Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tace Sannu yi hakuri,Matashi ne kyakyawa dan chamai chamai Dan gayu,ransa a bace yace Allah ya Isa wallahi Allah ya tsine Miki albarka,Kadada ta kyalkyale da dariya tace karka Yi hakurin Nima na janye hakurin dana baka,Kato dakai kakai sa'an mijin Fara Amma kana min Allah ya Isa harda tsinuwa,tashi yayi Yana goge fararen kayansa yace bazan taba yafe Miki ba ya juya yayi tafiyarsa,Kadada tace can ta matse maka ta koma gida.

Jawad Yana fita wayarsa ta fara ringing yaga daga office dinsa ne Yana dagawa yace Salim nace bazan shigo ba Kayi abinda ya dace,Salim Wanda a karkashin Jawad yake aiki yace sir documents din jiya zaka fada min inda suke sabo da ya kamata yau na shigar dasu,Jawad ya zauna saman bed dinsa Yana magana kamar me rada ya furta ka duba saman table dina suna nan kawai ya datse kiran tare da kwanciya bai dade ba bacci ya sace shi,Sallar azahar ce ta tashe shi bayan yayi Sallah ya koma bacci har 4pm sannan ya tashi yana mugun Jin yunwa,Wanka ya sheka tare da shiryawa cikin kana Nan Kaya marasa nauyi sannan ya gabatar da sallah ya fito hayaniyar su meenat yaji a garden suna ta wasa,Palona ya shigo a nutse banji motsi ba sai kamshinsa ko Ina na gidan kamshinsa yake shi yasa banyi tunanin shine ya shigo ba,Abeed yana jikina sai nono yake nema Yana ja min riga nace Kai yaro kiyayi kanka wannan yafi karfinka sai me tafiya da kafafunsa Kai ko rarrafe baka Fara ba wannan na babban mutum ne me hakora 32,yawwa yaro Abeedi wannan sai Bayya Maganarsa naji daga sama Bayyan uban waye zai kula wannan tarkacen

Anyi ruwan sama kin bar Yara suna Wasa a garden Yana fadar haka yaja tsaki yayi waje,mamaki ya kashe ni sai kace ni na haifesu na Shiga Uku ni daga wannan sai wancan ban Saba ba,Abeed na bawa Bintu na saka Hijab na tafi garden na tattaro su Ayana Muka dawo ciki nace wanka za ayi sai azo ayi karatu,Humaira Nanny ta kawo min daga Ni sai Yan yaran su Asmau suna bedroom,Hafeez Kuwa sun fita duk yaran ne masara wayo da su Ameera,Meenat ta fisu kiriniya ita na sura nace bari a fara miki na tafi da ita bedroom,Kaya na cire mata,na daura towel nima sabo da Kar na jika kayan jikina shi yasa na cire su na daura towel,Muka Shiga na Fara Mata wanka su Kuma can Ameera da shukrah suna fada akan remote,Garin fada suka bige Kuma gaba daya suka kwalla ihun kuka,Jawad Kansa yaji da sauri yazo palon garin Zan fito ruwa a toilet yasa na subale na fadi towel ya fadi nono a waje Allah yasa daga sama ya zame kasan a rufe yake, Meenat sai dariya da tsalle kyalkyal yaro ba hankali babu tunanin ko naji rauni ita faduwar Dariya ta bata kafin na tashi ta fito da gudu jikinta duk kumfa tana kwalawa Yaya Jawad Kira,a Palo ta ganshi yana raba fada tace kuzo Aunty ta Fadi ta sake shekewa da dariya harda rawa wallahi Naga nononta Yaya Zo ka gani yafi na Aunty Nawwara,Kaga Yaya yanda ta aura towel sai ya ballo wul ta juya sama da gudu tana tafi da tsalle,Jawad Kamar shi aka gani ya zuba tagumi ga Yara wannan yayi kuka wannan ya Fadi wannan yayi ta'adi, gashi sai rike shi sukeyi suna hayewa jikinsa yace Kai bala'in duniya sai kace Yayan mage

