Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mijinta yanzu abin ya bar Mata sai maza to dab kut...Dan kaza kazan...idan ku Yan kaza kaza ne.....Gwamma ta lailayo ashar harda daga kafa sama duk a cikin zagi ne su sun San Kalar zagin,Wai anyo maka harda na karkashin buje,Gwamma tace gwara na rataye kaina kowa ya huta,idan an Isa a kafa min fanka a dakina Ni Kuma a daren Zan rataye kaina,Tashuka tace yo sai da Fanka idan da gaske ne ga bishiya ga daji ga wuri kala kala sai ki tafi a boye Kinga kin huta duk kinbi kin hanamu sukuni sabo da muna auren yayanki,Gwamma tace duk sai an sake ku Kun Haifa min mugun iri zaku gani sai na dakko tsohuwar ajiya na hada tsafi gwara kowa ya kiyayeni ko na taso dodo

Tahantsi ta maye gurbin Kadada a unguwar su Ummiya babu Wanda Bai santa ba sabo da abin dariya
Ummiya ce ta aiketa ta Kai markade ta tafi da Dan nisa sanye take da Atamfa orange Riga da skert da mayafi tana tafiya taji ana ta Mata horn ta daure taki juyawa har motar tazo ta Sha gabanta lokaci guda aka sauke glass taga wani Dan matashi kyakyawa wankan tarwada Dan gayu,tace lafiya? Yace Wai baki ganeni ba? tace na sanka Zan tambaya ne, okay Ina Wanda ke zaune kusa da wani matashi me daukan hoto Wanda kuke ta Masa tsiya har ya gaji ya maida wayarsa aljihu to ai Ni Ina gefensa,oh me karatun Qur'ani har nace ma ustaz ayi damu,yace yes ashe kin gane Ina ne gidanku? Tahantsi ta nuna Masa yace dan Allah bani number dinki tun ranar Kika birgeni naji Ina sonki, Tahantsi tace to bawan Allah daga ganin sarkin fawa sai miya tayi Zaki? Please ki bani baki San me Allah ya tsara ba,Kadada tace to gashi Zan baka Amma karka dameni da Kira Ni ba yarinya bace da Zan zauna Ina shiririta Tahantsi uwar son girma daga an girmi su Kadada da shekara biyu kacal,ya karba haka yayi godiya ya wuce Yana tafiya ta dura Masa ashariya tace me zanyi da shi Ni sai yanzu ma na gano Kansa irin na Baban Kadada ne Kamar faranti Zan fadawa Kadada tayi sabon Baba a kano tayi Dariya tace tab ta juya ta tafi.












AsmaBaffa
10/6/22, 22:13 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
81-85

NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA.



Page naku ne

Leemat
Maryam Bello









Kadada Fitsari an kasa sai da Farooq ya riketa ta kankameshi sannan ta samu tayi fitsari da kyar tana kuka,Hakuri yake bata a Haka ya Mata wanka ya Mata gashi da ruwan zafi kin yarda tayi sai kadan sannan ya koya Mata wankan tsarki sosai tayi,shima wanka yayi tare da tsarkake jikinsa sannan ya daukota daure da towel ya dawo da ita,ta tsaya da kafafunsa Amma Kadada ta kasa sai a kujerar mirror ya ajiye ya cire bedsheet din da ya lalace yaje ya zuba a washing machine ya wanke ya shanya ya dawo wajenta,jikinta ya goge Mata sosai da gashinta ya shirya abarsa tsaf shima ya shafa Mai ya canja kaya wata shada me karamin dinki yayi kyau sai annuri yake,Dubai gown ya sa Mata wata pink and blue me kyau tayiwa Binta sugar kyau sosai,Gashinta ya gyara Mata ta Kama abinta da ribbon Kalar kayan,ta shafa powder da lipgloss tana ta faman Fushi, Farooq yace my Mazarkwaila tace naam my attaruhu me yajin bala'i,Dariya yayi yace Ashe bakin Bai mutu ba,to Kai ka tsaga min da Zan daina magana Ni ka kwantar dani na gaji Promise land dina zai fara zagwanyewa,Farooq ya Kama Dariya yace lallai Kuwa promise Land,Kadada tace ae dazu wanne Alkawari ne baka min ba kana ciki ai kaga ya Zama promised Land,Alkawari yanzu Kika Fara ji indai Ina ciki Kuma fa ba a cikawa,Allah ya shiryeka mugu abokin criminal Dan Allah ka tafi ni ka Nemo min abinci kace ka bani kanka Kuma gashi Nan a jikinka wallahi baka kyautawa,Farooq ya fita Yana dariya zaije gida daga Nan ya musu take away na lunch.

