Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kafadar Amana tana ta ciyar dashi saida ya koshi sosai sannan a karshe ta bashi kankana yasha,
Brush ta kawo masa sabo ya tsaftace sannan ya dinga kora zobon,
Amana kuwa abincin itama taci ta kwashe komai ta gyara room din tare da kara wanke toilet din ko Ina kamshi yakeyi,
Alim saman bed yajata suka shige sai wasanni sukeyi a ciki.
Huzaifa yaga Alim shuru yaki fitowa sai mamakin rashin kunyarsa yakeyi a gidan surukai, Badriyya tace ai mu nan gidan ba ruwan wani da wani,lallai rayuwarku tana birgeni a gidan nan kowa harkarsa yakeyi cewar Huzaifa.

Har magriba Baba Basu dawo ba,Huzaifa har ya fito jikin mota suka hadu dasu Baba sun dawo an kwaso Baba kamar kayan wanki yana ta numfarfashi,har dakin Baba yaje suka gaisa harda yar hira sama sama sannan ya masa ya jiki,Baba yana nishi yace ina wannan dan marasa mutuncin dan uwanka mijin Amanata
Huzaifa ya sosa kai Baba yana dakin Amana yanzu ma jiransa nakeyi ya fito mu tafi kar dare yayi,
Sanda Baba ya jawo a kusa dashi ya rafkawa Huzaifa a kansa nan take wajen ya kumbura,dan ubanka fitar minshi daga gidanaa na tsaneshi,Huzaifa dafe da kansa yace Baba lafiya kara daga sandar yayi da niyyar kwala masa Badriyya ta fado dakin ta tare tace ni ka dakeni Baba akan ka daki wannan me sukayi maka?

Huzaifa ne ya janye Badriyya yana bawa Baba hakuri suka fita,
Amana ne suka fito tare da Alim kamar zasu hadiye juna,sallama yayiwa mutan gidan kaf tare da yi musu kyautar ruwan kudi,Huzaifa kuwa Badriyya ya kashe da kudi sai Haladu da Sakina.

Huzaifa yacewa Alim malam dan Allah ka shiga wajen Baba ka fito mu tafi dare nayi mana,
Murmushi Alim yayi, Amana tace karka damar min miji dariya sukayi gaba daya.
Suna shiga Baba ya dinga zagin Alim da Bala'i. Yace kuma dole ka sakar min yata gadon tsiya, Amana ce take kuka haba Baba wannan butulcine,Baba yace Butulcin Ubanki akan sun bamu yan kudi da yi mana wannan gidan.gidan banza gidan wofi nan fa Ba irin cin mutuncin da Baba baiwa Alim ba,Alim sai hakuri yake bashi tunda shi Bai San dalilin zagin da Baba ke masa ba.
A hankali yace Baba kayi hakuri amma bazan iya sakin matata ba,
Baba sai da yaja nishi sosai sabo da azaba ciwo yace da yake uwarka ce ta haifa min ita ko kai nafika iya shege na fika tantiranci,ka tambaya kaji gogaggen dan duniya ne ni nafi karfin uwarka ma.
Amana cikin kuka tace Baba wai Mene haka dan Allah,Jan hannun Alim tayi muje kawai na bika mu koma Lagos.
Baba yace kije gidan uwarwa kai na fiku tasha wlh,kaje ka kawo min takardar yata kuma saki uku tafi ka bani waje ke kuma na fada miki idan kika kuskura kika bar garin nan namu to ban yafe miki ba,

Amana tace Baba iya garin nan ko ka yarda na fita na zagashi yace ae iya garin nan zaki zauna,ko gidana zaki bari to ki zauna iya garin nan kiyi ta yawon duniyarki amma a anan garin.

Shi Baba ganinsa ya kafawa Amana tarko,Alim yace Baba na tafi Allah kara lfy ya zaro damin kudi ya ajiye masa,Baba ba kunya ya karbe tare da Jan tsaki
Amana suna fitowa waje tacewa Alim sallami Huzaifa ya tafi gida ni kuma ka jirani muje wani gida a garin nan tunda Baba Bai hanani fita a nan ba.