Ina ciki na tashi Meenat tana shigowa na fara Mata bala'i nace wallahi idan Kika fada sai na zaneki da Kika fita wa Kika fadawa? Meenat tayi Miki Miki tace bance komi ba,Yaya Jawad Kawai na fadawa,babu ruwanki da naji ciwo shine kike min Dariya haka duniya tace? abinda Zaki min kenan na Fadi kiyi dariya ba tausayi,Meenat yarinya ba ganewa take ba dariyarta take boyewa ta rike Hannu na tana faman dariya Allah Aunty kece ai....ta sake kyalkyalewa da dariya nace fita na fasa Miki wankan sai dai ki zauna da kumfarki get out na koreta tayi waje da gudu,na leka na hango Jawad a Palo da yaran nace wata ta shigo layi ya ja, Kamar me screening,Ameera ta taho na Mata ta tafi bedroom,na sake lekowa nace wata ta shigo wasu Suka taho su biyu su ma,Meenat Kuwa da kuka ta koma wajen Jawad da kumfarta tace ni anki a karasa min wankan Kuma shopping za aje da su Yaya Hafeez, Jawad yace matsa ko na mareki babu me Miki wanka yau tunda baki da hankali ke da wanka sai kinyi hankali tunda Kika ce Kinga Aunty ba kaya,.

Meenat ta Kara volume na kuka tace ai ni bance ba Kaya na ganta ba Nononta na gani sai ta sake kyalkyalewa da dariya ta daina kukan tace Yaya kaga yanda ta Fadi tana gwada irin faduwar da nayi ta bawa Jawad dariya shima,yace to karki sake fadawa kowa ba kyau kinji tace to,yace jeki ki durkusa ki bata hakuri kice baza ki sake ba,ta koma da gudu tayi yanda Jawad yace sannan na Mata wankan itama,a haka dukkan su sai da na musu wanka Saura su Humaira da Abeed Yan Yara,hijab na saka na tafi karbo su Abeed Humaira tana cinyarsa na karasa gabansa ya kalleni yaso yayi dariya yace ai gwara ki jefar da towel a gaba na yanzu ke wacce rashin basira ce zata sa ki zauna da towel gaban Yara ki godewa Allah su Hafeez basa nan da yanzu sunji,baki na turo da shagwaba nace ni bani yarinya na tafi,na dauke Humaira na juya,Jawad harda cewa inda kwadayi da wulakanci,yarinya tayi auren kudi za aci bati dama kin Fara bawa Abeed nono Yana Sha tunda Kinga ba a dade da tsige shi ba nono bai isheshi ba sai na siyo Miki magani kina Sha ruwan nono zaizo tunda naji ance sun girma sai ki shayar da su sai na Kara Miki kudin.

Juyowa nayi idona ya kawo kwalla nace kaga ba ruwana da Kai babu ruwana da Kai ka daina kulani shikenan,Kuma wallahi sai dai na shayar da Kai yafi karfin Yara,Kuma Allah zai kaimu sai kazo tukun Allah yasa naga bakinka saina bara shi gida biyu ka jawa kanka,Jawad dama shi baya so tayi nishadi yafi so yayi ta bata haushi,waye zai kula wannan trash din naki,tarkace na Miki Kama da kalarki, Juyawa nayi na tafi kawai Ina saka tsiyar da Zan tsula masa

Su Hafeez ne Suka dawo abinda nace su siyo Suka siyo min,Bayan Nima nayi wanka Muka Yi Sallar la'asar,Yara ga cin abinci da tsuro tsuro in ka zuba suci kadan,anjima su Kuma dawowa haka nake fama,kwata kwata na hanasu kallon tashar cartoon sai dan lokaci kadan kadan sabo da ba birgewa bace Kuma ba wayewa bace a bar Yara basu da aiki sai kallon cartoon duty na mace ta koyawa Yara addini Susan waye Allah iya mu'amula sabo da su amfani alumma Nan gaba,ba Kawai yaro sabo da kudi ko wayewa basu da aiki sai wasanni da kallon film ko cartoon basu San waye Allah ba Basu San addini ba bare mu'amula me kyau,shi yasa nake hanasu kallo sai dai nayi ta koya musu karatun Qurani da hadisai ta sigar da yaro zai iya dauka,Susan waye Allah menene Islam Haka na Fara kokarin fahimtar dasu kafin ma su koma school.

