Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Amma da kyar yake daurewa har sai da ya daina kwana gidan Mum saboda tashin hankali yake shiga yanda Yake kallon Amana tana kashe kala,gashi sai kara kyau da girma takeyi har akayi arba'in Aabid yayi wayo sosai gwanin sha'awa
Ranar kuwa da ta cika arba'in ranar Alim zuwansa gidan Mum yafi Goma yana jira yaga Amana ta Zama ready su tafi gida,Amma sai yaji Mum tace kano zasu tafi tare da Amana su zaga dangi,

Da bacin rai ya koma gida,Saida Amana suka gama zaga dangin lagos sannan suka wuce kano kwanansu 4 suka dawo lagos,washe gari Mum tace shirya maza na kaiki gidanki,wannan mijin naki kamar zai dakemu kina gani da kyar ya gaishe ni.

Amana ma tayi missing mijinta,har gida Mum ta kaita da yamma misalin 5pm,
Nan Alim ya fara fushi yana shagwaba,da kyar Amana ta lallashi abinta, yana dawowa daga Sallar magrib,yasa Amana ta kara bawa Aabid Nono ya koshi ya tattarashi ya kaishi wajen hajja,

Amana tace idan yayi kuka fa?,Alim ya ce can da matsalarsa yazo ya kankane komai ya barni cikin wahala,
Ranar Amana taga ta kanta a hannun Alim,ya gurjeta son ransa,

Sunji dadinsu sosai,Alim kara nutsewa yayi akan so da kaunar Amanarsa,
Kullum yana manne da ita ba sauki ba daga kafa,itama Amana hakan take irinsu daya.
Saida Alim yayi Hutu na 2wks sannan ya koma aiki,

Wata yarinya ce wacce sukayi university da Alim a london Teema take matukar son Alim,kullum sai tazo office dinsa kan ita sai ya aureta,Alim Amanarsa ta isheshi,bazai iya mata kishiya ba Sam,
Yanda yake mutuwar son matarsa me zai ci da wata,yayiwa Teema bayani amma taki yarda,shi kuma Bai son wulakanta dan Adam musamman yanda sukayi schl daya,yana ganin mutuncinta.

Yauma kamar kullum tana office dinsa,dabara ce ta fado masa yace Baza ki iya kishi da matata ba,Teema tace haba dai ai ni nafi karfin ko wacce kucaka, ka kirata mu hadu kaga yanda za ayi sai abinda nace dole ma ta hakura,
Murmushi Alim yayi,Teema da kuri tace kirata mana tazo na fada mata amma da sharadi idan ta yarda dole ka aureni,Alim yace kwarai kuwa.

Amana ya kira a waya tana jikin mirror tana sheka kwalliya ta daga,Alim yace kizo Office yanzu wata tana son ganinki wai zata aureni zata iya kishi dake shine nace kinfi karfinta ni mijin tace ne amma taki ji,wai sai ta ganki.

Kamar an watsa mata ruwan Zafi haka Amana ta mike, gyale ta figa a hannunta ko yafawa bata yi ba,Aabid dama yana wajen Hajja,motar da tafi ko wacce tsada da kyau a gidan ta shige tare da fisgarta sai office din Alim,Teema kuwa harda fitowa waje tana jiran Amana,
Alim sai dariyar mugunta yakeyi yasan yau Teema ko mari daya ne sai tasha a hannun Amana,

Motar Amana ce ta Parker tun daga parking kasan ba lafiya,tana fitowa Teema ta sume a tsaye ganin Amana,tunaninta Amana ba wata me kyau ko hadaddiya bace tunda tasan Mum kewa Alim aure,
Tun kafin Amana ta karaso daga yanda Amana take tafiyar gadara da takama gashi kana ganin idanunta kasan a bushe suke sun goge da duniya,
Duk wajen ya dauki kamshin Amana,shigarta kanta abin kallo ne wajen tsada da haduwa,
Alim ya fito waje yana ta faman murmushi da Ido ya nunawa Amana Teemace me son zama kishiyarta,Teema kuwa ta maza tayi,tare da hade rai wai itama shegiya ce,wajen Alim ta matsa tana masa wani kallo,
Hannu ta daga wai zata rike hannun Alim,dan Amana ta gani tasan suna soyayya.