Tahantsi ce ta Kira lokacin Kadada tana Kan gado tana kuka zafi ya isheta,Wayar ta daga Tahantsi tace na shigesu Mene ne ko wata mutuwar akayi? Kadada tace da Zan fada Miki amma ance tunda mun shiga musulunci baza mu fada ba, Tahantsi tace wayyo Ina ma Sai yanzu Zaki Shiga Bayan kin fada min fada min ke,Kadada tace ai ya Zama dole bazan iya shanye wannan bacin ran ba Tahantsi ta duro Mata ashar Yar burar......kinsha Anaconda Kawai,kice Farooq ya tura Miki Anacondarsa,Kadada ta Kama Dariya tace ke Tahantsi Anaconda Kuma ai ta min girma wannan ai sai Jawad Anaconda sai Fara tana can munafuka Wai harda buyar min a bayan kofa na hankado shegiya ya tafi da ita, Tahantsi tana dariya tace ta gaji Allah sarki Fara me Anaconda Allah ya tsare, Tahantsi tace ke Kuwa taki nasan har rawar Shoki take a ciki ko? Kadada tace uban Shoki tayi Fara ce dai take Mata Disko a ciki, wayyo Disko Stick sai Najla cewar Tahantsi,Kadada tace Nasha azaba Tahantsi wlh gwara ya mare sau Hamsim ya hada min da kutufo,Tahantsi ta kyalkyale da dariya tace rufe bakinki ki boye sirrinki ba kyau baza mu sake zancen ba daga yau Bari na Kira Fara nace Ina hanyar Lagos muji suna ta dariya.

Ni Kuwa da asubar ya sake zaunar dani a ruwan zafi ya rikeni Ina so na tashi ba dama gishiri ya zuba a ruwan sosai nasha wahala,ya min wanka na tsarkake jikina sai naji Dadi kuma,nayi brush tare da Alwala,shima yayi wanka tas ya tsarkake jikinsa ya daura Alwala sannan ya sa rigar wanka ya nadoni a towel Muka fito, dake ya canja bedsheet wannan bai bari ya baci ba ya ajiyeni a hankali Yana cewa Sannu my White Angel Wai jiya Bollywood tv na kamo ne ko MBC? Dariya nayi nace oho maka Kai ka sani,kiss ya manna min a gisho yace gaskiya tukunyar zumarki a cike take,me? na tambaya yace Honey pot,dukansa nayi da Wasa nace ka kyaleni,Dariya yake Yana kallona Yana tsokanata ihun da nake azo a taimakeni,yace na tabbata wani yaji a gidan Nan jiya white Angel baki kyauta ba,Yara shike Nan sun San me nayi gashi yau Sunday,nace sauri ka shiryani mu koma Palo Kar su Fara zuwa gaisheka naji kunya,yace haba jiya duk na musu warning Kar Wanda yazo gaisheni da safe sai da Yamma,a gurguje ya fara murza min lotion hakan ma Sai da ya tsaya ya latse min boobs sannan ya gama ya zabo doguwar riga Arabian gown me shegen kyau ya sa min,ya zauna ya gyara min gashina Sosai ya Kama min sannan ya dakko powder ya zauna a gabana ya shafa min harda jambaki,ya kalli idona yace kinsha kuka ya dakko tozali ya zizara min kadan nayi kyau kuwa, sannan ya shafa min turaruka ya shirya shima cikin farar jallabiya Kamar wasu larabawa haka Muka koma,Sallah yaja mu Muka Yi sannan ya gyara dakin da Kansa dama ya gyara toilet tunda yayi wanka,daukana yayi Muka fito palonsa ya zaunar dani,yace basai munyi kallo ba jiya ai na kamo channel din,harararsa nayi da Wasa yayi Murmushi ya kunna kallo sannan ya fito daga part din.