Da dare ma yaran duk tuwo suke so manyan ne basa so Muna kitchen da su Nawwara mukayi aikin suna tayani Ina koya musu,Muka gama na yiwa su Hafeez faten doya da kifi sai Kuma kowa ya dawo shi faten yake so,yara sai hakuri haka na basu ban San ko gogan Yana cin tuwo ba ban ma kulashi da abincin ba.

Shima bai fita ba bare ya siyo yayi tunanin Zan kawo Masa tunda Ina kawowa sai yaga Shuru,shima bai Nema ba yasha Madara sa snacks, su Ayana su Uku Suka tafi can wajensa aka barni da su farida,Salma,Sultan da sauran Hafeez ma muna zaune Muna ta labari,Hafeez yace Aunty Wai Ina Yar uwar Nan taki sarkin ashariya ya sunanta ma? nace Kadad a sunanta,nace Nima na iya Kawai akwai dalilin da bana dura muku ita,a Raina kudina na tuna yace idan nayi ashar a Gaban Yara minus dubu dari,nace dubu dari ba nan take ba ni nayi ashariya Allah kiyaye,Hafeez yace Aunty Nima Yaya yace Ina gama degree zai min aure nace Kai ka kiyayi kanka kana yaronka ka fada matsala,yanzu ga misali ka gani a kaina tunda aka min aure yau kwana na daya tal amma ban huta ba tun safe nake kula da Yara gashi da dare ban huta ba,duk abinda akace ibadane ba dadi tawa kaddarar ta raino ce shi yasa Babana yace sai hakuri,Waleed yace amma ai akwai soyayya,nace Kai Waleedi kyale Harkar Nan Kawai Allah ya bamu lada,da Sanda Ina budurwa shanawa nake a gari duk sati sai muje kasuwa da kawayena sau Uku muna abubuwa yanzu Kuwa sai dai nayi girki da aikin yara idona ya kawo kwalla nace wallahi Babanku ni ya haifawa nima ashe Ina can Kano Kuna Lagos ana ta tara min Yara na zaci abinci zanci na koshi na huta tunda ga kudi ga kayan dadi ashe ba haka bane Ina ganin Dan kula da Yara nawa abin yake

Su Hafeez suna ta dariya suka ce Yi hakuri yanzu Aunty tun daga kwana daya tal har kin karaya yaushe aka fara ma me akayi da maza, banga laifinki ba kina yarinya Kuma Amarya har an kawo Miki bataliyar Yara kiyi Hakuri,a raina nace wayyo Hafeez baku sani ba ni na jawa kaina yanzu idan Ummiya taji sai taci ubana karyar da na musu,a fili nayi murmushin yake nace ba damuwa ai haka Allah ya tsara gwara na rike ku ai a raina nace Allah ya Isa Asif tun a iya yini daya na Fara raina kaina ga wata uwar gajiya tun safe ban huta ban huta ba ga hayaniyar Yara ai muna Hira sama sama na koma kasan tiles na kwanta ban San nayi bacci ba ma,su Hafeez harda wani tafiya part din Jawad, Hafeez ya ganshi Yana ta aikinsa da takardu yace Yaya Aunty ta gaji tayi bacci a kasa Muna hira Muka ga tayi bacci kaje ka dakko ta,Jawad yace to goodnight kuje,ko ta kaina bai bi ba har ya gama aikinsa ya taho da su Ayanah Yana zuwa yace ke tashi ki Kai su suyi fitsari ki kwantar da su,Idona na bude na fashe da kuka na Fara burburwa da Shure shure nace ni Allah na gaji dan Allah ka yanke Naira Ashirin a cikin Albashina ka barni nayi bacci,Wai ashirin kacal yace Minus dubu dari to Ina Jin dubu dari zai yanke na mike zumbur na rungume Ayanah Ina Yan Yara anzo bacci inyee inyee to ku taho muje muyi kwanciyar mu,har Muka tafi Jawad yana tsaye a wajen Kamar an dasa shi tunda yake bai taba ganin me son banza Irina ba,Kai ya jinjina ya wuce part dinsa, Yogourt yasha tare da yin Shirin bacci ya kwanta tare da yin adduar bacci ya kwanta.