Kafin ta ruko hannun Alim,Alim yayiwa Amana magana da Ido wai kullum haka take takura masa a Office,shi wlh ya gaji zai aureta,Amana da hannu ta yanka wuyanta wai sai ta yankashi,murmushi yayi,Teema kuwa taje tana hada hanunta dana Alim wai zata rike, Amana ta fincikota baya tare da kifa mata maruka har uku,
Tare da shake Teema ke karamar yar Iska kin sanni kuwa,Teema Ido ya firfito sai hawaye,sakinta Amana tayi tare da ja baya tana, bana Cece kuce da mutum na wuce nan,Dalla ja rubabben bakinki dake yar kauye zaki taba mijina da kazamin Hanunki kwartuwa ana zubar da aji ana bin maza,nafi karfin kishi dake,
Warning na miki kika kara zuwa Office din mijina sai nayi daga daga dake, Alim munafuki harda cewa sorry Teema kinga abinda nake fada miki gashi fuskarki ta kumbura kika ki yarda,ba laifina bane,

Teema share kwalla tayi tace amma Alim kayi asarar halinka wlh,sam bansan haka ka Zama lusari sakarai ba,kai da kake dodon mata amma mace yarinya karama jibi yanda ta ke Baka Umarni,Alim yace uhm wlh kuwa ganemin hanya Teema aini a kanta na gama lalacewa,ta shanyeni na shanyeta idan ba ita rayuwata Baza ta yuwu ba,kinganta to bana jin yaren kowa sai na Honey ta,

Teema fuska kumbure tace Allah yaji kanka Alim,wlh ka haukace aikin banza kayi asara dai,kuma marin da tamin Allah ya Isa wlh Bazan yafe ba,
Alim yace taba mata miji da kikayi bata ce miki Allah ya Isa ba sai ke dan ta dan mareki,hukunci ta miki a duniya kafin Allah ya miki nasa,karki sake ki zagi mata ta wlh a nan zansa a tara miki gajiya uban waye ya kawoki Office din mijinta,
Amana tace a bar mana Office yanzu ehe, Baby muje gida an tashi a Office yau Baza ka zauna ba sai gobe kuma,
Alim yace an gama ranki ya dade,ya kwaso wayoyinsa ya rufe Office yabi Amana,yace Securities su kai motocinsa gida Madam tace a tashi a Office haka,
Amana harda jin dadi Alim yabi maganarta,abinda idan yaga dama idan ta yi ba dai dai ba sai ta gane kurenta ba wani mijin tace.

Teema kuwa motarta ta shiga tace Amma na maru wlh,wannan jarabace da ace na kulata Dukan tsiya zata min,ga shegen iya mari,hannunta laushin tsiya Amma idan ta dakeka sai kaji ajikinka,
Kamar namijine ya mareni,yaje ya zauna da jarabar matarsa,mijin tace shege,dan iska,tsinanne ta dakeni Amma ko a jikinsa koma ya mata fada.wannan Alim ai shine dan iskan marar mutunci suje can su karaci jarabarsu ko kallonsa wlh Bazan kara ba tunda bashi da mutunci haka Teema ta dinga zage zage har ta koma gida.
A ranar ta nemo tsohon saurayinta me sonta da take masa wulakanci suka shirya zai turo ya kwashi tsohuwa Teema..domin Teema Sa'ar Aleem ce 33years itama.

Amana a mota sai faman dariya sukeyi da Alim yanda Teema tayi,Amana tace sai ni wlh har aja Dani ko wacce shegiya ce, tana driving Alim ya mika mata hannu ta rike tare da hadewa da sitiyari tana tukinta,

Tana Driving Alim na tabe tabensa a jikinta,yana dora hannunsa a kirjinta Amana tayi slow da mota ta kara fincikar motar,yana kara tabawa Amana ta gangare kasa tace zo ka karbi driving bazan iya ba ai sai kasa muyi hatsari ai,
Dariya Alim yayi tare da cewa na gaji ban iyawa,na daaina tabaki muje pls,
Driving taci gaba har gida,

Wannan shekarar Amana da Alim sukaje aikin Hajji again suka koma umrah tare da Aabid dinsu,Amana na zuwa schl tana karatunta sosai yanzu tana final year,

Salma ta gidan Deeni kwaro tana dauke da ciki haka matan su Hamza ma,
Shekarar Aabid biyu a duniya Amana ta samu ciki za ayiwa Aabid kani ko kanwa,
Murna sukeyi sosai,tana gama degree dinta da wata biyu ta santalo Danta Namiji shima,
Ranar suna aka sa masa sunan Baban Amana Sulaiman suna ce masa Irfan,

Aabid an girma an zama dan saurayi,
Amana tana jin dadinta suna zamansu lafiya ita da Alim da yaranta,
Sai abinda sukeso, har ansa Aabid a schl, Amana ba abinda bata Yiwa Alim don ta faranta masa,sai abinda yakeso,kullum Amana cikin gyaran jiki da kwalliya a haka take kara susuta Alim,ya gama matowa a kanta,akan Amana sai dai a mutu,