Sai ga Hafeez yayi knocking nace shigo ya shigo da sallama na amsa Abeed Yana hannunsa yace Aunty Ina kwana Yana kallona har na tsargu nace lfy ya ka tashi yace Alhmdllh Ina Yayan? Nace baku hadu ba yanzu ya fita, a'a to sai idan wani part din ya shiga bari yazo,sai kallona yake nace Hafeez lafiya Naga kana kallona? Yace no gani nayi kamar kinyi kuka ne Aunty ko da Yayana kuka Yi fada? Murmushi nayi nace wanne irin fada ana zaune lafiya,su Meenat ne Suka Fado da gudu Aunty...Aunty Good morning suka Fado saman cinyata,Ayana ta zauna a cinyata idona na runtse Nan danan idona ya cika da hawaye sabo da azaba, Hafeez ya gani sai ya dauke kai yayi kamar bai gani Ina kuka ba na goge idona a wayance,Shine yace dalla Malamai ku tasar Mata a jiki baku da aiki sai ku fada jikin mutum,tashi sukayi Suka koma gefena suna gaisar dani Ina amsawa,nace Hafeez kawo Abeed,ya Mika min shi, Meenat sai da ware min mayafina ya Fadi kasa sabo da rashin jinta,Jawad ne ya shigo da basket na abinci a hannunsa,ya gansu yace ba nace Kar Wanda ya shigo min part ba sai Yamma,ke Asmau ba a gabanki na fada ba sabo da ku kunnen Kashi ne daku shine kuka Zo ko

Kai Yaya mune da kunnen Kashi cewar Meenat tana taba gashina sai lokacin yaga Hafeez ga gashina a Bude ai Kuwa sai masifa ku fita in mun fito ayi surutun Suka ki tashi cikin tsawa yace get out ...Suka Mike suka fita Banda Hafeez Jawad yace Kai da ka zauna dakinka ne tashi ka fita Malam ko kunya baka ji kaje ka kaiwa Asif passport dinka tunda Dan Iska ne Kai next week zaka tafi school,Hafeez yace Allah ya kaimu ya fita Yana murna zai bar kasar.

Abeed aka manta a hannuna na kwantar dashi a kirjina tunda cinyata ba dama,Jawad sai yanzu ya kula yace Dan Allah sauke yaro duk kin raba min nono Ni da shi Ina ga Wanda yaron Nan yake samu ni bakya barina na huta Haka ajiyeshi na maida shi,sai zare Ido yake, Dariya nayi ya dakko mayafin yace Meenat ce ta cire ko nace ae yace Hafeez ya ganar min wannan anyi Dan iskan yaro wlh Yana Gama karatu shi da Ahmad Zan musu aure su koma gidansu da matansu su ma,Ina kallo ya maida Abeed sannan ya dawo ya hada Mana tea ga farfesu da chips da sauran abubuwa harda kunun gyada