Tsakar dare Yana bacci ya juya yayi ruf da ciki Nan ya fara mafarkin sex dinsa daya Saba,Yana ta yiwa katifa Yana Nishi da gurnaninsa,lokacin Kuma naji Farida tana ta zazzabi dake su Uku suna bed dina tana ta nishi na fito sabo da na fada Masa ko da magani ya bani a bata.
Ina zuwa bakin kofar bedroom dinsa na dinga Jin gurnani da Nishi sai kace rago,handle na Murda na Shiga gaba daya a saman bed na hango shi ya jefar da blanket a kasa,baki na rufe da hannuna na tsaya a kansa Ina mamaki a hankali nace ohhh wannan kaji kuka irin na rago inama wannan rago ne Allah da a yau sai na jashi na tafi kasuwar Yan awaki da shi na siyar da na samu kudi dan a kalla na siyar da shi dubu tamanin da na samu banza kudi a banza,in sanwa Ummiya dubu biyar a ciki,Kadada Naira Hamsim ladan ganin ido,Daddy dubu daya,Farisa da Hamziyya Naira dari dari, Baba Kuwa ko ficika

Ina lissafina naji yayi wani lakwas yayi shuru,da sauri na dan matsa baya kadan nayi sallama da karfi,nasan lokacin ya farka amma ba lallai Yana hayyacinsa ba nace na shigo ya juyo da sauri ya kalleni fa mun hada Ido amma dake baya ganewa yace tsaya Ina zuwa karki shigo,Ina kallo ya jawo blanket ya rufe jikinsa sannan yace murda handle kofar a bude take,na dinga dariya a raina Ina tsaye a room din kusa da shi yace wani na Murda handle








Masu Sharhi Ina godiya matuka aci gaba da gashi please





AsmaBaffa
08033933642.
10/6/22, 22:02 - Buhainat: 🌏JIKAR MAGUZAWA 🌏
31-35


Official

By
AsmaBaffa


SADAUKARWA NE GA
ZAINAB GARBA BUTALAWA


KUDIN JIKAR MAGUZAWA 300 NE

MASU BANK TRANSFER 0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39


MASU YOUTUBE CHANNEL WASU BASA NEMAN IZINI SUKE MAIDA NOVEL AUDIO KU DINGA NEMAN IZNI DAN ALLAH.



_Ina mata y'an kwalisa ma'abuta gyaran jiki macce Mai gyara daban take ga zuciya mijinta muna da kayan mata da supplement na gyaran jiki kala muna hadin amare da uwargida Dana masu jego muna da set Mai hade da kaza Mai kwai 3 da cicicibe da kifi da galam 3 na tsime da Burkett din gumba 2 da garuruka da zuma wanna set na maccen da ta isa ne muna hadin shi 20k akwai karami set na 15k akwai na 10k akwai na 5k_

_Muna da zuma Bata gindin kishiya ga wadda kishiya ke muzguna mata wanna Zuma In kinyi anfani da ita miji salab zaiji Daya shiyasa indai ba macce cikin matsala take ba bamu Bata ita_


_Muna da magunguna masu jawo hankali maigida da kara martaba dasa alhere ga maruwacin namiji_