Ga tsananin biyayyar da Amana ke masa,uwa uba ga iya kwanciyar aure,ta gama da Alim gaba daya, baya ganin kowa a gabansa sai Amana.
Kullum cikin soyewa suke basa iya zama ba tare da juna ba,
Bayan bikin Ameer dan Autan Mum da Amaryarsa Minat.
Alim yace Amana taje tayi masters,haka ya kara biya mata private schl ta fara masters,
Tana gama masters ta kara samun cikin na Uku,
Wata tara ta haifo yarta mace zukekiyar gaske me kama da Alim,Daga nan Alim yace ta huta haka da haihuwa sai nan gaba an dan dade.

Yaran su dagwas dagwas dasu gwanin sha'awa su uku, Aabid kullum baya fara'a cikin muzurai yake da kaninsa Irfan ya masa Abu ko Mufeeda kanwarsa zai samu ya zanesu,baya daukan raini kamar Babban mutum haka yake,
Yanzu ya daki mutum ba ruwansa,mugune Aabid na karshe,baya wasa da Yara,ko cikin Yara ya shiga yan uwansa sai dai kaji Kukan Yara ya bubbugesu ba ruwansa,kannensa ma tsoronsa sukeyi,
Mugun tsoron Amana sukeyi yaran nata don sun San idan sukayi laifi ba ruwanta zata hukuntasu,shi yasa suka taso masu hankali nutsatsu ko ina suka je zaka gansu cif a nutse,kallo Idan Amana ta musu sun San me take nufin.
Alim ne ke shagwaba su ma baya son ana taba su.

Alim ne kwance a bedroom dinsa Amana na gefensa,Mufeeda ta kwankwasa kofa Dad...Dad....ta kwalawa Alim kira, Alim ya mike tare da bude kofa,lfy Mufeeda? Ni a wajenka zan kwana Ya Aabid dukana yakeyi,wai muyi bacci,
Amana ce tazo wajensu tace Baza ki kwana ba Mufee ki koma Bed dinki,me ya kaiki wajensu ke dana ce ki je dakin Hajja ki kwana,

Kuka Mufeeda ta fara ni...ni bana son wajen Ajja.
Alim ya kalli Amana tare da yin magana kasa kasa yace yarinyar zata hanani sakewa yau,kin kuma san Bazan iya jure rashinki ba,
Amanace ta riko Mufee tana lallashinta ta maidata dakin Su Irfan ta dorata a Bed dinta,Aabid sai fushi yakeyi su baza su kwana da mace daki daya ba,
Momy pls mu baza ta kwana a room dinmu ba.
Amana tace zan taka wuyanka Aabid ka rufe min baki,kunyi karatu kuwa yau kaida Irfan?yes Momy cewar Irfan,gobe zan duba na gani ai Amana ta furta.

Shuru Aabid yayi Irfan yace sorry Mum zan kula da ita,
Hararar Aabid Amana tayi tare da cewa idan naji kukan yarinyar nan Aabid saina karyaka.
Shuru sukayi Amana ta dinka masifa ta kashe musu light tare da rufawa kowa blanket ta rufe musu kofar ta koma wajen mijinta, suka fara baje Harkar da suka saba ta sunna..wajen Sunna basa sanya.




ALHAMDULILLAH





Ina matukar farin ciki da godiya ga Allah daya bani ikon kammala wannan littafin CIRANIN AMANA.
Godiya da jinjina gareku readers,masu sharhi,godiya etc,masu yin Document,masu kirana a waya

Bazan manta daku ba mutanena na:
AsmaBaffa fans club

taskar fiddausi so dangi

Hause of Hausa Novel

Zauren Queen mermu

Samarin Bana fans

Maraicin so fans
Da sauran groups da wanda nake ciki da wanda bana ciki na gode sosai Allah ya bar kauna.



Next coming novel dina nan gaba Insha'allah
DUK INDA TA FADI.
Poster din novel din zaku ga guy din frnd dina ne sosai da sosai,yanda muke dashi yasa na sashi a poster University daya mukayi class dinmu daya.labarin ba nasa bane kar readers kuce labarin saneπŸ˜‚ sai na huta sosai zan fara New novel.

Ku karba readersπŸ‘ŠπŸ‘ŠπŸ‘ŠπŸ‘ŠπŸ‘ŠπŸ‘Š 1 blow irin na Amana nayi wa ko wacce.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜πŸ˜πŸ˜πŸ˜ Am gonna miss u all 😭😭😭😭 Bye.

πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘πŸ‘



AsmaBaffa

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment