tsada sabo da kaga ita aikin kudi ake da ita,Farooq yace Allah yasa Yan biyu ta haifo, 'ya Daya ta haifo haka aka fada min a waya hankalina bazai kwanta ba sai na ganta,Jawad yace yau Juma'a fa get in mu kaiki,yace Kira ta hantsi su fito mu tafi har Fara,ana Kiran Tahantsi tana dagawa da masifa lafiya shayi muke sha kin fada min jakarki ta Haihu na Miki barka to ba shike nan ba sau Nawa kike so na Miki barka,Kadada har zata zundomo ashar sai ta fasa tace kuyi ku fito ke da Fara zamu tafi kauye,Allah sa ba Gwamma ce ta mutu ba,in ta mutu ma ai Tasha Miya ita kam,ga su Yaya Farooq suna jira zamu Zo kusa da gidan Baba kuyi sauri,Kisan ya Zaki da Baba ku fito,Baba ya tafi Rimin gado ziyara wa babban abokinsa sai sanda aka ganshi,ku shirya to,Kadada aka shiga bayan mota ita daya Suka tafi,Kadada ana cikin tafiya tace a tsaya bakin wani shop,inda ake siyar da Apple da guava ciki Kuma lemuka,suna kallonta ta fita ta ciko Leda da Apple da Ayaba da lemo Kuma da yawa,ta Shiga ta jido lemuka ta buga Gaban mota a bude boot suka bude ta saka lemuka carton biyar ,ta rufe ta shiga mota tace muje,Farooq yace na mene wannan? Yan gida za a kaiwa tsaraba inji ku, Kaji aikin hankali cewar Farooq Kuma ba sai ki fada Mana ba,ban iya roko ba,Jawad dai magana ba fiye Yi yayi ba sai yaga dama,waya ma yake tayi Yana tura sakonni,Suna zuwa muka fito wannan lokacin Riga da skert na saka na lace purple mayafi na yafa da jaka a hannu takalmina me tsini,duk da ban Saba tafiya da shi ba amma nayi kokari,Jawad haushi yaji na Sako mayafi naci kwalliya,Ina kallonsa ya bata rai,Yi nayi Kamar ban gani ba na shiga gefen Tahantsi,Ta hantsi ta dinga masifa duk na girmeku ya za ayi ku sani a tsakiya sabo da Kun Raina min hankali,Kadada tace to Jaraba Kai Kamar an kifa kwarya koma gefe ni na shiga tsakiya Fara a barta a saitin mutuminta,Yaya Jawad ka saita Mudubinka na mota Fara ta sheka kyau,Murmushi yayi Farooq ya juyo da Kansa Wai zai ga kwanlliyar Jawad yasa hannu ya Murda Kan Farooq Gaban mota yace kayi abinda ya kawo mu, Ta hantsi ta saka earpiece a kunne tana bin wakar christoci Haleluya....Haleluya....in the name of Jesus,Kadada ta tabe baki tace ke Kuma haka Kika tabe, kudi ake samu pastors baki ga sunfi liman kudi ba,gwara nayi can na Zama sister ta church,Kinyi asara Tahantsi na furta,tace kudi na jefar da Zaki ce nayi asara ko Kuwa Maidawa ne ya mutu,Yaya Jawad ta saka turare da zata fito,yace Kyaleta Tahantsi zanyi maganinta gani take har yau budurwa ce,Kadada tace ki daina yaudarar kanki Fara da aurenki kibi musuluncinku sai ki dinga Iskanci iri iri

Sharesu nayi muna tafiya kowa Shuru su Tahantsi ne kawai suke surutunsu da Kadada jefi jefi Ina sa baki,Tahantsi tace na taho da babbar tsaraba tana jaka sai naje Zan kaiwa ko wanne a gidanmu,Muna wucewa ta layin wata Kasuwa Jawad yaga Hijabai a rataye yace tsaya a Nan aka tsaya,nasan me zaiyi Hijab ya siyo kato me Hannu ya dawo ya miko min,ta mudubi na kalleshi zanyi kuka,Kadada ta bigi kafadar Tahantsi tace Kinga soyayya,Ina gani Wai zata Yi kuka kema ki koya,Kadada tace na haddace na dauki darasi, Fara an Fadi ba nauyi,hijab din na karba na saka,sannan na cire mayafin na maida jaka, handkerchief ya Miko min Yana Murmushi na karba na goge jambaki.