_Akwai Zuma kiba da hip sati Daya Kinga result_

_Muna hadin kiba duk ramar ki duk bushewa ki kinka sha shi sai ke ciciko_


_Fanin supplement ma ba'a bar mmn mujaheed abaya ba tana da nagyaran fata da kara haske akwai na gyaran brst na gyaran hip na kiba
Kamar su Lady capsule 4500
Sugar wanita 3500
Glutathione 3500
Vitamin e 3k
Gluta white 3500
Royal jelly 3500
Apetamin 3k_
_Frozen collagen 3500
Da sauran su insha Allah duk Wani supplement Zaki same su ga mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa
Ina wadda sanyi ke Hana ta jindadin gidan miji_
_Y'ar uwa kiyi bayani abaki dai2 da type dinki indai sanyi ki Hana Miki jindadin aure ku budewa GABA ku rashin niima to kedai yima mmn mujaheed bayani zata baki dai2 Dake mun tanade set din maganin sanyi 4500 Wanda zai fatataki sanyi Kuna kashe ne_

_Mmn mujaheed y'ar mutan skwatawa muna zaune garin kebbi state
08066726866_

_Kayan mu iya kudinka iya shagalin kane_




PAGE NAKU NE

Alhusna
Amina Adamu Usman
Bilkisu Tambari
Maman Murtalah
Umma Khursum
Oum Nuaima
Rukey Muaz
Aisha Sunusi
Mummy Hibbat
Smb collections
Hussaina Abdullahi
Maimuna Umar
Zakiyya Bello
Maryam T Baliya
M.j collections
Maman Nusy
Ruma
πŸ’”πŸ’”






Fuskewa nayi kawai nayi sallama harda bata rai sannan ya amsa nace Farida ce bata da lafiya tana zazzabi in kana da magani ka bani a bata,no asibiti ce dani ba magani ba,akan wannan sai kin tashe ni a bacci Ina bacci na me Dadi kin yanke min shi,a Raina Dariya nayi nace dama Ina so in tambayeka Ashe kana da cutar...? Yanzu naji kana ta gurnani da Zan shigo har naji sai na tuna masu fyarfyadiya nayi,Ido ya tsura min yaga alamar da gaske na ji,yace ae itace Watarana harshena har fashewa yake,Sannu Allah ya bada lafiya bani magani,kin tashi yayi ya nuna min wani first aid box yace zaki ga paracetamol na Yara ki dauka ya juya tare da gyara kwanciyarsa,idan zazzabin bai sauka ba ki sanar dani,to nace nayi waje abina,Ina komawa na tasheta da kyar ta tashi na bata maganin tana ta rawar sanyi,tace ruwa na dakko na Bata ta Sha da yawa,zumbur ta Mike tace amai na kaita toilet da sauri tayi aman ruwan da maganin,bakinta na wanke Mata na gyara toilet din muka fito na Bata maganin again nace to kwanta ta kwanta sannan na lullubeta, su Abeed kuwa suna wajen Bintu Asmau dakinsu da wasu yaran Suma