Haka kuwa Huzaifa ya tafi Amana ta dauko kaya a hand Bag Babba tace muje,Alim yace nifa tsoro nakeji kar Baba yayi mana wani Abin,
Dariya Amana tayi tace rana zafi inuwa kuna both Mum naka da Babana ai kawai muyi me dalili mu rufta kawai Baaaba komai ta fanjama fanjama.
Dariya Alim yayi tare da lakace mata hanci,taja Hannun Handsome Alim suka Sha kwana ta wani lungu.





AsmaBaffa

Tnx all
CIRANIN AMANA




140-145



Official



By
AsmaBaffa







QUEEN MERMU AGAIN,THS PAGE IS FOR UUUUUU





Corner su Amana sukesha kawai ba ji ba gani har Alim ya gaji yace gaskiya honey a tsaya am so tired daga cewa ba nisa nan nan sai Shan corner mukeyi da layika,
Kafeshi tayi da Ido duk ya jigata saboda Sam Bai Saba da wahala ba,gashin kansa ya hargitse harda bige kafarsa domin wajen ma ya dan yi jini kadan,
Lazy kawai kamar ba Namiji ba,yanci zamu karba wajen iyayenmu Amana ta furta tana kada masa idanuwa,murmushi Alim yayi kinga karfa wani yazo wucewa ya kallar min farin da kike min da ido am gealous,
Kuma taya zamu karbi yanci a haka wai ma ina zamu،hope dai baza mu Dade ba kinsan Aabid dina yana can Mum zata kara lalata minshi da wasu halaye kina gani yaron yanzu kullum boyeshi takeyi a room dinta ko ganinsa bamayi a gidan makaranta ma ba kullum take bari yana zuwa ba,yaron kafin na zo nan na ganshi duk ya rame,idan yace Momy ko Daddy Mum makeshi takeyi,wlh na rasa yanda zanyi da Abin ga Aabid saurin girma gareshi...

Nasan komai fa ba sai ka fada min ba Allah zai kawo mafita kaji sai hakuri,kwalla Alim ya share da sauri kar Amana ta gani,ita kuwa Amana ta gani amma sai tayi kamar bata gani ba,Naushinsa tayi kadan a kirji ba shiri ya saki kara ouchhhh.....be a man,u have to be strong fa muje ta kama hannunsa oya muje kawai,
Sun kara tafiya me Nisan gaske kamar zasu bar garin sannan suka isa wani dandasheshen wani gida dan karami harda gate yasha tiles da flowers.
Gidan ta kwankwasa wata dattijuwar mata ta bude tare da fitowa nan take matar ta washe baki tare da cewa barka da zuwa Hajiya,
Amana tace yawwa suka gaisa,matar Sa'adatu tace Hajiya lafiyar gidan kikazo dubawa domin nasan mun biya kudin hayarmu
Amana tace Sa'adatu wannan miji nane shine me gidan nan mun dawo zamu zauna a saman benen tunda dama iya kasan na Baku haya nace Ku dinga hawa kuna gyara min sama kar a bar mana gida da dirty,
Murmushi Sa'adatu tayi tace hakane komai yana nan tsab a part dinku wato upstairs,bari na kira mijina,
Malam Salisu ne ya fito suka gaisa cikin mutunci sannan Amana ta masa bayani ta kama Alim suka haura sama part dinsu,domin gidan part biyu ne,kasa 3 bed room ko wanne da toilet,sai Palo kitchen da toilet,saman ma haka take komai da komai. Sa'adatu da Malam Salisu sai yaransu 3 babbar macece yar 20yrs Iklima,kamal da Yahaya suna part din kasa.

Alim shi kam mamaki yakeyi Amana yaushe take da gida bari su huta zai tambayeta,
Suna shiga abin mamaki latest dubai furniture ne a saman yasha Alatu,sosai an kawata part din da kaya na Alfarma amma komai a rufe da ledarsu.
Amma Sabo da Sa'adatu na gyara shi kullum ta kulle da key kal kal komai suke sai kamshi ko ina ke yi kasancewar Sa'adatu me tsafta ce.suna shiga ya shige bedroom kalar bed din sun birge Alim tafiya yayi da niyyar fadawa bed din domin ya gaji caraf Amana ta damkoshi tare da jawoshi baya tare da kakkabe masa rigarsa wai zai bata jikinsa,