A baki ya dinga bani Yana ci shima har Muka gama ya maidawa masu aiki ya dawo ya kwantar dani a kujerar Wai na huta ya dire gwiwoyinsa a kasa ya fara min tausa Ina Jin dadin tausar Kuwa, sai ga Kiran Tahantsi na daga,tace Fara gobe da zanzo Lagos,da sauri na zabura nace Dan Allah ki sassako min sabara da ararrabi a Kauye ki daga ki kawo min a wajen rauni na Zan barbada, Tahantsi Dariya harda rike ciki tace Fara duk Anaconda ce tayi barna haka? Dariya ta bani nace ni dai ki rabu dani,dama ba zuwa zanyi ba karya nake Idan kinji sauki kije ki kaiwa Kadada agaji Farooq ya mata barjen dambu yau tas,Jawad Yana ji kunya ta kamani na kashe wayar ba shiri,yace da kin gama wayarki ai Babyna nasan baza ki Fadi sirrinmu ba
Tausa yake min harda Waka reciever gidan Dadi,na matsu ki fara Jin dadi kiji yanda Area take aiki,Ido na rufe Ina dariya a raina.

Farooq Kuwa Yana dawowa ya iske Kadada ta dage Riga pant din a kasa tana ta fitata Reciever da mufici ga ac ta ware ta,Dariya ta Kama Farooq,yace a'a babu lafiya kece nace ki tsaya in Miki ruwan zafi sosai,Kadada zafi ya isheta ta fashe da kuka tace kayi min yanzu wayyo tana fifita,ya dauketa Bayan ya ajiye take away na lunch ya Shiga toilet ya hada ruwa me zafi da gishiri ya gasata sosai Tasha zafi Amma ta samu sauki sosai sai da ya canja ruwa sau Uku sannan ya barta Haka ya wanke ta ya dakko ta tace barni haka idan na sake ji ya dawo zafin sai Kawai ka Kuma Yi min barni da towel Dina bana son kwalliyar, yace to ya bata abinci taci, tace Kai Dan Fari iyayensa sun Sha wahala kafin a samu ciki kwanciya tayi bacci ya dauketa,Farooq ya zauna Yana kallonta yana Jin wani sonta marar misaltuwa a ransa har ya kwanta shima Suka dinga bacci,ranar sun Sha jinya shi da Jawad.

Washe gari Tahantsi saurayin data hadu da shi yace zaizo da kyar ta yarda ita Sam bai Mata ba,haka dai tayi wanka ta shirya cikin doguwar rigar atamfa blue dinkin me aljihu tayi kyau sosai,tana fesa turare ya kirata a waya yace Ina kofar gidan,Ummiya ta fadawa sannan Ummiya tace ki kawo shi palon can karki tsaya da mutum a kwararo,Tace to ta fita,tana fita mamaki ya kamata ganin wata motar daban mutum daban ya fito, Tahantsi ta kalleshi tace laaa Dan karya me daukan hoto a jirgi Ina kasan wancan guy din,harararta yayi yace ki daina ce min Dan karya, Tahantsi tace yo kayi abarka kazo kana Jin kunya daga baya kenan, Kawai kace ka tuba yanzu ka daina,Murmushi yayi kadan yace Wanda yazo jiya yarona ne dama sawa nayi ya Nemo min gidanku,nace me ya faru? Daureki zanyi Kara Zan kaiku Kuna ce min Dan karya, Tahantsi tace ashe za ayi yaki Kuwa,shugo to tace ya fito Yana taku dai dai dama Allah ya zuba Masa Iyayi da fankama,yasha wata Gezna sky, Tahantsi ta juyo tace ka dinga taku da jikinka kana tafiya Kamar kabi Hanya kwibin bazawara,Matashin yace Mene kwibin bazawara? tace hanya irin ta Kauye wacce ko machine baya iya bi sai Keke sai a kafa keken ma da kyar to irin wannan hanyar hausawa suke cewa kwibin Bazawara,Murmushi yayi yace ai ku ba a ka daku akan magana.

Cikin palon ta Masa iso ba komai a ciki sai katon carpet sabo me kyau,fita tayi ta kawo Masa ruwa da lemo sannan ta zauna a gefe tace Ina yini,yace lfy ya Mama ya gidan naku? tace lafiya lau,me yasa kasa aka Nemo gidanmu ko Nima so kake ka rinjayeni da irin Harkar taku ta social media Ni dai bani da kudin saka Kaya me tsada ban San Kuma inda Zan samo haya ba,haka in samo Hayar gida me kyau da iPhone ta Yan karya sabo da na fito tar a Kara min filter bada ni ba,ku dai da zakuyi Allah ya bada sa'a kuje kuyi ta Aron mota bakwa Jin tsoron Allah,ku samu gida me kyau a ara muku ga shiga jirgi duk sabo da ku Tara fans,kune tiktok kune Instagram, Twitter,Ina laifin ma ka tsaya a Facebook dinmu na gargajiya,Dariya yakeyi sosai yace dan Allah saurareni tace to,yace Taya Kika Zama musulma? tace ni da Yar uwata Kadada ta koma Fatima Binta sugar Ni Kuma Nana Khadija,yace Nice name amma nayi murna sosai ku Maguzawa ne? Tace ae yace mu Fulanin Taraba ne Iyayena a Nan Kano suke da Zama ni a Lagos nake Zama in kin ganni a Kano to na kawowa Mum and Dad ziyara ne.
Ko sunana baki tambaya ba, Tahantsi tace Taya irinku kuke da suna Daya Ni Kam ka rike abinka,yace ke dai kin bawa zuciyarki Dan karyar social media ne ko? tace ae yace wallahi ni in ba sako aka tura min ba bana budawa bani da time, Sunana Aliyu Haidar gidanmu mu uku ne kawai dukkanmu maza akwai yayana Usman Yana da aure da matarsa da yarsa daya, sai Ni sai Autanmu Islam shine Wanda ya dauke Ni a airport.

Nace Masha Allah yace Babanmu Babban likita ne Maman mu Lecturer ce, nayi primary da secondary Dina duka a Taraba sannan nayi firt degree na a Georgia,nayi second degree na a turkey akan Business Kuma gashi Alhmdllh Business nake sosai Ina da shaguna a Kano kanina ke kula da su Ina da wasu a Lagos da yarana sannan da office Dina da komai,yanzu Haka na gama Gina gidana a Lagos a can zan zauna da matana Banda ra'ayin Zama a arewa sai da yawo Inshaallah.

Tun farko na ganki kin min na zaci style din gashinki ne ya birgeni sabo da ya Miki kyau, Tahantsi tace dan Allah yanzu dama ya min kyau? Yace sosai ma,Bayan na dawo gida nayi ta Dana sani akan ban karbi contact naki ba,abin ya dameni sosai fa,hmm in fada Miki na gaji dai na fadawa Mama gashi gashi tana ta dariya Dana bata labarinki tace hmm Allah yasa ta aureka sai ka musuluntar da ita,baki ga yanda mum Dina ke sonki ba sabo da tana so inyi aure dama kinsan Lagos Mata Yan Iska sunyi yawa to tsoro take ji Kar yaronta ya lalace sai gashi nayi gamo a jirgi, shi yasa na dage nasa yarona ya dinga nemanki inda Naga taxi dinku ta nufa a nan nace yabi sai gashi katsam ya Gano min ke I was so happy daya fada min kece,nace ka tabbatar yace min ae shine fa nazo, Nana Khadija idan ba damuwa Ina sonki Ina kaunarki wlh tsakani da Allah Kuma aurenki zanyi in kin Amince,sannan Zan baku adrees din gidanmu kuyi duk wani bincike a kaina Daya dace, Tahantsi tace Haba yanzu naga saurayi amma da ka turo min wani da Kai Kamar an kifa faranti

Dariya yayi yace yaron Nawa tace Allah Kansa Kamar na Baban Kadada,yace tana Ina Kuwa? Nace ai jiya aka kaita Lagos gidan mijinta,tana auren wani Farooq abokin Jawad,yace wanne Farooq nasan dai wani Farooq Ibrahim Dangana tace shine wlh,yace Jawad din ma na sanshi wani me Kama da balarabe Mamansa balarabiya ce asali Yana da mahaukatan kudi,Babansa bai dade da mutuwa ba,tace kwarai to Yar uwarmu yake aure Fara,ga mamanta a Nan gidan itace take rikeni yanzu,Allah sarki ka Shiga ka Mata gaisuwa mijinta satinsa biyu da mutuwa yace Allah ya Masa rahma tace Ameen.