Kaina na kifa a jikin kujera Ina ta goge hawaye su Kadada su kadai Suka San kuka nake suna ta tuntsira Dariya suna leka min fuska,Jawad yace ka Kara gudu lokacin Sallah ya kusa ai suna da masallaci a kauyen,Kadada tace kato ma kuwa Yana nan,har Muka Zo kwanar da zamu shiga Kauye mota bata Shiga sai dai ka bada ajiyar motarka a wajen masu machine ka hau machine,Kuma ba Napep,Muka fito gaba daya Jawad Yana mamakin daji irin wannan ace da mutane a ciki ko da yake Yana gani a kudu ma,masu machine biyar Suka taso, sai naga Daddy yazo shima an wuce da shi a machine, Hannu na daga Masa nace Daddyyy....ya dago min hannu,motoci Uku Muka gani masu tsada sunyi parking a wurin tamu ta hudu,ana zuwa Kadada data hantsi sune gaba sunyi nisa,Farooq ya hau nasa,Zan hau nawa jawad yace shi zai hau na hau bayansa,haka ya fara hawa na hau bayansa yace ki rikeni karki fado nace to ban rike ba ai akwai kunya,ana tafiya yace karfa ki Fado,nace a'a

Muna zuwa ana ta hudubar Sallar Juma'a Suka Yi Alwala zasu tafi liman har ya Kai karshen khuduba ya fara adduarsa yanda ya Saba wance da bata da lafiya Allah ya Kara Mata lafiya,wance.... Tahantsi tace wannan Liman din Anya na kirki ne kullum sai dai yayi ta zancen Mata,yaci gaba yaranmu da suke gida basu samu mijjn aure ba Allah ka kawo musu miji......Yarinyar Nan Kadada Allah ya shiryeta ta karbi musuluncin,Kadada ta sheke da dariya tace liman ya takura min shi yasa sai saka Hijab nake ya jaja min an karbi adduarsa,su Jawad suna ji suna ta dariya Suma,Farooq yace Ni na taba Jin liman haka kowa sai ka Fadi matsalarsa a gari,Jawad gefe ya Jani yace Wai Kinga Daddy ko? Nace ae yace yau Kadada za a musuluntar a daura Mata aure, na rigada tuni na sanar da iyayen Farooq komai Kuma sunji Dadi yanzu ma Babansa da dangi suna cikin masallacin,Kuma Farooq da Kadada basu sani ba fa,yace yanzu zanji ta bakin Kadada Farooq Kuwa mun gama da Iyayensa ba sai ya sani ba,Kadada ya Kira gefe yace yau gamu ranar Juma'a a garinku,kin shirya karbar musulunci yau a daura aure? Kadada tace ae amma shi ya yarda Farooq din? Ae yace,ki fadawa iyayenki,Kadada tace tab ai baza su yarda ba,Kawai bari na shiga mu gaisa daga masallaci sai cikin Kano idan ba Haka ba yau a gidan nan bazan kwana lafiya ba zasu iya kasheni, Farooq yace mun tafi Sallah ki gama kizo tace to,kallona tayi tace Fara ku shirya muje mu fito,Muka fadawa Tahantsi tace to ku muje Yara Suka dauki kayan da Kadada ta siyo tsaraba,Suna ta murna,Ina shiga Suka yayyameni Fara haka Kika koma balarabiya,a jirgin kuka sauka? Nace ae kawai,Gwamma harda shewa tana daga Hannu ta rike hanci Muka kalli Hammata Dariya ta kamamu muka kalli juna,Tahantsi ta fito da shaver da uban yawa ta dinga bawa kowa package Daya wajen Sha biyar kenan,Suka dinga tambaya mene ne,a dinga aske gashin hammata shi yasa duk na siyo muku duk da nasan kowa package Daya a rana zata kare sabo da ciyawa,Tashuka Kuwa karyewa ma zasu dinga Yi cewar Kadada,tace bari naje na kalli iyayena kafin suji na musu Tawaye,Gwamma ce ta fatalo shaver tace Naga Kamar Reza me mirki sai ta fashe da kuka amma yaran Nan bakwa kaunata so kuke na yanke jikina,Tahantsi ta dauka tace to Gwamma kyale abarki har ki bari maaskin dare ya gaji da gani shi yazo ai yayi Miki kwal kwal

Muna ji an idar da Sallah Muka fito Muka ji ance jama'a a tsaya akwai baiwar Allah da zata Musulunta bamagujiya Kuma za a daura Mata aure yanzu, Gwamma tace jama'a ku tsaya kuji wata jininmu zata shiga musulunci,kowa maza da Mata Yara da manya Suka kasa kunne suna Jin wace,Gwamma tace wannan kwai bankadaddiya ko wace,Kakannina Kuwa dadi Suka ji su dake musulmai ne,Muna zuwa Kadada ta shiga Masallaci aka bata Hanya ana kabbara Allahu Akbar, Tahantsi tace an rakata tabi bayan Kadada, suka shiga tare Liman ya Kalli Kadada yace Addua ta fada,sai ya bada sanarwa tace musulunci shine sadakin Aurenta,Farooq yayi zaune mamaki ya kamashi wato Jawad ne ya hada wannan tuggun zai Masa auren dole,tunda yaga Babansa da danginsa ya sare, bayan anyi khudubar aure da sharudansa nan take aka radawa Kadada kalmar shahada ta maimaita akace aure ya dauru,wanne suna kike so,Kadada ta karbi speaker tace Fatima Binta kowa zai iya kirana da Binta Sugar mangoro me Zaki,aka fara dariya