Ledar dake lullube da katifa ta kwaye nan ta leka kasan bed din fes dashi Sa'adatu na daga katifa ta share da moping,sip ta bude ko ina bedsheet ne kalakala sun kai 5 masu kyau ko wanne room da kalolinsu,duk ta da musu turaren ajiya a ciki sai kamshi sukeyi,share room din tayi tare da moping cikin zafin nama dan babu abinda babu a part din na amfanin gida komai Sabo kamar sabuwar Amarya nan ta shimfida bedsheet wani Mai kyau na gaske,room freshner ta fesa da turaren wuta ta kunna, toilet ma ta kara wanketa fes fes, kafin kace me room din ya dau kyau, palo ta fito Alim ta hango a tsaye yana ta layin gajiya sai rufe ido yakeyi gashi Amana ta hanashi zama wai zai bata kayansa,

Ido suka hada ta kashe masa ido daya tare da jan hannunsa ta kaishi har kan bed din riga ta cire masa da wando daga shi sai tight da singilet sannan tace oya slip kafin sallar isha bari na kara sa aikin,sai binta yake da kallo wani farin ciki ya cika masa zuciya.
Ficewa tayi haka tabi ko ina a upstairs part dinsu ta cire ledar kayan ta gyara komai ta share ta goge ta kunna kamshi sannan ta kunna Ac ta duka dakunan kasancewar da wuta tuni gida ya dau kamshi,waje ta fita ta siyo taliya spagetti da kayan miya hade da danyen kifi harda indomie da kayan shayi da wasu abubuwan na amfani da babu,direct kitchen ta shige kamar kitchen din Amarya komai na harkar kitchen akwai kayan abinci ne kawai babu fridge ta kunna ta zuba lemuka da ruwan robar da suka siyo sannan ta fara girki, ko gas babu sai kerozine da ta siyo ta cika katona resho ta,ta kunna miyar jajjage tayi tasha kifi ta dafa taliya sai coffee da ta hada ta cika musu flask ta shirya abincin a dining sannan ta gyara kitchen din kamar ba a ciki tayi girki ba,toilet ta fada a dayan bed room din wanka tayi sosai,
Ba sallah takeyi ba tana fitowa gashinta ta busar da hand drier da ta taho da ita a jakarta sannan ta shafa lotion dinta ta shirya cikin wata gaunt iya gwiwa me dogon hannu peach color toilet ta koma ta wanke kayan data cire tare dana Alim data cire masa ta Shanya su.
Zama tayi ta rangada kwalliya sai kamshi takeyi sannan ta dauki jakarta ta koma dakin da Alim ke ciki,tana shiga ta tadda shi ya tashi sai mika yakeyi da salati bakinsa dauke da addua

Sabulu da sabon soso ta kai masa toilet sannan ta dawo ta zauna kusa dashi ta zo zata rungumeshi Alim ya buga tsalle ya ja baya,
Tana dariya tace lfy? Murmushi yayi yace rana ta dake ni dazu ga tafiya munyi da kafa nayi dirty ai sai ki shafi dirty na,
Amana tana murmushi ta karaso kusa dashi suna facing juna tace see u kaji kamshin da kakeyi kuwa zaka ce kayi dirty,babu me cewa kayi wani tafiyar kasa,come here joooo ta afka tare da hugging Alim harda cusa kanta a kirjinsa tare da manna masa kiss normal babu wani canji saima kamshi da yakeyi,
Brush da toothpaste ta mikawa Alim to maza yi wanka ka fito tare da mika masa towel ya shige ta rufo masa kofar.

Wasu sabuwar farar jallabiya da sabuwar singlet da boxers ta dakko cikin wanda ta siyowa Alim da taje cikin Kano hospital kai Baba shine suka je ShopRite ita da Sakina sai ta ajiyesu da nufin idan ta koma lagos zata bashi.