Haka Muka Yi baccinmu sai da asuba banyi niyyar tashinsu ba amma duk Wanda suka Fara tasawa sai da na tashe su Muka Yi sallah har su Asmau, Ina koya musu azkhar sannan wasu suka koma bacci tunda ba school sunday wasu Kuma Suka fara kukan yunwa,Kawai kitchen na wuce direct na Kira Yan aiki Suka tayani cikin lokaci kalilan na gama shirya breakfast su Bintu na sa suka yiwa dukkan yaran wanka tare da shirya su cikin kana Nan Kaya dama duk kana man Kaya ne da su ban taba ganin wani Atamfa a cikin kayansu ba har manyan su Hafeez ne kawai masu shaddoji da yadika Suma ba wani sakawa suke ba.
Abincin ma masu aiki ne Suka hada musu tea da komai manyan ma Suka zo Suka Yi serving kansu,kafin nayi wanka na shirya masu aiki sun gyara gidan ko Ina sai sheki da kamshi ke tashi,bedroom Dina na gyara kawai na shirya cikin kayan lefena wani lace me tsada na saka fari dinkin Riga da zani buba irin Wanda ake daura zanin akan rigar,Haka na daura naci dauri na nayi kyau sai kace zanje biki Ina Fitowa yaran suka Yi ta gaisheni suna cewa kinyi kyau Aunty,Waleed a hankali yace Yaya Ya auro babbar halitta,wucewa nayi kitchen banyi Niyyar Kai Masa breakfast ba amma dai na hada komai nasa a tire na wuce bangarensa,Ina tafiya Hafeez yace sai naga bana ganin Aunty tana zuwa part din Yaya kamar ba acan take kwana ba,Ahmad Yana kasa da murya yace ka taba gani ai basa zuwa a kan idon Yara sulalewa suke Yi a boye Kar a gani tana zuwa, Hafeez yace yau bazan Yi bacci ba sai na gani da idona tana wucewa taje ko shi yake zuwa

Shi kuwa gogan Ina shiga Naga yasha wanka cikin kana nan kaya ya fito Palo zai fita,yayi kyau sosai da sosai Ina kwana nace, Alhmdllh ya furta kawai yana tafiya ya furta na koshi yayi waje da sauri Yana cewa nayi tafiya ki kula da kowa sai Nan da 2weeks,da sauri na tambaya Ina lekawa compound sabo da sauri yake wacce kasar? Na tambaya, tsayawa yayi har na karasa gabansa da tire na yace min Sweeden ya fada Yana Shiga motarsa kafin ya rufe nace ko tea baza ka Sha ba? na furta da kunkuni,kallona yayi kadan Kamar bazai Yi magana ba yace Ina tea din to? a wata Yar ceramic kettle me kyau na tsiyaya Masa a cup Yana kamshi daukan cup din yayi yace sai me? nace ga chips ga pepper chicken Ina shagwaba,yace bafa birgeni kike Yi ba ganin dama nayi yaja tsaki ya dauki iya tea dinsa a cup zai rufe motar nace ka dawo min da cup dina Kar a batar min ku maza haka kuke duk abinda kuka dauka bakwa dawowa mace da shi spoon dina Kar a batar min, yace iko da kayana Zaki min ke Kika zuba min in zubar ma Mana Ina ruwanki yaja Tsaki tare da furta rufe min mota,hannayensa na kalla cup da waya ce a hannayensa da kafa na tura Masa kofar na rufe driver yaja suka bar gidan mamakina ko Kaya bai dauka ba masu aiki su Haruna na bawa suka cinye bani da aiki masu aiki sun gama komai,yaran na jawo na Fara musu kitso da kayan ado iri iri,kowacce da Kalar nata sun dade rabon da a musu kitso sai uban gashi duk ya lalace,Hafeez ne ya dawo ya kawo min. Sabuwar waya me kyau tekno spark 9 yace Aunty gashi