Aure ya dauru tsakanin Fatima Binta da Angonta Farooq Ibrahim Dangana, amma ango ya bawa amaryarsa kyautar kudi dubu dari biyar,Aminin ango ya bawa Amarya dubu dari biyar,Baban Farooq yace ya biya Mata aikin Hajji wata shekarar,ana ta kabbara kafin kace me Kadada ansha kyauta harda masu ishirin da Hamsim, Tahantsi tace a bata speaker aka Mika mata tace kowa ya sheda Kadada Ta koma Fatima Binta Sugar ta Musulunta Kuma an daura Mata aure,Nima Kadada ta Musulunta me ya rage nima mene amfanina Zan Musulunta a fada min me zance,masallaci aka kaure da kabbara yayin da can gida su Gwamma da duk Yan gida Suka haukace Kadada ce,Gwamma harda dirza kanta a kasa sabo da bakin ciki ta dinga goga goshinta a kasa sai da yayi jini sabo da bakin ciki,tace ayi maza a tarewa su Kadada Hanya,sai Jin sanarwa Suka sake Yi Tahantsi ta Musulunta ta koma Nana Khadija,liman harda cewa Tahantsi ta zabi suna me daraja sunan uwar gidan manzon Allah (s.a.w) Nana Khadija uwar gida ran gida shahidiya Allahu akbar, Tahantsi yanda aka yiwa Kadada kyauta itama Haka aka Mata har kujerar Makkah, liman yace zaku iya tafiya sai a samu masu koya musu addini yanda zasu fahimci Allah,Jawad a ransa yace uhmm kaji liman yasan kalmata, Farooq shi iyayin liman dinne yake bashi dariya, Tahantsi a gaban mutane tace to su Binta sugar anyi aure sai a daukin Dangana,Kadada tace bana son wulakanci sunan Surukina ne fa a gabanmu ai cin Fuska ne,aka kwashe da dariya sai lokacin mutane Suka tuno sunan baban Farooq Ibrahim Dangana,liman yace Alhmdllillahi yarinya tayi hankali tayi kunya, Fitowa sukayi Suka sameni nesa da masallacin na tari Jawad nace ga masu machine muje wlh naga Yan gidan nan sun Fara zagaye haushi zai sa su Mana duka, nace ga baban Kadada can da Adda, Farooq tuni ya dane machine sabo da tsoro,ta hantsi da Kadada Suka hau daya ni da Jawad Muka hau daya,Baban Kadada ya biyo ta da gudu tace me Machine tsaya ka Wana min machine din Nan ka bashi wuta,Ta hantsi tace juya kofar gidanmu Baban Kadada ya bisu da gudu,Me machine yace karfa ya muku Illa,ba abinda zaiyi Suka ce, Suka sauka a machine Kadada tace Zan biyaka saki salansa yanda zai cika garin nan da kara ka wuce ta kofar gidan damu sau Uku,Haka me machine ya sauka Suma Suka sauka ya balle salansa duk Yan gidan sun fito ba Wanda ya iya Kai Sara suna kallo aje a juyo da su Tahantsi har sau Uku da uban gudu,Gwamma ta fito da lemuka ta watso musu ku tafi bama sha ba mu ba ku,Kayi hakuri Baba Allah ne ya shiryeni,ka Taushi Babata Tashuka,Baban Kadada ya kutuntumo mata ashar, Me machine yaja Suka tafi,gidan Maguzawa Kuwa Gwamma sai rasgar kuka take jikokinta sun Musulunta sunyi abin kunya.

Suna karasowa Muka ji salansa a sake,Farooq yace yaran Nan basa ji,suna zuwa Muka wuce sai cikin kano,Muna hanya duk na gaji kaina ya fara ciwo na kwanta a jikin Kadada,Jawad ya juyo ya kalle da kullawa yace Mene ?nace kaina ne sai na Fara kuka,Haushi ya Kama Kadada tace dalla dagani raguwar banza daga ciwon Kai sai kuka,Farooq dai bai ce komai ba,Jawad yace ka sauri mu shiga gari a siya Mata magani,Farooq ya ware wuta amma Jawad yace Kai baka iya driving ba Yana ta masifa

Please Login or Register in order to submit comment