Yana fitowa ta mika masa mai me tsada da kamshi ya shafa sama sama,turarukanta ta mika masa ya shafa sannan cike da mamaki tambayoyi cike a zuciyarsa yasa kayan da ta bashi dai dai shi kamar an auna yayi kyau sumarsa sai sheki takeyi,comb dinta ya karba ya taje kansa,
Tunes ce ke kwakularsa Bai gama Shan mamaki ba saida Amana ta jawoshi Palo saman dining food flask hadaddun gaske nan suka ci suka Sha suka godewa Allah,
Kwanikan ta kwashe suka koma Palo ya jawo Amana jikinsa suka kwanta a kan 3seater suka mamuki juna domin a kan jikinsa ta kwanta,

Ga plasma TV Amma ba a hada kayan kallonba
Gashin Amana dake matukar fidda kamshi ya fara shafawa a hankali kana ya fara magana kasa kasa Amana tashi zaune muyi magana,ba musu ta Mike tare da Zama suna gugan juna,yace tambayarki zanyi duk wannan Abubuwan ina kika samosu wai I mean gida,food,kayan jikina etc.

Murmushi tayi sannan ta Mike tace ina zuwa bedroom ta shiga handbag ta bude ta ebo wasu takaddu guda uku ta fito dasu ta zauna kusa da Alim tace Babyna ba Abin mamaki bane,
Wannan gidan daka gani gidanka ne,sanda ina gidanka ina Kula da Aabid dina kana bani kudi masu yawa haka duk wata a accnt dina kana biyana kudi kafin a daura mana aure

Numfashi ta ja tace to da kudin da kake bani na sai maka wannan gidan har kayan dake ciki dalilina kuwa ko Mum tace ka sakeni nasan baza ka iya ba idan ma ka sakeni kaga sai na fada ma na dawo gidan nan da Zama har Allah ya dai daita komai,Ko iyayena basu San da gidan nan ba,Badriyya da Ya Hamza ne kadai suka sani domin su na turawa kudin nace su sai min gida,to sai suka ga wani ya gida wannan wai baya son gidan garin ya masa kauye da yawa shine suka fada min nace su siya min da shedu,
Takardar shedar gidan ta mika masa da sunan Alim da komai a jiki daya takardar ta kara mika masa ga wannan shi kuma takardar kayan da aka zubane gashi,kayan sawa dana Baka shekaran jiya munje kai Baba hospital Kano city na siya ma da niyyar na Baka idan na koma lagos suna cikin akwati da yawa gobe zan dauko ma a gidanmu

Abinci kuma kana bacci na siyo kayan dafawa na yi mana duk cikin kudin da ka bani dazu a gidanmu,
Mamakin Amana ya cika Alim gaskiya Amana macece ta gari duk da basu da kudi amma gashi Abin duniya Bai dameta ba,da wasu ne ai iyayensu da yan uwansu zasu bawa komai har cutar mijin zasu dingayi

Firgigit ya rufe bakinsa sakamakon Amana data hade masa su waje daya.
Mika mata takardar yayi yace wannan gida ni Alim na mallakawa mata ta halak malak shi ga takaddu rikesu,
Amana cike da shagwaba tace Allah Baka isa ba yaro dankwali yaja hula,kaza ta janye zakara kayi gida a garinmu wooooo

Dariya Alim yayi yace bazan karba ba kukan shagwaba Amana ta fara dole sai ya karba ita me zatayi da gida,ai bata fatan ta zauna ba a gidan mijinta ba,dole Alim ya karba sabo da rigimar Amana,sallar isha yayi da nafeela yaja Amana suka fada Bed nan Alim ya shiga romancing dinta ya fara magana da.....

Mum ce zaune gefen Abba ga su dan Auta,Abba ya kalleta yace Ina Nura ki fada masa gobe ya dauki matarsa su koma gidansa an karasa masa ginin gidansa anyi komai,nan take Mum ta hade rai tace yanzu duk Fadin gidan nan Alhaji sai kace sai sun koma gidansu fisabilillah,Aabid ne ya shigo room din tare da Islam yar gidan Nura,
Mum ce ta dauki jikokinta tace ai Ku muna nan tare daku ko? Aabid cikin masifa da kuka yace ni Bana sonki Momyna new Anty nake nema da Daddyna,make masa baki Mum tayi ta jefoshi kasa Ku fita yan iskan yara kunyo halin iyayenku.