Yanzu kin yarda kina so na? Tahantsi tace to gashi nan dai ka bari muci gaba da muamularmu zuwa wani lokaci ai zaka Gane na fada ma idon son ya kamani ko ya kace? Dariya yayi yace shi yasa nake sonki akwai bada nishadi,tace sai nan gaba ma tana tsiyaya Masa lemo Yana ta kallonta,Tahantsi tace Allah yasa ba Anaconda bace da Kai,yace mota? tace a'a wa yake ta mota share zancen Watarana na fada ma yace to.

Har ciki yaje ya gaida Ummiya ya Mata Ta'aziyya kadada tace surukar Jawad kenan wannan,Ummiya ta harareta suka fita,ya Dan Dade kafin ya Mata sallama ya Bata dubu talatin wai ayiwa Daddy sadaka, Tahantsi tayi godiya ta rakashi ya tafi ta dawo gida ta nunawa Ummiya tace to ai anyi Masa sadaka ana Kan Yi ma Sai ta arba'in kawo dubu goma ki rike sauran,tace Ummiya ai ta min yawa ga dubu ashirin sai na dauki goma ya Isa,Ummiya tace an gode kina sonsa kenan? Tahantsi tace Haba Ummiya Baki ga kalarsa ba ne wa zai ce baya son Aliyu Haidar, yaro son kowa kin Wanda ya rasa,yaro Dan fillo kyakyawa ga kudi ga gayu ga hankali ga addini,Kawai ayi bincike, Ummiya tace to yanzu Kinga ba Daddy bamu da Namiji shakiki a garin nan, danginmu kuma arna ne baza su kallemu ba,Babana a Kauye yake kawai Zan Fadawa Baban Najla sai ya wuce Miki gaba Kawai ni Kinga Takaba nake,Kuma baza ayi gaggawa ba mubi komai a nutse, Tahantsi tace to Ummiya,Babar Ummiya tana gidan itama taji Dadi da ita ake hirar.

Abba Kuwa biki ana ta shirye shirye shi da Safna komai na gidan sai da ya canja,ga Jawad ya Kara Masa jari abin sai Wanda ya gani soyayya suke sosai da Safna bangare Daya Kuma Umma tana makale a zuciyar Abba,Bangaren Umma Kuwa cikin kawayenta wata Hajiya Lami itace ta shirya har Kauye ta samu Umma tana ta tuka tuwo wajen magriba,duk Umma ta rame,tana Shiga tace Hajiya Barira ashe kece ma a gindin murhun,Umma hayaki ya rufe Mata Ido tace Hajiya Lami shugo kece a garin,tace dare zai min sauri nake mijina bai san na taho ba,Umma ta Sha majina ta goge fuskarta da rigarta sannan ta rufe tuwon dawar da ta gama tukawa,ta dakko tabarma Suka zauna,tace Ina Yan gidan fa? Sun Shiga makwafta gaisuwa,tace to bari kiji abinda ya kawoni mijinki Alhaji Nasir aure zaiyi ya kusa aure wallahi bikinsa Saura sati biyu Kuma da Yar kawarki Hajara yarta Safna dai da Kika sani to ita zai aura in Zaki San me kike ki sani tana Gama fada ta mike tace na tafi ki dai Yi aure ki fito ki koma gidanki ta tafi ta bar kauyen Dan Kar ma a ganta.