Nace wow Yayanku ne ya bada ku siyo min? Hafeez yace a'a kudi ya bamu jiya yace yau zaiyi tafiya mu kashe shine Muka Yi Karo Karo Muka siya Miki waya yanzu anci gaba kina ta amfani da karamar Vivo gashi ko dannuwa bata yi,farin ciki ya kamani nace kaii Allah ya muku Albarka nace Kash Hafeez kuyi hakuri an sarkafe ni da sasarin aure amma da sai nayi rawa,Ahmad yace Aunty point of correction igiyar aure dai,Nawa sasari ne a Ina ka taba ganin Amarya irina,layina na saka Suka dan saita min abubuwa na,Hafeez ya duba kaf bani da number Jawad yace Aunty ya Naga baki da number Yaya? Nace na haddace ta a kaina ai number masoyi haddarta akeyi,kiyi saving kin huta Hafeez ya saka number Yaya Jawad yace Aunty me za a saka Honey,Hubby,darling Baby? Nace sa Masa dankalin hausa shi ya dace da shi Yayanku ai sak dankalin hausa,Meenat tayi tafi tace wallahi ba shine ba yayanmu Sugar ne,Ashe Yara suna ji,Farida tace a sa Masa Handsome yaya,nace Kai Hafeez dankali dan hausa karka sake ka canja min suna,Hafeez dai ya saka Sweet potato ya sa min number dinsu Ina ta yiwa Asmau kitso itace ta karshe daga ita an gama su Humaira Yar yarinya ita akwai gashi rarrafe take yi bata son a taba Mata gashi Kuma yau dole sai na Mata ko calaba ce na sa Mata abun ado beats Ina gamawa Asmau na dauko Humaira na matseta a cinyata yanda baza tayi motsi ba,Ina taba gashinta ta Fara ihu amma ko kulata banyi ba sai da na gama tas sannan na sake ta,beats dinne ban saka ba a hakan ma Sai da nasa su Meenat suna Mata Wasa da wayo har na saka Mata duk sai Suka Yi kyau ko wacce Kalar nata daban,wayata Suka dauka bayan na bude snap chat suna ta yin pics harda ni Suka Yi munyi kyau kuwa Hafeez gaba daya ya turawa Jawad ta Whatsapp yaga Yan kannensa chas sun dawo Yan gayu,yaji dadi.

Washe gari da Yamma Abba yazo a motarsa shi kadai,Me aiki ce tazo ta fada min Baban me gidan ya zo Abba Yayan mahaifinsa,Kice ya shigo na yafa mayafi fari Kalar lace dina yaran ma suna bedroom suna Wasa Ni kadai ce a Palo sai hayaniyarsu a daki zaka ji,Abba ne ya shigo da sallama na amsa tare da mikewa tsaye nace sannu da zuwa Abba,kallona yayi sai yau ya taba gani na,nace zauna ya zauna kuwa durkusawa nayi tare da gaida shi ya amsa har da sakin fuska,ruwa da lemuka na kawo masa,anci sa'a Abba da son gaisuwa ko Indai zaka durkusa har kasa ka gaida shi to an gama, lemon ya Sha yace Ina Jawad din ne wajensa nazo,nace laaa Abba yayi tafiya yau Yana Sweeden maybe ma yanzu Yana jirgi,Abba yace ikon Allah to idan kunyi waya kice nazo nemansa ya kirani,kema bari na fada Miki yaran nan Zan dawo na kwashe su ai bai dace kina yarinya a barki da Yara ba haka gani Ina raye da iyalaina mene amfanina,Murmushi nayi nace Abba ba komai wlh Zan rike ai Kuma ya kamata ku huta amma kuyi magana da Jawad abinda yace shike nan yace to shike nan bari na koma,turaruka na kawowa Abba nace gashi Abba kayi amfani da su, bazan taba iya bashi a nawa ba sai a Jawad sababbi naje na kwaso uku nace a raina ko Babana sai yaci sa'a Zan bashi bare wani Abba,Abbo mato da dai Ummiyace sai na bata amma Baba ya min laifi bare wani Abba,yayi godiya ya tafi na Masa Allah ya tsare.
nace in Jawad ya dawo na fada masa

Abba tun a mota yace wannan matar tasa ai Mai hankali ce ban San Haka take ba to ga Kuma Hajiya Barira ta matsa a kwaso Yara ya na iya dole na karbo Mata Yara,Yana komawa gida ya iske Hajiya Barira ta hakimce tana cika tana batsewa,yace Umman yara Yana murmushi,Hmm tace Kawai tace yau bana Jin Zan iya girki Kuma bazan iya cin na Yan aiki ba sabo da haka ka Shiga kitchen ko jullof din shinkafa ka Yi min yanda Watarana kake min ai ka Dade baka

Please Login or Register in order to submit comment