Abba ne ya jawosu jikinsa ya fara lallashinsu sannan ya fara balbale Mum da masifa sosai,Dan Auta yace gaskiya Mum wlh bakya kyautawa ki dinga dubawa dan Allah.
Zakinsa Mum tayi ya tashi ya bar dakin amma Mum tace dole Nura da matarsa ma a gidanta zasu zauna baza su taba komawa gidansu ba,matar Nura har kuka tayi tace dan Allah Mum kiyi hakuri ai nan Mum ta kurma ihu da kukan karya tace matar Nura ce ta zageta babu wanda ya saurareta.

Yau kwanan Amana da Alim Uku a gidansu dake garin,sun siyo kayan abinci komai da komai,sannan Amana ta dakkowa Alim wasu kayansa na wajenta,itama ta kwaso nata Sulemanu Harka da yan gidan ba wanda Yasan a inda Amana take kwana domin idan tazo duba jikin Baba zasuyi hira da yan gidan da iyaye har Ummanta amma ba wanda ya taba tambayarta a ina take Zama,Badriyya kadai ce ta tambaya Amana ta bata labarin komai,Badriyya tace Good gwara haka,Huzaifa ma ya sani sai dariya yakeyi mace ta rike Namiji.

Da ATM card din Alim suke cire kudiin da suke amfani dashi Amana ta San code number dinsa komai tare sukeyi soyayya suke Sha kawai danma Amana na period ai maybe da tuni tayi ciki.

Sati daya tsakani Mum ta samu Abba tace ya kamata Alim ya dawo gida haka nifa ban yarda da yaron nan ba,masifeta Abba yayi ya fara ki yayeni wlh zan baki mamaki shashasha uwar Banza,
Tsaki Mum taja tare da ficewa ta fara neman Number Alim cike da fushi,
Alim kwance kan cinyar Amana suna kallon news kiran Mum ya shigo,ya kai hannu zai daga Amana ta kwace wayar tace karka daga ka jirani zuwa dare zamu kirata back.
Murmushi Alim yayi yace nasan bakya fake mission Allah kaimu.
Waya ta daga ta kira wani dan daba dan wiwi tace ya Akayi Sa'idu kunkuru Amana ce mu hadu A shagon Bilya No sleeping no sitdown ka gane? Cikin muryar daba yace an gama Baabaa sa'a dai chau wlh ba yawa.
Tana gama waya Alim ya fara kishi da masifa,da kyar ta shawo kansa ta ganar dashi dalilinta sannan yayi shuru.

Da dare kuwa ta jashi har shagon no sleeping no sitdown wasu tantiran yan kwayane da wiwi.
Ko Ina kallon Alim akeyi dan gayu bature
Suna zuwa Kunkuru yace fada min matsalarki,nan Amana ta musu bayani suka Sha dariya,wayar Alim ta dauka tare da dan nawa Mum kira ta mikawa kunkuru,

Cikin muryar Basawa Bilya Kunkuru ya ce Hello Iyya danki Alim ya mana yawa yanzu zamu cika masa aiki,Mum taji murya kamar ta mugyanbo ta fashe da kuka tace dan Allah karku taba min dana ko nawa kuke so za a baku wayyo na shiga uku,
Duk Mum ta rikice,Amana ce ta amshe wayar tare da canja muryar katon gardi tace Hajiya kuyiwa danku zaman makoki kawai ba kudi muke bukata ba,munyi kidnapping dinsa zamu aikashi Can,Mum ta fashe da kuka Amana tace Baabaa ba yawa a fede min shi.
Alim ya tafi duniyar tunanin da mamakin Amana yaji kwanya masa mintsini ba shiri ya rafka kara,sai Mum ta kwalla kara ta cikin wayar ta fara kwalawa yayanta da Baban Alim kira.

Abban Alim.....Nura....na shiga uku Nura.....Ku fito kuji shike nan Alim wayyo ina zan sa kaina na shiga uku dan Autana Ku fito.
Kit Amana ta kashe wayar Alim baki daya ta cire simcard din tasa sabo a ciki,tayiwa su Kunkuru sallama tare da basu kyautar kudi.

Sun kusa zuwa gidansu a dan wani lungu me duhun tsiya Alim ya manne Amana a jikin wata katangar gidan wasu ya fara tsotse bakinsa baji ba gani,Ya bita da mirza dukiyar fulaninta,sun fita daga hayyacinsu sosai a lungu wani dan tsoho yazo wucewa ya kunna torchlight me mugun haske ya dallesu da ita nan take tsoho ya saki salati da karfi harda kuka ya fara shike nan karshen duniya yazo tamu ta kare shegu tambadaddu,kara haskasu yayi yaga ko kallonsa basuyi ba sai kara salo sukeyi Amana ta juye Alim ya koma shine a jikin katangar, sai sakin kalamai sukeyi wa junansu na tsantsan kauna

Tsohonne ya kara matsawa ya dallesu sosai Allah ya shiryeku watsatsu iyayenku nacan kunzo nan kuna lalata tir daku,Amanace ta juyo tsoho yace munafuka maza ki bari ya lalataki ki kaiwa Ubanki cikin shege har gida,akan kinganshi Bature Nasara asarar duniya shine kika tsaya yana wannan tabargaza dake...yiiiiiiiii......tsoho ya fashe da kuka yace wlh Ku bar nan ko nayi maka ihun kwarto,Alim yace matatace fa,ai tsoho kururuwa yasa yace karshen zamani yanzu karuwarka har ta Zama matarka yanzu daurawa kanku aure kukeyi,Amana zatayi magana tsoho ya kurma ihu ga kwarto ai nan danan jama'a suka fito ta kudu da arewa da sanduna,Alim shi nufinsa su tsaya sai ya kare kansa,Amana ta tartare skert tace wlh baza su saurareka ba dukan tsiya zasuyi mana a kauye ne fa ba lagos ba Arewa fa ba kudu ba.

Zo mu gudu wlh kafin musha sanduna, Alim yace oh God ni da matata wai wannan ai sa Ido ne,Alim yaga mutanen da gaske suke Bai San sanda yaja hanun Amana ba suka arce sai a palonsu suka tsaya suka kulle ko Ina da key suna haki

Mutanen har kofar gidan su Alim suka ja birki tsoho ne ja gaba yace asararru Ku fito in kun isa,Amana ce ta leko tare da Alim ta saman bene ta haskosu da torch tace Baba tsoho kun gammu wullu,Alim yayi dariya tare da rungumo Amana su Baba tsoho suna kallonsu sai tsotsar juna sukeyi,
Tsoho ya kwalla da karfi in kun isa Ku fito baku cika marasa Kungs ba ai,Alim ya kwala da karfi shima yace Baza mu fito ba kuma dole mu kwashi duniyarmu,Tsoho ne ya kada kai yace Allah yana kallonku zaiyi maganinku ne duniya zata ladaftar daku karuwai.






AsmaBaffa masu comment tnx alot love u.
✳CIRANIN AMANA✳



145-150



Official



By
AsmaBaffa





MAMAN WALEEDA INA KIKA BOYE NE?


WANNAN PAGE NA 'YAN ASMABAFFA FAN'S CLUB NE DUK WACCE TAKE WANNAN GP TO PAGE DIN NAN NAKUNE LOVE U ALL.





Alim dai mamakin sa'ido na yan kauyen yakeyi Bai Saba ganin hakan ba Sam,
Sabo da haka ya dage dole sai ya ganar da tsohon nan gaskiya kar ya kala masa sharri
Alim ya kwallo da karfi Baba tsoho ka fahimceni mana matata ce pls ka gane,tsoho dai ya kara haskesu yace kai ni nan dan zamani ne harda hada dan turancinsa kalleni da kyau noti a small boyi ni big ne zaka mai Dani gara, uwarka ka yiwa ba ni ba shegen yaro,
Tsaki Alim yaja tare da dafe kai Amana tace ka kyaleshi kaima kasan fa ba ganewa zaiyi ba,
Tsoho yace kinyi da uwarki Abinda yasa muke yiwa irinku Wa'azi Ku tuba Ku daina saboda idan Allah ya tashi kamaku sai a hada da mu na gari wanda bamuji ba bamu gani ba wlh baza mu yarda da Ku a cikin garin nan ba,indai na isa sai nasa an koreku daga garin nan muna ji muna gani Ku jawo a kifar da garin ko ayi mana girgizar kasa,to Ku sani billahillazi la Ila ha illahuwa

Please Login or Register in order to submit comment