Umma ihu ta saki ta rufe bakinta ta cire tare da sake Dora hannunta a Kai ta sake kurma ihu ta toshe bakinta,tace wayyo Allah na shiga Uku yanzu haka Nasir zai min,Namiji ba amana yanzu Ni zaiwa Haka sai kuka Umma Kamar karamar yarinya kuka take tana tsinewa kawarta Hajara tace Zan dawo wlh yarki sai ta bar min gida sai nasa an saketa sannan na lakada Mata shegen duka a Haka Yan gidan Suka iske Umma tana ta kuka tana sambatu ba Wanda ya kulata tana ta kuka ta kalli mamanta tace na rantse da Allah Inna idan Baku kwato min yanci na ba wajen Alhaji Nasir ba sai na gudu na bar garin nan, suka Bude Baki suna kallonta,Babanta yace wanne yanci ya rage Miki a wajen mijin da Baki da igiyarsa shashasha,Umma ta sake Kurma ihu tana na Shiga Uku na jawa kaina budurwa zai aure Yar gidan kawata wayyo gwara ma na mutu na huta...






Kuna Sanya da sharhi fans Zan daina typing bana Jin Dadi.






AsmaBaffa
10/6/22, 22:13 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
86-90

NA KUDI NE
MALLAKIN JIKAR MAGUZAWA PAID GROUP



Official

By
AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA ZAINAB GARBA BUTALAWA




Page naku ne

@Jiddah
Auntyn Khairat








Umma ba Wanda ya kulata har ta gaji da kukanta ta tashi ta zubo tuwonta ta ci ta koshi sannan taje tayi Sallah tana idarwa ta kwanta a wajen tana tunanin 'ya'yanta Kar a azabtar mata dasu,kirji ta dafe tuna yanda ta dinga zaluntar su Meenat tace nasan ma dole ayiwa yarana tunda yanzu Mata da yawa basa rike Dan wani bare Safna da ta sansu sarai tana kwance sai hawaye Allah kasa Kar ta azabtar min da yara,Allah ka Kare min yarana,taliyar data dinga dafawa su Nawwara ta tuna taliya da Mai da yaji da sassafe kullum yaranta su karya da shayi da bread ga kwai da dankali da farfesu, mikewa tayi tare da Zama dirshan tace to ko Najla Zan roka ta kwashe min yarana ta rike a wajenta kafin na koma,Kai wannan basu da mutunci ta hanyar da mutunci ya bi ma jinin maguzawan nan basu bi ta hanyar ba,Kar na jawo Nasha ashariya a banza,Umma rasa mafita tayi ta hakura tare da zubawa sarautar Allah Ido Kawai.

Yau haka na yini Jawad ba inda yaje Kawai jinyata yakeyi motsi idan nayi sai yace mene,yau Ina ganin gata ban taba sanin ya damu dani haka ba sai yau,Wanka da komai shine ke min abinci ma a baki yake bani Sai na koshi,Yanzu ma bayan nayi Sallar Isha sai gashi har ya dawo daga masallaci hannunsa dauke da Leda katuwa da kayan ciye ciye iri iri,Ido Muka hada Ina zaune a saman sallaya ya sakar min Murmushi kaina na sadda kasa sabo da wata kunyarsa nake ji idan na tuna abinda Suka faru tsakaninmu,yayi kyau sosai amma kunyar fada Masa nake sai nayi shuru sai dai nayi ta kallonsa, zai fita yace Ina zuwa bari naje wajen yaran nan Naga me suke Yi,to nace ya fita Yana zuwa ya iske su suna ta Wasa har su Asmau,Yace kunyi Sallah Kuwa? Suka ce ae munci abinci munyi karatu ma da Assignment Muna gama wasanmu sai muyi Shirin bacci,yace yayi kyau Aunty tace a gaida ku bata da lafiya,Meenat tayi tafi tare da hantsilawa saman gado tace Kaine ka hanata zuwa ka kwace ta ai gobe zata dawo ne wajenmu baza mu bari ta

Please Login or Register in order to submit comment